2025-02-20@08:58:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14

«na da ayyuka»:

    A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci. Bayan taron, ya kuma amsa tambayoyin ‘yan jaridu, game da yadda kwamitin sulhu na MDD zai karfafa kwarewarsa ta gudanar da ayyuka, da matsayin kasar Sin kan batun Gaza da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)    
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’el Baghae ya ce gwamnatin kasar Iran zata aika tawaga mai karfi zuwa kasar Lebanon don halattar Jana’izar Sayyid Hassan Nasarallah wanda za’a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa. Bakha’I ya kara da cewa,  zamu halarci Jana’izar a kasar Lebanon, kuma zamu aika da tawaka wacce zata kunshi manya-manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini. A ranar Talatan da ta gabata ce wani jami’an kungiyar ta Hizbullah, ya bada sanarwan cewa baki daga kasashe 79 ne zasu halarci jana’izar. Sheikh Ali Daher shugaba kwamitin gudnar da jana’izar ya kara da cewa, ranar zata kasashen ranar sabonta bai’a da marigayin da kuma wanda ya gaje shi. A ranar 27 ga watan Satumba shekara ta...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi da marecen jiya Lahadi inda ya tabo  muhimman  batutuwa da su ka shafi kasar ta Lebanon da kuma yammacin Asiya. Sheikh Na’im Kassim ya ce wajibi ne ‘yan sahayoniya su janye sojojinsu daga kudancin kasar ta Lebanon domin babu wani dalili na cigaba da zamansu. Shekih Na’im Kassim ya bayyana ranar 23 ga watan nan na Febrairu ta jana’izar Shahid Sayyid Hassan  da kuma shahid Hashim Safiyuddin a  matsayin ranar jaddada mubaya’a ga tafarkin da ya tafiyar da rayuwarsa a kansa da shi ne gwgawarmaya. Babban makatakardar kungiyar ta Hizbullah dai ya gabatar da jawabi ne na tunawa da jagororin Hizbullah da su ka gabata, inda...
    Binciken shiyya-shiyya na ayyukan ya nuna cewa shiyyar Kudu-maso-Kudu ta geo-siyasa ce ta kan gaba a jadawalin ayyuka 114 da aka yi watsi da su, inda Jihar Akwa Ibom ke kan gaba da ayyuka 87. An nakalto cewa kawo yanzu gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya zuba Naira biliyan 47.93 cikin ayyuka 36 na kwamitin kudi da manufofin gwamnatin tarayya (FGPC) da ya gada, da kuma Naira biliyan 4.04 cikin 51 na ayyukan gaggawa (EIPs) da ya gada daga gwamnatin da ta shude, adadin da ya kai Naira biliyan 51.96. Shiyyar Arewa maso yamma ta biyo bayansu da ayyuka 44 da aka yi watsi da su, wanda jihar Zamfara kadai ke da ayyuka 33 da ba a kammala ba....
    Gwamnatin tarayya ta yabawa gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa kammala aikin kaso 97 na ayyukan tituna da ya gada daga gwamnatin da ta gabata a jihar. Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Auyo yayin kaddamar da shirin wayar da kan jama’a da gwamnati da al’umma a jihar Jigawa. Badaru wanda ya nuna gamsuwarsa matuka, ya ce gwamnatin jihar ta kammala ayyukan tituna guda 23 cikin 26 da ta gada. Ya kara da cewa sauran ayyukan tituna guda uku sun kusa kammaluwa domin amfanin al’umma da ci gaban tattalin arzikin jihar. Ya kuma bayyana cewa gwamnati mai ci za ta kawo karin ayyukan raya kasa, don haka akwai...
    Babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Cai Qi, ya yi kira a ranar Laraba, da a ci gaba da yin kokari wajen kawar da ayyukan da ba su da ma’ana, da rage nauyin da ke wuyan jami’an kananan matakai, don tabbatar kyakkyawan salon aiki tsakanin ’yan jam’iyya da jami’ai wajen cimma burin da aka sa a gaba a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 14 wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025. Cai, wanda kuma mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ne, kuma mamba a sakatariyar kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a wani taro na matakin koli game da wannan batu. Taron ya bayyana cewa, ya kamata a mayar da hankali wajen...
    A wani umurnin da ya bayar Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Alilul Khami’nae ya sanya babban sakataren kungiyar Hizbullah a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Bayan shahadar Sayyed Hassan Nasarallah da kuma Sayyed Hashim safiyuddeen An zabi sheikh Na’em Kasim a matsayin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah a kasar Lebanon. Kafin haka dai Shahid Sayyed Hassan Nasarallah ne mai wakiltar jagoran a kasar ta Lebanon. Sheikh Qasim dai  ya taka rawar a zo a gani  wajen yakin da kungiyarsa ta shiga da HKI na watanni 15.. Kuma ana saran shi ne zai zama mai fitar da kungiyar zuwa tudun na tsira daga halin da ta shiga ciki ya kuma ci gaba da yakar kungiyar.
    “An zargi Asibitin da yin aiki ba tare da rajista ba da kuma yin ayyukan likitanci a cikin wani gidan haya da ake ganin bai dace da ayyukan kiwon lafiya ba.   “Bincike na farko ya nuna cewa, wani dattijo kuma shugaban Al’umma ya rasu sakamakon tiyata da aka yi masa a Asibitin, yayin da wasu rahotanni suka nuna cewa, majinyata da dama sun tsira da kyar daga bisani aka kai su wasu Asibitoci don samun kulawar gaggawa.   “Da isar su, tawagar binciken ta gano asibitin a cikin wani mawuyacin hali da rashin tsafta,” in ji shi.
    Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin. Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba filin saukar jiragen sama na birnin Beirut, yayin da shi kuma Sayyid  Hashim Safiyuddin za a binne shi a mahaifarsa ta Deir-Kanun dake kudnacin Lebanon. Wani bayanin da Sheikh Na’im Kassim ya yi, shi ne cewa bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrallah an zabi Sayyid Safiyuddin Hashim, saidai gabanin su sanar da kwanaki shi ma ya yi shahada. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce, taken...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya  yaba wa yadda kungiyar Hamas ta jajurce da ci gaba da wanzuwa a dunkunle duk da cewa kwamandan dakarunta Muhamamd Dhaif ya yi shahada. Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya gabatar da jawabi ne na tunawa da zagayowar lokacin shahadar Salih al-Simad wanda daya ne daga cikin manyan shugabannin Ansarullah, ya kara da cewa, ci gaba da wanzuwar kungiyar ta Hamas yana daga cikin muhimman ayyukan da Muhammad Dhaif ya aiwatar a lokacin rayuwarsa. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya mika sakon ta’aziyyar shahadar Muhammad Dhaif ga kungiyar ta Hamas, tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan jagorori abin koyi saboda ruhinsa na imani mai karfi, azama da ruhi na...
    Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.
    Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki. Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi kan kudurin sa na ci gaba da kammala duk bada wadansu mukamai na magoya bayan sa fda suke a Karkara. Ya yi kira da mambobin kungiyar da wadanda suka amfana da taimakon kungiyar,su ci gaba da aiwatar da abubuwan da suka sa a gaban su, saboda ayyukan alkahairin da suka fara zai samar da babbar gudunmawar ci gaba a wasu shekaru ma...
    A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu. Adeleke ya yi nuni da cewa, sake sabunta wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yunkurin ‘yan adawar siyasa na kasar nan, kan yunkurinsu na gayawa ‘yan Nijeriya bayanan karya kan manufar wannan yarjejeniyar. Ministan ya ci gaba da cewa, Kungiyar ta Makomar Ma’adanan Kasa, za ta bai wa kasashen biyu damar fahimtar yadda za a samar da tsare-tsare da dabaru da kuma ayyukan da ya kamata...
    Yayin da dokar haramtawa hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Palasdinu ta MDD (UNRWA) yin aiki a Isra’ila ke gab da fara aiki, kwamitin sulhu na majalisar ya kira wata budaddiyar muhawara dongane da batun, inda wakilin Sin da wakilan sauran kasashe suka sake bayyana goyon bayansu ga hukumar. Wakilin Sin na dindindin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga Isra’ila da ta daina dakatarwa da kai wa hukumar hari, kana ta dakatar da zartar da dokoki masu ruwa da tsaki, yana mai kira ga kasashen duniya su ci gaba da goyon bayan hukumar wajen gudanar da ayyukanta da marawa MDD da kwamitin sulhun baya, wajen daukar matakan gaggawa domin tabbatar da hukumar ta gudanar da ayyukanta. Yankin Gabashin...
۱