2025-02-01@04:07:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 107
«Yan bindiga»:
CMG Ya Gabatar Da Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara Cikin Nasara
Iran ta mayar da martani game da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na tilastawa Falasdinawan Gaza komawa kasashen Jordan da kuma Masar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya yi watsi da shirin na Trump a wani sako a kan shafinsa na X. Baghaei ya ce, kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ta...
Tinubu ya gode wa shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, da shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka, Akinwumi Adeshina, saboda ƙoƙarinsu na samar da karin wutar lantarki a Afirka. Ya kuma ce yadda masu zuba jari ke gamsuwa da shirye-shiryen gwamnatinsa ya sa aka samu jarin dala biliyan shida a ɓangaren samar da makamashi a shekarar da...
Sabbin waɗanda aka rantsar sun haɗa da Hon. Sanusi Khalifa, babban mashawarci kan albarkatun ƙasa; Hon. Haladu Ayuba, Mai Bada shawara kan daidaita ɗabi’un jama’a; Hon. Jidauna Tula, babban shawarcesa kan harkokin Shari’a da kuma Hon. Adamu Bello da aka sanya a matsayin babban mashawarci a ɓangaren kasuwanci da masana’antu. Sauran sun haɗa da...
Bugu da ƙari, dokar za ta bai wa direbobin da ke jigilar fasinjoji damar kula da yanayin fasinjojin da za su ɗauka ta yadda in sun ga yara dole sai sun tantance wanene ya ɗaukosu kuma meye nasabarsu dukka da nufin daƙile satar yara da safararsu. Sannan gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokar...
Babban rukunin gidajen rediyo da telabijin na kasar Sin (CMG) ya yi wani nuni na musamman na fitilu a jikin wasu manyan gine-gine guda 2 na kasar Afirka ta Kudu da na kasar hadaddiyar daular Larabawa ta UAE. Nunin fitilun da aka yi a jikin ginin “The Leonardo”, gini mafi tsayi a kasar Afirka ta...
Aragchi Yace Duk Wani Harin Da Aka Kaiwa Cibiyoyin Nukliyar Kasar Iran Hakan Wata Musiba ce Ga Yankin Asiya Ta Yamma
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas...
Gwamnatin kasar News Zealand ta fitar da sabbin sharudda ga yahudawan HKI masu neman Visar Shiga kasar, daga ciki sai sun bada tarihin aikin sojen da suka yi a cikin kasarsu. Takaita irin yahudawan da zasu shiga kasashen duniya bayana yakin Gaza dai, zai sanya wani tunani a zukatan yahudawan HKI musamman wadanda suka shiga...
Dan Majalisar Dattijan Amurka Ya Mayar Da Martani Kan Kalaman Trump Na Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da...
Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da...
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da...
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a...
Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Kungiyar Rapid Support Forces sun kai hari kan matatar mai ta Al-Jili da ke birnin Khartoum na kasar Sudan Mayakan kungiyar dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan matatar mai ta Al-Jili da ke birnin Khartoum Bahri, wadda ita ce matatar mai mafi girma a kasar Sudan, wadda take...
Sulhu da ‘Yan Bindiga Ya Fi Zubar Da Jinin Ɗan Adam A Kaduna – Uba Sani
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu gagarumar nasara wajen yaki da miyagun laifuka, inda ta kama wasu da ake zargi da aikata manyan laifuka da dama. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Salman Dogo Garba ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan Bompai Kano. ...
Kungiyar masu ruwa da tsakin masana’antu a fannin mai ta Najeriya NEITI da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, na kokarin kwato kusan dala biliyan shida da kuma wani naira biliyan 66 da gwamnatin tarayya ke bin gwamnatin tarayya bashin. Sakataren zartarwa na hukumar Mista Orji Ogbonnaya Orji, wanda ya...
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da...
Haka kuma, an naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta. Ya samu ƙwarewa a fannonin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen ƙara ƙarfin tsarin kuɗi na jihar. An kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai...
Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya bayyana damuwarsa game da matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka na dakatar da taimakon kasashen waje daga Amurka yayin da sabuwar gwamnatin Amurka ke aiwatar da sabbin manufofinta na ketare, kamar yadda mai magana da yawun Guterres ya bayyana. “Ya yi kira da a yi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Akan ce ‘Noma tushen arziƙi’ kuma mutane da dama za su iya bayar da labarin da ke tabbatar da hakan; domin kuwa ko ba komai idan mutum ya samu abinci ya ci ya ƙoshi babban arziƙi ne. Wasu ’yan Najeriya kan shuka kayan abinci a unguwanninsu don sama...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gudanar da taron tattaunawa da wakilan baki kwararru wadanda ke aiki a kasar da wadanda suka samu lambar yabo ta Abota ta Gwamnatin Sin. Yayin taron wanda ya gudana jiya Lahadi, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, Li Qiang ya kuma mika gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta...
Shettima ya yi alkawarin cewa, bisa umarnin shugaban kasa, gwamnati za ta hada hannu da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kan hanyoyin da hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa, da ma’aikatun sufuri na tarayya da na Jihohi za su hada kai don dakile yawaitar hadurran tankar...
MOFA: Ya Kamata Amurka Ta Daina Siyasantar Da Batun Gano Inda COVID-19 Ta Bulla
Na’im Kassim Ya Dora Wa Amurka da Faransa da MDD alhakin Abinda Zai Faru Idan Isra’ila Ba Ta Janye Daga Labanon Ba
Abinda Ya Faru A Lebanon Nasara Ce Akan Isra’ila Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi na farko bayan cikar kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki da HKI. A jawabin nasa sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa a lokuta da dama sun yi tunanin mayar da martani akan keta tsagaita wutar...
A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da katin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a matsayin martani ga abokai a jihar Iowa ta kasar Amurka, inda ya ce, Sin da Amurka na da manyan muradun bai daya, da damar yin hadin gwiwa, kuma suna iya zama abokan...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi ƙarin haske dangane da barazanar harin ’yan ta’adda da ta yi gargaɗin aukuwarsa a bayan nan. Da yake yi wa manema labarai jawabi, Kwamishinan ’Yan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya ce sun ɗauki matakan da suka dace biyo bayan barazanar harin ’yan ta’adda musamman a yayin taron...
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani mutum da matarsa da dansa da wasu mutane biyu a Bwari da ke babban birnin tarayya, Abuja (FCT). LEADERSHIP ta tattaro cewa, an kai harin ne a unguwar Chikakore da ke Kubwa da misalin karfe 12 na safiyar ranar Litinin. Shugaba Xi Ya Yaba Da Ci Gaban...
A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar ta samu ci gaba mai inganci wajen zurfafa raya zamanantarwarta a cikin “yanayoyi masu sarkakiya da kalubale” a tsakanin watanni 12 da suka gabata. Ya furta hakan ne yayin gudanar da wata kasaitacciyar liyafar maraba da sabuwar shekara ta kasar Sin. Ana Shirin...
Ya kuma yi gargadi cewa rashin ɗaukar matakai na gyara tattalin arziƙi zai ci gaba da haifar da asara mai yawa, inda tallafin man fetur da na musayar kuɗaɗe ke laƙume kashi biyar cikin ɗari na GDP na ƙasar. Wannan, in ji shi, babban ƙalubale ne ga cigaban tattalin arziƙin Nijeriya.
Sakamakon farko na zaben shugaban kasa da babbar hukumar zaben kasar Belarus ta fitar da jijjifin safiyar yau Litinin ya nuna cewa, Alexander Lukashenko ne ya lashe zaben, inda ya samu kashi 86.82 cikin dari na adadin kuri’un da aka kada. A bisa dokar kasar ta Belarus dai, ana ayyana duk dan takarar shugaban kasa...
Kwamishinan ya yi ikirarin cewa ayyukan Madakin Gini na nuna rashin jajircewa ga waɗanda suka zaɓe shi. “Madakin Gini ya bayyana cewa ba ya cikin waɗanda suka goyi bayan shi da suka zabe shi. Saboda haka, babu dalilin ci gaba da kasancewarsa a wannan muƙamin idan ba ya wakiltar buƙatun mutanen Dala. Da zarar shugabannin...
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba da irin gudunmawar da darikar Tijjaniyya ke bayarwa wajen samar da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmin kasar nan. Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron Mauludin bana 2025 na marigayi Sheikh Ibrahim Nyass, jagoran darikar Tijjaniyya...
Jagoran kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa: A shirye suke su tunkari duk wani harin Amurka kuma ya gargadin sojojin haya Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya tabbatar da cewa: Amurka ta yi amfani da dukkan karfinta wajen tallafawa haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma kokarin murkushe al’ummar Falasdinu, yana mai jaddada...
Ana zargin ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun ɓullo da sabon salon cin hanci inda suke tatsar jami’o’i da sauran manyan cibiyoyin ilimi na tarayya. Kafar yaɗa labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa ’yan majalisar suna barazana ga kowane shugaban jami’a ya ba su cin hancin Naira miliyan takwas kafin sun amince da kasafin...
Tinubu Ya Isa Tanzania Don Halartar Taron Makon Makamashi Na Afrika
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ci-gaban zamani ya zo da sauye-sauye da dama a fannonin rayuwa daban-daban ciki har da kasuwanci. A yanzu hanyar sadarwa ta zamani, ko intanet, tana taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa da ɓangarori da dama. Tuni ’yan Najeriya da dama suka yi balaguro suka...
Wani fashewa da ake zargin daga abubuwan fashewa ne da wani mai hakar zinariya ya ajiye a Sabon Pegi, ƙaramar hukumar Mashegu a Jihar Neja, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda da jikkatar mutane shida a ranar Lahadi. Rahotanni sun nuna cewa Yushau, wani mai haƙar haƙar zinariya, ya ajiye abubuwan fashewar ne a gida...
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi...
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar UYemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi, ya yabawa mutanen kasar kan jajircewarsu wajen yakar makiya Amurka da HKI da kuma saudiya, har zuwa nasarar da suka samu a kansu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Al-huthi yana fadar haka a yau Lahadi, a wani jawabin da aka watsa...
Sojojiun HKI A Kudancin Kasar Lebanon Sun Kashe Mutane Fararen Hula Wasu Kuma Suka Ji Rauni A Yau Lahadi
Ministan kiwon lafiya na kasar Lebanon ya bada sanarwan cewa sojojin HKI a kudancin kasar sun kashe fararen hula 15 sannan wasu 83 suka ji rauni a safiyar yau. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana cewa mutanen kudancin kasar Lebanon sun komawa gidajensu da suke kudancin kasar kan iyaka da...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda...
’Yan bindiga sun kai hari garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta. Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta, Alhaji Auwalu....
An sace aƙalla mutum 22 a wasu sabbin hare-hare da ake zargin ’yan bindiga da kaiwa a ƙauyen Kugauta da ke Kusheka da kuma Kitanda da ke Gashere a masarautar Kumana da ke Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna. Wani mazaunin yankin, Emmanuel Johnson, ya bayyana wa Aminiya cewa hare-haren sun afku ne da misalin...
CMG Ya Gabatar Da Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin A Amurka Da Myanmar Da Indonesia Da Habasha Da Faransa Da Jamus Da Paraguay
Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an...
“Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni. “Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara...
Ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna (PPRO), DSP Mansir Hassan ba da aka tuntube shi har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a rundunar arewaci ta rundunar sojin ’yantar da al’ummar Sinawa wato PLA, gabanin Bikin Bazara. Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin kolin JKS kuma shugaban hukumar koli mai kula da ayyukan soji (CMC), a madadin kwamitin kolin da hukumar CMC, ya mika gaisuwar sabuwar...
Mutane Na Yawan Tambaya Ta Yaushe Zan Yi Aure – Firdausi Yahaya
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar...