2025-02-21@14:53:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 242

«Kaciyar Mata»:

    Hukumomi a birnin Quetta na Ƙasar Pakistan, sun kama wani mutum mai shekaru 50, kan zargin kashe ’yarsa mai shekaru 15 a duniya, saboda ta ƙi daina ɗora bidiyonta a kafar TikTok. Rahoton ’yan sanda ya nuna cewar, mutumin ya dawo da iyalinsa daga Amurka zuwa Pakistan kwanan nan kafin aikata kisan. Hisbah ta kama...
    Isra’ila ta dakatar da sakin fursunonin Palasɗinawa ba zato ba tsammani yayin da ake ci gaba da musayar fursunoni da waɗanda aka kama ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, a cewar rahoton Army Radio. Hukumomi ba su bayyana dalilin dakatarwar ba, kuma babu tabbas kan lokacin da za a ci gaba da tsarin. Wani Ɗan...
    Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta kira zanga-zangar adawa da ƙarin data da kiran waya a Najeriya. NLC ta umarci rassanta na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya da su shirya domin fara zanga-zangar daga ranar Takara 4 ga watan Fabrairu mai kamawa. Ta bayyana cewa manufar zanga-zangar ita ce ganin an janye karin kashi...
    Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba. Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi. Ministan ya ce Iran ta riga...
    Kungiyar fursunonin Falasdinu ta ce za a sako wasu karin Falasdinawa 110 daga gidajen yarin Isra’ila a yau Alhamis a mataki na uku na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas. Ana sa ran galibin Falasdinawan da aka ‘yantar za su isa yankin Radana na Ramallah da ke yammacin gabar kogin...
    Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU) ta bayyana cewa jami’o’in gwamnati da dama a Najeriya sun shafe sama da watanni uku ba tare da wutar lantarki ba da za su gudanar bincike ko darussa ba. Kungiyar ta kuma yi barazanar ɗaukar tsattsauran mataki kan gwamnatocin jihohi da kamfanoni da suka ki fara biyan sabon mafi ƙarancin...
    Kazalika gwamnan ya amince da naɗa Sunday Alex daga Ƙaramar Hukumar Bassa, da Joyce Ramnap daga Langtang ta Kudu, da Sylvanus Dongtoe daga Shendam, da kuma Nicholas Baamlong daga Qua’an Pam, sai Cornelius Doeyok daga Ƙaramar Hukumar Qua’an domin maye gurbin waɗanda ya sallama.   Idan ba a manta ba a baya ma gwamnan ya...
    Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau,...
    Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake  gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar. A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a...
    Bikin bazara shi ne biki mafi dadewa da muhimmanci a bukukuwan gargajiya na Sin. Kuma bikin na ci gaba da kara bazuwa da samun karbuwa a fadin duniya. A kwanakin baya-bayan nan, kasashe da hukumomin kasa da kasa da dama sun gudanar da shirye-shirye da nune-nunen dake da alaka da bikin bazara, kuma jama’a a...
    Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar,...
    Wata matashiya mai shekaru 20 ta shiga hannun ‘yan sanda bisa zarginta da ƙona matar ɗan uwanta da ke naƙuda da tafasasshen ruwan zafi. A tattaunawarta da Aminiya, matashiyar ta ce ɓacin rai ne ya kai ta ga ƙone matar lokacin da musu ya kaure a tsakaninsu. Jirgin Max Air ɗauke da fasinjoji 59 ya...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Duk wani hari da aka kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai fuskanci mayar da martani cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Harin da Amurka da yahudawan sahayoniyya suke kai wa kan cibiyoyin nukiliyan kasashe, nau’in hauka ne kuma zai jefa yankin cikin bala’i....
    Kungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta tabbatar da ficewar ƙasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar a hukumance. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ECOWAS ɗin ta fitar, tana mai cewa har yanzu ƙofa a buɗe take ga waɗannan ƙasashe, a duk lokacin da suka sauya shawarar sake komawa....
    Hadakar Kasashen Sahel na AES, sun yi ban kwana da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO a hukumance bayan shekaru 50 na kasancewa mamba a cikinta. Ya zuwa wannan Laraba, 29 ga Janairu, bangarorin biyu sun raba gari duk da cwa kungiyar ta ECOWAS ta baiwa kasashen wa’adin watannin shida...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a...
    Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta yi tsokaci a karon farko kan  labarin da ke yawo cewa sojojinta sun kama ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji. Rundunar tsaron ta sanar da gaskiyar lamarin ne bayan raɗe-raɗin kama Bello Turji ya karaɗe kafofin sada zumunta. Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya sanar cewa babu...
    Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta yi tsokaci a karon farko kan  labarin da ke yawo cewa sojojinta sun kama ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji. Rundunar tsaron ta sanar da gaskiyar lamarin ne bayan raɗe-raɗin kama Bello Turji ya karaɗe kafofin sada zumunta. Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya sanar cewa babu...
    “Ƙungiyar Al-Hilal ta gode wa Neymar bisa gudunmuwar da ya bayar, kuma tana masa fatan alheri a nan gaba,” in ji ƙungiyar. Wannan matakin ya zo ne yayin da ya rage wata bakwai kafin ƙarshen kwantaragin Neymar, wanda ya kai shekara biyu da ƙungiyar. A Al-Hilal, ana biyan Neymar Yuro miliyan 150 a shekara. Lokacin...
    Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na...
    Ana ci gaba da fada mai tsanani a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo tsakanin sojojin gwamnati da kuma mayakan kungiyar M 23 da suke samun goyon bayan kasar  Rwanda. A yau Litinin wannan kungiyar ta sanar da cewa ta kama garin Goma da shi ne babban birnin yankin gabashin kasar ta DRC. Wannan sanarwar dai ta...
    A kalla sojojin Najeriya 20 ne su ka kwanta dama daga cikinsu har da kwamanda a wani hari da ake dangantawa kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP. ‘Yan ta’addar sun kai harin ne dai a  ranar Juma’ar da ta gabata a kan sansanin bataliya ta 146 dake Malam-Fatori a akan iyakar Najeriya da Nijar a jihar...
    An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko. An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025. Shi ma firaministan kasar Labanon Najib...
    Shugaban kasar Kenya William Ruto a wata sanarwa da ya fitar ya sanar da cewa, zai gudanar da wani babban taro na musamman na kungiyar kasashen gabashin Afirka EAC a cikin sa’o’i 48 masu zuwa tare da halartar shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi da shugaban Rwanda Paul Kagame. Taron dai na zuwa ne a daidai...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa: A shirye suke su tunkari duk wani harin Amurka kuma ya gargadin sojojin haya Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya tabbatar da cewa: Amurka ta yi amfani da dukkan karfinta wajen tallafawa haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma kokarin murkushe al’ummar Falasdinu, yana mai jaddada...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Tun a shekara ta 2000 al’ummar Lebanon suka tabbatar da cewa su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta jaddada cewa: Daidaiton sojoji da al’umma da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke kare...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ci-gaban zamani ya zo da sauye-sauye da dama a fannonin rayuwa daban-daban ciki har da kasuwanci. A yanzu hanyar sadarwa ta zamani, ko intanet, tana taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa da ɓangarori da dama. Tuni ’yan Najeriya da dama suka yi balaguro suka...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana damuwarta kan ambaliyar rowa a gonakin shinkafa da dama a Shonga, da ke karamar hukumar Edu ta jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Rafiu Ajakaye ya fitar,  ya ce  Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya  kafa kwamitin da zai binciki musabbabin ambaliyar. A cewarsa ana sa ran kwamitin...
    Harkar Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa Da Tawagar Sin A MDD Ta Shirya Ta Nuna Al’adun Gargajiya
    Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar UYemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi, ya yabawa mutanen kasar kan jajircewarsu wajen yakar makiya Amurka da HKI da kuma saudiya, har zuwa nasarar da suka samu a kansu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Al-huthi yana fadar haka a yau Lahadi, a wani jawabin da aka watsa...
    Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya,...
    Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewa watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Gasar Firimiyar Ingila. Hakan ya biyo bayan shan kashin da ƙungiyar ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a karawar mako na 22 na gasar Firimiyar. Hakan ya kai United matsayi na...
    Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF...
    Kungiyar kwamishinonin kudi ta kasa ta jinjinawa kokarin gwamnatin jihar Jigawa na bunkasa Ilmin ya’ya mata. Shugaban kungiyar kuma kwamishinan kudi na jihar Ekiti, Mr Akim Oyebode ya bayyana hakan a lokacin da suka ziyarci Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnati dake Dutse. Mr Akim Oyebode ya ce kungiyar tana alfahari da ayyukan raya...
    Shugaban kotun tafi da gidanka na jihar Taraba, Useni Galadima, ya tasa keyar wasu mutane shida gidan yari bisa samunsa da laifin karya dokar zartarwa mai lamba biyar, 2023, wanda gwamna Agbu Kefas ya bayar.   Wanda ake zargin, Suleiman Musa mai shekaru 30, daga Jos, jihar Filato; Adamu Umar mai shekaru 40 daga Bauchi,...
      Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta samar da matakan dakile yawaitar kauran likitocin daga jihar zuwa wasu kasashe, domin neman ingantacciyar rayuwa.   Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dakta Amina El-Imam ta bayyana haka, a lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin kungiyar likitoci ta kasa, a Ilorin.   A cewarta gwamnatin ta amince da biyan...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan yara miliyan 5.4 ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, inda aka yi hasashen za a samu Karin masu wannan matsala su miliyan daya nan da...
    Majalisar dokokin jihar Jigawa ta jaddada aniyar ta na hada kai da ofishin kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF domin samun nasarar aiwatar da tsare-tsare da za su inganta rayuwar yara da marasa galihu a jihar.   Mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Sani Isyaku Abubakar, ya bada wannan tabbacin lokacin da ya karbi...
    Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69...