2025-04-25@04:49:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2588
«yankin Somaliland»:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Najeriya ta amince kuma ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki. Hakan ya biyo bayan tsoma bakin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi wanda ya roƙi shugaba Bola Tinubu a madadin maniyyatan ta hannun Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON. Ficewar Kawu a jam’iyyarmu zai kawo zaman lafiya – Shugaban NNPP na Kano An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aure Hukumar NAHCON a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh, ta dage cewa ɓullo da hada-hadar kuɗi ta amfani da kati zai shafi shirin hukumar na gudanar da ayyukan hajjin 2025. Shugaban ya damu matuƙa da cewa amfani da katin banki na dole da...
Sabbin ‘yan sama-jannatin da aka tura, za su gudanar da gwaje-gwaje da bincike game da yanayin rayuwa a sararin samaniya, da kimiyyar karamar fizgar kasa ko jazibiyya (micro-gravity physics) da sabbin fasahohin sararin samaniya. Kazalika, za su kuma yi tafiye-tafiye mabambanta a sararin samaniya don kakkafa shingayen kariya daga baraguzai da tarkacen sararin samaniya, da kuma girkewa da dawo da na’urorin da aka makala a wajen tashar. Ya zuwa yanzu dai, ‘yan sama jannatin kasar Sin 26 ne suka yi nasarar zuwa sararin samaniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Tsoffin kwamishinoni na Jihar Kano kamar su Hon. Diggol, Hon. Abbas Sani da Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Baffa Bichi su ma sun koma APC. Hakazalika, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada wanda ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADP a zaɓen 2023, ya sauya sheƙa zuwa APC. Ana kallon wannan sauya sheƙar a matsayin wani babban tagomashi ga jam’iyyar APC musamman a Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano, ta mayar da martani da nuna jin daɗi ga ficewar Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, zuwa Jam’iyyar APC kwanan nan, inda ta ce ficewarsa za ta kawo zaman lafiya a jam’iyyar. Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan Sanata Kawu Sumaila ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC. An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aure Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni Da yake zantawa da manema labarai a Kano, Shugaban NNPP na Jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya yi watsi da muhimmancin tafiyar da jam’iyyar tare da Kawu, inda ya bayyana shi a matsayin, “Wani mai taurin kai” wanda kasancewarsa a...
Bugu da kari, masharhanta da dama na ganin karin harajin fito ba zai warware matsalar da Amurkan ke ciki ba. Ko shakka babu idan Amurka na son ta tunkari wannan kalubale bisa gaskiya, sai ta sauya tsarin ilimi, ta kuma bunkasa fannin kirkire-kirkirenta, da daga martabar masana’antu, da zuba jari na dogon lokaci a fannin, ba wai matakin jeka-na-yika na gajeren lokaci, irin wannan na baiwa kasuwa kariyar cinikayya ba. A daya hannun kuma baya ga illar da wannan kare-karen haraji ya haifar, matakan kasashen da lamarin ya shafa na ramuwar gayya na iya haifar da hauhawar farashi na gaggawa, da jefa tattalin arzikin sassa daban daban cikin halin komada, a maimakon fatan da gwamnatin Amurkan ke yi na...
Kafafen watsa labarun HKi sun amabci cewa daya daga cikin sojojinsu ya halaka a Gaza, yayin da wasu 7 su ka jikkata. Kafafen watsa labarun na HKI sun ce, Harin da aka kai wa sojojin ya kunshi harbi daga kwararren maharbi da kuma harba makamin dake fasa motoci masu sulke. An ga jiragen sojan mamaya suna tsananta hare-hare a yankin da lamarin ya faru, saboda su sami damar dauki gawar sojan nasu da kuma wadanda su ka jikkata. Tashar talabijin ta 12; ta HKI ta ambaci cewa;Ana gwabza fada ne a arewacin Gaza, kuma mazauna yankin suna cewa sun ga jiragen sama masu yawa suna kai da komo. Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare masu yawa a yankin Arewacin Gaza,...
Jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-haren a kan biranen San,a,Sa’adah da kuma Hudaidah na kasar Yemen. Kamfanin dillancin labarun “Saba’a” na kasar Yemen ya nakalto cewa sojojin na Amurka sun kai hare-hare har sau uku a dutsen Naqam, wanda yake gabashin birnin San’aa. Kamfanin dillancin labarun na “Saba’a” ya kuma ce, jiragen yakin Amurka din sun kai hare-haren ne a tsakanin marecen jiya Laraba da kuma safiyar yau Alhamis. Daga cikin wuraren da aka kai wa harin jiya da marecen da akwai Sahlin dake karamar hukumar Ali-Salim. Sau 6 Amurkan ta kai wa yankin hare-hare. Da safiyar yau Alhamis kuwa jiragen yakin na Amurka sun kai hare-hare a gundumar Sa’adah. Wasu yankunan da su ka fuskanci hare-haren su ne,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A daidai lokacin da sabani yake yin tsanani a tsakanin India da Pakistan, bayan wani hari da aka kai a Kashmir da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 26, ministan tsaron kasar Pakistan Khajah Asif ya ce; matukar India ta keta hurumin kasarsa, to kuwa za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani. Minista Khajah Asif ya kuma gargadi kasar ta India da ta guji keta hurumin kasar Pakistan. Asif ya kuma bukaci India da ta gudanar da bincike akan harin da aka yi a ranar Talata a yankin Kashmir, kuma ta nesanci yin wani abu wanda zai jefa yankin cikin yakin da ba a san yadda karshensa zai kare ba. Haka nan kuma ya ce; Tushen matsalar tana nan a...

Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
Ya ce, “Muddin muna da kwarin gwiwa, da karfin goyon bayan juna da hadin kai, za mu kai ga kawar da manufofi masu illa, da wanzar da daidaito da ci gaba a manufofin jagoranci a fannin kare yanayi da samar da ci gaba. ” (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ban da haka, yadda gwamnatin Trump ba ta da tabbas a kan manufofinta na haraji yana kuma ba kasashen duniya mamaki. Ba a jima ba da gwamnatin Amurka ta sanar da matakinta na harajin ramuwar gayya a kan kasashen da ke ciniki da ita, sai kuma ga shugaba Trump ya sanar da dage harajin a kan wasu kasashe na kwanaki 90. Kuma kashegari sai aka ji ya yi barazanar cewa, in dai ba a kai ga cimma daidaito a shawarwari ba, to, Amurka za ta maido da harajin. Ban da haka, gwamnatin Amurka ta kuma yi gyara ta ba-zata a kan dokokinta na haraji, inda ta cire harajin ramuwar gayya a kan kayayyakin lataroni da suka hada da wayar salula...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce a yanzu jihar na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya. Ya ce, a matsayinsa na babban jami’in shari’a da tsaro a Jihar Yobe, yana da haƙƙin ganin an bi doka don tabbatar da cewa jihar ta samu zaman lafiya. An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin karɓar lambar karramawa da aka yi masa shi da wasu shugabnnin da Ƙungiyar Inganta zaman lafiya ta “Peace Building Development Consult” (PBDC) ta yi musu. Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar...
Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7. An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri a sayar da shi kafin a sa’ar kuɓutar da shi daga masu son sayar da shi. An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji Waɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin Zamba da ke Abuja, yayin da...
Hukumar lura da gidajen bashin ma’aikatan gwamnatin tarayya (FGSHLB) ta sanar da cewa ta fara tattara jerin sunayen ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya amma ba su biya bashin gidajen da suka karɓa ba. Shugabar sashin sadarwa da hulɗa da jama’a na FGSHLB, Ngozi Obiechina, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis a Abuja, inda ta ruwaito cewa shugabar hukumar, Salamatu Ahmed, tana cewa wannan matakin yana nufin dawo da dukiyoyin da aka yi rance daga ma’aikatan da suka yi ritaya amma ba su kammala biyan bashin ba. Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya: Jigon Ziyarar Xi A Kudu Maso Gabashin Asiya Salamatu...

Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma wasu mutane da dama masu fafutuka a shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na lumana takunkumi. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya bayyana manufar takunkuman da Amurka ta kakabawa al’ummar Iran da cewa; A fili take nuna kyama ga masu yanke shawaran Amurka kan al’ummar Iran da kuma nuna rashin mutunta doka da hakkin dan Adam ne. Ya kara da cewa: Dogaro...
Jami’in kasar Yemen ya jaddada cewa: Kwanaki masu zuwa za su aiwatar da abubuwan mamaki da za su ba abokan gabanmu mamaki! Daraktan sashin yada labarai na fadar shugaban kasar Yemen Zaid Al-Gharsi ya jaddada samun gagarumin ci gaba a karfin sojojin kasar Yemen musamman a fannin fasaha da makamai. Ya yi nuni da cewa, kasar Yemen na gab da samar da sabbin makamai da za su bai wa kowa mamaki. A cikin wata hira da tashar talabijin ta Al-Alam, Zaid Al-Gharsi ya yi magana game da irin goyon bayan da kasar Yamen ke ba wa yankin Zirin Gaza, inda ya yi nuni da mahimmancin hare-haren soji kai tsaye kan makiya ‘yan sahayoniyya tare da jaddada fifikon karfin kasar Yemen...
Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da ya kunshi munanan shaida daga fursunonin Zirin Gaza da ke tsare a gidan yarin Negev da sansanin Ofer na gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila. Rahoton ya bayyana yadda ake ci gaba da yin fyade da cin zarafi ga wadanda ake tsare da su a Gaza. Wanda ake tsare da shi a sansanin Ofer ya bayyana cewa da gangan masu gadin sansanin suke kara radadin yadda wanda...

Gwamnatin Siriya Tana Daukan Matakan Matsin Lamba Kan Gwagwarmaya Domin Samun Yardan ‘Yan Sahayoniyya
Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a cikin yankunan Siriya, a cikin abin da gwamnatin Isra’ila ta kira “yankin da ke da kariya,” wanda ya hada da mamaye wasu sassan garuruwan Quneitra da Dara’a. Majiyoyin cikin gida a garin Nawa da ke cikin karkarar Dara’a na cewa, mahukuntan kasar Siriya na ci gaba da daukan matakan matsin lamba, ta hanyar shugabannin kabilu da kwamandojin ma’aikatar tsaro a Dara’a, na tilastawa bangarorin da...
Ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumar kula da gidajen Radiyo da Talabijin ta kasa NBC sun shirya taron yini biyu ga masu fafutukar siyasa da masu sharhi kan harkokin yada labarai. Taron na da nufin tsaftace harkar siyasa da inganta fahimtar juna tsakanin ‘yan siyasa a jihar. An zabo mahalarta taron ne daga jam’iyyun siyasa daban-daban da gidajen rediyo a fadin kananan hukumomi 44 na jihar. A nasa jawabin, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa, a karshen taron, mahalarta taron za su fahimci ladubban da suka shafi harkokin siyasa. Ya yi Allah wadai da karuwar kararrakin batanci da sunan...
“Ka koma gefe – ba wai kabar wa abokan hamayyarka takara ba, amma don sabbin jini matasa ‘yan Nijeriya da za su iya ciyar da al’umma gaba da sabbin kuzari da tunani.” in ji shi. Ya kara da cewa, ya kamata shugaban kasa ya yi tunani a kan nagartattun abubuwan da yake son bari bayanshi da kuma yadda tarihi zai tuna da shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda. A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22 a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba. A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar. Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda. ...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba da umarnin gaggawa da a yi cikakken sauyi ga dabarun tsaron ƙasa, yana mai umartar shugabannin tsaro su ɗauki matakan gaggawa don daƙile ƙaruwar tashin hankali da kashe-kashe jihohin Borno, Filato, Binuwai, da Kwara. Tinubu, wanda ya gana da shugabannin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce dole ne a kawo ƙarshen kashe-kashe a jihohin da abin ya shafa. “Ya isa haka,” in ji Shugaba Tinubu yayin da ya sake yin tir da kai hari ga ’yan Najeriya ba tare da wani dalili ba. Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, ya shaida wa manema labarai cewa shugabannin tsaron sun yi wa shugaban ƙasa cikakken bayani kan halin da...
Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami’an jam’iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya na ƙasa. Gwamnonin PDP, a taron da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo, sun amince da Koshoedo a matsayin mukaddashin sakatare har sai lokacin da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas za su zaɓi cikakken sakatare wanda Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar zai amince da shi. Kotun Ƙoli, a hukuncin da ta yanke kan wanda ya cancanci ya riƙe muƙamin tsakanin Sanata Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye, ta ba jam’iyyar ikon yanke shawara kan shugabanninta. Sai dai a wata takarda da Alhaji Gurama Bawa, jami’in gudanarwa na mukaddashin shugaban jam’iyyar ya fitar, ta ce...
Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, ya ba wa dakarun rundunar wa’adin wata guda su fatattaki sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta Mahmud a da ta ɓulla a Jihar Kwara. Oluyede ya ba da wannan umarnin ne a lokacin da yake jawabi ga sojojin a ziyarar da ya kai Barikin Sobi da ke Ilorin, babban birnin jihar. “Daga wata mai zuwa, ba na son in ƙara jin mostin waɗannan ’yan ta’addan a yankin Dam ɗin Kainji,” in ji babban hafsan sojin. Ya umarce su da su kawar da ’yan ta’addan daga ƙananan hukumomi biyun da suka addaba, yana mai jaddada cewa yana son a kammala aikin cikin wata mai zuwa. Nijar, Mali da Burkina Faso sun kafa gidan...
Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES), sun sanar da shirinsu na ƙaddamar da gidan rediyo na haɗin gwiwa. Ƙasashen guda uku, waɗanda duk a halin yanzu suke ƙarƙashin mulkin soja, sun jaddada cewa sun kafa gidan rediyon ne da nufin daƙile farfagandar ƙasashen waje da kuma isar da “ingantattun bayanai na gaskiya” ga ’yan ƙasarsu. Sanarwar tasu ta kasance bayan ƙaddamar da gidan talabijin ɗinsu na intanet na haɗin gwiwa da suka yi a watan Disamba na 2024, wanda suka bayyana a matsayin dandamali da aka samar domin “yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.” Baya ga waɗannan ayyukan watsa labarai, a baya ƙungiyar ta nuna sha’awarta ta kafa kamfanin jiragen sama na yankin da...
Amurka ta kai wasu sabbin hare-hare ta sama a Yaman, a daidai lokacin da kasar Larabawar ke ci gaba da nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza. Gwamnonin Sana’a da Sa’ada su ne wuraren da Amurka ta kaddamar da sabbin hare-hare a safiyar Alhamis. A birnin San’a, jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare 6 a yankin Barash da ke gabashin Dutsen Nuqum. Har ila yau Amurka ta kai hari a unguwar Al-Jarf da ke gabashin gundumar Sha’ub ta lardin Sana’a. A arewa maso yammacin kasar, an kai wasu hare-hare 6 ta jiragen yakin Amurka a yankin Sahlin da ke gundumar Al Salem a gundumar Sa’ada. Har ila yau, Amurka ta kai wasu jerin hare-hare ta sama kan lardin Al-Hudaidah, inda...
Aljeriya sun kori fiye da bakin haure 1,100 zuwa Nijar a rana guda, al’amarin da ba a taba ganin irinsa ba. Bakin hauren da hukumomin Aljeriyar suka bayyana da basa bisa ka’ida, an kora su a cikin hamadar sahara a ranar Asabar din da ta gabata, Inda sukayi tattaki zuwa kan iyakar kasar Nijar, kasar da dubban bakin haure ke bi domin zuwa Libya da Aljeriya domin isa Turai. Wannan dai shi ne karo na farko da aka kori bakin haure da dama daga kasar Aljeriya a lokaci guda. A cewar kungiyar ‘Alarme Phone Sahara’ ta Nijar da ke taimakawa bakin haure a cikin hamada, an kori mutane 1,140 a lokaci guda, adadin da ba a taba ganin irinsa ba....
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, za ta karbi bakuncin taron farko na kasa da kasa kan kare hakkin bil adama a Gabas ta Tsakiya. Shugaban Hukumar Al’adu da Sadarwa ta Musulunci Mohammad Mehdi Imanipour ya bayyana cewa, za a gudanar da taron farko na kasa da kasa kan batun kare hakkin bil’adama kan Gabas ta Tsakiya a lokaci guda a Tehran, Qom da Isfahan daga ranar 28 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu. Hakkin dan adam na daya daga cikin batutuwan da suka fi muhimmanci a cikin al’ummomi, saidai a baya bayan nan wasu gwamnatoci sun yi watsi da yancin dan adam gaba daya. Mohammad Mehdi Imanipour ya ce “A yau, misali karara na take hakkin bil’adama shi ne kisan kiyashi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun zamanin kaka da kakanni ake gudanar da ƙananan sana’o’i, waɗanda al’umma ke dogaro da su don biyan buƙatunsu na yau da kullum. Irin waɗannan sana’oi sun haɗa da saƙa, jima, fawa, suyan ƙosai ko masa da dai sauransu. A da can masu waɗannan sana’o’i sun dogara ne da masu wucewa a bakin hanya don siyar da hajojinsu ko kuma waɗanda suka samu a yayin da suka ɗauki tallar kayan sana’ar tasu. Sai dai a wannan zamani masu waɗannan sana’o’i na fuskantar barazana daga wurin ’yan zamani ’yan bana bakwai da suka shigar da zamani ciki suke neman kwace musu ragama ta hanyar amfani da kafofin sada zumunta wajen tallata hajojinsu. NAJERIYA A...
Ba a kan batun tekun kudancin kasar Sin ne kawai Philippines ta rura wutar rikici ba, har ma tana son taimaka wa Amurka kan batun da ya shafi yankin Taiwan, amma muna iya cewa, munafunci dodo ne tabba ya kan ci mai shi, in ji malam Bahaushe. (Murtala Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti. “An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan sun gama jinya,” in ji sanarwar. Rundunar ‘yansandan ta ce Baba-Beru, mazaunin Kofar Mazugal a karamar hukumar Dala, na cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo kafin faruwar lamarin. Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, ya yabawa bajintar jami’an da suka dakile yunkurin ‘yan fashin tare da jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar. ...
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta son gwabza yakin kasuwanci da karin harajin kwastam, amma kuma ba za ta rungume hannu ta zuba ido ba idan yakin ya kaure, yana mai nuni da cewa, idan har Amurka ta zabi fafata yakin kasuwanci, Sin za ta sha damarar yakin har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi. Sai dai kuma duk da haka, ya ce idan Amurka na son a tattauna, Sin za ta bar kofarta a bude domin yin hakan. Bugu da kari, dangane da batun yadda a baya-bayan nan kafafen yada labarun kasar Panama suka soki Amurka kan yin katsalandan da nuna babakere a kasashen yankin tsakiyar Amurka, musamman a kasar ta...

Shawarar Tabbatar Da Tsaro A Duniya Ta Samar Da “Kyakkyawan Fata” Ga Duniya Mai Fama Da Tashin Hankali
Na uku, ba da ra’ayin samun tsaro kafada da kafada, inda aka jaddada cewa, ya dace kasa da kasa su yi fatali da ra’ayin nuna wa juna fito-na-fito, kana, su fuskanci dimbin kalubalen tsaro cikin hadin-gwiwa. Na hudu wato na karshe, tallata ra’ayin tabbatar da tsaro mai dorewa, wato a maida hankali kan dorewar tsaro na wani dogon lokaci. Alal misali, yayin da ake daidaita rikicin wani yanki, bai dace a dogara kan matakan soja kadai ba, ya kamata a nemo mafita tun daga asalin rikicin. Wannan shawarar tsaron da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ta samu amincewa sosai daga mutanen kasa da kasa, inda ya zuwa yanzu, ta riga ta samu goyon-baya daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa...
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya gana da babban mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu, da hafsan hafsoshin tsaro na ƙasa, Christopher Musa. Rahotanni dai na nuna sun shiga taron ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 3 na rana. Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC Wannan dai shi ne karo na farko da Tinubun ke ganawa da jagororin tsaron tun bayan dawowarsa daga Faransa da Birtaniya ranar Litinin. Kafin dawowarsa dai, ‘yan siyasa da dama da sauran al’umma sun koka ka yadda shugaban ya shafe sati biyu a ƙasashen duk da cewa matsalar tsaro na ci gaba da...
Rashford ya yi watsi da yiwuwar komawa Landan, inda yace ba lallai bane ya cigaba da wasa a karkashin Ruben, inda yake da burin zama a kungiyar da zata buga gasar Zakarun Turai a badi, majiyoyi na kusa da dan wasan sun tabbatar Rashford har yanzu bai tattauna kan makomarsa ba kuma baya shirin yin hakan har zuwa tsakiyar watan Yuni. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdurrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC. Sumaila ya tabbatar wa Aminiya ficewarsa a wani saƙon kar ta kwana, bayan wallafa wa a shafinsa na Facebook. Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC “Gaskiya ne na koma APC. Damuwata a ko yaushe ita ce walwalar al’ummar mazaɓata,” in ji shi. Sanatan ya jaddada cewa matakin da ya ɗauka na sauya sheƙar ya yi shi ne domin inganta rayuwar al’ummar mazaɓarsa, da kuma tabbatar da ci gabansu mai dorewa. Kawu dai ya daɗe da raba gari da tafiyar Kwankwasiyya da NNPP da ya...

Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa. Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2 kowanne ga iyalai biyar da suka rasa rayukan ‘yan uwansu, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 10. Ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jinya ga wadanda ke karbar magani a Asibitocin jihar. A yayin da yake godiya, Sarki Maiyamba ya ce, hatsarin na Easter ya girgiza daukacin masarautar Tangale, amma ya amince da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wanda ya ce hakan...
A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yake-yaken karin haraji da kasuwanci ba su haifar da komai illa tauye halastattun hakkoki da muradun dukkan kasashe, tare da kawo cikas ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma yin tasiri mara kyau ga tsarin tattalin arzikin duniya. Yayin ganawarsa da shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev, shugaba Xi ya yi bayanin cewa, kasar Sin tana da muradin yin hadin gwiwa tare da kasar Azabaijan wajen kiyaye tsarin kasa da kasa a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa dokokin da aka amince da su a duniya, da yin tsayuwar daka wajen kare halastattun hakkoki da muradu, da kare daidaito da adalci...
Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya samun karuwar hargitsi a cikin harkokin tattalin arzikin na duniya da dama yake fama da matsala. Jami’in ya yi bayani ne bayan sake yin hasashe akan ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda aka fitar a cikin rahoto a ranar Talatar nan. Asusun bayar da lamunin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin duniyar zai bunkasa da kaso 2.8 % a cikin 2025, da hakan yake nuni...
Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa. An fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa. Daga cikin lambobin yabon din da tawagar ta Iran ta lashe da akwai gwala-gwalai 4, azurfa 3 da kuma tagulla.
Ministan harkokin wajen Iran wanda ya ziyarci kasar China, ya bayyana cewa, tattaunawa da mahukunta wannan kasa ta yi kyau, kuma ba da jimawa ba, shugaban kasar Iran zai kai Ziyara can kasar. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci bayan ganawa da takwaransa na China ya ce; Na yi doguwar ganawa da ministan harkokin wajen China, wacce take mai muhimmanci, kuma kusan dukkanin bangarorin da suka shafi alakar tsakanin kasashenmu biyu mu ka tattauna, haka nan kuma batutuwa da su ka shafi siyasar kasa da kasa.” Arakci ya kara da cewa; Da akwai fahimtar juna a tsakaninmu, musamman abinda ya shafi batun makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, da tataunawar da ake yi da Amurka.” Haka nan kuma ya...
Hukumar lafiya ta duniya (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu fama da wannan cutar. Hukumar lafiyar ta duniya ( w.h.o) ta kuma yi ishara da yadda ‘yan mamaya su ka lalata bangarorin da suke kula da cutuka na musamman a cikin asibitoci. Ita ma hukumar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa; masu fama da cutar koda a yankin suna fama da matsaloli na rashin Magani, kuma daruruwa daga cikinsu sun mutu saboda hakan. Haka nan kuma ta yi ishara da yadda mutane 400 daga cikinsu su ka rasu, da hakan yake nufin kaso 40% na adadin masu wannan cutar. A gefe daya, ma’aikatar kiwon lafiyar...
Ƙungiyar shugabannin majalisun jihohin Nijeriya ta yi tur da matsalolin tsaron da suka addabi jihohin Filato, Borno, Binuwai, Neja, da kuma Kwara a baya-bayan nan. Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ɗauki matakan gaggawa domin daƙile bala’in da jihohin a kwanan nan suka tsinci kansu a ciki. Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Ibadan da ke Oyo mai dauke da sa hannun shugabanta, Adebo Ogundoyin. Ya bayyana cewa kashe-kashen dubunnan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba ya janyo musu asarar gidajensu, da dukiyoyinsu, yana haifar...
Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na jihar sun sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Daga cikin jiga-jigan da suka sauya sheƙa har da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyya, da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar reshen jihar. Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya Sanarwar ficewar ta su ta zo ne bayan kammala taron sa’o’i shida da suka gudanar a gidan gwamnatin jihar, kamar yadda sanarwar da Sanata daga jam’iyyar, James Manager, ya bayyana. “Duk wani dan PDP na jihar har da gwamna, da tsohon gwamna Okowa, da shugaban majalisa, da shugaban jam’iyyar, da duk ciyamomin ƙanannan hukumomi...
Gwamna Oborevwori, wanda ya samu nasara a zaben gwamna na 2023 a karkashin jam’iyyar PDP, ya samu tarba daga manyan jami’an APC. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bugu da kari, kasar ta samar da cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara 3,081, baya ga likitocin yara da na mata a fadin kasar da yawansu ya kai 373,000. Kana fiye da kashi 90 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yanzu sun mallaki kayan aiki da sassan kula da lafiyar yara masu inganci. Ba a cikin kasarta kawai take kokarin inganta kiwon lafiyar mata da kananan yara ba, har ma da kasashen duniya, domin kwararrun likitocin Sin da aka tura don ba da agaji a kasashen waje sun gudanar da ayyukan kula da lafiyar mata da yara a kasashe da yankuna 44, ciki har da wasu kasashen Afirka. A cikin 2024 kadai, tawagogin...
Ba wannan ne karon farko da ake zargin wasu ‘yan ƙasashen waje da kai hare-hare a Nijeriya ba. A baya an yi zargin cewa ƙungiyoyi kamar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sakkwato da Zamfara, sun samo asali ne daga ƙasashen waje. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Maryam Abubakar, ɗaya ce daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ’yan ƙalilan da suka yi nasarar bin sahun iyayensu a harkar fim. Matashiyar jarumar, wadda aka fi sanin ta da Maryam Intete a masana’antar, ta yi bayani a kan matsayinta na wadda iyayenta suka suka a cikin cikin harkar fim. Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa A wannan tattaunawar, jarumar ta yi bayani game da gogewarta da yadda ake samun daukaka a Kannywood, da wasu abubuwa game da ita kanta da iyayenta, da kuma sana’ar fim da dai sauransu. Wace ce Maryam Abubakar? An haife ni ne a Kano kuma a nan na girma....
Wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ake kira Mahmuda tana ci gaba da kafuwa da ƙara ƙarfi tare da addabar jama’a a wasu garuruwa na ƙananan hukumomin Ilesha Baruba da Kemaanji da Kaiama da Baruten na Jihar Kwara. Bayanai sun ce ’yan ƙungiyar sun sami mafaka ne a gandun dajin Kainji Lake National Park, kuma daga can ne suke kai hare-hare a garuruwan da ke makwabtaka da dajin har ma da wasu sassa na Jihar Neja. DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa CONMEBOL ta buƙaci a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta 2030 Bayanai sun ce ko a Juma’ar da gabata sai da mayaƙan suka kashe wasu fulani huɗu, ɗan sa-kai da wani saurayi mai shekaru 19....
Garuruwan da aka fi tsananta wa harajin sun haɗa da Gijinzama da aka tilasta musu biyan Naira miliyan 8.5, Dakolo da aka karɓi Naira miliyan 5 da buhun wake 20, sai Kibari da Kunchin Kalgo da suka biya Naira miliyan 20, Sungawa da Naira miliyan 15, da kuma Yalwa da aka tilasta su biyan Naira miliyan 2.7. Bayan rasuwar Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga mai suna Dogo Gide ya sa harajin Naira miliyan 100 a kan ƙauyuka 23 da ke ƙaramar hukumar Tsafe. A ƙarshen makon da ya gabata kuma, mazauna ƙauyen Dankurmi a ƙaramar hukumar Maru sun fuskanci sabon harajin Naira miliyan 60. Wani mazaunin ƙauyen Dan Jibga, Muhammad Dogo, ya bayyana cewa bayan kashe mutane biyu...

Rohoton Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Ya Tabbatar Da Tafka Manyan Laifukan Cin Zarafin Bil-Adama A Siriya
Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka 72 da ke kunshe da jerin munanan laifukan da aka yi wa fararen hula a gabar tekun Siriya, yana mai bayyana shi a matsayin “neman shafe wata al’ummar daga kan doron kasa a kan tubalin sabanin Mazhaba”. Rahoton wanda masu fafutuka 12 suka shirya, ya zo ne bayan kisan kiyashin da aka fara a ranar 6 ga Maris. Rahoton ya yi nuni da wani tsari...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya. Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taɓa rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Kudancin Amurka (Conmebol) ta gabatar da buƙata a hukumance ta ƙara yawan ƙasashen da za su halarci Gasar Kofin Duniya ta 2030 zuwa ƙasashe 64. Haɗakar ƙasashen Sifaniya da Morocco da Portugal ne za su karɓi baƙuncin gasar, bayan buɗe ta a ƙasashen Argentina da Paraguay da kuma Uruguay. Matar da aka haifa ‘babu mahaifa’ ta haihu Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan mutuwar Fafaroma Francis Gasar Kofin Duniya ta 2026 ce ta farko da ƙasashe 48 za su halarta, to amma Conmebol na son a faɗaɗa gasar ta 2030 domin murna cika shekara 100 da fara gasar. “Hakan zai bai wa ƙasashen duniya damar kallon gasar, don haka ba wanda za a bari a...
Sai dai daga baya suka fara yawo da makamai suna kama mutane, suna yanke musu hukunci har da kashe wasu. Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa a yanzu mutane ba sa iya zuwa gonakinsu da ke nisan da kilomita biyu saboda tsoron ‘yan ƙungiyar. Ya ce kashi 50 cikin 100 na mutanen garin sun tsere. Baya ga haka, ƙungiyar ta haramta noma a yankin. “Kashi 95 cikin 100 na mutanen manoma ne, amma yanzu sun ce ba za mu iya yin noma ba. Mutuwa tana kusa da mu saboda yunwa,” inji shi. Wannan lamari na ƙara bayyana irin ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a Nijeriya, musamman a jihohin da ake kyautata zaton sun fi samun kwanciyar hankali. Daga kanmu,...
‘Yan majalisar dokokin Aljeriya, sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila. ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya da wakilan jama’a na kasar a zaman majalisar dokokin kasar, sun yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila ke aikatawa akan al’ummar Gaza, tare da nuna cikakken goyan bayansu ga falasdinawa. Mahalarta taron sun yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta yi amfani da dokar da ta haramta daidaita alaka da gwamnatin mamayar Isra’ila. Mustapha Yahi, sakatare-janar na National Democratic Rally (RND) ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da wakilin jaridar Al-Alam: inda yake cewa “Mun sake yin Allah wadai da ci gaba da ta’addancin isra’ila. Abdelaali Hassani Cherif, shugaban kungiyar Movement of Society for Peace (MSP),...
Guo Jiakun ya kara da cewa, kasar Sin ta kiyaye amfani da tsarin kimiyya da babu rufa-rufa a ciki mai baje komai a faifai, tare da nuna goyon baya da kuma shiga cikin kokarin da kasashen duniya ke yi na gano ainihin inda cutar ta samo asali. Ya bukaci Amurka da ta daina siyasantar da lamarin, da amfani da batun gano asalin cutar a matsayin makami, kana ya nemi Washington ta guji yin kafar ungulu ga wasu kasashe, da dora wa wasu laifi, da yin watsi da tababar da ake ta nunawa a game da ayyukanta masu nasaba da cutar. Kazalika, ya jaddada bukatar ganin Amurka ta warware matsalolin da kasashen duniya suka nuna damuwa a kai tare da...
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’ar ta ce, “Shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar na da inganci kuma masu gamsarwa ne, don haka kotun ta samu wanda ake tuhuma da laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.” A cewar mai gabatar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba-Sorondinki, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Janairu, 2023, a unguwar Rijiyar Zaki da ke Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A shekarar 2024, an kammala jigilar fasinjojin da yawansu ya kai biliyan 1.46 a filayen jiragen sama na kasar Sin yayin da yawan tashi da saukar jiragen sama ya wuce miliyan 12.4, adadin sun karu da kashi 15.9 bisa dari da kuma kashi 5.9 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Hakan ya nuna cewa, duka alkaluma masu alaka da harkokin sufuri sun kafa tarihi. Kazalika, a ranar 21 ga wata, kungiyar filayen jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da kwalejin nazarin kimiyya da fasahar jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da sauransu sun fitar da “Rahoton kimanta ingancin hidimar filin jirgin sama na shekarar 2024”, inda rahoton ya ce, akwai daidaito...
Ana kallon Cunha a matsayin wani da zai iya bayar da gudunmawa wajen dawo da Manchester United kan ganiyarta, Cunha ya kasance wanda ya fi zurawa Wolverhampton kwallaye a raga a kakar wasa ta bana inda ya zura kwallaye 16 a dukkanin gasa. United na shirin fuskantar gogayya daga kungiyoyi da dama na gasar Firimiya kan Cunha, inda Liverpool, Arsenal, Chelsea da Newcastle duk sun kasance suna zawarcin dan wasan gaban a bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Har ila yau, an rubanya ayyukan tuntubar da ake yi game da yanayi da kuma gudanar da bincike na musamman kan yiwuwar wargajewar da za a iya samu daga yanayin. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A safiyar jiya Litinin ce Fafaroma Francis mai shekaru 88 ya koma ga mahaliccinsa, bayan da ya yi fama da mutuwar ɓarin jiki da kuma bugun zuciya, kamar yadda Fadar Vatican ta sanar. Shugaban na mabiya ɗariƙar Katolika ya shafe makonni 5 a asibiti a farkon wannan shekara, sakamakon harbuwa da cutar limoniya, amma ya koma gida a watan da ya wuce, bayan da ya samun sauƙi. An sanya dokar hana fita ta sa’o’i 12 a Neja Hanyoyin da za a magance rikicin Filato — Masana Fadar Vatican ta tabbatar da cewar a ranar Asabar ne za a gudanar da jana’izar Fafaroma Francis a majami’ar St. Peter’s Basilica. A safiyar Talatar nan ce dai fadar Vatican ta saki hoton Fafaroma...
Shugaban hukumar al-adun musulunci da sadarwa a nan Iran Mohammad Mehdi Imamipour ya bayyana cewa za’a gudanar da taron kasa da kasa na kare hakkin bil’adama a karon farko a nan kasar Iran tare da mahangar kasashen gabas. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Imanipour yana fadar haka a yau, ya kuma kara da cewa za’a bude tarurrukan ne a nan birnin Tehran, Qom da kuma Esfahan a lokaci guda daga ranar 28 ga watan Afrilu zuwa 2 ga watan mayu. Labarin ya ce matsalar kare hakkin bil’adama yana daga cikin al-amuran da ake nuna faska biyu a cikin al-amura da dama a duniya, musamman kan abinda yake faruwa a kasar. Imanipour y ace suna son gudanar...
A yayin ziyarar, mataimakin shugaban kamfanin LEADERSHIP Mike Okpere, ya bayyanawa uwargidan shugaban kasa irin ayyukan agaji da Kamfanin LEADERSHIP ke gudanarwa tare da yin fatan hada hannu da shirin tallafin fata na gari ‘Renewed Hope Initiative (RHI)’ da nufin karfafawa mutane 1,000 da ayyukan yi. A cewar Okpere, shirin zai mayar da hankali ne wajen samar da sana’o’in dogaro da kai a sassa daban-daban na tattalin arziki da suka hada da rini, kamun kifi, dinki da dai sauransu. Ya yi nuni da cewa, manufar ita ce a taimaka wa daidaikun mutane su samu ‘yancin cin gashin kansu da kuma zama masu amfani a cikin al’umma. Uwargidan shugaban kasar, wacce ta yi marhabin da shirin tallafin, ta...
Brigadier General Ali Mohammad Naeini, kakakin dakarun dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar ya bayyana cewa dakarunsa a shirye suke fiye da ko wani lokaci wajen kara kan iyakokin JMI daga makami. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran Naeini yana fadar haka a yau Talata a wani taro da kafafen yada labarai a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa a dai-dai lokacinda kasar ta cika shekaru 46 na nasarar juyin juya halin musulunci a kasar dakarun na IRGC suna cikin shirin da basu taba irinsa ba don kare kan iyakokin JMI. Kafin haka, a farkon wannan watan jami’an gwamnatin JMI sun bayyana cewa kasar tana cikin shiri mai kyau na kare kan iyakokin kasar mai tsarki,...
A ranar 17 ga watan Afrilun da muke ciki ne wakilai ko ministocin noma na kasashen kungiyar BRICS suka taro a Brazilian a kasar Brazil inda suka rantaba hannu kan shelanta shirin namusamman na bunkasa ayukan noma da kuma harkokin samar da abinci da kuma wadatar da shi ga kasashen duniya farko ga kasashen kungiyar. Shirin dai ya hada da na shekara ta 2021-2024 da kuma na 2025-2028, wadanda kungiyar zata aiwatar da su tare. Shirin ya hada da bunkasa ayyukan noma da samar da wuraren ajiye kayakin noma da kuma taimakawa kananan ayyukan noma a kasashen kungiyar saboda smaar da manoma wadanda zasu yi noma mai yawa nan gaba. Sannan rage abubuwan da ke hana ayyukan noma ci gaba...
Iyalan Alhaji Surajo Ilyasu Malumfashi (RADIO NIGERIA KADUNA) dana Alhaji Idris Ahmed Accama na farin cikin sanar da bikin aure na ‘ya’yansu, Muhammad Auwal Idris da Zainab Surajo Malumfashi. Za’a gudanar da bikin auren ranar Asabar, 3 ga Mayu, 2025, a Masallacin Juma’a na Dan Fodio, Dake Anguwan Sunusi, Jihar Kaduna. Za a daura auren da misalin karfe 11:00 na safe, sannan ana sa ran ci gaba da liyafa kai tsaye bayan kammala daurin auren. Iyalan suna gayyatar dangi, abokan arziki da duk masu fatan alkhairi su halarta tare da murnar wannan babban biki, wanda ke nuna sabon babi a rayuwar amarya da ango. Surajo Ilyasu Malumfashi
Gwamna Umar Mohammed Bago, ya sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 12 a birnin Minna na Jihar Neja. Wannan dai na zuwa ne sakamakon hare-haren da ya janyo salwantar rayuka da aka samu a bayan nan a babban birnin. Hanyoyin da za a magance rikicin Filato — Masana HOTUNA: Yadda Pantami ya kai wa Sheikh Jingir ziyarar ta’aziyya A cewar gwamnan, an haramta zirga-zirgar baburan ’yan acaɓa da masu Keke Napep daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safiyar kowacce rana. Gwamnan ya bayyana hakan a yayin wani taro na musamman da ya gudana da masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro da ya ƙunshi sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a Fadar Gwamnatin jihar a ranar Talata....
Kamfanoni da masana’antun America da dama sun dakatar da harkokinsu, dubban mutane sun rasa aikin yi. Don haka wannan mataki bai haifar da sakamakon da Mr. Trump ke bukata ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda kasuwar hannayen jari ta shiga cikin rudani, gami da hali na rashin tabbas da manoman America suka samu kansu biyo bayan maida martani da China tayi na ramuwar gayya. Domin kuwa sai da gwamnatin America ta kashe kimanin dala biliyan 30 wajen tallafawa manoman kasar kan asarar da suka tafka, biyo bayan harajin da China ta kakabawa wasu daga cikin amfanin gonar America da ake shigar da su China. Sabo da haka a nan za mu iya bugun gaba mu ce “Kwalliya...
Sai dai a hakika, ba dole ne kasar Lesotho, da sauran kasashen Afirka su mika wuya ga kasar Amurka, don ta ci zalinsu yadda ta ga dama ba. Kamar yadda Charles Olunaiju, wani masanin kasar Najeriya, ya rubuta a cikin wata makalarsa da jaridar Vanguard ta wallafa, kasar Amurka ba za ta samu biyan bukata a yakin ciniki da ta tayar ba, saboda dunkulewar duniya sakamakon dimbin cinikin da ake yi tsakanin kasashe daban daban, da hadewar sassan duniya da cudanyar mabambantan al’adu, wadanda aka samu bisa tushen ci gaban fasahohi, sun haifar da wani yanayi mai armashi da ba za a iya sauya shi ba. Mista Olunaiju ya kara da cewa, a matsayin wata dabarar tinkarar rikici, kasashen...
Hare-haren da aka kai kan al’ummomin kananan hukumomin Bokkos da Bassa da ke Jihar Filato, sun sake jefa jihar cikin wani mummunan tashin hankali. Sama da shekaru 20 ke nan wannan matsala ta ki ci ta ki cinyewa a jihar da ke yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya, inda take ci gaba da lakume rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, tare da lalata dukiyoyi. HOTUNA: Yadda Pantami ya kai wa Sheikh Jingir ziyarar ta’aziyya Gwamna ya dakatar da basarake kan satar mutane da yankinsa Hare-haren baya-bayan nan, musaman daga ranar 28 ga watan Maris zuwa yanzu, a kananan hukumar Bokkos da Bassa da ke jihar Filato sun sun yi sanadiyar asarar rayukan mutane sama da 100...
Wasu shugabannin duniya da suka bayyana niyyarsu ta halartar jana’izar sun haɗa da Donald Trump na Amurka, Emmanuel Macron na Faransa, Luiz Inacio Lula da Silva na Brazil, da Volodymyr Zelensky na Ukraine. Ana sa ran jana’izar za ta samu halartar manyan baƙi daga sassan duniya, tare da girmama rayuwar Fafaroma Francis da ayyukansa da ya yi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da ci gaba a kan tafarkinta. Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Babu kyakykyawan fata kuma ba za a fitar da rai ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da yake jawabi a taron da gwamnonin kasar suka yi a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar a yau, ya yi jawabi kan shirin tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai cewa: Tun...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba su da niyyar gudanar da tattaunawa da Amurka a fili Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba ta da niyyar yin shawarwari da Amurka a fili a bainar jama’a.” Araghchi ya rubuta a shafinsa na Twitter da safiyar yau Talata cewa, “Lokacin da ya amince da gabatar da muhimmin jawabi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, har yanzu Iran da Amurka ba su sanya ranar da za a yi shawarwarin zagaye na gaba ba, wanda za a fara...
Haka kuma, ya soki jam’iyyar Galadima wato NNPP, yana mai cewa tana cike da rikice-rikice, saɓanin APC a ƙarƙashin shugabancin Ganduje wadda ke tafiya cikin daidaito. Okpala ya kammala da cewa Ganduje ya mayar da hankali wajen ciyar da jam’iyyar APC gaba, kuma ba zai tsaya sauraren “maganganun marasa tasiri” kamar na Galadima ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Munanan abubuwan da suka faru na zubar da jini bayan wasa tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli a Libya A kusa da filin wasa na birnin Tripoli an ga abubuwan na zubar da jini bayan wasan da aka yi tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli, lokacin da wasu motocin ma’aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin hadin kan kasa suka bindige magoya bayanta da gangan. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa bayan an kammala wasan ne wata mota dauke da makamai ta kutsa cikin wurin da jama’a ke cunkoso, inda suka bi ta kan wasu matasa, lamarin da ya haifar da firgici da hargitsi. An kuma ji karar harbe-harbe a wurin, lamarin da ya ta’azzara lamarin tare da jikkata wasu da ke...
Sheikh Isa Ali Pantami ya ziyarci Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir domin yi masa ta’aziyyar rasuwar Sheikh Sa’idu Hassan Jingir a garin Jos, fadar Jihar Filato.
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da basaraken yankin Masarautar Uwano Kingdom, Dakta George Oshiapi Egabor, nan take saboda matsalar yi garkuwa da mutane a yankin. Dakta George Oshiapi Egabor shi ne Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode a Karamar Hukumar Etsako ta jihar. Kakakin gwamnan, Fred Itua, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa an dakatar da basaraken ne har sai abin da hali ya yi, saboda yawan samun kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a masarautarsa a baya-bayan nan. Ya ce tuni jami’an tsaro suka tsare sakataren basaraken, Cif Peter Omiogbemhi, sakamakon wani sabon hari a da ya yi ajalin wani bafade, Cif John Ikhamate. Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72 An...
An tsinci gawar wani matashi da budurwarsa a tube bisa gado a cikin dakinsa a yakin Alo da ke Karamar Hukumar Ankpa a Jihar Kogi. An tsinci gawara masoyan ne a gidan hayan da saurayin ke zama ranar Juma’a da ta gabata. Mai gidan hayan mai suna Salisu Ibrahim ne ya nemi agajin jama’a sakamakon rashin ganin matashin ya bude kofarsa da safe kamar yadda ya saba. Daga nan ne ya sanar da dan uwan matashin da kuma ’yan sanda, inda suka so aka balla kofar dakin, inda aka samu masoyan sun kwanta dama. Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72 HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban...
Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da aka kai a Jihar Binuwai ya ƙaru zuwa 72. Adadin ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawarwaki 13 a ranar Litinin a ƙananan hukumomin Ukum da Logo.Adadin ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawarwaki 13 a ranar Litinin a ƙananan hukumomin Ukum da Logo. Da farko a ranar Lahadi Gwamna Hyacinth Alia a yayin da yake jawabin Ista a wani coci, ya sanar a yayin cewa an gano gawarwaki 59. Daga bisani aka gano ƙarin gawarwaki a cikin jejin yankunan da aka kai hare-haren. Kakakin gwmanan jihar, Isaac Uzaan, ya bayyana cewa an gano ƙarin gawarwaki 12 a Ƙaramar Hukumar Uku sauran mutum ɗaya kuma a Logo. Tsakanin daren ranar Alhamis da...
A yayin harin, mutane da dama sun gudu zuwa dazuka, amma sun fara dawowa yayin da zaman lafiya ya fara samuwa. “Yanzu mutane sun fara dawowa garin kuma abubuwa sun fara dawowa dai-dai,” inji wani mazaunin yankin. Wani dagacin ƙauyen, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce an samu zaman lafiya kuma al’umma sun fara komawa harkokinsu na yau da kullum. “Muna gode wa sojojin bisa yadda suka daƙile harin cikin gaggawa,” inji shi. Wannan ba shi ne karo na farko da aka kai hari a Buni Yadi ba, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a game da buƙatar ƙarin tsaro a yankin. Mazauna yankin na kira ga gwamnati da ta tura ƙarin sojoji don hana faruwar irin...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya mika ta’aziyya game da rasuwar shugaban ‘yan darikar katolika na duniya Paparoma Francis. A wani sako da ya aike a jiya Litinin, Pezeshkian ya ce Paparoma Francis a matsayinsa na shugaban darikar Roman Katolika ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yada koyarwar Yesu Almasihu. Shugaban ya ce Paparoma ya yi kokari wajen samar da zaman lafiya a duniya, da yekuwar samar da adalci, da ‘yanci, da mu’amala da tsaro a tsakanin addinai. Daya daga cikin shi ne bayyanannen matsayinsa na yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza da kuma kiran da ya yi na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa mata da kananan yara Falasdinawan...
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta hadin gwiwa daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare da Iran a hukumance, a cewar wata takardar aiki da aka wallafa a yanar gizo a jiya Litinin. Shugaban kasar Rasha da takwaransa na Iran Masoud Pezeshkian sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 17 ga watan Janairu bayan wata tattaunawa da bangarorin biyu suka yi a birnin Moscow. Yayin da a ranar 8 ga watan Afrilun nan majalisar dokokin Rasha ta Duma ta amince da yarjejeniyar kana majalisar dattawan tarayyar kasar suka amince da yarjejeniyar a ranar 16 ga Afrilu. Bisa yarjejeniyar da aka cimma, kasashen biyu na da burin zurfafa da fadada dangantakarsu a dukkan fannonin da...
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana gamsuwarsa da yadda tattaunawa tsakanin kasarsa da Iran ke gudana, yana mai bayyana ta a matsayin mai matukar kyau. Da yake magana da manema labarai a fadar White House jiya litinin, Trump ya ce tattaunawa da akayi da jami’an Iran sun yi matukar inganci. A ranar 12 ga watan Afrilu ne aka gudanar da zagayen farko na tattaunawar wacce ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka a shiga tsakanin kasar Oman a birnin Muscat. Haka zalika a ranar Asabar 19 ga watan Afrilu bangarorin sun yi wa ta biyu a birnin Rome na kasar Italiya, a shiga tsakanin kasar Oman. kasashen biyu sun bayyana kwarin gwiwar cewa za a ci gaba da...
Kwamitin kasa da kasa kan yaki da fari a yankin Sahel (CILSS) ya yi wani gargadi na musamman kan sake bullar ‘’kwarin dango’’ a yankin Sahel, wanda ke da hadarin yin illa nan gaba. Shafin yanar gizo na CILSS ya bayar da rahoton cewa, “Kwananan kwararru kan yaki da fari sun fitar da sanarwar sake bullar farar kwarin dango a kasashen Sahel da dama.” CILSS ta yi gargadin cewa “, wannan na iya haddasa matsala sosai a lokacin noma a yankin da ya riga ya kasance mai rauni’’. Yayin da ake fuskantar wannan barazana, CILSS na ganin cewa, ya zama wajibi a ba da goyon baya mai dorewa ga kasashendake sahun gaba wajen fuskantar irin wannan matsala na yankin Sahel,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ko kun san tanadin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya yi game da Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa da ayyukansa da alhakin da ya rataya a wuyansa? Kundin na tsarin mulkin ƙasa shi ne dai kundin dokoki mafi ƙarfi a Najeriya wanda ya ƙunshi tanade-tanade a kan dukkan al’amuran da suka shafi alhakin da ya rataya a wuyan shugabanni da ma al’ummar ƙasa. Kuma kamar yadda ya tanadi yadda ake gudanar da dukkan al’amuran ƙasa, haka ya ayyana ƙarfin ikon da kowane shugaba yake da shi, da iyakarsa da ma yadda zai iya miƙa wannan ƙarfin iko ga wani don gudanar da ayyukansa. NAJERIYA A YAU: Me ya sa matsalar tsaro “ta gagari gwamnati”...
A daren yau ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala ziyarar aiki ta makonni uku a Turai, inda ya gudanar da muhawara da manyan jami’an ƙasa da ƙasa don inganta dangantakar Najeriya a fannin tsaro da ci gaban tattalin arziki. Jirgin shugaban ya sauka ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja da misalin ƙarfe 9:50 na daren ranar, inda ya samu tarɓa daga manyan jami’an gwamnati, ciki har da Sakataren Gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Shugaban Ma’aikatan Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila; Mai Ba da Shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare, Sanata Atiku Bagudu, da Ministan Birnin Tarayya, Barrister Nyesom Wike. Zuba Jari Daga Kasashen Waje A Noman...
Kasar Cambodiya ce zangon ziyararsa ta karshe. Inda kasashen biyu suka amince da gina al’umma kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani, wanda kamar yadda bangarorin biyu suka jaddada, ya dace da muhimman muradun jama’ar kasashen biyu. La’akari da kalubalan da ake fuskanta a tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kasar Sin ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya. Kuma ziyarar shugaba Xi a kudu maso gabashin Asiya a daidai lokacin da duniya ke fuskantar barazanar bangaranci da daukar matakai bisa radin kai da Amurka ta rike a matsayin makamin mu’amalantar sauran kasashen duniya, ta sa kaimi ga samar da zaman lafiya da wadata a yankin da ma duniya baki daya. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burnley United tare da takwararta ta Leeds United sun samu nasarar dawowa gasar Firimiya bayan samun nasara a mabanbantan wasannin da suka buga. Burnley ta doke Sheffield United da ci 2-1 da yammacin yau domin samun wannan nasarar, hakazalika Leeds United ta samu nasara akan Stoke City da ci 6-0 a daya wasan na yau, dukkan kungiyoyin biyu zasu buga gasar Firimiya Lig ta badi. Alex Iwobi Ya Kafa Tarihi A Gasar Firimiya Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Yayinda kungiyoyin Firimiya Southampton da Leicester City suka koma gasar Championship su kuma Burnley da Leeds United sun samu nasarar tsallakawa zuwa gasar Firimiya a kakar wasa ta badi....
Ya kara da cewa, kowace kasa za ta yi asara idan an gudanar da cinikin duniya bisa ka’idar fin karfi. Sin na fatan kara hadin gwiwa da sauran kasashe don tinkarar kalubale tare da yaki da babakere, ta yadda za su kare muradunsu bisa adalci da daidaito.(Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
A ranar Litinin ɗin nan aka wayi gari da fastocin takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 na Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. An liƙa fastocin wuri-wuri da suka haɗa da shataletale da turakun wutar lantarki da allunan tallace-tallace daban-daban a wasu manyan tituna da ke ƙwaryar birnin na Bauchi. HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa fastocin masu ɗauke da saƙon “Kaura for President” an manna su a wasu manyan hanyoyi da suka haɗa da titin jirgin ƙasa, Sabon Titin Karofi da kuma Ƙofar Dumi. Ɗaya daga cikin matasan da ke aikin manna fastocin, Aminu Auwal, ya shaida wa Aminiya cewa wasu...

Darajar Cinikin Sarin Kaya Da Sayen Kayan Masarufin Sin Ta Karu Da Dala Biliyan 452.5 a Rubu’In Farkon Bana
Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta tabbatar da tsare-tsaren da kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar suka tsayar don gaggauta kyautata tsarin tafiyar da ciniki daidai da zamani, da ingiza ingantaciyar bunkasuwar cinikin sarin kaya da sayen kayan masarufi bisa matakai daban-daban. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar Sin ta fitar a rubu’in farko wato daga watan Janairu zuwa Maris na bana, darajar wadannan bangarori ta karu da dalar biliyan 452.5 a wadannan watanni uku, wanda ya karu da kashi 5.8% bisa na makamancin lokacin bara, kana adadin ya kai kashi 10.4% bisa na dukkan GDPn kasar. Nagartacciyar bunkasar wadannan sana’o’i na nuna goyon baya na tsarin habaka bukatu cikin gidan kasar da tafiyar da tattalin...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu na yau za yi magana dangane da “Rage kisasfin kudan ma’aikatar harkokin wajen Amurla da kimani kasha 50% da kuma tasirinsa ga matsayin Amurka a duniya da kuma cikin gida. Wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan, rahe kasafin kudi na ma’aikatar harkokin wajen kasar da kasha 50%, saboda haka kuma ya rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancin kasar da kananan ofisoshin jakadancin kasar fiye da 30 a yankuna daban daban a duniya amma mafi yawansu a nahiyar Afirka. Dangane da wannan matakin da gwamnatin kasar Amurka masana daga ciki ga wajen kasar ta Amurka masu yawa...
Kasashen Masar da Kuwaiti sun fitar da sanarwa a yau Litinin ta yin tir da kiraye-kirayen da wasu yahudawa masu tsattsauran ra’ayi suke yi domin a rusa masallacin kudus, suna masu yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa domi a tsayar da tsokanar da Isra’ilawa suke yi. Kasashen biyu dai sun fitar da wannan sanarwar ne bayan da wasu yahudawa su ka watsa wani faifen bidiyo na tarwatsa masallacin Kudus da kuma maye gurbinsa da gina wajen bautar yahudawa. Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta bayyana cewa: “Jamhuriyar Larabawa ta Masar tana yin tir da kakkausar murya akan kiraye-kirayen da masu tsattsauran ra’ayin ‘yan share wuri zauna suke yi na tarwatsa masallacin Kudus. Haka nan kuma Masar din ta yi kira...
A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya. Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce ta kalubalantar yadda ake take hakkin bil’adama a duniya, musamman mai dai yadda ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa a Gaza. Haka nan kuma yadda ya rika yin kira da HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi, da kashe mata da kananan yara. Fizishkiyan ya kuma kara da cewa; Wadannan matakan da Papa Roman ya dauka...
Har ila yau, rahoton ya nuna cewa, yayin da adadin yabanya ke karuwa a cikin gida, kuma karuwar bukatunsu ke raguwa, akwai hasashen raguwar bukatar shigo da nau’o’in amfanin gona cikin kasar daga ketare. (Mai Fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar kula da kasuwannin kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, adadin kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin ya zarce miliyan 57 ya zuwa karshen watan Maris, wanda ya kai kaso 92.3 bisa dari na jimillar baki daya. Kazalika, a rubu’i na farko, adadin sabbin kamfanoni masu zaman kansu da aka kafa a kasar ya kai miliyan 1.979, wato karuwar kashi 7.1 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, kuma ya zarce matsakaicin ci gaban da aka samu a shekaru ukun da suka gabata. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...