2025-04-16@03:42:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 872

«Karagwal»:

    Jami’in ya ce, barazanar da Amurka ke yi game da kara tsananta matakin da za ta dauka, kuskure ne dake nuna muguwar aniyarta ta dakile moriyar sauran kasashe, kuma tabbas Sin ba za ta amince ba ko kadan.   Kasar Sin ta sake nanata ra’ayinta cewa, ba wanda zai ci gajiyar tayar da zaune tsaye...
    LEADERSHIP tana karrama mutane da ƙungiyoyin da suka taka rawar gani a fannoni daban-daban kamar gwamnati, kasuwanci da al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motocin kamfanin sufurin Borno Express na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane 18 kowacce. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Litinin, bayan wani fashewa mai ƙarfi a harabar garejin....
    Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta Jihar Katsina sun ce ’yan bindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara. Maharan sun kuma kashe akalla mutum shida, inda suka sake kai wani hari a yankin Ƙaramar Hukumar Ɗandume ta jihar. Rahotanni sun ce...
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin...
    Hakazalika, Lin Jian ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su bi ka’idojin yin shawarwari da samun ci gaba da more fasahohi da juna, da kiyaye bin ra’ayin bangarori daban daban, da kin amincewa da ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD...
    Jam’iyyar Labour (LP) ta yi barazanar dakatar da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, da ɗan takarar shugaban kasa na 2023, Peter Obi, idan ba su daina abin da aka kira “aikin da ba a goyon baya” ba. Wannan barazanar ta fito ne bayan taron kwamitin zartarwa na Jam’iyyar (NEC) da aka gudanar a Abuja, inda...
    Fulham ta kawo ƙarshen wasanni 26 da Liverpool ta yi a jere ba tare da rashin nasara ba a gasar Firimiyar Ingila ta wannan kakar. Fulham ta yi nasarar doke Liverpool da 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31. Liverpool ce ta fara zura ƙwallo a ragar Fulham ta hannun Mac...
    Aƙalla mutane 30 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sun mutu a wani mummunan hari da kungiyar ‘yan sa kai ta cikin gari ta yi a yankin Dansadau na karamar hukumar Maru, jihar Zamfara. Kamar yadda wani masani kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana daga bayanan sirri, harin ya faru ne...
    Da ya ke magana kan ziyarar tawatar NBTE, Rector ɗin ya ce aikin sahalewa na da matuƙar muhimmanci domin gano irin ƙoƙari da azamar makaranta a cikin shekaru biyar da suka gabata da nufin tabbatar kayan koya da koyarwa da malamai suna nan kan tsarin da aka amince da tafiyar da su tun da farko....
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yada wasu hutunan bidiyo wanda yayi kama da na jiragen yakin kasar ne kan kasar Yemen, inda suka yi ruwan boma bomai a kan su a matsayin yan ta’ada wadanda suke shirin yakar Amurka, amma daya baya shaidu sun ta tabbatar da cewa taron ta yan kasar ta Yemen...
    Dakarun Soji  Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai. Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa. Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar...
    Dakarun Soji  Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai. Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa. Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar...
    A bisa wannan dalili ne yasa akwai bukatar mutane su rungumi fannin noman Aya, duba da cewa; hanya ce ga wanda ya zuba jarinsa a fannin, zai iya kara samar wa da kansa kudaden shiga. Sai dai, akasari an fi yin nomanta a Arewacin Nijeriya, musamman ma kuma a Jihar Katsina. Haka zalika, fannin na...
    Ya kuma bukaci jama’a musamman mazauna Damaturu da su kwantar da hankulan su, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.   Abdulsalamu ya bada tabbacin aniyar gwamnati na wanzar da zaman lafiya da tsaro, yayin da ya yi gargadi kan yada labaran karya da ka...
    Gwamnan ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan tare da addu’ar Allah ya karvi ibadu. “Ina addu’ar Allah ya ci gaba da ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da hadin kai a tsakani. Za mu ci gaba da shaidar bukukuwan Sallar. “Ina kuma gode wa shugabannn addininmu bisa koyar da...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana sharuddan da Tehran ta gindaya na ci gaba da tattaunawa kan shirinta na nukiliya, yana mai jaddada aniyar kasar ta fuskar diflomasiyya tare da tsayawa tsayin daka kan muradun kasa. Da yake magana a wani taron sabuar shekarar Nowruz tare da jami’an Iran, jakadu, da wakilan kasa...
    Gwamnatin kasar Sin ta yi kakkausar suka da bayyana adawarta ga matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya.” A cikin wata sanarwar da ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin na Amurka, wanda ya kasance daukar mataki bisa radin kai, da kuma kariyar cinikayya da cin zarafin tattalin arziki. Sanarwar ta kara da...
    Sakatare janar na majalisar dinkin duniya ya ce ba wanda zai ci ribar yakin cinikayya a yayin da ake ta cacar baka kan harajin fito da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa duniya.  Antonio Guitess ya yi wannan gargadin ta bakin kakakinsa inda ya yake bayyana cewa, “ba wanda ke yin nasara a yakin...
    Ta kuma bukaci Amurka da ta daina amfani da harajin fito a matsayin makami don dakile ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, da kuma tauye hakkin samun halaltacciyar ci gaba na al’ummar Sinawa. (Mohammed Yahaya)     Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu nay au zai yi magana kan cewa “Amurka ba zata taba zama mai sulhuntawa tsakanin HKI da Falasdinawa ba” wanda ni tahir amin zan karanta. A dai dai lokacinda rikicin gaza ya zama matsalar ta duniya a halin yanzu, da dama daga cikin masana suna ganin gwamnatin Amurka...
    Wakiliyar musamman ta MDD akan Falasdinu Francesca Albanze ta sanar da cewa; Bayanan da jaridar ” New York Times”  masu kunshe da hotuna na laifin kashe masu aikin ceto a Rafah, suna dakile riwayar Isra’ila.” Wakiliyar ta MDD ta fada wa tashar talabijin din Aljazeera cewa, abindaya faru kisan kiyashi ne’ sannan ta kara da...
    Direba da kwandastan motar bas sun tsere domin tsira da rayukansu, inda suka bar fasinjoji a ciki yayin da wata motar bas ta BRT ta kama wuta a Maryland da ke Jihar Legas da safiyar ranar Asabar. Majiyar Channels TV da ke wajen da lamarin ya faru, ta ce motar ta taso ne daga yankin...
    Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani. Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu...
    Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) da asusun lamuni na duniya (IMF) sun nuna damuwa game da tabarbarewar tattalin arziki daga sabbin harajin da gwamnatin Trump ta laftawa duniya, suna masu gargadin cewa hakan zai iya kawo cikas ga harkokin kasuwanci da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya. A cikin wata sanarwa da ta fitar, WTO...
    Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda...
    Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda...
    Kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, ta shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka na kakaba harajin kwastam kan abokan cinikayyarta. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta ce, harajin kwastam da Amurka ta kakaba, ya matukar take halaltattun...
    Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio tattaunawa da manema labarai yayin da ’yar majalisar ta shigar da ƙara a gaban kotu. Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙorafin da lauyan da ke...
    Kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, ta shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka na kakaba harajin kwastam kan abokan cinikayyarta. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta ce, harajin kwastam da Amurka ta kakaba, ya matukar take halaltattun...
    An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP). Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito...
    An kashe wani sufeton ɗan sanda a yayin wani kwanton ɓauna da wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a kwalejin horar da rundunar ’yan sanda (PMFTC) Camp Limankara, Gwoza a Borno.  Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa majiyar Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 0600 a ranar...
    Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci...
    Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a kasashen Turai ko Geneva Ali Gahraini ya yi tir da amincewar da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta yi da zargin kasar ta take hakkin bil’adama a taronta na baya-bayan nan abirnin Geveva. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baraini yana cewa, hukuncin da...
    Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini tare da shan alwashin ramuwar gayya game da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta musu kankan kayayyakin da ake shigowa da su kasar.  Gwamnatoci da kamfanoni da dama sun sanar da matakan gaggawa na samar da matakan dakile matakin da Amurkan ta dauka kansu....
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar. A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi,...
    Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar. Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce wannan shiri ne da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito,...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Alhamis ta lalata wani sashe na shahararren gidan Ado Bayero da ke ƙofar Nassarawa a Kano. Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a hawa na tara na ginin da cibiyar Jami’ar Northwest University take. Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Ruwan sama...
    Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka...
    Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a...
    “A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya fara rangaɗin wuraren haƙar ma’adanai da masana’antu, inda ya fara ziyarar aiki a wani kamfani mai zaman kansa na Comet Star Industry da ke Ƙaramar Hukumar Anka.   “Ma’aikatar, mallakin Prince James Uduji OON, tana sarrafa kusan tan 1,000 a kullum. Tana da cikakkun kayan aiki da sabbin...
    An shiga firgici da safiyar Alhamis  ɗin nan, bayan wani kwale-kwale na kamfanin Lagos Ferry Services (LAGFERRY) ya kama da wuta a tashar jirgin ruwa ta Ipakodo da ke Ikorodu, a Legas inda mutane da dama suka jikkata. Majiyoyi sun ce tashin wutar ta haifar da wata babbar gobara da ta tashi daga injin jirgin...
    Jami’ar Bayero Ta Kaddamar da shirin amfani da adaidaita Sahu wajen zirga zirga a Jami’arA wani gagarumin yunkuri na bunkasa zirga zirga da walwalar dalibai, Shugaban Jami’ar Bayero Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya kaddamar da shirin amfani da babura masu kafa uku ko adaidaita a harabar jami’ar a hukumance. Wannan yunƙurin na nufin samar...
    Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga har suka yi ƙarfi. Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye...
    Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su.   Ya kara da cewa, masu garkuwa da...
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar...
    Wani rikici tsakanin matasan ƙungiyoyin Sara-Suka ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku a unguwar Yantifa da ke Jos ta Arewa, a Jihar Filato. Shaidu sun ce matasan sun far wa juna da makamai irin su adduna, wanda ya sa mazauna yankin tserewa don tsira da rayukansu. Tinubu ya yi ta’aziyyar...
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in...