2025-02-21@14:28:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 181

«Gwadabawa»:

    Gwamnatin Washington, ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba shugaban kasar Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, zasu fara tattaunawa kan batun Ukraine da nufin tsagaita wuta don kawo karshen yakin da kasashen biyu ke yi ta hanyar tattaunawa. Shugaban na Amurka ya sanar a ranar Laraba cewa ya yi doguwar...
    Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara jaddadawa Sarkin Jordan Abdullahi II kan shirinsa na kwace yankin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan ya maida shi wurin shakatawa, da kuma kan cewa kasar Jordan da Masar ne zasu dauki nauyin kula da Falasdinawa kimani miliyon 2 a Gaza a cikin kasashen su. Tashar talabijin ta Presstv...
    Al’ummar Jihar Jigawa sun yi kira ga Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi da ya yi amfani da kyawawan tsarin da gaskiya wajen zabar wadanda za su ci gajiyar shirye-shiryen bada tallafin karfafa sana’o’i. Sun kuma bukaci gwamnatin jihar da ta yi amfani da tsarin bayar da tallafin karfafa al’umma ma gwamnatin tarayya na (FADAMA)...
    Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa tawagogin kasashe 79 za su halarci bikin tunawa da marigayi babban sakataren kungiyar Sayyid Hassan Nasrallah da kuma shugaban majalisar zartarwarta Sayyid Hashem Safieddine. Sheikh Ali Daher, kodinetan babban komitin jana’izar Nasrallah da Safieddine, ya bayyana a wannan Talata a yayin wani taron manema labarai...
    Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba...
    “Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin. “A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin. “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta...
    A ci gaba da kokarinta na samun tagomashi a fannin tattalin arziki da ci gaban jihar ta hanyar kawo sauyi a harkar noma, gwamnatin jihar Jigawa na shirin hada gwiwa da wani kamfani da ke samar da dabino  da bayar da shawarwari a harkar noma, wanda ke da ofishi a Najeriya a kasar Saudiyya domin...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A...
    Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya gargaɗi Hamas da ta yi gaggawar sakin Isra’ilawan da take tsare da su a hannunta. Netanyahu ya ce ya bai wa ƙungiyar wa’adin zuwa ranar Asabar da ta saki Isra’ilawan da take garkuwa da su kamar yadda aka amince a yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu ta tanada. Gwamnatin Kano...
    Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa...
    Da marecen jiya Litinin ne aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakin ministocin harkokin wajen Iran da na Saudiyya akan shirin Donald Trump na korar Falsdinawa daga Gaza,inda kasashen biyu su ka ki amincewa da shi. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci, da takwaransa na Saudiyya Faysal Bin Farhaan, sun nuna kin amincewarsu...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara jaddada kudurinta na yin hadin gwiwa da wani kamfanin sarrafa dabino da kayan marmari domin inganta noman dabino da alkama a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bada wannan tabbaci a lokacin da tawagar Babban Daraktan kamfanin, Dakta Abubakar Musa Bamai ta ziyarci shi a gidan Gwamnati dake Dutse, Babban...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa matukar Falasdinawa ba su saki fursunonin  Isra’ila ba daga nan zuwa Asabar, to za a kawo karshen tsagaita wutar yakin da aka yi, da komawa yaki. Shugaban kasar ta Amurka ya shata wa’adin 12: 00 Na ranar Asabar a matsayin lokacin karshe na mika fursunonin. Shugaban...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa shirin korar  al’ummar Zirin Gaza zai hada da kwace ‘yancinsu na komawa kasarsu. Trump ya fada a wata hira da tashar Fox News cewa shirin da yake yi a kan Gaza ya kunshi fitar da daukacin al’ummar yankin da kuma sake gina abin da ya kira ‘’Sake farfado...
    A kokarinta na karfafa hadin gwiwa da tabbatar da gaskiya da rikon amana, hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa (JG-PCACC) ta kai ziyarar ban girma ga takwararta da ke Abuja. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na JG-PCACC Alhaji Yusuf Suleiman...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata taba zama don tattaunawa da kasar Amurka ba a dai-dai lokacin take kara takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka bikin ciki shekaru 46 da samun nasarar juyin juya...
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan ziyara ta gwamnan, za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Bankin na Duniya.   Cikin jawabin sa a wurin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa dangantakar ta Bankin Duniyar.   “Ina so in fara da nuna godiya ta ga Bankin Duniya game...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaban Ƙasa kuma tsohon uban gidansa, Olusegun Obasanjo. Obasanjo da Atiku sun yi ganawar ne a yayin ziyarar da tawagar Atiku ta kai gidan Obasanjo da ke mahaifarsa a Jihar Ogun. A ranar Litinin ne Atiku tare...
    Gwamnatin tarayya ta yabawa gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa kammala aikin kaso 97 na ayyukan tituna da ya gada daga gwamnatin da ta gabata a jihar. Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Auyo yayin kaddamar da shirin wayar da kan jama’a da gwamnati da...
    Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman...
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas. Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na X cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuradiyya a Najeriya. Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina...
    Tsohon Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Hudu Ari, ya ce bai damu da korar da aka yi masa ba, amma yana nan a kan bakansa cewa Aisha Binani ta jam’iyyar APC ce, ta lashe zaɓen gwamna na 2023. An dakatar da Hudu Ari bayan da ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen tun...
    Wani babban jami’in Ƴansanda, ASP Shafi’u Bawa, na rundunar 61 Police Mobile Force (PMF), an tsinci gawarsa a dakinsa a garin Kontagora, Jihar Neja, a ranar Asabar, bayan da ake zargin ya kashe kansa. Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gano gawar ASP Bawa rataye a saman silin ɗin ɗakinsa. Mahaifinsa, Malam Usman Bawa, ne...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar da kiran taron kasahen larabawa a karshen wannan watan na Febrairu da ake ciki domin tattauna batun tilasta wa Falasdinawa yin hijira daga Gaza a karkashin shirin Amurka da Isra’ila. Da safiyar yau Lahadi ne dai ma’aikatar harkokin wajen ta Masar ta bayyana cewa za ta karbi bakuncin...
    LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na kin amincewa da kalaman Netanyahu dangane da korar Falasdinawa daga Zirin Gaza Kasar Saudiyya ta jaddada yin tofin Allah tsine, da kuma karfafa kin amincewa da kasashen Larabawa suka yi dangane da furucin Benjamin Netanyahu kan neman korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado. A cikin wata sanarwa da...
    Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa...
    Shugaban Ukraine, Bolodymyr Zelensky ya ce duk wata tattaunawa da za a yi kan makomar kasarsa, wajibi ne a sanya kasashen yamma da Amurka da Rasha da kuma Ukraine din a ciki. A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Bolodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna kai tsaye da shugaba Bladimir...
    Iran ta bukaci taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta OIC, game da shirin shugaba Donald Trump na Amurka na kwace Gaza da kuma korar al’ummar Zirin. Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa haramtaccen shirin” na shugaban kasar Amurka kan Gaza ya gamu da...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da Isra’ila “tana cikin hadari” kuma “zata iya rugujewa,” Bassem Naïm, ne wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar, ya bayyana hakan ga kamfanin AFP, yayin da tattaunawar da ake yi kan mataki na biyu na tsagaita bude wuta, da ya kamata...
    “Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a...
      Mata a Karamar Hukumar Danja suna kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta gyara hanyar Tsangamawa a Babban Rafi saboda yawan rasuwar mata masu juna biyu da jariransu.   Sun yi wannan kira ne a yayin wani taron gaggawa da manyan jiga-jigan al’umma suka shirya domin tattauna matsalar da ta dade tana addabar jama’a...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya gana ta tawagar shoura ta kungiyar Hamas a safiyar yau Asabar a nan Tehran inda ya bayyana cewa mayakan kungiyar sun sami nasara a kan Amurka da HKI a yakin da suka dora masu na tsawon watanni 15. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta...
    Hukuma mai kula da samar da magungunan HIV/AIDS ko (UNAISD) ta MDD ta bada sanarwan cewa mai yuwa mutane kimani miliyon 6 ne zasu mutu a duk fadin duniya a cikin shekaru 4 masu zuwa saboda rashin samun tallafin Amurka a cikin shirin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayyana cewa, a...
    Kasashe 79 na duniya sun yi watsi da matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na kakabawa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC takunkumi, suna masu cewa matakin na raunana tsarin dokokin kasa da kasa. Wadannan kasashen  da suka hada da Canada, Jamus, Faransa, Afirka ta Kudu da kuma Mexico, a wata...
    Shirin Inganta rayuwar al’umma na jihar Jigawa ya  raba katinan cire kudi na ATM a kananan hukumomi 10 daga cikin 27 domin al’umma su sami tallafin naira dubu saba’in da biyar biyar na gwamnatin Tarayya. Shugaban shirin na jihar, Malam Mustapha Umar Babura ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Yayi...
    MA’aikatar harkokin wajen kasar Venezue ta sanar da cewa; Abinda Amurkan ta yi sata ce a tsakar ranar Allah da ta yi wa dukiyar al’ummar Venezueal, tare da cewa za ta dauki dukkanin matakan da su ka dace domin sake dawo da jirgin saman nata.” Sanarwar ta kuma zargin ministan harkokin wajen Amurka Marco Robio...
    Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa. Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wata tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a safiyar yau Juma’a...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran ya sabawa ka’idojin dokokin kasa da kasa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa sun sabawa ka’idojin dokokin kasa da...
    Majiyoyin sojin Sudan sun sanar da cewa: Sun sake samun nasarar kwace iko da babban birnin kasar Khartoum Majiyoyin sojin Sundan sun sanar da cewa: Cikin dan gajeren lokaci sun samu nasarar sake kwace iko da birnin Khartoum fadar mulkin kasar daga mamayar dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, bayan da suka yi...
    A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe,...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar  na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a ranar 6 ga watan nan cewa, shaharar da kallon fina-finai na lokacin hutu na Bikin Bazara na al’ummar Sinawa ya yi manuniya ce a kan dimbin albarkar da kasuwar masarufi ta kasar Sin ke da ita, da karfin kasar na raya...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa : Gabadayen Falastinu tun daga kogi har zuwa teku ta al’ummar Falasdinawa ce. Jagoran ya jaddada goyon bayan Iran ne ga gwagwarmayar Falasdinawa kan kasarsu mai dimbin tarihi, tun daga kogin Jordan zuwa tekun Bahar Rum, kamar shafin offishin jagoran ya...
    Ministan tsaron Isra’ila, Isra’ila Katz ya umarci sojojin gwamnatin kasar da su shirya wani shiri na “ficewar” Falasdinawa daga zirin Gaza. Umarnin Katz ya biyo bayan shawarar Shugaba Donald Trump na tilastawa Falasdinawa Gaza barin zirin da kuma sanya Amurka ta mamaye yankin da yaki ya lalata. “Na umurci IDF da su shirya wani shiri...