2025-03-17@11:47:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 458

«gidauniyar Aliko Dangote»:

    A jiya Lahadi ne dai kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kai hare-hare akan iyakar Lebanon ta yankin Hermul Ma’aikatar tsaron Syria ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta riya cewa; harin nata martani akan wani hari da aka kai a can cikin kasar wanda ta jinginawa HIzbullah, da kuma ya yi sanadiyyar mutumar jami’an tsaro uku. Kungiyar ta Tahrirush-sham ta yi amfani da makamai rokoki da atalare  wajen kai hari daga kan iyaka. Tuni dai kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta karyata zargin na kungiyar Tahrirus-sham. Ofishin da yake kula da watsa labaru na Hizbullah ya bayyana cewa; Babu gaskiya a cikin labaran da ake watsawa na cewa Hizbullah tana da hannu a...
    A daren ranar Lahadi Barcelona ta buga wasa mafi kayatarwa a wannan kakar wasanni ta bana bayan ta doke abokiyar karawarta Athletico Madrid duk da cewar Athletico din ta jefa kwallaye biyu a ragar Barcelona a minti 70 na wasan. A kokarin da take yi na sake darewa kan teburin Laliga, Barcelona ta zura kwallaye 4 a cikin minti 20 domin komawa gida da maki uku, Lewondowski, Ferran Torres da Lamine Yamal ne su ka jefawa Barcelona kwallayenta. Yunkurin Neman ‘Yancin Kan Taiwan Ya Shaida Yunkurin Lai Ching-te Na Neman Mulki Irin Na Kama Karya Ta Hanyar Demokuradiyya Ba Don Tarbiyantar Da Mutane Nake Yin Fim Ba -Amina Shehu Lulu Julian Alvarez na Athletico Madrid ya fara bude kasuwa a...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya ba da sanya hannu a kan takardun yarjeniyar samar da zaman lafiya wanda kasashen Armenia da Azerbaijan suka yi. Ya kuma taya mutanen kasashen murmurnar wannan nasara. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana taya kasashen biyu murna a jiya lahadi, ya kuma kara da cewa, Iran a ko yauce tana fatan zaman lafiya a kasashe makobata da kasar sabuda dalilai da dama daga ciki Iran tana amfani da kasashe makobta don kyautata yanayin tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu. Firai ministan kasar Armenia Nikol Pashjinyan a zantawarsa ta wayar tarko da shugaban kasar Iran ya ce: Gwamnatinsa zata yi kokarin ganin an aiwatar da yarjeniyar daki daki kamar yadda...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa hare-haren ta’adanci wadanda sojojin Amurka da Burtaniya suka kai kan yankuna da dama a kasar ba zasu hana mutanen kasar ci gaba da kare Falasdinawa a Gaza ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Al-huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabata a jiya Lahadi da yamma. Ya kuma kara da cewa sojojin kasar zasu ci gaba da kai hare hare kan katafaren jirgin ruwan yaki mai daukar jiragen saman yaki na Amurka dake cikin Tekun maliya. Sannan zasu ci gaba da kai hare hare kan jiragen HKI da na Burtania da na Amurkan masu wucewa ta tekun malia kamar yadda ta bayyana...
    Shugaban kasar Angolan João Lourenço, wanda kuma shi ne ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka (AU) ya yi kira ga gwamnatin Congo Democradiyya da mayakn M-23 su kawo karshen yaki kafin taron tattauna batun tsagaita wuta a gabacin kongo nan gaba. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afirca News” ya nakalto shugaban yana kira ga bangarorin biyu su tsagaita wuta da misalign tsakiyar daren jiya Lahadi don a tattauna batun samar da zaman lafiya cikin Nutsuwa. Majiyar fadar shugaba Lourenco na cewa yakamata tsagaita wutan ya hada har da rashin kokarin mamayar karin iko a wasu wurare. Da kuma dakatar da fada. Da kashe fararen hula da sauransu. An shiya cewa gwamnatin kongo Democradiyya da kuma wakilan yan...
    Firai ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya bukaci kungiyar tarayyar Afirka AU ta bunkasa aikin cibiyar yaki da cututtuka na kungiyar wato CDC don biyan bukatun kiwon lafiya na kasashen nahiyar gaba daya. Kamfanin dillancin labaran Sputnic na kasar Rasha ya nakalto Abiy Ahmed yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da daraktan hukumar ta CDC a birnin Adis Ababa a ranar Jumma’an da ta gabata. An kafa cibiyar yaki da cututtuka ta kungiyar tarayyar Afirka (CDC) ne, a shekara 2016, sannan ta fara aiki a shekara ta 2017 don kawo ci gaba a harkokin kiwon lafiyar a nahiyar Afirka. Gwamnatin kasar China ce ta taimaka aka gina gine-gine cibiyar, aka kuma fara amfani da su a shekara ta 2023....
    Gidauniyar Aliko Dangote, a cikin shirye-shiryenta na 2025, na bayar da tallafin abinci ga ‘yan Nijeriya, ta ƙaddamar da rabon abinci, inda ta ware kimanin Naira Biliyan 16 domin tallafa wa talakawa ‘yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu nakasa. Shirin da fiye da mutum miliyan ɗaya ne za su rabauta da tallafin buhunhunan shinkafa mai nauyin kilo 10 daga wannan tsarin na gidauniyar Aliko Dangote. NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar, Shugaban gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce an tsara yin rabon shinkafar buhu miliyan ɗaya ne ga ‘yan Nijeriya...
    Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta buƙaci Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya nemi afuwar ɗaliban malamin bisa abin da ta kira rashin adalci da aka musu. Idan kuwa bai yi hakan ba kafin ƙarshen watan Ramadan, za su maka shi a kotu. An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da gidauniyar ta fitar, wadda Sayyadi Aliyu Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya sanya wa hannu. A cewar takardar, dole ne El-Rufai ya fito ya yarda da laifinsa sannan ya nemi afuwar gidauniyar, ɗalibanta da jagoranta, Sheikh Ɗahiru Bauchi. Gidauniyar ta zargi tsohon gwamnan...
    Kalmar demokuradiyya kalma ce da jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te ke yawan ambata, amma aikin da ya yi bai bi hanyar demokuradiyya ba. A baya-bayan nan, Lai Ching-te ya gabatar da wani shirin neman ‘yancin kan Taiwan, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokuradiyya ce mai mulkin kanta. Lai Ching-te ya kan yin amfani da demokuradiyya don ya cuci jama’ar yankin Taiwan da sauran kasashen duniya, amma a wannan karo kowa ya san yunkurinsa na neman mulki irin na kama karya ta hanyar demokuradiyya. Ya kamata a yi amfani da demokuradiyya don tabbatar da hakkin jama’a, a maimakon kawo illa ga hakkin jama’a. Jama’ar yankin Taiwan suna neman zaman lafiya, da samun ci gaba, da yin mu’amala,...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin mayar da Filin Idi na Ƙofar Mata zuwa Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa don Harkokin Addinin Musulunci. Sabuwar cibiyar za ta zama wajen gudanar da taruka da karatuttukan addini maimakon barin filin ana amfani da shi sau biyu a shekara don Sallar Idi. HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma Akwai ’yan ƙwaya a cikin sarakunan gargajiya — Obasanjo Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron buɗa-baki da ya shirya a Fadar Gwamnatin jihar a ranar 15 ga watan Ramadan. Taron ya samu halartar Mambobin Majalisar Malamai, inda suka tattauna kan haɗin kai da kuma rawar da malamai ke takawa wajen wanzar...
    “…The composition and functioning of the legislatibe council, howeber, pointed to the fact that, it was nothing more than a mere rubber-stamping institution…”. (Fagge & Alabi, 2007: 5b). Wadancan kalamai na sama cikin harshen Turanci, na yin nuni ne da cewa, “yan majalisun Nijeriya a wancan lokaci da Turawan Birtaniya ke mulkarmu, ba su kasance komai ba, face “yan-abi-yarima ne cikin harkokin zaman majalisar. Duk abinda aka yanke a majalisar, kawai sai dai su sanya-hannu ne akai. Ba su da ikon tabbatar da wani kudiri, koko yin watsi da shi. Tun da, hatta mafi yawan adadin mutanen da ke cikin zauren na majalisar, za a samu cewa, gwamna ne ya zabe su da hannunsa, kamar yadda a rubutun baya aka...
    Hajiya Asta Shehu Timta, mahaifiyar mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta ta riga mu gidan gaskiya. Wata sanarwa da Masarautar Gwoza da ke Jihar Borno ta fitar ta ce Hajiya Asta ta rasu ne yammacin jiya Asabar bayan shafe shekaru 80 a duniya. Yadda za a girka ‘Kamoniya’ An kama malama tana lalata da ɗalibinta Haka kuma, Hajiya Asta ita ce mahaifiyar Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwoza, Yarima Abba Kawu Shehu Timta. Masarautar ta ce za a yi jana’izar marigayiya Hajiya Asta Shehu Timta a yau da Lahadi bayan sallar azahur a Fadar Sarkin Gwoza. A lokacin rayuwarta, Hajiya Asta Shehu Timta ta kasance tsohuwar malamar makaranta kuma har zuwa rasuwarta tana taimakawa wajen ci gaban ilimi a...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran y ace gwamnatin kasar Amurka bata da hakkin tsarawa kasar Iran yadda zata gudanar da manufofinta harkokin waje, wannan ya wuce tun bayana nasarar juyin juya hali musulunci a kasar a shekara ta 1979. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X. Aragchi yana maida martani ne ga shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya tuta sojojinsa suka kai hare-hare kan kasar Yemen a jiya Asabar, don kada su hana jiragen ruwan HKI wucewa daga tekun Red Sea. Kuma ya ce: Ya gargadi Iran ta dakatar da tallafin da take bawa kungiyar Ansarullah. Don itace da alhakin duk abinda kungiyar take yi. Ministan ya kara da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baka’e ya tir da kungiyar kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya,wato G7. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma yi All..wadai da zarge zagren kungiyar wadanda suka hada da zargin Iran da kokarin mallakar makamin Nukliya, da hadsa fitina a kudancin Asia. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran yace dukkan wadannan zarge-zarge basa da toshe. Sannan ya zargi kasashen kungiyar na G7 da goyon bayan HKI a kissan kiyashin da ta aikata a Gaza. Kafin haka dai kasashen kungiyar ta G7 sun kammala taronsu a kasar Canada a ranar jumma’ar da ta gabata inda suka, suka fidda bayanin bayan...
    Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta  Hamas ta yi Allawadai da Hare-haren Amurka da Birtaniya akan kasar Yemen Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da bayani na yin tir da hare-haren da jiragen yakin Amurka da Birtaniya su ka kai wa Birnin San’aa a jiya Asabar da dare. Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta fitar da bayani na yin Allawadai da Amurka saboda harin da ta kai wa Yemen din, tana mai bayyana abinda ta aikata da cewa abin kunya ne da nuna goyon bayan ga laifukan da HKI take aikatawa akan al’ummar wannan yankin. Kungiyar Jiahdul-Islami ta kuma yi jinjina ga kasar Yemen saboda yadda su ka tabbatar da jarunta ta asali irin ta Larabawa da musulmi wajen nuna goyon bayan...
    A lokacin da Abba Musa angon da za a daura wa aure, da wasu mutum huɗu suka kama hanya zuwa kauyen Murno daga garin Boto a Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, babu wanda ya yi tunanin cewa shi angon da ’yar uwar amaryarsa, Raihanatu Sulaiman za su rasa ransu mintoci kadan kafin a daurin auren. Kafin ɗaurin auren ne Abba Musa da Maryam Sulaiman amarya da kuma Rainahatu Sulaiman (’yar uwar amarya) da Misbahu Ahmad (abokin ango) da direban motar sun tafi garin Murno da ke da nisan kilomita 5 daga Boto domin gaisawa da ’yan uwan amaryar kamar yadda aka saba a al’adar Hausawa. Soja ya shafe mako guda da harsashi a cikin ƙwaƙwalwarsa Nijar ta kori...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna. A wata tattaunawa ta wayar tarho, Araghchi da Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp sun tattauna hanyoyin inganta alakar juna da sabbin abubuwa dake faruwa a yankin da na kasa da kasa. Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya nanata tsarin kasar na kulla kyakkyawar alaka ta diflomasiyya da kasashen. Iran da kasashen Turai dai na tattaunawar ba-zata kai a kai tun shekara ta 2021, shekaru uku bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar iran – tare da maido da takunkumin da Washington ta kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. bangarorin kasashen Turai da suka shiga yarjejeniyar nukiliya –...
    Rahotannin dake fitowa daga Falasdinu na cewa wani hari da Isra’ila ta kai a arewacin zirin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa tara, ciki har da ‘yan jarida uku a cikin gida, in ji ma’aikatan lafiya. An kai harin ta sama a wata mota a garin Beit Lahiya da ke arewacin zirin yau Asabar. A cewar likitocin, mutane da dama sun samu munanan raunuka, tare da jikkata a ciki da wajen motar. “An kai shahidai tara zuwa asibiti, da suka hada da ‘yan jarida da dama da ma’aikata daga kungiyar agaji ta Al-Khair, sakamakon harin da aka kai wa motar da wani jirgi mara matuki a garin Beit Lahia, tare da luguden wuta a yankin,” in ji kakakin hukumar tsaron farar...
    Kasar Sin ta bayyana matukar adawa da zarge-zargen kungiyar G7 kan tekun kudancin kasar da manufofinta na tattalin arziki, kuma ta bayyana korafinta ga kasar Canada. Ofishin jakadancin kasar Sin dake Canada ne ya bayyana haka a yau Asabar. A cewar ofishin jakadancin, sanarwar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 da sanarwar ministocin game da tsaron teku, sun yi shisshigi cikin harkokin gidan Sin, kana sun bata mata suna. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A jiya juma’a ne dai firma ministan kasar Iraki Muhammad Shi’ya al-Sudani ya sanar da cewa sojojin kasar sun kashe babban dan ta’adda Abdullahi Makki wanda ake yi wa lakabi da Abu Hadiza. Al-Sudani ya kara da cewa; Iraki taba cigaba da samun nasara akan ‘yan ta’adda, bayan da jami’an tsaro na kasa da kasa su ka yi nasarar kashe Abdullahi al-makki, wanda ya kasance a matsayin  mataimakin shugaban abind ake kira da Daular Musulunci a Iraki da Syria.
    Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’oi ta nuna rashin jin dadinta da wasu manufofi na Gwamnatin tarayya musamman ma irin nau’oin harajin da ake cirewa duk wata ya maida albashinsu ya kasance tamkar miyar da babu Gishiri bare Maggi ko kuma Daddawa, shi yasa karin da aka yi na mafi karancin albashi na Naira 70,000 ya zama tamkar tafiyar Kura ne inda take yin Gaba ta kuma koma Baya. Wannan bayanin ya fito ne bayan da aka kammala taron kwamitin zartarwa na kungiyar manyan ma’aikatan Jami’oi na 50 wanda aka yiu a Jami’ar Gwamnatin tarayya ta Otuoke, Jihar Bayelsa, inda kungiyar ta nuna damuwarta kan manyan lamurra wadanda suke damuwar jin dadin ‘yan kungiyarta,kamar yadda ake samun toge a albashi inda bai...
    Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau. Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa:  Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma  aiki tare.” Baya ga batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu,  da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, Anwar Karkash ya zo da wasiki daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.
    Kusan sojoji 1,300 ne kungiyar kasashen gabashin Afirka ta SADC su ka fice daga kasar jamhuriyar Demokradiyyar Congo, a lokacin da mayakan kungiyar ‘yan atwaye ta M23 suke cigaba da kama yankunan kasar. Wani mai sharhi akan al’amurran siyasar kasar ta Congo, Christian Moleka ya yi gargadi akan sake dagulewar al’amurra a gabashin kasar wanda dama can yana fama da matsalolin tsaro. Janyewar da sojojin na SADC su ka yi daga cikin kasar tana a matsayin wani babban koma baya ne, alhali gwmanatin Kinshasha tana fatan ganin wadannan sojojin sun taka rawa wajen takawa mayakan M23 birki,kamar yadda su ka taba yi a 2023. Sojojin na Congo suna fama da karancin kayan aiki da makamai, da hakan ya bai wa...
    Kimani makonni biyu Kenan jumhuriyar Najer tana fama da karancin man fetur a gidajen man kasar, wanda ya rage zirga-zirgan ababen hawa a duk fadin kasar har da Yemai babban birnin kasar, har’ila yau ya shafi harkokin tattalin arzikin kasar. Shafin yana labarai na yanar gizo IR News, ya bayyana cewa bayan da gwamnatin sojojin kasar ta kasa magance matsalar a cikin gida, ta tura wata tawaga karkashin jagorancin Ministan man fetur na kasar zuwa tarayyar Najeriya tare da bukatar ta aiko mata tataccen man fetur don magance matsalar. Labarin ya kara da cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya dai tuni ta amince da bukatar, tare da bada umurnin a aikawa Jumhuriyar ta Niger tankunan man fetur har 300. Wasu wadanda suka...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye ta bada sanarwan cewa a shirye take da saki fursinonin HKI da Amurka, har ma da gawakin wasu 4, idan HKI ta dawo kan ci gaba da aiwatar da abubuwan da yarjeniyar tsagaita wuta a tsakaninta da HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani Jami’in kungiyar yana fadar haka a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, wasu daga cikin wadanda suke tsakanin kungiyar da HKI ne ya bata wannan shawarar, sannan ya kara da cewa, sai dai wannan matakin yana da sharudda, kuma sune HKI ta amince ta dawo kan tattaunawa marhala ta biyu don aiwatar da yarjeniyar da aka cimma...
    Da yake jaddada cewa ya kamata mutane su fahimci cewa a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, ba wai shi kadai ke wakiltar mazabarsa da jam’iyyarsa ba, har ma da yankin da ba a taba rike wannan mukami ba tsawon shekaru 46 da suka gabata.Shugaban majalisar ya bukaci wadanda ke sukar sa da su yi shiru da bakinsu. Akpabio ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa ba wai kansa kadai yake wakiltar ba, al’ummar yankin Neja Delta gaba daya ba yake wakilta. A yayin da yake jawabi a kan batun samar da kujerun zama da ya shafi Natasha Akpoti-Oduaghan, wanda ya kai ga zargin cin zarafi, Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa mutane suna ihu ne kawai ba tare da fahimtar ka’idojin...
    An tabbatar da mutuwar wata mata da har yanzu ba a bayyana sunan ta ba bayan ta yi tsalle ta faɗa kogin Legas daga gadar Third Mainland a Jihar Legas. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne daga wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Juma’a cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4 na yamma kusa da bakin ruwan kogin da ke hanyar jami’ar Legas. Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar “Tawagar ’yan sandan ruwa da ke aiki a wurin sun gano ta gaɓar ruwan da ke hanyar jami’ar Legas...
    Takardar da aka yi nazari a karshen watan Janairu ta nuna cewa a watan Fabrairun 2025, an ware shirin samar da mai na kan naira zuwa jirgin dakon mai hudu ne kawai, rukuni hudu zalla, kuma a watan Maris, dakon man biyu ne kawai aka yi da ya kai ganga 950,000 (ganga miliyan 1.9 ga watan). Wannan yana wakiltar rabon ganga 61,290 a kowace rana kasa da makasudin 385,000 bpd a karkashin tsarin. Karancin samun danyen mai ya tursasa wa matatar man Dangote garzaya wa kasashen waje domin neman danyen man. A baya-bayan nan kamfanin ya samu gangar danyen mai miliyan 12 daga Amurka. Duk da dai har yanzu matatar Mai ta Dangote ba ta fito a hukumance ta yi...
    Na hudu, kudurin Sin shi ne inganta hadin gwiwa ta hanyar tattaunawa, tare da adawa da neman kwamitin sulhu na MDD ya shiga tsakani. Bugu da kari, ministan ya ce Sin za ta tsaya kan dabarar daukar matakai daya bayan daya da saka alheri da alheri, da neman cimma matsaya ta hanyar tattaunawa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani direban motar bas ya murƙushe wata yarinya ’yar shekara biyu a ƙoƙarin gujewa kamun jami’an hukumar kare haƙƙin jama’a na Jihar Edo. Lamarin ya faru ne a kan titin Ring Road da ke birnin Benin a ranar Laraba lokacin da jami’an hukumar suka yi artabu da wani direban motar bas a lokacin da suke ƙoƙarin kama shi. Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar Mun ceto Najeriya daga faɗa wa mummunan yanayi — Tinubu Shaidu sun ce lamarin ya ta’azzara ne a lokacin da jami’an da ke aikin suka tunkari direban inda yake ƙoƙarin tserewa ya sauya hanyar motar, amma jami’an sun kama sitiyarin motar. “Motar ta murƙushe wata yarinya da ke tsaye kusa da...
    Alhaji Dangote, hamshakin attajirin nahiyar Afirka, ya ce sun hada kai da gwamnatin jihar ne wajen tabbatar da ganin an raba abincin ga mabukata a kowace jiha dake fadin Nijeriya. Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin abincin a matakin kasa na wannan shekara, ya ce aiwatar da wannan shiri ya nuna tsantsar halin nuna jinkai da kulawar Alhaji Aliko Dangote wajen kawar da yunwa da fatara a Nijeriya. Gwamnan wanda mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce za a raba buhun shinkafar guda dubu 120, mai nauyin kilogram 10 a daukacin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano. A jawabinta ga manema labarai, Babbar Darakta kuma Babbar jami’ar gudanarwar gidauniyar Aliko...
    An kusa shiga mako guda daga lokacin da aka fara fuskantar karancin mai a gidajen man fetur da hakan ya jefa masu ababan hawa cikin damuwa. Rabon man fetur da kamfanin SONIDEP yake yi bai wadatar da masu abubuwan hawa ba, yana kuma kawo cikas a harkokinsu na yau da kullum. Da akwai dalilai da dama da su ka haddasa karancin man fetur din, sai dai al’ummar kasar suna son ganin mahukunta sun fito fili sun yi musu bayanin abinda yake faruwa. Wani mazaunin birnin Yemai Assoumane Hamadou suley ya fada wa manema labaru cewa; Ba mu da cikakken bayani akan abinda yake faruwa, domin mahukanta da ya kamata su fito su yi bayani, ba su yin hakan. Su kuwa...
    Shugaban kungiyar agajin Falasdinawa ta “UNRWA’ wacce MDD ta kafa, ya yi gargadin rushewarta da hakan zai hana Falasdinawa na yanzu samun ilimi, haka nan kuma bayar da kayan agaji da bukatun yau da kullum ga mutane miliyan 6 a Falasdinu. Shugaban kungiyar Agajin Philippe Lazzarini ya fada wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa; Da akwai hatsari da gaske da kungiyar take fuskanta na rushewa, da hakan zai kara dagula yanayin da al’ummar Falasdinu suke ciki.” Philippe Lazzarini ya kara da cewa; Idan hakan ta faru, to mun sadaukar da falasdinawan da suke rayuwa a wannan lokacin da hana su ilimi. Tun bayan farmakon Aksa 2023 ne dai  HKI da Amurka su ka dauki matakin haramta kungiyar da dakatar da...
    Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da kungiyar al-Shabaab ta kai a wani otel da ke garin Baledweyne, inda shugabannin kabilu ke ganawa ya kai mutane 10, kamar dai yadda majiyoyin ‘yan sanda na kasar ta Somalia suka tabbatar. Sannan kuma bayanin hukumar ‘yan sandan ta kasar Somalia ya tabbatar da cewa, akasarin wadanda suka rasa rayukansu fararen hula ne. A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani otel da ke birnin Baledweyne da wata mota da aka shakare da bama-bamai, kafin daga bisa suka shiga cikin otal din suka kai farmakin da ya dauki tsawon yini guda. Majiyoyin ‘yan sandan sun tabbatarwa kamfanin dillanmcin labaran Reuters cewa, hudu daga cikin ‘yan ta’addan...
    Kwamatin duba Shirin samar da abincin buda baki na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse, ya yaba da kyakkyawan yanayin kosai da kunu da ake samarwa domin rabawa masu azumi a cibiyar bada abincin ta 2 a mazabar Kiyako ta karamar hukumar Birnin Kudu. Shugaban Kwamatin kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isyaku Abubakar, ya bayyana haka a lokacin rangadin kwamatin. Ya bayyana bubukatakarin kayan miya wajen dafa shinkafar da ake rabawa masu azumi. Da ya ke mayar da jawabi, mai samar da abincin buda baki a cibiyar mazabar Kiyako da ke Babaldu, Salisu Sabo, ya ce suna samar da abincin buda baki da ya hada da shinkafa dafa-duka da kunu da kosai, ga masu azumi 300 a kowace...
    Motocin dai, an bai rundunar soji Uku, yayin da rundunar ‘yansanda ta Mopol ta karbi daya. Kwamandan Barikin Soji na Birnin Kebbi, Manjo A. P. Azubuine, ya bayyana godiyarsa na goyon baya da gwamnatin ke basu wajen yaki da ‘yan ta’adda a fadin jihar.   Shi ma a nasa bangaren, ACP Aliyu Jega, kwamanda Mopol 36 da ke Birnin Kebbi, ya mika godiyarsa ga gwamnan, inda ya kara da cewa, Motar za ta taimaka musu wurin sauke nauyin da ya rataya akansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Amurkawa masu goyon bayan Falasdinu sun gudanar da gangami a unguwar manhatan na birnin Nuyork don neman sakin Mahmoud Khalil daya daga cikin masu gwagwarmaya kan tafarkin samun yencin Falasdinawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kama Mahmoud Khalila da kuma tsareshi ya ingiza matasa da dama a Amurka suka nuna goyon bayansu a gareshi, wasu kuma suka fito zanga-zangar neman a sake shi. Mahmoud Khalil dai, ya kammala karatunsa ne a Jami’ar Colombia na birnin News na kasar Amurka. Sannan ya shahara da goyon baya ga al-ummar Falasdinu. Banda haka yana da ‘Green Card wanda ya bashi damar zama a kasar Amurka na dindin din. Amma a rahotannin da suke fitowa gwamnatin kasar tan son...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau , shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu karin bayani sannan mu ji ra’ayin masana dangane da su gwagwadon lokacinda muke da shi da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… masu sauraro shirimmu nay au zai yi magana dangane da ‘Maida Martanin Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran ga zabin zabi biyun da shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bawa kasar dangane da shirinta na makamashin Nukliya na kasar, tattaunawa ko yaki’. Jagoran...
    Babban Rajistara na Sashen kula da lafiyar Koda a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe (FTHG), Dr. Fidelis Linga, ya yi kira ga jama’a da su kula da lafiyarsu domin kaucewa kamuwa da cututtukan koda. Ya bayyana hakan ga manema labarai a Gombe yayin bikin Ranar Koda ta Duniya. Dr. Fidelis Linga ya jaddada cewa wasu munanan dabi’u kamar shan barasa, da taba, da cin abinci mara kyau, da zama babu motsa jiki na daga cikin dalilan da ke haddasa karuwar cututtukan da suka shafi Koda. Ya yi nuni da mahimmancin yin gwaje-gwaje a asibiti akai-akai, da cin abinci mai kyau, da  motsa jiki domin hana cutar koda. Ya bayyana cewa, a duniya gaba ɗaya, mutane miliyan 850 na...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi a ranar Alhamis don wata ganawa ta musamman. Da isarsa filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa, Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ne ya tarɓe shi. Obi ya ziyarci Gwamna Bala Mohammed a fadar gwamnati, inda suka yi wata ganawar sirri. Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa Da Taɓarya A Bauchi Gwarzon Ɗan Kasuwa Na Shekarar 2024: Benedict Peters Duk da cewa dalilin ziyarar bai fito fili ba, ana hasashen cewa yana da alaƙa da shirin siyasar 2027, inda ake ta raɗe-raɗin haɗakar ‘yan adawa domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki. Taron ya ƙara hura...
    Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta fara rabon tallafin kudi naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas ga iyaye mata marayu dari biyu da saba’in da bakwai da masu bukata ta musamman a jihar Sokoto domin tallafawa kananan sana’o’i.   Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Shugaban shirin, Malam Lawal Maidoki ya bayyana cewa, matakin ya yi daidai da kudurin wanda ya kafa na rage radadin tattalin arziki a tsakanin marasa galihu.   Ya bayyana cewa an zabo mutane 12 da suka ci gajiyar tallafin daga kowace karamar hukumar jihar 23 da suka hada da zawarawa 10 ko marayu mata da kuma nakasassu biyu a kowace karamar hukumar.   Ya ce kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai...
    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗi a baya-bayan nan dangane da ƙaruwar yanayin zafi a sassan ƙasar, yayin da jihohi da dama suke fuskantar ƙarin matsanancin zafi. Gargaɗin ya kuma nuna cewa, tsananin zafin da za a yi fama da shi cikin kwanaki uku ko huɗu masu zuwa wanda zai haddasa damuwar da yanayin na zafi kan haifar a jihohi goma sha tara na ƙasar daga yankin arewa ta tsakiya da yankin gabashin ƙasar. Kan haka ne muka tuntuɓi likita domin ya yi mana ƙarin bayani game da cututtuka biyar da aka fi kamuwa da su a lokacin zafi da kuma hanyoyin kare kai. Sanƙarau – Dakta Hassan Ibrahim, likita a asibitin Biba da ke jihar Kaduna ya...
    Hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA) ta jaddada kudirinta na kula da titunan gwamnatin tarayya da inganta ababen more rayuwa a fadin kasar nan.   Daraktan hukumar ta FERMA, Injiniya Kabiru Iliyasu Dan-Mulki ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) daga gidan rediyon tarayya (FRCN) da kuma gidan talabijin na Najeriya (NTA) Kaduna a ofishinsa da ke Kaduna.   Injiniya Dan-Mulki ya jaddada babban nauyin da ya rataya a wuyan hukumar ta FERMA na tabbatar da cewa titunan gwamnatin tarayya sun kasance masu kyau domin saukaka zirga-zirga a fadin kasar nan. Ya bayyana muhimmancin hada hannu da masu ruwa da tsaki, musamman kafafen yada labarai, domin wayar da kan...
    Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace. Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa. “Amma da suka hango...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta fitar da sanarwa inda ta yi maraba da matakin. ta bayyana wannan mataki a matsayin wanda ke nuna hakikanin matsayin al’ummar Yemen da gwamnatin kasar na goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Falastinu. Har ila yau kungiyar ta yi kira ga dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma ‘yantatun kasashe a duniya da su kara zage damtse wajen matsin lamba ga ‘yan mamaya da magoya bayansu...
    Ministan harklokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce kasarsa na goyon bayan sake farfado da yarjejeniyar farko ta Iran da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi. Mista Lavrov ya jaddada goyon bayan Moscow ga sake farfado da muhimmiyar yarjejeniya da Iran da manyan kasashen duniya suka rattabawa hannu a shekarar 2015. “Mun tattauna halin da ake ciki a yankin Tekun Fasha da kuma shirin hadin gwiwa,” in ji Lavrov a wata hira, a cewar kamfanin dillancin labarai na Tass, yayin da yake amsa tambaya kan ko batun Iran na cikin tattaunawar da ake yi tsakanin Rasha da Amurka. Rasha ta tattauna halin da ake ciki dangane da yarjejeniyar da Iran ta kulla da Amurka yayin da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu. Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi Shin yin sulhu da ’yan fashin daji ita ce mafita? Kuma yaya halin yankunan da suka ƙulla irin wannan yarjejeniya yake a yanzu? Shirin NAJERIYA A YAU, zai yi duba kan yadda wasu al’umma ke ƙoƙarin tsira daga matsalar tsaro ta hanyar yarjejeniya...
    Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau. Kundin rahoton ya kuma bayyana cewa, a shekarar 2025 gwamnatin kasar za ta kara zage damtse wajen raya kauyukan dake rabe da birane da gyara gine-ginen da suka tsufa. Ga duk wanda yake shiga yankunan kauyuka da ke cikin birane (kamar unguwannin masu karamin karfi) ko wadanda suke rabe da su zai ga ba su da kyawun gani, domin kayayyakin alatu da kayatattun gine-gine da ababen more...
    Mohammad Reza Aref mataimakin shugaban kasa na farko a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata karbi umurni daga wata kasa dangane da shirin makamashin nukliya ta zaman lafiya na kasar ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Aref yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa, JMI ta na ci gaba da jajircewa da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dora mata, dangane da shirin kasar na amfani da fasahar Nukliya. Sai dai har yanzun ba zata nemi shawara ko karbi umurni daga wata kasa a kan amfani da wannan fasaha mai dimbin amfani ba. Mataimakin shugaban kasar ya ce, sinadarin Nukliya ya na da matukar amfani kuma...
    “Bayan samun rahoton, jami’in ‘yansanda reshen Faskari ya yi gaggawar tara tawagar jami’an tsaro zuwa wurin.   “Rundunar ta hanyar amfani da dabaru, ta yi kwanton bauna, inda ta rikita ‘yan bindigar da ruwan harsashi wanda ya hakan ya ta tilasta musu guduwa da raunuka daban-daban, an yi nasarar ceto dukkan mutanen 30 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba, kuma an kwato dabbobin da suka sace.   “Kwamishanan ‘yansandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yaba wa jami’an da suka nuna kwazo da jajircewa wajen gudanar da aikin ceto, ya bukaci jama’ar jihar da su ci gaba da bayar da hadin kai ga rundunar ta hanyar samar da sahihin bayanai a kan...
    Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba. Alhaji Sani Isayku Abubakar ya yi wannan kiran ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin domin duba aikin dafawa da kuma rabon abincin azumi a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwaram. Ya ce rangadin duba rabon abincin azumi na daga aikin majalisa na duba ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da inganci da kuma shugabanci nagari. Alhaji Sani Isayku Abubakar tare da Yan kwamatin sun...
    Da jijjifin safiyar yau Laraba ne aka harba rukunin taurarin dan’adam masu karamin zango daga doron kasa guda 18 a cikin roka kirar Long March-8 Y6, daga cibiyar harba kumbo ta kasuwanci ta lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin. Taurarin na dan’adam da aka harba, wanda rukuninsu shi ne na biyar a cikin nau’o’insa, sun shiga falakin da ake so cikin nasara, kamar yadda hukumar kula da kimiyya da fasahar sararin sama ta kasar Sin (CASC) ta bayyana. Hukumar ta kara da cewa, taurarin za su kasance rukunin taurarin dan’adam na kaddamar da ayyukan intanet na kasuwanci na kasar Sin. Wannan aiki na bincike da aka kaddamar na farko daga sashe mai lamba ta 1 na tashar harba kumbon,...
    Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya, yayin da yake magana da ‘yan majalisun kasar Amurka. Sai dai shugaban bai san sauye-sauyen da kasashen Afirka suka samu ba, wadanda tun tuni suka daina dogaro da kasashen yammacin duniya. A daura da haka, ana iya ganin fahimtar matsayin kasashen Afirka mai dacewa, a cikin maganar da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a kwanan baya, yayin da yake amsa tambayar da...
    Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”
    Shugaban ofishin yada labarai a Gaza Salama Marouf, ya yi Allah wadai da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, saboda kin janyewa daga yankin Salahul Din a kudancin Gaza da kuma ci gaba da kutsawa da da kai hare-hare a cikin Rafah. Marouf ya yi gargadin cewa wadannan ayyuka na nuni da irin mummunan nufi da haramtacciyar kasar Isra’ila ke da shi da kuma yadda take ci gaba da aikata laifuffuka kan al’ummar Palasdinu. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Marouf ya bayyana cewa, a cikin kwanaki goman da suka gabata, sojojin Isra’ila sun kara zafafa hare-hare,  duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Ya yi nuni da lamari na baya-bayan...
    Kasar Ukraine ta bayyana aniyarta ta amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar, game da dakatar da bude wuta nan take tsakaninta da Rasha har tsawon kwanaki 30, biyowa bayan fara tattaunawa da tawagar Amurka a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin wakilan Ukraine da na Amurka da aka fitar a jiya Talata ce ta tabbatar da hakan, bayan sassan biyu sun shafe sa’o’i suna tattaunawa. Sanarwar ta ce akwai yiwuwar tsawaita yarjejeniyar, kuma Amurka za ta tuntubi Rasha kasancewar amincewarta zai tabbatar da cimma nasarar matakin. Baya ga hakan, Amurka ta amince da dage matakin dakatar da musayar bayanan sirri, kuma za ta ci gaba da baiwa Ukraine tallafin tsaro, yayin da kuma sassan biyu...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne. “Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.” Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da...
    Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas. Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar...
    Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da daruruwan fasinjoji a ranar Talata a wani yunkurin ci gaba da ta da hankali da wata kungiyar ’yan aware ke yi a Kudu maso yammacin Pakistan. ’Yan bindigar sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan mai duwatsu da ke iyaka da Afghanistan da kuma Iran. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani babban jami’in gwamnati mai kula da harkokin sufurin jiragen kasa Muhammad Kashif ya shaida wa AFP cewa adadin mutane da aka yi garkuwa da su ya kai 450. Sai dai kuma shafin jaridar rnz na intanet ya ruwaito cewa, daga...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a wani bangare na kokarinsa na yada albarkar watan Ramadan. A cewarsa, kula da marayu ba kawai nauyin zamantakewa ba ne, amma wata gagarumar ibada ce da ke karfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma. Da yake jawabi yayin taron rabon kayan, sakataren gidauniyar, Bashir Muhammad King, ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace. Ya...
    An kora Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United gida a Gasar cin Kofin FA na bana, bayan Fulham ta doke ta da ci 2-1 har gida a filin wasanta na Old Trafford a makon da ya wuce. Manchester United ta yi bankwana da gasar ne alhali ita ce ke mai riƙe da Kofin FA da ta lashe a bara, bayan nasara a kan Manchester City, lamarin da ya ba ta damar buga Gasar Europa a kakar bana. ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’ An hana tashe bana a Kano — Nalako Kungiyar Old Trafford ta koma matsayi na 14 a kasan teburin Firimiya da maki 34, bayan da ta ci...
    A nata ɓangaren, Amurka ta ce za ta yi amfani da wannan dama don fahimtar matsayin Ukraine kan kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin ta da Rasha. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da Matatar Dangote domin sayar mata da ɗanyen man fetur a farashin naira za ta ƙare a wannan wata na Maris. Sai dai kamfanin ce yana tattaunawa da Matatar Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira. An hana tashe bana a Kano — Nalako NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Sanarwar ta NNPC na zuwa ne bayan wasu rahotonni sun ce kamfanin ya dakatar da sayar wa matatar mai a farashin naira, kamar yadda suka ƙulla yarjejeniya tun da farko. Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye ya fitar a ranar Litinin ta ce ba...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi imanin cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake dawo da yaki a zirin Gaza ba ta da amfani, tana mai cewa tattaunawar tsagaita bude wuta ce hanya daya tilo da Isra’ila za ta iya ceto rayukan ‘yan kasarta da take garkuwa ranar Litinin 10 ga watan Maris, kungiyar ta ce Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu na kawo cikas ga aiwatar da yarjejeniyar saboda wasu dalilai na rajin kansa da kuma na siyasa kawai. Hamas ta kuma kara jaddada aniyar ta na aiwatar da yarjejeniyar, inda ta bayyana aniyar ta na kaddamar da shirin tsagaita wuta a mataki na biyu ba tare da bata lokaci ba. Har ila yau kungiyar ta ce gwamnatin Isra’ila...
    Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta. Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali da Nijar. Ci gaba da huldar tattalin arziki da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, na daga cikin jigon rangadin da shugaban Ghana ya kai a kasashen na AES. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta...
    Jakadan kasar Rasha na din din din a cibiyoyin MDD da suke Vienna, ya bayyana cewa dakatar da aiwatar da yarjeniyar shirin Nukliya na kasar Iran wanda ake kira JCPOA, wacce kuma aka samar da shi a shekara ta 2015, da kasashen yamma suka yi, shi ne ya haddasa dukkan matsalolin da suka biyo baya. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto, Mikhail Awliyonov yana fadar haka a hirar da ta hada shi da jaridar Ezustiyo na kasar Rasha. Jakadan ya kara da cewa a tsakanin shekara ta 2021 da kuma 2022 an tattauna da kasashen yamma kan yadda za’a aiwatar da yarjeniyar JCPOA da kasashen bayan da kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar a shekara ta 2018,...
    Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kwara ta ce ta fara bincike kan kisan da aka yi wa Alhaji Idris Abubakar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar, ya ce an harbe shugaban ne a ranar 8 ga Maris, 2025 a kofar gidansa da ke Oke-Ose, a unguwar Ilorin. A cewar sanarwar Jami’an ‘yan sanda sun garzaya inda lamarin ya faru nan take, inda suka gano kwamson harsashi guda biyar da aka yi amfani da su wajen yin harbin. Ya bayyana cewa Hukumar Binciken Laifukan Jiha (SCID) ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Ta kuma bada...
    Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar haƙƙin ɗan Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta na faɗin alabarkacin baki, wanda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba ta. Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta fitar a ranar 8 ga watan Maris, SERAP ta ce muddin ba a kiyaye wannan gargaɗi ba za ta ɗauki matakin shari’a nan da sa’o’i 48. Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun matamaikin shugabanta,...
    Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel din nan uku da suka balle daga kungiyar Ecowas. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kasashen uku na Sahel. Saidai a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na Nijar, hukumomin kasar sun tabbatar da cewa kasashen sun tabbatar da aniyarsu ta karfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashensu a fannonin siyasa, tattalin...
    Kasar Qatar ta bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da ta sanya ido kan cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta bayyana cewa, Doha ta bukaci hukumar ta (IAEA) da ta sanya damar gudanar da bincike da ka’ida daga hukumar ta MDD, kan dukkanin cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. Jakadan dindindin na Qatar a Majalisar Dinkin Duniya, Jasem Yacoub al-Hammadi, ya bukaci gwamnatin Isra’ila da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta ce “Al-Hammadi ya jaddada bukatar kasashen duniya da cibiyoyinta su tabbatar da alkawurran da suka dauka a karkashin kudurorin kwamitin sulhu na MDD, da babban taron...
    Bayanai da kungiyar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar, sun ce rikicin baya-bayan nan tsakanin bangarorin da ke dauke da makamai da suka hada da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTC) da kungiyoyin dake da alaka da tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000 a cikin kwanaki biyu kacal. Wannan tashin hankalin, ya fi shafar yankin yammacin Syria, wanda ya kara ta’azzara halin da ake ciki. A baya dai kungiyar ta bayar da rahoton cewa, an kashe akalla mutane 237 da suka hada da 142 wadanda ba mayakan ba ne a yankin gabar ruwan kasar ta Syria, tun bayan fara kazamin fada a ranar Alhamis din da ta gabata....
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa, gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon na nan da karfinta, duk da asarorin da ta yi da kuma sadaukarwa. A wata hira da yayi da tashar talabijin ta Al Manar, Sheikh Qassem ya bayyana cewa, ‘yan gwagwarmaya a kasar Lebanon sun yi nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta kawo karshen hare-haren da Isra’ila a lokacin da suke kara jajircewa. Ya jaddada cewa “a koyaushe ana ci gaba da tuntubar juna tsakaninsu da shugaban majalisar Nabih Berri, kuma ba mu yi wata tattaunawa a cikin rauni ba.” Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa, muddin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta ci gaba da mamayar yankunan Lebanon, to dole ne a tunkare ta ta...
    Fiye da fursunoni 40 na Isra’ila da ke hannun kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa ne suka mutu a hare-haren da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka yi ta kaddamarwa kan al’ummar yankin tun  daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, kamar yadda wani rahoton baya-bayan nan na jaridar New York Times ya bayyana. Binciken, wanda jaridar ta New York Times ta buga a wannan  Asabar, ya ce fursunoni 41 daga cikin fursunoni 251 na Isra’ila da ake tsare da su a Gaza, an kashe su ne ta hanyar bama-bamai da Isra’ila ta yi ta jefawa kan yankin. Binciken ya dogara ne akan rahotanni da kuma binciken soji kan mutuwar fursunonin, da hirarraki da sojoji da jami’an Isra’ila, da kuma wasu daga cikin dangin wadanda...
    Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun  zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da gidajen jama’a da aka wawushe da kuma wadanda aka kona. Wannan dai na zuwa ne bayan wani tashin hankali da ya barke a yammacin kasar ta Syria, inda aka ga wasu dauke da makamai masu alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin kasar ta Syria da kuma dakarun tsaron cikin gida a cikin faifan bidiyo suna aikata munanan laifukan yaki da suka hada da kisan  fararen...
    Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya, ya shirya taro domin bikin ranar mata ta duniya da ake gudanarwa a ranar 8 na watan Maris din kowacce shekara. Taron mai taken “Labarinta, Makomarta” wanda ya gudana ranar Juma’a a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin dake birnin Abujan Nijeriya, ya hada mata daga dukkan bangarorin rayuwa, inda suka yi waiwaye kan ci gaban da suka samu da ma tsara hanyar tabbatar da daidaiton jinsi.   Da yake jawabi yayin taron, jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai, ya nanata muhimmancin bikin na wannan shekara kasancewar ya zo daidai da cikar Yarjejeniyar Beijing ta tabbatar da daidaiton jinsi ta MDD, shekaru 30 da kulluwa. A Mai Da Duniya Ta Zama Ta Kasa Da Kasa...
    Gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar congo ta ware kudi da sun kai dalar Amurka miliyan 5 akan duk wanda ya kamo mata shugabannin  kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 da su ka hada Corneelle Nangaa, Sultani Makenga da kuma Betrand Bisimwa. Sai dai duk da kudade masu tsokar da DRC din ta sanya akan shugabannin kungiyar su uku, abin da kamar wuya,saboda ganin yadda wannan kungiyar take ci gaba da kutsawa cikin manyan birane tana shimfida ikonta a cikinsu. A halin yanzu biranen Goma da Bukavu da suke a gabashin wannan kasa sun shiga karkashin ikon mayakan kungiyar ta M 23. Dubban mutane ne dai su ka rasa rayukansu yayin da wasu dubun dubata kuma su ka bar gidajensu zuwa inda za...
    Abin haka yake, akwai kasashe sama da 190 a duniyarmu, idan kowace kasa na bin manufar ba kanta fifiko, to nuna fin karfi zai zama a ko ina a duniyarmu, kuma kasashe masu karamin karfi su ne za su fi fuskantar matsalar. Amma abin farin ciki shi ne, har yanzu akasarin kasashen duniyarmu na rungumar adalci da zaman daidaito, kuma karin kasashe na rungumar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama. A sa’i daya kuma, kasashe masu tasowa na kara karfinsu, inda suka riga suka zama muhimmin karfin da ke kiyaye zaman lafiya da sa kaimin ci gaban duniya. Mutanen kasashen yamma su kan ce, “Moriya ta fi zumunta muhimmanci da dorewa”. Amma a ganin Sinawa, ya kamata abota...
    Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar da rahoton cewa, adadin fararen hula da aka yi kisan kiyashin na baya-bayan nan daga tsiraru ‘yan Alawite ya kai mutane 1,018 tun daga ranar alhamis zuwa wannan Lahadi. Kungiyar sa ido ta ce jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria da kuma kungiyoyin da suke kawance da su da suka da alaka da alkaida, sun kashe fararen hula 745 na Alawi a cikin kwanaki uku da suka gabata, wanda ya haura adadin da aka sanar a lokutan baya. Sai dai Fox News ta buga misali da wata ‘yar Alawiyya, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa sama da mutane 4,000 ne aka kiyasta an kashe...
    Wasu ’yan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah reshen Jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar yayin da maharan suka biyo sawunsa suka harbe shi a ƙofar gidansa da ke yankin Oke Ose na birnin Ilorin. Malaman Tsangaya Sun Bai wa Gwamna Inuwa Lambar Yabo Ta ‘Khadimul Qur’an’ Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Muhammad Abdullahi, wani hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan hulɗa da al’umma da harkokin Fulani, ya tabbatar da faruwar lamarin. “Eh, an kashe shi jiya da daddare. Wasu ’yan bindiga ne suka harbe shi. “A yanzu haka ana shirin yi masa jana’iza, amma tun a jiya ’yan...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin...
    Minnaro kafin mutuwarshi shi ne babban likitan kungiyar ta Barcelona, kungiyar ta fitar da sanarwar mutuwarshi ana dab da fara wasan, hakan ne ya sa aka dakatar da wasan domin nuna girmamawa gareshi da kuma jajantawa yan uwa da abokan arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A karon farko alkaluman ta’addaci a yankin Sahel da ke nahiyar Afirka ya zarce na jimillar sauran sassan duniya, a cewar rahoton cibiyar GTI mai bincike kan ta’addanci a matakin duniya. Rahoton ya nuna yawan kashe-kashe masu alaka da ta’addanci a Sahel, “ya zarce rabin jimillar adadin a duniya.” Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol Ramadan: Hisbah ta rufe shagon caca a Kano Alkaluman sun nuna an kashe mutane 3,885 a yankin daga cikin mutane 7,555 da aka kashe a fadin duniya a dalilin ta’addanci. Rahoto ya kara da cewa a yayin da adadin a matakin duniya ya ragu daga kimanin 11,000 a shekarar 2015, lamarin ya ninku sau 10 a yankin daga shekarar 2019,...
    Ya ce: “Za mu yi amfani da dandamalin Taron Kasuwanci na Faransa da Nijeriya domin isar da saƙon da Shugaban Ƙasa ke son mu isar a wannan shekara.   “Wannan shekara, 2025, ita ce shekarar da za a ƙarfafa tattalin arziki da zamantakewa a Nijeriya kamar yadda Shugaban Ƙasa ya alƙawarta. Kamar yadda kuka ji a lokuta da dama, tattalin arzikin mu ya fara samun ingantacciyar nasara. Farashin abinci da ya hauhawa a baya yana sauka.   “Darajar Naira na fara nuna alamun daidaituwa, kuma duk shirin gyaran tattalin arzikin da Shugaban Ƙasa ya aiwatar suna fara samun nasara, kuma da yardar Allah, za mu kai ga burin da muke nema.”   Ministan ya amince da cewa kowace ƙasa da...
    A dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar mata ta duniya kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadi da HKI saboda kissan mata kimani 12.000 a gaza a cikin yakin tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar Hamas na fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurla da kasashen Turai, idan magana ta zo kan matan Falasdinawa wadanda HKI ta kashe, suna nuna faska biyu. Kashe mata Falasdinawa ba take hakkin mata ne ba, tunda HKI ce ta kashe su. Kungiyar ta kara da cewa HKI ta kashe mata 12,000 sannan ta raunata wasu dubbai, haka ma ta kori wa su da dama daga godajensu.
    Ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohammad Bin Abdurrahman Al-Thani, ya kara nanata matsayin kasar na kin duk wani yaki kan shirin Nukliyar kasar Iran, ya kuma yi kira ga Amurka da Iran su warware wannan matsalar ta ruwan sanyi. Ko hanyar diblomasiyya. Kafin haka dai JMI ta sha nanata cewa shirinta na makamashin na zaman lafiya ne. Sannan don haka ne ta amince ta kulla yarjeniyar shirin nukliya ta zaman lafiya  da manya manyan kasashen duniya, a shekara ta 2015 daga ciki har da kasar Amurka. Amma shugaban kasar Amurka na lokacin Donql Trump ta fidda kasar daga yarjeniyar sannan ta dorawa kasar takunkuman tattalin arziki mafi muni don tursasa mata ta sake zama don sabuwar tattaunawa da ita. Mohammed...
    5. Damfara da Alkawurra na Bogi: Wasu na bayar da alkawurran aure da ba su da gaskiya don cimma wasu burika nasu. Yadda Za Ka Kare Kanka • Ka guji aika hotuna na sirri ko bidiyo ga wanda ba ka sani sosai ba. • Kar ka yarda da duk wani alkawari da ba ka tabbatar da gaskiyarsa ba. • Ka duba asalin mutum kafin ka yi amanna dashi da bayanan ka. • Yi taka-tsantsan da sakwannin da kake fitarwa a yanar gizo. • Ka daina amfani da intanet wajen yin mu’amala da wanda ba ka da isasshen sani a kansa. • Idan kana fuskantar barazana, ka sanar da hukuma ko wani da ka yarda da shi. Labari Domin Karfafa Gwiwa...
    Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, Hussein Ibrahim Taha, ya bayyana goyon bayan kungiyar ga shirin Larabawa na sake gina zirin Gaza. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta gudanar da wani zama na musamman na majalisar ministocin harkokin wajen kasashe mambobi a kungiyar, taron da ya gudana a birnin Jeddah na kasar Saudiyya a wannan  Juma’a, inda suka tattauna halin da ake ciki dangane da ayyukan wuce gonad a iri na Isra’ila a Falastinu. A cikin jawabinsa, Sakatare-Janar na Kungiyar Hadin Kan Musulunci ya tabbatar da goyon bayansa ga shirin sake gina zirin Gaza, wanda taron kolin kasashen Larabawa ya amince da shi, tare da jaddada hakkin al’ummar Palasdinu na ci gaba da zama a cikin kasarsu....
    Wasu alkaluma da suka fito daga Babban Bankin Nijeriya CBN sun suna cewa, a 2024, Asusun ajiyar Nijeriya rufe ne a kan Dala biliyan 40.877. Wani masani a fannin tattalin arziki da ke da zama a jihar Legas Ibukun Omoyeni, a wani hasashe da ya yi kan shekarar 2025 ya bayyana cewa, Nijeriya ta fuskanci wasu bin ka’dojin yarjejeniyar karbar bashi, inda ya kara da cewa, baya ga batun kafin a shiga shekarar 2026, akwai wasu basussuka na waje Nijeriya ta ciwo wandanda kuma, ba su riga sun gama nuna ba, wanda akalla zai iya kai wa Dala biliyan 1.33 a duk shekara ko kuma sama da haka wadanda suka hada da biyan kudin ruwa na rancen, inda mai yuwa,...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi kira ga masu dafa abincin buda baki a karamar hukumar Kafin Hausa da su kasance masu gaskiya da adalci wajen ciyar da masu azumi a wannan watan na Ramadan. Mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ayyuka na musamman, Alhaji Abdulkadir Bala T.O yayi wannan kiran yayin da yake duba cibiyoyin ciyar da masu azumi na Dan Modi a cikin garin Kafin Hausa. Alhaji Abdulkadir Bala T.O ya yaba da kokarin wasu daga cikin masu dafa abincin, yayin da ya nuna rashin jin daɗi kan yadda wasu suka karya yarjejeniyar da aka gindaya masu. A nasa jawabin, Shugaban karamar hukumar Kafin Hausa, Alhaji Abdullahi Sa’idu Nalayi, ya tabbatar da cewar, Karamar hukumar za ta...
    Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya buɗa-baki a Fadar Gwamnati da ke Abuja, inda ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar nan na kan hanya gyaruwa nan ba da jimawa ba. A yayin jawabinta, ta jaddada muhimmancin tausayi da jin-ƙai a tsakanin rayuwar ɗan adam. Wani mutum ya yanke jiki ana salla a Masallaci, ya rasu a asibiti Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha Ta buƙaci kowa ya kasance mai aikata alheri tsakaninsa da Allah, ba don neman yabo ko amincewar mutane ba. A yayin buɗa-bakin, Farfesa Azeezat Adebayo, Shugabar Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Ilorin, ta bayyana cewa tausayi da jin-ƙai su ne ginshiƙai na kyakkyawar rayuwa a tsakanin al’umma. Ta tunatar da mahalarta...
    A lokacin ganawar ta su, Dantsoho ya shedawa Daraktar yin ayyukan da ake gudanarwa a Hukumar ta Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa. Da take mayar da jawabi Daraktar Janar ta Cibiyar ta bayyana tawagar ta NPA shawarar ta kan yadda za a kara inganta ayyukan NPA, musamman a bangaren samar da saukin yin kasuwanci, domin a kara habaka gasar yin kasuwanci da kuma kara tara kudaden shiga. Kazalika, Hukumomin biyu, sun bayyana fatan kan hadakar a tsakaninsu, domin a samar da sauye-sauyen da a za su samar da sakamako mai kyau. Hukumar ta NPA, ita ce aka dorawa nauyin tafiyarwa da kuma tafiyar da ayyukan Tashoshin Jirgen Ruwan Kasar. Ana sa ran wannan hadakar a tsakanin NPA da PEBEC, za...
    Har ila yau Wang Yi, ya ce Sin da Amurka za su kasance a doron duniya na tsawon lokaci, don haka dole ne su nemi yadda za su yi zaman jituwa cikin lumana. A cewar Wang Yi, mutunta juna muhimmiyar ka’ida ce ta hulda kasashen biyu. Da yake tsokaci game da matakin Amurka na sanya karin haraji kan kayayyakin kasar Sin bisa fakewa da batun Fentanyl, Wang Yi ya ce, bai kamata Amurka ta saka alheri da sharri, ko kuma kakaba haraji ba. Yana cewa, tu’ammali da maganin Fentanyl a Amurka, matsala ce da ya kamata kasar ta warware da kanta. Ya kara da cewa, ba zai yiwu a yi tunanin za a danne kasar Sin, sannan kuma a ci...
    A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%. A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi. Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen...
    Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade dalar Amurka biliyon $860 (Euro 800bn) don karfafa kasashen Turai da kuma Ukrania. Shugaban kungiyar ta EU Ursula von de Leyen yace a karon farko tsaron kasashen yake komawa kansu bayan da Amurka ta dauki nauyin hakan tun bayan yakin duniya na II. A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tace ba zata ci gaba da kashewa wadannan kashe kudade don tsarunsu ta kungiyar tsaro ta...