2025-02-22@21:52:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 19

«Ivory Coast»:

    Bayan shekaru 47, Faransa ta janye daga sansanin sojinta mafi girma a kasar Ivory Coast A hukumance Faransa ta mayarwa kasar Ivory Coast babban sansanin soji da ta mamaye kusan shekaru hamsin a kusa da birnin Abidjan, a wani bangare na yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla. Filin tashar jiragen ruwa na Port Bouet, wanda ke dauke da bataliyar sojoji na 43 da na ruwa, ya shaida bikin mika ta, inda aka daga tutar Ivory Coast a farfajiyar sansanin, kuma an canza sunan ta da sunan babban hafsan soji na farko a Ivory Coast, Thomas Dakine Ouattara, wanda hakan ya kawo karshen kasancewar Faransa a kasar tun shekarar 1978. Ministan tsaron kasar Ivory Coast, Tene Berahima Ouattara, ya jaddada cewa:...
    Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Shirye-shiryen Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
    Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran. Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin. Bangarorin sun bayyana kyakyawan fatan musayar bayanai da shirye shirye a tsakaninsu da nufin karya laggon kafofin yada labarai na kasashen yamma dake yada gurbatattun bayanai da rahotanni kan kasashen. jakadan na NIjar, ya kuma yi tinu da irin kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.
    Kwamandan sojan na Iran  Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa, Iran tana da cikakken shirin na aiwatar da umaranin babban kwamandan sojin kasa, kuma akidarmu ta yaki, ta ginu ne akan kariya, amma kuma a lokaci daya za mu fuskanci duk wanda ya kawo mana hari, da karfi. Birgediya  janar Hamid Wahidi ya bayyana hakan ne dai a lokacin bikin kaddamar da lambobin yabo da sadaukarwa ga iyalan shahidai na sojan sama, inda ya ce: “A wannan lokacin da ake ciki, Muna cikin wani yanayi mai matukar hatsari a duniya, amma a ranar sojan sama jagoran juyin juya halin musulunci ya shata mana ka’idoji masu kima da za mu yi aiki da su da, kuma za su kasance wadanda...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin lamba, yana mai jaddada cewa; Kasarsa ba ta neman yaki da wata kasa, sai dai tana kokarin karfafa dangantakar abokantaka da kasashen makwabta. Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai lardin Bushahar inda ya gana da al’umma tare da jinjinawa sadaukarwar shahidai musamman shahidan wannan lardin, a daidai lokacin da ake cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rediyo na daga cikin kafofin da al’umma da dama suka dogara da su don jin labarai, shirye-shirye da kuma samun nishadi. Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da al’umma da dama kai musamman duba da yadda aka bayar da shaidar cewa tafi kowace kafa saurin yaɗa bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Sai dai a wannan gaɓa ana ganin gidajen rediyo a Arewacin ƙasar nan na samun koma baya, la’akari da yadda a wasu lokutan wasu suke rufe harkokinsu su ɓace...
    Babban hafsan hafsishin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Bakri ya bayyana cewa sojojin Iran a shirye suke fiye da ko wani lokaci don kare JMI daga makiyanta. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Bakiri ya bayyana haka ne a lokacinda yake tattaki na bukukuwan cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a nan birnin Tehran a safiyar yau Litinin. Ya ce: Halin da sojojin JMI suke ciki yafi na ko wani lokacin kyau, don haka a shirye suke su gudanar da ayyukansu a duk lokacinda bukatar haka ta taso. Dangane da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kuma, Janar Bakiri ya bayyana cewa, jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul...
    Sojojin Sudan suna kokarin canza ma’aunin yaƙin kasar bayan da suka sun tunkari birnin Khartoum fadar mulkin kasar domin yantar da shi gaba daya Babban birnin kasar Sudan, Khartoum, shi ne tushen rikicin kasar da a halin yanzu aka shafe makonni ana gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan dakarun kai daukin gaggawa, amma fadan ya kara kamari a ‘yan kwanakin da suka gabata. Sojoji suna kara ci gaba da tunkarar babban birnin kasar bayan fitattun sojojin kasar da suka hada da sojoji da mayaka masu goyon bayan sojoji da hukumar leken asiri da dakarun tsaron Sudan da suke sansanin Haddab da ke bangaren arewa maso gabashin yankin Gabashin Nilu a arewa maso gabashin Khartoum suka doshi birnin na Khartoum da...
    Shugaban Ukraine, Bolodymyr Zelensky ya ce duk wata tattaunawa da za a yi kan makomar kasarsa, wajibi ne a sanya kasashen yamma da Amurka da Rasha da kuma Ukraine din a ciki. A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Bolodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna kai tsaye da shugaba Bladimir Putin, idan har hakan ne zai kawo karshen yakin da suka kwashe kusan shekara uku suna gwabzawa. Sai dai shugaba Zelensky ya sake nanata bukatarsa ta karin makamai domin ci gaba da samun nasara kan Rashar.
    Iran ta ce a shirye take ta tallafa wa Burkina faso a yakin da take da ta’addanci. Wannan bayyanin ya foto ne bayan wata ganawa tsakanin Firaministan Burkina Faso Rimtalba Jean Emmanuel Ouédraogo da jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Burkina Faso, Mista Mojtaba Faghihi a Ouagadougou. Taron dai ya baiwa mutanen biyu damar sake yin nazari kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashensu. A cikin wannan yanayi, Iran ta bayyana aniyar ta na tallafawa Burkina Faso, a kokarinta na dakile matsalar rashin tsaro. Tehran, ta bakin jakadanta, ta kuma bayyana sha’awarta kan sauran fannonin hadin gwiwa, kamar su noma, masana’antu, likitanci da al’adu. Ya ce Iran a shirye take ta ba da dukkan goyon bayan da ya dace ga Burkina...
    Xi: Kasar Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da IOC Don Inganta Wasannin Olympic Na Duniya 
    Mahukunta gidan Radiyon tarayya na kaduna sun kai wa iyalan Alhaji Bala Albabello ta”aziya wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar litini 3 ga watan fabrairu na shekarar 2025. Shugaban gidan Radion, Malam Buhari Awwalu ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan marigayin dake Tudun Jukun a zaria. Malam Buhari Awwalu ya jajantawa iyalan marigayin,inda ya yi addu’ar Allah ya bai iyalan hakurin rashin sa,kuma ya sa a rinka tunawa da kyawawan dabi’un sa na taimakawa marasa karfi da kuma Dora al’umma akan turbar kasuwanci. Ya kuma roki Allah da ya sanya shi a aljannar firdausi. Da ya ke jawabi a masadin iyalan,Alhaji Hassan Abdulwahab ya yi bayanin cewa marigayi Albabello ya sadaukar da rayuwar sa ce wajen hidimtawa al’umma. Cikin...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, wani jami’in kungiyar wanda baya son a bayyana sunansa ya ce kungiyar a shirye take a fara tattaunawar.. A wannan tattaunawa dai ana saran za’a fayyace filla-filla kan yadda al-amura zasu kasance a nan gaba a zirin gaza. Labarin ya kara da cewa jami’an Hamas sun bayyana haka ne a ranar da aka yi musayar fursinoni da HKI a garin Khan Yunus....
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya  yaba wa yadda kungiyar Hamas ta jajurce da ci gaba da wanzuwa a dunkunle duk da cewa kwamandan dakarunta Muhamamd Dhaif ya yi shahada. Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya gabatar da jawabi ne na tunawa da zagayowar lokacin shahadar Salih al-Simad wanda daya ne daga cikin manyan shugabannin Ansarullah, ya kara da cewa, ci gaba da wanzuwar kungiyar ta Hamas yana daga cikin muhimman ayyukan da Muhammad Dhaif ya aiwatar a lokacin rayuwarsa. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya mika sakon ta’aziyyar shahadar Muhammad Dhaif ga kungiyar ta Hamas, tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan jagorori abin koyi saboda ruhinsa na imani mai karfi, azama da ruhi na...
    Ya kara da cewa, “a halin yanzu ,ana gudanar da aikin shimfida tagwayen hanyoyi a cikin tsakiyar garin Argungu da sauran wasu ayyukan ci gaba a masarautar. Saboda haka, wannan wata dama ce na kara shirye-shirye don tarbar baki da ke zuwa kallon shirin daga cikin gida da ketare. Wannan al’ada ce fitacciya a masarautar Argungu.   “Muna godiya da fahimta da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, da mahalarta wannan biki,” in ji Mataimakin Gwamnan jihar Kebbl Sanata Abubakar Umar Tafida.
    Shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na shekarar 2025 sun gabatar da wata “liyafar al’adu” mai kyau da ban sha’awa, kuma mai fasahohi ga masu kallo na gida da waje, bisa sabbin dabaru. Ya zuwa karfe 2 na sanyin safiyar yau Laraba, a dukkan kafafen yada labarai, yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG ya kai sau biliyan 16.8, wanda ya karu da kashi 18.31 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Bugu da kari, yawan masu kallon shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na 2025 ta hanyar talabijin yayin da aka watsa shi kai tsaye a cikin kasar, ya kai kashi 78.88 cikin dari, wanda ya kafa sabon tarihi a cikin...
    Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya fitar da jerin shirye-shiryen shagalin murnar bikin bazara na bana a yau Talata. Shagalin na bana zai kunshi nau’o’in shirye-shirye daban-daban, kamar wake-wake da raye-raye da wasannin kokawa na gargajiya da na siddabaru da sauransu, domin murnar zuwan sabuwar shekarar gargajiya ta Sin tare da masu kallo dake fadin duniya. A lokaci guda, wasu kafafen yada labarai 2,900 a kasashe da yankuna sama da 200 dake fadin duniya, za su kama tashoshin talabijin na CGTN na kasar Sin na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Rashanci da sauran dandamali dake amfani da harsunan waje har 82, wajen watsawa tare da bayar da rahotannin shagalin bikin bazara na bana....
    Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya bayyana damuwarsa game da matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka na dakatar da taimakon kasashen waje daga Amurka yayin da sabuwar gwamnatin Amurka ke aiwatar da sabbin manufofinta na ketare, kamar yadda mai magana da yawun Guterres ya bayyana. “Ya yi kira da a yi la’akari da halin da ake ciki don tabbatar da ci gaba da samar da muhimman ayyukan ci gaba da na jin kai ga al’ummomin da ke da rauni a duniya,” in ji Stephane Dujarric ga manema labarai. ” Ya ce akwai al’umomin da suka dogara da wannan tallafin,” inda ya kara da cewa Amurka na “daya daga cikin manyan masu ba da agaji” a duniya....
    An gudanar da gwajin wasan kwaikwayo karo na biyar na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025 jiya Lahadi. Ya zuwa yanzu, an kammala dukkanin ayyukan share fagen shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa na CMG na 2025. (Safiyah Ma)
۱