2025-04-03@10:21:09 GMT
إجمالي نتائج البحث: 312
«Kyautatawa»:
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi ƙarar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio a Majalisar Ɗinkin Duniya. Ta gabatar da kokenta a zaman taron mata da aka gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a birnin New York, inda ta nemi ƙungiyoyin kare dimokuraɗiyya na duniya su bi...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gamayyar ƙungiyoyin manyan makarantu na gwamnatin Jihar Adamawa sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a yau Talata, 11 ga watan Maris. Ma’aikatan manyan makarantun da suka haɗa da masu karantarwa da waɗanda ba sa karantarwa sun shiga yajin aiki ne bayan wa’adin yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ya ƙare a jiya...
Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a...
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin. Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji...
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa...
Da yake jawabi a wurin taron, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, kwamandan OPHK, ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma dawo da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Shuaibu ya jaddada aniyar rundunar na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta...

Iran Ta Ce Shirinta Na Makamashin Nukliya Na Zaman Lafiya Ne, Kuma Ba Zata Tattauna Da Amurka Karkashin Barazana Ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba. Kamfanin dillancin labaran IP na...
’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku bisa zargin lalatawa da kuma satar wayoyin lantarki a ƙauyen Bororo da ke Ƙaramar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa. An cafke ababen zargin ne da wayoyin lantarkin yayin wani sintiri da jami’an ’yan sanda suka gudanar a ranar 9 ga wannan wata na Maris. Abin da ya sa...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa, sun fara horas da mata 600 kan inganta muhalli ta hanyar bola jari. Shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Jigawa JISEPA, Alhaji Adamu Sabo ya bayyana haka a wajen taron tunawa da ranar mata ta duniya da kuma...
Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da...
Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana. Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da...
Abin da ya sa wannan tsari ya yi daban shi ne ba wai domin irin tsarin gine-gine da za a yi ba; akwai allunan batun siyasa da kuma ‘yancin Falasdinawa. A jawabinsa a wajen taron, shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira da a samar da tsare-tsare guda biyu da za su tafi lokaci...
Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin. Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi...
A yammacin ranar Alhamis da ta gabata ce sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka aukawa Falasdinawa masu ibada bayan sun gudanar da sallar tarawihi a masallacin Al-aqsa, inda suka kore su daga masallacin da karfi, tare da hana su yin I’itikafi a cikin masallacin. Da yake tsokaci a cibiyar yada labaran Falasdinu, Ziad Abhais, mai bincike...
Kasashen Jamus, Faransa, Birtaniya da Italiya “sun yi maraba” da shirin kasashen Larabawa na sake gina Gaza. A cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da ministocin harkokin wajen kasashen suka fitar a birnin Berlin, sun ce shirin idan an aiwatar da shi zai bada damar gaggauta warware mummunan halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza....
A dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar mata ta duniya kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadi da HKI saboda kissan mata kimani 12.000 a gaza a cikin yakin tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar Hamas na fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da...
Majaliar Dattawa ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar ba. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar. Kotu ta saki...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a yau Juma’a yahudawa 800 sun kutsa cikin iyakar Lebanon, zuwa kabarin wani malamin yahudawa Rabbi Ashi. Sun kuwa isa wurin ne a karkashin rakiyar sojojin mamaya. Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce, kabarin malamin yahudawan dai yana a cikin iyakar Lebanon ne dake kallon matsugunin ‘yan share wuri...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa; Tattaunawa da Amurka kaskanci ne, ga shi kuwa al’ummar Iran tana da tunani ne irin na Ashura, ba ta karbar kaskanci. Limamin na Tehran ya yi ishara da yadda duniya ta ga yadda Donald Trump ya wulakanta shugaban kasar Ukiraniya, don haka ya kamata...
An Bukaci ‘yan fansho suyi gangami ganin jinkirin da ake samu wajen biyan su kudaden su. An shawarci kungiyar ’yan fansho ta tarayya da ta zaburar da mambobinta kan jinkirin rage basussukan da gwamnatin tarayya ta amince da su. Jami’in hulda da jama’a na kungiyar ’yan fansho na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Alhaji Muhammad Mamman,...
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana dakatar da ita da Majalisar Dattawa ta yi, a matsayin rashin adalci. An dakatar da ita ne biyo bayan ta ƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan tsarin zama a zauren majalisa a ranar 20 ga watan Fabrairu. Doyin Okupe:...
Kakakin babban sakataren MDD ya bayyana damuwarsa kan abubuwan da suke faruwa a yankin yamma da kogin Jordan, inda sojojin HKI suke ci gaba da rusa gidaje, da bata yanyuyi da kuma dukan Faladinawa da suka hadu da su a yankin arewacin yamma da kogin na Jordan. Tashar talabijin ta Presstva anan Tehran ya nakalto...
“Ina son in nuna jin daɗina ga Babban Hafsan Sojin Sama, wanda kafin ziyarar tasa a yau, ya aiko da wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan hafsoshi daga hedikwatar domin jajanta mana da al’ummar Zamfara. Ya aika da tawaga zuwa Zamfara a lokuta biyu daban-daban. “Ina son nanata cewa a...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa yadda ta nuna damuwarta kan harkokin tsaro a jihar. Mataimakin Sufeta na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya, AIG Ahmed Ammani, ya bayyana haka a lokacin da ya kai wa Gwamna Umar Namadi ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse babban...
Majalisar Dokokin ECOWAS, ta kafa wani kwamiti na musamman domin tattaunawa da shugabannin kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar da suka fice daga kungiyar, tare da kokarin magance matsalolin siyasa a yankin Yammacin Afirka. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, wanda mamba ne a Majalisar ECOWAS, ya tabbatar da haka a wata tattaunawa...
Shugaban Amurka Donald Trump ya shaidawa kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas cewa zai ba da izinin sake kai sabbin hare-hare a zirin Gaza muddin kungiyar bat a saki sauran Isra’ilawan da ta yi garkuwa da sub a. Barazanar ta Trump ta zo ne a wata tattaunawa kai tsaye a Doha tsakanin wakilinsa kan al’amuran da...
Sakatare-janar na kungiyar malaman musulmi ta duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da su hada kai da al’ummarsu wajen goyon bayan Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi, ya yi kakkausar suka kan ci gaba da goyon bayan da Amurka ke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai, ya ce, Iran tana kokarin ganin cewa an gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi domin tattauna batun barazanar tilasta mutanen Gaza yin hijira. Haka nan kuma ya ce, wannan tunanin na korar falasdinawa daga Gaza, ba wani abu ba ne sai cigaba da kisan kiyashi, ta hanyar amfani...
Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda. Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a...
Gwamnan ya jaddada cewa yana da burin ganin an kammala waɗannan ayyuka domin amfanin al’umma, musamman hanyoyi da filin jirgin sama da ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan...
“A kan batun kafafen yada labarai, muna son mu yi taka-tsan-tsan don kada mu wuce gona da iri. Al’amari ne da ke cikin Majalisar Dattawa, kuma yin hakan ta hanyar kafafen yada labarai na iya daukar mana hankali. Zauren kwamitin zai iya ɗaukar mutane da yawa, kwamitin yana da mambobi kusan 23 ko 24. Muna...
Fa’iza Muhammad wacce aka fi sani da Fa’iza Badawa, daya ce daga cikin mawakan Kannwood. Ita ta yi wakar fim din Oga Abuja, daya daga cikin finafinan suka yi tashe, ya kuma fito da basirar mawakiyar. Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Mai barkwanci ya yi kuskuren liƙe bakinsa da sufa-gilu Kasancewar ta yi aure, mutane...
Tun ranar 4 ga watan nan da muke ciki, Amurka ta fake da batun maganin Fentanyl, da nufin kakabawa Sin karin harajin kwastam na kashi 10% kan kayayyakin kirar kasar Sin da za ta shigar da su kasar Amurka. Game da wannan mummunan mataki mai sabawa ka’idar cinikin duniya da karya lagon tsarin kasuwanci tsakanin...
Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda za a sake gina yankin na Gaza. Bayanin bayan taron kungiyar ya kunshi cewa, shirin sake gina Gaza, yana nufin sake hade yankin da yammacin kogin Jordan a karkashin iko...
Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza. Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu...
A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda a yayin taron, wani dan jarida ya gabatar da tambaya game da matakin Amurka, na sake kakabawa Sin karin harajin kashi 10 cikin dari, bisa fakewa da batun sinadarin kashe radadi na Fentanyl. Game...
A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce: ya kamata...

Hamas Ta Ce Yarjeniyar Tsagaita Wuta Ne Kadai Za Ta Kubutar Da Fursinonin Yahudawa Daga Hannun Kungiyar
Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya...
Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar...

Hamas Ta Bukaci Falasdinawa A Birnin Qudus Su Sabawa Dokar Takaita Yawan Masu Shiga Masallacin Al-Aksa A Kudus
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kashe akalla yara 16 tun farkon wannan shekara ta 2025 a yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ayed Abu Eqtaish, daraktan kungiyar ‘ The Defense for Children International’ a yankin yamma...
Kungiyar Hamas ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a yankin yamma da Kogin Jordan tana rusa gidajen Falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nur- Ashamsh, a ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Nihad Ashawish shugaban kwamitin mai kula da sansanin yan gudun hijirar...
Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin...
Fira ministan hakar Habasha Abiy Ahmed ya sami kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mamhud a birnin Mogadishu na Habasa a ranar Alhamis da ya kai ziyara domin bunkasa alaka a tsakainin kasashen biyu. Sabani a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna ya kunno kai ne a shekarar da ta gabata, bayan...
Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF da kuma bankin duniya, manya-manyan cibiyoyin kudade a duniya sun ce ba zasu bada kudade don sake gina kasar Lebanon ba, sai sun cika wasu sharudda zuwa wani lokaci. Kuma sune samar da huldar jakadanci da HKI da kuma kwance damarar kungiyar Hizbullah. Jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon ta...

Kasashen Afrika Ta Kudu, Malasiya Da Colombia Zasu Hana Jiragen Ruwa Dauke Da Makamai Tsayawa A Tashoshin Jiragen Ruwansu
Shuwagabannin Afrika ta Kudu, Malasiya da kuma Colombia sun jaddada matsayinsu nah ana jiragen ruwa dauke da makamai zuwa HKI tsayawa a tashishin jiragen Ruwan kasashen su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, Firaiministan kasar Malasiya Anwar Ibrahim da Shugaban kasar Colmbia Gustavo Petro...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kamfanin Microsoft ya kori ma’aikata biyar bayan da suka nuna rashin amincewa da kwangilar da kamfanin ya kulla da sojojin Isra’ila. A rahoton cibiyar yada labarai ta Falasdinu, ma’aikatan sun gudanar da zanga-zangar ne a hedkwatar Microsoft da ke Redmond a birnin Washington, sanye da riguna masu dauke da taken nuna adawa da amfani da...