2025-02-21@14:57:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 923

«Gwamna Zulum»:

    Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin...
    Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da...
    Kungiyar kwallon kafa ta Real Balladolid ta zargi Manchester City da karfafa gwiwa ga daya daga cikin ‘yan wasanta, Juma Bah domin ya soke yarjejeniyarsa ya koma buga Premier League da buga wasa. Dan wasan mai tsaron baya, ya sanar da kungiyar ta Sifaniya ranar Talata cewar yana so ya katse yarjejeniyarsa, saboda ya koma...
    Jami’ar Michigan ta Amurka ta dakatar da karatun wasu daliban jami’ar saboda rawar da suka taka, a zanga-zangar goyon bayan Gaza a yakin watanni 15 da suka yi da HKI. Kamfanin dillancin labaranSahab ya nakalto kamfanin dillancin labaran Mehr yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, hukumar Jami’ar Michigan ta kori wasu daliban daga...
    Ƙungiyoyin alarammomi da matasa daga jihohin Arewa sun nuna goyon bayansu a kan taron karatun Kur’ani na ƙasa da ake shirya gudanarwa a Abuja a ranar 22 ga watan Fabrairu. Shugaban ƙungiyoyin, Kwamred Murtala Mohammed Garba, wanda aka fi sani da Gamji, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya...
    11-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin...
    A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa. Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya...
    Iyalai da dama da ’yan fashin daji suka raba da matsugunansu a wasu jihohin Arewa-maso-Yamma da Arewa-maso-Gabas sannan daga bisani kuma aka kore su daga birnin Abuja, inda suka samu mafaka a halin yanzu, suna wani hali a wasu sassan Jihar Nasarawa da ke makwaftaka da Babban Birnin Tarayya Abuja. Binciken da wakilinmu ya yi...
    Gwamnatin tarayya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa wajen bunkasa kiwon dabbobi domin dorewar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan. Ministan kula da ci gaban harkokin dabbobi Alhaji Idi Mukhtar Maiha ya bayyana haka, a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi a...
    Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa...
    Har ila yau ya ce, idan aka yi maganar mukaman da gwamnatin tarayya da ta jihohi suka bai wa wasu daga cikinmu, ba yana nufin cewa; an taimaki masana’antar ba ne, domin kuwa; mafi yawancin wadanda suka samu wadannan mukamai, babu wani ci gaba ko hobbasa da suka yi wajen ciyar da Masana’antar Kannywood gaba....
    Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance...
    An miƙa wa Majalisar Dokokin Kano ƙorafi kan abin da aka bayyana a matsayin ƙarin wa’adin aiki na wasu manyan jami’an gwamnati ba bisa ƙa’ida ba. A ƙunshin ƙorafin an yi zargin cewa ana ƙara wa manyan jami’an wa’adin aiki ta hanyar amfani da Dokar Zartarwa Ta 1 ta 2025, wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kaddamar da sabbin na’urori masu linzami da na tsaro Babban sakataren rundunar da ke sa ido kan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya sanar da kaddamar da wasu sabbin na’urori masu linzami da na tsaro a cikin tsarin baje kolin “Malik Ashtar”, wanda za a...
      Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta biya fiye da Mahajjata dubu uku da suka kammala aikin Hajjin shekarar 2023 kudaden da Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta mayar masu.   Mai Magana da Manema Labarai na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, shine ya bayyana hakan sannan ya kara da cewa an turawa kowane...
    Aƙalla matasa 150 masu kirkire-kirkire daga yankin Arewa sun hallara a Kano don halartar “Innovate North” Business Development and Innovation Hackathon, wani shiri da ke da nufin ƙarfafa harkokin kasuwanci da sauya fasalin dijital. Yayin da take jawabi a taron, Maryam Lawan Gwadabe, wacce ta shirya gasar kuma ita ce wanda ta kafa Blue Sapphire...
    Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa; Abubuwan da suka nuna irin girman dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanya makiya takaici Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Baqiri ya jaddada cewa bayyanar irin girman da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suke da shi ya sanya...
    Kasar Kenya na amfani da damar ci gaban fasahar kasar Sin don kara dogaro da samar da wutar lantarki a kasar. Darektan ma’aikatar kula da harkokin rarraba wutar lantarki ta kasar Joseph Siror ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa,...
    ‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa...
    Sojojin Sudan sun kwace iko da wani birni da ke arewacin Kordofan daga hannun ‘yan tawayen kasar na Rapid Support Forces Rundunar sojin Sudan ta sanar da cewa ta sake kwace iko da birnin Umm Rawaba, birni na biyu mafi girma a arewacin jihar Kordofan da ke kudancin kasar daga hannun dakarun kai daukin gaggawa...
    Hakanan ma akwai su yi aiki duk irin halin da suka samu kansu, su san yadda lamurran ilimi za su tafi kamar yadda ya dace.Ko mai dai menene hanyoyin ko wuraren da jami’an ilimi za su iya yin aiki suna da yawa da kuma yadda za su samu ci gaba ta kowane hali suka tsinci...
      Ga kuma yadda za ku hada: Da farko za ku wanke tsamiya sai ku dafa ta ku tace ta, sannan ku wanke danyar citta, sai ku nikata ku samu roba mai kyau ku tace tsamiyar tare da cittar ku sanya suga da filebo sai ku juya sosai ku sanya a firij ko ku sanya...
    A jiya Jamu’a, wakilin CMG ya samu labari daga ofishi mai kula da aikin ceton mutane daga bala’in girgizar kasa da ya abku a gundumar Tingri karkashin birnin Shigatse na kasar Sin cewa, yanzu haka, an kafa gidajen wucin gadi 7733, da tantuna 9941, tare da tsugunar da mutane 47787 da bala’in girgizar kasa ya...
    Jam’iyyar APC a Jihar Osun, ta kori Tsohon Gwamnan Jihar kuma Tsohon Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola, bisa zargin cin amanar jam’iyyar. Wannan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da shugabannin jam’iyyar na Ƙaramar Hukumar Ilesa ta Gabas suka gabatar. Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok bayan Hisbah ta daina kamensu Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar...
    Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki. Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan...
    Tun bayan ’yan kwanaki da Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar cewa Hukumar ta daina kamen masu aikatawa da yada baɗala, sai dai ta yi musu wa’azi, aka fara ganin yaɗuwar bidiyoyin da suka saɓa da al’ada da Addinin Musulunci suna ɓulla kafofin sada zumunta. Daga watan Disamban 2024...
    Kwamitin zai bincike kamar yadda aka bada sharuddan da za ta ayi amfani da su lokacin bincike, domin ta gano ta yaya lamarin maganganun da ake yadawa,da ake zargin abubuwan da suke da alaka da badana wanda mataimakin shugaban jami’ar ne aka ce akwai kokarin da ya yi domin ya sayi mukaman Bursar da rajistara,...
    A wannan hirar, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatuil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da cece-ku-ce kan ɗaukar nauyin wani taron Al-Ƙur’ani da aka shirya. Da yake magana jim kaɗan bayan wata lacca ta musamman a sakatariyar JIBWIS ta ƙasa da ke Abuja a wannan makon, shugaban ya bugi...
      Kayan hadi: ”Yayan Hulba (gongoni 2, Aya (gongoni 3), Ridi (gongoni 1)   Ga kuma Yadda za ku hada: Wadannan kayan hadin ku soya su duka amma sama-sama sai ku bar su su huce sanna ku daka ko ku nika ku tankade.   Yadda ake amfani da ita: Za ku dinga diban cokali 2...
    Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya...
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana bayyana matakan da sabuwar gwamnatin Amurka zata dauka idan har tana son sake samun yardar samun yardar kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-jazeera ta kasar Qatar a birnin...
    Shugaban kasar Iran Ma’suod Pezeskiyan tare da majalisar ministocinsa sun sabonda bai’a da jagoran juyin juya halin musulunci, wanda ya kai kasar ga samun nasarar tumbuke gwamnatin sarki Muhamma Reza Sha sannan ya sannan ya kaisu ga nasarar kafa JM a Iran,  shekaru 46 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya...
    Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na...
    Shi ma da yake jawabi, shugaban kungiyar masu tuka ‘yar kurkurar, Jamilu Isyaku ya bayyana jin dadinsa ga Gwamna Radda bisa amsa kiran da suka yi masa na biya masu bukatunsu kan sama masu da keke napep mai amfani da lantarki da kuma ba da tabbacin yin amfani da su yadda ya kamata.
    Jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aikin soje na zamani duk da cewa wasu daga cikin jiragen tsoffin kira ne. Kamfanin dillancin labaran Sahaab na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na JMI yana fadara haka. Ya kuma kara da cewa sojojin saman kasar sun samarda wasu sabbin kayakin aikin Soje wadanda...
    “Sauran abubuwan baje kolin da aka kwato daga hannun mutanen biyu sun hada da: bindigogi guda uku da aka kera a cikin gida; bindiga guda da aka yi a gida guda biyu; bindigar zamani guda daya; bindigar gida guda daya; cartridges guda uku da 9mm mara komai da gatari mai kan karfe. “Wani farmakin da...
    Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan...
    Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da...
    Shugaban ya kara da cewa, a shekarar farko ne ake fara girbe reshensa, sannan kuma bishiyar tasa na daukar tsawon shekara 50 ana amfana da ita. “A shekara, sau biyu ake girbe Inibi, sannan idan aka ajiye ganyensa a kan tebur, yana shafe daga kwana 45 zuwa 50 ba tare da ya lalace ba”, in...
    Kafafen watsa labarun Amurka sun sanar da cewa wani karamin jirgin sama ya fadi akan wata cibiyar kasuwancin dake Philadelphia  a jihar Pennsylvania tare da kashe mutane 6 da suke cikinsa. Kafafen watsa labarun na Amurka sun ce ‘yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe gobarar da ta tashi a cikin gidaje da dama a yankin...
    Bayan da su ka kwace iko da birnin Goma dke gabashin kasar DRC, kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta sha alwashin kama hanyar shiga  babban birnin kasar Kinsasha. Wani daga shugabannin kungiyar ta M 23, Corneilla Nangaa ya furta cewa,: manufarmu  ita ce, muna yin yaki ne...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da  duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako...
    Hajjatul-Islam Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi da ya jagoranci Sallar juma’a a Tehran a jiya juma’a ya bayyana Imam Khumaini ( r.a) a mastayin daya daga cikin fitattun mutanen da duniyar musulunci ta samu a wannan zamanin. Hujjatul-Islam Wal Muslimin ya ce, Shakshiyya din Imam Khumaini ta ginu ne akan ilimomi na addini,filiku da...
    A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana alhininta na shahadar babban hafsan mayakan rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas Muhammad Dhaif  tare da wasu abokan aikinsa, tare da bayyana rawar da  suka taka a fagen gwagwarmaya. Kungiyar ta Hizbullaha ta mika sakon ta’aziyya da kuma barka akan shhadar Muhammad Dhaif ga kungiyar...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin...