2025-04-12@20:50:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 59

«faɗan daba»:

    ’Yan sanda sun cafke wasu mutum takwas da ake zargi da faɗan daba a yankin Ƙofar Na’isa zuwa Ƙofar Ɗan Agundi da ke ƙwaryar birnin Kano. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas Kiyawa ya ce a ranar Alhamis da ta gabata ce suka samu kiraye-kirayen waya cewa wasu sun fito da makamai suna faɗan daba, lamarin da ya sanya aka tura jami’ai domin ɗaukar mataki. Kakakin ’yan sandan ya ce a wannan lokaci babu wanda aka kama sakamakon arcewa...
    Wani jirgi mai saukar ungulu ya faɗa cikin kogin Hudson da ke birnin New York a Amurka.   Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayyana cewa mutum shida da ke cikin jirgin – fasinja biyar da direban jirgi guda sun mutu.   Magajin garin New York Eric Adams ya ce jirgin na ɗauke da wani iyali su biyar daga Spain har da yara uku.   Ya ƙara da cewa tuni aka tsamo gawarwakin mutum biyar ɗin daga ruwa.   Wakilin BBC ya ce har yanzu ana aikin ceto domin koƙarin zaƙulo tarkacen jirgin da masu bincike za su buƙata don gano abin da ya haddasa haɗarin.   Shaidu sun ce jirgin ya tarwatse ne tun a sama inda kuma ya faɗa...
    Kantoman Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, ya amince da naɗin sabbin kantomomi na ƙananan hukumomi 23 da ke faɗin jihar. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Ribas, Farfesa Ibibia Lucky Worika ya fitar a safiyar wannan Larabar a birnin Fatakwal. ’Yan bindiga sun kashe masunta 3 a Sakkwato Likitocin Nijeriya dubu 16 sun yi ƙaura zuwa ƙetare — Ministan Lafiya Sanarwar ta ce Ibas ya kuma amince da sauya duk majalisun gudanarwa na ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin jihar da a baya aka dakatar da ayyukansu. Sanarwar ta ce naɗin sabbin masu kula da gudanarwar ƙananan hukumomin zai fara aiki ne nan take daga ranar Litinin, 7 ga watan Afrilu. Sunayen kantomomin ƙananan hukumomin Ribas  
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama. Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano. Kano, jiha ce da hamayyar siyasa da rikicin masarauta ya dabaibaye ta. Akwai hamayyar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyun NNPP mai mulki a jihar da takwararta ta...
    Wasu mutane huɗu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun mutu a sakamakon hatsarin mota a Jihar Nasarawa. Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar SP Nansel Rahman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya auku ne lokacin da ‘yan fashin ke ƙoƙarin tserewa jami’an. Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati “A ranar 25 ga watan Maris ne rundunarmu ta samu wani kiran gaggawa kan wasu ‘yan fashi na tsaka da ta’asa a bayan filin wasa na ƙaramar hukumar Keffi. “Bayan samun kiran ne kwamishinan ‘yan sanda Shettima Jauro Mohammed ya ba da umarnin bin bayan ‘yan fashin nan take. “Suna cikin guje...
     Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya yi murabus daga mukaminsa. An tabbatar da murabus din nasa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar. Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din a hukumance, inda ya nuna jin dadinsa da irin gudunmawar da Janar din sojan ya bayar a lokacin da yake gudanar da aikinsa. Rasha Da Ukraine Sun Amince Da Tsagaita Wuta A Tekun Black Sea Kasuwar Kayayyakin Masarufi Ta Sin Za Ta Ci Gaba Da Nuna Yanayin Bunkasa Bisa Daidaito A Bana LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Manjo janar Idris (mai ritaya) shi ne...
    A cewarsa ya zaɓe shi ne bisa la’akari da kwarjininsa da kuma gwanintarsa. Farfesa Worika yana da digiri na uku a fannin Dokar Muhalli ta Ƙasa da Ƙasa da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya. Ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da harkokin ilimi da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Naɗinsa yana cikin ƙoƙarin gwamnatin Jihar Ribas na amfani da ƙwararru ‘yan jihar domin samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tsaro. Farfesa Worika ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Okrika a Jihar Ribas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Shugaban riƙo na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da naɗin Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Ribas. Wata sanarwa da ta fito daga Fadar Gwamnatin da ke birnin Fatakwal a wannan Talatar, ta ce naɗin ya biyo bayan nazari kan ƙwarewar Farfesan da gogewarsa a fannoni daban-daban. Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Naɗin sabon Sakataren Gwamnatin na zuwa ne a daidai lokacin da Ibas ya amince da murabus ɗin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, George Nwaeke, yana mai gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacinsa. Ibas ya ce naɗin Farfesa Worika ya yi...
    Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022. A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim: Za mu so ki gabatar da kanki? Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood. Mene ne tarihinki a takaice? To ni ‘yar asalin garin Kano ne. An haife ni a garin Dakatsalle da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano. Na yi makarantun firamare da sakandare duk a Dakatsalle, bayan na gama sakandare sai aka yi min aure, daga baya Allah Ya kawo ni cikin birnin Kano. Ke nan kin taɓa yin aure? Eh na taɓa yin aure,...
    Ya kuma buƙaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da haƙuri da fahimtar juna domin haɗa kai tare da tabbatar da goyon baya ga jam’iyyar. A nasa ɓangaren, Sakataren APC na Zamfara, Hon. Ibrahim Umar Dangaladima, ya gode wa Shugaban Ƙasa Tinubu da Minista Matawalle bisa wannan tallafi. Ya ce shinkafar ta zo a daidai lokacin da jama’a ke fuskantar wahalar rayuwa, kuma ya yi alƙawarin cewa ’yan jam’iyyar za su ci gaba da haɗa kai da kaunar juna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantad da Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Iba a matsayin gwamnan rikon kwarya na Jihar Rivers. Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, da Shugaban Ma’aikatan Fadar  Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, da wasu hadiman Shugaban Kasa sun halarci wannan gajeren bikin rantsuwar da aka gudanar a Fadar Gwamnati a ranar Laraba. Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers a ranar Talata, 18 ga Maris, domin magance rikicin siyasa wanda ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ‘yan majalisar dokokin jihar, duk da hukuncin da Kotun Koli ta yanke. A yayin ayyana dokar ta-baci na tsawon watanni shida, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa halin rashin tsaro da matsin lamba...
    Da wannan sabon matsayi, Farfesa Pate, zai haɗa kai da sauran ƙwararru da ke aiki domin tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da inganta shigar da al’umma cikin harkokin shugabanci, wanda ake kyautata zaton ƙwarewarsa za ta taimaka wajen tsara sabbin hanyoyi da cibiyar WSCIJ za ta amfana.   WSCIJ, wacce an sanya mata suna daga fitaccen marubuci kuma masanin adabi, Farfesa Wole Soyinka, cibiya ce mai zaman kanta da ke amfani da binciken ƙwaƙwaf a aikin jarida domin ƙarfafa dimokuraɗiyya da inganta tsarin shugabanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Seyi Tinubu, ɗan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa, mahaifinsa ne kaɗai shugaban ƙasar da ba shi da burin azurta kansa da kuɗin talakawa. Har wa yau ya ƙara da cewa shi kaɗai ne shugaban da ke bai wa matasa damammaki a gwamnatinsa. Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano Ana zargin wa da ƙani da yi wa almajiri yankan rago a Adamawa Seyi ya faɗi hakan ne yayin yi wa wani dandazon matasa jawabi a Yola, babban birnin Jihad Adamawa. Seyi Tinubu wanda ke ci gaba da shawagi a wasu jihohin ƙasar yana buɗa-baki, ya ce a kwanakin wasu sun dage wajen sukar mahaifinsa, sai dai hakan ba zai sa ya yi ƙasa a gwiwa ba...
    Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi da tsohon Kwamishinan sa ido da tantance ayyuka Muhammad Diggol sun gana da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin a Abuja.  Taron ganawar wanda ya haɗa sauran masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan samar da ci gaba a Jihar Kano da kuma ciyar da ƙasa gaba. MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau ya wallafa hotunan ganawar da aka yi tare da bayyana muhimmancin haɗin gwiwa wajen samun ci gaba mai ɗorewa. “Ci gaban jiharmu da ƙasa a kodayaushe yana kan gaba a ajandarmu, za...
    An tabbatar da mutuwar wata mata da har yanzu ba a bayyana sunan ta ba bayan ta yi tsalle ta faɗa kogin Legas daga gadar Third Mainland a Jihar Legas. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne daga wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Juma’a cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4 na yamma kusa da bakin ruwan kogin da ke hanyar jami’ar Legas. Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar “Tawagar ’yan sandan ruwa da ke aiki a wurin sun gano ta gaɓar ruwan da ke hanyar jami’ar Legas...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da tuni Najeriya ta faɗa cikin mummunan yanayin matsin tattalin arziƙi ban da gwamnatinsa ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci. Da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana wa wata tawagar tsofaffin ’yan majalisa cewa dole ne gwamnatinsa ta ɗauki matakai domin tabbatar da kyakkyawan makoma ga ƙasar. Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu “Tsawon shekaru 50, Najeriya na kashe kuɗin ’ya’yanmu wajen samar da man fetur ga maƙwabtan ƙasashe. Dole ce ta sa muka tsara makomar yaranmu,” in ji shi. Shugaban ya amince da cewa ana fuskantar ƙalubale...
    Shugaban Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Mista Peter Tanko Dogara, ya tabbatar da aniyarsa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sarakunan gargajiya domin samar da tsaro da samar da ayyukan ci gaban ƙaramar hukumar. Mista Dogara ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai zuwa ga masarautu shida da ke ƙaramar hukumar, inda ya jagoranci ɗaukacin jami’an majalisar ƙaramar hukumar don gudanar da ziyarar. ’Yan bindiga sun sace mutum 10 da raunata 2 a Kaduna Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo A dai cikin makon nan ne Shugaban ƙaramar hukumar tare da tawagarsa suka ziyarci fadar Sarkin Kagoma, Mista Paul Zakkah Wyom; Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammadu...
    Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya haɗa hannu da kamfanonin ƙasar Sin don samar da ingantattun fasahohin zamani da inganta noma, sufuri da ma’adanai na jihar.   A ranar Talata ne gwamnan ya karbi baƙuncin masu kamfanoni na ƙasar Sin a gidan gwamnati da ke Gusau.   A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa gwamna Lawal ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar a ziyarar aiki a ƙasar Sin daga ranar 15 zuwa 21 ga watan Fabrairun 2025, domin yin haɗin gwiwa a muhimman sassa.   Sanarwar ta ƙara da cewa, tawagar ta Zamfara ta yi hulɗa da kamfanonin Zhong Zhao International Group, Phoenix Wings, Shenzhen HighGreat Innovation Technology Development Co., Ltd,...
    Sabbin hadiman da aka naɗa za su fara aiki nan take, tare da kawo sabbin dabaru domin inganta sadarwa a gwamnatin jihar. Wannan shiri kuma na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnatin na ƙarfafawa matasa guiwa da rage rashin aikin yi a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Aƙalla mutane 26 ne suka riga mu gida sakamakon ɓarkewar cutar Sanƙarau a wasu ƙananan hukumomi huɗu na Jihar Kebbi. Da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Kwamishinan Lafiya, Yanusa Ismail, ya bayyana cewa an samu adadin mutane 248 da ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikin samfura 11 da aka gwada a ɗakin gwaje-gwaje, an tabbatar da cewa uku daga ciki kalau suke. Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi A cewar kwamishinan, ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Gwandu, Aleiro, da Jega, inda aka samu asarar rayuka 15 a Gwandu, shida a Jega, huɗu a Aleiro, ɗaya kuma a Argungu. Ya...
    ’Yan sanda sun cafke tsohon shugaban ƙasar Philippines,  Rodrigo Duterte a filin jirgin saman birnin Manila a wannan Talatar. Mista Duterte ya faɗa komar ’yan sandan ne bisa sammacin Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, jim kaɗan da saukarsa daga birnin Hong Kong. Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya Hatsaniya ta ɓarke a filin jirgin saman lokacin da ’yan sanda suka kama Mista Duterte, sakamakon tirjiya daga masu tsaron lafiyarsa da likitansa da kuma lauyoyinsa, wadanda ke zargin cewa an take masa haƙƙinsa da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi. Fadar shugaban ƙasar Ferdinand Marcos ta ce tsohon shugaban na fuskantar tuhumar kisan...
    Ya ce ya sha jan hankalin shugabannin jam’iyyar kan waɗannan matsaloli, amma ba a ɗauki mataki ba. Bayan ficewarsa daga APC, El-Rufai ya ce zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan jam’iyyarsa domin ganin an samar da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar dokokin jihar sunan Ibrahim Yakubu Adamu domin tantancewa da tabbatar da naɗinsa a matsayin sabon Kwamishina. Kakakin Majalisar, Alhaji Jibrin Falgore ne ya bayyana hakan yayin da yake karanta wasiƙar gwamnan a zaman majalisar da ya gudana a yau Litinin. Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Ko dai Gwamna Fubara ya yi murabus ko a tsige shi — APC Aminiya ta ruwaito cewa, Ibrahim Yakubu Adamu wanda gwamnan ke shirin naɗawa muƙamin kwamishina shi ne Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Kano, KNUPDA. Falgore ya ce nan gaba kaɗan za su aika masa goron gayyata domin tabbatar da buƙatar gwamnan. Kazalika, majalisar ta kuma tabbatar da dokar...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin...
    Ana sa ran shirin zai inganta samar da abinci, rage rikice-rikicen Makiyaya da Manoma, da kuma samar da damarmaki ga miliyoyin ‘yan ƙasa da ke dogaro da kiwo a matsayin sana’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da mutane bakwai da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ƙauyen Anchuna da ke masarautar Ikulu a ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna. An samu rahoton cewa harin wanda ya auku a daren ranar Larabar, ya jefa al’ummar yankin cikin firgici yayin da maharan suka mamaye ƙauyen da suke da yawa, inda suka yi ta harbe-harbe kafin daga bisani su tafi da su. Wani mutum ya yanke jiki ana salla a Masallaci, ya rasu a asibiti Sojoji sun hallaka mai haɗa wa Boko Haram bam a Sambisa Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Kukah, ɗan gidan fitaccen malamin kirista, Bishop Hassan Kukah, ya tabbatar...
    Dakarun Sojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram tara, ciki har da ƙwararren mai haɗa wa ƙungiyar bama-bamai, Amirul Bumma a wani samame da suka kai a dajin Sambisa da ke Jihar Borno. Majiyoyi sun bayyana cewa sojojin sun kai farmakin ne a Ƙaramar Hukumar Bama, ƙarƙashin rundunar Operation Desert Sanity 4, bayan samun bayanan sirri. Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha Doyin Okupe: Tsohon kakakin shugaban ƙasa ya rasu Boko Haram sun yi ƙoƙarin tsayawa da su fafata, amma sojojin sun yi nasarar fatattakar su. Bayan kammala artabun, mayaƙan sun dawo wajen da gadajen asibiti domin kwashe waɗanda suka jikkata, wanda hakan ke nuna girman asarar da suka yi. Daga cikin waɗanda aka kashe akwai babban jagoran...
    Sojojin sun kuma ƙwato makamai masu yawa. Bayan artabun, Boko Haram sun yi yunƙurin kai farmakin ramuwar gayya ta hanyar birne bama-bamai a hanyoyin da sojojin za su bi. Sai dai dakarun sun gano sama da guda 10 daga cikin abubuwan fashewar kuma sun tarwatsa su, wanda hakan ya hana aukuwar asarar rayuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shamsedeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na Tarayya. Naɗin nasa, wanda aka amince da shi a yau Talata, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya. Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ana iya tuna cewa, tun a watan Disambar da ya gabata ne aka bayyana Ogunjimi mai shekaru 57 a matsayin magajin Madehin. Daga baya wani aka naɗa wani kwamitin ƙwararru da zai tantance wanda ya haɗa da manyan daraktocin daga a ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya yi...
    Bidiyon batsa ya ja wa wasu ’yan Tiktok biyu hukuncin ɗaurin shekara guda kowannensu a gidan yari bayan an gurfanar da su gaban kotu a Jihar Kano. Kotun Majiatare da ke Norman’s Land a Ƙaramar Hukumar Fagge ta yanke wasu ’yan Tiktok din hukunci ne bayan samun su da laifin saɓa wa dokokin Musulunci da kuma tsarin zamantakewar al’ummar jihar. ’Yan TikTok ɗin da suka haɗa da Ahmad Isa da Maryam Musa waɗanda dukansu ’yan unguwar Ladanai ne da ke yankin Hotoro ne. Sun gurfana a kotu ne bayan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta cika hannunta da su. Jami’an tsaro sun hana jama’a kwasar mai bayan hatsarin tanka a Taraba Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok...
    Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja Bayan murabus ɗin nata, nan take ’yan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Nijeriya. ’Yan majalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayin mace ta farko kakakin majalisa. Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ’yan jam’iyyar APC...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ya sa dole a yi tattalin kuɗin da ake kashewa. An saba  a watan Ramadana ana yawan yin girke-girke da kayan buɗa-baki iri-iri, amma kuma wannan azumin ya zo cikin yanayi na matsin tattalin arziki. NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya a Yau ya duba hanyoyin da za ku yi girke-girken da yawa yadda aka saba cikin sauki ba tare da kashe maƙudan kuɗaɗe ba. Domin sauke shirin, latsa nan
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta sanar da naɗin Dakta Mustapha Muhammad Ali, a matsayin sabon Sakataren Hukumar. Sanarwar naɗin na ƙunshe ne a cikin wata takarda da shugaban sashin hulɗa da Jama’a na hukumar, Muhammad Ahmad Musa, ya fitar bayan amincewar kwamitin gudanarwa na NAHCON a taron da aka gudanar na ranar 26 ga Fabrairun 2025, bisa tanadin sashi na 8 na dokar da ta kafa NAHCON ta 2006. NAHCON Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kuɗin Kujerar Aikin Hajjin 2025 zuwa 10 ga Fabrairu Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince Da Kwangilar Aiki Da NAHCON Bayan Sabunta Yarjejeniya  Dakta Mustapha Muhammad Ali, wanda ƙwararre ne wajen tabbatar da gudanarwa da kuma aiwatar da manufofin inganta aikin Hajji a Nijeriya, zai...
    Shugabannin Jam’iyyar APC, ciki har da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni, da sauran manyan jagorori, sun gana a daren Talata a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. An gudanar da taron ne domin shirye-shiryen babban taron jam’iyyar na ƙasa da za a yi a yau a hedikwatar APC. Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Wannan shi ne taron farko da za a yi taron tun bayan hawan Shugaba Tinubu kan mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023. A bara, an tsara shirya waɗannan taruka ne a watan Satumba, amma aka ɗage su ba tare da saka sabuwar rana ba. A baya-bayan nan, tsohon gwamnan Jihar Kaduna,...
    Samar da dabino zai samu sauyi mai mahimmanci a Jihar Jigawa bayan da wani kamfani daga kasar Saudiyya mai samar da dabino da gwamnatin jihar suka ƙulla yarjejeniya domin ƙara yawan amfanin gona. Ta wannan haɗin gwiwa za a kawo sababbin fasahohin zamani da irin dabino masu yawa don shigar da su cikin tsarin noma. Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin Ramadan A cewar bayanai daga Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), Saudiyya ita ce ƙasa ta biyu mafi girma wajen samar da dabino na duniya, inda take samar da tan miliyan 1.61 na dabino. Masar ita ce ƙasa mafi girma wajen samar da dabino, inda...
    An naɗa wasu dattawan Afirka da suka yi mulki a ƙasashen yankin a matsayin masu shiga tsakani domin warware takaddamar da ta ɓarke a tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin Dimokuraɗiyyar Kongo. Ƙungiyoyin raya ƙasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) ne suka naɗa tsoffin shugabannin Habasha da Kenya da Nijeriya domin sanya idanu a kan batun sulhu a Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo inda yaƙi ya ƙazanta a gabashin ƙasar. Manoman tumatir na tafka asara saboda faɗuwar farashi 40% na matan Kano sun fuskaci cin zarafi a gida —Shugaban Majalisa Shugabanin ƙasashen gabashi da kudanci da ma yammacin Afirka ne suka yi naɗin a wani yunƙuri na kawo ƙarshen yaƙin basasa a gabashin Kongo, tare da cimma matsaya kan batun...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    Mutane huɗu sun rasa rayukansu, wasu 10 kuma sun samu raunuka bayan wata motar bas ƙirar Hummer ta kama da wuta a garin Gwaram da ke Jihar Jigawa. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandaren gwamnati ta Government Girls Unity Secondary School da ke Gwaram. Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno  Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya ce motar ta taso daga Ƙaramar Hukumar Zaki daga Jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram. Sanarwar ta bayyana cewa...
    Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa. Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar, ya samu fitowar masu zaɓe sosai tare da ingantaccen tsaro. Gwamna Adeleke ya yaba da yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana, inda ya buƙaci al’umma su ci gaba da kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ko matsin lamba ba. Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke An Yanke Wa Mutane 5 Hukuncin Kisa Bayan Sun Kashe Wani Bafullatani A Jihar Osun Da yake jawabi...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. Domin sauke shirin, latsa nan
    Shirin Trump Na Gaza Rubio ya bayyana cewa shirin Trump shi ne kaɗai mafita a yanzu, duk da cewa ƙasashen Larabawa da na duniya suna goyon bayan kafa ƙasar Falasdinu tare da Isra’ila. A nasa bangaren, Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya ce kafa ƙasar Falasdinu ce kaɗai hanya ta samar da zaman lafiya a yankin.
    “A binciken da ake yi, an gano dukkan kayayyakin da aka sace bayan an sayar da su kan kudi naira 80,000, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifin aikata laifin.” PPRO ya kara da cewa, ‘yansanda na ci gaba da neman mutum na uku da ake zargi mai suna Ibrahim Danmariya, wanda ake kyautata zaton shi ne mai karbar kayan da aka sace. Abdullahi ya bukaci mazauna yankin da su lura kuma su kai rahoto ga ofishin ‘yansanda mafi kusa. “Muna kira ga jama’a da su bayar da bayanai masu amfani da za su kai ga kama wanda ake zargi da gudu. “Muna tabbatar wa jama’a cewa za a yi amfani da duk bayanan cikin sirri,” in ji Abdullahi.
    Hukumar Zaɓe Mai ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda  gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki. Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa. Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula da ofishin...
    Ana ci gaba da gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Jihar Katsina, inda ake fuskantar ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a, da kuma zargin sayen ƙuri’u a wasu rumfunan zabe. Jami’an tsaro, ciki har da ‘yansanda da NSCDC, sun sanya dokar taƙaita zirga-zirga tare da tura jami’ai wurare masu muhimmanci domin tabbatar da tsaro. A garin Tsani, rahotanni sun nuna cewa mutum biyu kacal aka gani a rumfar zabe, yayin da aka hango motar sintiri da APC na jami’an tsaro. Annobar Cutar Murar Tsuntsaye Ta Yadu A Jihohin Filato Da Katsina Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace Tsohon Daraktan NYSC, Janar Tsiga A rumfar Birchi ta Kudu, inda aka yi rajistar masu zabe 808, kaɗan daga cikinsu ne...
    Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda  gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki. Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa. Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Tinubu ya isa Ethiopia domin halartar taron AU A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula...
    A takardar, wadda mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya sa wa hannu, Idris ya ce: “Rediyo ko yaushe hanya ce ta samun ingantaccen bayani kuma abin dogaro ne ga al’umma, musamman a lokutan da ake fuskantar matsaloli.   “A ‘yan shekarun nan, rediyo ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa ga duniyar mu. Tare da faɗin isar sa da sauƙin samun sa, rediyo yana da ikon ilimantarwa da ƙarfafa mutane su ɗauki matakan da suka dace don yaƙi da sauyin yanayi.”   Idris ya ambato jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron COP29 na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi wanda aka gudanar a birnin Baku na...
    Gwamnatin Kano ta bayyana aniyarta na kafa Hukumar Kula da Masu Buƙata ta Musamman a wani mataki na tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar jihar. Kwamishiniyar Mata da Yara masu bukata ta musamman, wacce Daraktar Jin Daɗi ta ma’aikatar, Binta Muhammad Yakasai, ta wakilta, ta bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa na yini guda da masu ruwa da tsaki kan kafa Hukumar Kula da Mutanen da ke da Bukatu na Musamman (PWDs) a Jihar Kano. Tana jaddada aniyar gwamnati na ƙarfafa PWDs, Yakasai ta ce, “Wannan taro ba kawai haɗuwar ra’ayoyi ba ne, amma wani mataki ne na tabbatar da adalci, haɗawa da ƙarfafa wani muhimmin ɓangare na al’ummarmu.” Ta bayyana manyan dalilai guda biyar da ke nuna bukatar kafa...
    Kamfanin Siminti na BUA ya raba magungunan cututtuka daban-daban na kimanin naira miliyan 35 a ƙananan asibitoci da ɗakin shan magani 16 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Wamakko a Sakkwato. Daraktan Kamfanin BUA, Injiniya Yusuf Halliru Binji, a wurin rabon tallafin maganin ya ce BUA ya ba da tallafi ga asibitoci da ɗakunan shan magani 16 a tsarin da yake da shi na sadaukarwa ga al’ummar da suke kusa da shi, a kowace shekara akan bayar da magani don saukaka samun magani ga jama’ar. Binji ta hannun Alhaji Sada Suleiman da ya wakilce shi ya ce kamfanin BUA a tsarinsa na rama alheri ya ɗauki wannan da muhimmanci domin ƙarfafa dangantaka. “Babu tantama dole mu bayyana farin ciki ga irin...
    Kamfanin Dangote na Peugeot Automobiles Nigeria Limited (DPAN), wanda ke kera wa da tallata motocin Peugeot a Nijeriya, ya fara tarawa da haɗa sabuwar Peugeot 3008 GT a masana’antarsa da ke Kaduna. Peugeot 3008 GT, mai injin 1.6-lita turbo mai ƙarfi, ya ƙara yawan jerin motocin da ake haɗawa a masana’antar DPAN, wanda ya ya ke samar da 301 sedan da Peugeot 5008 mai kujeru bakwai. Wannan sabon samfurin yana da Faisal kamar fitilun, da hasken rana mai iya buɗewa, da tayoyin 17-inch alloy. Matatar Dangote Ta Bai Wa Ɗalibai 473 Tallafin Karatu Zanga-zanga: Ku Kawo Ƙarshen Rashin Wutar Lantarki Da Ta Addabi Jihohi- Gwamnatin Kaduna  Hakanan, an samar da fasahar ABS don hana birki shanye wa, ESP don hana...
    Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya miƙa wa Majalisar Dokokin jihar sunayen zaɓaɓɓun kwamishinoni 16 domin tabbatarwa. Shugaban Majalisar, Danladi Jatau ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar da ya gudana ranar Litinin a birnin Lafiya. Atiku da Obasanjo suna ganawar sirri Ɗalibi ya kashe abokin karatunsu da gatari a Nasarawa Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin sabbin kwamishinonin da gwamnan ya zaɓa har da tsohon Shugaban Masu Rinjayen a majalisar dokokin jihar, Umar Tanko-Tunga da wani tsohon mamba a majalisar, Mohammed Agah-Muluku. Kakakin Majalisar ya buƙaci kowane ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun kwamishinonin da su gabatar da kwafi 30 na duk bayanansu daga yanzu zuwa ranar Alhamis tare neman su hallara a gaban majalsiar a ranar Litinin ta makon...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yammacin ranar Asabar. Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari Sanarwar ta ce naɗin sabon Sakataren Gwamnatin zai fara aiki ne a hukumance daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Fabarairun 2025. Sanarwar ta ce an naɗa sabon Sakataren Gwamnatin wanda ya shafe sama da shekaru talatin yana aikin gwamnati la’akari da ƙwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban na wajen ganin an cimma muradin gwamnati mai ci na ciyar da Jihar...
    Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Trump Ya Hana Maza Masu Sauyin Jinsi Shiga Wasannin Mata Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara,...
    Masarautar Fika da ke Jihar Yobe ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a filin wasa na Dabo Aliyu da ke garin Potiskum. An buɗe gasar ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe. Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano Gasar wacce aka fara a shekarar 2011 ta bunƙasa zuwa wani gagarumin taron wasanni a yankin, wadda ke haɗa ƙungiyoyi daga ƙananan hukumomi huɗu na yankin da suka haɗa da Fune, Potiskum, Fika, da Nangere. A shekarar 2017 aka gudanar da gasar karo  na biyu, lamarin da ya ƙara tabbatar da gasar a matsayin...
    Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara.   Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi da ‘yan bindiga.   “Dole ne in yaba wa sojoji, DSS, da ‘yan sanda, musamman ma Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, bisa nasarar aiwatar da wannan gagarumin kame.   “Ina so in jaddada cewa waɗannan nasarori da aka samu tare da wasu na daƙile ‘yan bindiga a jihar, sun samo asali ne daga haɗin kai da goyon bayan da gwamnatin jihar Zamfara ke baiwa ɗaukacin...
    Ya ƙara da cewa, “Da har yanzu ina cikin wannan gwamnati, zan fadi gaskiya a cikin tarurruka na sirri, kuma idan ba a ɗauki mataki ba, zan yi magana a fili. Duk wanda ke shakkar haka, ya duba tarihin aikin gwamnati na tun daga 1998.” El-Rufai ya kuma soki wasu da ya kira “’yan amshin shata” a gwamnatin Tinubu, yana mai cewa suna amfani da kuɗaɗen tsaro don kare duk wani abu da gwamnati ke yi, ko da kuwa ba abin karewa bane. Ya buƙaci Bwala da ya tuna cewa “Alkawari na farko shi ne ga Allah da ƙasa, kafin wani mutum ko hukuma.”
    Haka kuma, an naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta. Ya samu ƙwarewa a fannonin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen ƙara ƙarfin tsarin kuɗi na jihar. An kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Gudanarwa. Aikin sa shi ne kula da gudanar da ayyukan ma’aikatu. Injiniya Abubakar Sadiq kuma an naɗa a matsayin Mataimakin Manajan Darakta na Hukumar Samar da Ruwa da Tsabtace Muhalli a Ƙauyuka (RUWASA). An ɗora masa alhakin inganta samar da ruwa da tsabtace muhalli a yankunan karkara. Haka kuma, an kafa kwamiti na musamman domin farfaɗo da Hukumar Sufuri...
۱