2025-02-24@18:17:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 28
«Tsawaita Rajistar»:

Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen...
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga...
Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi. A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya,...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Shirinsa kan Zirin Gaza yana da kyau, amma ba zai tilasta aiwatar da shi ba, sai dai zai ci gaba da ba da shawara kawai An gudanar da wani zaman taron koli na kasashen Larabawa a kasar Saudiyya, inda aka tattauna Shirin kalubalantar kudirin shugaban Amurka Donald Trump dangane...
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa...
Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan...
Masu lura da gasar sun ce kwarewar na’urar wajen yanke hukunci ya karu zuwa kashi 96.4 idan aka kwatanta da kashi 95.7% a kakar da ta gabata. “Babu wanda yake shakku kan tasirin da ko da kuskure daya wajen yanke hukunci zai yi,” in ji wani babban jami’in kwallon kafa, Tony Scholes. Ya ci gaba...
Kasashen Iran da kuma Lebanon sun tattauna kan dangantakar dake a tsakaninsu dama halin da ake ciki a yankin. A wata tattaunawa ta wayar tarho da yammacin yau Asabar, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Lebanon din Youssef Raji sun jaddada muhimmancin mutunta juna da hadin gwiwa. Iran da Lebanon suna da...

Malaman Yahudawa Fiye Da 300 Sun Rattaba Hannu Akan Takardar Kin Amincewa Da Shirin Donald Trump A Yankin Gaza
Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza. Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba. Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Bayyana Rashin Amincewarta Da Shiga Tattaunawa Karkashin Matsin Lamba
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba,...

Jagoran Ya Ce: Fitowar Mutane A Ranar 11 Ga Watan Fabrayru Alamace Ta Hadin Kan Kasa Sannan Jawabi Ga Barazanar Da Kasar Take Fuskanta
A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama...

Amurka Tana Son Ta Maida Rasha Da China Gefe A Duk Wata Tattaunawa Ta Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Iran
Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya...
Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu...
Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba...
Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa...
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe...
Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na kin amincewa da kalaman Netanyahu dangane da korar Falasdinawa daga Zirin Gaza Kasar Saudiyya ta jaddada yin tofin Allah tsine, da kuma karfafa kin amincewa da kasashen Larabawa suka yi dangane da furucin Benjamin Netanyahu kan neman korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado. A cikin wata sanarwa da...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa...
Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da...
Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da...
Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na...

Wani Tsohon Ma’aikacin MDD Ya Yi Kira Ga Amurkawa Su Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Amurka Da Natanyahu
Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za a ci gaba da bada tallafi ga al’umma a dukkan mazabu 30 na ‘yan majalisar dokokin Jihar. Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake kaddamar da bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Miga wanda Shugaban majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya...

Tunawa Da Ranar Wadanda Aka Yi Wa Kisan Kiyashi: Majalisar Dinkin Duniya Ta Wayar Da Kan Dalibai A Abuja
Ishara ”Kada Mu Manta” taron, ya ba da haske game da lokutan soyayyar dangi da alakar kud da kud da ke wanzuwa a cikin iyalai na Yahudawa da al’ummomin kafin Holocaust da alhakinmu na kare hakkin kowa na rayuwa cikin mutunci da zaman lafiya. Da yake gabtar da jawabi a yayin taron jakadan kasar...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar...

Falasdinawa Sun Gudanar Da Bukukuwan Tarbar Fursunonin Falasdinawa 114 Da Aka Sako Daga Gidan Yarin Isra’ila
Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan...