2025-02-21@14:23:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 401
«Makaranta»:
Kungiyoyin farar hula masu yaki da zazzabin cizon sauro, rigakafi da abinci mai gina jiki (ACOMIN), reshen jihar Taraba, ta koka kan matsalar karancin kayan gwajin cutar kanjamau a jihar. Shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Muhammad Danburam ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan hukumar yaki da cutar kanjamau...
Makiyaya sun koka bisa abin da suka kira tsangwama da tsana da wasu manoman tabar wiwi ne suke nuna musu tare da yi musu barazanar ƙone gidajensu a inda suke zaune shekaru aru-aru. Makiyaya Fulani sun yi ƙorafi ne bayan manoman tabar wuri sun kafa musu ƙahon zuƙa a inda suke zaune a yankin Oja-Badun...

Amurka ta kakaba wa babban mai shigar da kara na kotun ICC takunkumi kan binciken laifukan yakin Isra’ila
Amurka ta kakaba takunkumi kan babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa dangane da binciken da kotun ta ICC ke yi kan yiwuwar aikata laifukan yakin Isra’ila a Gaza da sojojin Amurka. Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta sanar da kakabawa Karim Khan takunkumi a matsayin martani ga umarnin shugaba...

Kasuwannin Kayayyakin Da Ake Yawan Sayen Su A Lokacin Bikin Bazara Goma Sun Inganta Kashe Kudi Sama Da Yuan Biliyan 1.6
Yau Alhamis, ma’aikatar kula da kasuwanci ta Sin ta sanar cewa, tun bayan kaddamar da bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, manyan ayyukan da suka shafi bikin sun sa yawan kudin da aka kashe ta intanet da kuma a zahiri ya zarce yuan biliyan 1.6. An ba da rahoton cewa, bikin sayen kayayyakin...
An yi nasarar watsa liyafar bikin fitilu na gargajiya na Sin na 2025 ta CMG jiya Laraba a mabambantan dandamali, lamarin da ya samu yabo sosai. Alkaluman masu kallo ta talabiji da sauran kafofi na zamani sun karu sosai fiye da bara. Kididdiga ta nuna cewa, an kalli liyafar da aka watsa kai tsaye ta...
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100...
Wata ɗalibar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi, Faith Aluko Adesola, ta rasa ranta bayan da wata babbar mota ta murƙushe ta. Jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, Alhaji Rabi’u Muhammad ne, ya tabbatar da faruwar lamarin. Majalisun Tarayya sun amince da kasafin kuɗin N54.9trn na 2025 Kwastam ta lalata magungunan...
A ranar Talatar da ta gabata, Jakadan kasar Sin a Amurka, Xie Feng ya jaddada cewa, kakaba haraji ko yakin ciniki ba za su iya magance matsaloli ba, ballantana kuma kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 20 da kafuwar babbar kungiyar ‘yan kasuwar kasar Sin da...
Kalaman Trump Marasa Kan-gado Game Da Gaza Za Su Kara Tsananta Halin Da Ake Ciki A Gabas Ta tsakiya
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa. A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara. Tashar talabijin din Aljazira ta...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bankaɗo ma’aikatan bogi 2,363 da ke karɓar jimillar N193,642,097.19 a kowane wata bayan gudanar da tantancewar ma’aikatan gwamnati. Gwamna Dauda Lawal ya kafa kwamitin tantance ma’aikata a watan Agustan bara don tabbatar da biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000. Kakakin gwamnan, Sulaiman Idris, ya bayyana cewa binciken ya nuna akwai ƙananan...

Shugaban kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Son Shiga Yaki Amma Tana Shirye Wajen Fuskantar Barazana
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya karbi bakuncin tawaga daga kasar Saudiyya karkashin jagorancin Sheikh Nuhu Idris Fallata shugaban hukumar Saudiyya mai kula da ciyar da Alhazai. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, tawagar ta zo ne domin ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa da dansa ya rasa. Sheikh Fallata ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda...
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: ‘Yan Sudan miliyan 30 ne suke bukatar agaji kuma lamarin yana kara ta’azzara Mataimakin shugaban ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Edmore Tondlana ya yi gargadin cewa: Al’amura a Sudan suna kara tabarbarewa, yayin da ake ci gaba da fama da tashe-tashen hankula,...
Rundunar sojin saman Ukraine, ta ce jirage marasa matuƙa 140 ne suka kai mata hare-hare cikin dare. Hare-haren sun fi ƙamari a yankunan Odessa da Kharkiv, a cewar sojojin. Rundunar sojin saman ta kuma ce ta samu nasarar kare wasu hare-haren daga ciki, yayin da ta tabbatar da kakkaɓo 85 daga cikin jiragen. Hakan na...
Gwamnatin jihar Sokoto ta ce tana kokarin samar da sauki da kuma tsarin zuba jari mai inganci wanda zai iya karfafa gwiwar masu zuba jari daga kasashen waje da na cikin gida zuwa jihar. Wakilin Gwamnatin jiha kuma shugaban karamar hukumar Wamako Alh. Umar Ahmad Dundaye ya bayyana haka ne a wajen rabon magunguna...
Dakarun Operation Fansan Yamma sun dakile ayyukan ta’addanci a jihohin Zamfara da Sokoto daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2025. A cewar wata sanarwa da kodinetan cibiyar yada labarai na Operation Fansan Yamma Laftanar Kanar, Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce harin ya yi sanadin fatattakar ‘yan ta’adda da dama da suka...
Ƙungiyar malamai ta NUT-FCT da ma’aikatan ƙananan hukumomi na NULGE sun fara yajin aiki na dindin a yau Alhamis, sakamakon gazawar shugabannin ƙananan hukumomi wajen aiwatar da sabon albashi mafi ƙarancin na ₦70,000 da aka amince da shi tun Disamba 2024. Ƙungiyoyin sun koka cewa duk da cewa sauran ma’aikatan FCT sun fara karɓar sabon...
Ƙungiyar malamai ta NUT-FCT da ma’aikatan ƙananan hukumomi na NULGE sun fara yajin aiki na dindin a yau Alhamis, sakamakon gazawar shugabannin ƙananan hukumomi wajen aiwatar da sabon albashi mafi ƙarancin na ₦70,000 da aka amince da shi tun Disamba 2024. Ƙungiyoyin sun koka cewa duk da cewa sauran ma’aikatan FCT sun fara karɓar sabon...
Hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS) ta sanar da wani gagarumin shiri na kara yawan kudaden shiga na jihar zuwa sama da Naira biliyan 100 nan da shekarar 2025. Shugaban hukumar Dr. Zaid Abubakar ne ya bayyana hakan a yayin da hukumar ke bitar ayyukan hukumar na shekarar 2024 da kuma tsare-tsarenta na...
Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano Ambasada Haruna Zago ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Ɗaya daga cikin ma’aikatan hukumar ne ta tabbatar da haka Hausa rasuwar Haruna Zago a asibiti. A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2023 Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa Haruna Zago a matsayin Shugaban...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da barazanar da Isra’ila da Amurka ke yi kan batun musayar fursunoni. Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya fada cewa Isra’ila tana kaucewa aiwatar da wasu tanade-tanade na yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” yana mai gargadin cewa ba za a sako mutanen da ake garkuwa da su ba...
Kasashen Iran da kuma Turkmenistan sun kudiri anniyar karfafa alakar dake a tsakaninsu a bangarori daban-daban, in ji shugaba Masoud Pezeshkian. A wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen Turkmenistan Avazgeldyevich Meredov a birnin Tehran, shugaban na Iran ya ce “An bayar da umarnin da suka wajaba ga hukumomin da abin ya shafa...
A yau Laraba, kafar yada labarai ta CGTN ta hada gwiwa da tashar watsa labarai ta lardin Heilongjiang na kasar Sin ta kamfanin CMG, wajen shirya wani bikin musayar al’adu na kasa da kasa, wanda ya shafi gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya dake gudana a Harbin, gami da bikin fitilu na gargajiyar kasar Sin....
Taro kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI da ya gudana a Paris na Faransa, ya ja hankalin duniya. Masu rattaba hannu 61 ciki har da Faransa da Sin da India, sun fitar da wata sanarwa cewa za su nace wajen raya wannan fasaha bisa ka’ida ba tare da rufa rufa ba, kuma ta kowane bangare....
Tsohon Hadimin Shugaban Ƙasa a fannin Ƙimar Ƙasa da Zamantakewa, Fela Durotoye, ya bayyana yadda ya ƙi karɓar tayin cin hancin Naira biliyan biyar yayin da yake aiki a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Yayin da yake jawabi a wani taro a Abuja, Durotoye ya ce wani jami’i da ya ce shi limamin coci ne, ya...
Alkaluma daga hukumar kula da jigila da sayen kayayyaki ta kasar Sin sun nuna cewa, darajar jigilar kayayyakin jama’a da aka yi a kasar Sin a shekarar 2024, ya karu da kaso 5.8 zuwa yuan triliyan 360.6, kwatankwacin dala triliyan 50.28, idan aka kwatanta da 2023. Zuwa karshen 2024, kasar ta samar da cibiyoyi 151...

Jagoran Ya Ce: Fitowar Mutane A Ranar 11 Ga Watan Fabrayru Alamace Ta Hadin Kan Kasa Sannan Jawabi Ga Barazanar Da Kasar Take Fuskanta
A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama...

Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Bisa Matakin Kara Harajin Kwastam Kan Ma’adanan Karfe Da Goran Ruwa Ba
Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Bisa Matakin Kara Harajin Kwastam Kan Ma’adanan Karfe Da Goran Ruwa Ba
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya miƙa wa sabon Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi sandar sarauta, a wani biki da aka gudanar a filin wasa na garin Bama. A yayin bikin, Gwamna Zulum ya yi alƙawarin kammala titin Maiduguri zuwa Banki domin bunƙasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya, Kamaru da Chadi. Dokokin gyaran...
Dokokin Gyaran Haraji sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi a tsakanin ’yan majalisar. Tun da farko, an gabatar da ƙudirorin guda huɗu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar, amma an haɗe su zuwa guda ɗaya domin sauƙaƙa nazari a kansu. An yi zanga-zanga kan hare-haren...
Wakilin LEADERSHIP Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi
Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace...
NAFDAC Ta Rufe Shaguna Da Wuraren Ajiyar Magunguna Marasa Inganci A Legas
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja. Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja. Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data Noman rani ne zai...
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya...
Majalisar Wakilai ta buƙaci Hukumar Kula da Sadarwa (NCC) ta janye ƙarin kashi 50 na kuɗin waya da data da ta amincewa kamfanonin sadarwa su yi. Wannan dai na zuwa ne a yayin da ɗan majalisar daga Jihar Bayelsa, Oboku Oforji ya gabatar da ƙudirin kan lamarin. Majalisar ta ce ƙarin bai kamata ba a...
Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan...
Kasar Aljeriya ta yi marhabin da shirin Iran na gudanar da taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a zirin Gaza, wanda shugaban na Amurka ya ce yana son karbe iko tare da raba al’ummar kasar baki daya. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya gabatar da shawarar gudanar da wani zama na...
Wakilin LEADERSHIP Hausa Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi

Jaridar Telegraph Ta Ce; Shugabannin Sojojin Iran Sun Bukaci Jagora Da Ya Soke Fatawar Haramci Kera Makamin Nukiliya
Jaridar Daily Telegraph ta watsa labarin cewa: Shugabannin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Khamenei da ya janye fatawarsa kan haramcin mallakar makamin nukiliya Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta watsa rahoton cewa: Shugabannin sojojin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da haramcin...
Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba...
Ya ce: “A baya, muna da wasu hukumomi da ke ƙayyade farashin kayan abinci, amma domin kasuwanci na ’yanci da bunƙasa harkokin noma, gwamnati ba ta ga dacewar ci gaba da hakan ba. “Yanzu abin da gwamnati ke yi shi ne ta tabbatar da cewa ana samar da isassun kayan abinci, domin idan abu...
An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa. Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya?...
“Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin. “A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin. “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta...

’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A...
Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban sun ce, dole ne kamfanin ya samar da mafita mai dorewa tare da maido da wutar lantarki a tashar wutar lantarki ta ‘Kwara Poly feeder’ da ke rarraba wutar ga al’ummomin yankin.
Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa...