2025-04-07@00:31:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 721

«Mahi Ibrahim Inyass»:

    Majaliar Dattawa ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar ba. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar. Kotu ta saki...
    Kasashen Iran da kuma Iraki sun nuna damuwa kan tashe tashen hankulan dake faruwa a Siriya. A wata sanarwa da ta fita ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana matukar damuwarta kan yadda tashe-tashen hankulan da ke yaduwa a fadin kasar ta Siriya, tana mai gargadin cewa, wannan yanayi mara kyau zai share fagen rashin...
    Jagoran kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya baiwa masu shiga tsakani wa’adin kwanaki hudu na tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai a Gaza, yana mai gargadin cewa idan har Isra’ila ta ci gaba da toshe hanyoyin kai kayan agaji a Gaza, to dakarun Yemen za su ci gaba da kai...
    Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta kan cewa kasar nan ta yi asarar tiriliyoyin naira sakamakon ayyukan masu hakar ma’adanai ta barauniyar hanyoyi musamman a jihohi. Gwamnatin ta kuma cafke da gurfanar da ‘yan kasan waje su hudu wadanda suka shiga harkar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, yayin da wasu mutane 320 kuma aka cafke kan...
    Alake ya bayyana cewa majalisar zartarwar ta amince da wani sabon shiri na inganta tsari da kuma dakile asarar kudaden shiga a fannin ma’adinai. A wani bangare na shirin, ya ce gwamnati za ta tura fasahar tauraron Dan’adam don sa ido kan muhimman wuraren hakar ma’adinai da kuma bin diddigin ayyukan ma’adani. Alake ya kara...
    Shugaba Zelensky   na Ukiraniya zai kai ziyara kasar Saudiyya a ranar Litinin, gabanin bude tattaunawar da za a yi tsakanin kasarsa da kuma Amurka da zummar kawo karshen yaki da Rasha. Shugaban na kasar Ukiraniya ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa; Manufar ziyarar tashi ita ce haduwa da yarima mai jiran gado...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa; Tattaunawa da Amurka kaskanci ne, ga shi kuwa al’ummar Iran tana da tunani ne irin na Ashura, ba ta karbar kaskanci. Limamin na Tehran ya yi ishara da yadda duniya ta ga yadda Donald Trump ya wulakanta shugaban kasar Ukiraniya, don haka ya kamata...
    Shugaban Rukunonin Kamfanin Flour Mills Mista John Coumantaros ne, ya tarbi Dantsoho, a lokacin ziyarar aikin, inda suka tattauna kan ci gaban da ake ci gaba da samu da kuma yadda za a mayar da hankali, wajen zuba hannun jari kan aiki, musamman domin Tashoshin Jiragen Ruwan, su raba. A na sa martanin Dantsoho, ya...
    Wani mutum mai shekara 52, Salihu Byezhe, ya yanke jiki ya faɗi yayin da ake Sallar Asuba a wani masallaci da ke ƙauyen Gudaba, a Ƙaramar Hukumar Kuje a Babban Birnin Tarayya, kuma daga baya ya rasu a asibiti. Wani mazaunin yankin, Musa Dantani, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis bayan Byezhe...
    Tsohon Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Dakta Doyin, Okupe, ya rasu. Dakta Doyin Okupe ya rasu ne bayan fama da jinya a sakamakon cutar kansa. Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun ya tabbatar da rasuwar Doyin Okupe ta wata sanarwa a safiyar Juma’a.  
    Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade...
    Kungiyar ta yi tir da tsarin da hukumar kulawa wutar lantarki ta yi,wanda take neman ta ba masu amfani da wuta, nau’i- nau’in da suke ko ta kai su,ba domin komai ba don wata magana ta kara bunkasa samun wutar lantarki fiye da irin halin da ake ciki yanzu. Kamar dai yadda kungiyar tace tsarin...
    Ana ci gaba da takun saka tsakanin Rasha da Faransa biyo bayan kalaman Emmanuel Macron na baya-bayan nan game da kayyade makaman nukiliya. Moscow ta dauki wadannan kalamai a matsayin barazana kai tsaye, yayin da Paris ke kare matsayinta ta hanyar jaddada bukatar kare Turai, Wanda ya nuna yadda ake samun rashin jituwa sosai kan...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da jami’an Birtaniya suka yi na cewa Tehran na barazana ga tsaron kasar ta Burtaniya. A cewar jami’an Iran, Ingila na zargin Iran da wani abu da ta yi fice a kai. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya mayar da martani da kakkausan lafazi...
    Wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, wanda mutane 15,257 daga fadin kasashe 38 suka bayar da amsa, ya bayyana cewa manufar sanya muradun Amurka gaba da komai tana da mummunan tasiri kan dangantakar Amurkar da Turai, yayin da adadin wadanda suka aminta da Amurka daga kasashe kawayenta daga cikin masu bayar...
    Sakatare-janar na kungiyar malaman musulmi ta duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da su hada kai da al’ummarsu wajen goyon bayan Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi, ya yi kakkausar suka kan ci gaba da goyon bayan da Amurka ke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana...
    Har ila yau, jim kadan bayan ficewar Zelenskyy daga Washington, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Jamus da Faransa da Italiya da kuma Birtaniya suka yi gaggawar mara masa baya, yayin da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kakkausar suka ga Ukraine wanda a cewar Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ta...
    Allah Ya yi wa babban malamin Musulunci a Najeriya Sheikh Sa’idu Hassan Jingir rasuwa, bayan fama da rashin lafiya. Marigayi Sheikh Sa’idu Hassan Jingir shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na II na Ƙasa Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bida Wa Iqamatis Sunan (JIBWIS). Ana sa rana gudanar jana’izarsa da misalin ƙarfe biyu 2:00 na rana a...
    Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai, ya ce, Iran tana kokarin ganin cewa an gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi domin tattauna batun barazanar tilasta mutanen Gaza yin hijira. Haka nan kuma ya ce, wannan tunanin na korar falasdinawa daga Gaza, ba wani abu ba ne sai cigaba da kisan kiyashi, ta hanyar amfani...
    Jaridar Telegraph da ake bugawa a Birtaniya ta buga wata kasida da a ciki ta bayyana  zancen aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya a matsayin abin dariya wanda yake son komawa da gaske bayan da ya kasance abin dariya. Marubuciyar wannan kasida Allison Pearson ta ce ba a taba yin wani lokaci da fira ministan...
    Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona. Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar...
    A wani yunkuri na bunkasa sana’o’in hannu da kuma karfafa wa masu bukata ta musamman, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ta kaddamar da wata cibiyar kasuwanci ta mata masu sarrafa kayayyaki tare da baiwa masu bukatar su 450 a yankin Karfi. Wannan yunƙurin na da nufin ƙarfafa su...
    Yayin da watan Ramadan ya shiga kwana na 6, masu lura da al’amura da dama na kokawa kan tsadar kayan marmari a Kano, wanda suke ganin wani muhimmin bangare ne na karin kumallo da ake yi a sahur da kuma lokacin buda baki.   Malam Bello Ibrahim da Abdulmajeed Baba, masu amfani da ’ya’yan itatuwa...
    An yi kira ga al’ummar musulmi da su kara yawan ruwa da ‘ya’yan itatuwa a lokacin azumin watan Ramadan domin inganta sinadaran jiki.   Wani kwararre a fannin lafiya a Jami’ar Ilorin, Farfesa AbdulRahman Afolabi ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin, jihar Kwara.   Ya ce...
    An yanke wa wasu mutum uku da aka kama da laifin fyaɗe hukuncin ratayewa da kuma dandaƙewa a Jihar Kaduna. Kwamishinar Kula da Walwalar Jama”a, Hajiya Rabi Salisu, ta bayyana fatan cewa hukuncin da kotu ta yanke wa masu laifin zai zama darasi ga masu muguwar ɗabi’ar ta fyaɗe. Da take sanar da hakan a...
    Jakadan JMI a hukumar makamashin Nukliya Mohsen Naziri ya bayyana cewa sabbin takurawar da kasashen yamma, musamman Amurka suke wa kasarsa ba zasu yi tasiri ba. Banda hakan zasu cutar da wadanda suka dora mana su, Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Naziri yana fadar haka a Jawabin da ya gabatar  a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fiye da wata guda ke nan bayan da Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai  har...
    Wani gini mai hawa biyu ya rufta a yankin Lekki da ke Jihar Legas wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu shida. Jami’an bayar da agaji daga hukumomin LASEMA da NEMA sun ceto waɗanda suka jikkata kuma an kai su Babban Asibitin Marina domin kula da lafiyarsu. Majalisar Kano ta yi...
    Hakika, kasar Sin ta nuna bajinta a kan habakar da take samu a fagen kere-keren mutum-mutumi musamman ma a yayin bikin bazara na shekarar 2025 inda aka jero wasu mutum-mutumi 16 suka gudanar da raye-raye masu kayatarwa a wani bangare na shagulgulan jajibirin bikin. Yadda mutum-mutumin suka rika kwarkwasa da rawa da juyi ya yi...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya ba da gudummawar Riyal biliyan 40 ga wata kungiyar agaji da mai rajin ganin an sako fursunoni mabukata da aka samu da laifin aikata laifuffuka wandanda  ba na son rai. A duk shekara, a cikin watan Ramadan, wannan kungiya mai zaman kanta ta...
    Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar kan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, inda ta zarge shi da cin zarafinta. Kwamitin ya bayyana ƙorafin a matsayin “mattacen ƙorafi tun kafin a duba shi.” Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio...
    Bayan wannan jawabi, Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafi bisa dokar majalisar, imda ta zargi Akpabio da cin zarafinta da kuma amfani da matsayinsa ba daidai ba. Ta kuma nemi izinin miƙa ƙorafin ga majalisar a hukumance. Majalisar ta tura ƙorafin zuwa Kwamitin ladabtarwa domin ci gaba da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare....
      Ya kuma bukaci kwamitin da ke da alhakin rabon kayayyakin da su hada kai da shugabannin al’umma da na addini a yankunansu domin ganin an raba kayan abincin yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul  tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan...
    Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel kan zargin almundanar naira biliyan 700. EFCC ta tsare tsohon gwamnan ne bayan ya amsa gayyatar ta a ranar Talata domin amsa wasu tambayoyi kan zargin karkatar da kuɗi da wata ƙungiya mai rajin yaƙi da...
    Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza. Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu...
    “Wannan kasafin kuɗin ya nuna sabon gagarumin fifiko a kan harkar tsaro, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, ma’adanai, noma, da sauran sassa masu matuƙar tasiri kan jin daɗin al’umma da cigaban tattalin arzikin su.”   Ya ƙara da cewa shekarar 2025 ita ce “shekarar tabbatar da cigaba,” inda sauye-sauyen da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola...
    Sai dai, Firaministan Ukraine Denys Shmyhal ya ce, har yanzu Kyiv na da isassun makamai da za ta kai wa dakarunta dake yaki a gaba-gaba.   “Taimakon kayayyakin Soji na Amurka yana da mahimmanci kuma yana ceton dubban rayuka, don haka, Kyiv za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta ci gaba da alaka...
    Rahotanni sun nuna cewa kasar Yamen ta gargadi isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gaza, kana ta yi alkawarin fadada hare-harenta a tel Avivi matukar ta dawo da kai hari kan alummar falasdinu, Tace: matakin da isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin agaji da jin...
    A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce:  ya kamata...
    Masarautar Katsina ta ba wa dagattai da masu unguwaninta horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya. An gudanar da taron ilmantarwar na tsawon kwanaki uku ne a kan yadda za a assasa zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar sasanci don samun aminci mai dorewa. Shugaban kamfanin tuntuba na Green...
      Yayin da al’ummar Musulmai  a Najeriya da duniya ke fara azumin watan Ramadan, Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta aike da sakon fatan alheri, tana kira da a yi amfani da wannan lokaci mai daraja wajen sabunta zukata da nuna tausayi da karfafa hadin kai a kasa.   A cikin wata sanarwa da...
    Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin...
    Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna  a halin yanzu sun isa kasar Poland. Jaridar “Bloomberg” ta bayyana...
    A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso. Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kira ga gwamnatin kasar Turkiya ta sake tunani kan kalamanta dangane da JMI. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a jiya Litinin, a taron mako mako da ya saba gabatarwa a ko wace litinin. Ya yi...
    Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya...
    Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya...