2025-04-29@15:49:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 776
«Wamban Kano»:
Ba wannan ne karo na farko da shugaba Trump ya nuna girman kai da rashin sani game da Afirka ba. A watan da ya gabata, lokacin da yake bayani game da dalilin da ya sa gwamnatinsa ke rage gudummawar jin kai da take bayarwa a duniya, ya ce a baya, Amurka ta samar wa kasar Lesotho gudummawar dala miliyan 8, amma “ba wanda ya taba jin sunan wannan kasa”. Amma ita wannan kasar da ko sunanta shugaba Trump bai taba ji ba, ya sanya ta cikin jerin kasashen da ya sanar da zai kakaba musu haraji, har ma ya sanya mata haraji na kaso 50%. Idan ba mu manta ba kuma, a wa’adin shugabancinsa na farko, shugaba Trump ya taba...
Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu. A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0. Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta, ya taɓa buga wasa a duka ƙungiyoyin. Yana fatan ya zama kocin farko da zai jagoranci Arsenal ta lashe kofin Zakarun Turai. Wannan ya sa magoya bayan Arsenal ke fatan ganin ƙungiyarsu ta yi abin mamaki a wasan da za a fara da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
“Lokacin da abubuwa suka fara lalacewa a lokacin shugaba Buhari, na fito na faɗi gaskiya. Lokacin da tsarin sauya fasalin Naira ya jefa jama’a cikin wahala, na ƙalubalanci gwamnati duk da cewa jam’iyyar APC ce ke kan mulki. Na fi biyayya ga Nijeriya fiye da kowane mutum,” in ji shi. El-Rufai ya ƙaryata jita-jitar cewa fushinsa da gwamnatin Shugaba Tinubu ne ya sa ya fice daga APC. Ya ce yana da shekaru 65, kuma babu wani abu da ya rage masa a siyasa da zai nema, sai dai kawai yana jin cewa matsalolin Nijeriya sun yi tsanani sosai wanda ba zai zauna ya yu shiru ba. “Zan iya yin ritaya cikin kwanciyar hankali, amma Nijeriya na fuskantar babbar barazana. Wannan...
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne. Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin. A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’imKasim ya bayyana cewa, kungiyarsa tare da Sojojin kasar da kuma mutanen kasar ne zasu tabbatar da ci gaban kasar Lebanon a wannan halin da ake ciki. Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta nakalto sheikh Na’im kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Litinin, jawabinda kafafen yada labarai da damaa suka watsa kai tsaye. Sheikh Qasim kasar Lebanon zata ci gaba da zama mai karfi idan gwamnatin kasar ta dakatar da hare-haren da HKI take ci gaba da kawowa a kan kasar, da kwato dukkan yankunan kasar da aka mamaye, har’ila yau da kuma ci gaba da hadin kai tsakanin masu gwagwarmaya, sojoji da kuma mutanen kasar. Shugaban kungiyar...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da shirin rigakafin mahajjata na shekarar 2025 a yankin Hadejia da ke shiyyar arewa maso gabas ta jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Hadejia. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jaddada kudirin hukumar na ba da fifiko ga lafiya da kuma tsaron mahajjatan jihar. Ya ce, kare lafiyar mahajjatan jihar nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar. “Shirin rigakafin da muka fara yana nuna shirinmu na tabbatar da nasarar aikin Hajjin shekarar 2025. Ina ƙarfafa mahajjata su ba da haɗin kai tare da bin ƙa’idojin lafiya yayin wannan tafiya mai albarka.” “Ina kuma ƙarfafa ku da ku zama masu bin doka da...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin cewa, babu wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a baya-baya nan, haka kuma bangarorin biyu ba su cimma wata yarjejeniya ko su tuntubi juna game da batun haraji ba. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan kasuwa na duniya da su shiga harkokin tattalin arziki da zuba hannun jari a Iran. A yayin bikin bude baje koli karo na bakwai na baje kolin kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa kasashen ketare (Iran Expo 2025) a safiyar yau Litinin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi maraba da baki na kasashen waje da suka halarci wannan baje kolin, yana mai cewa, “Ko...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas ga manufofinta na ketare. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Rudun gwamnatin yahudawan sahayoniyya, wadda take ganin za ta iya gindaya wa Iran abin da ya kamata ko kuma bai kamata ba, rudun tunani ne da ya yi nesa da hakikanin gaskiya, ta yadda bai cancanci mayar da martani ba. Araqchi ya kara da cewa: “Duk da haka,...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin da ta gabata, Araqchi ya bayyana ci gaba da killace yankin Gaza da rashin abinci da magunguna, tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin dan Adam. Ya dauki Amurka da sauran masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya a matsayin masu hannu a kisan kiyashi da laifukan yaki...
Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada wajabcin komawa kan Shirin tsagaita bude wuta a Gaza Wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman ta jaddada a yau Litinin cewa: Akwai tsananin bukatar komawa ga Shirin tsagaita bude wuta a Gaza. A lokacin da take ba da shaida a zaman kotun kasa da kasa kan wajabcin da ya hau kan haramtacciyar kasar Isra’ila na kiyaye hakkokin mazaunan yankunan Falasdinawa, ta jaddada wajabcin isar da kayayyakin agajin na gaggawa ga Zirin Gaza, inda ta bayyana cewa: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres na yin duk wani kokari na kawo karshen matsalar jin kai da fararen hula ke fuskanta a yankunan Falasdinawa da aka mamaye da yankunan Falasdinawa da ba a mamaye ba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Saboda haka, Litinin 28 ga Afrilu, 2025, za ta kasance 30 ga Shawwal 1446AH, yayin da ranar Talata 29 ga Afrilu, 2025 za ta zama farkon watan Zulki’ida 1446AH.” Sanarwar ta ci gaba da cewa, Sarkin Musulmi na mika sakon fatan alheri ga al’ummar Musulmi, ya kuma bukace su da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani wanda ake zargi da safarar sassan jikin ɗan Adam ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya shafe sama da shekara 10 yana sayar da sassan jikin mutum don samun kuɗi. Dubun mutumin sun cika ne a ranar Asabar din da ta gabata inda sojoji suka kama shi a yankin Kulanla Odomoola da ke Jihar Ogun. A furucinsa da ya amsa laifin, wanda ake zargin ya amince da sayar da sassan jikin mutum ga masu buƙata don samun kuɗin shiga. “Na dogara ne da sayar da sassan jikin mutum tsawon shekaru 10 da suka gabata. Yawancin sassan da nake sayarwa ina tono su ne daga sabbin kaburbura a makabartu, yayin da wasu kuma nake samun su daga gawarwakin da aka...
A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya. Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu. Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata, jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National ” bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Ya kuma bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta gabatar da duk wani taimakon da JMI take bukata a yayin tattaunawar. A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta...
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar. “Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa. “Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne. “Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kawar da ta’addanci ta hanyar hadin kan kasashen yanki Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai a birnin Pahalgam na kasar Indiya, tare da nuna alhini da juyayinsa ga gwamnati da al’ummar kasar Indiya, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin domin yakar ta’addanci da kuma tsayawa tsayin daka kan wannan barazana ta bai daya. Pezeshkian ya zanta ta wayar tarho a yammacin jiya Asabar da fira ministan kasar Indiya Narendra Modi, inda suka tattauna kan sabbin al’amuran da suke faruwa a yankin na Indiya, da kuma alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Indiya.
Bugu da kari, an fi samun kyautatuwa a bangaren samar da kayayyaki, inda yawan ribar da aka samu a farkon watanni 3 na bana ya karu da 7.6%, saurin karuwar ya kai 2.8%. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu. “Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.” Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura. “Za a gudanar da babban taron karramawa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa, domin naɗin sabbin muƙamai da Masarautar Daura za ta yi.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
A wata hira da Jammaje ya yi da rfI Hausa an jiyo shi ya na cewa sunana Kabiru Musa Jammaje haifaffen Jihar Kano, nayi karatu a Bayero Unibersity da ke birnin Kano inda na karanci English kafin in tafi kasar Amurka domin zurfafa karatu, bayan na dawo gida Nijeriya kuma na shiga Jami’ar koyo daga gida ta NOUN inda na karanci ‘Education Administration and Planning’. Jammaje ya ci gaba da cewa a yawace yawacen da na yi na tafi kasashe irinsu Afirika Ta Kudu da kasar Kenya inda a wancan lokacin sai na lura cewa mutanen wadannan kasashen biyu suna yi wa duk wani dan Nijeriya wani kallo na daban sakamakon abin da suka ga ana nunawa a wasu...
“Muna kira ga sauran kungiyoyi, ‘yan siyasa, masu hannu da shuni tare da gwamnatoci, cewa kofarmu a bude take wajen neman taimakon kayan abinci, tufafi da makamantan su.” In ji Goni Alhaji Goni ya kara da cewa, gungiyar su ta direbobi, ta na da mambobin sama da 30,000 a fadin jihar Yobe. Ya ce, kullum suna kan hanya, yau ace wannan ya yi hadari ya karye, gobe wannan ya rasu. “Saboda haka mu na rokon gwamnatin jihar Yobe tare da Hukumar Sake Raya Arewa Masu Gabas da sauran kungiyoyi, su kawo wa marayun mu daukin gaggawa.” In ji shi. A nashi bangaren, Kodinatan YFM a jihar Yobe, Malam Sadiq Muhammad ya ce, sun zabi bai wa marayun...
Sojojin na kasar Yemen sun sake kai hari akan sansanin sojan saman a “Nivatim” na HKI a karo na biyu a cikin sa’o’i 24. Majiyar sojan kasar ta Yemen ta ce wannan shi ne karo na hudu da suke kai hari akan manufofin HKI a cikin sa’o’i 24. Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sa’ri ya fada a wata sanar wa ta tashar talabijin cewa; sojojin kasar sun kai hari da makamai masu linzami da su ka fi sauti sauri wajen kai wa sansanin na “Nivatim” hari wanda yake a cikin yankin Naqab a Falasdinu dake karkashin mamaya. Janar Sari ya kuma kara da cewa; hare-haren da suke kai wa HKI yana a karkashin ci gaba da taya Falasdinawa fada...
Ministan harkokin cikin gidan Iran Askandar Mumini wanda ya kai Ziyara zuwa wurin da gobarar ta tashi ya sanar da cewa adadin wadanda su ka jikkata sun kai 750 da kuma wadanda su ka rasa rayukansu zuwa 14. Sai dai kuma daga baya ma’aikatar shari’a ta kasar Iran din ta ta sanar da karuwar wadanda su ka kwanta dama zuwa 21 Mai shigar da kara na gundumar Hurzumgan, Mujtaba Kahraman ya sanar da cewa; Daya daga cikin aikin da suke yi shi ne tantance wadanda su ka su ka rasa rayukansu. Haka nan kuma ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu sun tabbatar da mutuwar mutane 21. Har ila yau ya bayyana cewa bayan tantance gawawwakin wadanda su ka rasa...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Musulmai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa dukkan mahajjatan da suka yi rijista domin aikin Hajjin 2025 dole ne su gudanar da binciken lafiya cikin wannan mako. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Yunusa Muhammad Abdullahi, ya fitar, inda ya bayyana cewa aikin na da nufin tantance lafiyar mahajjata kafin tafiya wannan tafiya ta ibada. Binciken lafiyar ya haɗa da gwajin ciki na dole ga mata masu shirin zuwa Hajji. Abdullahi ya bayyana cewa wannan mataki ba domin hana kowa yin Hajji ba ne, sai don tabbatar da cewa an tanadi cikakken tallafin lafiya musamman ga mahajjatan da ke fama da cututtuka kamar...
Sunana Fatimah Zahra Mazadu Daga Jihar Gomben Nigeria: Ba abun da ke janyo haka sai sakaci da rashin wayo, ta wani fannin kuma aljihu da halin maza dan suma suna nan a gari, za ka ga wata ta birgeka amma taka ta gida ka gagara kashe mata dan tayi kyau, sannan ba yadda za a yi kina kara girma kina komawa jeji, ai a lokacin da ki ka dade da namiji a lokacin ne ya kamata ki kara wanka akan wanda ki ke dan maida hankalinsa kacokam a kanki, tsabta naki kwalliya naki jan hankali naki. Na daya zai fara hangen na waje, na biyu zai dinga nisanta dake, ko da ko ba mai ra’ayin kwalliya sosai bane, ba zai...
Kwanan nan, wakiliyar CMG ta zanta da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev wanda ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin. A yayin zantawar, shugaba Aliyev ya waiwayi dadadden tarihin cudanyar kasashen biyu da ma zumuncin da ke tsakaninsu, kuma ya yi imanin da cewa, kasancewar dukkansu kasashe masu tasowa ne, kasashen biyu za su hada hannu wajen bayar da karin gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya. Shugaba Aliyev ya ce, “Muna ganin kasar Sin jagora ce ga kasashe masu tasowa na duniya, kuma tana taka rawar gani a wajen hada kan kasa da kasa, musamman ma wajen yayata ruhin Bangdun, ciki har da martaba ikon mulki da cikakkun yankunan kasa na sauran kasashe, da rashin...
“Abin takaici ne ganin yadda jami’an CJTF biyu da aka kashe a ranar Juma’a, sannan kuma wasu mutane 10 da suka je daji neman itace aka kashe su yau. “Mun riga mun birne mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kuma an kwashe waɗanda suka ji rauni zuwa Maiduguri domin nema musu kulawar likitoci,” in ji Sarkin. Ya yi addu’a Allah ya jiƙan mamatan ya kuma bai wa waɗanda suka jikkata lafiya. Sarkin ya yaba wa gwamnati da sojoji bisa ƙoƙarinsu amma ya buƙaci a ƙara amfani da sabbin fasahohin zamani da kayan yaki masu ƙarfi domin yaƙar ‘yan ta’addan. Ya yi gargaɗin cewa waɗannan hare-hare na iya tsoratar da manoma wajen komawa gonakinsu yayin da lokacin shuka ke gabatowa....
Alkaluman zuba jari na kasashen waje sun hau kan mizani mai kyau a rubu’i na farko, a kan hakan kuwa, kasar Sin za ta kara bude kofarta domin maraba da jarin waje na duniya. Har ila yau ana sa ran karin kamfanonin waje za su zuba jari da gudanar da kasuwanci a wannan kasa mai albarka. Lokaci zai tabbatar da cewa, kasar Sin ta taba zama kyakkyawan wurin saka jari da ya dace, kuma tana kasancewa haka ma a yanzu, kana babu makawa a nan gaba za ta ci gaba da zama hakan ga ‘yan kasuwa na kasashen waje. (Mai fassara: Bilkisu Xin) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...

Iran ta Bayyana cewa: TattaunawarMuscat Wata Dama Ce Ta Samun Zaman Lafiya Kan Batutuwan Masu Sarkakiya
Mai ba da shawara ga Jagoran juya juya halin Musulunci kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Tattaunawar Muscat wata dama ce ta samun zaman lafiya kan batutuwa masu sarkakiya Ali Shamkhani mai ba Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin siyasa ya yi tsokaci kan tattaunawar ba na kai tsaye ba da ake yi tsakanin Iran da Amurka a babban birnin kasar Omani na Muscat. A cikin jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na twitter, Shamkhani ya bayyana cewa: Fiye da kwanaki 100 ke nan da Trump ya hau kan karagar mulki, yana mai cewa: “Ba a warware manyan batutuwan da suka shafi Yemen, Gaza, Ukraine, da rikicin haraji ba, baya ga gibin kasafin kudi, har yanzu ba...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da magance cin zarafin da Amurka ke yi ita kadai, ba wai kawai don kare hakki da moriyarta ba, har ma da kiyaye moriyar kasashen duniya. Ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Tajikistan Sirojiddin Muhriddin. Ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi harajin kwastam yayin da suka hadu a birnin Almaty domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen tsakiyar Asiya da kasar Sin karo na shida. Wang, ya nanata cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin tabbatar da gudanar da kasuwanci cikin ‘yanci,...
Zulum ya bayyana wasu matsaloli da ke kawo tsaiko, ciki har da ƙarancin sojoji a yankunan Timbuktu Triangle, Tumbus, tsaunin Mandara, da kan iyakar Nijeriya da ƙasashen Sahel. Ya roƙi Ministan Tsaro da ya turo ƙarin manyan makamai da motocin yaƙi na zamani zuwa Borno domin taimaka wa sojoji. A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura ƙarin kayan aiki da jami’an soja don magance matsalar tsaro a Borno da Arewa Maso Gabas. Ya ce shugaban ƙasa ya umarce su da su tabbatar da samar da duk abin da ake buƙata domin murƙushe ‘yan ta’adda a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...

An Gudanar Da Dandalin Kirkire-kirkire Na Kafofin Watsa Labarai Na Duniya Karo Na 4 A Birnin Qufu Na Kasar Sin
A jiya Juma’a, an gudanar da taron dandalin tattaunawar kirkire-kirkire na kafofin watsa labaru na duniya karo na 4, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice da gwamnatin lardin Shandong dake gabashin kasar Sin suka dauki nauyin shiryawa a birnin Qufu na lardin. Taron dandalin mai taken “Musanya da yin koyi da juna da ma amfani da kimiyya da fasaha na kasancewa karfin wayewar kai a yayin da ake neman sauye-sauye da ci gaba”, ya samu halartar wakilai kusan 300 daga kungiyoyin kasa da kasa da hukumomin watsa labarai na kasashe da yankuna 95, da cibiyoyin masana na kasar Sin da na kasashen waje, da ma kamfanonin ketare da dai sauransu ta...
Gwamnatin Jihar Kano ta gano matsaloli a cikin tsarin albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi, inda aka gano ma’aikata 247 da suka yi ritaya ko kuma sun mutu, amma suna ci gaba da karɓar albashi. Wannan bayani ya fito ne daga cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Musa Muhammad, ya fitar. A cewar sanarwar, wannan bincike ya gudana ne a yayin da ake gudanar da aikin tantancewa domin gyara tsarin albashin ma’aikatan gwamnati a jihar. Har Yanzu Da Akwai Jihohin Da Malaman Makaranta Ke Karbar Albashin Naira 18,000 NLC Ta Yi Zanga-Zanga A Ofishin Wike, Ta Nemi A Biya Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Albashin N70,000 Sanarwar ta bayyana cewa, duk da cewa waɗannan ma’aikatan sun yi ritaya ko...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar kwallon kafa ta PSG – wadda tuni ta lashe gasar League 1 ta Faransa na daya daga cikin kungiyoyin da ake ganin za su lashe gasar Zakarun Turai ta bana saboda karfin da tawagar take da shi sannan kuma kungiyar a gine take hadi da kwararren mai koyarwa, Luis Enrikue, tsohon kociyan Barcelona da Roma da tawagar kasar Spaniya, yana daya daga cikin kwararrun masu horarwa. Kungiyar za ta kara da Arsenal a wasan na kusa da karshe. Wani shahararren masanin wasanni dan kasar Sifaniya, Guillem Balague na ganin PSG ce za ta lashe gasar. ”Suna da duk wani abu da ake bukata domin lashe kofin, sun iya rike kwallo, a yanzu kungiyar na da karfi, tana da...
Manyan kungiyoyin kwallon kafa Barcelona da Real Madrid zasu sake haduwa a wasan da ake yima kallon wasa mafi kayatarwa da akeyi a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a halin yanzu. Manyan kungiyoyin biyu duka na da dadadden tarihin iya taka leda da nuna kwarewa a harkar kwallon kafa, nasarorin da suka samu a kwallo ya sa ana yimasu kallon gagarabadau kokuma ace daukakakkun kungiyoyin kwallon kafa a Duniya. UEFA: Mbappe Zai Jagoranci Real Madrid Yayin Da Ta Ke Fatan Kafa Sabon Tarihi A Santiago Copa Del Rey: Real Madrid Ta Buƙaci A Sauya Alƙalin Wasa A Karawarta Da Barcelona Yau Asabar Barcelona da Real Madrid zasu buga wasan karshe na kofin Copa Del Rey a filin wasa na De La...
Karo na hudu kenan da Arsenal ta kara da Real a kofin Zakarun Turai, inda ta ci uku aka yi canjaras daya. A ranar 29 ga watan Afrilu Arsenal za ta karbi bakuncin PSG a wasan farko, kafin a buga na biyu mako daya bayan haka. Kungiyar dai ita ce a mataki na biyu a kan teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila inda a wannan satin ake saran Liberpool za ta zama zakara a bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bayan ya sake daga sabowar tutar kasar Siriya a cibiyar MDD da ke birnin NewYork ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad Al-shaibani, ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya jumma’a inda ya roki kwamitin ya dagewa kasarsa takunkuman tattalin arziki wadanda aka dorawa gwamnatin da ta shude. Jaridar Middle eart Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Al-shaibani ya na cewa takunkuman suna hana ruwa guda a cikin al-amura da dama a kasarsa, kuma suna hana kafuwar gwamnatinsa su kamar yadda ya dace. Ministan ya ce dage takunkuman ya zama wajibi don samun ci gaban kasar don kuma rage matsin lamban da mutanen kasar suke ciki. Kasashen yamma musamman Amurka da tarayyar Turai da kuma MDD...
Mazauna Ƙauyen Batakashi da ke ƙaramar hukumar Garki a Jihar Jigawa sun yaba wa Gidauniyar Aliko Dangote bisa tallafin abinci da ta kai musu. Wasu daga cikin mazaunan da suka tattauna da wakilinmu sun bayyana farin cikinsu kan wannan karamci, tare da fatan alheri ga gidauniyar. Daya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, Malam Umar Abdullahi, ya ce gidauniyar ta kawo sassauci ga al’umma bayan iftila’in gobara da ya cinye gidaje kusan 45 a kwanan nan. Haka shi ma Malam Usman Auwal, ya nuna farin cikinsa, inda ya yaba da gwamnatin jihar Jigawa da kuma Gidauniyar Dangote, bisa tallafinsu ga al’umma. A jawabinsa yayin kaddamar da rabon tallafin na buhunan shinkafa guda 500 masu nauyin kilogiram10, Shugaban ƙaramar...

A Karon Farko A Tarihi Adadin Lantarki Da Sin Ke Iya Samarwa Ta Karfin Iska Da Hasken Rana Ya Zarce Wanda Ake Iya Samarwa Ta Amfani Da Dumi
Sashen masana’antun samar da sabbin makamashi na kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a shekarun baya bayan nan, a gabar da ake ta aiwatar da managartan matakai na bunkasa tattalin arziki ba tare da fitar da iskar Carbon mai dumama yanayi ba. Tun daga shekarar 2013, adadin kayayyakin samar da lantarki daga karfin iska da aka kafa a Sin sun ninka har sau 6, yayin da na samar da lantarki daga karfin rana suka ninka sama da sau 180. Ya zuwa yanzu, sabbin kayayyakin samar da lantarki ta wannan hanya da ake kafawa duk shekara a kasar Sin, sun kai kaso sama da 40 bisa dari kan na daukacin kasashen duniya, adadin da ya yi matukar ba...
Gwamnan ya bayyana cewa ba za a yi amfani da kudin al’umma ba ga mutanen da ba za su iya kula da mahajjata yadda ya kamata ba. Gwamna Radda ya kara da cewa ya yi taro da shugabannin kananan hukumomi guda 34 domin tabbatar da cewa malaman da suka cancanta ne kadai aka zaba a matsayin masu koyarwa a ayyukan aikin hajjin bana. Ya kuma yi alkawarin kafa kwamitin yada labarai domin yada ayyukan aikin hajjin tare da ba da kulawa ta musaman kan shawarwarin da aka bayar kan rahoton da kwamitin aiki hajjin ya gabatar. Da yake gabatar da rahoton, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Katsina kuma Amirul Hajj, Alhaji Tukur, ya bayyana wasu muhimman batutuwa da...

Kasar Sin Ta Goyi Bayan Rawar Da Hukumar IAEA Ke Takawa Wajen Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diflomasiyya
Li ya kara da cewa, Sin da Rasha sun bayyana goyon baya ga Iran wajen karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da hukumar IAEA. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cikin wannan mako, gidan talabijin na Real Madrid ya fitar da wani faifan bidiyo da ke sukar lamirin alƙalin da zai hura wasan. A baya kuma, Real Madrid ta taɓa rubuta wasiƙa a watan Fabrairu tana ƙorafin cewa alƙalai a Sifaniya ba sa musu adalci. Haka kuma, a watan Oktoban 2024, kulob ɗin ya ƙaurace wa bikin bayar da kyautar Ballon d’Or saboda rashin bai wa ɗan wasanta Vinicius Junior kyautar gwarzon ɗan kwallon duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Muscat Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Kama Hanyar Zuwa Birnin Domin Ci Gaba Da Tattaunawa Da Amurka
Ministan harkokin wajen Iran ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a yau domin gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya sanar da cewa: A yau ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a karkashin jagorancin tawagar diflomasiyya da fasaha don shiga zagaye na uku na shawarwarin da ba na kai tsaye ba da Amurka ta hanyar shiga tsakanin mahukuntan Oman. Baqa’i ya bayyana cewa: Bangarorin biyu sun amince da gudanar da tarukan fasaha tare da halartar manyan jami’an shawarwari, yana mai bayanin cewa “bisa tsarin da Oman ta shirya da kuma hadin gwiwa tsakanin Iran da Amurka, za a gudanar da tarukan...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi kashedin kan illar ci gaba da killace Gaza da kuma hare-haren ta’addancin ‘yan mamaya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da rashin hukunta ‘yan sahayoniyya kan kisan gillar da suke yi a zirin Gaza da Gabar yammacin kogin Jordan, da kuma mamayar wasu yankunan kasar Labanon da Siriya yana da matukar barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan ci gaba da ayyukan wuce gona da iri da na ta’addancin yahudawan sahayoniyya a Gaza da Lebanon.
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta inganta fahimtar juna tsakanin Indiya da Pakistan Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya sanar a yau Juma’a cewa: kasarsa a shirye take ta yi aiki mai kyau a fagen sulhunta tsakanin Indiya da Pakistan don inganta fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu a wannan mawuyacin lokaci. Da yake tsokaci game da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan tsakanin Indiya da Pakistan, Araqchi ya bayyana cewa: “Indiya da Pakistan kasashe ne ‘yan uwan juna kuma masu makwabta da Iran, kuma suna da alakar al’adu da wayewa tun shekaru aru-aru.” Ministan harkokin wajen na Iran ya kara da cewa: “Suna daukar kasashen Indiya da Pakistan a matsayin sauran...
Sashin ma’adinai da ba na karfe ba ta kashe kudin makamashi da kashi 33.7 zuwa naira biliyan 118.49, kuma masana’antar yadi, tufafi da takalmi kudin da ya kashe ya karu sau hudu, wanda ya kai naira biliyan 26.45 a shekarar 2024, idan aka kwatanta da naira biliyan 6.97 a shekarar 2023. Rahoton ya ce duk da an samu karin wutar lantarki a cikin masana’antu a shekarar 2024, da adadin karin wuta na awa 13.3 a kwace ranar da ya karu daga awa 10.6 a shekarar 2023. Kazalika karin kudin wuta ya karu da kaso 200 ga wadanda suke amfani da rukunin A, don haka kudaden da masana’antun ke kashewa wajen biyan kudin wuta nan ma ya karu sosai....
“Saboda ragin farashin litar man fetur da Dangote ya yi ne. Gidan man yana da tsohon mai da ya saya a farashin da ya fi wannan, kuma ba zai sayar da shi a asara ba. “Wannan dalilin ne ya sanya muka rufe gidajen man tun ranar Talata. Da yiwuwar mu bude nan gaba.” Kazalika, wani ma’aikacin gidan man, ya tabbatar da cewa suna ‘yan wasu gyare-gyare ne amma za su sake budewa. Ya kuma ce, gidan man zai fara sayar da man fetur ga jama’a a ranar Talata kan kudi naira 910 a kowace lita. Rahotonni sun tabbatar da cewa sauran abokan huldar matatar man Dangote, kamar su AP, Ardoba, da Optima, sun yi ta sayar wa...
Wasu mutane 13 sun faɗa a komar ’yan sanda ka zargi da zubar da ciki da kuma mutuwar wata budurwa ’yar shekara 18 a Jihar Bauchi. Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ana tuhumar huɗu daga cikin mutanen da aikata laifin fyade, zubar da ciki da kuma mutuwar budurwa a garin Misau da ke Ƙaramar Hukumar Misau. Wakil ya ce, a ranar 4 ga Afrilu, 2025 sun samu bayanai ewa, kimanin watanni hudu da suka gabata, wasu matasa biyu a yankin Lariski da ke Misau, sun kama wata yarinya mai shekaru 18 da suka yi ta yi lalata da ita sau da yawa. Ya ce a lokacin da suka lura tana ɗauke da juna biyu, sai...

Sojonin Yemen Ta Kakkabo Jiragen Yakin Amurka Wadanda Kimarsu Ya Dalar Amurka Miliyon $200 A Makonni 6
Sojojin kasar ayemen sun kakkabo jiragen yaki na kasar Amurka wadanda ake sarrafashi daga nesa a kan kasar Yemen, da dama wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka miliyon $200 a cikin makonni 6 kacal. Tashar talabijin ta Pressstv a nan Tehran ya bayyana cewa wadan nan jiragi suna aikin leken asiri ne a kan kasar ta Yemen, kuma duk da cewa suka tashi fiye da kafa 40,000 a sama, amma sojojin yemen suna iya kakkabosu. Wannan yana zuwa ne a dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donar Trump ya kara umurnin a kara yawan hare-haren da ake kaiwa kasar ta Yamen. Mafi yawan hare-haren da suke kaiwa yana kasa mata da yara da kumalalata kamfanoni da kuma cibiyoyin samar da ruwa...
Irin wannan zanga-zangar, ta sha ban-ban, da irin wadda ake gudanawar a kasashen da suka ci gaba kuma suke gudanar da mulki, irin na Dimokiradiyya, kamar da kasar Amurka, Birtaniya, Isara’ila da sauransu. Sashe na 40, na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, ya bai wa ‘yan kasar ikon haduwa a waje guda su kuma yi hudda da sauran jama’a. Kazalika, sashe na 11 na yarjejeniyar nahiyar Afirka, da ke magana kan ‘yancin ‘bil’Adama, wanda ita kanta Nijeriya ta rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar na barin ‘yan kasar su gudanar da zanga a cikin lumana. Amma sai dai, abin takaicin duk da ‘yancin na wannan sashen, mahukunta Nijeriya, suna yawan take wannan ‘yancin, kan...
A kokarinta na ganin an gudanar da jarrabawar hadin gwiwa ta hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB, gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025. An dauki wannan matakin ne bayan nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a kokarin baiwa daliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ba tare da wata matsala ba. A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, Ismail Garba Gwammaja ya fitar, ya ruwaito kwamishinan yana cewa. “Dakatar na da nufin hana duk wani cikas da zai iya kawo cikas ga aikin jarrabawar da kuma tabbatar da cewa ‘yan dalibai za su iya zana jarabawarsu ba tare da wani shamaki...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsoffin kwamishinoni na Jihar Kano kamar su Hon. Diggol, Hon. Abbas Sani da Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Baffa Bichi su ma sun koma APC. Hakazalika, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada wanda ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADP a zaɓen 2023, ya sauya sheƙa zuwa APC. Ana kallon wannan sauya sheƙar a matsayin wani babban tagomashi ga jam’iyyar APC musamman a Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A daidai lokacin da sabani yake yin tsanani a tsakanin India da Pakistan, bayan wani hari da aka kai a Kashmir da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 26, ministan tsaron kasar Pakistan Khajah Asif ya ce; matukar India ta keta hurumin kasarsa, to kuwa za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani. Minista Khajah Asif ya kuma gargadi kasar ta India da ta guji keta hurumin kasar Pakistan. Asif ya kuma bukaci India da ta gudanar da bincike akan harin da aka yi a ranar Talata a yankin Kashmir, kuma ta nesanci yin wani abu wanda zai jefa yankin cikin yakin da ba a san yadda karshensa zai kare ba. Haka nan kuma ya ce; Tushen matsalar tana nan a...
Ya buƙaci jama’a da su ci gaba da tallafa wa jami’an tsafta domin tabbatar da tsaftar muhalli a jihar. Aikin tsaftar muhalli na wata-wata, wanda ake yi a ƙarshen kowane wata, ana dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wasu awanni domin tsaftace muhalli a faɗin Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar ta ƙara da cewa, ’yan kasuwa 1,000 za su samu jarin fara aiki na Naira 150,000 kowannensu, da nufin sauya akalar kasuwancin su zuwa sana’o’i na zamani a faɗin Jihar Zamfara. A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta bullo da shirye-shiryen ƙarfafawa da dama tare da samar da damarmaki don cimma manufofinsa na ceto. “Waɗannan tsare-tsare ba wani kebantaccen abu ba ne, wani ɓangare ne na babban burinmu wajen samar da jihar Zamfara mai albarka don haɗa abokan hulɗa don magance ɗimbim matsalolin zamantakewa da tattalin arziki. “Yawancin tsare-tsare na rage raɗaɗin talauci da wannan gwamnati ta bullo da su sun yi tasiri ga rayuwar dubban ‘yan jihar, ƙudirin...
Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda. A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22 a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba. A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar. Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda. ...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun zamanin kaka da kakanni ake gudanar da ƙananan sana’o’i, waɗanda al’umma ke dogaro da su don biyan buƙatunsu na yau da kullum. Irin waɗannan sana’oi sun haɗa da saƙa, jima, fawa, suyan ƙosai ko masa da dai sauransu. A da can masu waɗannan sana’o’i sun dogara ne da masu wucewa a bakin hanya don siyar da hajojinsu ko kuma waɗanda suka samu a yayin da suka ɗauki tallar kayan sana’ar tasu. Sai dai a wannan zamani masu waɗannan sana’o’i na fuskantar barazana daga wurin ’yan zamani ’yan bana bakwai da suka shigar da zamani ciki suke neman kwace musu ragama ta hanyar amfani da kafofin sada zumunta wajen tallata hajojinsu. NAJERIYA A...
Rashford ya yi watsi da yiwuwar komawa Landan, inda yace ba lallai bane ya cigaba da wasa a karkashin Ruben, inda yake da burin zama a kungiyar da zata buga gasar Zakarun Turai a badi, majiyoyi na kusa da dan wasan sun tabbatar Rashford har yanzu bai tattauna kan makomarsa ba kuma baya shirin yin hakan har zuwa tsakiyar watan Yuni. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa. Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2 kowanne ga iyalai biyar da suka rasa rayukan ‘yan uwansu, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 10. Ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jinya ga wadanda ke karbar magani a Asibitocin jihar. A yayin da yake godiya, Sarki Maiyamba ya ce, hatsarin na Easter ya girgiza daukacin masarautar Tangale, amma ya amince da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wanda ya ce hakan...
Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa. An fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa. Daga cikin lambobin yabon din da tawagar ta Iran ta lashe da akwai gwala-gwalai 4, azurfa 3 da kuma tagulla.
Garuruwan da aka fi tsananta wa harajin sun haɗa da Gijinzama da aka tilasta musu biyan Naira miliyan 8.5, Dakolo da aka karɓi Naira miliyan 5 da buhun wake 20, sai Kibari da Kunchin Kalgo da suka biya Naira miliyan 20, Sungawa da Naira miliyan 15, da kuma Yalwa da aka tilasta su biyan Naira miliyan 2.7. Bayan rasuwar Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga mai suna Dogo Gide ya sa harajin Naira miliyan 100 a kan ƙauyuka 23 da ke ƙaramar hukumar Tsafe. A ƙarshen makon da ya gabata kuma, mazauna ƙauyen Dankurmi a ƙaramar hukumar Maru sun fuskanci sabon harajin Naira miliyan 60. Wani mazaunin ƙauyen Dan Jibga, Muhammad Dogo, ya bayyana cewa bayan kashe mutane biyu...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: China da Rasha abokan hulda ne na tushe ga Iran bisa kyakkyawan tsari Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana kasashen China da Rasha a matsayin abokan huldar na tsari a kan tubalin manyan tsare-tsare ga Iran, kuma ya dace kasashen uku su ci gaba da tuntubar juna a fannoni daban daban. A yayin da ya isa birnin Beijing, yayin da yake amsa tambaya game da makasudin ziyararsa a kasar China a jajibirin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, Araqchi ya bayyana cewa: Kasashen China da Rasha abokan hulda ne na kut-da-kut da Iran. Sun kasance tare da Iran a lokutan wahala, kuma abu ne mai...
“Yaron ya kuma ce akwai lokacin da ta ba shi wani lemun tsami da yake zaton an saka wani abu a ciki kafin abin ya faru. Ya bayyana cewa ta sha maimaita wannan aika-aikar a kansa,” Wakil ya ƙara da bayani. Wakil ya ce a yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin da ake zarginta da shi. Ya ce za a ci gaba da tantance bayananta, sannan a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya. Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taɓa rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan
Ya roƙi matasa da su zauna lafiya kuma su riƙa kai rahoton duk wani abu na barazana ga jami’an tsaro, domin nemo mafita game da hare-haren da ke ci gaba da faruwa. Garba Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da makiyayan shida ke kiwo. “Da maharan suka fara harbi, ɗaya daga cikin makiyayan da ya tsira ne ya kira ya ba mu labari. Ina samun labarin, na garzaya wani shingen sojoji da ke Latiya, inda na kai rahoto. Daga nan jami’an tsaro tare da ni muka tafi wajen, mun tarar da shanun da tumakin da aka kashe,” in ji shi. Shugabannin ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da GAFDAN a jihar, Ibrahim Babayo da...
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’ar ta ce, “Shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar na da inganci kuma masu gamsarwa ne, don haka kotun ta samu wanda ake tuhuma da laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.” A cewar mai gabatar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba-Sorondinki, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Janairu, 2023, a unguwar Rijiyar Zaki da ke Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sahun farko na Alhazan Najeriya zai tashi zuwa kasa mai tsarki a ranar 9 ga watan Mayun 2025. Hakan na kunshe ne a cikin bayanin bayan taro da Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, ta yi da Shugabannin Hukomomin Kula da Jin Daɗin Alhazai na Jihohi a ranar 22 ga watan Afrilun 2025. Manufar taron ita ce tantance matakin shirin da kowace Hukumar Alhazai ta Jiha ta kai. Wata sanarwa da mataimakiyar daraktar watsa labarai ta hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce shugaban hukumar, Farfesa Abdullah Saleh Usman, ya tunatar da mahalarta taron cewa harkar Hajji na cikin matakin karshe na shirye-shirye kafin fara aikin Hajjin shekarar 2025. Ya bukaci jihohi da su sanar da NAHCON matsayin da...
A yayin ziyarar, mataimakin shugaban kamfanin LEADERSHIP Mike Okpere, ya bayyanawa uwargidan shugaban kasa irin ayyukan agaji da Kamfanin LEADERSHIP ke gudanarwa tare da yin fatan hada hannu da shirin tallafin fata na gari ‘Renewed Hope Initiative (RHI)’ da nufin karfafawa mutane 1,000 da ayyukan yi. A cewar Okpere, shirin zai mayar da hankali ne wajen samar da sana’o’in dogaro da kai a sassa daban-daban na tattalin arziki da suka hada da rini, kamun kifi, dinki da dai sauransu. Ya yi nuni da cewa, manufar ita ce a taimaka wa daidaikun mutane su samu ‘yancin cin gashin kansu da kuma zama masu amfani a cikin al’umma. Uwargidan shugaban kasar, wacce ta yi marhabin da shirin tallafin, ta...
Majiyar fadar Vatican ta bada sanarwan cewa za’a gudanar da jana’izar paparuma Francis a ranar Asabar mai zuwa 26 ga watan Afrilu a dandalin st. Peter dake birnin Vatican amma za’a ajiye gawarsa don yi mata kallo na karshe a daga gobe Laraba a St. Peter’s Basilica har zuwa ranar Jana’izar. Shafin yanar gizo na labarai “Africa News” ya bayyana cewa paparoma Francis ya mutane a ranar 20 ga watan Afrilu yana dan shekara 88 a duniya, kuma fatansa a cikin jama’a da kuma jawabinda na karshe kwana guda ne kafin rasuwarsa. Labarin ya kara da cewa paparoman ya shahara da son talaka, da kuma wadanda aka zalunta, musamman al-ummar Falasdinu, wadanda yahudawan HKI suke yiwa kissan Gila tun sdhekara...
Janar Tukur ya yaba wa sojojin bisa jajircewa da kwarewa da suka nuna a yayin aikin, wanda ya kai ga kwato tarin makamai da alburusai da sauran su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da ci gaba a kan tafarkinta. Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Babu kyakykyawan fata kuma ba za a fitar da rai ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da yake jawabi a taron da gwamnonin kasar suka yi a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar a yau, ya yi jawabi kan shirin tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai cewa: Tun...
Munanan abubuwan da suka faru na zubar da jini bayan wasa tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli a Libya A kusa da filin wasa na birnin Tripoli an ga abubuwan na zubar da jini bayan wasan da aka yi tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli, lokacin da wasu motocin ma’aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin hadin kan kasa suka bindige magoya bayanta da gangan. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa bayan an kammala wasan ne wata mota dauke da makamai ta kutsa cikin wurin da jama’a ke cunkoso, inda suka bi ta kan wasu matasa, lamarin da ya haifar da firgici da hargitsi. An kuma ji karar harbe-harbe a wurin, lamarin da ya ta’azzara lamarin tare da jikkata wasu da ke...
Wang Yi ya ce, yana son yin aiki tare da Monday Semaya, domin aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa cudanya da hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu, da daukaka zumuncin kawancen Sin da Sudan ta Kudu a bisa manyan tsare-tsare. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ta ce, sakamakon dukan da ta sha, ta samu karaya a kafa da kuma raunin da ya shafi kunnenta. Sai dai Shu’aibu ya musanta wannan ikirarin, inda ya tabbatar da cewa, an kama dan uwanta ne a yayin wani samame da aka gudanar a wurin wani shagali a birnin Katsina. A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne da laifin yin sojan gona da kuma yunkurin dakatar da jami’an Hisbah a lokacin da suke bakin aiki. Da yake karin haske game da gaskiyar lamarin abinda ya faru, Shuaibu ya ce, an hana Hauwa shiga cikin ofishin Hisbah ne saboda irin tufafin da take sanye da su na rashin da’a, kuma ta yi yunkurin marin daya daga cikin...
Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna ta hanyar wayar tarho da takwarorinsa na Switzerland da Pakistan Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi wata ganawa ta hanyar wayar tarho guda biyu a yammacin jiya Lahadi tare da ministocin harkokin wajen kasashen Switzerland da Pakistan. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Switzerland Ignazio Cassis ta hanyar wayar tarho a yammacin jiya Lahadi, inda suka tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwan kasa da kasa tare da yin musayar ra’ayi a kansu. A yayin wannan tattaunawa, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana jin dadinsa ga rawar da kasar Switzerland ta taka a shawarwarin nukiliyar kasar cikin...
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Babban abin da suke bukata a duk wata tattaunawa shi ne a dage takunkumi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i, ya jaddada cewa babban bukatar Iran a duk wata tattaunawa ita ce a dage takunkumin da aka kakaba mata ta hanyar da za ta kai ga samun sakamako mai ma’ana. Isma’il Baqa’i ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na mako-mako da yake yi a yau litinin cewa: A kwanakin baya ministan harkokin wajen kasar Iran ya ziyarci kasar Rasha, sannan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Italiya, a gefen shawarwari ba na kai tsaye ba tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka. Ya kara da cewa: A...
Wasu Falasdinawa sun yi shahada a cikan kwana na 35 a sabon yakin da yahudawan sahayoniyya suka sake daurawa kan Zirin Gaza Sojojin gwamatin mamayar Isra’ila suna ci gaba da yakin kisan kiyashi a Zirin Gaza tun bayan sake ci gaba da yau tsawon kwanaki 35 da suka gabata, bayan da Fira minista Benjamin Netanyahu ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma yana gudanar da wannan ta’asa ne tare da goyon bayan siyasa da na sojan Amurka, sannan kungiyoyin kasa da kasa gami da gwamnatocin kasashe sun daukin matakin yin shiru da rashin gwada wani yunkurin kalubalantar wannan danyen aiki. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama tare...
“Amfanin gonakin duka sun isa girbi. Wasu ma sun fara girbi lokacin da ambaliyar ruwa ta afku. Ba mu san dalilin da ya sa aka sako ruwan ba tare da sanarwar mutanenmu ba” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa babu wani kamfen batanci da zai hana Gwamna Dauda Lawal aiwatar da ayyukan da suka shafi al’umma a fadin jihar. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da sadarwa na gwamna, Malam Salihu Nuhu Anka ya rabawa manema labarai a Gusau. A cewar Anka, Gwamna Lawal ya fara aiki ne a wani aikin ceto, kuma tuni mazauna jihar suka fara cin ribar dimokuradiyya. Ya bayyana cewa hankalinsa ya karkata ne kan kalaman da ya bayyana a matsayin maras tushe da wani tsohon Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Magaji Dosara ya yi, yayin wani taron manema labarai a Kaduna, inda ya kalubalanci kalaman da Gwamna Lawal ya...
Amurka ta sake kai wani hari ta sama kan babban birnin kasar Yemen, Sana’a, inda ta kashe fararen hula akalla 12 tare da jikkata wasu fiye da 30 na daban. Mummunan harin na Amurka an kai shi ne a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a a unguwar al-Farwa da ke gundumar Sha’ub a safiyar ranar Litinin. Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu yayin da mutane da dama ke makale a karkashin baraguzan gine-gine da aka wargaza a harin. A gefe guda kuma, Amurka ta kai hare-hare a yankunan lardin Sa’ada, a arewa mai nisa na kasar, da tsakiyar Ma’rib, da yammacin Hudaydah. Dama kafin hakan a ranar Lahadi, Amurka ta kai wasu hare-hare ta sama a Yemen,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da barazanar HKI na kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar kasar don hana kasar abinda take kira makaman Nukliya. Ministan ya kara da cewa kasar Iran zata iya kare kanta ko da Amurka ce ta takaleta, kuma Amurka ta san hakan. Sannan ya ce HKI bata taba kaiwa Iran hari a bay aba kuma ba zata taba kai mata hari ba. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya buga wannan labarin a jiya Asabar ya kuma nakalto ministan yana cewa kasashen Rasha da Iran basu taba karfafa dangantakar tsakaninsu fiye da yanzu ba. Aragchi ya kara da cewa kasashen Iran Rasha da kuma China suna aiki tare don tabbatar da zaman...
Bayan taro na biyu tsakanin JMI da Amurka a birnin Roma na kasar Italiya a jiya Asabar an gayyaci ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi don gabatar da Jawabi a wani taro wanda mahukuntan kasar Amurka suka shirya. Kamfanin dillancin labarai IP na kasar ya nakalto masu shirya taron na cewa an gayyace Abbas Arichi don gabatar da jawabin ne don muhuntan Amurka su ji ta bakin wadanda suka kore a sanin amfanin makamashin nukliya ta zaman lafiya da kuma tattaunawa a kansa. Labarin ya nakalto wadanda suke gudanar da taron wato ” The Carnegie International Nuclear Policy Conference” wanda za’a fara a gobe litinin, na cewa taron yana taimakawa mahukuntan kasar Amurka sanin kan yadda jami’an diblomasiyya yakamata...
Majiyar labarai daga kasar Lebanon sun bada sanarwa kama wasu mutane wadanda suke shirin Cilla Makamai kan HKI. Jaridar Arab News ta yanar gizo ta kuma kasar Saudiya ta bayyana cewa a makon da ya gabata ma an kama wasu mutane wadanda ake zargi da cilla makaman roka kan HKI daga kudancin kasar ta Lebanon. Amma dangane da kwance damarar kungiyar Hizbullah kuma shugaban kasar Lebanon Jesept Aun ya ce wannan al-amarin ba abu ne mai sauki ba, sai dai a jira lokacinda ya dace na yin hakan. Aun ya kara da cewa duk wani kokari na kwance damarar kungiyar hizbullah kawo karshen zaman lafiya a kasar Lebanon ne. Kafin haka dai shugaban kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim a jawabin...
Ya kuma ce, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na yakin karin haraji ko yakin kasuwanci. Kuma wannan ba wai don kare muradu da martabar kasar Sin ba ce kawai, har ma da kare tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, tare da tabbatar da daidaito da adalci. A cewarsa, “Idan har wata kasa ta dage kan kakaba mana yakin haraji ko kuma yakin kasuwanci, to tabbas za mu yi gaba-da-gaba da ita ba tare da tsoro ba, kuma tabbas za mu dauki kwararan matakan mayar da martani.”(Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
A shekaru 70 da suka wuce, kasashen yamma sun yi wa taron Bandung kallon taro na kasashe matalauta, amma kuma ga irin yadda ya haifar da kyakkyawan sakamako ga mikewar kasashen. A zamanin yau, lokacin da kasar Amurka ke ta kara kakaba harajin kwastam a kan sauran kasashen duniya, muna farin cikin ganin yadda kasashe masu tasowa ke hada kansu, da rike tsaronsu da ci gabansu a hannunsu, suna kuma rungumar akidun zaman lafiya da hadin gwiwa da bude kofa don tinkarar yadda kasashe masu karfi ke neman cin zalin kasashe masu karamin karfi da ma rashin tabbas da ake fuskanta a duniya. Yau da muke waiwayen taron Bandung, za mu gano cewa, ko-ba-dade-ko-ba-jima za mu ga bayan nuna...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yaba Da Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka Zagaye Na Biyu A Birnin Roma
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tattaunawa da Amurka an yi ta ne cikin yanayi mai inganci da hangen nesa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, wadda Oman ta shiga tsakani a birnin Roma na kasar Italiya, da cewa an gudanar da shi cikin yanayi mai ma’ana da hangen nesa. A cikin wata sanarwa bayan tattaunawar, Araqchi ya yi nazari kan yanayin tattaunawar, inda ya bayyana cewa: “Sun gudanar da shawarwari na tsawon sa’o’i hudu a ci gaba da zaman da aka yi a baya, kuma sun samu kyakkyawar fahimta kan ka’idoji da manufofi da dama.” Ya ci gaba da cewa: An amince da a ci...
A yayin wannan ziyara har ila yau, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, yakin cinikayya zai gurgunta tsarin cinikayyar kasa da kasa, da haifar da mummunan tasiri a kan tattalin arzikin duniya, da tarnake halaltacciyar moriyar kasashen duniya, musamman ma ta kasashe masu tasowa. Sai dai kuma, yayin da ake fuskantar karuwar masu nuna ra’ayin kariyar ciniki a duniya, kasar Sin za ta tsaya kan kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, kuma za ta ci gaba da samar da dimbin gudummawa ga yunkurin raya tattalin arzikin duniya, in ji shugaban kasar Sin. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
A nawa raayin hakan ba zai zama lefi ba indai har tsakani da Allah suke son junansu. Lokacin fira daban lokacin ziyara kuwa shi zuwa yake yi babu wani lokaci a yadda na fahimci topic din. Ni dai zan tsara shi ne ranar Alhamis bayan sallar la’asar zuwa sallar magrib idan ma firar ta dauki lokaci sosai kenan ya isa tunda ana waya ko chart. A shawarce hakan sai na ga ba lefi bane duba da an zama daya kuma wannan shi ne zai kara sa nutsuwa a zukatanku na tabbacin kowannenku ya san babu wasu da suke kulawa, sannan zai rage karairayin da ake samu wajen sutura ko gidajenmu ko ababen hawanmu dama abokai ko kawayen da muke kulawa....

An Fara Bikin Ranar Sojin A Iran 18 Ga Watan Afrilu Tare Da Gudanar da Fareti A Gaban Shugaban Kasar
An fara gudanar da bukukuwan ranar soji a Iran a ranar 18 ga watan Afrilu ta hanyar gudanar da faretin soja a gaban shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian An fara faretin soji na sojojin kasar Iran a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin birnin Tehran fadar mulkin kasar a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar sojoji ta 18 ga watan Afrilu. A jiya Juma’a 18 ga watan Afrilu ne sojojin kasar Iran suka fara faretin soji na murnar zagayowar ranarsu da kuma irin bajintar jarumtakar sojojin kasar, a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin babban birnin kasar Tehran. A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA na Iran, faretin ya samu halartar shugaban kasar Mas’ud...
“Amfani da haraji a matsayin makami don matsin lamba da son rai yana nuni da tsarin siyasa na rashin haɗin kai da kare tattalin arziƙi da kuma zambar tattalin arziƙi. Wannan ba abu ne na adalci ba ko mai kyau – yana nufin zaman ‘Amurka da tafi kowa’ da kuma ƙaruwar ƙarfin Amurka,” in ji shi. Jakadan ya kuma yi gargadi cewa ƙasashe masu tasowa za su fi shan wahala daga wannan tsarin haraji, kuma hakan zai fi cutar da ƙasashen Afrika, ciki har da Nijeriya. Ya bayyana cewa, “Amurka ta ɗauki mataki mara son Rai, na cewa ‘ samun ribar kasuwanci sai an yi zamba’ wanda ya kai ga kai wa ƙasashen Afrika haraji mai yawa, wanda ya saɓa...
Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke nuni da cewa an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, GCON shiga fadar shugaban kasa, inda ta bayyana ikirarin a matsayin shirme, kage da kuma karya gaba daya. Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa na ofishin mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya sanyawa hannu, ta ce rahoton da wasu shafukan da ba su da tushe suka yada shi, na cikin jerin labaran karya da aka kitsa domin haifar da rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa. Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan wani yunkuri ne mai rauni na cin mutuncin mutum da ofishin Mai Girma, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima....
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su, a wani samame da ta gudanar cikin gaggawa tare da tabbatar da ganin an dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce a ranar 16 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 1:45 na rana, tawagar hadin guiwa da ta kunshi jami’an ‘yan sanda da kuma jami’an kare hakkin jama’a (CPG) suna sintiri a kan babbar hanyar Anka-Gummi, inda suka gano wata mota samfurin Peugeot 206 da suka yi garkuwa da su a gefen hanya. A cewar sanarwar, ba tare...
Kungiyar Sarakunan Afirka ta jaddada muhimmancin gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a Najeriya. Da yake jawabi a wajen bikin nadin Alhaji Aliyu Dauda a matsayin Sardaunan Najeriya na farko, wanda aka gudanar a Yankari, Jihar Bauchi, Shugaban Kungiyar, Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen ci gaban kasa. Alhaji Ibrahim Haruna ya ce, masarautun ba wai kawai suna zama uba ga al’umma ba ne, kawai har ila yau suna bada gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa. Ya bayyana cewa goyon baya da gudunmawar da Alhaji Aliyu Dauda ke bayarwa ga masarautun gargajiya, musamman a Arewacin Najeriya, ne ya sa aka zabesa domin karbar wannan gagarumar...
Yau Asabar Washington da Tehran, ke tattauanwa a birnin Rome na kasar Italiya, wace ita ce ta biyu a shiga tsakanin kasar Oman kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Tattaunwar wacce ba ta gaba-da-gaba ba an gudanar da irin ta a ranar Asabar data gabata a birnin Muscat na kasar Oman, inda bangarorin biyu suka bayyana tattaunawar da mai armashi. Gabanin tattaunawar ta yau, Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce akwai yuwuwar kulla yarjejeniya da Amurka idan har Washington ba ta gabatar da wasu bukatu na da suka wuce da tunani ba”. Araghchi ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov, a ranar Juma’a a birnin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp