2025-02-22@06:27:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 782
«Kotun Duniya»:
Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan...
Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da...
Shugaban ya kara da cewa, a shekarar farko ne ake fara girbe reshensa, sannan kuma bishiyar tasa na daukar tsawon shekara 50 ana amfana da ita. “A shekara, sau biyu ake girbe Inibi, sannan idan aka ajiye ganyensa a kan tebur, yana shafe daga kwana 45 zuwa 50 ba tare da ya lalace ba”, in...
Kafafen watsa labarun Amurka sun sanar da cewa wani karamin jirgin sama ya fadi akan wata cibiyar kasuwancin dake Philadelphia a jihar Pennsylvania tare da kashe mutane 6 da suke cikinsa. Kafafen watsa labarun na Amurka sun ce ‘yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe gobarar da ta tashi a cikin gidaje da dama a yankin...
Bayan da su ka kwace iko da birnin Goma dke gabashin kasar DRC, kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta sha alwashin kama hanyar shiga babban birnin kasar Kinsasha. Wani daga shugabannin kungiyar ta M 23, Corneilla Nangaa ya furta cewa,: manufarmu ita ce, muna yin yaki ne...
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako...
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Kamfanin na Biba Atlantic da Didam, sun sana son ra’ayin a cikin wasikar su ta samun umarni tare da samun bayanan sirri, daga gun ma’aikata, ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ya ba su dama tabka badakala da aikata cin hanci da rasahawa. Kazakla, sanarwar ta bayyana cewa, daga...
Bisa alkaluman da hukumar kula da zirga-zirgar layin dogo ta kasar Sin ta bayar, tun daga kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara na Sin daga ranar 14 zuwa ranar 30 ga watan Janairu, yawan fasinjojin da jiragen kasa suka dauka ya kai miliyan 206 a kasar, kuma an yi zirga-zirgar fasinjojin cikin kwanciyar...
Gwamnonin tafkin Chadi da suka haɗa da Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, sun zaɓi gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a matsayin sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin. Sanarwar na cewar, an zaɓi Gwamna Buni ne a ranar Juma’a a ƙarshen taron ƙungiyar gwamnonin tafkin Chadi karo na 5 da aka gudanar a Maiduguri. ’Yan...
Bugu da ƙari, Naira miliyan 267.6 an ware su domin shirye-shiryen Addinin Musulunci da tallafa wa waɗanda suka Musulunta, yayin da Naira miliyan 589 za a yi amfani da su wajen bincike kan harkokin tsaro da kuma yaƙi da bara a tituna. Jimillar kasafin kuɗin Jihar Kano na shekarar 2025 ya kai Naira biliyan 719.75,...
Alkaluma daga ma’aikatar kudi ta kasar Sin sun nuna cewa, kudin shigar kamfanoni mallakin gwamnatin Sin ya karu da kaso 1.3 a shekarar 2024. A cewar ma’aikatar, kamfanonin sun samu karuwar yuan triliyan 84.72, kwatankwacin dala triliyan 11.7 na kudin shiga a 2024. Jimilar ribar da suka samu a shekarar 2024 kuma, ta karu da...
A kan yawan samun hauhawan farashin man Garima yace kungiyar na samun saukin farashin sawo man man daga matatar Dangote Refinery da ta MRS duba da cewa, farashinsu na da sauki sosai. Garima da yake yin tsokaci a kan yawan samun hauhawan farashin man a kasar nan, ya bayyana cewa, ‘ya’yan kungiyar na samu sayen...
Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro sun kai samame a wasu gidajen jama’a a birnin, inda suka kama wasu da ake zargin ɓarayi ne tare da ƙwato kayayyakin da aka sace. Wasu daga cikin kayayyakin da aka ƙwato da suka haɗa da: naɗin igiyoyin wutar lantarki masu...
An bayyana dangantakar cinikayya tsakanin kasar Sin da Afrika a matsayin wadda ta taimaka wajen gaggauta ci gaba da samar da irin zamanantarwar da nahiyar ke bukata domin ta kasance cikin takara a duniya. Muya Guo, shugabar sashen Sin a bankin Stanbic na Kenya ne ta bayyana haka yayin wata hira a Nairobin Kenya, inda...
Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya, wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar kowace shekara, ana fara bukukuwan ne da karfe 9:33 na safe, na ranar 1 ga Fabrairu, 1979, ga...
“Kamafanin na LNG na kasa, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin azrikin Nijeriya da kuma kara bayar da goyon baya wajen ganin ana fitar da kaya zuwa ketare, kuma zamu tabbatar da cewa, an kara karfafa hadaka a tsakanin Hukumar da Kamfanin.” Inji Dantsoho. “Rarar da Nijeriya ta samu na hada-hada ta kai...
Wasu sojoji da har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka bayan da wani da ake zargin wani direba da ya bugu cikin barasa ne ya kutsa cikin su a yankin Shomolu da ke Jihar Legas. Lamarin ya faru ne ’yan mintuna kaɗan bayan da sojojin suke kan...
Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan...
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana kan zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a...
Masu haƙar zinare aƙalla mutum 10 sun mutu wasu da dama sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a kansu a wani filin haƙar ma’adinai yankin Koulikokro na ƙasar Mali. Hukumomin yankin sun bayyana cewa mata ne yawancin masu haƙar zinaren da abin ya rutsa da su mata ne, kuma an kasa ciro gawarwakinau, “saboda tsananin sarƙaƙiyar...
Ana zargin wani ɗan ƙabilar Ibo mai suna Oguchwku da yin lalata yaran makarantar Firamare masu shekaru 9 da 10 da haihuwa, kuma ‘ya’yan Hausawa ne. Aminiya ta bibiyi lamarin a inda ta garzaya Cibiyar Kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Ƙofar Gayan Zariya a Jihar Kaduna. Shekara...
A kwanakin baya, jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun adawa sun zargi APC da ruruta wutar rikicin da ke tsakaninsu, inda suka yi zargin cewa jam’iyya mai mulki na neman murkushe ‘yan adawa domin tabbatar da ci gaba da mulkin Shugaba Tinubu a 2027. APC ta musanta wadannan ikirari. Tun da aka hambarar da jam’iyyar PDP,...
Da yake magana ta cikin shirin siyasa na talabijin Channels, ministan ya ce, shugaban kasa bai yi wasu tafiye-tafiyen da suka isa ba. “Har yanzu wannan gwamnatin sabuwa ce. An rantsar da shi a 2023. Ta fuskancin duniya har yanzu shi sabon shugaban kasa ne. Yana bukatar tattaunawa da ganawa da takwarorinsa domin gina alaka...
“Da na tambaye shi dalili, sai ya ce al’ummominmu suna fama da barnar ‘yan bindiga da hakan ke janyo asarar rayuka da garkuwa da mutanenmu tsawon shekaru zuwa yanzu ba tare da samun mafita da shawo kan lamarin ba.” Gwamnan ya ce bayan rokon, ya zauna da masu ruwa da tsaki ciki har da mashawarcin...
Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin...

Tunawa Da Ranar Wadanda Aka Yi Wa Kisan Kiyashi: Majalisar Dinkin Duniya Ta Wayar Da Kan Dalibai A Abuja
Ishara ”Kada Mu Manta” taron, ya ba da haske game da lokutan soyayyar dangi da alakar kud da kud da ke wanzuwa a cikin iyalai na Yahudawa da al’ummomin kafin Holocaust da alhakinmu na kare hakkin kowa na rayuwa cikin mutunci da zaman lafiya. Da yake gabtar da jawabi a yayin taron jakadan kasar...
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci da kasar Kazakhstan a wata ganawa da firaministan kasar Kazakhstan Olzhas Bektenov. A yayin taron na ranar Alhamis, Aref ya bayyana bukatar samar da karin kwamitocin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Bayan goron gayyata day a...
Dakarun Ezzeddine al-Qassam, reshen kungiyar gwagwarmayar Hamas masu dauke da makamai, sun sanar a jiya Alhamis shahadar babban kwamandan kungiyar Mohammad “Abu Khaled” Deif tare da wasu manyan kwamandoji da dama, a wani bangare na farmakin guguwar al-Aqsa. Da yake magana a cikin wani faifan bidiyo da aka fitar ta kafar yada labaran soji ta...
Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu. Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar...

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba
Idris ya ce: “Waɗannan bala’o’i ne da yawancin su ɗan’adam ke haddasawa, kuma ba za mu bari su ci gaba da faruwa ba. “Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen faɗakar da jama’a da wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman masu wannan haramtacciyar sana’a. Wannan...
Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba. Ita...
Mayaƙan Boko Haram aƙalla 5,000 da suka tuba sun koma cikin al’umma da iyalansu, a cewar Cibiyar Yaƙi da Ta’addabnci na Ƙasa. Cibiyar, wadda ke ƙarƙashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Sha’ani Tsaro ta bayyana cewa babu ko mutum ɗaya da cikin tubabbun mayaƙan na Boko Haram da ya sake ɗaukar makami. Ta bayyana cewa...
Dakta Tingilin ya ce a cikin wannan shekarar, gwamnatin Jihar Katsina ta yi kasafin kudi na naira miliyan dubu 50 domin tabbatar da samar da tsabtataccen ruwan sha a kananan hukumomi 20 na cikin jihar. Ya kara da cewa kwamitin karbar korafe-korafe da aka kafa, an kafa shi ne domin duba aikace-aikacen shirin SURWASH da...
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada aniyar Iran na bunkasa alaka da kasar Qatar a dukkan fannoni Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi nuni da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Qatar, yana mai jaddada aniyar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na bunkasa alaka da kasar Qatar a fannoni daban daban....
Kotun da ke shari’ar manyan laifuka a duniya tana gab da fitar da sammacin neman kama wadanda suka aikata muggan laifukan Darfur na kasar Sudan Mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Karim Khan, ya sanar da cewa ofishinsa zai bukaci fitar da sammacin kama wadanda ake zargi da aikata ta’asa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin shure-shure Jam’iyyar PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya? Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna. Tuni wasu ma suka fara ɗigaayar tambaya a...
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce an samu ci gaba sosai a yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashe da yankuna 160 na duniya a shekarar 2024. Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, yawan kayayyakin da kasar ta fitar ya karu da kaso 7.1 a shekarar, wanda ya kai yuan triliyan...
Karamar Hukumar Birnin kudu ta jihar Jigawa ta bada tabbacin hada kai da duk wata hukuma ko kamfani dake da muradin cigaban yankin. Shugaban karamar hukumar, Dr. Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin lokacin da wakilan rukunin kamfanonin kasar Sin wato China suka ziyarce shi a ofishinsa. Yace karamar hukumar Birnin kudu tana sahun...
Dandalin sada zumunta na TikTok ya sanar da hada gwiwa da kamfanin tallace-tallace ta kafofin zamani na Aleph Holdings da dandalin sayayya kan intanet na kasar kenya wato Wowzi, wanda ake sa ran zai bunkasa tattalin arziki mai nasaba da kirkire-kirkiren jama’a a kasar Kenya. Carl Jordon, shugaban sashen tallace tallace da harkokin cinikayya a...
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa rahotanin da ya samu game kyawawan dabi’u da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje suke nunawa a kasashen da suke, yana mai cewa hakan zai zaburar da matasa kan dabi’un da ke kara martabar kasa. Shugaban ya yabawa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin da ya karbi wasiku...
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kori kwamishinoni guda biyar daga muƙamansu. Wannan ma cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Architect Samuel Jatau, ya fitar da yammacin ranar Alhamis. Ɓarayin dabobbi sun shiga hannu, an ƙwato awaki 85 a Gombe Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai Sanarwar ta bayyana cewa...

Jigilar Fasinjoji Da Jiragen Kasa Masu Zirga Zirga Cikin Biranen Sin Suka Yi Ta Karu Da Kaso 9.5 A 2024
Adadin jigilar fasinjoji da jiragen kasa masu zirga zirga cikin biranen kasar Sin suka yi a shekarar 2024, ya karu da kimanin biliyan 2.8 ko kuma kaso 9.5 a kan na shekarar 2023. A cewar ma’aikatar kula da sufuri ta kasar, a baran, jimilar jigilar fasinjoji da jiragen suka yi ya kai biliyan 32.24. Zuwa...
Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu

JMI Ta Cika Shekaru 46 Cib Da Nasarrar Juyin Juya Halin Mususlunci A Kasar, Wani Irin Ci gaba Ne Ta Samu A Cikin Wannan Lokacin
A ranar 11 Ga Watan Fabarainu na wannan shekarar ne JMI take cika shekaru 46 cib da samun nasara, da kuma kafa JM a Iran, wadanne nasarori ne kasar ta samu a cikin wannan lokaci?. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kadan daga cikin nasarorin da kasar ta samu daga ciki. 01-Tsawon...
Hukumar Kula da Hanyoyi da Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA), ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran wasu motocin aiki guda biyar. Haka kuma, hukumar ta kashe Naira miliyan 250 domin sayen sabbin motoci domin amfanin da su. Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani...

Kafafen Yasa Labaran Sweden Sun Tabbatar Da Mutuwar Selwan Momika Wanda ya Kona Alkuranai A Kasar A shekarum Baya
Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta...
Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun...
Shugabna Pual Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa ba zai dakatar da goyon bayana da yake bawa kungiyar yan tawaye ta M23 ba, wadanda a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kwace wurare da dama a arewacin Kivu na kasar DMC daga cikin har da birnin Goma babban birnin lardin. Shafin yanar gizo...