2025-03-31@13:10:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 153
«Gwamnati Ta Tabbatar da Kungiyoyin Hadaka a Matsayin Ginshikin Ci gaban Al umma»:
Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Nijeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ‘ƴan ƙasa. Kamfanin sadarwa na MTN ya fara amfani da sabon tsarin ƙarin kudin awanni kaɗan bayan da majalisar wakilai ta kasa ta bukaci gwamnati da ta dakatar da ƙarin.
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara jaddadawa Sarkin Jordan Abdullahi II kan shirinsa na kwace yankin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan ya maida shi wurin shakatawa, da kuma kan cewa kasar Jordan da Masar ne zasu dauki nauyin kula da Falasdinawa kimani miliyon 2 a Gaza a cikin kasashen su. Tashar talabijin ta Presstv...
An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan...
Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma...
Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma...
Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga...

Shugaban Kungiyar Hamas Yace: Iran Bata Gusheba Tana Taimaka Mana, Kuma Shirin Trump Na Kwace Gaza Zai Ya Lalace
Khalilul Hay, shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda ya halarci gangamin bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa ya na matsayin mataki na farko ne na kwatar kasar Falasdinu daga hannun wadanda suka mamayeta. Ya kuma kara da cewa JMI ta taimakawa kungiyar...
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman...
Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a...

Ministan Mai Na Iran Ya Ce: Hana Iran Fitar Da Man Fetur Zuwa Kasuwannin Duniya Mafarki Ne Na Shugaban Amurka
Siyasar tsananata matsin lamba kan Iran ta gaza cimma buri kuma hana fitar da man da Iran ke fitarwa mafarki ne da ba zai tabbata ba Ministan mai na kasar Iran Mohsen Paknejad ya bayyana matsayar matsin lamba da Amurka ke yi kan fitar da man kasar Iran a matsayin siyasa ta nuna gazawa, yana...

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Ce: Hamas Ta Yi Rawar Gani Wajen Kare Kanta
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da...
An bude atisayen soja kan teku bisa hadin gwiwar wasu kasashe a birnin Karachi na kasar Pakistan, a ranar 7 ga wata. Asitayen sojan da kasar Pakistan ta tsara ya samu halartar jiragen ruwan soja daga kasashe sama da guda 10, wadanda suka hada da Sin, da Indonesiya, da Japan, da Italiya, da Malasiya, da...
Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da...
Yadda ake amfani da shi: Za ku dinga shafa zumar a gabanku, ku barta na tsawon mintuna 30, sai ku wanke da ruwan dumi, sannan ku shafa Man Zaitun. Za ku dinga yin haka safe da yamma kafin kwanciya. Sannan ku dinga dafa ‘ya’yan hulba na tsawon mintuna 10 da ruwan da bai wuce...
Kwamandan rundunar sojin saman Iran ya bayyana cewa: Sun kai ga nasarar cimma matakin cin gashin kai a kere-keren kayayyakin aikin soja Kwamandan rundunar sojin saman Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa: Sojojin saman Iran na ma’aikatar tsaro da taimakon sojojin kasar sun cimma mataki dari bisa dari a fagen...
Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu...
Sakatariyar kwamitin JKS na babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta bayyana a taron hukumomin kwastam na kasar a ranar 7 ga wata cewa, darajar cinikin waje na kasar Sin ta zarce manufar da aka tsara ta yuan triliyan 43 a karon farko a shekarar 2024, inda ta karu da kashi 5 cikin...
Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci al’ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama. A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya jajanta musu tare da...

Shugaban Kasar Amurka Ya Sanya Hannu A Dokar Yin Tir Ta Kotun ICC Saboda Sammacin Kama Natanyahu Da Tayi
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya rattaba hannu a kan doka wacce ta yi allawadai da kutun kasa da kasa ta ICC saboda laifin fidda sammacin kama abokiyar Amurka firai ministan HKI da ta yi, sanadiyyar kissan kiyashin da ya yi a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump ya na...
Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta ki bada kai ga bukatun Amurka duk tare da barazanar sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio na fasa zuwa taron G20 a kasar Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ronald Lamola ministan harkokin wajen kasar Afirka ta kudu na cewa “kasarmu yentacciyar kasa ce, kan tsarin...
Biyo bayan nasarar da suka yi akan Alavés a ƙarshen mako, Barcelona za ta dawo taka leda a yau Alhamis don ƙarawa da Valencia a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey a filin wasa na Estádio de Mestalla dake Valencia. Barcelona na cigaba da jan zarenta a wannan...
Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a zaman lafiya da hakuri a tsakanin al’ummar garin Rimin Zakara sakamakon rikicin filaye da ya barke tsakanin al’umma da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Sarkin ya yi wannan roko ne a ziyarar da ya kai yankin bayan dawowarsa daga aikin...
Saka sunan Taye Taiwo a cikin jerin zakakuran yan wasan kungiyar ya nuna yadda dan wasan ya nuna bajinta da kuma yadda ita kanta kungiyar ta Marseille ta yaba da irin kokarin da ya yi a baya.
Ancelotti ya shaidawa manema labarai ranar Talata cewa “Bellingham ya samu rauni yayin atisaye amma kuma Vinicius Jr zai buga wasan gobe duk da cewar har yanzu ya na kan murmurewa daga raunin da ya ji a watan jiya Ya kuma ce Mbappe ya yi atisaye kamar yadda aka saba a yau, amma gobe...
Sojojin sama na JMI sun sami nasarar kakkabo jiragen yaki na makiyan da aka sawwara, tare da amfani da makami mai suna Majid a cikin atisayen sojojin sama da suke gudanarwa a kudu masu yammacin kasar. Jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa dai, suna da masu muhimmanci a yakin zamani a halin yanzu, don...
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar...

Sojojin Iran Sun Fara Atisayen Soje Karu Na Biyu Mafi Yawa A Bangaren Garkuwan Sararin Samaniyar Kasar
Sojojin JMI sun bada sanarwan fara isayen soje karo na biyu a yankun tsakiya da kuma kudancin kasarTashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa za’a fara wannan atisayen ne a yau Talata 04 ga watan Fabrairu, kuma atisayen zai fi maida hankali ne a kan garkuwan tsaron kasar , wanda kuma ya...
A yayin da rikici ya kaure cikin dare tsakanin jami’an tsaro da masu gine-gine a unguwar Rimin Zakara, mutane sun cinna wa gidan mai garin wuta. Da farko dai an samu rikici tsakanin mahukunta da mutanen yankin, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane huɗu tare da ƙone gidan mai unguwar. NCDC ta tsaurara matakan...
Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta cafke wasu matasa a yankin Sheka bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, yana mai cewa rikicin ya fara ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Yusuf Aminu, ɗan unguwar Sheka Babban Layi, wanda ake zargi da aikata...
Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909. Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14. Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001). Dan...
Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance...
Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya...

Limamin Juma’ar Tehran Ya Jinjinawa Wanda Ya Assasa Juyin Musuluncin A Iran Marigayi Imam Khumaini ( R.A)
Hajjatul-Islam Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi da ya jagoranci Sallar juma’a a Tehran a jiya juma’a ya bayyana Imam Khumaini ( r.a) a mastayin daya daga cikin fitattun mutanen da duniyar musulunci ta samu a wannan zamanin. Hujjatul-Islam Wal Muslimin ya ce, Shakshiyya din Imam Khumaini ta ginu ne akan ilimomi na addini,filiku da...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga...
Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan...
An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun tabbatar a jiya Laraba cewa: Sassan soja sun amince da nada Ahmed al-Sharaa da aka fi sani da (al-Jolani) a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar. Tun a jiya Laraba ce,...
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron gaggawa game da batun Kongo(Kinshasa) da kwamitin sulhu ya kira jiya Talata cewa, a halin yanzu, yankin gabashin Kongo(Kinshasa) yana cikin yanayi mai hadari. Ya ce Sin na goyon bayan mambobin kwamitin sulhu su hada kai tare da daukar kwararan matakai, ta...
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau,...
Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar,...
Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da...
Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as. Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara...
Haka kuma, an naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta. Ya samu ƙwarewa a fannonin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen ƙara ƙarfin tsarin kuɗi na jihar. An kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai...
Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe...
Real Madrid za ta fafata da Leganes, yayin da Barcelona za ta je Valencia a zagayen kwata fainal a Copa del Rey, bayan da aka raba jadawali ranar Litinin. Wani wasan da zai yi zafi shi ne tsakanin Atletico Madrid da Getafe, yayin da za a yi tata-ɓurza tsakanin Real Sociedad da Osasuna. Shin wannan...
Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewa watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Gasar Firimiyar Ingila. Hakan ya biyo bayan shan kashin da ƙungiyar ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a karawar mako na 22 na gasar Firimiyar. Hakan ya kai United matsayi na...

CMG Ya Gabatar Da Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin A Amurka Da Myanmar Da Indonesia Da Habasha Da Faransa Da Jamus Da Paraguay
Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF...
Hukumar kula da gandun daji na Hadejia ta ce wuraren shakatawa na kasa suna taka rawar gani ta fuskar kiyaye halittu, da magance matsalolin sauyin yanayi, da inganta bincike, da ci gaba, gami da samar da ayyukan yi a Najeriya. Mukaddashin jami’in kula da gandun dajin, Mista Jonah Moses ya bayyana haka a lokacin da...
Hukumar Kula Da Taswira Ta Jihar Kebbi (KEBGIS), ta tsara wani gagarumin shiri na samar da kudaden shiga na sama da Naira biliyan daya a shekarar 2025. Babban Manajan Hukumar, Bashiru Saidu Bakuwai, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan tabbatar da nadinsa a matsayin babban Manaja,...