2025-02-24@21:50:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 75
«Ragewa»:
Bayanin da babban bankin kasar ta Najeriya ya fitar, ya bayyana cewa an sami wannan koma bayan ne a cikin makwanni uku da su ka gabata. Bayanin na babban bankin na Najeriya ya ci gaba da cewa, kudaden ajiyar Najeriya na waje da a cikin watan Disamba sun kai dala biliya 40,887, sun ragu, sun...
Kotun manyan laifuka a kasar Tunisiya ta daure Shugaban kungiyar al-Nahdha ta masu kishin musulunci Rashid al-Ganushi, zaman kurkuku na tsawon shekaru 20. Haka nan kuma an daure wata ‘yar Jarida Shahrizad Ukkasha wacce take wajen kasar, zaman kurkuku na tsawon shekaru 22. Wata ‘yar jaridar da ita ma ta sami hukuncin dauri, ita ce...
A yayin zaman, Dakta Balarabe ta jaddada tsananin tasirin da katsewar wutar lantarkin ke yi ga muhimman ayyuka, musamman harkokin kiwon lafiya da harkokin kasuwanci a fadin jihohin da abin ya shafa. Ta bukaci ma’aikatan da ke yajin aikin da su maido da wutar lantarki yayin da ake ci gaba da tattaunawa don samun...
A wani rahoto na ibtila’i da ya afku a unguwar Ukubie da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa inda wata mata mai suna Madam Stella ta jefa ‘yarta ’yar shekara shida mai suna Rachael a cikin kogi saboda fushi. A cewar shaidu, Rachael ta je yin wanka a bakin kogi duk da...
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da bai wa ‘yan’uwansu haƙurin jure wannan babban rashi, har ila yau gwamna Dauda Lawal ya yi addu’ar Allah ya bai wa wadanda suka samu raunuka lafiya. Gwamnati za ta yi bincike domin ta gano dalilin afkuwar wannan gobara, domin kaucewa hakan a nan gaba....
Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta sanar da a ci gaba da yi wa maniyyata rajista har zuwa ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu, 2025. A daren Talata 4 ga watan ne hukumar ta amince da kara lokacin a taron da ta yi da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi. Wata sanarwa da...
Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce...

Wani Tsohon Ma’aikacin MDD Ya Yi Kira Ga Amurkawa Su Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Amurka Da Natanyahu
Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta...
An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara. Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar...

Sheikh Na’im Kassim: Za A Yi Jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah A Rana 23 Ga Febrairu Da Ake Ciki
Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin. Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba...
Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow. Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin...
A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa. Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya...
Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya...
Shi ma da yake jawabi, shugaban kungiyar masu tuka ‘yar kurkurar, Jamilu Isyaku ya bayyana jin dadinsa ga Gwamna Radda bisa amsa kiran da suka yi masa na biya masu bukatunsu kan sama masu da keke napep mai amfani da lantarki da kuma ba da tabbacin yin amfani da su yadda ya kamata.
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga...
Sarkin ya yi addu’a Allah ya jiƙansa, ya gafarta masa, kuma ya bai wa iyalansa haƙuri.

Tunawa Da Ranar Wadanda Aka Yi Wa Kisan Kiyashi: Majalisar Dinkin Duniya Ta Wayar Da Kan Dalibai A Abuja
Ishara ”Kada Mu Manta” taron, ya ba da haske game da lokutan soyayyar dangi da alakar kud da kud da ke wanzuwa a cikin iyalai na Yahudawa da al’ummomin kafin Holocaust da alhakinmu na kare hakkin kowa na rayuwa cikin mutunci da zaman lafiya. Da yake gabtar da jawabi a yayin taron jakadan kasar...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar...
Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba. Ita...
Shugaban kasar Amurka ya rattaba hannu kan dokar ba da damar tsare bakin haure kusan 30,000 a sansanin Amurka da ke tsibirin Guantanamo Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce yana son gidan kurkukun sojoji da ke Guantanamo Bay, wanda aka kebance domin tsare fursunonin da ake zargi da ta’addanci, ya kasance a shirye domin...
Sabbin waɗanda aka rantsar sun haɗa da Hon. Sanusi Khalifa, babban mashawarci kan albarkatun ƙasa; Hon. Haladu Ayuba, Mai Bada shawara kan daidaita ɗabi’un jama’a; Hon. Jidauna Tula, babban shawarcesa kan harkokin Shari’a da kuma Hon. Adamu Bello da aka sanya a matsayin babban mashawarci a ɓangaren kasuwanci da masana’antu. Sauran sun haɗa da...
Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as. Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara...

Sojojiun HKI A Kudancin Kasar Lebanon Sun Kashe Mutane Fararen Hula Wasu Kuma Suka Ji Rauni A Yau Lahadi
Ministan kiwon lafiya na kasar Lebanon ya bada sanarwan cewa sojojin HKI a kudancin kasar sun kashe fararen hula 15 sannan wasu 83 suka ji rauni a safiyar yau. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana cewa mutanen kudancin kasar Lebanon sun komawa gidajensu da suke kudancin kasar kan iyaka da...

Falasdinawa Sun Gudanar Da Bukukuwan Tarbar Fursunonin Falasdinawa 114 Da Aka Sako Daga Gidan Yarin Isra’ila
Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan...