2025-04-22@04:06:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3603

«da matsalar»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Mayakan kungiyar ta’addanci ta ISIS sun sake kunno kai a garuruwan Deir ez-Zor da Hasaka na kasar Siriya Yankunan Deir ez-Zor da Hasakah dake arewa maso gabashin kasar Siriya suna ci gaba da samun karuwar bullar ayyukan ta’addancin kungiyar ISIS tun daga farkon wannan wata. Hare-hare 13 sun kai sune kan Dakarun Syrian Democratic Foeces ta (SDF) ta Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka da kuma fararen hulan yankunan, lamarin da ya janyo hasarar rayuka. A cewar kungiyar kare hakkin bil- adama ta Syria, hare-haren sun bambanta wajen aiwatar da su, daga harin kwanton bauna zuwa na kai hari kai tsaye, wanda ke nuni da yadda kungiyar ta canza yanayin kai hare-hare a yankunan saboda matakan tsaron a garuruwan. Wadannan...
    · Amfani da intanet cikin tsaro: Wayar da kai tana koya maka yadda za ka yi amfani da wayar salula, kwamfuta, da sauran na’urori cikin kwarewa da tsaro. · Sanin sirrinka da darajarsa: Mutum zai fi kulawa da bayanansa na sirri da yadda za su iya amfani da su wajen cutar da shi idan ya samu ilimi. Abubuwan Da Ya Kamata Ka Kula Da Su 1. Kada ka bude kowanne sako ko imel da bai fito daga tushe da ka yarda da shi ba. 2. Kar ka rika danna kowanne link da ba ka tabbatar da amincinsa ba. 3. Rika sabunta (update) wayarka ko kwamfutarka domin gyara kura-kurai na tsaro. 4. Amfani da kalmar sirri (password) mai karfi da bambanta...
     Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka hada da kwamandojin ‘yan tawaye a shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher. Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: A ranar Alhamis ne sojojin kasar Sudan tare da hadin da tallafin dakarun hadin gwiwa na kungiyoyin fafutuka, da hukumar leken asiri ta kasar da ‘yan sanda, suka dakile wani mummunan hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support...
    “Amfani da haraji a matsayin makami don matsin lamba da son rai yana nuni da tsarin siyasa na rashin haɗin kai da kare tattalin arziƙi da kuma zambar tattalin arziƙi. Wannan ba abu ne na adalci ba ko mai kyau – yana nufin zaman ‘Amurka da tafi kowa’ da kuma ƙaruwar ƙarfin Amurka,” in ji shi. Jakadan ya kuma yi gargadi cewa ƙasashe masu tasowa za su fi shan wahala daga wannan tsarin haraji, kuma hakan zai fi cutar da ƙasashen Afrika, ciki har da Nijeriya. Ya bayyana cewa, “Amurka ta ɗauki mataki mara son Rai, na cewa ‘ samun ribar kasuwanci sai an yi zamba’ wanda ya kai ga kai wa ƙasashen Afrika haraji mai yawa, wanda ya saɓa...
    Iran da Amurka za su shiga zagaye na biyu na tattauna batun taƙaita shirin nukiliyar Tehran a yau Asabar. Masu shiga tsakani za su haɗu a birnin Roma bayan zagayen farko na tattaunawar da aka yi a makon jiya a Oman. Ministan harkokin wajen Iran ya ce za a iya cimma yarjejeniya idan Amurka ba ta gabatar da wasu sharuɗa da Tehran ba za ta yi bi ba. Shugaba Trump ya sha yin barazanar yin amfani da ƙarfin soji idan Iran ta ƙi amincewa da wata yarjejeniya. Ana ta samun bayanan da suka ci karo da juna game da abubuwan da Washington za ta gabatar da yarjejeniyar. Tehran ta yi bayani ƙarara cewa ba za ta taɓa yadda da batun...
    Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke nuni da cewa an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, GCON shiga fadar shugaban kasa, inda ta bayyana ikirarin a matsayin shirme, kage da kuma karya gaba daya.   Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa na ofishin mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya sanyawa hannu, ta ce rahoton da wasu shafukan da ba su da tushe suka yada shi, na cikin jerin labaran karya da aka kitsa domin haifar da rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa.   Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan wani yunkuri ne mai rauni na cin mutuncin mutum da ofishin Mai Girma, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima....
    Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su, a wani samame da ta gudanar cikin gaggawa tare da tabbatar da ganin an dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.   A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce a ranar 16 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 1:45 na rana, tawagar hadin guiwa da ta kunshi jami’an ‘yan sanda da kuma jami’an kare hakkin jama’a (CPG) suna sintiri a kan babbar hanyar Anka-Gummi, inda suka gano wata mota samfurin Peugeot 206 da suka yi garkuwa da su a gefen hanya.   A cewar sanarwar, ba tare...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci Kiristoci da su yi tunani a kan darussa, muhimmaci, da kuma kyawawan dabi’u na makon Easter.   Gwamna AbdulRazaq a wani sako da ya aike a Ilorin, ya taya mabiya addinin kirista a jihar da ma fadin Najeriya murnar bikin Easter.   Gwamnan ya ce nasarar da Yesu Kiristi ya samu a fuskantar wahala, wanda bikin Ista ke alamta, ya kamata ya fitar da imani ga Allah da kuma yuwuwar da ba su da iyaka da ke zuwa tare da samun bangaskiya mara girgiza cikin ikonsa.   Ya yi addu’ar Allah ya sa lokacin Easter ya kawo farin ciki da jin daɗi mara iyaka ga kowane gida a jihar da kuma bayansa  ...
    Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Barr. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya mika sakon taya murna ga al’ummar kiristoci a jihar da ma sauran sassan jihar bisa nasarar kammala azumin Easter na kwanaki 40.   A madadin shugabanni da membobin majalisar ta 10, shugaban majalisar ya yaba wa mabiya addinin kirista saboda sadaukarwar da suka yi da kuma ci gaban ruhaniya a wannan lokaci mai tsarki.   Duk da haka ya yaba musu bisa sadaukarwar da suka yi a wannan lokacin kuma fatan sabunta ruhi da aka samu a lokacin Azumi ya kawo zaman lafiya, farin ciki, da wadata ga kowa.   Barr AbdulMalik Sarkin Daji, ya amince da muhimmiyar rawar da shugabannin addinin Kirista ke takawa wajen jagorantar al’ummar Nijar cewa majalisar...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da atisayen harbe-harbe ga sabbin ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar.   Ya ce, atisayen zai fara ne daga ranar 19 ga Afrilu zuwa 11 ga Mayu 2025 a kauyen Tsohon Kafi da ke Birnin Kudu.   A cewarsa, makasudin bayar da horon shi ne don inganta shirye-shiryen gudanar da aiki, da dabarun sarrafa makamai, da kuma kwarjinin sabbin jami’an ‘yan sandan da aka dauka, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da kwarewa da...
    Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo. An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi. Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, a kan hanyarsu ta zuwa Jami’ar Babcock don taron shekara-shekara na GYC Africa. Kakakin rundunar, SP Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da ceton, ya ce da samu rahoton sace daliban, kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya tura ’yan sanda na musamman tare da ’yan banga da maharba cikin daji domin ceto su da kuma...
    Shugaban ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin cewa, ako da yaushe, kofar Hukumar ta NPA, bode take domin hadaka wacce ta zarce ta gudanar da baje koli. Dakta Dantsoho ya kara da cewa, an samar da tsarin na EPT domin a tabbatar da cewa, ana fitar da kaya zuwa waje, ta hanyar yin amfani da na’urar zamani. “Wannan na zai taimaka matuka wajen kaucewa samun jinkiri da kuma mai-maita aiki da Hukumar ta saba fuskanta a baya,” A cewar Dantsoho. Kazalika, Dantsoho ya bayyana cewa, domin a samu sauki wajen kai kaya a tsakanin masu kananan da matsakaitan sana’oi, musamman duba da cewa, tsarin na EPT, zai taimaka matuka ga guraren da ake adana kaya a...
        Kungiyar Sarakunan Afirka ta jaddada muhimmancin gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a Najeriya. Da yake jawabi a wajen bikin nadin Alhaji Aliyu Dauda a matsayin Sardaunan Najeriya na farko, wanda aka gudanar a Yankari, Jihar Bauchi, Shugaban Kungiyar, Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen ci gaban kasa. Alhaji Ibrahim Haruna ya ce, masarautun ba wai kawai suna zama uba ga al’umma ba ne, kawai har ila yau suna bada gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa. Ya bayyana cewa goyon baya da gudunmawar da Alhaji Aliyu Dauda ke bayarwa ga masarautun gargajiya, musamman a Arewacin Najeriya, ne ya sa aka zabesa domin karbar wannan gagarumar...
    Jam’iyyar adawa ta SDP buƙaci Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin siyasa a Najeriya su dai shagala da batun zaɓen 2027, su mayar da hankalinsu wajen magance matsalar tsaro da ke ƙara mayar da ƙasar tamkar filin kisa. SDP ta bayyana cewa kashe-kashe ɗaruruwan mutane da ke faruwa a faɗin ƙasar nan – Arewa da Kudu – musamman a makonnin da suka gabata, na da matuƙar tayar da hankali. Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na SDP, Araba Rufus Aiyenigba, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a, cewa abubuwan takaicin sun hada da da kisan mafarautan Jihar Kano a jihar Delta, baya ga ayyukan ’yan ta’adda da hare-haren da a ka yi wa mutane sama da 100...
    Wannan nasarar ta nona irin namijin kokarinda Bankin ya yi na kara habaka samar wa da kansa kudaden shiga duk da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta. Bugu da kari, kadarorin Bankin sun karu zuwa jimmlar kaso 47 daga Naira tiriliyan 20 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 30, a shekarar 2024. Kazalika, abokan huddar Bankin sun karu zuwa kashi 45, wanda kudaden da suka ajiyarsu ya karu zuwa Naira tiriliyan 22 a shekarar 2024, sabanin yadda ya ke kan Naira tiriliyan 15, a shekarar baya. Duk da samun hauhawan farashin kaya a kasar, Bankin ya samu karin kudaden shigar Bankin, sun karu zuwa kashi 38.9, sabanin kashi 36.1. Bankin na da yakinin samun ribar shiyar da ta...
    Ilimi na da muhimmanci wajen gina al’umma, amma ga daliban Makarantar Firamare ta Bare a karamar Hukumar billiri, Jihar Gombe, wannan lamari ya zama kamar mafarki mai wahalar tabbatuwa. Duk da ikirarin da Gwamnatin Jihar Gombe ke yi na cewa, tana fifita ilimi ta hanyar manyan ayyuka kamar gine-ginen makarantu masu hawa biyu a kowace mazabar Sanata, a halin da ake ciki a Makarantar Firamare ta Bare ba ta san da hakan ba. Wannan makaranta tana nuna sakaci da gazawar masu mulki. An kafa makarantar ce a shekarar 2005 karkashin shirin Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Gombe (SUBEB). Tun daga lokacin har zuwa yanzu, ba a taba samun gyara ko ci-gaba ba. Maimakon zama alamar ci-gaba, makarantar ta...
    A cewarsa, hakan ya kuma jawo lalata gonakin na Tumatirin da ke wasu sassan jihar. Yadakwari ya kara da cewa, hakan ya tilastawa manoman Tumatir da dama a jihar dakatar da nomansa, duba da irin mummunar asarar da suka yi. Ya ci gaba da cewa, manoman Tumatir da suka fara lura da barkewar cutar ce suka sanar da kungiyar, inda kuma kungiyar ta shigo cikin lamarin ta kuma gano cewa, cutar ce ta sake dawowa gonakin manoman na Tumatir. A cewarsa, maoman Tumatir a jihar, sun shafe shekaru suna yin asara sakamakon barkewar cutar, wanda hakan ya sanya wa manoman rashin sha’awar ci gaba da noman nasa. “Mun gano bullar annobar ce a wasu gonakin da aka shuka Tumatir a...
    Yau Asabar Washington da Tehran, ke tattauanwa a birnin Rome na kasar Italiya, wace ita ce ta biyu a shiga tsakanin kasar Oman kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Tattaunwar wacce ba ta gaba-da-gaba ba an gudanar da irin ta a ranar Asabar data gabata a birnin Muscat na kasar Oman, inda bangarorin biyu suka bayyana tattaunawar da mai armashi. Gabanin tattaunawar ta yau, Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce akwai yuwuwar kulla yarjejeniya da Amurka idan har Washington ba ta gabatar da wasu bukatu na da suka wuce da tunani ba”. Araghchi ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov, a ranar Juma’a a birnin...
    Iran ta yi tir da Allah wadai da kakkausan lafazi da harin Amurka na baya baya nan kan tashar mai ta kasar Yemen, wanda ya yi sanadin mutuwar gomman mutane tare da lalata dukiya mai yawa. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghai, ya kira harin da Amurka ta kai a matsayin keta kundin tsarin mulkin MDD da kuma dokokin kasa da kasa karara. Misata Baghai ya ce : “Hare-haren da Amurka ta kai kan kasar Yemen, a matsayin cikakken goyon bayanta ga mamaya da kuma kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniya ta ke yi a yankunan Falasdinawa, ya sanya Amurka ta zama mai hannu dumu-dumu a kan laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Falastinu da kuma yankin.” Akalla mutane 80...
    Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya yi Allah wadai da kalaman da kiraye kirayen da ake na “kwance damarar” kungiyar Hizbullah, yana mai kiransa da cewa wani yunkuri ne na raunata kasar Lebanon da kuma ci gaba da fadada manufofin Tel Aviv. Sheikh Naim Qassem ya bayyya hakan ne a wani jawani da ya gabatar da kai tsaye ta talabijin jiya Juma’a. Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a karshen shekarar da ta gabata da nufin kawo karshen kazamin rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 4,000 a kasar Labanon. Sheikh Qassem ya jaddada cewa ci gaba da kokarin da...
    Kasashen Nijar da Najeriya sun sha alwashin inganta dangantaka a tsakaninsu domin cin moriyar juna a matsayinsu na makobta. Wannan bayyanin ya fito bayan tattaunawa data wakana tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen biyu a birnin Yamai bayan kwashe watanni ana takaddama. Yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai Nijar an gudanar da wani babban taro tsakanin shugabannin diflomasiyyar kasashen biyu don sake farfado da hanyoyin hadin gwiwa a bangarori da dama da suka hada da tattalin arziki da tsaro. Ministan harkokin waje da hadin gwiwa na  Nijar Bakary Yaou Sangaré da takwaransa na Najeriya Yusuf Maitama Tuggar sun gana a ranar 16 ga ga watan nan, lamarin dake nuni da wani gagarumin sauyi na dangantakar da ke tsakanin...
    Amurka ta sanar cewa ta rage yawan sojojinta a kasar Syria da rabi, tana mai cewa ta yi nasarar yaki da kungiyar IS, duk da cewa kungiyoyin masu da’awar jihadi na ci gaba da fafutuka a wannan kasa mai rauni. Wannan shawarar ta zo ne kusan watanni uku bayan hawan Donald Trump kan karagar mulki, bayan da ya dade yana adawa da kasancewar Amurka a can. Amurka dai ta shafe shekaru da dama tana da sojoji a Syria, a matsayin wani bangare na kawancen kasashen duniya da ke yaki da ISIS. A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon Sean Parnell ya fitar, ya ce za a rage yawan dakarun Amurka a Siriya zuwa kasa da dakaru...
      Makera, Jihar Kaduna – Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya halarci bukukuwan Easter tare da al’ummomin Kiristoci na Gundumar Makera, inda ya bukaci su yi amfani da lokacin wajen tabbatar sa saƙon bangaskiya, yabo, da sadaukarwa da ke tattare da bikin. A jawabin da ya gabatar, Hon. Liman ya jaddada muhimmancin bikin Easter a matsayin lokaci na sabunta dogaro da Allah. Ya kuma bukaci mabiya addinin Kirista da su rungumi koyarwar hakuri, kauna, da kuma fifita bukatun wasu akan nasu. Kakakin ya kuma yi kira ga daukacin jama’ar Jihar Kaduna da su ci gaba da bunkasa zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da bambancin addini, kabila ko ra’ayin siyasa ba, yana mai...
    Bisa labarin da babban bankin jama’ar kasar Sin ya fitar, ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2025, jimillar cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen waje 1,160 ne suka shiga kasuwar hada-hadar lamuni ta kasar Sin, wadanda suka hada da cibiyoyin hada-hadar kudi masu zaman kansu da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasuwanci a kasashe da yankuna fiye da 70, wadanda ke rike da takardun lamuni da yawansu ya kai yuan tiriliyan 4.5, adadin da ya karu da sama da yuan biliyan 270 daga karshen shekarar 2024. Kazalika, jimillar darajar kasuwar lamuni ta kasar Sin ta kai yuan tiriliyan 183, wanda ke matsayi na biyu a duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Bugu da kari, saboda karancin masu sayen Kwan, musamman sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi, ana kara samun masu sayen Kwan don amfani da shi, wanda hakan ya sanya ake ci gaba da samun Kwan da ba a sayar ba. Misali, a makwanni biyu da suka gabata a garin Jos, an samu matukar raguwar farashin Kwan, inda ake sayar da shi kasa da Naira 3,900 zuwa Naira 4,000. Sai dai, a wannan makon an dan samu karin farashin, wanda ya kai daga Naira 4,200 zuwa 4,300. Daya daga cikin irin wadannan masu kiwon Kajin na gidan gona, Muhammad Bello Ibrahim, ya bayyana bacin ransa kan yadda wannan matsala ke ci gaba da faruwa. “Masu sana’ar kiwon Kajin...
    Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane da aka samu da laifi a jihar za su fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya. Okpebholo ya bada tabbacin a shirye yake ya sanya hannu akan sammacin kisa na waɗanda aka yankewa hukunci a jihar idan kotu ta same su da laifi. An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a Neja PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike Gwamna Okpebholo ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Uromi, inda ya tattauna da shugabanni da ’yan uwa na yankin unguwar ’yan Arewa mazauna Esan. “Ku tuna cewa Majalisar Dokokin Jihar Edo (EDHA) ta zartar da wani ƙudiri...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kazalika, Injiniya Xie ya kara da cewa, a cikin rubu’in farko na bana, sashen masana’antu na kasar Sin ya taka rawar gani wajen samun ci gaba ba tare da tangarda ba sakamakon ingantuwar tsari da zurfafa ayyuka wajen samar da sabbin ginshikan bunkasa ci gaba mai inganci. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An tsinci gawar wani tsoho mai suna Haruna Abdullahi mai shekara 75 daga garin Gumel na Jihar Jigawa a ƙofar babbar kasuwar Kure Ultra Modern Market da ke Minna a Jihar Neja. Babu wanda zai iya cewa ga musabbabin mutuwarsa, amma ’yan kasuwa sun shaida wa Daily Trust  cewa, an tsinci gawarsa da safiyar ranar Juma’a a babbar ƙofar shiga kasuwar. Ya kashe masoyin tsohuwar matarsa bayan sakinta a Neja PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike Kakakin rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin. Ya ce, “A yau Juma’a 18/4/2025 da sanyin safiya, an tsinci gawar wani wanda aka bayyana sunansa da Haruna Abdullahi mai kimanin shekara 75...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Duk da cewa Atiku ya dage yayin tattaunawar da ya yi da manema labarai bayan ziyarar cewa ganawar ba ta batun siyasa ba ne, amma jawabin El-Rufai ya nuna karara akwai siyasa a cikin ganawar. Bayan ziyarar ‘yan adawa kwanaki kadan da na gwamnonin APC, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya isa gidan Buhari sa’o’i kadan bayan tawagar Atiku, wanda ya kara tsananta siyasa. Ya kuma ba da tabbaci ga ra’ayin cewa shugabannin jam’iyyar APC sun damu da siyasar tsohon shugaban kasar. Masu lura da al’amura siyasa sun bayyana cewa kalaman da Ganduje ya yi bayan ganawar, ya tabbatar da cewa APC na yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa Buhari ya kasance tare da jam’iyya...
    Waɗanda suka take wa Ministan sawu a tafiyar su ne jagororin hukumomin yaɗa labarai da wayar da kai da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa. Ya yi zama daban-daban tare da ƙwararru inda suka tattauna kan yadda za a inganta ƙwarewa da kuma kayan aiki na zamani na kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya.   Ya ce: “Ina sanar da ku waɗannan abubuwan ne domin jaddada ƙudirin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an samu cigaba mai ɗorewa a fannin watsa labarai a ƙasar nan.   “Wannan ne ma ya sanya muke gudanar da irin wannan taron bita na ministoci, da kuma shirin ƙaddamar da Taron Tattaunawa da Jama’a a sassan ƙasar nan nan gaba kaɗan.” Idris ya kuma...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata halarci zaman tattaunawa da kasar Amurka kan shirin kasar na makamashin Nukliya tare da fatan bangaren Amurla ma tana bukatar cimma yarjeniya da ita, matukar Amurka bata kawo wani abu wand aba zai yu Iran ta amince ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin Mosco a lokacinda shi da tokwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov suke amsa tambayoyin yan jarida. Ministan ya kara da cewa tawagarsa zata je taron birnin Roma tare da fatan tattaunawar zata yi kyau. Ya kuma kara da cewa takunkuman tattalin arziki mafi muni wanda Amurka ta dorawa kasar da kuma yin...
    Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan birnin Telaviv da kuma kan jirgin yakin Amurka saboda tallafawa falasdinawa a Gaza, da kuma maida martani kan hare-haren Amurka kan kasar a jiya Alhamis. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar na Yemen Burgediya Janar Yahayah Saree yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa sojojin kasar ta yemen sun cilla makami mai linzami samfurin Zulfikar kan wani sansanin sojojin HKI a kusa da tashar jiragen sama na Bengerion dake birnin Yafa (telaviv. Saree ya kara da cewa sojojin, har’ila yau sun kai wasu hare-hare kan jiragen yaki masu daukar jiragen saman yaki na Amurka Harry Truman da kuma USS...
    Hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kaiwa lardin Hudaida ya karu zuwa 74. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnmatin kasar ta Yemen na fadar haka a yau Jumma’a ta kuma kara da cewa dukkan mutanen da suka mutu a hare-haren jiragen yakin Amurka a cibiyar man fetur na Ras Isa a birnin Hudaida fararen hula ne. babu wani mayakin kungiyar Ansarulla ko guda a cikinsu. Labarin ya kara da cewa jiragen yakin Amurka wadanda suka taso daga jiragen ruwa masu daukar jiragen sama na Amurka masu suna USS Harru Truman da kuma USS Carl a tekun red sea, sau kai hare kan ras Isa ne har sau biyu, hare na biyun ya fada ne kan...
    Kasar Chaina ta musanta zargin shugaban kasar Ukraine ga kasar, dangane da tallafawa kasar Rasha da makamai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar wajen kasar China Lin Jian yana fadar haka a safiyar yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasar China bata taba daukar bangaren a yakin na Ukraine ba, kuma ra’ayinta shi ne shiga tsakanin don kawo karshen yakin. Kafin haka dai shugaban kasar Ukraine Volodimir Zelesky ya zargi gwamnatin kasar China da tallafawa kasar Rasha da makamai a yakin da kasarsa take fafatawa da ita. Zelesky ya ce a wannan karon kasar China ta aikawa Rasha makaman Atilari da kuma PorwerGun. A can baya ma gwamnatin kasar ta Ukraine ta zargi kasar...
    Wani mutum mai suna Muhammad Ma’aba daga ƙauyen Fujeregi da ke Ƙaramar hukumar Gbako a Jihar Neja, ya mutu a hannun tsohon mijin matar da yake shirin aura. Rahotanni sun bayyana cewa, wata Ƙungiya ƙarƙashin jagorancin tsohon mijin matar mai suna Alhaji Yikangi, daga ƙauyen Yikangi Chikan ne suka kai wa Ma’aba hari a tsakanin garin Saganuwa da Fujeregi. PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, tsohon mijin ya saki matar mai suna Fatima Suleiman sau uku, amma ya dage cewa ba za ta ƙara aure ba — ko da ta samu sabon mai neman aurenta....
    Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancinta har kimani 30 a kasashen duniya, amma mafi yawansu a kasashen Afirka. Shafin yanar gizo na labarai Afrika News ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurkan na fadar cewa gwamnatin shugaban Trump tana son ta rage yawan kashe kudade a ma’aikatar don amfani da su a cikin gida. Labarin ya kara da cewa gwamnatin tana son rage kudaden da ma’aikatar take kashewa a kan ofisoshin jakadunsu da kasha 50% da kuma rage tallafin da take bawa wasu kungiyoyi a wadan nan kasashe har da kasha 75%. Labarin ya kara da cewa kasashen da shirin ya shafa dai akwai  Lesotho, Eritrea, Afrika ta tsakiya, Congo Brazavile, Gambia,...
    A cikin dan kankanin lokacin da wannan hukuma ta fara aiki, ta horar da matasa sama da 100,000 horo kan shirye-shiryen koyon sana’o’i daban-daban a fannonin noma, ICT, kananan sana’o’i da dai sauran su, gwamnatin jihar ta bayar da tallafi da jarin sama da Naira biliyan 1.7 ga wadannan matasa domin fara sana’o’i. Har ila yau, ya saukaka wa wadannan matasa rayuwa sa suka cancanta a cikin jihohi da tarayya. Jihar jigawa jiha ce mai girma ta kuma yi fice a fannin noma a kokarin gwamnati na inganta rayuwar al’umma ta hanyar sabbin manufofin noma da ya zama abin a yaba. Domin tabbatar da samar da wadataccen kayan aikin noma akai-akai, gwamnatin jihar ta zuba Naira biliyan 5 ga kamfanin...
    Ndume, ya yaba wa jarumtakar dakarun Nijeriya, amma ya buƙaci ƙarin matakan tsaro. Ya buƙaci gwamnati ta taimaka wa ƙungiyoyin tsaron al’umma da kayan aiki da makamai na zamani. Wannan harin na daga cikin jerin hare-haren da ake fama da su a Jihar Borno a cikin ‘yan kwanakin nan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe a ranar Alhamis ta tabbatar da cewa an samu kwanciyar hankali a unguwar Otobi da ke Ƙaramar hukumar Otukpo biyo bayan wani mummunan hari da ya tilastawa mazauna garin barin gidajensu. Kakakin rundunar ’yan sandan, CSP Catherine Anene a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakiliyarmu, ta kuma yi watsi da rahoton sabbin hare-haren da aka kai kan unguwannin Emichi, Okpomaju da Odudaje, inda ta bayyana su a matsayin rahoton ƙarya don yawo tsoratar da jama’a. An kashe sojoji, fararen hula da dama a Borno ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista “Unguwar Otobi yanzu akwai kwanciyar hankali, mun bar wasu jami’anmu tun ranar Laraba ana gudanar da bincike,” in ji...
    Ya yi bayanin cewa aikin hanyar mai nisan kilomita 700 da ya tashi daga Abuja ya wuce Kaduna ya nufi Zariya zuwa Kano zai yi matukar rage yawan aukuwar hatsari da cunkoson ababen hawa da zarar aka kammala shi. “Muna da sashe na 1, 2, 3. Sashi na 1 yana Abuja da Neja, sashe na 3 kuma yana Kano, kuma sashen Kano da ke tsakanin Zariya zuwa Kano tuni Julius Berger ya kammala shi, don haka gaba daya titin, 350, shi ne kilomita 240 da Julius Berger ya kammala. “Sauran kilomita 140 da 2, 240 ta 2 shi ne 480. 140 ta 2 shi ne 280. Amma shugaban kasa ba kawai kammala 280 din ne ba, ya ma kara kusan...
    Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba. Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce maharan sun mamaye unguwannin ne da misalin ƙarfe 11:15 na daren Alhamis. Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana Matan da suka tsira daga Boko Haram na buƙatar tallafin musamman Ɗaya daga cikin majiyar sojojin ta ce, kafin a aike da wata tawagar sojoji daga Gwoza, maharan sun riga sun afkawa jama’a  da sansanin sojan Yamtake. “Muna jiran tawagar masu ƙarfafa musu su...
    Ita Jihar Yobe,rashin biyan sabon mafi krancin albashi da tsohon na Naira 30,000 ga Malaman makarantun ta na Firamare da Sakandare, hakan ta kasance ne saboda rashin amincewa tsakanin Kungiyar NUT da kuma Kungiyar ma’aikatan Kananan Hukumomi ta kasa (NULGE). A ma’aikatar ilimin bai daya ta Jihar Abia, bangaren Kungiyar Malaman makaranta NUT, da reshen Kungiyar kwadago ta kasa (NLC), LEADERSHIP ta Lahadi ta gano cewa har yanzu Gwamntin Jihar bata fara biyan mafi karancin albashin ba. An samu tsaikon yin hakan ne saboda niyyar ita gwamnatin ta dauki su Malaman makaranta matsyin kwararru ta cire daga tsarin albashi na ma’aikatan gwamnati,inda za ta fara biyansu da tsarin albashi na Malaman makaranta(TSS). Kamar yadda Shugaban kungiyar kwadago na Jihar NLC,Okoro...
    Jawabin shugaban majalisar, ya biyo bayan dambarwar hankalin al’ummar kasar ne, bayan shelar ranar 18 ga watan Maris da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na ayyana dokar ta-baci na tsawon wata shida a Jihar Ribas. Matakin ya zo ne daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari, inda aka dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara tare da rusa majalisar dokokin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Maimakon ya bai wa babban jami’in nasu kudin ya raba wa mutanensa, sai ya zabi rarraba musu shi da kansa”, kamar yadda wata majiya ta shaida wa wannan jarida. Sai dai, wata majiyar ta shaida wa wakilinmu a ranar Larabar da ta gabata cewa, an gayyaci ‘yansandan ne zuwa babban birnin tarayya Abuja, domin ladabtar da su. An gayyaci jami’in da sauran yaransa zuwa hedikwatar ‘yansanda da ke Abuja, domin daukar matakan ladabtarwa, in ji majiyar. Kamar yadda siginal mai dauke da kwanan wata na ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, wadda LEADERSHIP ta samu, ya nuna cewa; ‘yansandan da shugaban tawagarsu, DSP Aliyu Adejembi, za su bayyana a hedikwatar ‘yansan da ke Abuja, domin amsa tambayoyi kan rashin da’a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta tsakiya Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar dogaro da karfinsu a hade ba tare da bukatar shiga tsakani daga kasashen waje ba. Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya tarbi ministan tsaron kasar Saudiyya Khalid bin Salman a yammacin jiya Alhamis, wanda ke ziyarar aiki a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dauke da wata babbar tawagarsa. Shugaban na Iran ya jaddada cewa Iran ta kuduri aniyar karfafa alakar ‘yan uwantaka a tsakanin kasashen musulmi. Pezeshkian ta kara da cewa: Saboda wata wasiyya ta...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar ba na kai tsaye ba da Amurka a birnin Roma a ranar Asabar Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa zai tafi birnin Roma a ranar Asabar domin halartar zagaye na biyu na shawarwari ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai jaddada cewa sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha ya kunshi muhimman batutuwa. A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA, Araghchi ya ce: Roma ba ita ce mai masaukin baki ba, a’a, a maimakon haka, wajen da za a yi shawarwarin, gwamnatin Oman ce ta kasance mai daukar nauyin shawarwarin ba na...
    Adadin wadanda suka mutu sakamakon luguden wuta da Amurka ta yi kan tashar jiragen ruwan Ra’as Issa ta Yemen ya kai mutane 38 Ofishin kula da kiwon lafiya na lardin Al Hudaidah ya watsa rahoton cewa: Adadin mutanen da suka yi shahaida da wadanda suka jikkata sakamakon harin da Amurka ta kai kan cibiyar man fetur ta Ra’as Issa da ke lardin Al-Hudaidah a yammacin kasar Yemen ya karu zuwa shahidai 38, tare da jikkata sama da mutane 100. A yammacin jiya alhamis ne rundunar kawancen da Amurka ke jagoranta ta aikata wani mummunan laifi kan fararen hula a gundumar Al-Hudaidah da ke yammacin kasar Yemen. Majiyoyin cikin gida sun shaidawa Al Masirah Net cewa: Jiragen yakin kawancen da Amurka...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Tal al-Za’atar da ke gabashin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza. A cewar majiyoyin yankin, gidan da aka kai harin na dangin Nasiyo ne, kuma yana dauke da ‘yan gudun hijira daga iyalai sama da biyar a cikinsa, inda harin ya turbude su a karkashin baraguzan gine-gine.
    Masu wannan fahimta sun yi imanin cewa duk lokacin da mutum ya ji baya son wani abu to a wurinshi wannan abin ba mai kyau ba ne. Haka nan kuma duk lokacin da mutum ya ji cewa ga wani abu amma shi ne ya kwanta mashi, toh wannan abin shi ne mai kyau. Babban misalin da wadannan masu ra’ayi suke jaddadawa da nanatawa a kullum shi ne cewa a lokacin da mutum ya yi tsammanin cewa wani abu na da kyau a ra’ayinshi, to idan ya je cikin wata al’ummar zai tarar da cewa wannan abin barna ko wani abin ki. Misali da shan giya, caca da sauransu. Da irin wannan nazari ne aka samar da mafi shaharan nazariyyar nan...
    Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na kawo sauyi da kuma zamanantar da kafafen yada labarai na Najeriya da watsa shirye-shirye ta hanyar hadin gwiwa da inganta fasaha.   Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ne ya bayar da wannan tabbacin a taron manema labarai na 2025 da aka gudanar a cibiyar ‘yan jarida ta kasa da ke Abuja ranar Alhamis.   Da yake jawabi bayan dawowar sa daga taron kungiyar masu yada labarai na duniya (NAB) a birnin Las Vegas na kasar Amurka, ministan ya ce taron mai taken “Fasahar, The Trend, The Future,” ya samar da wani dandali na yin cudanya da masu ruwa da tsaki a duniya kan sabbin abubuwa da suka...
    Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Zamfara, ta tura jami’ai 415 a fadin jihar domin tabbatar da tsaro a duk lokacin bukukuwan Easter.   Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar jihar, ASCII Umar Mohammad M. ya fitar, ya ce jami’an sun jibge a wuraren ibada daban-daban da sauran muhimman wurare a fadin kananan hukumomi 14 na jihar domin tabbatar da tsaro da kuma gudanar da bukukuwan lafiya.   A cewar sanarwar, kwamandan jihar, Sani Mustapha, ya jaddada kudirin hukumar NSCDC karkashin jagorancin kwamandan Janar, Dakta Ahmed Abubakar Audi, na magance matsalolin tsaro a fadin kasar nan.   Ya kuma tabbatar da cewa rundunar a jihar Zamfara ta shirya...
    Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gombe, Bello Yahaya ya bayar da umarnin tura isassun jami’ai a fadin jihar domin samar da isasshen tsaro kafin bukin Easter, da kuma bayan bikin Easter.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar a Gombe.   A cewarsa, an tura jami’an dabarun dakile hare-hare zuwa muhimman wuraren da suka hada da wuraren ibada, wuraren shakatawa, kasuwanni, da sauran wuraren taruwar jama’a.   Ya kuma ce, kungiyoyin sintiri da jami’an tsaron cikin za su kasance a kasa domin sanya ido kan ayyukan da kuma gaggauta daukar matakin magance duk wata matsala idan ta taso.   Kwamishinan ya lura cewa rundunar...
    Rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai ta yi nasarar aiwatar da wasu hare-hare ta sama guda biyu, inda ta auka wa maboyar ‘yan ta’adda a yankin Sambisa na jihar Borno da kuma Kudancin Tumbun.   A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, ya ce harin farko ya afku ne da misalin karfe 5:30 na safe a Kollaram- sanannar tungar ‘yan tada kayar baya, a ranar 15 ga watan Afrilu, inda aka kawar da mayaka da dama tare da lalata muhimman ababen more rayuwarsu.   Farmaki na biyu kuwa ya biyo bayan da misalin karfe 3:55 na rana a garin Arra na Sambisa, bayan binciken sirri da bincike...
    Masarautar Gumel ta ce za ta bayar da dukkan goyon baya da hadin kai da ake bukata domin ci gaban yankin kasuwancin da ba shida shinge na Maigatari a jihar Jigawa.   Mai Martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmad Mohammad Sani ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin Jiha mai kula da shiyyar fitar da kaya ko kasuwanci maras shinge na Maigatari a fadar sa.   Ya ce, nan ba da dadewa ba majalisar masarautar za ta shirya taro da hakiman Gundumomi da Unguwanni da Kauyuka domin fadakar da al’ummarsu kan gudunmawar da suke bukata domin samun nasarar wannan yankin.   Sarkin wanda ya samu wakilcin Dallatun Gumel, Alhaji Musa Ayuba ya ce aikin noman rani da...
    Cibiyar Nazarin Dimokuradiyya ta Aminu Kano a Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta shirya taron shekara-shekara karo na 23 don tunawa da cika shekaru 42 da rasuwar Malam Aminu Kano.     A nasa jawabin, Shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya jaddada muhimmancin taron shekara-shekara wajen kiyaye manufofin da Malam Aminu Kano ya tsaya a kai.   Farfesa Haruna Musa wanda mataimakin shugaban jami’ar kula da harkokin ilimi ya wakilta, ya bayyana cewa jerin laccoci an yi niyya ne don ba da damar fahimtar juna dangane da yanayin tarihi.   “A ci gaba da kokarin da jami’ar mu ke yi na karfafa al’adun dimokuradiyyar Najeriya, muna gayyatar manyan mutane duk shekara don gabatar da laccoci a gidan Mambayya kan...
    Gwamnatin jihar Neja za ta fara gudanar da zirga-zirgar jiragen sama daga sabon filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu da aka kaddamar a Minna, tare da kamfanin Overland Airways Limited.   Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in kula da zirga-zirgar jiragen sama na Overland, Captain Edward Boyo ya raba wa manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja.   Ya bayyana cewa an shirya fara jigilar jiragen a ranar 23 ga Afrilu, 2025, wanda zai hada Minna zuwa Abuja da Legas, manyan biranen siyasa da kasuwanci na Najeriya.   Kyaftin Boyo ya bayyana cewa, haɗin gwiwa da kamfanin na Overland Airways—kamfanin jiragen sama masu zaman kansu mafi dadewa a Najeriya—yana wakiltar wani muhimmin ci gaba...
    Hakazalika, kamfanoni 43 da aka bayyana sun ba da shawarar raba jimillar Naira tiriliyan 1.678 ga masu hannun jarinsu, tare da yaba wa abokan huldarsu. A cikin 2024, bangarori na kasuwancin Nijeriya ya gamu da kalubale masu yawa na tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa wadanda suka yi matukar tasiri ga ayyukansa. Masana’antun sun fuskanci matsin lamba daga hauhawar farashin kayayyaki, faduwar darajar Naira, hauhawar kudin ruwa, karin kudin wutar lantarki, karancin tallace-tallace, yawan haraji da kuma tabarbarewar tsaro. A cikin wannan babbana al’amari, kamfanoni a manyan sassan tattalin arziki sun ba da rahoton sakamako mai karfi na kamfanoni da kuma bayar da lada ga masu hannun jari. Idan za a kimanta halin da ake ciki, babban jami’in...
    Akwai kuma Sanata Adeniyi Adegbonire dan jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya, Sanata Seriake Dickson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Bayelsa ta Gabas, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan jam’iyyar APC, daga mazabar Borno ta tsakiya. Sauran sun hada da; Sanata Banigo Ipaligo dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Ribas ta Yamma, Sanata Jarigbe Jarigbe dan jami’yyar PDP, daga Koros Riba ta Arewa, Sanata Ekong Sampson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom ta Kudu, Sanata Sani Bello dan jami’yyarAPC, daga mazabar Neja ta Arewa sai kuma Sanata Aniekan Bassey, dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom. Majalisar ta kafa wannan kwamtin ne, biyo bayan kudurin da Sanata Aniekan Bassey na mazabar Arewa da Gabas daga Akwa Ibom, ya gabatar mata...
    Uwargidan Gwamnan Sakkwato Hajiya Fatima Ahmad Aliyu ta ɗauki nauyin ragon suna da abinci da kayan barka ga duk wata mata da tahaifi ’yan uku a jihar. Hahiya Fatima ta sanar da haka ne a ranar Laraba nan a lokacin da ta yi takakkiya takanas zuwa garin Ƙaurar Yabo da ke Ƙaramar Hukumar Yabo domin kai ragunan suna da kayan barka da na suna ga wata mai jego mai suna Malama Bela’u, wadda ta haifi ’yan uku a garin. Daga cikin kayan da ta kai wa mai jego kyauta, har da buhun abinci goma da akwatunan tufafi da tsabar kudi Naira dubu dari biyar. A bayanin da mataimaka wa gwamna kan harkokin kafofin...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa, Iran a shirye take yin aiki tare da Saudiyya a dukkanin bangarori, domin cin gajiyar al’ummomin kasashen biyu da ma duniyar musulmi, tare da yin ishara da cewa, dukkanin ci gaban da Iran ta samu a dukkanin bangarori na ilimin kimiyya da fasaha, a shirye take ta taimaka ma  Saudiyya a wadannan bangarori. Wannan na zuwa ne a lokacin da Ministan tsaro Yarima Khalid bin Salman dan uwa ga Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya gana da Ayatollah Khamenei a Tehran da yammacin jiya Alhamis don mika sakon Sarki Salman na Saudiyya. Jagoran ya ce: “Mun yi imanin cewa dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta...
    Shugaban ofishin siyasa na Hamas Khalil al-Hayya ya sanar da cewa, kungiyar a shirye take ta shiga cikin tattaunawa don tabbatar da cimma cikakkiyar yarjejeniyar musayar fursunoni, da tsagaita bude wuta a Gaza, da janyewar Isra’ila daga yankin, da kuma kaddamar da yunkurin sake gina yankin. A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar, al-Hayya ya bayyana cewa, kungiyar Hamas a shirye take ta sako dukkan fursunonin da ‘yan gwagwarmaya ke tsare da su domin samun adadin fursunonin Falasdinawa da aka amince da su a halin yanzu da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila. Ya jaddada cewa, dole ne irin wannan yarjejeniyar ta hada da dakatar da yakin gaba daya, da janyewar sojojin Isra’ila baki daya daga Gaza,...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiyya za su iya zama abin koyi ga hadin gwiwar yankin, yana mai jaddada cewa hadin kan kasashen musulmi wani lamari ne da ake bukata don samun zaman lafiya, tsaro, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa a yankin. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da ya yi da ministan tsaron kasar Saudiyya Yarima Khalid bin Salman da tawagarsa a birnin Tehran, bayan da ministan na Saudiyya ya isa babban birnin kasar Iran domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin da alakar kasashen biyu. Shugaban na Iran ya jaddada zurfafa dangantakar addini da al’adu da tarihi a tsakanin kasashen musulmi, yana mai jaddada wajabcin karfafa hadin...
    Karamin Ministan Tsaro a Najeriya Bello Matawalle, ya caccaki masu sukar lamirin Shugaban Kasa Bola Tinubu game da nuna wariya ga yankin Arewacin Najeriya. Matawalle ya ce Tinubu kadara ne ga Arewa kuma ba shi da fatan da ya wuce ganin ya magance matsalolin da suka addabi yankin kafin 2027. Cikin wani jawabi da mai taimaka masa kan sha’anin siyasa Ibrahim Danmaliki Gidan Goga ya fita, Matawalle ya ce ba a taba samun lokacin da ake yin dimokradiyya mai tsafta kamar a zamanin Bola Tinubu ba. ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista Ya ce duk masu kushe salon mulkinsa kawai suna huce haushin rashi ne da yada farfaganda da karairayi. “Mutanen Arewa suna da wayewar...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya mika rubutacciyar wasikar jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Araghchi, wanda ya je birnin Moscow a matsayin shugaban tawagar diflomasiyya don ganawa da wasu manyan jami’an Rasha, ya gana da Putin a yammacin ranar Alhamis. Ministan ya gabatar da sakon Jagoran ga shugaban kasar Rasha tare da bayyana ra’ayoyi da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da batutuwan da suka shafi ajandar huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaban yanki da sauran batutuwa na kasa da kasa. Araghchi ya tabo yarjejjeniyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da shugaba Putin da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian suka rattabawa hannu a birnin Moscow a...
    Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci. Fani-Kayode ya yi gargadin cewa, rikicin da ake fama da shi na da kamanceceniya da yadda aka kirkiri tashe-tashen hankula a zabukan shekarar...
    Iran ta jaddada shirinta na fadada huldar soji da kasar Saudiyya a wani bangare na batutuwan da ziyarar ministan tsaron kasar Saudiyya Tehran ta kunsa. Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri ya shaidawa Yarima Khalid bin Salman a Tehran a wannan Alhamis cewa “Kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da sojojinsu za ta kawo yanke kauna ga makiyanmu da kuma sanya farin ciki ga abokanmu da sauran musulmi”. Bagheri ya godewa Saudiyya a kan halartarta a matsayin mai sa ido a babban atisayen sojojin ruwa na tekun Indiya (IONS), wanda aka fi sani da IMEX 2024. Iran, Rasha, da Oman ne suka gudanar da atisayen a tekun Indiya, tare da halartar tawagogin masu sa ido...
    Mata da ’yan mata da suka tsira daga tashin hankalin ‘yan Boko Haram a Arewa Maso Gabashin Nijeriya na fuskantar matsaloli masu yawa, ciki har da shiga tsananin damuwa da fuskantar nuna wariya da rashin samun dama na neman kuɗi da kuma uwa-uba rashin samun kulawar gwamnati da na al’umma. A lokacin tashin hankali da yaƙe-yaƙe mata da yara ne suka fi shan wahala sosai daga munanan hare-haren da ke shafar lafiyar jikinsu da ta ƙwaƙwalwarsu, sannan sun fi kowa faɗawa matsalar tattalin arziƙi da shiga cikin ɗimuwa. Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista Tun farkon fara rikicin Boko Haram a watan Yulin 2009, mata da...
    Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni  ta sayo ton 2,000 na hatsi iri-iri domin ƙarfafa samar da abinci da kuma tabbatar da shirin tunkarar kakar bana a matsayin gudun ko ta kwana. A cikin wata sanarwa da Yusuf Ali, mai bada shawara ta musamman kan harkokin dabarun sadarwa na zamani (SSA) ga gwamna Buni ya ce,  Kwamishinan ma’aikatar noma da albarkatun ƙasa, Ali Mustapha Goniri, ya kai ziyarar duba irin hatsin a shagunan bunƙasa noma na jiha  da ke kan titin Gujba da ke Damaturu. ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista ISWAP sun ruguza gadar Mandafuma a Borno Da yake zantawa da manema labarai a yayin ziyarar, Ali Mustapha ya bayyana kyakkyawan fata...
    He Yongqian ta kara da cewa, bangaren Sin na fatan kokari tare da bangaren Turai, don kiyaye tsarin cinikayya bisa ra’ayin bangarori daban daban tare da kungiyar WTO a matsayin tushensa da bin ka’idojin cinikayya.   Game da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin karo na 137, wanda aka fi sani da Canton Fair dake gudana, He Yongqian ta ce, ya zuwa yanzu, masu sayayya fiye da dubu 110 daga kasashe da yankuna 216 sun halarci bikin, adadin ya karu da kashi 10 cikin dari bisa na karo na 135. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na MDD game da yankin manyan tabkuna na Afirka a ranar 16 ga wata cewa, sakamakon ci gaba da kai hare-hare na kungiyar M23 a baya-bayan nan, ya ta’azzara yakin gabashin Kongo DRC, kuma daukacin yankin manyan tabkuna sun fada cikin rudani. Dole ne kasashen duniya su yi aiki tare kuma su hada kai don kawar da wannan mummunar yanayin cikin gaggawa.   Fu Cong ya jaddada cewa, dole ne a gaggauta tsagaita bude wuta domin hana shi ci gaba da ruruwa. Babu wata hanyar soji da za ta magance rikicin gabashin Kongo DRC, kuma tattaunawa ta siyasa ita ce kawai mafita. Dole ne...
    Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki. Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki. ISWAP sun ruguza gadar Mandafuma a Borno ’Yan bindiga sun sace makiyaya 5, da shanu 1,200 a Kaduna Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin ƙoƙarin haɗin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB)...
    Wasu ’yan ta’addan da ake zargin suna da alaƙa da ISWAP sun tayar da wata na’ura mai fashewa a kan gadar Mandafuma da ke kan hanyar Biu zuwa Damboa da tsakar daren wayewar garin ranar Talata. Kamar yadda majiyar Zagazola Makama ke cewar, wannan harin na bam da waɗannan ‘yan ta’addan suka jefa ya lalata gadar ta Mandafuna gaba ɗayanta. Dangote: Har yanzu gidajen mai ba su rage farashin mai ba ’Yan bindiga sun sace makiyaya 5, da shanu 1,200 a Kaduna A cewar majiyar, wannan lalacewar gadar a halin da ake ciki ya kai ga katsewar hanyar da ke tsakanin ƙauyen Mandafuma da garin Biu wadda ita ce hanyar da ta haɗa garin Biu da Maiduguri Jihar Borno. Kamar...
    Ban da wannan kuma, alkaluman PMI wato masu bayyana yanayin sayayya da ake ciki ta fuskar sana’o’in samar da kayayyaki a watan Maris ya samu karuwa cikin watanni 2 a jere, matakin da ya bayyana bukatun kasuwanni na kara samun kyautatuwa. Har ila yau, Sin ta kafa cikakken tsarin sana’o’i, da ingantattun manufofin dake da nasaba da su bayan kokarin da take yi a shekaru da dama, matakin da ya aza tubali mai inganci ga bunkasuwar tattalin arzikinta.   Bayan ga batun dorewa, Sin ta bayyana kuzarinta mai karfi a fannin samun bunkasuwa. A cikin shekarun baya-bayan nan, Sin ta sauya salon tattalin arzikinta daga matakin dogaro da zuba jari, da fitar da kaya waje, zuwa habaka bukatun cikin gida...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki kasar Malaysia daga ranar 15 zuwa 17 ga wata. Inda bangarorin biyu suka amince da gina al’ummar Sin da Malaysia mai kyakkyawar makomar bai daya bisa manyan tsare-tsare da samar da wasu sabbin shekaru 50 masu muhimmanci na dangantakar da ke tsakanin Sin da Malaysia.   A ra’ayin Xu Liping, masani mai nazarin harkokin kudu maso gabashin Asiya na cibiyar kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin, daukaka matsayin dangantakar da ke tsakanin Sin da Malaysia, na nufin cewa, an kara samun amincewar juna bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, kana ana ci gaba da fadada moriyar juna. Hakan zai taimaka wa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu a...
    “Na gode Allah, babu wanda ya jikkata, kuma an kai rahoton lamarin ofishin ‘yansanda.” Ofishin yaɗa labaranta ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce “ƙoƙarinta na kare gaskiya da wakiltar al’ummarta bai kamata a mayar da shi barazana ko tashin hankali ba.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Sakon jagora ga shugaban kasar Rasha yana da alaka da ci gaban kasa da kasa da na yanki Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a birnin Moscow na kasar Rasha cewa: Abu ne da ya dace a rubuta sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha dangane da ci gaban kasa da kasa da na yanki da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Araqchi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Vnukovo da ke birnin Moscow a yau, yayin da yake amsa tambayar da wakilin IRNA ya yi masa kan...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bada muhimmanci game da tattaunawa da ita kuma a shirye take ta magance matsaloli da takaddamar da ake yi kan Shirin makamashin nukiliyarta Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Kazim Gharibabadi ya bayyana cewa: zagayen farko na tattaunawar da ba na kai tsaye ba da aka gudanar a birnin Muscat na kasar Oman tsakanin Iran da Amurka, ba a samu wani babban sabani ba, kuma an yi shi ne domin tantance muhimmancin bangarorin biyu da kuma bayyana matsayinsu. Gharibabadi ya kara da cewa: A wannan zagayen tattaunawan Iran ta nuna muhimmancin tattaunawar da kuma rashin son bata lokaci, yana mai cewa amincewa da shawarar da Amurka ta yi na gudanar da shawarwari ba wai...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta yi kira ga Birtaniya da ta kama ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta gabatar da bukatar fitar da sammacin kame ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar da yake ziyara a Birtaniya. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa: Cibiyar Hind Rajab Foundation da ta mayar da hankali kan neman gurfanar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki, ta mika bukatar kama Gideon Sa’ar a birnin Landan na Birtaniya. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun jiyo ofishin ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila na cewa babu wata niyyar takaita ziyarar Sa’ar...
    Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila suka yi luguden bama-bamai a kan tantunan ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da suka rasa matsugunansu, Tun da tsakar daren jiya ne jiragen suka fara luguden wutan kan tantunan ‘yan gudun hijiran zuwa wayewar garin yau Alhamis, inda wutar bama-baman suka kone gawarwakin yara da mata, bayan shahadan mutane da dama. Rahotonni sun bayyana cewa: An hae-haren sun janyo shahadan yara da mata...
    Mutane fiye 300 ne suka mutu a cikin kwanaki a wani kazamin fada a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton cewa: Sama da fararen hula 300 ne aka kashe a wani kazamin fada na kwanaki biyu a yankin Darfur na kasar Sudan mai fama da rikici. Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun kaddamar da hare-hare a ranakun Juma’a da Asabar a kan sansanonin ‘yan gudun hijira biyu da ke fama da matsalar yunwa a arewacin Darfur da kuma babban birnin da ke kusa, inda rahotannin farko suka nuna cewa sama da mutane 100 ne suka mutu, ciki har da yara 20 da ma’aikatan...
    Bugu da kari, illar matakin na Amurka na iya gurgunta salon hada-hadar kudade, da kwadago, da kirkire-kirkire da kasuwannin kasa da kasa ke cin gajiyarsu.   Bisa la’akari da tarihi, mun san cewa Sin da Amurka kasashe ne dake da banbance-banbance ta fuskar ci gaba, da yanayin gudanar masana’antu da karfin tafiyar da su, amma duk da haka ci gaban sassan biyu ya dunkule wuri guda, ta yadda illata sashe daya na iya haifar da koma baya ga dukkanin bangarorin biyu.   Ga misali, yayin da gwamnatin Amurka ke ta yayata manufar karin harajin ramuwar gayya, kamata ya yi mu lura cewa, Amurka na shigo da tarin hajoji da aka kammala sarrafawa, da wadanda ake kara sarrafawa a cikin kasar...
    A ranar 17 ga watan Afrilun nan, yayin ziyarar aiki ta shugaba Xi jinping a kasar Cambodia, an yi bikin kaddamar da shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Cambodia, wanda CMG ya shirya a birnin Phnom Penh.   Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Inda ya ce a shirye CMG yake ya yi aiki tare da abokai daga sassan daban daban na kasar Cambodia domin ci gaba da zurfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da samar da karin haske a fannin musayar al’adu, da sanya sabon kuzari a aikin gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tsakanin Sin da Cambodia. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya bayyana cewa shiga wani yanki da ba a fahimtar yaren juna ɗauke da makamai na iya janyo fargaba da tashin hankali. “Ka yi tunanin idan wasu daga Kudu sun shigo ƙauyanku ɗauke da makamai kuma ba ku fahimtar yaren juna — za ku ji tsoro. Haka nan idan mutanenmu suka shiga yankin Kudu da makamai, su ma za a ji tsoro,” in ji shi. Rurum ya ce zai gana da shugabannin ƙungiyoyin masu farauta a jihar domin daƙile wannan ɗabi’a, ya kuma buƙace su da su nemo hanyar nema wa kansu asiri . “Wasu su tafi farauta su dawo ba tare da sun kamo ko ɓeran daji ba. Bai dace su ci gaba da haka ba. Ya kamata mu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A karo na biyu a cikin mako guda, matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur. Daga ranar 16 ga Afrilu, 2025, farashin man fetur zai tashi daga N865 zuwa N835. Wannan dai shi ne karo na biyu da aka rage farashin a cikin mako guda yayin da matatar man Dangote a baya ta rage farashin daga N880 zuwa N865 kan kowacce lita. Najeriya da gwamnatin sojin Nijar sun sasanta Ka dawo Najeriya ka magance matsalar tsaro —Obi ga Tinubu Sai dai kuma, har ya zuwa ranar Laraba, farashin bai canja ba a galibin gidajen mai da suka haɗa da cibiyoyin sayar da man fetur na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL). Yayin da ’yan kasuwa ke...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horaswa gaa malamai daga dukkan kananan hukumomi 27 domin shirya su, su horar da maniyyata aikin hajjin 2025 na jihar. Darakta Janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya ga sabbin masu wa’azin aikin hajjin na kananan hukumomi. Ya ce masu gudanar da aikin, an zabo su ne daga kowace karamar hukuma 27 na jihar domin gudanar da aikin hajjin mai zuwa. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce su kuma masu gudanar da aikin za su horas da maniyyatan a cibiyoyin da aka kebe a kananan hukumominsu na jihar. Ya bayyana cewa, an shirya taron bitar ne domin...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horaswa gaa malamai daga dukkan kananan hukumomi 27 domin shirya su, su horar da maniyyata aikin hajjin 2025 na jihar. Darakta Janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya ga sabbin masu wa’azin aikin hajjin na kananan hukumomi. Ya ce masu gudanar da aikin, an zabo su ne daga kowace karamar hukuma 27 na jihar domin gudanar da aikin hajjin mai zuwa. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce su kuma masu gudanar da aikin za su horas da maniyyatan a cibiyoyin da aka kebe a kananan hukumominsu na jihar. Ya bayyana cewa, an shirya taron bitar ne domin...
    Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci. Hadin Gwiwar Kasashen Asiya Da Afirka Na Habaka Karfinsu Na Dogaro Da Kai Da Cin Moriya Tare Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace...
    A kokarin ta na ci gaba da inganta ayyukan ta, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta gudanar da bitar sanin makamar aiki ga malaman bita na kananan hukumomin jihar 27. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo wanda ya jagoranci gudanar ta taron a shelkwatar hukumar dake Dutse, ya ce an shirya taron ne domin nusar da malaman ayyukan daya rataya a kawunan su domin cimma burin da aka sanya a gaba. A cewar sa, hukumar zata sanya malaman bitar a cikin kwamitocin hukumar daban-daban domin samun nasarar gudanar da aikin hajjin bana. Yana mai cewar, a matsayin su na jagororin maniyata aikin hajji, akwai bukatar su kasance da maniyata tare da fadakar dasu akan aikin hajjin...
    Ministan Harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya je kasar Rasha a safiyar yau Alhamis don isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei zuwa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan sakon na zuwa ne rana guda da amincewar majalisar dojojin kasar Rasha ta dangantaka ta musamman tsakanin kasashen biyu, mai tsawon shekaru 20. Har’ila yau da kuma kwanaki biyu kafin a gudanar da tattaunawa na biyu tsakanin Iran da Amurka dangane da shirin ta na makamashin Nukliya a birnin Roma na kasar Italiya. Masana dai sun bayyana cewa kasashen Rasha da Iran suna kara dankon zumunci a tsakaninsu ne a dai-dai lokacinda al-amura da dama...
    Majalisar kasa ta kasar Rasha ta amince da yarjeniyar dangantaka ta musamman tsakanin kasar da JMI a ranar 8 ga watan Afrilun da muke ciki sannan ana saran shugaban kasa Vladimir Putin zai sanyawa yarjeniyar hannu a nan gaba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa yarjeniyar ta musamman mai kuma dogon zango na shekaru 20 zai bawa kasashen biyu damar tallafawa juna da kuma aiki tare da bangarori daban-daban wadanda suka hada da tsaro makamashi kimiyya da fasaha da sauransu. Labarin ya kara da cewa idan yarjeniyar ya fara aiki kasashen biyu suna da damar kyautata dangantaka a tsakaninsu, wanda zai rage dogaro da suke yi da kasashen yamma a bangarori da dama. Dangantakar Tehran da...
    Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa kimani yara 3,500 suka rasa rayukansu a kokarin ketara tekun Medeteranina a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Spunic na kasar Rasha ya nakalto hukumar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar dangane da hakan. Labarin ya kara da cewa, wannan ya nuna cewa akalla yaro guda ne ya ransa ransa a ko wace rana. Kuma kashi 7/10 daga cikinsu sun halaka ko sun bace ne su kai ba ba tare da rakiyar iyayensu ba. Har’ila yau rahoton ya kara da cewa akalla mutane 20,803 suka halaka a tsakiyar tekun na Mediterranean a kokarinsu na tsallakawa zuwa kasashen na turai. Daga karshe hukumar...
    Sayyid Ammar Hakim shugaban jam’iyyar ‘ تيار الحكمة الوطني’ na kasar Iraki ya bayyana cewa kasar Iraki ce kasa ta farko wacce zata amfani da tattaunawa tsakanin Iran da kasar Amurka. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sayyid hakim yana fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa kasashen Iran da Iraki suna da gangantaka da musulunci makobtaka da kuma al-adu masu yawa. Don haka a duk lokacinda Amurka suka kyautata tsakanin Iran da Amurka kasashen biyu suna iya bude kan iyakokinsu don mu’amala da juna ba tare da Amurka ta shiga tsakanin ba. A wani waje a cikin jawabinsa Hakim ya amince da ruwan da gwamnatin kasar Amurka ta taka wajen kauda tsohuwar gwamnatin kama...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi na kwatar yencinsu da kuma kasarsu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka masu goya mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran wannan sanarwan tazo ne bayan da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta samar da wani kuduri dangane da rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya.   A dai-dai lokacinda aka kara yawan tashe-tashen hankula a kasar Falasdinu da aka mamaye tsakanin HKI da kuma Falasdinawa masu gwagwarmaya. Kungiyar kasashe masu musulmi mafi rinjaye wato OIC ta yanke  shawara kan cewa bai kamata kasashen su samar da huldar...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da wani babban kwamiti kan kidayar jama’a da gidaje mai zuwa, inda ya umurci mambobin su gabatar da rahoton farko cikin makonni uku. Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, a wajen taron da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce kidayar na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa da kuma tsare-tsare na gaskiya.   Ya lura cewa ingantaccen bayanan yawan jama’a yana da mahimmanci don yanke shawara mai inganci a cikin manyan sassan kamar kiwon lafiya, ilimi, tsaro, da kuma tsara tattalin arziki. Shugaban ya jaddada cewa, an gudanar da kidayar jama’a ta karshe a shekarar 2006, wato kusan shekaru ashirin da suka wuce,...