2025-03-22@01:13:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 946

«Almajirai»:

    Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki 57 da kasar Ukiraniya ta harba zuwa yankuna mabanbanta na kasar. A yau Laraba ne ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta sanar da cewa; An harbo jiragen marasa matuki 35 da aka harba wa yankin Kursk dake yammacin Syria a jiya da dare. Sai...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin da take mayar da martani ga tambayar da wani dan jarida ya yi mata a taron manema labaru na yau 18 ga wata cewa, kasar Sin ta damu matuka kan halin da ake ciki a tsakanin Falasdinu da Isra’ila,kuma tana...
    A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya...
    Ƙungiyar Hamas ta ɗora alhakin hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar yau Talata a Zirin Gaza kan Amurka. A wata sabuwar sanarwa da Hamas ta fitar, ta ce Amurka ce ke da “alhakin kisan gillar” da aka yi a Gaza bayan da ta bayyana cewa Isra’ila ta shaida wa Amurka shirinta na kai hare-haren gabanin kai...
    Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce, “A daren yau mun koma yaƙi a Gaza.” Hamas ta zargi Isra’ila da karya yarjejeniyar tsawon kusan wata biyu, tana mai cewa hakan na barazana ga lafiyar fursunonin da ke tsare a Gaza. Amma Isra’ila ta ce Hamas ce ke ƙin sakin fursunonin tare da bijirewa yarjejeniyar sulhu....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majiyar gwamnatin kasar Yemen ta basa sanarwan kai hare-hare har sau biyu kan kataparen jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki na kasar Amurka dake cikin Tekun Red sea, wato USS Harry Truman. Inda suka cilla makami mai linzami guda da kuma jiragen yake wadanda ake sarrafasu daga nesa kan jirgin. Har’ila yau sojojin yamen sun...
    A ranar Juma’a, fadar Kremlin ta ce Shugaba Putin ya aike saƙo zuwa ga Trump ta hannun manzon Amurka na musamman, Steve Witkoff, yana bayyana cewa Rasha tana nazarin batun tsagaita wuta amma tana taka-tsantsan. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta kai ga samun mafita, amma ya jaddada cewa...
    Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Husi ya bayyana cewa; Matukar Amurka ta ci gaba da kai wa Yemen hare-hare, to suna da hanyoyi da za su iya gasa mata aya a hannu masu yawa. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yi ishara da yadda dubun dubatar mutanen Yemen su ka fito a cikin birnin...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Dukkanin batutuwan  da Musulunci da kuma al’kur’ani maigirma suke bijiro da su, sun ginu ne akan ginshikin gaskiya da kuma adalci. Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Idan har wadannan ginshikan biyu su ka zama ana aiki da su a cikin al’umma, to za a...
    Dan Mahadi Karubi, wanda  yana  ya jagoranci boren 2009 bayan zaben shugaban kasa, ya bayyana cewa an daukewa mahaifin nashi daurin talalar da aka yi masa bisa umarnin ma’aikatar sharia. Shi dai Mahadi Karubi an yi masa daurin zaman gidan ne bayan hargitsin da ya jagoranta bayan zaben shugaban kasar da aka yi a 2009....
    Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kama Lawal tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Mayu. A wata shari’a daban, kotun ta kuma bayar da umarnin kama Jibrilla Muhammad, tsohon Manajan Darakta na Kamfanin Zuba Jari da Kadarorin Kano (KSIP), bisa zargin ɓatan Naira miliyan 212.4. A gefe...
    Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta inda ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Falasɗinawa a Zirin Gaza. Sabbin hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar sun kashe fiye da mutum 200 ciki har da mata da yara tare da jikkata daruruwa a yayin da ake ci gaba da kai gawawwaki asibiti. Mahaifina ne kaɗai shugaban da bai...
    Yau Litinin da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya kira wani taron manema labarai, inda kakakin hukumar kididdiga ta Sin, Fu Linghui ya yi bayani kan yadda tattalin arzikin kasar ke gudana a cikin farkon watanni biyu na bana da suka gabata. Kididdiga na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Fabrairu...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf a wannan Litinin ɗin ya rantsar da sabon Kwamishinan Ma’aikatar Tsarawa da Bunƙasa Gidaje ta Kano, Ibrahim Yakubu Adamu. Wannan dai shi ne karo na huɗu cikin ƙasa da shekaru biyu ke nan da gwamnan yake faɗaɗa majalisar zartarwa jihar ta Kano. Ana zargin wa da ƙani da yi wa almajiri...
    Iran ta ce za ta fifita diflomatisyya ta tsakaninta da kasashe makobtanta na yankin. Ministan harkokin wajen kasar ne Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar kan harkokin diflomasiyya a yankin, yana mai bayyana cewa kasashen da ke makwabtaka da kasar na cikin tsarin Jamhuriyar Musulunci. “Makwabtanmu sune fifikonmu,” in ji ministan harkokin wajen Iran a...
    Al’ummar kasar Yemen sun gudanar da wani gagarumin ganganmi a fadin kasar, inda suka lashi takobin tinkarar ta’addancin Amurka ta hanyar kara karfin soji, da hada karfi da karfe, da kuma abokan gaba shakat. Gangamin ya zo ne bayan da jagoran gwagwarmayar kungiyar Ansarullah Abdul Malik al-Houthi ya bayyana cewa kasar a shirye ta ke...
    Iran ta bayyana anniyarta ta yin hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiya ta duniya IAEA. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Kazem Gharibabadi ya ce Tehran “na maida hankali” wajen hada kai da hukumar ta IAEA. A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Gharibabadi ya yaba da tattaunawa mai ma’ana” da...
    Rundunar ’yan sandan Adamawa ta cafke wani ƙani da yayansa — Aliyu Abdulmalik da Ibrahim Abdulmalik — kan zargin yanke kan wani almajiri ɗan shekara 10, Abdallah Lawali. Bayanai sun ce ’yan uwan junan biyu sun aikata wannan ta’asa ce a ranar 7 ga watan Maris a unguwar Sarkin Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Jada....
    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana shirin tuntuɓar takwaransa na Rasha Vladimir Putin da zummar tattauna batun kawo ƙarshen yaƙin Ukraine. Trump ya shaida wa manema labarai hakan a cikin jirgin shugaban ƙasa na Airforce One a kan hanyarsa ta zuwa Washington daga Florida cewa yana ƙoƙarin ganin cewa yaƙin ya zo ƙarshe. Madalla...
    A jiya Lahadi ne dai kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kai hare-hare akan iyakar Lebanon ta yankin Hermul Ma’aikatar tsaron Syria ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta riya cewa; harin nata martani akan wani hari da aka kai a can cikin kasar wanda ta jinginawa HIzbullah, da kuma ya yi sanadiyyar mutumar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya ce; Abinda ake watsawa a matsayin wasikar shugaban kasar Amurka shaci-fadi ne, domin har yanzu, mu ba mu watsa abinda ta kunsa ba.” Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai banbanci a tsakanin yadda Donald Trump yake Magana a fili...
    Kasar Yemen ta sanar da cewa Amurka da ta sake kai wasu hare-haren a gundumar Hudaidah akan wani kamfani na auduga. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto majiyar Ansarullah ta  kasar Yemen din tana cewa; Sojojin na Yemen sun kai hare-hare da makamai masu linzami har 18 akan jiragen ruwa na dakon jiragen...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya ba da sanya hannu a kan takardun yarjeniyar samar da zaman lafiya wanda kasashen Armenia da Azerbaijan suka yi. Ya kuma taya mutanen kasashen murmurnar wannan nasara. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana taya kasashen biyu murna a jiya lahadi, ya kuma kara da...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa hare-haren ta’adanci wadanda sojojin Amurka da Burtaniya suka kai kan yankuna da dama a kasar ba zasu hana mutanen kasar ci gaba da kare Falasdinawa a Gaza ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Al-huthi yana fadar haka a wani...
    Shugaban kasar Angolan João Lourenço, wanda kuma shi ne ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka (AU) ya yi kira ga gwamnatin Congo Democradiyya da mayakn M-23 su kawo karshen yaki kafin taron tattauna batun tsagaita wuta a gabacin kongo nan gaba. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afirca News” ya nakalto shugaban yana...
    Gidauniyar Aliko Dangote, a cikin shirye-shiryenta na 2025, na bayar da tallafin abinci ga ‘yan Nijeriya, ta ƙaddamar da rabon abinci, inda ta ware kimanin Naira Biliyan 16 domin tallafa wa talakawa ‘yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu nakasa. Shirin da fiye da mutum miliyan ɗaya ne za su rabauta da tallafin buhunhunan...
    Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ta cafke shahararriyar jarumar  nan ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya. Bayanai sun ce hukumar mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta cafke Murja Kunya bisa zargin wulaƙanta takardar Naira. NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da kukan rashin aikin yi da a ko da yaushe ke ci gaba da addabar ‘yan Najeriya, a wasu lokutan ba rashin aikin yi ne matsalar ba, waɗanda za su cike guraben ayyukan ne suka yi ƙaranci a Najeriya. Alƙaluma na ci gaba da bayyana dubban ‘yan...
    Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma  a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya. Janar Hossein Salami ya bayyana hakan...
    An yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya da su tabbatar da dorewar tashar Rediyon Nigeria (FRCN) Kaduna a matsayin abim tunawa da marigayi Firimiyan  tsohuwar jihar Arewa, Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, ya bari. Masu sauraron tashar sun yi wannan kira a cikin bayanai daban-daban yayin da suke tsokaci kan bikin cika shekaru...
    An yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya da su tabbatar da dorewar tashar Rediyon Nigeria (FRCN) Kaduna a matsayin abim tunawa da marigayi Firimiyan  tsohuwar jihar Arewa, Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, ya bari. Masu sauraron tashar sun yi wannan kira a cikin bayanai daban-daban yayin da suke tsokaci kan bikin cika shekaru...
    Kalmar demokuradiyya kalma ce da jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te ke yawan ambata, amma aikin da ya yi bai bi hanyar demokuradiyya ba. A baya-bayan nan, Lai Ching-te ya gabatar da wani shirin neman ‘yancin kan Taiwan, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokuradiyya ce mai mulkin kanta. Lai Ching-te ya kan...
    A ranar Juma’a ce Amurka ta bai wa Jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, wa’adin sa’o’i 72 ya tattara komatsai ya fice daga ƙasar. Hakan na ƙunshe cikin wata ’yar taƙaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’iakatar harkokin wajen Amurka, Chrispin Phiri ta fitar. Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA Mahaifiyar...
    Hajiya Asta Shehu Timta, mahaifiyar mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta ta riga mu gidan gaskiya. Wata sanarwa da Masarautar Gwoza da ke Jihar Borno ta fitar ta ce Hajiya Asta ta rasu ne yammacin jiya Asabar bayan shafe shekaru 80 a duniya. Yadda za a girka ‘Kamoniya’ An kama malama tana...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar JMIa bude yake ga kasashen Turai don tattaunawa da fahintar juna kan matsalolin da bangarorin biyu suke sabani a kansu, tare da mutunta hurumin Juna. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiyaAsabar a lokacinda yake zantawa...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran y ace gwamnatin kasar Amurka bata da hakkin tsarawa kasar Iran yadda zata gudanar da manufofinta harkokin waje, wannan ya wuce tun bayana nasarar juyin juya hali musulunci a kasar a shekara ta 1979. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baka’e ya tir da kungiyar kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya,wato G7. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma yi All..wadai da zarge zagren kungiyar wadanda suka hada da zargin Iran da kokarin mallakar makamin...
    Duk da kokarin da ma’aikatan asibitin suka yi na ceto shi, rahotanni sun ce ya samu raunuka da dama ciki har da guda daya a zuciya. Jaridar Irish Mirror ta ruwaito cewa ‘yansanda suna tsare da Eghomwanre har zuwa lokacin da zai gurfana a gaban alkali Michele Finan a kotun gundumar Dublin. A yayin shari’ar,...
    Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran manjo  janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin tunawa da shahid Mahadi Bakiri a garin Tabriz ya bayyana cewa;; Babu yadda za ayi jamhuriyar musulunci ta Iran ta bude tattaunawa da Amurka a karkashin barazana, yana mai kara da cewa; yin gwawarmaya da jajurcewa a gaban...
    A lokacin da Abba Musa angon da za a daura wa aure, da wasu mutum huɗu suka kama hanya zuwa kauyen Murno daga garin Boto a Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, babu wanda ya yi tunanin cewa shi angon da ’yar uwar amaryarsa, Raihanatu Sulaiman za su rasa ransu mintoci kadan kafin a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kamitin Zakka na Masarautar Hadejia ya raba zakkar kayayyakin amfanin gona da na kudi kimanin naira miliyan 63 a gundumar Birniwa dake Jihar Jigawa. Sakataren kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Injiniya Isma’ila Barde, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon zakka ga mabukata a gundumar Birniwa. Injiniya Isma’ila Barde ya lissafa abubuwan da aka bayar...
    Daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2024, an gudanar da taron kasa da kasa na “Fahimtar kasar Sin” a birnin Guangzhou. A yayin taron, fiye da baki 600 na kasar Sin da kasashen waje, ciki har da tsohon firaministan kasar Lebanon Hassan Diab, sun hallara don tattaunawa da yin musayar ra’ayi kan...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna. A wata tattaunawa ta wayar tarho, Araghchi da Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp sun tattauna hanyoyin inganta alakar juna da sabbin abubuwa dake faruwa a yankin da na kasa da kasa. Babban jami’in...
    Gwamnatin Trump na duba yiwuwar sanya takunkumin hana zirga-zirga ga ‘yan kasashen duniya 41 a wani bangare na yaki da kwararar bakin haure da aka kaddamar a farkon wa’adin shugaban na Amurka na biyu. Wani bayanin cikin gida da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nakalto ya nuna cewa an rarraba wadannan kasashe zuwa rukuni...
    Rahotannin dake fitowa daga Falasdinu na cewa wani hari da Isra’ila ta kai a arewacin zirin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa tara, ciki har da ‘yan jarida uku a cikin gida, in ji ma’aikatan lafiya. An kai harin ta sama a wata mota a garin Beit Lahiya da ke arewacin zirin yau Asabar. A cewar...
    ’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya.  Farashin kayan abincin ya karye ne a lokacin da wasu ’yan kasuwar suka riga suka saye amfanin gona suka boye...
    A jiya juma’a ne dai firma ministan kasar Iraki Muhammad Shi’ya al-Sudani ya sanar da cewa sojojin kasar sun kashe babban dan ta’adda Abdullahi Makki wanda ake yi wa lakabi da Abu Hadiza. Al-Sudani ya kara da cewa; Iraki taba cigaba da samun nasara akan ‘yan ta’adda, bayan da jami’an tsaro na kasa da kasa...