2025-02-20@08:54:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 22
«sana o in adana kayayyaki na»:
Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar. Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana. Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci. Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani. Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma,...
Abin ban takaicin shi ne duk wannan hauhawar farashi da karin harajin zai haifar a kan talakawa zai kare, domin kuwa farashin kayayyakin da ake kerawa daga irin wadannan ma’adanai na Karafa da Sanholo zai yi tashin gwauron zabo. A bayyane take cewa kasashen da wannan karin haraji ya shafa ba za su rungume hannuwansu ba su sanya ido Amerika ta ci karenta ba babbaka, babu shakka su ma za su dauki matakan ramuwar gayya, ta hanyar kakaba haraji a kan kayayyakin da Amerika ke fitarwa. Wannan lamari zai haifar da yakin ta fannin kasuwanci, abin da ba zai amfanawa kowa ba.
“Jami’anmu na kara zage damtse wajen ganowa tare da wargaza ma’ajiya da wuraren ajiya ba bisa ka’ida ba inda ‘yan fashin suka rika tara kayayyakin da aka sace. Dole ne FCT ta kubuta daga hannun wadannan miyagun abubuwa.” Aikin dai ya biyo bayan nasarar da aka samu a makon da ya gabata inda rundunar tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa da ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya kafa, suka kama tare da kwato kayayyakin more rayuwa da aka lalata. Disu ya yaba wa mazauna yankin bisa ci gaba da ba su goyon baya, ya kuma bukace su da su kasance cikin taka tsan-tsan, yana mai jaddada cewa kare kadarorin jama’a wani nauyi ne da ya rataya a wuyansu....

Kasuwannin Kayayyakin Da Ake Yawan Sayen Su A Lokacin Bikin Bazara Goma Sun Inganta Kashe Kudi Sama Da Yuan Biliyan 1.6
Yau Alhamis, ma’aikatar kula da kasuwanci ta Sin ta sanar cewa, tun bayan kaddamar da bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, manyan ayyukan da suka shafi bikin sun sa yawan kudin da aka kashe ta intanet da kuma a zahiri ya zarce yuan biliyan 1.6. An ba da rahoton cewa, bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, wanda ma’aikatar kula da kasuwanci, da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da kuma gwamnatin birnin Beijing suka shirya tare, tun daga ranar 7 ga watan Janairu, ya sa kananan hukumomi daban daban da kuma dandamalin kasuwanci ta intanet sun mayar da hankali kan lokacin bikin bazara, kuma sun kaddamar da ayyuka fiye da 100 don...
Alkaluma daga hukumar kula da jigila da sayen kayayyaki ta kasar Sin sun nuna cewa, darajar jigilar kayayyakin jama’a da aka yi a kasar Sin a shekarar 2024, ya karu da kaso 5.8 zuwa yuan triliyan 360.6, kwatankwacin dala triliyan 50.28, idan aka kwatanta da 2023. Zuwa karshen 2024, kasar ta samar da cibiyoyi 151 na jigilar kayayyaki na kasa da sama da wuraren ajiyar kayayyaki 2,500 a kasashen waje. Haka kuma ta bude sabbin hanyoyi 168 na jiragen dakon kayayyaki na kasa da kasa a baran. A cewar Hu Han, jami’i a cibiyar tattara bayanan da suka shafi jigila ta kasar, ingantawa kayayyakin aiki da suka shafi jigila da daukaka tsarin hanyoyin jigila sun bunkasa ware albarkatu ga bangaren...
Sin Ta Ayyana Matakan Bunkasa Harkokin Sayayya Da Zuba Jarin Waje
Kungiyar kula da harkokin jigilar kayayyaki da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta samar da adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin a watan Janairun da ya gabata cewa, wanda ya nuna cewa, yawan bukatun ajiye kaya a Sin ya bunkasa cikin sauri duba da karuwar bukatun sayayya a lokacin bikin sabuwar shekara, kuma sana’o’in adana kayayyaki na ci gaba da samun bunkasuwa. Adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin ya kai kashi 52.5%, a watan Janairun da ya wuce, wanda ya karu da kashi 1.9% bisa na watan Disamban da ya gabata, adadin da ya kai koli a cikin watanni 10 da suka gabata. Sakamakon manufofin tabbatar da tattalin arziki da ingiza bunkasuwa, da ma yadda aka koma aiki bayan hutun...
Sama Da Masu Amfani Da Kayayyakin Laturoni Miliyan 20 Ne Suka Nemi Tallafin Musayar Kayan Laturoni
Wani sabon babi na takaddamar cinikayya a duniya na kunno kai biyo bayan sabon matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da Sin ke shigowa da su kasarsa, lamarin da ke ci gaba da rura takun sakar kasuwanci a duniya. Tabbas wannan ba maganar haraji ce kawai ba, gwaji ne na juriya, dabaru da tasiri a duniya. Wannan lamarin ya kara kamari bayan da Sin ta mayar da martani ta hanyar ramuwar gayyar kakaba haraji kan wasu kayayyakin Amurka da ke shigowa kasar. Wannan lamarin dai ba sabon abu ba ne, kuma ya ginu ne a kan takaddamar kasuwanci da ta dade take ci gaba da tabarbarewa a tsakanin kasashen,...
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta gabatar da kayan agaji ga gwamnatin jihar Zamfara domin tallafawa wadanda gobara ta shafa a wata makarantar Islamiyya da ke Kaura Namoda. A lokacin da take mika kayayyakin, Darakta Janar na Hukumar Hajia Zubaida Umar, ta ce matakin ya nuna damuwar gwamnatin tarayya kan halin da wadanda abin ya shafa ke ciki. Babbar Daraktar wanda shugaban NEMA shiyar Sokoto, Aliyu Shehu Kafindangi ya wakilta, ya ce tallafin ya hada da kayan abinci kamar buhunan shinkafa, da masara, da man girki, da kayayyakin amfani gida. A baya dai Hajiya Zubaida Umar ta ziyarci wadanda lamarin ya rutsa da su wadanda har yanzu suke ci gaba da karbar magani a asibitin...
Alkaluman farashin kayayyakin masarufi na kasar Sin (CPI), wanda ke auna matakin hauhawar farashin kayayyakin, sun daga da kaso 0.5 bisa dari a watan Janairu. Adadin ya karu ne kan kaso 0.1 bisa dari da ya kasance a baya, galibi saboda hutun bikin bazara na sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, a cewar hukumar kididdigar kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu damar baiwa karin wurare hidima, mun fadada zirga-zirga daga Indode da Adama zuwa Mojo, Dire Dawa, da kuma wurin ajiye kaya na Sabata.” Uma ya kara da cewa, EDR yana maye gurbin tsoffin kayayyakin aiki da sabbi, da kuma gyara wadanda suka lalace, kana ya kara yawan jiragensa daga jiragen kasa takwas zuwa 21 da taragu 892 zuwa 935. Yana mai cewa “Jajicewar da muka...
Masana’antar kera kayayyakin laturonin sadarwa ta kasar Sin ta samu ci gaba mai sauri a shekarar 2024, inda karin darajar manyan kamfanoni a fannin ya karu da kashi 11.8 cikin dari bisa ta shekarar 2023, kamar yadda bayanai suka nuna a hukumance a jiya Alhamis. Adadin kudaden shiga na manyan kamfanoni na wannan fanni ya karu da kashi 7.3 cikin dari a bara, idan aka kwatanta da shekarar 2023 zuwa yuan triliyan 16.19 kimanin dalar Amurka tiriliyan 2.26. a cewar bayanai daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin. Hakazalika, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a wannan lokaci, adadin ribar da wadannan kamfanoni suka samu ya karu da kashi 3.4 cikin dari bisa ta shekarar 2023 zuwa...
Sakatariyar kwamitin JKS na babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta bayyana a taron hukumomin kwastam na kasar a ranar 7 ga wata cewa, darajar cinikin waje na kasar Sin ta zarce manufar da aka tsara ta yuan triliyan 43 a karon farko a shekarar 2024, inda ta karu da kashi 5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023, kuma ta ci gaba da rike matsayinta na kasa mafi girma a fannin cinikin kayayyaki a shekaru takwas a jere. A shekarar 2024, an fuskanci karuwar rashin tabbas da rashin zaman lafiya a waje, duk da haka hukumar kwastam ta samar da hidimomi mafi kyau domin saukake da sa kaimi ga inganci da daidaiton yawan...
Majalisar Wakilan Tarayya ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyare-gyare ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri da suka haɗa da ɗaurin rai da rai ga waɗanda ke da hannu wajen sarrafawa da shigo da magungunan jabu. Da kuma gaggarumin tara ga ’yan kasuwar da aka samu da laifin yin mu’amala da jabun kayayyaki. ’Yan bindiga sun mamaye masallaci da awon gaba da masallata a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Hakan ya biyo bayan wani ƙuduri kan muhimmancinsa ga jama’a da ɗan majalisa, Tolani Shagaya ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci kan...
“Canada, Mexico da Sin su ne suke sayen rabin duk kayayyakin amfanin gona da Amurka ke fitarwa. Kasuwanni ne da muke bukata babu makawa don raya tattalin arzikin Amurka. Sanya haraji kan manyan kasuwannin fitar da kayayyakin guda uku na noma da kiwo na Amurka, musamman na dogon lokaci zai haifar da mummunan sakamako,” in ji sanarwar. Tabbas! abin da manoman suka fada gaskiya ne, domin ko a shekarar 2018, karin harajin da Amurka ta kakkaba a kan kayayyakin kasar Sin, ya janyo kasar ta Sin wadda a baya ita ce ta fi shigo da wake na Amurka, ta sanya karin harajin kashi 25 cikin 100 na ramuwar gayya kan kayayyakin da Amurka ke fitarwa. Kuma a yanzu ma, Sin...
Sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar kwanan baya a kan kara haraji na kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl, a yau Talata, ma’aikatar cinikayya da takwararta ta kudi ta kasar Sin sun fitar da wata sanarwa cewa, Sin ta dauki matakan mayar da martani a kan Amurka tare da fara aiwatarwa. Matakan da suka jibanci lamarin sun hada da cewa, da farko, kasar Sin za ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, daga ranar 10 ga Fabrairu. Sannan na biyu, kasar Sin ta yanke shawarar shigar da rukunin kamfanonin US PVH...
A kwanan nan, kasar Amurka ta sanar da sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su zuwa kasuwannin Amurka. Wannan mataki ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda kuma zai lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka a fannin cinikayya. Yanzu haka, kasar Sin ta ce za ta kai kara ga kungiyar WTO, gami da daukar matakan da suka wajaba wajen kare moriyarta. A ganin kwararru masu nazarin al’amuran duniya, dalilin da ya sa sabuwar gwamnatin kasar Amurka daukar matakin nan na sanya karin haraji shi ne domin neman tilastawa sauran kasashe su biya kudi, ta yadda kasar Amurka za ta samu damar sassanta matsalar tattalin arziki da...
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jarida game da shirin Japan na aiwatar da matakan hana fitar da kayayyaki zuwa Sin, ciki har da semiconductor. Kakakin ya bayyana cewa, shirin bangaren Japan na aiwatar da matakan, zai kawo cikas ga tsaro da kwanciyar hankali na tsarin masana’antu, da gurgunta mu’amalar kasuwanci na yau da kullum dake tsakanin kamfanoni, da kuma lalata muradun kamfanonin kasashen biyu. Dangantakar Cinikayya Da Sin Ta Budewa Afrika Kofar Samun Ci Gaba Ana ɗar ɗar Kan Mutuwar Sojoji Bayan Da Mota Ta Kwace A Legas Sin na fatan kasar Japan za ta ji ra’ayoyin masana’antu, ta kuma gaggauta gyara ayyukan da ta yi bisa tushen kiyaye ka’idojin tattalin arziki da cinikayya...
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce an samu ci gaba sosai a yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashe da yankuna 160 na duniya a shekarar 2024. Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, yawan kayayyakin da kasar ta fitar ya karu da kaso 7.1 a shekarar, wanda ya kai yuan triliyan 25.45, kimanin dala triliyan 3.55, shekaru 8 a jere ke nan ana samun wannan ci gaba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan yi rangadi a wurare daban daban kafin bikin bazara na kasar, kana kafin bikin na wannan shekara, shugaban ya ziyarci lardin Liaoning dake arewa maso gabashin Sin. Sai dai wadanne fannonin ya mai da hankali a kai, yayin wannan ziyara? Abu na farko da shugaba Xi ya lura da shi, shi ne aikin sabunta fasahohin masana’antu. A rangadinsa na wannan karo, shugaban ya ziyarci wata masana’antar sarrafa kayayyakin karfe, inda ya duba yadda ake kokarin amfani da sabbin fasahohi a wurin, kana ya nanata bukatar samar da kayayyaki masu inganci, wadanda ba za su gurbata muhalli ba. Yankin Gabashin Kongo(Kinshasa) Yana Cikin Yanayi Mai Hadari Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar da Aikin Titin Koko–Zuru...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin. Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar. Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan gagarumin tallafi, da ya haɗa da bayar da kayayyaki da jari ga rukunin al’umma daban-daban. Yana mai nuni da cewar, wannan mashahurin shiri ya nuna kyakkyawan hangen nesa na Shugaban karamar hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, wajen tallafa wa mutanen karkara da ke fama da kalubale daban daban. Namadi, ya kaddamar da rabon tallafi ga mutane fiye da 350 a karamar hukumar Sule Tankarkar....