2025-02-21@14:58:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1114
«Sabon Tsari»:
Gwamnatin Tarayya tayi kira don samun tsarin visa mai sassauci ga kamfanonin Najeriya da ke neman kafa masana’antu da kasuwanci a ƙasashen waje. Ministan Yada Labarai da Wayarda Kan Jama’a, Mohammed Idris, shine ya yi wannan kiran a Addis Ababa, Ethiopia, yayin da ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wani taro da mambobin...
Ya ce: “A bara, na wakilci Nijeriya a Indonesiya, kuma na gano cewa akwai manyan kamfanoni hamsin daga Indonesiya da ke aiki a Nijeriya, amma ba mu da ko kamfanoni biyar daga Nijeriya da ke aiki a Indonesiya. “Idan suna son zuwa ƙasar mu su yi kasuwanci saboda yawan mutanen mu da kuma damar...
Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta haramta wa Gwamnatin Tarayya riƙewa ko kuma yi wa kuɗaɗen ƙananan hukumomi 44 na jihar katsalandan. Mai Shari’a Musa Ibrahim Muhammad ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, biyo bayan ƙarar da wakilan ƙananan hukumomin jihar suka kai na kare ‘yancinsu na cin gashin kai dangane da kuɗaɗen da...
Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran. Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin. Bangarorin sun bayyana...
Bisa ga yadda wasu fina-finan kasar Sin ke samun karbuwa a kasuwannin kasa da kasa, ciki har da fim din “Ne Zha 2”, a yau Litinin an kaddamar da bikin “Tafiya a kasar Sin bisa fina-finan kasar” a gidan tarihi na fina-finai na kasar Sin dake nan birnin Beijing, wanda hukumar kula da fina-finai ta...

Kasar Sin Ta Taya Mahmoud Ali Youssouf Murnar Zabarsa Da Aka Yi A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar AU
A kwanan nan ne dai aka gudanar da taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU karo na 38, inda aka zabi ministan harkokin wajen kasar Djibouti Mahmoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar AU na tsawon shekaru hudu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya taya shi murna a yau 17...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa kokarin da makiya suke yi na haifar da sabani a tsakanin al’ummar kasar ta hanyar yi musu barazana ya ci tura. Babban tattakin da al’ummar kasar suka yi a ranar 10 ga watan Fabrairu ya nuna cewa barazanar makiya ba ta...
Kungiyar Hamas ta jinjinawa kungiyar tarayyar Afrika ta AU kan yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza bayan da kungiyar ta soki Isra’ila da keta dokokin kasa da kasa a jawabin rufe taron da ta yi na kwanaki biyu a Addis Ababa. Hamas ta ce tana matukar godiya da matsayin...
Iran ta bayyana cewa za ta aike da tawaga a matakin koli zuwa jana’izar mirigayi babban sakataren kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon Hassan Nasrallah. Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce kasar za ta halarci gagarumin bikin mai matukar muhimmanci, Tunda farko dai kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta...
Bangaren kungiyar Hamas da ke dauke da makamai ya tabbatar da shahadar wani daga cikin jami’in kungiyar a wani harin Isra’ila. Muhammad Ibrahim Shaheen, ya yi shahada ne a wani harin da wani jirgin yakin Isra’ila ya kai a Sidon. Kassam Brigades ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi tsayin daka kan zalincin Isra’ila,...
Kungiyar M23 Ta Kwace Wani Birni Na Biyu A Gabashin DR Congo Rahotanni daga Congo na cewa Kungiyar yan tawayen DR Congo ta M23 ta kutsa birnin Bukavu birnin mafi girma a gabashin kasar, inda ta kwace ofishin gwamnan lardin. Bayanai sun ce mayakan sun kutsa cikin birnin ba tare da fuskantar wata tirjiya ba,...
’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe a kauyen Jalingo da ke Ƙaramar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a Damaturu ranar Litinin....
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Hon. Abdullahi Abbas, Hon. Aminu Aliyu Tiga, da Jam’iyyar APC ne suka shigar da karar inda suke kalubalantar wasu hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi da suka hada da Babban Bankin Nijeriya (CBN), Asusun raba kudi na Tarayya (FAAC), da kuma dukkan kananan hukumomi 44 da ke Kano a gaban kotu....
Ministan tattalin arziki na kasar Iran Abdunnaser Himmati yana halatan taro dangane da matsaloli da kuma dammakin da kasashen masu tasowa suka fama da su a birnin Riyad na kasar Saudiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Himmati yana halattan wannan taro na kwanaki biyu ne tare da gayyatar tokwaransa na...
Ministan tsaron HKI Israel Katz ya bayyana cewa gwamnatin HKIba zata bar a kafa kasar Falasdinu ba, saboda hakan barazana ce ga samuwar HKI. Israek Kazt ya bayyana haka ne a lokacin ganawar jami’an gwamnatin HKI da tawagar kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a taron...

Kungiyoyin Hamas Da Jihadul Islami Da Hamas Sun Yi Tirsa Da HKI Kan Azabtar Da Falasdinawa A Gidan Yarin Ofer
Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca. Tashar talabijin ta Presstv na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine. Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta...
Gwamnatin Katsina ta kashe kimanin Naira biliyan 5.4 domin bai wa mata 3,610 tallafin kiwon awakai. Gwamna Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da shirin raba tallafin awakan a gundumar Dan-Nakolo da ke Ƙaramar Hukumar Daura ta jihar. Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin shirin, an raba wa mata 3,610 awakai huɗu-huɗu...
Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu ayyukan hukumar bai tsaya a kan kula da tsaftace muhalli da abinci kadai ba, suna kula da tasirin sauyin yanayi da kuma fadakar da al’umma yadda za su amfana da trallafin sauyin yanayin da ake samu daga Majalisar Dinkin Duniya. A nasa jawabin, Babban Manajan Daraktan kamfanin,...
Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar, Xi Jinping ya halarci wani taron tattaunawa na kamfanoni masu zaman kansu a yau Litinin. Xi, wanda har ila yau shi ne shugaban kwamitin tsakiya na sojin kasar, ya gabatar da muhimmin jawabi bayan sauraron ra’ayoyin wakilan ‘yan kasuwa masu zaman kansu....
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa...
Gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da matakan korar ‘yan Nijeriya daga ƙasar, inda ake sa ran mutane 85 za su iso Lagos, yayin da wasu 116 ke tsare. Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Tafawa...
Kungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tsallake zuwa matakin zagaye na 16 a gasar zakarun Turai, amma kuma sabon kocin na fatan ganin ya lashe babbar gasar ta kasar Sifaniya.
Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Malamai Kan Sa Yara Aikin Wahala
Shirin Trump Na Gaza Rubio ya bayyana cewa shirin Trump shi ne kaɗai mafita a yanzu, duk da cewa ƙasashen Larabawa da na duniya suna goyon bayan kafa ƙasar Falasdinu tare da Isra’ila. A nasa bangaren, Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya ce kafa ƙasar Falasdinu ce kaɗai hanya ta samar da zaman lafiya a...
Mai Martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya buƙaci a riƙa tona asirin malaman tsubbu a duk inda suke. Sarkin wanda shi ne shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, ya buƙaci malaman Musulunci da su riƙa fallasa duk masu fakewa da rigar malumta suna ayyukan tsubbu. Basaraken ya buƙaci malaman addini da “su tsaftace harkar tasu,...
Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin ta yi hira da shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, dake ziyarar aiki a kasar Sin, a baya bayan nan a birnin Beijing. Yayin hirar, Zardari ya bayyana cewa, ci gaban kasar Sin al’amari ne mai kyau, kuma Sin ba ta taba zama mai mamaya ba. Bisa...
Kwanaki 30 bayan tsagaita wutar yaki a Gaza, sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankuna mabanbanta. Bugu da kari, sojojin na HKI suna cigaba da rushe gidajen Falasdinawa a cikin yankin yammacin kogin Jordan. Minsitan kudi na HKI Byetrael Smotrach ya ce, a kowace shekara za su rushe gidaje a yammacin kogin...
Rahotanni da suke fitowa daga Bukavu sun ambaci cewa ‘yan tawayen kungiyoyin M 23 da kuma AFC sun kwace iko da filin sauran jiragen sama na Kavumu wanda yake da tazarar kilo mita 45 daga birnin. mutanen sun kauracewa zirga-zirga akan titunan birninna Bukavu saboda rashin tabbacin abinda zai biyo baya. Mafi yawancin ‘yan siyasa...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya yi kira ga kasasnen larabawa da na musulmi da su nuna cikakken goyon bayansu al’ummar Falasdinu domin dakile makircin hadin gwiwa a tsakanin Amurka da Isra’ila na korar Falasdinawa daga gidansu. Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran, Abbas Arakci ya bayyana hakan ne a lokacin da...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi da marecen jiya Lahadi inda ya tabo muhimman batutuwa da su ka shafi kasar ta Lebanon da kuma yammacin Asiya. Sheikh Na’im Kassim ya ce wajibi ne ‘yan sahayoniya su janye sojojinsu daga kudancin kasar ta Lebanon domin babu wani dalili...
Wani jirgin sojin Najeriya ya jefa wa fararen hula bom inda ya kashe fararen hula bakwai a yankin Yani da ke Ƙaramar Hukumar Safana ta Jihar Katsina. Mamatan sun hada da mutum shida ’yan gida ɗaya, kamar yadda wani shaida ya bayyana. Hakan na zuwa ne bayan wasu jami’an tsaro da suka hada da ’yan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faɗuwar a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an...
Bishop na Cocin Katolika da ke Kontagora, Babban Rabaran Bulus Yohanna ya gudanar da bikin aure ga ma’aurata ashirin da daya a jihar Neja. A lokacin da yake jawabi yayin bikin daurin aurea cocin St. Mark Catholic da ke Nsanji Nkoso a karamar hukumar Magama ta jihar Neja, Bishop din ya bayyana cewa, bai kamata...
Najeriya ta nuna adawa da wani yunkuri na sake fasalin Sashen Harkokin Siyasa, Zaman Lafiya da Tsaro na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) (PAPS), saboda damuwa game sanadin da ka iya tabarbarewar hanyoyin zaman lafiya da siyasa na kungiyar. Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya sanar da wannan matsayi a madadin Shugaba Bola...
Ƙungiyar Gamayyar Jam’iyyun Siyasa ta Ƙasa (IPAC), reshen Jihar Katsina, ta bayyana amincewarta da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Laminu Lawal Boyi, ya bayyana cewa IPAC ta gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da bai wa...
An samar da ruwan sha a yankunan Danbatta, da Makoda da Minjibir dake gundumar Kano ta Arewa bayan kwashe kimanin shekaru goma. Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana haka a wani rangadin da ya kai kananan hukumomin uku domin tantance yadda ake samar da ruwan sha ga al’umma. Umar Doguwa...
Wasu fusatattun matasa sun banka wa ofishin ’yan sanda na yankin Ifon, da ke Ƙaramar Hukumar Ose wuta a Jihar Ondo. Lamarin ya faru ne bayan da ake zargi ’yan sanda da azabtar da wani matashi har ya mutu a hannunsu. An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun NAFDAC ta gano wajen da...
Wasu fusatattun matasa sun banka wa ofishin ’yan sanda na yankin Ifon, da ke Ƙaramar Hukumar Ose wuta a Jihar Ondo. Lamarin ya faru ne bayan da ake zargi ’yan sanda da azabtar da wani matashi har ya mutu a hannunsu. An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun NAFDAC ta gano wajen da...

Kasar Sin Ta Kammala Gina Jirgin Ruwan FPSO Na Farko Na Duniya Mai Karfin Rikewa Da Adana Iskar Carbon
An kammala aikin gina wani jirgin ruwa sabon kira mai bambaro saman ruwa, da samarwa, da adanawa, da saukewa wato FPSO a takaice, wanda ke da na’urar rike iskar carbon da wurin adanawa, a Shanghai, a cewar Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin. Jirgin dai shi ne irinsa na farko a duniya kuma ana...
A watan Janairun wannan shekara ta 2025, an fara fitar da sabbin fina-finan Hausa masu dogon zango sama da 10, wadanda ake nunawa a tasoshin ‘YouTube’ daban-daban, bayan wasu da yawa da aka kwana biyu ana haskawa ta kafar. Manyan fina-finai, musamman masu dogon zango da kamfanin Saira Mobies ke daukar nauyi, mai suna Labarina;...
Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, kwamfutar da kasar Sin ta kera da kanta ta zamani na uku mai sarrafa bayanai tare da warware matsaloli cikin matukar sauri ko kwamfutar quantum a takaice, wato Origin Wukong, ta samu masu amfani da ita sama da miliyan 20 daga sassan duniya...
An tsinci gawar wani Sufeton ’Yan Sanda, mai suna Haruna Mohammed, a cikin wani ɗakin otal a Jihar Ogun. Marigayin, wanda ke aiki da Hedikwatar ’Yan Sanda ta Ishashi a Jihar Legas. NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa saboda tsaro Ya je...
Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu...
Masu lura da gasar sun ce kwarewar na’urar wajen yanke hukunci ya karu zuwa kashi 96.4 idan aka kwatanta da kashi 95.7% a kakar da ta gabata. “Babu wanda yake shakku kan tasirin da ko da kuskure daya wajen yanke hukunci zai yi,” in ji wani babban jami’in kwallon kafa, Tony Scholes. Ya ci gaba...
Shirin Inganta Muhalli da Samar da Ruwan sha da kuma bunkasa aikin gona ACRESAL a jihar Jigawa yace zai zabo garuruwa masu wahalar shiga guda 6 domin sanya musu fitilun kan titi masu amfani da hasken rana. Shugaban shirin na jihar Jigawa, Alhaji Yahaya Muhamamad Uba Kafin Gana ya bayyana haka ga manema labarai a...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin....
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya ce: Tuntubar juna tsakanin Iran da Iraki ya zama wajibi don inganta matakan tsaro tsakanin kasashen biyu Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin siyasa Majid Takht Rawanji ya jaddada da cewa: Ziyarar da ya kai zuwa Iraki ta zo ne bisa tsarin tuntubar juna ta fuskar siyasa da...
Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Nan da wasu ‘yan makonni za a fara tilastawa Falasdinawa mazauna Gaza fara yin gudun hijira Ministan kudin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana tuntubar Amurka domin tattaunawa kan aiwatar da shirin shugaban Amurka Donald Trump na...
Nijar Za Ta Yi Taron Tattauna Batun Komawa Mulkin Siyasa