2025-03-31@13:59:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1107

«radiyo»:

    Gwamnatin kasar Amurka tana shirin dakatar da bada kudade ga hukumar GAVI wacce take samar da alluran riga kafi don tallafawa kasashe masu tasowa daga ciki har da tarayyar Najeriya. Jaridar Daily Trus ta Najeriya ta nakalto wata sanarwa daga hukumar USAID bayar inda take cewa gwamnatin shugaba Donal  Trump yana son janye tallafin da...
    A yayin da ake tunkarar bikin ƙaramar sallah, hankalin Musulmi a ko ina a duniya, ya karkata zuwa ga hidimar wannan rana ta musamman, musamman a fannin ado da sabbin kaya. A wata ziyarar da Aminiya ta kai babbar kasuwar tufafi da kayan ado ta Kwari da ke Kano, ta tarar da kasuwa cike maƙil...
    Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin  raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci,...
    Manzon musamman na ministan harkokin wajen Iran a kan Syria, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya gana da karamin minista a gwamnatin kasar Katar inda su ka tattauna halin da ake ciki a kasar Syria, haka nan kuma sun jaddada wajabcin shigar da dukkanin bangarorin al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da gwamnati. A jiya Laraba...
    Majalisar Dattawa, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya. A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong (APC – Kuros Riba), ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200....
    Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke...
    Majalisar Dinkin Duniya ta nuna fargaba kan yadda ake ci gaba da samun karuwar matsalar jin kai a zirin Gaza, inda ta bayar da rahoton cewa akalla Falasdinawa 142,000 ne suka rasa matsugunansu a cikin mako guda kacal saboda tsanantar hare-haren bama-bamai na Isra’ila. Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya bayyana a wani taron manema labarai...
    Bayanai daga falasdinu na cewa an kashe Hamas Abdul-Latif al-Qanou wani kakakin kungiyar Hamas a wani harin da Isra’ila ta kai a arewacin Gaza. Kamfanin dillancin labaran Quds na Falasdinu ya bayar da rahoton  cewa, jami’in ya yi shahada ne a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa a garin Jabalia...
    A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Masu zanga zangar sun kuma bukaci a tsagaita bude wuta da kuma sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza. Sun rike alluna masu dauke da hotunan wadanda  ake tsare da su a Gaza...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu. A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira hadin kan kasashen duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinu gabanin ranar Kudus ta Duniya. Kungiyar ta yi kira da a samar da hadin kai a kasashen duniya a ranar Juma’a da Asabar da Lahadi masu zuwa domin nuna goyon baya ga Gaza da Kudus, yayin da...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga al’ummar kasar da su nuna hadin kai a yayin bukukuwan ranar Kudus ta duniya wato ranar JUma’ar kashe ta watan Ramadana da ke gabatowa, yana mai jaddada cewa hakan zai nuna matukar goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Falastinu. Pezeshkian, ya bayyana hakan ne...
    Kantoman Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya dakatar da dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da jami’an gwamnatin jihar nan take. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Ibas, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa izinin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi. Gwamnatin Tarayya ta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, da dama daga cikin matasan Najeriya na fama da matsaloli masu tarin yawa, musamman wajen ciyar da kansu da biyan buƙatunsu na yau da kullum. Wannan na faruwa ne sakamakon halin da tattalin arziƙin ƙasa ke ciki, rashin aikin yi, da kuma tsadar rayuwa. NAJERIYA A...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce kasar Amurka ta yi amfani da batun kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje, kamar jerin sunayen kamfanoni, wajen sanyawa sauran sassa takunkumai bisa hujjar “barazana ga tsaron kasa, da kuma keta manufofin diplomassiyar Amurka”, wanda hakan ya zama wani babban mataki na nuna fin...
    Sanarwar ta umarci dukkanin waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar aiki ga Sakatarorin ma’aikatun da suke jagoranta. Idan babu Sakatare, sai miƙa ragamar ga babban Darakta mafi girma ko Shugaban Harkokin Gudanarwa. Wannan umarni zai fara aiki daga ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300...
    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 27 da buhunan shinkafa 300 ga mutanen da gobara ta shafa a ƙananan hukumomi uku da ke mazaɓarsa a Jihar Yobe. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Machina, Nguru, da Yusufari. An kama mutum 3 kan zargin sata da...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wasu mutum uku da ake zargi da laifin sata da kuma ƙone gidan wani Bature a unguwar G.R.A, kusa da gidajen ’yan majalisa a jihar. Waɗanda aka kama sun haɗa da Hannatu Ibrahim mai shekaru 28 daga Kumo, Ahmed Adamu mai shekaru 20, da Abubakar Ibrahim mai shekaru...
    Darakta a ofishin lura da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da mataimakin shugaban kwamitin kasa na Amurka mai lura da alakar Sin da Amurka Evan Greenberg. Yayin da suke zantawa a yau Laraba, Wang ya jinjinawa Greenberg, bisa tsawon lokaci da ya shafe yana ingiza...
    Mai Magana da yawun gwamnatin Iran malam Fatima Muhajirani ta yi ga al’ummar Iran da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin halartar jerin gwanon ranar Kudus ta duniya, wacce take fatan ganin ta taka rawa wajen taimakawa al’ummar Falasdinu. Muhajirani wacce ta yi bayanin haka a wata hira ta tashar talbijin ta kuma kara da...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya amince da bukatar ma’aikatar shari’a na yin afuwa ga wasu fursunoni sannan kuma da rage yawan shekarun wasu na zaman gidan kurkuku. Yin afuwar ga fursunonin dai ya zo saboda shiga sabuwar shekarar hijira shamshiyya ta 1404 da kuma karatowar karamar salla ra 1446. Bugu...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su....
    Aƙalla mutum biyu ne suka rasu, yayin da wani ya jikkata a wani hatsarin mota da ya auku kusa da Sinimar Eldorado da ke kan titin zuwa Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar da faruwar lamarin. Gidauniyar Daily Trust da WRAPA sun ’yanta fursunoni 21 a Kaduna...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin...
    Gidauniyar Daily Trust (DTF) tare da haɗin gwiwar ƙungiyar WRAPA, Hamu Legal, da Bahama Chambers, sun biya tarar fursunoni 21 domin su samu damar fita daga gidajen gyaran hali a Jihohin Kaduna da Katsina. A Kaduna, an ’yanta mutum 17 bayan da DTF da abokan aikinta suka biya tarar su har Naira miliyan biyu da...
    Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a...
    Ko da yake an samu rage yawan hare-haren Boko Haram a baya-bayan nan, rahotanni na nuna cewa suna ƙara kai hare-hare kwanan nan. Tun daga shekarar 2009, rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 200,000 tare da tilasta wa miliyoyin mutane tserewa daga gidajensu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi...
    Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi...
    Bayan gazawar tattaunawar da hukumar ta IAEA ta yi da Tehran, babban daraktan hukumar Rafael Grossi ya jaddada muhimmancin komawa kan teburin shawarwari nan gaba don tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta ce tattaunawar da ta yi da wani babban jami’in...
    Aƙalla mutum 24 ne suka rasu a wata gobarar daji mai muni da ta auku a tarihin Koriya ta Kudu baya ga mummunar ɓarna da ta haddasa. Mukaddashin shugaban ƙasar ya sanar a ranar Laraba cewa wutar dajin ta rabu kashi daban-daban har fiye da goma tun ƙarshen mako, inda ta laƙume wasu yankunan kudu...
     Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya yi murabus daga mukaminsa. An tabbatar da murabus din nasa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar. Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da...
    Manjo-Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, ya yi murabus. Wannan dai na zuwa ne bayan shafe watanni bakwai kacal da karɓar muƙamin. Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Mustapha Muhammad ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Larabar....
    Fadar Gidan Gwamnatin Amurka (WhiteHouse), ta ce Rasha da Ukraine sun amincewa Jiragen jigilar kayayyakin kasuwanci gudanar da zirga-zirga cikin aminci a tekun Black Sea ba tare da kai musu hare-haren soji ba. Amurka ta fitar da wannan sanarwar ne bayan jami’an Amurka sun gana da wakilan kasashen biyu a Saudiyya a ranar Talata. Dole...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan wasikar da shugaban Amurka Donald Trump ya aike kan shirin nukiliyar Iran ba. Sai dai ya ce ana shirin mayar da amsa kuma za a mika ta hanyoyin da suka dace nan ba da jimawa ba....
    Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen...
    Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen ƙetare (NIDCOM), ta bayyana cewa an kuɓutar da ‘yan Nijeriya 956 daga gidajen yarin Libya tare da mayar da su gida cikin watanni ukun farkon shekarar 2025. Shugabar hukumar, Hon. Abike Dabiri-Erewa, ta ce waɗanda aka dawo da su sun haɗa da mata 683, maza 132, yara 87,...
    A yanzu nan ne Aminiya take samun labarin rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Baba Ƙarƙuzu ko Ƙarƙuzu na Bodara. Hakan dai na kunshe ne cikin wani sako da jarumi a masana’antar Kannywood kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya wallafa a shafinsa na Instagram. SShi...
    Hakan ya sa, rundunar FOB ta yi kira da akawo musu dauki ta sama baya ga aikewa da karin tawaga ta kasa domin tallafawa. Duk da haka, tawagar ta sake cin karo da Bam a kan hanya.   Duk da cewa, ba a samu cikakken bayanin harin ba a lokacin rubuta wannan rahoton, amma an...
    Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta gamu da cikas a ƙoƙarinta na neman yankar tikitin shiga Gasar  Kofin Duniya ta baɗi, bayan da ta tashi canjaras 1-1 da Zimbabwe. Victor Osimhen ne ya fara ci wa Nijeriya kwallo a minti na 74 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa...
    Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen...
    Hukumar zaɓen Nijeriya (INEC), ta bayyana cewa ƙorafin da aka gabatar kan batun yi wa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti Uduaghan kiranye bai cika ƙa’ida ba. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan bayanai da wayar da kan al’umma na  hukumar, Sam Olumekan, ya fitar a yau Talata. Dalilin...
    A ƙoƙarinta na tallafa wa marayu da mabuƙata, gidauniyar Zakkah da Wakafi a Gombe ta raba wa yara marayu da mabuƙata 100 kayan Sallah. Da yake jawabi a lokacin rabon tufafin, Shugaban gidauniyar, Amir Abdullahi Abubakar Lamido, ya ce al’adar gidauniyar ce ta riƙa zaƙulo mabuƙata tare da tallafa musu musamman a lokutan bukukuwan Sallah....
    A zantawa ta water tarho ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Turkiya sun bukaci kasashen musulmi su magance matsalar jinkai da kayakin agaji na Falasdinawa a kasarsu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Hakan Fidan na kasar Turkiya da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi suna fadar haka...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya musanta zargin kasar Amurka na cewa wasu jiragen ruwan JMI suna amfani da tudan kasar Iraqi sun kai kawo a ruwayen yankin. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fadawa Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran, kan cewa Aragchi yana fadar haka ne a jiya litinin, a...