2025-04-03@20:41:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 483
«xYan Najeriya Mazauna kasashen waje»:
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya gana da masu ruwa da tsaki a harkokin sufuri domin tattauna yadda ake ci gaba da aiwatar da aikin inshorar motoci na wasu motocin da ke bin hanyoyin jihar Kano. Taron wanda ya samu halartar shuwagabannin kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW), kungiyar masu...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsakanin Hausawa akan yi wa jaririya wani nau’i na kaciyar mata, wanda ake kira yankan angurya, kwana bakwai da haihuwarta. Ko mene ne alfanu ko illar wannan al’ada ga ’ya’ya mata? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba DAGA LARABA: Yadda...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya nada Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Marigayi Sayyid Hassan Nasrullahi tsohon babban sakataren kungiyar...

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Amincewa Da Tsarin Bada Tallafi A Mazabu
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewarsa ga manufar majalisar, ta bullo da tsarin bada tallafin sana’oi na mazabu ba tare da jinkiri ba. Shugaban Majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da rabon tallafi wanda wakilin mazabar Kanya a majalisar dokokin jihar,Alhaji Ibrahim Hashim...
Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar mafarauta sun kashe wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a Dajin-madan, da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi. Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a safiyar ranar Laraba, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce an kashe ‘yan bindigar ne ta...
Kasar Afirka Ta Kudu ta ga yadda Palasdinawa suka jajirce wajen kare kansu daga HKI ne, ya sa ta gurfanar da HKI a gaban kutun ICC don kawo karshen kissan kiyashin da yahudawan suke masu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kasar Afirka ta gudu dai tana dade tana goyon...
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kebbi, ta kama wasu bakin haure 165 tare da mika su ga hukumar kula da shige da fice ta kasa shiyar jihar domin gudanar da bincike. A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar ya fitar kuma ya mikawa gidan rediyon Najeriya a jihar Kebbi,...
Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce...
Ministan ya kara da cewa, za a kaddamar da kashin farko na gyaran madatsar ruwan a tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2025. Ya kuma kara jaddada muhimmancin wannan aiki na tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2025 ba.
Haruna, mazaunin Unguwar Kanawa Dutse Abba, an rahoto cewa, ya jagoranci ‘yan bindiga uku – Shago Yaro, Tanimu Ayuba, da kuma Lamido Dantajiri zuwa gidan dansa, Alhaji Anas da misalin karfe 1 na dare, inda suka tarar ba ya gida, amma suka yi awon gaba da matansa biyu, ‘ya’yansa uku, kaninsa, da matar kaninsa. ...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, an kashe sojoji 2 a yankin kusa da Tubas dake Arewacin yammacin kogin Jordan. Kafafen watsa labarun sun kuma ce, maharin ya isa wani shinge na soja dake kusa da Tayasir, ya kuma boye a cikin hasumiyar da masu tsaro ke zama a ciki, sannan ya bude wa...

Jeremy Corbyn Ya Bukaci Ganin An Hukunta Isra’ila Da Masu Ba Ta Makamai Akan Kisan Kiyashin Falasdinawa
Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan ranar 7 ga watan Okotoba 2023. Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa; A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara...

Wani Tsohon Ma’aikacin MDD Ya Yi Kira Ga Amurkawa Su Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Amurka Da Natanyahu
Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta...
HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mutanen da ke da sha’awar shiga harkar noma don sama wa kansu abin da za su ci ko kuma don samun kuɗaɗen shiga na fuskantar ƙalubale. Wannan ƙalubale ya haɗa da ƙarancin ilimin noman, da na irin shuka, da rashin gonaki da dai sauran su. NAJERIYA A YAU:...
Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin ta fitar, ya zuwa karfe 6:30 na yammacin ranar 3 ga watan Febrairun 2025, agogon Beijing, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finai wato box office na sabuwar shekarar bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ya kai yuan biliyan 8.257, kwatankwacin dalar Amurka biliyan...
Shuwagabannin kasashen turai guda uku wato EU3 sun bayyana cewa daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar ya fi karfinsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran yana fadar haka a wata hira ta musamman da ta hada ta da tashar. Mohammad Eslami ya...

Wasu Hukumomi A MDD Sun Bada Sanarwan Cewa HKI Ta Fadada Yaki Kan Falasdinawa Daga Gaza Zuwa Dukkan Kasar Falasdinu
Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan...

Shugaban Kasar Amurka Ya Ce Nan Ba Da Dadewa Ba Zai Kara Kudin Fito Na Kayakin Da Ake Shigo Da Su Amurka Daga Kasashen Turai
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara...
Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta sanar da cewa ta kwato mutane 23 da masu garkuwa da mutane su ka kama a cikin dajin Kajuru da ke karamar hukumar Kajuru. Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan ya sanar a jiya Lahadi cewa sun kwato mutanan ne a ranar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da Gwamnatin Kano ta sanar cewa ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aura da ’yan mata da zawarawa a jihar batun ke ta shan suka daga ɓangarori daba-daban. Wasu na ganin jihar na da wasu buƙatun da suka fi auren gatan muhimmanci da ya...
La’anannen dan siyasar Sweden din nan mai kyamar addinin Islama, Rasmus Paludan, ya sake tozarta kur’ani mai tsarki a birnin Copenhagen na kasar Denmark. Paludan mai shekaru 43 shugaban jam’iyyar adawa ta kasar Denmark Stram Kurs, ya sake haifar da cece-kuce ta hanyar aikata wannan aika aika a wajen ofishin jakadancin Turkiyya da ke Denmark....
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba...
Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da...
Iyalai da dama da ’yan fashin daji suka raba da matsugunansu a wasu jihohin Arewa-maso-Yamma da Arewa-maso-Gabas sannan daga bisani kuma aka kore su daga birnin Abuja, inda suka samu mafaka a halin yanzu, suna wani hali a wasu sassan Jihar Nasarawa da ke makwaftaka da Babban Birnin Tarayya Abuja. Binciken da wakilinmu ya yi...
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa; Abubuwan da suka nuna irin girman dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanya makiya takaici Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Baqiri ya jaddada cewa bayyanar irin girman da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suke da shi ya sanya...
‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa...
Tun bayan ’yan kwanaki da Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar cewa Hukumar ta daina kamen masu aikatawa da yada baɗala, sai dai ta yi musu wa’azi, aka fara ganin yaɗuwar bidiyoyin da suka saɓa da al’ada da Addinin Musulunci suna ɓulla kafofin sada zumunta. Daga watan Disamban 2024...

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Bayyana Matakan Da Amurka Zata Bi Don Kyautata Dangantaka Da Iran
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana bayyana matakan da sabuwar gwamnatin Amurka zata dauka idan har tana son sake samun yardar samun yardar kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-jazeera ta kasar Qatar a birnin...

Shugaban Kasa Da Ministocinsa Sun Jaddada Bai’a Ga Wanda Ya Kafa JMI A Safiyar Yau Asabar A nan Iran
Shugaban kasar Iran Ma’suod Pezeskiyan tare da majalisar ministocinsa sun sabonda bai’a da jagoran juyin juya halin musulunci, wanda ya kai kasar ga samun nasarar tumbuke gwamnatin sarki Muhamma Reza Sha sannan ya sannan ya kaisu ga nasarar kafa JM a Iran, shekaru 46 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya...
Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na...
Jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aikin soje na zamani duk da cewa wasu daga cikin jiragen tsoffin kira ne. Kamfanin dillancin labaran Sahaab na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na JMI yana fadara haka. Ya kuma kara da cewa sojojin saman kasar sun samarda wasu sabbin kayakin aikin Soje wadanda...
Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan...
Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da...
Bayan da su ka kwace iko da birnin Goma dke gabashin kasar DRC, kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta sha alwashin kama hanyar shiga babban birnin kasar Kinsasha. Wani daga shugabannin kungiyar ta M 23, Corneilla Nangaa ya furta cewa,: manufarmu ita ce, muna yin yaki ne...
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Kamfanin na Biba Atlantic da Didam, sun sana son ra’ayin a cikin wasikar su ta samun umarni tare da samun bayanan sirri, daga gun ma’aikata, ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ya ba su dama tabka badakala da aikata cin hanci da rasahawa. Kazakla, sanarwar ta bayyana cewa, daga...
A kan yawan samun hauhawan farashin man Garima yace kungiyar na samun saukin farashin sawo man man daga matatar Dangote Refinery da ta MRS duba da cewa, farashinsu na da sauki sosai. Garima da yake yin tsokaci a kan yawan samun hauhawan farashin man a kasar nan, ya bayyana cewa, ‘ya’yan kungiyar na samu sayen...
Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro sun kai samame a wasu gidajen jama’a a birnin, inda suka kama wasu da ake zargin ɓarayi ne tare da ƙwato kayayyakin da aka sace. Wasu daga cikin kayayyakin da aka ƙwato da suka haɗa da: naɗin igiyoyin wutar lantarki masu...
Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan...
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana kan zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a...
“Da na tambaye shi dalili, sai ya ce al’ummominmu suna fama da barnar ‘yan bindiga da hakan ke janyo asarar rayuka da garkuwa da mutanenmu tsawon shekaru zuwa yanzu ba tare da samun mafita da shawo kan lamarin ba.” Gwamnan ya ce bayan rokon, ya zauna da masu ruwa da tsaki ciki har da mashawarcin...

Tunawa Da Ranar Wadanda Aka Yi Wa Kisan Kiyashi: Majalisar Dinkin Duniya Ta Wayar Da Kan Dalibai A Abuja
Ishara ”Kada Mu Manta” taron, ya ba da haske game da lokutan soyayyar dangi da alakar kud da kud da ke wanzuwa a cikin iyalai na Yahudawa da al’ummomin kafin Holocaust da alhakinmu na kare hakkin kowa na rayuwa cikin mutunci da zaman lafiya. Da yake gabtar da jawabi a yayin taron jakadan kasar...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar...
Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba. Ita...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin shure-shure Jam’iyyar PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya? Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna. Tuni wasu ma suka fara ɗigaayar tambaya a...
Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce an samu ci gaba sosai a yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashe da yankuna 160 na duniya a shekarar 2024. Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, yawan kayayyakin da kasar ta fitar ya karu da kaso 7.1 a shekarar, wanda ya kai yuan triliyan...
Dandalin sada zumunta na TikTok ya sanar da hada gwiwa da kamfanin tallace-tallace ta kafofin zamani na Aleph Holdings da dandalin sayayya kan intanet na kasar kenya wato Wowzi, wanda ake sa ran zai bunkasa tattalin arziki mai nasaba da kirkire-kirkiren jama’a a kasar Kenya. Carl Jordon, shugaban sashen tallace tallace da harkokin cinikayya a...
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa rahotanin da ya samu game kyawawan dabi’u da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje suke nunawa a kasashen da suke, yana mai cewa hakan zai zaburar da matasa kan dabi’un da ke kara martabar kasa. Shugaban ya yabawa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin da ya karbi wasiku...