2025-04-02@20:16:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 306
«Yada Labarai»:
Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025. A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar...
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa masu yi wa kasa hidima NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutum takwas. Majiya mai tushe ta bayyana hakan ga gidan rediyon Najeriya...
Babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Cai Qi, ya yi kira a ranar Laraba, da a ci gaba da yin kokari wajen kawar da ayyukan da ba su da ma’ana, da rage nauyin da ke wuyan jami’an kananan matakai, don tabbatar kyakkyawan salon aiki tsakanin ’yan jam’iyya da jami’ai wajen cimma burin da aka...
Wata gobara da ta tashi a Ƙauyen Zago da ke Ƙaramar Hukumar Danbatta a Jihar Kano, ta ƙone gidaje, amfanin gona, da dabbobi, lamarin da ya janyo wa mazauna ƙauyen asara mai tarin yawa. Gobarar, ta fara ne da safiyar ranar Laraba, inda ta ƙone gidaje da dama tare da lalata hatsi da sauran amfanin...
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da bai wa ‘yan’uwansu haƙurin jure wannan babban rashi, har ila yau gwamna Dauda Lawal ya yi addu’ar Allah ya bai wa wadanda suka samu raunuka lafiya. Gwamnati za ta yi bincike domin ta gano dalilin afkuwar wannan gobara, domin kaucewa hakan a nan gaba....
Sakamakon yadda kasar Sin take ci gaba da zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni, da kyautata bude kofa ga ketare bisa matakin koli, ya sa kasar ta Sin za ta ci gaba da kara azama kan bunkasar tattalin arziki. Za kuma ta ci gaba da nuna kuzari kan raya kanta tare da amfanar...
An kuma samu labarin cewa ɗalibin ya rasa mahaifinsa a wasu shekarun baya, lamarin da ya mahaifiyarsa wadda tsohuwar malamar makaranta ce ta ci gaba da ɗaukar nauyin karatunsa tun daga lokacin. Rahotanni sun nuna cewa matsalarsa ta ƙara tsananta tun bayan dawowarsa makaranta a bara, inda abokan karatunsa suka tara kuɗi domin biya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A da akan kwashe kwanaki ana bukukuwan aure a ƙasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin biki da zaman ajo zuwa buɗar kai da sayen baki. Sai dai waɗannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa. Ko mene ne dalilin wannan sauyin? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin...
Ministan ya kara da cewa, za a kaddamar da kashin farko na gyaran madatsar ruwan a tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2025. Ya kuma kara jaddada muhimmancin wannan aiki na tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2025 ba.
Haruna, mazaunin Unguwar Kanawa Dutse Abba, an rahoto cewa, ya jagoranci ‘yan bindiga uku – Shago Yaro, Tanimu Ayuba, da kuma Lamido Dantajiri zuwa gidan dansa, Alhaji Anas da misalin karfe 1 na dare, inda suka tarar ba ya gida, amma suka yi awon gaba da matansa biyu, ‘ya’yansa uku, kaninsa, da matar kaninsa. ...
A Talatar nan Majalisar Dokoki ta kasa ta ci gaba zama don hanzarta kammala aiki kan ƙudirin sabuwar dokar haraji mai cike da ruɗani da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata. Bayan zaman farko a ranar 14 da watan nan na Janairu, ta dage zama zuwa ranar 28 domin kwamitoci su kammala aikin tantance...
Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen...
Guinea-Bissau Na Neman Karfafa Hadin Gwiwar Kafofin Yada Labarai Da Sin
Mai yiwuwa Atletico Madrid za ta fara wasa da wannan zubin: Musso, Llorente, Gimenez, Witsel, Azpilicueta, Correa, Gallagher, Koke, Lino, Sorloth, Griezmann. Mai yiwuwa Getafe zata fara da wannan zubin: Letacek, Iglesias, Duarte, Alderete, Rico, Alena, Dakonam, Arambarri, Sola, Uche, Mayoral.

Shugaban Kasar Amurka Ya Ce Nan Ba Da Dadewa Ba Zai Kara Kudin Fito Na Kayakin Da Ake Shigo Da Su Amurka Daga Kasashen Turai
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta nuna adawa da rashin amincewa da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasar Sin, kuma za ta dauki matakan da suka dace...
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba...
Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za a ci gaba da bada tallafi ga al’umma a dukkan mazabu 30 na ‘yan majalisar dokokin Jihar. Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake kaddamar da bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Miga wanda Shugaban majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya...
A yau Asabar, bayanai a hukumance sun nuna cewa, fiye da fasinjoji tsakanin yankuna miliyan 304 ne suka yi zirga-zirga a fadin kasar Sin a ranar Juma’a, rana ta hudu ta hutun bikin bazarar bana, yayin da aka samu yawan ziyarce-ziyarcen iyalai wanda ya ingiza yawon shakatawa. Wannan dai shi ne karo na farko na...
‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa...
Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan...
Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga...
Bisa alkaluman da hukumar kula da zirga-zirgar layin dogo ta kasar Sin ta bayar, tun daga kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara na Sin daga ranar 14 zuwa ranar 30 ga watan Janairu, yawan fasinjojin da jiragen kasa suka dauka ya kai miliyan 206 a kasar, kuma an yi zirga-zirgar fasinjojin cikin kwanciyar...
A kan yawan samun hauhawan farashin man Garima yace kungiyar na samun saukin farashin sawo man man daga matatar Dangote Refinery da ta MRS duba da cewa, farashinsu na da sauki sosai. Garima da yake yin tsokaci a kan yawan samun hauhawan farashin man a kasar nan, ya bayyana cewa, ‘ya’yan kungiyar na samu sayen...
’Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu 24 a wasu jerin hare-hare a wasu kauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara. ’Yan ta’adan sun kai hare-haren ne ranar Alhamis, a ƙauyukan Shinkafi da Jangeru da Shanawa da Birnin Yero. A garin Shinkafi, ’yan bindigar sun kashe mutum...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar...
Tsohon shugaban kamfanin Google Eric Schmidt, ya bayyana bullar kamfanin DeepSeek na Sin a matsayin wadda ta kawo muhimmin sauyi ga takara a fagen kirkirarriyar basira ta AI a duniya. Wannan na kunshe ne cikin wani sharhi da jaridar Washington ta wallafa ranar Talata, inda Eric Schmidt ya jaddada cewa, karfin Sin na yin takara...

Kafafen Yasa Labaran Sweden Sun Tabbatar Da Mutuwar Selwan Momika Wanda ya Kona Alkuranai A Kasar A shekarum Baya
Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta...
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara. Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi...
An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun tabbatar a jiya Laraba cewa: Sassan soja sun amince da nada Ahmed al-Sharaa da aka fi sani da (al-Jolani) a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar. Tun a jiya Laraba ce,...
Ministan Harkokin Wajen Benin Ya Yi Wa Sinawa Gaisuwar Sabuwar Shekara
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau,...
Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar. A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a...
Bikin bazara shi ne biki mafi dadewa da muhimmanci a bukukuwan gargajiya na Sin. Kuma bikin na ci gaba da kara bazuwa da samun karbuwa a fadin duniya. A kwanakin baya-bayan nan, kasashe da hukumomin kasa da kasa da dama sun gudanar da shirye-shirye da nune-nunen dake da alaka da bikin bazara, kuma jama’a a...
CMG Ya Gabatar Da Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara Cikin Nasara

Aragchi Yace Duk Wani Harin Da Aka Kaiwa Cibiyoyin Nukliyar Kasar Iran Hakan Wata Musiba ce Ga Yankin Asiya Ta Yamma
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas...
Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da...
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a...
Haka kuma, an naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta. Ya samu ƙwarewa a fannonin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen ƙara ƙarfin tsarin kuɗi na jihar. An kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai...

Na’im Kassim Ya Dora Wa Amurka da Faransa da MDD alhakin Abinda Zai Faru Idan Isra’ila Ba Ta Janye Daga Labanon Ba
Abinda Ya Faru A Lebanon Nasara Ce Akan Isra’ila Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi na farko bayan cikar kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki da HKI. A jawabin nasa sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa a lokuta da dama sun yi tunanin mayar da martani akan keta tsagaita wutar...
A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da katin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a matsayin martani ga abokai a jihar Iowa ta kasar Amurka, inda ya ce, Sin da Amurka na da manyan muradun bai daya, da damar yin hadin gwiwa, kuma suna iya zama abokan...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi ƙarin haske dangane da barazanar harin ’yan ta’adda da ta yi gargaɗin aukuwarsa a bayan nan. Da yake yi wa manema labarai jawabi, Kwamishinan ’Yan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya ce sun ɗauki matakan da suka dace biyo bayan barazanar harin ’yan ta’adda musamman a yayin taron...
Ya kuma yi gargadi cewa rashin ɗaukar matakai na gyara tattalin arziƙi zai ci gaba da haifar da asara mai yawa, inda tallafin man fetur da na musayar kuɗaɗe ke laƙume kashi biyar cikin ɗari na GDP na ƙasar. Wannan, in ji shi, babban ƙalubale ne ga cigaban tattalin arziƙin Nijeriya.
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi...
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar UYemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi, ya yabawa mutanen kasar kan jajircewarsu wajen yakar makiya Amurka da HKI da kuma saudiya, har zuwa nasarar da suka samu a kansu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Al-huthi yana fadar haka a yau Lahadi, a wani jawabin da aka watsa...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda...
An sace aƙalla mutum 22 a wasu sabbin hare-hare da ake zargin ’yan bindiga da kaiwa a ƙauyen Kugauta da ke Kusheka da kuma Kitanda da ke Gashere a masarautar Kumana da ke Ƙaramar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna. Wani mazaunin yankin, Emmanuel Johnson, ya bayyana wa Aminiya cewa hare-haren sun afku ne da misalin...