2025-03-26@12:43:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1255

«Kasuwancin Duniya»:

    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran ce zata yanke shawara a nan gaba kan matsayin kasarta, ba Trump ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yammacin jiya Alhamis ya jaddada cewa: Iran ce take da hakkin yanke shawara kan makomarta ba Trump ba, yana mai jaddada wajabcin sauya ra’ayi domin dakile duk wani takunkumin...
    Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Amurka da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ba su yi nasara a yakin da suka kaddamar kan ‘yan gwagwarmaya a Gaza ba Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Hossein Salami ya jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta samu...
    Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a...
    Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da al’umma ke murnar saukar farashin kayayyakin abinci kamar shinkafa da masara da sauran kayan hatsi. Shi ma farashin fulawa da ake amfani da shi wajen sarrafa burodi, gurasa da sauran maƙulashe ya sauka a kasuwa. Sai dai duk da saukar farashinta, al’ummar na ci...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce zai ci gaba da tallafa wa jihar Jigawa wajen gina tsarin kiwon lafiya na al’umma. Shugaban hukumar UNICEF a Najeriya, Dr. Shyam Sharan-Pathak ya bayyana haka a wajen bikin mika aikin ga gwamnatin jihar Jigawa na tsawon shekaru 3 na GAVI, a hukumance...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da aka gudanar karkashin hadin gwiwarta da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da shirin samar da rigakafin cututtuka a kasashe masu tasowa(GAVI) a cikin shekaru uku da suka gabata. Haɗin gwiwar wanda aka fara shi da...
    Gwamnatin jihar Kano ta dauki wani gagarumin mataki na bunkasa ilimin addinin musulunci a jihar ta hanyar hada hannu da kungiyar Agaji ta Musulunci da ke Birtaniya,  wato Muslim Charity For United Kingdom a turance. Wannan haɗin gwiwar na nufin tallafa wa makarantun Islamiyya da kayayyakin koyon  ilimi na zamani, da sauransu. A cewar daraktan...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Najeriya. Shugaban kasar a bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin, tarihin rayuwar Janar Babangida da gwagwarmayarsa yayin aiki, wanda aka gudanar a Abuja.   A yayin da...
    Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin. Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin...
    Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Uganda Jeje Odongo a cibiyar MDD da ke birnin New York. Yayin ganawar a ranar 18 ga wata, Wang Yi ya bayyana cewa, ana bukatar ra’ayin Afirka yayin da ake yada ra’ayin bangarori daban daban da kuma daidaita harkokin duniya baki daya. Ya...
    Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu. Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan...
    Jam’iyyar adawa ta NNPP ta rasa ɗaya daga cikin mambobinta a Majalisar Wakilai zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gwaram ta Jihar Jigawa, Yusuf Shitu Galambi. Shi ne ɗan jam’iyyar NNPP na farko da ya sauya sheƙa ya koma APC. Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida Hisbah ta...
    Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma. Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi. ’Yan bindiga...
    ’Yan bindiga sun kashe wasu ’yan kasuwar Gwari 12, tare da sace wasu yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Zariya bayan cin kasuwa. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tafoki da ke Jihar Katsina, bayan ’yan bindigar sun buɗe wa motarsu wuta. An haramta wa manyan tireloli aiki a Najeriya Jami’an tsaron al’umma 6...
    A wani ɓangare, an ware Naira biliyan 5.22 don gina gidaje 1,000 masu ɗaki biyu-biyu domin raba su kyauta ga waɗanda ambaliya ta shafa. Haka nan, an amince da Naira biliyan 9.76 don gina tituna bakwai da gyaran wasu a karkara
    Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa. Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka...
    Arziƙin hamshakin attajirin nan ɗan jahar Kano Alhaji Aliko Dangote ya ninka na bara inda ya ƙaru zuwa dala biliyan 23.9, wanda hakan yasa ya cigaba da kasancewa mutumin da yafi kowa dukiya a nahiyar Afrika kuma ya koma matsayi na 86 a jadawalin masu kudin Duniya kamar yadda mujallar Forbes mai ƙididdiga akan masu...
    Mutum shida daga cikin Jami’an Tsaron Al’umma na Jihar Sakkwato sun kwanta dama bayan wata musayar wuta da ’yan bindiga a Kamarar Hukumar Sabon Birni. Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka kai ɗauki ga al’umma da ’yan bindiga suka kai wa hari. A hanyarsu ne...
    Mutum shida daga cikin Jami’an Tsaron Al’umma na Jihar Sakkwato sun kwanta dama bayan wata musayar wuta da ’yan bindiga a Kamarar Hukumar Sabon Birni. Wasu majiyoyi sun bayyana cewa jami’an tsaron sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka kai ɗauki ga al’umma da ’yan bindiga suka kai wa hari. A hanyarsu ne...
    Kungiya mai gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamasa ta bayyana cewa tana iya sakin fursinoni yahudawa wadanda suke hannunta gaba daya a lokaci guda a marhala ta biyu ta musayar fursinoni tsakaninta da tare da sharadin ta cika al-kawulan da ta nauyi  alhakin aiwatar da shi a wannan karon. Daga cikin har da maida tsagaita wutan na...
    Dubban Falasdinawa ne suka kauracewa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Tun ranar 21 ga watan Jeneru na wannan shekara ta 2025, wato kwanaki biyu kacal da tsaida wuta a Gaza, sojojin HKI suka fadawa sansanin yan gudun hijira na Jenen inda suka fara fafatawa da dakarun Falasdinawa a yankin. Da nufin korarsu.  ...
    An yi zaman farko na tattaunawar sulhu a tsakanin kasashen Habasha da Somaliya a birnin Ankara wanda kasar Turkiya take a matsayin mai shiga tsakani. Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan fidan ya yi ganawa da  daban-daban da ministocin harkokin wajen kasashen na Habasha da Somaliya. Bayan wannan ganawar minstan harkokin wajen na Turkiya ya...
    Kungiyoyin Falasdina mabanbanta sun yi kira da a gudanar da taron musamman na al’ummar Falasdinu domin a tattauna hanyoyin da za a dakile batun tilastawa mutanen Gaza yin hijira. Kungiyoyin na falasdinawa sun bayyana hakan ne dai a wani taro da su ka yi a Gaza domin karfafa gwiwar mutanen wannan zirin su ci gaba...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gana da sarkin Katar  a jiya Laraba ya bayyana cewa; Siyasar Iran ta ginu ne akan kyautata alaka da kasashen makwabta, kuma tuni an cimma sabbin matakai a wannan fagen. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma fada wa sarkin na Katar Tamim Bin Hamad...
    Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya. Shugaban na kasar Amurka ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan sanarwar shirin kafa gwamnatin bibiya ko kuma ‘shadow government’ a turance da wata kungiya ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Kano tace za ta yi ne  ne dai al’umma da dama ke ta jefa ayar tambaya kan halascinta. Kungiyar dai ta bayyana cewa za ta kafa wannan...
    Taron dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da majalisar dattawan kasar a ranar Laraba ta gayyaci shugabannin hukumar leken asiri don gudanar da bincike kan zargin da dan majalisar dokokin Amurka, Perry Scott ya yi na cewa, hukumar bayar da tallafi ta kasa da kasa ta Amurka, USAID na tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki...
    Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za ta gudanar da bikin tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara karo na 11 a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu, 2025, a Bauchi, Jihar Bauchi. Taron, wanda aka shirya...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dokta Danjuma Adamu Ismaila a matsayin shugaban kwalejin koyon tukin jiragen sama ta Najeriya (NCAT) da ke Zariya. Sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Dakta Ismaila, kwararre kan harkokin sufurin jiragen sama, da manufofin tattalin arziki, ya...
    Shugaban kasar Iran da Sarkin kasar Qatar sun jaddada muhimmancin hadin gwiwa da taimakekkeniya tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamid Al Thani sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Tehran, inda suka jaddada karfin dangantakar da ke tsakanin kasashen...
    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki shugabancin Ukraine, inda ya bayyana cewar su ne suka haddasa yaƙin da Rasha ke yi da su. Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda ya ce yana mamakin yadda ba a gayyaci ƙasarsa zuwa taron tattaunawar zaman lafiya a...
    Jarin da kasar Sin ke zubawa wajen inganta lafiyar muhalli mai dorewa a duniya ya nuna muhimmiyar rawar da take takawa ta wannan fuskar. A shekarar 2024, kasar ta jagoranci duniya wajen zuba jarin sauya makamashi, inda ta zuba dalar Amurka biliyan 818 a wannan bangare. Wannan jarin ya sanya kasar Sin ta zama cibiyar...
    Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya gargaɗi ƙasashe cewa Najeriya ba za ta yarda da rashin girmamawa daga kowace ƙasa ba. Ya bayyana hakan ne bayan da Ƙasar Kanada ta hana wasu jami’an sojin Najeriya takardae izinin shiga ƙasar, duk da cewa an gayyace su don halartar wasannin Invictus a Vancouver. ’Yan bindiga...
    ’Yan bindiga sun kashe wasu mazauna ƙauyen Gwargwada da ke Ƙaramar Hukumar Kuje a saboda jinkirin biya musu kuɗin fansa. Mutanen da aka kashe, sun haɗa da Mohammed Danladi da Nasiru Yusuf, wanɗanda aka sace su ne a ranar Laraba tare da wani makiyayi da wata mata a mahaɗar Gwombe, a kan hanyar Gwargwada zuwa...
    A cewarsa, amincewar wani gagarumin yunkuri ne na tallafawa dorewar tsafar muhalli a jihar.   Ya yaba da yadda jihar ke ci gaba da kokarin inganta rayuwar ‘yan jiharta da kuma tsaftar muhalli.
    Wani sabon rikici ya sake kunno kai a tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu a Jihar Zamfara. Rigimar wadda ta kunno tsakanin APC da PDP ta samo asali ne tun bayan da wasu matasa suka yi yunƙurin hana wani taro na ɗan Majalisar Wakilai da za a gudanar a garin Maru. Mutum 10 sun rasu, an...
    Aƙalla mutum 11 sun shaƙi iskar ’yanci bayan kuɓuta daga hannun ƙungiyar mayaƙan Boko Haram masu iƙirarin jihadi a Jihar Borno. Waɗanda suka shaƙi iskar ’yancin na daga cikin mutanen da ƙungiyar Boko Haram ta sace a wani wurin kamun kifi a Doron Baga. Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane...
    Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya.  A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi,...
    Ta ce: “Fafutukar sa, hikimar sa mai zurfi, da jajircewar sa wajen cigaban ƙasa sun sa shi ya zama murya mai matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya. Za a yi kewar shawarwarin sa masu amfani da kuma gudunmawar sa ba tare da son rai ba wajen gina ƙasa.”   Idris ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Cif...
    Gwamnatin Amurka ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan yadda gwamnatocin da suka gabata suka riƙa sarrafa kuɗaɗen da aka fitar domin bai wa Nijeriya da wasu ƙasashen tallafi. Hakan dai ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurkan, Donald Trump ya ɗauka a watan Janairu na dakatar da duk wani tallafi da Amurkan ke bayarwa...
    Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun...
    Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa. Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran. Labarin ya nakalto Jagoran...
    Burgediya Janar Amir Ali Hajizadeh babban kwamandan sojojin sararin samaniya ya bada labarin cewa sojojinsa, zasu kai farmakin ‘Wa’adusadik na 3 nan ba da dadewa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Ali Hajizadeh yana fadar haka a jiya Talata, a hirar da ta hadashi da wata kafar yada labarai labaran kasar....
    Gwamnatin Jumhuriyar Nijer daga jiya Talata ta fara aikin hana yan Najeriya dauke da Passport na kungiyar ECOWAS shiga kasar. Kafin haka dai mutane daga kasashen ECOWAS suna shiga kasashen kungiyar ba tare da bukatar visar shiga ko wace kasa daga cikin kasashe kungiyar ba. Amma bayan da kasashe 3 Nijer, Burkina Faso da kuma...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma...
    Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar.     Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a...
    Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaron al’umma ta Jihar Kano mai suna ‘Kano State Security Neighborhood Watch.’ Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne tare da wasu ƙarin dokokin guda biyu, waɗanda suka haɗa da dokar gyara hukumar sufuri ta jihar da kuma wadda ta kafa cibiyar yaƙi da...