2025-04-15@09:47:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 131
«ɗanyen mai»:
Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari kan laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa makami a unguwar Fagge da ke Jihar Kano. Kotun da ke zamanta a yankin Mai Alluna ta yanke wa matashin hukuncin ne bayan bayan alƙali ya kama shi da laifin yunƙurin soka wa mahaifinsa almakashi saboda...
Wata ’yar kasar Jamus mai suna Alexandra Hildebrandt mai shekara 66 ta ja hankalin jama’a bayan ta haifi ɗanta na 10 ba tare da maganin haihuwa ba. Haihuwar ta faru ne a ranar 19 ga Maris a Asibitin Charité da ke Berlin da taimakon likita. Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato ’Yan bindiga...
Tsohon ɗan wasa, kuma tsohon mai horas da ’yan ƙwallon Super Eagles ta Najeriya, Christian Chukwu ya rasu. Christian Chukwu ya rasu ranar Asabar yana da shekara 74. Fashewar bam a mota ta kashe mutum takwas a Borno An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato Christian Chukwu ne kyaftin ɗin tawagar Super Eagles...
Jami’an tsaro sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Gwaska Ɗan Ƙarami da wasu mayaƙa 100 a Jihar Katsina. Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dokta Nasir Mu’azu ya bayyana matakin a matsayin wata gagarumar nasara a yaƙi da ’yan bindiga ake yi a jihar. An kama mutum 8 kan...
Al’ummar garin Idi Araba da ke Ƙaramar Hukumar Munshin a Legas sun wayi gari da fashewar wani abu mai ƙarar gaske, wanda ya tayar da gobara a wani garejin ’yan gwangwan da ke unguwar. Lamarin da ya faru ranar Alhamis na makon jiya ya yi sanadiyar mutuwar wani da ke sana’ar gwangwan mai suna Najib...
’Yan bindiga sun kai hari garin Mahuta da ke Ƙaramar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, inda suka harbi wani alkali, Rabiu Mahuta, a hannu da kuma dansa. A lokacin harin na daren Talata, maharan sun raunata mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 13, ciki har da matar alƙalin da kuma biyar daga...
Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan cibiyoyin da ke boye bayanai kan yadda ake biyan dalibai rancen kudi yayin da suke neman biyan kudaden makarantun daga hannun daliban. Sanarwar da Manajin Darakta na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr ya fitar ta bayyana cewa, sakamakon binciken...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin ɗanyen man fetur yake ƙara faduwa a kasuwannin duniya. Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan ƙasar, kama daga masana tattalin arziki zuwa jami’an gwamnati, kasancewar ɗanyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kuɗaɗen...
Guguwar ruwan sama ya lalata gidaje da dama a ƙaramar hukumar Shanga ta Jihar Kebbi. Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya jajanta wa al’ummar Garin Kestu da ke unguwar Atuwo a Ƙaramar hukumar Shanga, ya kuma buƙaci iyalan waɗanda abin ya shafa da su ɗauki lamarin a matsayin wata ƙaddara. Yadda Tinubu ya taimaka wa...
Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Da yake jawabi a taron...
Manchester City na nace kan buƙatar ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 27, yayin da take shirin rabuwa da ɗanwasanta na Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33. (UOL esporte – in Portuguese) Chelsea a shirye take ta biya fam miliyan 102 kan ɗanwasan Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24. (Fichajes...
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da sayar da ɗanyen mai da man da aka tace farashin Naira, maimakon amfani da dalar Amurka. Wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziƙin cikin gida, rage matsin lamba kan kasuwar musayar kuɗi, da kuma bunƙasa makamashi. ’Yan bindiga sun mamaye...
Wasu ’yan bindiga a ranar Lahadin da ta gabata sun kai harin ɗaukar fansar kashe ƙasurgumin ɗan ta’addan nan, Kachalla Isuhu Yellow da aka fi sani da Ɗan Isuhu. ’Yan ta’addan sun kai harin ne ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, domin ɗaukar fansar kashe jagoransu da jami’an tsaro suka yi...
Kotu ta dage shari’ar kisan Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayu, 2025, domin waɗanda ake tuhuma su fara gabatar da shaidunsu. Babbar kotu da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, ta ɗage shari’ar ne biyo bayan bayan ɓangaren masu ƙara su. gabatar da ga Manjo Janar U....
Hukumar Yaƙi Da Cututtuka Masu Yaɗuwa a Nijeriya, NCDC ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar sanƙarau a Nijeriya ya kai 151. Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna ƙaruwar waɗanda suka kamu da cutar daga 74 zuwa 156 a jihohin ƙasar 23. Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu...
Jami’an tsaro sun jiran kayan ado na ’yan kunnayen zinare su wuce ta na’urar binciken fasinjan jirgin sama kafin a gano kayan da aka sace a hukumance. An kama wani mutum mai shekara 32, mai suna Jaythan Lawrence Glider bisa zargin satar ’yan kunne biyu na zinare na sama da Dala Amurka 769,000 kwatankwacin Naira...
Ɗan wasan ƙasar Belgium, Kevin De Bruyne, ya sanar da cewa zai yi bankwana da ƙungiyar Manchester City ta Ingila a ƙarshen kakar bana. Fitaccen ɗan wasan tsakiyar mai shekaru 33 ya sanar da hakan ne cikin wata saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X. Tsohon Gwamnan Oyo Olunloyo ya riga...
Gwamnatin Jihar Borno ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo wajen yin kalamai masu nuna barazana da al’adunmu na rashin ɗa’a da rashin sanin ya kamata. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar yaɗa labarai da tsaron cikin gida ta jihar Borno ƙarƙashin Kwamishinanta Farfesa Usman...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda...
Wasu da ake zargin Boko Haram ne sun kai hari sansanin horas da ‘yan sanda na PMFTC da ke Limankara, a Gwoza, inda suka kashe Sufeton ’yan sanda guda ɗaya. Sun kai harin da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025, yayin da jami’an tsaro suka fita sintiri a ƙafa....
An kashe wani sufeton ɗan sanda a yayin wani kwanton ɓauna da wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a kwalejin horar da rundunar ’yan sanda (PMFTC) Camp Limankara, Gwoza a Borno. Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa majiyar Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 0600 a ranar...
An shiga firgici da safiyar Alhamis ɗin nan, bayan wani kwale-kwale na kamfanin Lagos Ferry Services (LAGFERRY) ya kama da wuta a tashar jirgin ruwa ta Ipakodo da ke Ikorodu, a Legas inda mutane da dama suka jikkata. Majiyoyi sun ce tashin wutar ta haifar da wata babbar gobara da ta tashi daga injin jirgin...
Kociyan Manchester City, Pep Guardiola, ya ce ɗan wasan gaban ƙungiyar, Erling Haaland, zai yi jinyar mako bakwai a sakamakon raunin da ya samu a idon sahunsa a wasan kofin FA da ƙungiyar ta fafata da Bournemouth a ranar Lahadi. Ɗan wasan na ƙasar Norway bai ƙarasa wasan ba, inda aka cire shi a minti...
Duk da haka, ɗalibai masu kammala makaranta sai sun jira amincewar Majalisar Jami’ar kafin su samu damar duba sakamakonsu. Ana sa ran wannan ci gaba zai inganta ayyuka a Jami’ar da kuma sauƙaƙa wa ɗalibai gudanar da harkokin karatunsu cikin sauƙi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta kaddamar da wani tsari na yanar gizo wanda zai baiwa dalibai damar shiga da duba sakamakon kammala karatunsu ta hanyar lambobi. Wannan sabon yunkuri shine karo na farko da cibiyar ta samar da sakamako ta hanyar irin wannan dandali. An sanar da shirin ne a cikin wata takarda...
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da kashe matafiya ’yan Arewa da aka yi a Jihar Edo. Saboda haka Sarkin ya ce suna dakon ganin hukuncin da za a ɗauka dangane da faruwar wannan mummunan lamari. Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka Dalilin...
Har yanzu dai kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan na ci gaba da tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far...
Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin...
Gwamnatin Jihar Kaduna, ta sanar da shirin ɗaukar ma’aikatan lafiya 1,800 aiki don inganta tsarin Kiwon Lafiya a Matakin Farko (PHC) a faɗin jihar. Wannan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin ma’aikata da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar. Ƙungiyar JNI ta raba wa marayu 50 kayan Sallah a Borno An sake harbe wani...
Akwai yiwuwar Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa wata dokar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) a wasan gasar La Liga wanda ta doke Osasuna. Rahotanni na cewa ƙungiyar Osasuna za ta shigar da ƙorafi kan wasan da Barcelona ta doke ta da ci 3-0, saboda zargin saɓa dokar FIFA kan amfani da...
Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Ɗan Mudale da ya addabi mazauna yankin Tsafe da kewaye. Rundunar ta ce a jiya Alhamis ne ta daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta jihar. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano...
Ɗaya daga cikin ƙasurguman ’yan ta’addan da suka addabi al’umma a Jihar Zamfara da kewaye, Kachalla Isuhu Yellow ya kwanta dama. BBC ya ruwaito cewa an kashe ƙasurgumin ɗan bindigar ne a yayin wani rikicin cikin gida da ya kaure tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga. Bayanai sun ce lamarin ya faru da yammacin yau Alhamis, bayan...
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi...
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi...
Daraktan Fim ɗin Mai martaba, Prince Daniel (ABOKI), ya ce ba gaskiya ba ne batun da ake yaɗawa cewa yana fuskantar tsangwama a Kannywwod saboda bambancin addininsa. A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Aboki ya ce shi ma batun cewa ana nuna masa bambamci a Nollywood saboda ɗan arewa ne ba shi da...
Ƙungiyoyin ƙwadago reshen Jihar Ribas sun yi barazanar ɗaukar mataki muddin gwamnatin Nijeriya ba ta janye dokar-ta-ɓacin da ta ayyana a jihar ba. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar gamayya da ƙungiyoyin ƙwadagon na NLC, TUC da JNC suka fitar a ranar 24 ga watan Maris. Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027...
1. Gibɗa a cikin Addini: Wannan ya ƙunshi yin gasa a ibada kamar sallah, ko azumi, ko karatun Alƙur’ani, da sadaka, ko mutum ya so ya zama hamshaƙin mai kuɗi da zai rinƙa taimaka wa addini da bayin Allah. Ko kuma mutum ya nemi ya zama malami ko jagora a addini don ya koyar da...
Za a ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya. Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna. Gaskiyar...
Wasu fusatattun matasa sun daka wawa kan kayan abincin tallafin azumi da ɗan Shugaba Nijeriya, Seyi Tinubu zai raba a Jihar Gombe. Aminiya ta ruwaito cewa duk da cewa bai kai ga zuwa jihar ta Gombe ba, amma kayan abinci da zai raba tuni sun isa jihar. Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar...
Wata mata mai suna Krystena Murray ’yar Amurka, wadda ta ɗauki ciki tare da haife jariri namiji ba tare da sanin cewa ba ɗanta ba ne, ta fara ɗaukar matakin shari’a a kan wani asibitin da ke taimaka wa mata samun ciki ta hanyar dashen ɗantayi (IBF). Matar tana zargin asibitin da yi mata dashen...
Al’ummar Jihar Kano, sun shiga shida ruɗani yayin da rikicin Masarautar jihar, ya ɗauki wani sabon salo game da shirin gudanar da bikin hawan salla. Tsagin sarakunan jihar na 15 da na 16, wato Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla duk da shari’ar da ke gudana kan rikicin...
Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Munna Albadawi da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno, ta lalata wasu gidaje 10 tare da salwantar da rayuwar yaro mai shekara 7 mai suna Abubakar Gargar. A cewar shugaban sansanin, Babangida Mahmud gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 asubahin safiyar...
Ya kuma nuna jin daɗinsa da irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Alhassan Yahayan, inda ya ce an ɗora ƙungiyar kan kyakkyawan turbar da ya kamata don ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunƙasa aikin jarida a Nijeriya. Yahaya ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin Jihar Gombe...
’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar...
’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar...
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kama Lawal tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Mayu. A wata shari’a daban, kotun ta kuma bayar da umarnin kama Jibrilla Muhammad, tsohon Manajan Darakta na Kamfanin Zuba Jari da Kadarorin Kano (KSIP), bisa zargin ɓatan Naira miliyan 212.4. A gefe...
Wata matashiya mai suna Aleysha Ortiz ’yar shekara 19 da ke Jihar Connecticut a Amurka ta dauki matakin shari’a a kan tsohuwar makarantar sakandaren gwamnatin da ta yi saboda gazawarta ta hanyar ba ta damar kammala karatu “da sakamako mai daraja” duk da ta kasance maras ƙoƙari. A watan Yunin shekarar bara ce, Aleysha Ortiz...
Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta buƙaci Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya nemi afuwar ɗaliban malamin bisa abin da ta kira rashin adalci da aka musu. Idan kuwa bai yi hakan ba kafin ƙarshen watan Ramadan, za su maka shi a kotu. An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a...
An kama wata malamar makarantar sakandare ta California a Amurka da ake zargi da lalata da wani ɗalibi mai shekaru 17. Wannan da ba shi ne karon farko ba da aka tuhumi wani da irin wannan hali ba a makaranatar. Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi...