2025-02-21@14:47:31 GMT
إجمالي نتائج البحث: 421

«Umar Farouk Ibrahim»:

    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya nada Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Marigayi Sayyid Hassan Nasrullahi tsohon babban sakataren kungiyar...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tsananta matsin lamba da ake son dauka kan Iran ba zai yi wani tasiri ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Manufar matsin lamba da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka kan Iran za ta sake yin kasa a gwiwa tare da rashin nasara....
    Jami’in tsaron kasar Iran ya karyata sabuwar da’awar jaridar New York Times ta kasar Amurka Jami’in tsaron kasar Iran ya musanta wasu sabbin zarge-zargen da jaridar New York Times ta Amurka ta wallafa game da zargin Iran cewa tana bunkasa ayyukannta na kera makaman kare dangi. Jami’in tsaron ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Tasnim...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran za ta mayar da martani ga duk wata barazana ko matsin lamba gwargwadon tsayin dakarta Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Iran ta sha tabbatar da cewa a shirye take ta gudanar da huldar siyasa da diflomasiyya don tabbatar da moriyar...
    Sojojin Sudan sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar Rundunar sojin Sudan ta sanar a yau jiya Talata cewa: Sojojinta da mayakan da suke goya musu baya sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar, kuma babban hafsan hafsoshin rundunar sojin kasar Janar Abdul-Fattah...
    Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa sun kusa da kama ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ya addabi yankin Arewa Maso Yamma, Bello Turji. Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana da tabbacin cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi kafin ƙarshen shekarar 2025. Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya  Tinubu...
    Mai martaba sarkin Jiwa a yankin birnin tarayya Abuja, Alhaji Idris Musa ya yi rashin mahaifiyarsa mai suna Hajiya Ramatu Ibrahim. Ta rasu ne a safiyar Lahadi kamar yadda sarkin malamai na masarautar malam Jibrin Yakubu Adam ya tabbatarwa Aminiya. Hajiya Mai Babbar Ɗaki, kamar yadda ake yi mata laƙabi, ta rasu ta bar...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci a ƙara adadin kasafin kuɗin shekarar 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2. Wannan buƙata na ckkin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zaman majalisar na ranar Laraba. Tinubu zai tafi Faransa daga nan ya zarce...
    Ancelotti ya shaidawa manema labarai ranar Talata cewa “Bellingham ya samu rauni yayin atisaye amma kuma Vinicius Jr zai buga wasan gobe duk da cewar har yanzu ya na kan murmurewa daga raunin da ya ji a watan jiya   Ya kuma ce Mbappe ya yi atisaye kamar yadda aka saba a yau, amma gobe...
    Shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya sanar da tsawaita wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025 zuwa ranar 10 ga Fabrairu, 2025. Karin wa’adin na zuwa ne biyo bayan koke-koke da aka kai wa hukumar na a kara wa maniyyatan da suka gaza kammala biyan kudinsu a kan...
      Yayin da Hukumar Kula da Hajji ta Kasa ta kara wa’adin biyan kudin Hajjin bana zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta umarci dukkan ofisoshin da suke alhakin yin rajista su tabbatar da an yi wa duk masu sha’awar tafiya Hajji rajista kafin ƙarshen wa’adin da aka...
    Sojojin sama na JMI sun sami nasarar kakkabo jiragen yaki na makiyan da aka sawwara, tare da amfani da makami mai suna Majid a cikin atisayen sojojin sama da suke gudanarwa a kudu masu yammacin kasar. Jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa dai, suna da masu muhimmanci a yakin zamani a halin yanzu, don...
    Kasar Afirka Ta Kudu ta ga yadda Palasdinawa suka jajirce wajen kare kansu daga HKI ne, ya sa ta gurfanar da HKI a gaban kutun ICC don kawo karshen kissan kiyashin da yahudawan suke masu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kasar Afirka ta gudu dai tana dade tana goyon...
    Jaridar Politico ta buga wani rahoton dake cewa sojojin kasar Ukiraniya suna fuskantar matsin lamba mai yawa, da kuma rashin kwararrun mayaka. Wannan matsin lambar da sojojin kasar suke fuskanta ya sa ana tunanin mayar da sojojin sama zuwa na kasa da tura su filin daga. Har ila yau jaridar ta ambaci yadda sojojin da...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi Amurka da ta kama Fira ministan “Isra’ila” Benjamin Netanyahu da yake ziyarar aiki a kasar. A wasu jerin sakwanni da kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta duniya ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa; Yadda Amurka ta karbi bakuncin Benjamin Netanyahu alhali ana...
    Kungiyar Hizbullah ta fitar da wani bayani a jiya Talata da ta yi Allawadai da takuhkumin da kasar Australia ta kakaba wa babban sakatarenta Sheikh Na’im Kassim. Bayanin na kungiyar Hizbullah ya kunshi cewa; Matakin, yana sake nuni ne da hakikanin fuskar wannan kasa da a kowace rana take tabbatar da cewa, ita makami a...
    Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta sanar da a ci gaba da yi wa maniyyata rajista har zuwa ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu, 2025. A daren Talata 4 ga watan ne  hukumar ta amince da kara lokacin  a taron da ta yi da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi. Wata sanarwa da...
    Kungiyar masu fama da cutar daji ta Najeriya reshen jihar Kano, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta bullo da tallafin kula da cutar a dukkan asibitocin gwamnati. Shugaban kungiyar Salisu Yusuf ne ya yi wannan kira a yayin wani taron manema labarai na bikin ranar cutar Daji ta duniya tta shekarar 025. Ya...
    Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar...
    Ministan ya kara da cewa, za a kaddamar da kashin farko na gyaran madatsar ruwan a tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2025.   Ya kuma kara jaddada muhimmancin wannan aiki na tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2025 ba.
    Babban wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong, ya gudanar da taron manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York, jiya Litinin bisa agogon birnin, domin gabatar da muhimman tsare-tsare na wa’adin shugabancin kasar Sin a kwamitin sulhu, na wannan wata. A cewar Fu Cong, a yayin wa’adin shugabancin kwamitin sulhu na MDD a...
    A kwanan baya, kasar Amurka ta kakaba wa kayayyakin kasar Sin da ake neman shigar da su cikin kasuwanninta karin harajin kwastam na kaso 10%, bisa dalilin wai Sin na sayar da magani mai suna Fentanyl a kasar. Hakika maganar Fentanyl din wani batu ne da kasar Amurka ta dade tana kokarin ruruta shi, inda...
    Majalisar Zartarwa ta ware naira biliyan 4.8 domin yaƙi da yaɗuwar cutar HIV a Nijeriya. Wannan na daga cikin matsayar da aka cimma a taron Majalisar Zartarwa da ya gudana a ranar Litinin kamar yadda Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya tabbatar. Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 Dalilin da...
    Haruna, mazaunin Unguwar Kanawa Dutse Abba, an rahoto cewa, ya jagoranci ‘yan bindiga uku – Shago Yaro, Tanimu Ayuba, da kuma Lamido Dantajiri zuwa gidan dansa, Alhaji Anas da misalin karfe 1 na dare, inda suka tarar ba ya gida, amma suka yi awon gaba da matansa biyu, ‘ya’yansa uku, kaninsa, da matar kaninsa.  ...
    Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa Iran za ta yi amfani da dukkan karfinta wajen kare shirinta na nukiliya cikin lumana. A yayin wata ziyara da ya kai wani baje kolin da ke nuna sabbin nasarorin da aka samu a masana’antar nukiliya...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Labanon ta shigar da sabon korafi kan yahudawan sahyuniya gaban kwamitin sulhu na MDD, inda ta yi Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan da yahudawan sahyuniya suka kai kan kasar Labanon, da kuma keta hurimun ikon kasar, da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma yau fiye da watanni biyu....
    Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan  ranar 7 ga watan Okotoba 2023. Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa;  A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara...
    A Talatar nan Majalisar Dokoki ta kasa ta ci gaba zama don hanzarta kammala aiki kan ƙudirin sabuwar dokar haraji mai cike da ruɗani da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata. Bayan zaman farko a ranar 14 da watan nan na Janairu, ta dage zama zuwa ranar 28 domin kwamitoci su kammala aikin tantance...
    Hukumar ICPC ta samu gurfanar da Mohammed Idris, wani jami’i a ƙofar shigen shiga wurin Hajji da ɗiban kaya na filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagas, kan laifin bayar da bayanan ƙarya da kuma cin da kuɗaɗen haram. A gaban Mai shari’a O.A. Fadipe na kotun laifuka ta musamman da ke Ikeja,...
    Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen...
    Sojojin JMI sun bada sanarwan fara isayen soje karo na biyu a yankun tsakiya da kuma kudancin kasarTashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa za’a fara wannan atisayen ne a yau Talata 04 ga watan Fabrairu, kuma atisayen zai fi maida hankali ne a kan garkuwan tsaron kasar , wanda kuma ya...
    Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta...
    Babbar Kotun Jihar Kogi ta tsige Alhaji Ahmed Muhammed Tajani Anaje daga kujerarsa ta Ohinoyi na Ƙasar Ebira. Kotun ta soke naɗin Alhaji Ahmed Muhammed ne a ranar Litinin, shekara guda bayan fara aikin basaraken. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Salisu Umar, ya kuma dakatar da basaraken daga gabatar da kansa matsayin Ohinoyi, har zuwa lokacin...
    Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin lashe wata dattijuwa mai shekara 67, kan zargin ta da maita. Kotun ya yanke musu hukuncin kisa ne a ranar Litinin bayan samun su da laifin kiran dattijuwar mai suna Ɗahare Abubakar, mayya sannan suka daɓa mata wuka...
    An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara.  Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar...
    Kwamandan makarantar horas da sojoji dake Zaria, Manjo Janar Ahmadu Bello Mohammed ya yi alkawarin inganta dangantakar da ke tsakanin makarantar da majalisar masarautar Zazzau. Ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wa mai martaba Sarkin zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ziyarar ban girma a fadar sa dake Zaria. Manjo Janar Ahmadu Bello, wanda...
    Babban kwamnandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran ya jaddada cewa: Makamai masu linzamin Iran za su iya kai hari kan kowane makiyi Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Husaini Salami ya tabbatar da cewa: Makamai masu linzami na Iran suna da karfin kai hari kan duk...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke da goyon bayan al’ummar Siriya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i ya tabbatar a yau Litinin, a taron manema labarai na mako-mako cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke samun goyon bayan al’ummar Siriya. Kakakin...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare kungiyoyin gwagwarmaya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare wannan gwagwarmaya da ta hana makiya numfasawa a yankin. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf...
    Gwamnatin mamayar Isra’ila ta tantance hanya ta musamman da jirgin da ya dauki fira ministan mamayar Isra’ila zuwa Amurka saboda tsoron kama shi! A wani mataki da ke nuni da yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kara nuna damuwa, jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar ta watsa rahoton cewa: Jirgin da ke dauke da fira ministan...
    Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yaba wa ƙoƙarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da harkokin rayuwar al’ummar Jihar Borno bayan tashe-tashen hankulan ’yan ta’adda da jihar ta yi fama da shi. EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa...
    Ko da yake har yanzu kotun ba ta bayar da cikakken bayani kan hukuncin ba, amma an gano cewa, shari’ar mai lamba HCO/05C/2024, Dakta Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutane biyu ne suka shigar da ita, inda suke kalubalentar hukuncin tsohon gwamnan jihar na Kogi.   Sai dai, jin ta bakin Ohinoyi, Alhaji Ahmed Muhammed...
    Shuwagabannin kasashen turai guda uku wato EU3 sun bayyana cewa daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar ya fi karfinsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran yana fadar haka a wata hira ta musamman da ta hada ta da tashar. Mohammad Eslami ya...
    Jakadan kasar Iran a Pakisatan ya bayyana bukatar shuwagabannin kasashen biyu su kara yawan musayar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, zuwa dalar Amurka biliyon $10. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Amiri Moghadam yana fadar haka a wani taro da aka gudanar tsakanin Jami’an kasashen biyu a cibiyar kasuwanci ta Rawalpindi a...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara...
    Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin. Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba...
    Ma’aikatan Agaji suna ci gaba da fito da gawawwakin shahidan Falasdinawa da Isra’ila ta rushe gidaje akansu, a tsawon lokacin yaki,wasu kuma akan hanyoyi. Wani jami’in agaji ya ce, bayan gushewar fiye da shekara daya na yaki, da wuya suke iya samun cikakkiyar gawar wani daga cikin shahidai, sai dai  rabi da rabi, a wasu...
    Da marecen jiya Lahadi ne dai shugaban Majalisar dokokin Iran  Mahmud Mashahadani ya iso Tehran domin fara ziyarar aiki da zai gana da jami’an gwamnatin kasar. Mataimakin shugaban Majalisar Shawarar musulunci ta Iran Hamid Ridha Haji Babbayi  da kuma shugaban kwamitin kawancen majalisun kasashen biyu ne su ka tarbi Mashhadani a filin saukar jiragen sama...
    Arsenal ta doke Manchester City a wani yanayi mai ban mamaki a filin wasa na Emirates dake birnin Landan, ƙwallaye da Odegaard, da Partey, da Skelly, da Harvertz da Nwaneri suka jefa ya sanya Man City cikin garari. Tun minti na 2 da fara wasan kyaftin ɗin tawagar Arsenal Martin Ordegaard ya jefa ƙwallo a...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba da ci gaban da Iran ta samu a fagage daban-daban, yana mai cewa kasar ta samu bunkasa a dukkan bangarori cikin shekaru 40 da suka gabata. Iran ta yau ba Iran ce ta shekaru 40 da suka gabata ba – mun ci...