2025-04-21@22:46:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3603

«da matsalar»:

    Wang Yi ya ce, yana son yin aiki tare da Monday Semaya, domin aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa cudanya da hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu, da daukaka zumuncin kawancen Sin da Sudan ta Kudu a bisa manyan tsare-tsare. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A daren yau ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala ziyarar aiki ta makonni uku a Turai, inda ya gudanar da muhawara da manyan jami’an ƙasa da ƙasa don inganta dangantakar Najeriya a fannin tsaro da ci gaban tattalin arziki. Jirgin shugaban ya sauka ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja da misalin ƙarfe 9:50 na daren ranar, inda ya samu tarɓa daga manyan jami’an gwamnati, ciki har da Sakataren Gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Shugaban Ma’aikatan Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila; Mai Ba da Shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare, Sanata Atiku Bagudu, da Ministan Birnin Tarayya, Barrister Nyesom Wike. Zuba Jari Daga Kasashen Waje A Noman...
    Kasar Cambodiya ce zangon ziyararsa ta karshe. Inda kasashen biyu suka amince da gina al’umma kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani, wanda kamar yadda bangarorin biyu suka jaddada, ya dace da muhimman muradun jama’ar kasashen biyu. La’akari da kalubalan da ake fuskanta a tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kasar Sin ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya. Kuma ziyarar shugaba Xi a kudu maso gabashin Asiya a daidai lokacin da duniya ke fuskantar barazanar bangaranci da daukar matakai bisa radin kai da Amurka ta rike a matsayin makamin mu’amalantar sauran kasashen duniya, ta sa kaimi ga samar da zaman lafiya da wadata a yankin da ma duniya baki daya. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burnley United tare da takwararta ta Leeds United sun samu nasarar dawowa gasar Firimiya bayan samun nasara a mabanbantan wasannin da suka buga. Burnley ta doke Sheffield United da ci 2-1 da yammacin yau domin samun wannan nasarar, hakazalika Leeds United ta samu nasara akan Stoke City da ci 6-0 a daya wasan na yau, dukkan kungiyoyin biyu zasu buga gasar Firimiya Lig ta badi. Alex Iwobi Ya Kafa Tarihi A Gasar Firimiya Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Yayinda kungiyoyin Firimiya Southampton da Leicester City suka koma gasar Championship su kuma Burnley da Leeds United sun samu nasarar tsallakawa zuwa gasar Firimiya a kakar wasa ta badi....
    Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
    Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
    A ranar Litinin ɗin nan aka wayi gari da fastocin takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 na Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. An liƙa fastocin wuri-wuri da suka haɗa da shataletale da turakun wutar lantarki da allunan tallace-tallace daban-daban a wasu manyan tituna da ke ƙwaryar birnin na Bauchi. HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa fastocin masu ɗauke da saƙon “Kaura for President” an manna su a wasu manyan hanyoyi da suka haɗa da titin jirgin ƙasa, Sabon Titin Karofi da kuma Ƙofar Dumi. Ɗaya daga cikin matasan da ke aikin manna fastocin, Aminu Auwal, ya shaida wa Aminiya cewa wasu...
    Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta tabbatar da tsare-tsaren da kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar suka tsayar don gaggauta kyautata tsarin tafiyar da ciniki daidai da zamani, da ingiza ingantaciyar bunkasuwar cinikin sarin kaya da sayen kayan masarufi bisa matakai daban-daban. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar Sin ta fitar a rubu’in farko wato daga watan Janairu zuwa Maris na bana, darajar wadannan bangarori ta karu da dalar biliyan 452.5 a wadannan watanni uku, wanda ya karu da kashi 5.8% bisa na makamancin lokacin bara, kana adadin ya kai kashi 10.4% bisa na dukkan GDPn kasar.   Nagartacciyar bunkasar wadannan sana’o’i na nuna goyon baya na tsarin habaka bukatu cikin gidan kasar da tafiyar da tattalin...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu na yau za yi magana dangane da “Rage kisasfin kudan ma’aikatar harkokin wajen Amurla da kimani kasha 50% da kuma tasirinsa ga matsayin Amurka a duniya da kuma cikin gida. Wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan, rahe kasafin kudi na ma’aikatar harkokin wajen kasar da kasha 50%, saboda haka kuma ya rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancin kasar da kananan ofisoshin jakadancin kasar fiye da 30 a yankuna daban daban a duniya amma mafi yawansu a nahiyar Afirka. Dangane da wannan matakin da gwamnatin kasar Amurka masana daga ciki ga wajen kasar ta Amurka masu yawa...
    Kasashen Masar da Kuwaiti sun fitar da sanarwa a yau Litinin ta yin tir da kiraye-kirayen da wasu yahudawa masu tsattsauran ra’ayi suke yi domin a rusa masallacin kudus, suna masu yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa domi a tsayar da tsokanar da Isra’ilawa suke yi. Kasashen biyu dai sun fitar da wannan sanarwar ne bayan da wasu yahudawa su ka watsa wani faifen bidiyo na tarwatsa masallacin Kudus da kuma maye gurbinsa da gina wajen bautar yahudawa. Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta bayyana cewa: “Jamhuriyar Larabawa ta Masar tana yin tir da kakkausar murya akan kiraye-kirayen da masu tsattsauran ra’ayin ‘yan share wuri zauna suke yi na tarwatsa masallacin Kudus. Haka nan kuma Masar din ta yi kira...
    Shugaban ma’aikatar shari’a ta Iran ya isa kasar China domin halartar taron shugabannin ma’aikatun shari’a na kasashen da suke mambobin kungiyar Shangai karo na 20. Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhsini Eiji wanda shi ne shugaban ma’aikatar shari’a ta jamhuriyar musulunci ta Iran, ya nufi kasar China a yau Litinin domin halartar taron kungiyar Shangai wanda shi ne irinsa karo na 20. Gabanin barinsa filin saukar jiragen sama na “Mehrabad” Eiji ya bayyana muhimmancin yin aiki a tare a tsakanin ma’aikatun shari’a na kasashen mambobin kungiyar Shanghai sannan ya kara da cewa: ” Taron na shugabannin ma’aikatun shari’a karo na 20 na kungiyar Shangai za a yi shi ne a garin Hangatsho, za kuma mu hatarta ne a karkashin bunkasa diflomasiyya ta...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; A kalla mutane 35 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 62 kuma su ka jikkata a cikin sa’o’i 24. Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta kara da cewa; Sojojin Mamaya sun kai wasu hare-hare a gabashin garin Beit-Hanun dake arewacin Gaza. A cikin hemar ‘yan hijira dake tsakiyar Gaza, Falasdinawa 3 sun yi shahada, bayan da jiragen saman a ‘yan mamaya su ka kai hari. A kudancin Gaza kuwa sojojin HKI sun tarwatsa wani gini na fararen hula a yankin Misbah dake arewacin birnin Rafah. Daga ranar 18 ga watan Maris na wannan shekarar zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 1864, yayin da wadanda...
    A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya. Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce ta kalubalantar yadda ake take hakkin bil’adama a duniya, musamman mai dai yadda ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa a Gaza. Haka nan kuma yadda ya rika yin kira da HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi, da kashe mata da kananan yara. Fizishkiyan ya kuma kara da cewa; Wadannan matakan da Papa Roman ya dauka...
    Sun buƙaci gwamnatin tarayya ta inganta tsaro a jihar, ta samar da wuraren tsaro a al’umma da gudanar da cikakken bincike kan hare-haren. Sun kuma sunyi kira ga al’ummar Nijeriya da su hada kai wajen tsayawa kai da fata kan kisan gilla da tashin hankali da ake yi a ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Har ila yau, rahoton ya nuna cewa, yayin da adadin yabanya ke karuwa a cikin gida, kuma karuwar bukatunsu ke raguwa, akwai hasashen raguwar bukatar shigo da nau’o’in amfanin gona cikin kasar daga ketare. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar Filato ta gudanar da wata zanga-zangar lumana domin nuna adawa da matsalar tsaro da ke addabar jihar. Zanga-zangar ta gudana ne makonni kaɗan bayan munanan hare-haren da aka kai a wasu ƙauyukan Bokkos da Mangu, waɗanda suka yi sanadiyyar aƙalla rayuka 100. Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis Waɗanda suka yi zanga-zangar sun haɗa da maza da mata da matasa har da tsofaffi ɗauke da alluna waɗanda aka rubuta wa saƙonni daban-daban. Bayanai sun ce maƙasudin zanga-zangar ita ce kiran gwamnati kan ta ɗauki mataki kan kashe-kashen da ake yi a yankin. Jihar Filato da wasu jihohin Arewa maso tsakiyar Nijeriya...
    Hukumar kula da kasuwannin kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, adadin kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin ya zarce miliyan 57 ya zuwa karshen watan Maris, wanda ya kai kaso 92.3 bisa dari na jimillar baki daya. Kazalika, a rubu’i na farko, adadin sabbin kamfanoni masu zaman kansu da aka kafa a kasar ya kai miliyan 1.979, wato karuwar kashi 7.1 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, kuma ya zarce matsakaicin ci gaban da aka samu a shekaru ukun da suka gabata. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
    Wannan amincewar da kammala aikin ginin cibiyar, babban nasara ce wajen inganta harkokin kiwon lafiya, da inganta bayar da kulawa ga lafiyar al’ummar jihar Yobe.   A cikin wannan ziyarar, Gwamna Buni ya sami rakiyar Sanata Musa Mustapha, mai wakiltar Gabashin jihar Yobe, Mai Baiwa Gwamnan shawara kan Ayyuka na Musamman, Hon. Kachallah Mai Hassan, Hon. Abdu Gulani, Mashawarcin Sufuri da Makamashi, da sauran manyan jami’an gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko. A cikin shirimmu da ya...
    Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Italiya, FIGC, ta sanar da jingine wasannin gasar gasannin Serie A, B, da C, saboda alhinin rasuwar shugaban ɗarikar Katolika, Fafaroma Francis. Shugaban hukumar FIGC, Gabriel Gravina ya ce, “Harkar ƙwallon ƙafa ta Italiya tana taya jimami ga miliyoyin al’umma kan rasuwar Mai Alfarma Fafaroma Francis. Ƙungiyoyin da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Juventus, Lazio, Parma Calcio, Cagliari, Fiorentina, Genoa, Torino, Udinese. A safiyar Litinin 21 ga Afrilu ne Fadar Cocin Katolika da ke Vatican City ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis mai shekaru 88, wanda ke shugabantar Cocin, kuma shugaban birnin Vatican City. Miliyoyin mutane a Italiya da kuma faɗin duniya sun shiga alhini saboda rasuwar malamin adinin. Wannan ya sa aka ɗauki matakin...
    Hukumar Hisbah ta kama wata mata mai sana’ar ɗan wake kan zargin ta da yin lalata da wani almajiri dan shekara 14 a garin Azare da ke Jihar Bauchi. Shugaban Hukumar ta Hisbah na shiyyar Katagum da ke Azare, Malam Ridwan Muhammad  Khairan ya bayyana cewar, ana zargin matar, wadda ake kira Baba Mai Ɗan Wake da laifin yin fasikanci ta hanyar tilasawa da yaudara da wani almajiri dan kimanin shekaru 14, bayan ta sanya masa maganin ƙarfin maza a cikin lemon kwalba don ya riƙa biya mata buƙata. Ya ce almajirin ya haɗu da Nana Mai Ɗan Wake da yake mata wanke-wanke a Sabuwar Tashar Jama’are ne, a cikin garin Azare, inda ta buƙaci ya riƙa zuwa gidanta yana...
    Wannan amincewar da kammala aikin ginin cibiyar, babban nasara ce wajen inganta harkokin kiwon lafiya, da inganta bayar da kulawa ga lafiyar al’ummar jihar Yobe.   A cikin wannan ziyarar, Gwamna Buni ya sami rakiyar Sanata Musa Mustapha, mai wakiltar Gabashin jihar Yobe, Mai Baiwa Gwamnan shawara kan Ayyuka na Musamman, Hon. Kachallah Mai Hassan, Hon. Abdu Gulani, Mashawarcin Sufuri da Makamashi, da sauran manyan jami’an gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da safiyar wannan Litin fadar Vatican ta sanar cewa da misalin ƙarfe 7.35 Agogon Vatican Fafaroma Francis, wanda sunansa na asali Cardinal Jorge Mario Bergoglio, ya rasu a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke bikin Ista. Ya mutu ne washegari da ya fito bainar jama’a a Dandalin St Peter’s, domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista. Fafaroma Francis ya yi fama da doguwar jinya, inda a watan da ya gabata ne aka sallame daga asibiti bayan ya shafe makonni biyar can sakamakon cutar sanyin haƙarƙari mai tsanani. Ga wasu abubuwa da Fafaroman ya yi fice a kansu: 1. Nuna adawa a fili ga wasu manufofin Donald Trump. Ya yi Allah wadai da yunƙurin Trump a mulkinsa na farko na...
    Wani magidanci ya ɗankara wa matarsa saki a ofishin ’yan sanda bayan an kama ta a wani otel. Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa an kama matar ce a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai maɓoyar dillalan miyagun ƙwaya da ’yan sara-suka a wasu otel-otel a garin Minna. Ya bayyana cewa sai bayan da aka kawo matar ofishin ’yan sanda, a yayin bincike suka gano cewa matar aure ce, bayan da suka tuntuɓi ’yan uwan mutanen da aka kama. Ya ce, “Sakamakon yawaitar yadda matasa suke tayar da zaune tsaye ne mataimakin gwamna Kwamred Yakubu Garba, ya umarci jami’an tsaro su ɗauki mataki a kansu. Yadda uba da ɗansa da wani ango suka rasu a bakin aiki a...
    Ta ce, sakamakon dukan da ta sha, ta samu karaya a kafa da kuma raunin da ya shafi kunnenta.   Sai dai Shu’aibu ya musanta wannan ikirarin, inda ya tabbatar da cewa, an kama dan uwanta ne a yayin wani samame da aka gudanar a wurin wani shagali a birnin Katsina.   A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne da laifin yin sojan gona da kuma yunkurin dakatar da jami’an Hisbah a lokacin da suke bakin aiki.   Da yake karin haske game da gaskiyar lamarin abinda ya faru, Shuaibu ya ce, an hana Hauwa shiga cikin ofishin Hisbah ne saboda irin tufafin da take sanye da su na rashin da’a, kuma ta yi yunkurin marin daya daga cikin...
    Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna ta hanyar wayar tarho da takwarorinsa na Switzerland da Pakistan Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi wata ganawa ta hanyar wayar tarho guda biyu a yammacin jiya Lahadi tare da ministocin harkokin wajen kasashen Switzerland da Pakistan. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Switzerland Ignazio Cassis ta hanyar wayar tarho a yammacin jiya Lahadi, inda suka tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwan kasa da kasa tare da yin musayar ra’ayi a kansu. A yayin wannan tattaunawa, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana jin dadinsa ga rawar da kasar Switzerland ta taka a shawarwarin nukiliyar kasar cikin...
    Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Babban abin da suke bukata a duk wata tattaunawa shi ne a dage takunkumi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i, ya jaddada cewa babban bukatar Iran a duk wata tattaunawa ita ce a dage takunkumin da aka kakaba mata ta hanyar da za ta kai ga samun sakamako mai ma’ana. Isma’il Baqa’i ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na mako-mako da yake yi a yau litinin cewa: A kwanakin baya ministan harkokin wajen kasar Iran ya ziyarci kasar Rasha, sannan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Italiya, a gefen shawarwari ba na kai tsaye ba tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka. Ya kara da cewa: A...
    Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin Mamayar Isra’ila ta tabbatar da cewa ba za a amince da ita ba a duk wani bincike laifukan sojojinta Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta sake tabbatar da rashin sahihancinta wajen binciken laifukan da sojojinta suka aikata. A yayin da take tsokaci kan binciken da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi kan harin da aka kaiwa ma’aikatan jinya a Gaza, kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, 21 ga watan Afrilun wannan shekara ta 2025: Akwai zabi daya tilo na yin adalci, ta hanyar kotun hukunta manyan...
    Wasu Falasdinawa sun yi shahada a cikan kwana na 35 a sabon yakin da yahudawan sahayoniyya suka sake daurawa kan Zirin Gaza Sojojin gwamatin mamayar Isra’ila suna ci gaba da yakin kisan kiyashi a Zirin Gaza tun bayan sake ci gaba da yau tsawon kwanaki 35 da suka gabata, bayan da Fira minista Benjamin Netanyahu ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma yana gudanar da wannan ta’asa ne tare da goyon bayan siyasa da na sojan Amurka, sannan kungiyoyin kasa da kasa gami da gwamnatocin kasashe sun daukin matakin yin shiru da rashin gwada wani yunkurin kalubalantar wannan danyen aiki. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama tare...
    Fadan Vatican ta mabiya darikar Katolika ta sanar da mutuwar  Paparoma Francis a yau Fadar Vatican ta bayyana a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo a yau Litinin cewa: Paparoma Francis, shugaban darikar Katolika dan Latin Amurka na farko, ya kawo karshen mulkin da ya yi fama da rikici, rarrabuwar kawuna, da tashin hankali a yayin da yake kokarin kawo sauyi a cibiyoyin majami’u. Cardinal Kevin Farrell ta hanyar gidan talabijin na Fadar Vatican ya shelanta cewa; Ya ku ‘yan uwa maza da mata masu daraja, tare da bakin ciki da alhini, ina sanar da mutuwar Fafaroma Francis”, da karfe 7:35 na safiyar yau (agogon gida), yana mai jaddada cewa: Francis, ya koma gidan mahaifinsa.” Fafaroma Francis yana da shekaru...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa babu wani kamfen batanci da zai hana Gwamna Dauda Lawal aiwatar da ayyukan da suka shafi al’umma a fadin jihar.   Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da sadarwa na gwamna, Malam Salihu Nuhu Anka ya rabawa manema labarai a Gusau.   A cewar Anka, Gwamna Lawal ya fara aiki ne a wani aikin ceto, kuma tuni mazauna jihar suka fara cin ribar dimokuradiyya.   Ya bayyana cewa hankalinsa ya karkata ne kan kalaman da ya bayyana a matsayin maras tushe da wani tsohon Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Magaji Dosara ya yi, yayin wani taron manema labarai a Kaduna, inda ya kalubalanci kalaman da Gwamna Lawal ya...
    Allah Ya yi wa Shugaban mabiya ɗarikar Katolika na duniya, Fafaroma Frasncis, rasuwa yana da shekaru 88. Fadar Vatican ce ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis a safiyar Litinin a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke bikin Ista. Ya mutu ne washegari da ya fito bainar jama’a a Dandalin St Peter’s,  domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista. A watan da ya gabata ne aka sallame daga asibiti bayan ya yi jinya na tsawon makonni biyar. Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron shi ne na farko wajen mika sakon ta’aziyya a cikin shugabannin duniya.
    Allah Ya yi wa Shugaban mabiya ɗarikar Katolika na duniya, Paparoma Frasncis, rasuwa yana da shekaru 88. Fadar Vatican ce ta sanar da rasuwar Paparoma Francis a safiyar Litinin a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke bikin Ista. Ya mutu ne washegari da ya fito bainar jama’a Dandalin St Peter’s,  domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista. A watan da ya gabata ne aka sallame daga asibiti bayan ya yi jinya na tsawon makonni biyar. Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron shi ne na farko wajen mika sakon ta’aziyya a cikin shugabannin duniya.
    Fadar Vatican ta sanar da mutuwar shugaban majami’ar katolika na duniya, Fafaroma Francis yana da shekaru 88 a duniya. A shekarar 2023 ne cocin ya zaɓi Fafaroman, wanda asalin sunansa shi ne Cardinal Jorge Mario Bergoglio a matsayin wanda zai jagorance ta, bayan saukar Fafaroma Benedict XVI daga kan muƙamin. Da safiyar Litinin ne ɗaya daga cikin jagororin cocin ya sanar cikin jimami game da rasuwar ta Fafaroma Fraincis, inda ya ce: “Ya ku ƴan’uwana, cikin alhini, ina sanar da ku game da rasuwar Babanmu a addini, Francis. Da misalin ƙarfe 7:35 na wannan safiya (Agogon Vatican), Bishop ɗin Roma, Francis ya koma ga mahalicci. Ya sadaukar da rayuwarsa baki ɗaya wajen bauta wa ubangiji da kuma coci.” “Ya koya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga tarin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu sabbin matsalolin na ƙara kunno kai. Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar hare-haren da ake zargin na ƙungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, da kuma sabbin kashe-kashe a sassan jihohin Filato da Binuwai, sai kuma ga wata sabuwar ƙungiya da ake zargin ta ’yan ta’adda ce mai suna Mahmuda ta ɓulla a Jihar Kwara. To ko mene ne ya haddasa wannan koma-baya ta fuskar tsaro? Shin a ganinku, me ya sa matsalar tsaro “ta gagari gwamnatin” Najeriya? NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi DAGA LARABA:...
    Ma’aikatan Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Bauchi guda huɗu sun rasu a yayin da suke aikin tsabtace madatsar ruwa ta Gubi. Wasu jami’ai da ke aiki a Madatsar Ruwa ta Gubi, sun bayyana cewa daga cikin mamatan har da wani uba da dansa da kuma wani wanda ke shirye-shiryen ɗaurin aurensa. “Abin ya faru ne a lokacin da suke aikin tsaftace ruwan da ake kula da ruwan da ake yi wa babban birnin Bauchi. Na samu labarin suna cikin tafki, sai suka ga wasu kifaye a cikin ruwan datti, ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin kama kifi, kifin ya yi zurfi, sai ya bi shi ya mutu. “Ana cikin haka, wani abokin aikinsa da ya ga abin da ya...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa tace uranium din ta tamakar jan layi ne a tattaunawar dake wakana tsakaninta da Amurka. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ne Kazem Gharibabadi ya bayyana hakan, inda ya ce hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne inganta sinadarin Uranium, yana mai jaddada cewa, wannan batu a matsayin jan layi a tattaunawar da Amurka. Mista Gharibabadi ya bayyana haka ne a yayin taron kwamitin majalisar dokoki kan tsaron kasar da manufofin ketare, inda ya yi wa ‘yan majalisar bayani kan shawarwari zagaye na biyu tsakanin Tehran da Washington, wanda ya gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya. Jami’in na iran ya kara da cewa tawagar kasar ta jaddada matsayinta na cewa Iran ba ta neman...
    Amurka ta sake kai wani hari ta sama kan babban birnin kasar Yemen, Sana’a, inda ta kashe fararen hula akalla 12 tare da jikkata wasu fiye da 30 na daban. Mummunan harin na Amurka an kai shi ne a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a a unguwar al-Farwa da ke gundumar Sha’ub a safiyar ranar Litinin. Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu yayin da mutane da dama ke makale a karkashin baraguzan gine-gine da aka wargaza a harin. A gefe guda kuma, Amurka ta kai hare-hare a yankunan lardin Sa’ada, a arewa mai nisa na kasar, da tsakiyar Ma’rib, da yammacin Hudaydah. Dama kafin hakan a ranar Lahadi, Amurka ta kai wasu hare-hare ta sama a Yemen,...
    Wani rahoto da jaridar New York Times ta Amurka ta fitar ya nuna cewa Amurka na neman rage kasantuwarta a duk duniya musamman a Afirka. Jaridar ta bayyana wani daftarin dokar shugaban kasa na sirri wanda ya tanadi “sake tsara tsarin ma’aikatar harkokin wajen Amurka. Sai dai ministan harkokin wajen kasar Marco Rubio, ya musanta wadannan shirye-shiryen. Batu na farko na shirin sake fasalin ma’aikatar harkokin wajen Amurka shi ne rage ofisoshin ma’aikatar harkokin wajen Amurka a bangaren sauyin yanayi, dimokuradiyya, da kare hakkin bil’adama, batutuwan da gwamnatin Trump ta shiga kafar wando guda dasu. Rahoton ya ce rage kasafin kudin zai kai ga rufe ofisoshin jakadanci a kasashen waje,  amma inda Amurka za ta rage yawan aikin diflomasiyya shi...
    Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis, ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza. A cikin sakonsa na bikin Easter, Paparoma ya yi tir da halin da ake ciki na jin kai a Gaza tare da yin kira da a tsagaita wuta. Paparoma Francis ya halarci bukukuwan Ista a wannan Lahadi, inda ya yi tir da halin da ake ciki na jin kai mai daukan hankali a Gaza.  “Ina kira ga bagarorin da su tsagaita wuta, a saki wadanda aka yi garkuwa da su, a kuma kai kayan agaji ga al’ummar falasdinu da kuma fatan samun zaman lafiya a nan gaba,” in ji shi a cikin sakonsa, wanda wani na hanun damansa ya karanto daga cocin St....
    Ana zargin wani ɗan kasar Indiya mai shekara 20 da tserewa da surukarsa mai shekara 40, kwanaki tara kacal kafin aurensa da ’yarta. Ma’auratan Rahul da Shibani, matasa ne ’yan Aligarh, a Jihar Uttar Pradesh ta Indiya, wadanda suka shirya yin aure a ranar 16 ga Afrilu na watan da muke ciki. Zaɓen 2027: Babu ɗan takarar da zai yi nasara ba tare da goyon bayan Arewa ba — Hakeem NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya An aika wa dangi katin gayyata domin halartar taron bikin, amma kwanaki tara kafin ranar bikin, sai wani iftila’i ya afku. Angon dan shekara 20 ya lallaba ya bace, amma bai tafi shi kadai ba; ya...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City dake buga babbar gasar Firimiya ta kasar Ingila ta koma gasar yan dagaji ta Championship bayan da tayi rashin nasara a guda a wasanta da Liverpool. Leicester wadda ta lashe gasar Firimiya a shekarar 2016 ta samu maki 18 kacal a wasanni 33 da ta buga, ta zura kwallaye 27 yayinda aka zura mata kwallaye 73 a ragarta, Leicester ta koma gasar Championship duk da cewar akwai sauran wasanni 5 da su ka rage ba a buga ba a gasar Firimiya ta bana. Yaushe Liverpool Za Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila? Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Kocin Leicester Ruud Van Nistelrooy ya karbi ragamar horarwar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da barazanar HKI na kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar kasar don hana kasar abinda take kira makaman Nukliya. Ministan ya kara da cewa kasar Iran zata iya kare kanta ko da Amurka ce ta takaleta, kuma Amurka ta san hakan. Sannan ya ce HKI bata taba kaiwa Iran hari a bay aba kuma ba zata taba kai mata hari ba. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya buga wannan labarin a jiya Asabar ya kuma nakalto ministan yana cewa kasashen Rasha da Iran basu taba karfafa dangantakar tsakaninsu fiye da yanzu ba. Aragchi ya kara da cewa kasashen Iran Rasha da kuma China suna aiki tare don tabbatar da zaman...
    Bayan taro na biyu tsakanin JMI da Amurka a birnin Roma na kasar Italiya a jiya Asabar an gayyaci ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arachi don gabatar da Jawabi a wani taro wanda mahukuntan kasar Amurka suka shirya. Kamfanin dillancin labarai IP na kasar ya nakalto masu shirya taron na cewa an gayyace Abbas Arichi don gabatar da  jawabin ne don muhuntan Amurka su ji ta bakin wadanda suka kore a sanin amfanin makamashin nukliya ta zaman lafiya da kuma tattaunawa a kansa. Labarin ya nakalto wadanda suke gudanar da taron wato ” The Carnegie International Nuclear Policy Conference” wanda za’a fara a gobe litinin, na cewa taron yana taimakawa mahukuntan kasar Amurka sanin kan yadda jami’an diblomasiyya yakamata...
    Shugaban kungiyar Asa’ib Ahl-Al-Hak, kungiya mai yaki da yan ta’adda a kasar Iraki, ya bayyana cewa idan shugaban kasar Siriya mai ci Abu Muhammad Al-Jolani ya kuskura ya taka kasar Iraki ana iya tsare shi sabuda gwamnatin kasar Iraki tana da sammashin kama shit un da dadewa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto shugaban kungiyar Qais Al-khazali yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa jita jitan da yake ji na cewa shugaban kasar ta siriya zai zo iraki a nan gaba, bai taso ba, lokacin zuwansa kasar Iraki bai yi ba saboda zarge-zargen da ake masa tun kafin ya kwace shugabancin kasar ta Siriya, akwai matsalolin doka sosai wadanda...
    Majiyar labarai daga kasar Lebanon sun bada sanarwa kama wasu mutane wadanda suke shirin Cilla Makamai kan HKI. Jaridar Arab News ta yanar gizo ta kuma kasar Saudiya ta bayyana cewa a makon da ya gabata ma an kama wasu mutane wadanda ake zargi da cilla makaman roka kan HKI daga kudancin kasar ta Lebanon. Amma dangane da kwance damarar kungiyar Hizbullah kuma shugaban kasar Lebanon Jesept Aun ya ce wannan al-amarin ba abu ne mai sauki ba, sai dai a jira lokacinda ya dace na yin hakan. Aun ya kara da cewa duk wani kokari na kwance damarar kungiyar hizbullah kawo karshen zaman lafiya a kasar Lebanon ne. Kafin haka dai shugaban kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim a jawabin...
    Gwamnaton kasar Kongo Democradiyya ta bada sanarwan haramta jam’iyyar Josept Kabila tsohon shugaban kasar. Shafin yanar gizo na labarai, Africa News ya nakalto ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar tana bada wannan sanarwan. Labarin ya kara da cewa, Josept Kabila ya shugabanci kasar ta kwango har zuwa shekara ta 2019, karkashin Jam’iyyarsa ta ‘the People’s Party for Reconstruction and Democracy (PPRD). Daga baya Kabila ya dorawa kansa gudun hijira zuwa kasashen waje a shekara ta 2023. Bai kuma sake dawowa ba sai ranar jummar da ta gabata. Kabila dan shekara 53 a duniya, ya shigo kasar kongo daga kasar Rwanda, sannan ya je ya gana da shuwagabannin kungiyar M23 a birnin Goma, inda daga nan suke ikonsu a kan yankunan...
    Mutum ɗaya ya rasu yayin da matasan gari suka yi taho mu gama da ‘yan bindiga lokacin kai hari garin Kware a Jihar Sokoto a daren Asabar. Shaidu sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin Kware, cibiyar ƙaramar hukumar Kware, da nufin aikata fashi. Mamba na ƙungiyar masu samar da tsaro ta cikin gari, Bello Mai Maciji, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun samu nasarar satar wani adadin kudi daga hannun Dan Balgore, wani sanannen mai kasuwanci a yankin. Gwamnatin Sakkwato Ta Siyawa ‘Yan Gudun Hijira Gidan Miliyan 100 ‘Yan Bindiga A Ƙarƙashin Jagorancin Turji Sun Kashe Manoma 12 A Sokoto Mai Maciji ya bayyana cewa, ‘yan fashin sun bayyana cewa suna da masaniya game da kuɗin kasuwancin...
    Sojojin mamayar HKI sun fara aiwatar da wani sabon kisa ta hanyar amfani da sabon salo akan Falasdinawa. Kai kace tsawon watanni 18 da su ka dauka suna amfani da makamai mabanbanta wajen kashe mutanen Gaza, bai isha sun cimma manufofin da su ka Sanya a gaba. Sabon salon kisa wanda  ya yi kama da “Kalankuwar Masu Cin naman mutum” bayan sun soya shi, shi ne abinda yake faruwa.  Isra’ila ta kai hari da jirgin yakin maras matuki na kunar bakin wake akan sansanonin ‘yan hijira da su ka yi dandazo a wuri daya. Iyalan Abur-Rus ne wannan jirgin kunar bakin waken ya fada a kansu  ya kashe da dama daga cikinsu ta hanyar kona su da ransu. Mutane 20...
    Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf. NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Nijeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa. “Nan da watanni shida mutanen Arewacin Nijeriya za su fayyace inda suka dosa, saboda haka zaɓi ya rage wa...
    Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Uba Builder, ya sake jaddada kudirinsa na kyakkyawan shugabanci wajen gudanar da harkokin karamar hukumar. Ya bada  wannan tabbaci ne yayin rabon Naira dubu hamsin hamsin ga mutane 70 da suka amfana da shirin noman alkama da karamar hukumar ta kirkiro. A cewarsa, mutane 165 ne aka saka cikin shirin, inda matasa 70 daga ciki ‘yan siyasa ne, wadanda a ke da bukatar canza rayuwarsu zuwa hanyoyin neman na kai, duba da cewa siyasa ba sana’a ba ce, illa tsarin shugabanci ne. Alhaji Muhammad Uba Builder ya ce an samar wa mahalarta shirin da filin noma, tare da gyaran filin, da samar da irin alkama da sauran abubuwan bukata, yayin da suke lura...
    Ya kuma ce, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na yakin karin haraji ko yakin kasuwanci. Kuma wannan ba wai don kare muradu da martabar kasar Sin ba ce kawai, har ma da kare tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, tare da tabbatar da daidaito da adalci.   A cewarsa, “Idan har wata kasa ta dage kan kakaba mana yakin haraji ko kuma yakin kasuwanci, to tabbas za mu yi gaba-da-gaba da ita ba tare da tsoro ba, kuma tabbas za mu dauki kwararan matakan mayar da martani.”(Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
      A shekaru 70 da suka wuce, kasashen yamma sun yi wa taron Bandung kallon taro na kasashe matalauta, amma kuma ga irin yadda ya haifar da kyakkyawan sakamako ga mikewar kasashen. A zamanin yau, lokacin da kasar Amurka ke ta kara kakaba harajin kwastam a kan sauran kasashen duniya, muna farin cikin ganin yadda kasashe masu tasowa ke hada kansu, da rike tsaronsu da ci gabansu a hannunsu, suna kuma rungumar akidun zaman lafiya da hadin gwiwa da bude kofa don tinkarar yadda kasashe masu karfi ke neman cin zalin kasashe masu karamin karfi da ma rashin tabbas da ake fuskanta a duniya. Yau da muke waiwayen taron Bandung, za mu gano cewa, ko-ba-dade-ko-ba-jima za mu ga bayan nuna...
    Kididdigar da hukumar kula da harkokin makamashi ta kasar Sin ta fitar a yau Lahadi ta yi nuni da cewa, zuwa karshen watan Maris din shekarar da muke ciki, yawan wutar lantarki da kasar Sin ke iya samarwa ya kai kilowatt biliyan 3.43, adadin da ya karu da kaso 14.6 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.   Daga cikin wutar lantarkin da ake samarwa, yawan wutar lantarki da ake iya samarwa bisa makamashin hasken rana ya kai kilowatt miliyan 950, adadin da ya karu da kaso 43.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kazalika, a sa’i daya kuma, yawan wutar lantarki da kasar ke iya samarwa bisa karfin iska ya kai...
    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya NDLEA, ta yi nasarar kama hodar iblis wadda aka ɓoye a cikin littattafan addini da ake shirin kaiwa Saudiyya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Hukumar NDLEA ɗin ta fitar a ranar Lahadi. Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas Hukumar ta bayyana cewa ta kama ɗauri 20 na hodar iblis ɗin wanda jimillar nauyinsu ya kai giram 500 a cikin littattafan addini. NDLEA ta ce jami’anta sun gano hodar ne a yayin da suke gudanar da bincike a wani kamfanin da ke jigilar kayayyaki a Legas a ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, yayin da yake shirin kai...
      Kungiyar Masu Babura Uku ta Najeriya, Jihar Kaduna ta Rantsar da Shugabannin Sassa Goma Sha Biyar da Manyan Jami’ansu don Gudanar da Harkokin Kungiyar a Tsawon Shekaru Hudu Masu Zuwa.   Mataimakin Kwamandan Hanya kuma Mataimakin Jami’in Wayar da Kai na Hukumar Kiyaye Haddura ta Tarayya (FRSC), Kaduna, Usman Garba, wanda ya yi magana da manema labarai bayan bikin rantsarwa, ya yaba wa kungiyar, yana mai cewa wannan ci gaba ne mai kyau ga kungiyar.   Ya ce Hukumar Kiyaye Haddura na farin ciki da wannan ci gaba saboda sabon tsarin shugabanci zai taimaka wajen magance matsalolin da suka shafi direbobin babura uku (Keke Napep) da hukumar ke fuskanta a jihar.   A cewarsa, yanzu hukumar za ta yi...
    An samu rahoton cewa, Fursunoni tara a gidan yari na Oko Erin a jihar Kwara a ranar 19 ga watan Afrilu, sun tsere. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa, da misalin karfe 10:00 na dare, wani ma’aikaci a gidan, mai suna Joseph Issa, ya sanar da faruwar lamarin. Rugujewar Gini A Legas: Adadin wadanda Suka Mutu Ya Kai Biyar, An Ceto 20 Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Vietnam Da Malaysia Da Cambodia Ba tare da bata lokaci ba, ‘yansanda suka yi gaggawar isa wurin, inda suka sake kama daya daga cikin wadanda suka tsere, mai suna Abdul Raman Misa mai shekaru 15. An mayar da Misa gidan yarin, yayin da ake...
    Da alama tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari, yana nema karbe kambun ɗaukaka da ’yan siyasa a baya suka riƙa bai wa tsofaffin shugabannin ƙasar nan biyu, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Cif Olusegun Obansanjo, wajen neman tabarrakinsu musamman a lokacin da zabe ya karato a kasar nan. Buharin wanda ya mulki kasar nan a tafarkin soja da kuma na farin hula daga bayabayan nan, a yanzu haka tauraronsa na haskawa, kuma yana ƙamshin turaren Ɗan goma, inda jiga-jigan ’yan siyasa daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP da SDP da kuma jam’iyyarsa mai mulki ta APC, suke nikar gari takanas zuwa gidansa da ke birnin Kaduna, tare da nuna irin kyakkyawan kusancinsa da su. Hakan dai na zuwa ne...
    A faransa ana ci gaba da tsare wata ‘yar Iran mai goyan bayan Falasdinu, bis azarginta da iza ta’addanci. Mahdieh Esfandiari (mai shekaru 35) ana tsare da ita tun ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan kama ta a binrin Lyon, inda ta ke da zama. Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ya yi Allah wadai da kama Mahdieh Esfandiari, yana mai yin Allah wadai da “manufofin kasashen Turai” wanda “ya kunshi murde adawa da “kisan kare dangi” da Isra’ila ta yi a Gaza. Ya kara da cewa ba a sanar da ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris da kuma iyalan yarinyar ba. A nasa bangaren, lauyan Mahdieh Esfandiari, Nabil Boudi, ya nuna rashin jin dadinsa...
    Hukumomi a jihar Benue dake Najeriya sun ce adadin wadanda suka mutu  a harin da ‘yan bindiga suka kai a hukumomin Ukum da Kogo ya kai 56. Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, a wata ziyara a yankin ya shaidawa manema labarai cewa  adadin wadanda suka mutu a harin ya kai 56. ”A yanzu, mutum 56 ne suka mutu wadanda ba su ji ba su gani ba, da suka hada da iyaye da maza da mata da kananan yara”, in ji shi. Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakai domin kawo karshen hare-hare a jihar. Gwamnan ya ce tuni gwamnatin jihar ta kara tura jami’an tsaro zuwa yankunan domin kwantar da hankula. Harin na zuwa ne kimanin...
    Ana sake gudanar da manyan zanga-zanga a manyan biranen Amurka a kan nuna adawa da tsare -tsare da manufofin gwamnatin Donald Trump. Masu zanga-zangar na zargin gwamnatin da keta haddin kundin tsarin mulki da ‘yancin jama’a. Wannan shi ne karo na biyu a wannan wata da dubban mutane suka yi tattaki a titunan Amurka domin nuna bacin ransu kan yadda Trump ke gudanar da mulkin kasar. Korafe-korafen masu zanga-zangar sun hada da korar baki daga kasar da korar ma’aikata da gwamnati ke yi da kuma zargin tauye ‘yancin fadin albarkacin baki. Kazalika masu zanga-zangar na nuna fishi kan irin ikon da Trump ya bai wa Elon Musk, attajirin duniya mai kamfanin Tesla – wanda ya kori ma’aikatan gwamnati sama da...
    Mutane da dama ne suka mutu sannan wasu sun jikkata sakamakon wasu sabbin hare-hare da jiragen yakin Amurka suka kai kan wasu yankuna na kasar Yemen. A daren jiya wayewar yau Lahadi, sojojin Amurka sun kai hare-hare ta sama akalla 20 a Sanaa babban birnin kasar Yemen, da kuma yammacinta da gabashi da kuma kudancin kasar. Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar Yemen suka sanar a ranar Asabar cewa kimanin mutane 80 ne suka mutu, yayin da wasu 150 suka samu raunuka sakamakon harin da Amurka ta kai a ranar Juma’a a tashar mai na Ras Issa da ke birnin Hudaidah. Hare-haren na Amurka a Yemen sun kara gurgunta halin da kasar ta Yemen ke ciki....
    Kawo yanzu an samu aƙalla mutum biyar da suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar ruftawar wani bene mai bene mai hawa uku da ya ruguje a unguwar Ojodu-Berger da ke Jihar Legas. Haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe 09.45 na safiyar ranar, inda hukumar kai ɗauki gaggawa tare da taimakon ’yan sanda suka gano cewa wani gini mai hawa uku ɗauke da gidan abinci da mashaya ne ya ruguje. Mayaƙan ISWAP sun tarwatsa gada a Yobe Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima Jami’in hukumar bayar da agajin, Ibrahim Farinloye, ya ce daga faruwar lamarin zuwa yanzu an ceto mutane 20 jimilla da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai. “Sai dai abin takaicin...
    “Mun zo nan ne a madadin gwamnatin tarayya domin ganowa da kuma jajanta muku rashin da aka yi, muna so mu tabbatar muku da cewa jami’an tsaro za su kawo karshen wannan kashe-kashen na rashin hankali.   “An yi mini cikakken bayani, kuma ina so in tabbatar muku cewa mun fahimci tushen wannan batu. Zamu kama wadanda suka aikata wannan aika-aika.   “Shugaban kasa ya damu matuka, kuma ya umarce mu da mu nemo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci shari’a, muna aiki tare da gwamnatin jihar domin daukar tsarin da zai hana faruwar wannan mummunan lamari, lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan hauka,” inji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tattaunawa da Amurka an yi ta ne cikin yanayi mai inganci da hangen nesa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, wadda Oman ta shiga tsakani a birnin Roma na kasar Italiya, da cewa an gudanar da shi cikin yanayi mai ma’ana da hangen nesa. A cikin wata sanarwa bayan tattaunawar, Araqchi ya yi nazari kan yanayin tattaunawar, inda ya bayyana cewa: “Sun gudanar da shawarwari na tsawon sa’o’i hudu a ci gaba da zaman da aka yi a baya, kuma sun samu kyakkyawar fahimta kan ka’idoji da manufofi da dama.” Ya ci gaba da cewa: An amince da a ci...
    Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Masu sasantawa Iran a birnin Roma suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu Ali Shamkhani mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa: Masu gudanar da shawarwari na Iran sun tafi birnin Roma ne domin yin shawarwari karo na biyu da Amurka kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. Ya ce masu yin shawarwari na Iran suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu. Shamkhani ya yi nuni da cewa: Masu shiga tsakani na Iran suna neman cimma cikakkiyar yarjejeniya bisa ka’idoji guda tara: tsanani, samar da lamuni, dage takunkumi, yin watsi da tsarin Libya/UAE, kaucewa...
    Wasu mutane sun yi shahida tare da jikkata sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Amurka ta kai kan kasar Yemen Ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta sanar a yammacin jiya Asabar cewa: An kashe mutane uku tare da jikkata wasu da dama a hare-haren da jiragen yakin kawancen da Amurka ke jagoranta suka kai a biranen Sana’a, Amran da Ma’arib. Ma’aikatar ta lafiya ta kara da cewa: ‘Yan kasar Yemen 7 ne suka jikkata sakamakon harin wuce gona da irin da Amurka ta kai kan unguwar Al-Nahda da ke gundumar Al-Thawra, sannan wani dan kasar ya jikkata a gundumar Al-Safiyah sakamakon wani hari da aka kai a makabartar Majel Al-Dama da ke babban birnin kasar, kuma ta yi nuni...
    Gwamnatin Rasha ta sanar da amincewarta da tsagaita bude wuta da Ukraine a wannan karo Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da tsagaita bude wuta na kwanaki uku na Ista, inda ya yi kira ga sojojin kasarsa da su kasance cikin shirin ko ta kwana idan Ukraine ta karya yarjejeniyar. Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da sanarwar tsagaita wuta na kwanaki uku na Ista, yana mai kira ga sojojin kasarsa da su “ci gaba da kasancewa cikin shiri don yiwuwar keta yarjejeniyar tsagaita wutan daga bangaren Ukraine, a sanarwar da fadar Kremlin na fitar. Putin ya fada a ranar Asabar cewa: “Tsarin tsagaita bude wuta zai nuna a fili gwamnatin Ukraine tana da ikon warware matsalar cikin lumana.”...
      Kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, don haka masu zuba jari na kasashen waje za su gane wa idonsu irin damammakin da aka samar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan ta’addar ISWAP sun tarwatsa wata gada da ta haɗa garin Ngirbuwa da garin Goneri a Ƙaramar Hukumar Gujiba da ke Jihar Yobe. Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda da ‘yan ta’addan suka lalata gadar nan ta Mandafuna da ta haɗa garin Biu da Damboa a Jihar Borno. JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar bana Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi Majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa harin ya afku ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ta hanyar amfani da wani bam wajen lalata sauran sassan gadar. Wannan aikin ta’addanci ya kawo cikas ga zirga-zirga tsakanin al’ummomin biyu da ma sauran al’ummomin yankin,...
    Labarin harin na zuwa ne kwana daya kafin cika shekara biyu da fara yakin basasar na Sudan tsakanin RSF da rundunar sojin kasar. Da yake magana da BBC a safiyar Lahadi, wani mazaunin Zamzam da ke aiki da wata cibiyar da ke tallafa wa mutane da abinci ya ce an kashe “matasa da yawa”. “An kashe masu aiki a cibiyar, haka ma an kashe likitocin da ke aikin kula da lafiya a cibiyar,” a cewar Mustafa mai shekara 34 cikin wani sakon murya ta WhatsApp. “An kashe kawuna da dan dan’uwana. An raunata mutane kuma babu magani ko asibitin da zai kula da su – suna mutuwa saboda zubar jini. “Har yanzu ana ci gaba kawo hari, kuma muna tunanin...
    Shugaba Vladimir Putin a yau Asabar ya umarci sojojin Rasha da su tsagaita buɗe wuta a Ukraine a wanan ranar ta Ista da kuma gobe Lahadi. Putin ya kuma yi kira ga Kyiv da ta yi hakan, yayin da ake ganin tattaunawar tsagaita buɗe wuta ta ci tura. Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu? Haka kuma, Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaƙi na sama da mutum 500 — kuma mafi girma tun bayan fara yaƙi a tsakanin kasashen biyu. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy, ya ce ƙasarsa ta karɓi sojoji fursunonin yaƙi akalla 277 waɗanda ke tsare a gidajen yarin Rasha, kamar yadda ya...
      Kazalika, ya ce, Sin za ta ci gaba da mai da hankali kan matakan da Amurka za ta dauka, kana za ta dauka matakin mai da martani don kare muradunta idan hakan ya wajaba. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A shekarar 2017, aka dauki matakin fadada kasashen da za su halarci gasar 2026 zuwa 48 bayan duka mambobin Fita sun kada kuri’ar amincewa da matakin, sannan a ranar 15 ga watan Mayu mai zuwa ne za a gudanar da taron FIFA na 75, kuma a nan ne za a tattauna bukatar ta Conmebol. Idan har aka amince da bukatar, gasar ta 2030 za ta kunshi karawa 128, daga karawa 64 da ake yi tsakanin 1998 zuwa 2022. Masu sukar matakin dai na cewa fadada gasar zai rage darajar tsarin da ake bi wajen tantance cancantar shiga gasar, yayin da kungiyar kare muhalli ta FFF ta ce shawarar buga gasar a nahiyoyi uku barazana ce ga muhalli. Tuni dai a...
    Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya shawarci Kanawa kan kada su bari bambance-bambancen aƙidu na siyasa su zama silar hana su zaman lafiya da haɗin kai. Ya faɗi hakan ne a jawabinsa lokacin da ya je yi wa Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ta’aziyar rasuwar mahaifinsa — Galadiman Kano, Abbas Sunusi. Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu? An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar Chadi Shettima ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai, yana mai bayyana Kano a matsayin madubin Arewacin Nijeriya. Yayin da yake nanata muhimmancin zaman lafiya, ya bayyana cewa kada a yi sake da Kano, inda ya buga misali da yadda rashin zaman lafiya ya ɗaiɗaita Jihar Borno. Shettima ya yi...
    Hyda ta bude kungiyar kwallon kafa ta ‘Breakthrough Football Academy’ a Kano watanni shida da suka gabata inda take da burin bai wa Kanawa dama su shiga duniyar wasanni inda a hirarta ta sashin Hausa na BBC ta ce ta zama kociya ce saboda tunanin da take da shi na taimakon al’ummar Kano bisa la’akari da irin taimakon da al’ummar Kano suka yi mata itama. Ta ce “Babban burina shi ne samun wasu daga cikin wadanda nake bai wa horo sun yi fice a duniyar kwallo.” Ta kuma kara da cewa wani karin burin nata shi ne a samu babbar kungiyar wasa ta mata zalla a Kano “Domin a Kano akwai matan da suka iya kwallon kafa amma saboda rashin...
    Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Irna” cewa; An sami cimma matsaya a tsakanin tawagogin Iran da na Amurka akan cewa a ranar Laraba mai zuwa za a dora daga inda akan tsaya a tattaunawar Nukiliya,” Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kara da cewa; Tattaunawar ta gaba za a yi ta ne a tsakanin kwararru, da zai kai ga shimfida ka’idojin da za a dora yarjejeniyar a kansu. A yau Asabar ne dai aka yi tattaunawa karo na biyu a tsakanin tawagogin Iran da na Amurka a cikin ofishin jakadancin kasar Oman dake birnin Rome na kasar Italiya. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da...
    Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa sojansu daya ya halaka a Gaza yayin da wasu 4 su ka jikkata bayan da aka kai wa motar da take dauke da su mai sulke hari. Majiyar ta kuma ce ana ci gaba da yin fada mai tsanani a tsakanin sojojin Isra’ilan da kuma ‘yan gwagwarmaya a yankunan daban-daban na zirin Gaza. Majiyar Falasdinawa ta ce; ‘yan gwgawarmaya sun tarwatsa wata tankar yakin HKI ta hanyar tashin wani bom da aka ajiye a kan hanya. An ga jiragen yakin HKI masu saukar angulu suna jigilar daukar wadanda su ka jikkata sanadiyyar harin. A gefe daya, Falasdinawa da dama sun yi shahada a wasu hare-hare da ‘yan sahayoniya su ka kai akan yankin...
    Tashar talbijin din “News Fox” ta kasar Amurka  mai ra’ayin ‘yan mazan jiya ta watsa wani rahoto da yake cewa; Daga lokacin da Donald Trump ya zama shugaban kasa, sau 6 sojojin Yemen su ka kakkabo jiragen sama maras matuki samfurin Mq9. Rahoton na tashar talabijin din Fox ya kuma yi ishara da yadda sojojin na Yemen su ka kakkabo jirgin sama marasa matuki da marecen juma’a, wanda shi ne karo na 6 tun daga ranar 3 ga watan Maris. Rahoton ya kuma kara da cewa; Kowane daya daga cikin jiragen sama marasa matuki  samfurin mq9 ya kai dalar Amurka miliyan 30.  Bugu da kari rahoton ya kuma bayyana cewa; Sau 35 sojojin Amurka suna kai wa kasar Yemen hare-hare,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An kuma buƙaci a ci gaba da siyasa cikin fahimta da girmama juna domin amfanin Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An kuma buƙaci a ci gaba da siyasa cikin fahimta da girmama juna domin amfanin Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rahotanni na cewa Mataimakin Gwamnan Bauchi, Auwal Mohammed Jatau, ya zabga wa Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, mari saboda kalaman suka da ya yi kan gwamnatin jihar. Wasu rahotanni na cewa Ministan ya yi wasu kalamai na caccaka ga Gwamna Bala Mohammed, lamarin da ya fusata mataimakinsa ya ɗauke Ministan da mari. An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar Chadi JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar bana Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a cikin motar da ke dakon wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, yayin da suke kan hanyar zuwa naɗin sarauta da kuma ɗaurin auren ’yar tsohon gwamnan jihar, Muhammad Abdullahi Abubakar SAN. Aminiya ta ruwaito cewa, a...
    A yayin wannan ziyara har ila yau, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, yakin cinikayya zai gurgunta tsarin cinikayyar kasa da kasa, da haifar da mummunan tasiri a kan tattalin arzikin duniya, da tarnake halaltacciyar moriyar kasashen duniya, musamman ma ta kasashe masu tasowa.   Sai dai kuma, yayin da ake fuskantar karuwar masu nuna ra’ayin kariyar ciniki a duniya, kasar Sin za ta tsaya kan kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, kuma za ta ci gaba da samar da dimbin gudummawa ga yunkurin raya tattalin arzikin duniya, in ji shugaban kasar Sin. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An shiga ruɗu da fargaba a garuruwan ƙasar Chadi da dama, sakamakon jita-jita da kafofin sada zumunta na yanar gizo ke yaɗawa cewa wasu matsafa na satar al’aurar maza. Tun daga birnin Moundou da ke kudancin kasar da lamarin ya fara samun asali, inda wasu matasa hudu suka yi ikirarin cewa an sace musu al’aurarsu ta hanyar bakar tsafi, na yaduwa kamar wutar daji a wasu manyan biranen ƙasar Chadi. Sakamakon jita-jita da bidiyoyi iri-iri da ake yadawa a shafukan sada zumunta, duk da cewa ba a tabbatar da wannan zargi a likitanci ko a hukumance ba, lamarin ya bazu tare da tada hankula har a tsakiyar N’Djamena, babban birnin kasar, inda wasu fusatattun mutane suka yi yunkurin kashe wani...
    Hukumar Shirya Jarrabawa Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta sanya Alhamis, 24 ga watan Afrilu, a matsayin ranar soma jarrabawar wannan shekarar maimakon ranar 25 ga wata da ta fara sakawa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dokta Fabian Benjamin ya fitar ranar Asabar. Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi A cewarsa, an samu sauyin ranar ne domin tabbatar da muhimman matakan da ta ɗauka sun yi daidai da tnade-tanaden sauran hukumomin da za su taimaka mata wajen gudanar da aikin. Dokta Benjamin ya ce a yanzu haka waɗanda za su rubuta jarrabawar za su iya fitar da katin shiga jarrabawar –...
    Dubban jama’a ne suka hallara domin ɗaurin auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi a Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Ministan Lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar. Cikin baƙi akwai Shugaban Kamfanin rukuin Media trust Malam Kabiru Yusuf da sauran manyan baƙi suka hallara a birnin domin ɗaurin auren da kuma naɗin sarautar “Makama Babba I da aka yi wa  tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar. Masu garkuwa za su mutu ta hanyar rataya a Edo – Okepebolo An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a Neja Alhaji Bala Ahmad babban limamin Bauchi ne ya jagoranci ɗaurin auren,  wanda Shettima ya kasance a matsayin waliyyin ɗiyar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masu iya magana kan ce, banza ba ta kai zomo kasuwa. Mai yiwuwa hakan ne ya sa matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka shiga ofishin ’yan sanda, su kuma fita ba tare da wani ya harare su ba, balle ya kama su. ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da ƙwacen waya da fyaɗe kai har ma da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa a tsakanin matasa. NAJERIYA A YAU: Ainihin Abin Da Ke Hana Matan Arewa Koyon Ilimin Kimiyya DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Ko yaya wannan dabara take aiki?...
    Gwoza dai tana daga cikin wuraren da Boko Haram suka mamaye a baya kafin sojoji su ƙwato ta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    To mun san ki a matsayin marubuciyar littafan Hausa. Shin ta ya kika tsinci kanki a duniyar rubutu? Hukuncin Ubangiji, na yi karance-karance da dama a baya, tun ina karamar secondary na fara rubuta labari a paper a shekarar 2016, idan na rubuta sai na ajiye. Lokacin da muka yi hutu da aka dawo aji na Hudu (a kasar Nijar shekara 4 muke yi a karamar secondary) a karamar secondary a lokacin na fara karantawa kawayena, idan an yi break, to bayan na gama karama secondry na ci gaba da rubutun a paper, a shekara ta 2019 na fara rubutu a yanar gizo har na fara yadawa. A 2016 mene sunan littafin da kika fara rubutawa? Gaskiya ba zan iya...
    Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo. An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi. Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, a kan hanyarsu ta zuwa Jami’ar Babcock don taron shekara-shekara na GYC Africa. Kakakin rundunar, SP Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da ceton, ya ce da samu rahoton sace daliban, kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya tura ’yan sanda na musamman tare da ’yan banga da maharba cikin daji domin ceto su da kuma...
    Bada shawara kan abinda ko abubuwan da su daliban suke bukatar zama da babban burin ko wane daga cikinsu,da yadda za su cimma burin abinda suke son zama a gaba. Bada taimakon lokacin da ake fuskantar matsalolin rayuwa da kuma karatu. Yin kwatance da Malamin makarnta wajen koyi da abubuwan da aka ga yana yi,irin hakan na karawa dalibai kwarin gwiwa, wajen daukar mataki kan irin abinda ya dace su yi,na taimaka masu daukar mataki daukar mataki na irin burin da suke bukatar cimmawa akan ilimi. Samar da hanyar tafiya tare da kowa Samar da hanyar da kowane dalibi zai gane tafiyar tare da shi ake yin ta,wannan ma wani abu ne da yake nuna babu wani bambanci kan yadda...
    Fadar Shugaban Ƙasa ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da irin waɗannan labaran ƙarya, tare da kira ga kafafen yaɗa labarai su riƙa tabbatar da gaskiya labari kafin wallafawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An fara gudanar da bukukuwan ranar soji a Iran a ranar 18 ga watan Afrilu ta hanyar gudanar da faretin soja a gaban shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian An fara faretin soji na sojojin kasar Iran a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin birnin Tehran fadar mulkin kasar a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan ranar sojoji ta 18 ga watan Afrilu. A jiya Juma’a 18 ga watan Afrilu ne sojojin kasar Iran suka fara faretin soji na murnar zagayowar ranarsu da kuma irin bajintar jarumtakar sojojin kasar, a kusa da hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke kudancin  babban birnin kasar Tehran. A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA na Iran, faretin ya samu halartar shugaban kasar Mas’ud...
    Kasar Yemen ta sanar da cewa: Amurka ta kaddamar da sabbin hare-haren wuce gona da iri kan garuruwan Sana’a, Sa’dah, da Al-Jawf Mahukuntan Yemen sun sanar da cewa: Amurka ta ci gaba da kai hare-hare kan kasar Yemen, inda ta kaddamar da wasu jerin hare-hare kan garuruwan Sana’a, Sa’dah da Al-Jawf. Wakilin Al-Alam ya ruwaito a yammacin jiya Juma’a cewa: Jiragen saman yakin Amurka sun kaddamar da hare-hare har sau shida a gundumar Bani Hushaysh dake arewa maso gabashin birnin Sana’a fadar mulkin kasar Yemen, inda suka yi luguden wuta a wurare da dama. A lardin Al-Jawf, an kai wasu hare-hare 4 ta sama a gundumar Bart Al Anan da yankin Al-Yatmah da ke gundumar Khab da gundumar Al Sha’af...
    Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da Vinson, gami da harbo jirgin sama kiran MQ-9. Dakarun gwagwarmayar sun bayyana a cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Yahya Sar’ie ya bayyana a tsakanin miliyoyin mutane a dandalin Al-Sabeen a ranar Juma’a cewa: Sun kai wani harin soji a kusa da filin jirgin saman Ben Gurion a yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami na “Zulfiqar”. Dakarun kasar ta Yemen sun tabbatar...
    Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata labarin da karaɗe kafofin sada zumunta cewa sojoji sun hana mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shiga Fadar Shugaban Ƙasa. Labarin da ya tayar da ƙura cewa sojojin sun tare ƙofar shiga fadar shugaban ƙasa da cewa umarni ne daga sama ya koma gidansa da ke makwabtaka da fadar shugaban kasa, zuwa lokacin da Shugaba Tinubu ya dawo daga ziyarar aiki da ya kai ƙasar Faransa. Wata sanarwa da Stanley Nkwocha, hadimin shugaban ƙasa kan yada labarai, ya fitar, ta ce, babu kashin gaskiya a labarin. Sanarwar ta kara da cewa hasali ma, masu yaɗa labarin karya sun ƙirƙirar shi ne da nufin haddasa saɓani tsakanin shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin nasa.