2025-02-21@14:57:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 238
«Wasannni»:
A nasa jawabin, Jatau ya bayyana cewa, duk da cewa kisan da aka yi wa wani malamin addini lamari ne mai ban tausayi, amma babu wata kwakkwarar shaida da ke alakanta lamarin da wata kungiya, addini ko kabilanci. Ya tuna irin abubuwan da suka faru a baya inda daga baya aka gano wadanda suka aikata...
Sauran su ne tsohon dan majalisar wakilai Hon. Godfrey Ali Gaiya da ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Jaba a majalisar dokokin jihar Hon. Henry Marah Zakarieh da sauransu. Gwamna Uba Sani ya godewa shugabannin jam’iyya a jihar bisa kokarin da suke na jawo mutane zuwa jam’iyyar sannan ya sake jaddada aniyar Gwamnatinsa na ci...
An Kammala Gasar Wasannin Lokacin Hunturu Ta Kasashen Asiya A Harbin
Ya ce kungiyar ta lura da yadda ake samun karuwar wasu cututtukan daji da aka yi watsi da su a Nijeriya kamar cutar Kansar colo-rectal, yara, obarian, da kuma ciwon daji na jini. Ya yi kira ga ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya, da ta mai da hankali sosai kan cutar daji da aka...
Jakadun kasashen larabawa da kuma na wasu kasashen duniya sun bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na korar Falasdinawa daga yankin Zirin gaza, saun kuma bayyana hakan a matsayin wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa. Shirin Trump na korar Falasdinawa daga Gaza dai ya fusata kasashen duniya musamman kasashen larabawa...
CBN ya ci gaba da cewa, dole ne dilolin su sayar da kudaden musayar ga masu hada-hadar sayar da kudaden, daidai da farashin kasuwar musayar kudade ta kasa, wato NFEM, musamman don a tabbatar da ci gaban tafiyar da farashin. Bankin ya kuma sanya kashi daya a cikin dari a tsakanin farashin da masu musayar...
Kasar Iran ta bayyana cewa: Barazanar gwamnatin mamayar Isra’ila ga jirgin saman da ke dauke da fararen hula na Lebanon cin zarafi ne ga ‘yancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine kan barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar...
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Zhang Xiaogang ya fitar da sanarwa kan batutuwan da suka shafi aikin soja a baya-bayan nan. Ya ce, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin. Kuma babu wata tsokana da sojojin Amurka za su yi da za ta iya canza wannan lamari, sabanin haka, za ta iya nuna...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kammala ziyarar da yake yi a Birtaniya. Kakakin ma’aikatar Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce ziyarar ta Wang Yi ta cimma nasara da kyawawan sakamako. Ya ce wannan shi ne karon farko da ministan harkokin wajen...
Cibiyar Ilimin Mata Ta Shirya Wa Sarakuna Da Malamai Taron Inganta Karatun Mata A Kaduna
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) karkashin jagorancin shugaban kasa Alhassan Yahaya, ta jaddada aniyar ta na inganta aikin jarida da kuma jin dadin ‘yan jarida a fadin Najeriya. Kungiyar tana aiki tukuru don ganin an zartar da kudurin dokar inganta kafafen yada labarai a majalisar dokokin kasar don karfafa masana’antar. A cikin...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A...
Binciken shiyya-shiyya na ayyukan ya nuna cewa shiyyar Kudu-maso-Kudu ta geo-siyasa ce ta kan gaba a jadawalin ayyuka 114 da aka yi watsi da su, inda Jihar Akwa Ibom ke kan gaba da ayyuka 87. An nakalto cewa kawo yanzu gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya zuba Naira biliyan 47.93 cikin ayyuka 36 na...
Tawagar ta tattaro hukumomi da suka hada da hukumar kula da yanayi (NiMET), hukumar kula da ayyukan ruwa, da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa. Wannan yana tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (OCHA). A duk duniya, OCHA, wacce ke...
“Ba wai kawai sun fatattake su ba ne, sun kwace makamansu, kuma tun a wancan lokacin, har yanzu, zai yi wuya ka ji wani labarin mahara a Tafawa Balewa, don haka, shawo kan kalubalen tsaro, dole sai an saka duk wasu masu ruwa da tsaki a cikin lamarin. “Tsammanin sojojin Nijeriya, ‘yansanda, ko DSS,...
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100...
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Li Qiang, zai halarci bikin rufe gasar wasannin lokacin hunturu ta kasashen Asiya karo na 9, wanda za a yi gobe Juma’a a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang na kasar Sin. Li Qiang zai kuma shirya liyafar maraba da shirye shiryen da suka...
Kwamandan sojan na Iran Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa, Iran tana da cikakken shirin na aiwatar da umaranin babban kwamandan sojin kasa, kuma akidarmu ta yaki, ta ginu ne akan kariya, amma kuma a lokaci daya za mu fuskanci duk wanda ya kawo mana hari, da karfi. Birgediya janar Hamid Wahidi ya bayyana...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bankaɗo ma’aikatan bogi 2,363 da ke karɓar jimillar N193,642,097.19 a kowane wata bayan gudanar da tantancewar ma’aikatan gwamnati. Gwamna Dauda Lawal ya kafa kwamitin tantance ma’aikata a watan Agustan bara don tabbatar da biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000. Kakakin gwamnan, Sulaiman Idris, ya bayyana cewa binciken ya nuna akwai ƙananan...
Yan wasa 11 na farko da Fc Porto za ta yi zubi dasu: Svilar, Mancini, Hummels, Ndika, Saelemaekers, Kone, Paredes, Angelino, Dybala, Pisilli, Dovbyk

Shugaban kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Son Shiga Yaki Amma Tana Shirye Wajen Fuskantar Barazana
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Bayyana Rashin Amincewarta Da Shiga Tattaunawa Karkashin Matsin Lamba
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba,...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da barazanar da Isra’ila da Amurka ke yi kan batun musayar fursunoni. Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya fada cewa Isra’ila tana kaucewa aiwatar da wasu tanade-tanade na yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” yana mai gargadin cewa ba za a sako mutanen da ake garkuwa da su ba...

Jagoran Ya Ce: Fitowar Mutane A Ranar 11 Ga Watan Fabrayru Alamace Ta Hadin Kan Kasa Sannan Jawabi Ga Barazanar Da Kasar Take Fuskanta
A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama...

Amurka Tana Son Ta Maida Rasha Da China Gefe A Duk Wata Tattaunawa Ta Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Iran
Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya...
Hukumar kula da ‘yan sama jannati na kasar Sin (CMSA), a yau Laraba, ta bayyana sunayen tufafin ‘yan sama jannati da motar zirga-zirga a duniyar wata na aikin binciken wata na kasar. CMSA ta ce, an sa ma tufafin na ‘yan sama jannati suna Wangyu, wanda ke nufin kallon duniyar sama, kuma ya yi daidai...

Kungiyar Hamas Ta Godewa Kasashen Duniya Wadanda Suka Ki Amincewa Da Shirin Trump Na Korarsu Daga Gaza
Kungiyar Hamas a Gaza ta godewa kasashen duniya musamman kasashen Jordan da Masar dangane da kin amincewarsu da korar Falasdinawa a Gaza. Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai kwace zirin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan zai tsugunar da su a kasashen Masar da kuma Jordan, suna so ko basa so....
Al’ummar Jihar Jigawa sun yi kira ga Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi da ya yi amfani da kyawawan tsarin da gaskiya wajen zabar wadanda za su ci gajiyar shirye-shiryen bada tallafin karfafa sana’o’i. Sun kuma bukaci gwamnatin jihar da ta yi amfani da tsarin bayar da tallafin karfafa al’umma ma gwamnatin tarayya na (FADAMA)...
Wakilin LEADERSHIP Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi
Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace...
Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan...
Wakilin LEADERSHIP Hausa Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Sake gina Gaza na bukatar kudi sama da dala biliyan 53 Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya fada a ranar Talata cewa: Sake gina yankin Zirin Gaza da yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya lalata yana bukatar kudi sama da dala biliyan 53, ciki har da sama da dala...
Sin Ta Ayyana Matakan Bunkasa Harkokin Sayayya Da Zuba Jarin Waje

’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato...
An ce, tsakanin shekarar 2000 zuwa 2023, kasar Sin ta samar da rance da yawansa ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 43 ga kasashen Afirka, don su raya bangaren samar da wutar lantarki. Kana a shekarun nan, kamfanonin kasar Sin sun gudanar da dimbin ayyukan samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka, kamarsu madatsar ruwa...
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa matukar Falasdinawa ba su saki fursunonin Isra’ila ba daga nan zuwa Asabar, to za a kawo karshen tsagaita wutar yakin da aka yi, da komawa yaki. Shugaban kasar ta Amurka ya shata wa’adin 12: 00 Na ranar Asabar a matsayin lokacin karshe na mika fursunonin. Shugaban...
Wani sanatan Amurka yana barazana ga shugaban kasar Tunisiya da neman rusa nasarar dimokuradiyyar kasar Sanatan Amurka Joe Wilson, dan majalisar wakilai daga shiyar kudancin jihar Carolina, ya kaddamar da hari kan shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id, inda ya dauke shi a matsayin “dan mulkin kama karya” tare da yin kira da a kakabawa Tunisiya...
3. Wallafa labarin a kasan wannan sanarwar a ɓangaren tsokaci. 4. Wallafa labarin a shafinka na sada zumunta na facebook tare da makala #tak na #GasarLabarunSoyayya #LeadershipHausa #GasarLeadership 5. A kiyaye ƙa’idojin Rubutun Hausa da kuma amfani da daidaitacciyar Hausa da aka amince a yi amfani da ita a hukumance. 6. Ka tabbatar ka sanya...
Babban hafsan hafsishin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Bakri ya bayyana cewa sojojin Iran a shirye suke fiye da ko wani lokaci don kare JMI daga makiyanta. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Bakiri ya bayyana haka ne a lokacinda yake tattaki na bukukuwan cika shekaru 46 da nasarar juyin juya...
Sam Nujoma, dan gwagwarmaya neman yencin kasar Namibiya karkashin gwamnatin wariyar launin fata ta Afrika ta kudu, ya rasu a jiya Lahadi kamar yanda gwamnatin kasar ta Namibi a ta bada sanarwa. Shugaban kasar ta Namibia mai ci, Nangola Mbumba ya ce tsohon shugaban kasar ya na jinya a as wani asbiti a babban birnin...
An yi wa dubban mutane gwajin lafiya kyauta a Indonesiya don kauce wa mutuwa da wuri. Za a yi gwajin ga ɗaukacin ‘ƴan kasar ne a ranar murnar bikin haihuwarsu, domin cika alkawarin da shugaba Prabowo Subianto ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe. Jarirai da ƙananan yara da kuma tsofaffi na cikin waɗanda za a...
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta gabatar da kayan agaji ga gwamnatin jihar Zamfara domin tallafawa wadanda gobara ta shafa a wata makarantar Islamiyya da ke Kaura Namoda. A lokacin da take mika kayayyakin, Darakta Janar na Hukumar Hajia Zubaida Umar, ta ce matakin ya nuna damuwar gwamnatin tarayya kan halin...
Duk da cewa, cikakken bayani kan wannan ziyara bai fito fili ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, LEADERSHIP ta tattaro cewa, ganawar ba za ta rasa nasaba da burin Atiku na tsayawa takarar shugabancin Nijeriya ba a zaben 2027 mai zuwa. Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, manyan ‘yan siyasar ba su...
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan ziyara ta gwamnan, za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Bankin na Duniya. Cikin jawabin sa a wurin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa dangantakar ta Bankin Duniyar. “Ina so in fara da nuna godiya ta ga Bankin Duniya game...

Kasafin 2025: Kar A Yi Sakaci Macizai Da Birai Su Haɗiye Dala Biliyan 1.07 Da Aka Ware Wa Kiwon Lafiya – Atiku
Ya kuma yi kira da a samar da tsari na gaskiya da rikon amana don bin diddigin yadda ake kashe kudaden da aka ware domin amfanin jama’a.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi kokarin dakile duk wani makirce-makircen da makiya ke kitsawa. Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga dimbin jama’a da suka halarci bikin cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a shekara ta...

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Ce: Hamas Ta Yi Rawar Gani Wajen Kare Kanta
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da...
Wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda (ASP), Shafi’u Bawa, da ke aiki da Rundunar 61 Police Mobile Force a Kontagora da ke Jihar Neja, ya hallaka kansa har lahira. Wani jami’in dan sanda ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar. Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu Aisha...
A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi...