2025-03-16@13:48:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2108
«mutanen kasar Somalia»:
Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA sun cafke wasu mutane da hodar iblis da suka ɓoye a cikin carbi da kuma takalma. A cewar hukumar, an cafke ababen zargin ne yayin da suke ƙoƙarin safarar hodar iblis ɗin zuwa ƙasa mai tsarki. Femi Babafemi, darektan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NDLEA ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa tare da hotunan hodar iblis ɗin da aka kama.
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA “A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo. “Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.” Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA “A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo. “Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.” Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar...
“…The composition and functioning of the legislatibe council, howeber, pointed to the fact that, it was nothing more than a mere rubber-stamping institution…”. (Fagge & Alabi, 2007: 5b). Wadancan kalamai na sama cikin harshen Turanci, na yin nuni ne da cewa, “yan majalisun Nijeriya a wancan lokaci da Turawan Birtaniya ke mulkarmu, ba su kasance komai ba, face “yan-abi-yarima ne cikin harkokin zaman majalisar. Duk abinda aka yanke a majalisar, kawai sai dai su sanya-hannu ne akai. Ba su da ikon tabbatar da wani kudiri, koko yin watsi da shi. Tun da, hatta mafi yawan adadin mutanen da ke cikin zauren na majalisar, za a samu cewa, gwamna ne ya zabe su da hannunsa, kamar yadda a rubutun baya aka...
Abinda ya sa nike fatan ganin na zama gwamna shi ne saboda banida wani burin da ya wuce in ga cewar matsalar tsaro ta kau a Nijeriya musamman Arewacin kasar inda wasu ke wasa da rayukan al’umma saboda wata bukata ta kashin kansu, wasu tsiraru na amfani da rayukan mutane a matsayin kasuwanci ko kuma don neman daukaka ya kara da cewa. A ci gaba da hirar Sadik ya amsa tambayar da aka yi mashi a kan fina-finan da yayi da kuma wadanda yake kallo a matsayin wanda yafi so a cikinsu, inda ya ce daga cikin fina-finan da ya fito wadanda kuma yafi so, akwai Mati Da Lado sai kuma wani fim mai suna Dan Marayan Zaki. Abinda ya...
A ranar Juma’a ce Amurka ta bai wa Jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, wa’adin sa’o’i 72 ya tattara komatsai ya fice daga ƙasar. Hakan na ƙunshe cikin wata ’yar taƙaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’iakatar harkokin wajen Amurka, Chrispin Phiri ta fitar. Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya zargi Ebrahim Rasool da kasancewa “ɗan siyasar wariyar launin fata mai ƙyamar Amurka,” lamarin da ya ƙara rura wutar rikicin diflomasiyya da ya kunno kai tsakanin Washington da Pretoria. A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne Shugaba Donald Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa Amurka...
Mai Martaba Sarkin Kauru dake Jihar Kaduna Alhaji Zakari Ya’u Usman ya bukaci samun hadin kai da aiki tare kana da hakuri da juna tare da ɗaukar banbance banbance dake tsakanin al’umma a matsayin wata baiwa. Alhaji Zakari Ya’u II yayi wannan horonne lokacin da aka taru a fadarsa dake Kauru domin shan ruwan azumin Ramadan. Mai martaban ya bayyanawa wadanda suka taru domin wannan aikin lada na shekara shekara cewa, akwai bukatar yafiya da ‘yan uwantaka a wannan lokaci na Ramadan tare da godiya ga Allah da ya sake nuna mana wannan watan mai albarka. Alhaji Zakaria Ya’u Usman yace akwai bukatar sadaukarwa da mika wuya ga Allah da kankantar da kai tare da fahimtar cewa wannan banbanci...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...
Hajiya Asta Shehu Timta, mahaifiyar mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta ta riga mu gidan gaskiya. Wata sanarwa da Masarautar Gwoza da ke Jihar Borno ta fitar ta ce Hajiya Asta ta rasu ne yammacin jiya Asabar bayan shafe shekaru 80 a duniya. Yadda za a girka ‘Kamoniya’ An kama malama tana lalata da ɗalibinta Haka kuma, Hajiya Asta ita ce mahaifiyar Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwoza, Yarima Abba Kawu Shehu Timta. Masarautar ta ce za a yi jana’izar marigayiya Hajiya Asta Shehu Timta a yau da Lahadi bayan sallar azahur a Fadar Sarkin Gwoza. A lokacin rayuwarta, Hajiya Asta Shehu Timta ta kasance tsohuwar malamar makaranta kuma har zuwa rasuwarta tana taimakawa wajen ci gaban ilimi a...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar JMIa bude yake ga kasashen Turai don tattaunawa da fahintar juna kan matsalolin da bangarorin biyu suke sabani a kansu, tare da mutunta hurumin Juna. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiyaAsabar a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Netherlands Caspar Veldkamp a jiya Asabar. Ministan ya kara da cewa dangantakar diblomasiyya tsakanin Dutch da Iran tsohuwar dangantaka ce. Sannan Iran tana da nufin fadada shi. A Nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Netherlands yay aba da yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu yake bunkasa. Sannan dangane da tsabirin kasar Iran guda uku, Abu Musa, Tumbe kucek da...
Gwamnatin da kuma mutanen kasar Somalia sun ki amincewa da shawarar shugaban kasar Amurka Donal Trump na korar Falasdinawa a Gaza zuwa kasar Somalia. Shafin yanar Gizo na ‘Africa News’ ya nakalto yan kasar Somalia da dama suna fadar cewa yan kasar da kuma gwamnati ba zasu amince da korar Falasdinawa a Gaza, zuwa kasar Somalia kamar yadda shugaban kasar Amurka Donal Trump yake bada shawara ba. Mohamed Mohamed Elmi Afrah daya daga cikin mutanen kasar Somalia wanda Shafin labarai na ‘Africa News’ yayi wa tambayoyi danganne da haka, yace: Ban tsamman cewa mutanen kasar Somalia zasu aminjce ba haka ma gwamnatin kasar. Kafin haka dai wasu da dama suna ganin korar Falasdinawa daga Gaza ra’ayin yahudawan sahyoniyya ne, amma...
Ministan harkokin wajen kasar Iran y ace gwamnatin kasar Amurka bata da hakkin tsarawa kasar Iran yadda zata gudanar da manufofinta harkokin waje, wannan ya wuce tun bayana nasarar juyin juya hali musulunci a kasar a shekara ta 1979. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X. Aragchi yana maida martani ne ga shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya tuta sojojinsa suka kai hare-hare kan kasar Yemen a jiya Asabar, don kada su hana jiragen ruwan HKI wucewa daga tekun Red Sea. Kuma ya ce: Ya gargadi Iran ta dakatar da tallafin da take bawa kungiyar Ansarullah. Don itace da alhakin duk abinda kungiyar take yi. Ministan ya kara da...

Ma’aikatar Harkokin Wajen JMI Ta Yi Allawadai Da Kungiyar G7 Wacce Ta Zargin Kasar Da Abubuwa Da Dama
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baka’e ya tir da kungiyar kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya,wato G7. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma yi All..wadai da zarge zagren kungiyar wadanda suka hada da zargin Iran da kokarin mallakar makamin Nukliya, da hadsa fitina a kudancin Asia. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran yace dukkan wadannan zarge-zarge basa da toshe. Sannan ya zargi kasashen kungiyar na G7 da goyon bayan HKI a kissan kiyashin da ta aikata a Gaza. Kafin haka dai kasashen kungiyar ta G7 sun kammala taronsu a kasar Canada a ranar jumma’ar da ta gabata inda suka, suka fidda bayanin bayan...
Saboda haka ne, hukumar ta shawarci manoman da ke da ra’ayin noma a kakar noman ta bana da su tabbatar sun tuntube ta, ko kuma tuntubar sauran hukumomin da ke hasashen yanayi, domin sanin lokacin da ya ya fi dacewa su yi shuka. Hukumar ta yi hasashen cewa, jihohin Zamfara, Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Filato, Bauchi, Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Neja, Kwara, Kogi, Abuja, Ekiti da kuma Ondo, za su fuskanci daukewar ruwan sama da wuri, inda aka kwatanta da na dogon zango da aka samu a daminar bara. Haka zalika, hukumar ta yi hasashen cewa; za a samu jinkirin ruwan sama a wasu sasssan jihohin Kaduna, Nasarawa, Benuwe, Legas, Kwara, Taraba, Oyo, Ogun, Kuros Riba, Delta, Akwa Ibom, Ebonyi,...
Duk da kokarin da ma’aikatan asibitin suka yi na ceto shi, rahotanni sun ce ya samu raunuka da dama ciki har da guda daya a zuciya. Jaridar Irish Mirror ta ruwaito cewa ‘yansanda suna tsare da Eghomwanre har zuwa lokacin da zai gurfana a gaban alkali Michele Finan a kotun gundumar Dublin. A yayin shari’ar, Garda Grainne Collier ya bayar da rahoton kama Eghomwanre, tuhuma, da kuma taka tsantsan. An ce wanda ake zargin yana fuskantar tuhume-tuhume da dama da suka hada da cin zarafin Babatunde a titin Anne South, da laifin cin zarafin abokinsa, Adetola Adetuilehin, a layin Duke, da kuma tashin hankali. Alkalin kotun mai shari’a Finan ya ba shi taimakon shari’a, inda aka tsare shi a gidan...
Da safiyar yau Lahadi, sojojin Amurka da Birtaniya sun ci gaba da kai wa kasar Yemen hare-hare, inda a bayan nan su kai wasu jerin hare-hare guda uku. Yankunan da hare-haren na Amurka da Birtaniya su ka shafa a cikin Yemen sun hada “ali Sabba”, dake gundumar Sahhar, da hakan ya yi sanadiyyar kashe daruruwan dabbobi. Haka nan kuma sojojin na Amurka sun kai wasu hare-haren a gabashin Majzar, dake gundunar “Ma’arib”. Tun da marecen Asabar ne dai sojojin na Amurka su ka shelanta kai wa Yemen hare-hare a biranen San’aa,Sa’adah, da Zammar. A birnin Sa’adah, kananan yara 4 sun yi shahada sai kuma wata mace, yayin da wasu mutane fiye da 10 su ka jikkata. Wasu yankunan da hare-haren...
Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin tunawa da shahid Mahadi Bakiri a garin Tabriz ya bayyana cewa;; Babu yadda za ayi jamhuriyar musulunci ta Iran ta bude tattaunawa da Amurka a karkashin barazana, yana mai kara da cewa; yin gwawarmaya da jajurcewa a gaban masu girman kai da daga hanci, yana daga cikin muhimman koyarwar alkur’ani mai girma da kuma tsarin musulunci. Manjo janar Salami ya kara da cewa; ta hanyar tsayin daka da dunkulewar al’umma wuri daya, za a kai ga samun nasara. Haka nan ya kara da cewa; A tsawon shekaru 46 da su ka gabata, al’ummar Iran ta kasance a cikin fadaka wajen fuskantar duk wata...

Kungiyoyin Falasdinawa Suna Cigaba Da Yin Allawadai Da Hare-haren Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta yi Allawadai da Hare-haren Amurka da Birtaniya akan kasar Yemen Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da bayani na yin tir da hare-haren da jiragen yakin Amurka da Birtaniya su ka kai wa Birnin San’aa a jiya Asabar da dare. Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta fitar da bayani na yin Allawadai da Amurka saboda harin da ta kai wa Yemen din, tana mai bayyana abinda ta aikata da cewa abin kunya ne da nuna goyon bayan ga laifukan da HKI take aikatawa akan al’ummar wannan yankin. Kungiyar Jiahdul-Islami ta kuma yi jinjina ga kasar Yemen saboda yadda su ka tabbatar da jarunta ta asali irin ta Larabawa da musulmi wajen nuna goyon bayan...
An kama wata malamar makarantar sakandare ta California a Amurka da ake zargi da lalata da wani ɗalibi mai shekaru 17. Wannan da ba shi ne karon farko ba da aka tuhumi wani da irin wannan hali ba a makaranatar. Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi Soja ya shafe mako guda da harsashi a cikin ƙwaƙwalwarsa An kama malama Dulce Flores, mai shekara 28 bayan da ta kulla dangantakar da ba ta dace ba da wani dalibi dan shekara 17 a makarantar sakandare ta Riberbank a 2023, a cewar ’yan sandan Riverbank. Malamar wacce take koyar da harshen Sipaniya tana aiki a makarantar tun 2016. Haka kuma a cewar shafinta na...
A lokacin da Abba Musa angon da za a daura wa aure, da wasu mutum huɗu suka kama hanya zuwa kauyen Murno daga garin Boto a Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, babu wanda ya yi tunanin cewa shi angon da ’yar uwar amaryarsa, Raihanatu Sulaiman za su rasa ransu mintoci kadan kafin a daurin auren. Kafin ɗaurin auren ne Abba Musa da Maryam Sulaiman amarya da kuma Rainahatu Sulaiman (’yar uwar amarya) da Misbahu Ahmad (abokin ango) da direban motar sun tafi garin Murno da ke da nisan kilomita 5 daga Boto domin gaisawa da ’yan uwan amaryar kamar yadda aka saba a al’adar Hausawa. Soja ya shafe mako guda da harsashi a cikin ƙwaƙwalwarsa Nijar ta kori...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kamitin Zakka na Masarautar Hadejia ya raba zakkar kayayyakin amfanin gona da na kudi kimanin naira miliyan 63 a gundumar Birniwa dake Jihar Jigawa. Sakataren kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Injiniya Isma’ila Barde, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon zakka ga mabukata a gundumar Birniwa. Injiniya Isma’ila Barde ya lissafa abubuwan da aka bayar a matsayin zakka, da suka hada da buhunan Gero 668, da Bahunan Dawa 152 da bahunan shinkafa 8 da rabi da Kuɗi kimanin naira miliyan 17 da dubu ɗari tara da goma sha shida. A nasa jawabin, Shugaban kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Barrista Abdulfatah Abdulwahab wanda babban limamin masarautar Hadejia Ustaz Malam Yusuf Abdurrahman ya wakilta, ya yaba wa al’ummar Birniwa bisa bayar da...
Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta fara atisayen tantance gwanintar harbi na shekarar 2025 daga ranar Litinin 17 zuwa 19 ga watan Maris a Barikin Yar Gaba da ke Dutse, Jihar Jigawa. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya ta 26 Armoured Brigade, Laftanar Uzoma Egwu-Ukpai, ya sanyawa hannu aka kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse. Sanarwar ta bayyana cewa, atisayen tantance gwanintar harbi ana yi ne domin auna ƙwarewar jami’an soji wajen sarrafa makamai da ingancin harbinsu. Laftanar Uzoma Ukpai ya shawarci al’umma da kada su firgita yayin atisayen idan suka ga sojoji suna kai-komo ko suka ji karar harbi, musamman mutanen da ke zaune...
Kafofin yada labaran kasar Rasha sun yi ta jinjina wa wani sojan kasar a matsayin jarumi saboda ci gaba da fafatawa a yankin Kursk tsawon mako guda bayan harbin da aka yi masa a ka. Mutumin da ba a bayyana sunansa ba, wanda aka ruwaito cewa yana cikin Brigade na 155 na Marine na Rukunin Pacific Fleet na Rasha, ya ci gaba fafatawa da sojojin Ukraine a Kursk lokacin da aka harbe shi. Nijar ta kori wasu kamfanonin China 3 daga ƙasar Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa A lokacin an harbi hular kansa, amma yana tunanin tabbas harsashin ya huda cikinta. Ya samu kumburi a saman idonsa, wanda daga ƙarshe ya sa...
Ya kara bayanin cewar Jami’ar za ta dauki sahun dalibanta na farko wato shekarar karatu ta 2025, inda ya kara jaddada aniyar gwamnati ta bada damar samun yin karatu na ilimi mai zurfi tare da bunkasa shi. Ministan har ila yau ya ce zai taimaka wajen tabbatar da cewar Jami’ar ta samu nata kason daga Hukumar kula da ilimin manyan makaratun ta kasa, domin hakan zai taimakawa bunkasa Jami’ar cikin wani lokaci nan gaba. Ya ci gaban da bayanin “Zan tabbatar da cewar Jami’ar ta samu taimako na gidauniya kula da ilimi mai zurfi ta lamurran manyan makarantu ta samun kudade daga wurinta wannan shekarar. Don haka wannan rana ce ta farin ciki ga al’ummar Kudancin Kaduna, al’ummar Jihar Kaduna,...

Tsohon Firaministan Lebanon: Rashin Fahimta Da Shakku Daga Waje Ba Za Su Iya Dakatar Da Ci Gaban Kasar Sin Ba
Daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2024, an gudanar da taron kasa da kasa na “Fahimtar kasar Sin” a birnin Guangzhou. A yayin taron, fiye da baki 600 na kasar Sin da kasashen waje, ciki har da tsohon firaministan kasar Lebanon Hassan Diab, sun hallara don tattaunawa da yin musayar ra’ayi kan taken “Yin gyare-gyare-zamanintarwa irin ta kasar Sin da sabbin damammakin ci gaban duniya”, inda suka samu ra’ayin bai daya na gudanar da hadin gwiwa. A tattaunawar da ya yi da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, Hassan Diab ya bayyana cewa, fahimtar kasar Sin yana da matukar muhimmanci, domin kasar na bude kofarta ga duniya. A cikin...
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta kori manyan jami’an wasu kamfanonin CNPC da WAPCO da SORAZ na China daga ƙasar. Haka nan, gwamnatin ta kuma soke lasisin wani babban Otel na China da ke birnin Yamai. Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa ’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a Katsina Gwamnatin Nijar ɗin na zargin kamfanonin da ƙin mutunta dokokin aiki a ƙasar da ma na yarjejeniyar aiki da suka sanya wa hannu. Wasu majiyoyi na kusa da gwamnatin sun tabbatar da cewa tun a ranar Larabar da ta gabata Shugaba Janar Abdourahmane Tchiani ya bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga manyan daraktacin kamfanonin CNPC mai aikin haƙar man fetur...
A baya-bayan nan, jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te, wanda ya kira kansa da “mai rajin neman ‘yancin kan Taiwan”, ya kara ikirarin cewa bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan ba sa karkashin ikon juna, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokradiyya ce mai mulkin kanta. Amma duk yunkurin Lai Ching-te ba zai iya canza gaskiyar da duniya ta amince da ita ba, wato Taiwan ba ta taba zama kasa ba, kuma ba za ta taba zama ba a nan gaba. Sunan yankin Taiwa a MDD shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Manufar Sin daya tak a duniya ra’ayin bai daya ne na al’ummomin duniya, kuma bisa ka’idar ne kasashe 183 suka kulla huldar diflomasiya da Sin....
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya nada tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, a matsayin mai ba shi shawara ta musamman, kuma mai kula da shirin samar da sauyi a fannin kiwo. Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa, ya tabbatar da nadin na Jega a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a da ta wuce. Kalaman Lai Chin-te Na Shan Suka A Fadin Taiwan NPA Za Ta Yunkuro Don Zamanantar Da Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya – Dantsoho Sanawar ta ce, Tinubu ya yi fatan nadin na Jega, zai kawo ci gaba a harkar noma da kiwo, tare da karfafa yunkurin raya kasar. Kafin wannan nadin na Jega, ya...
Amurka ta baiwa jakadan Afrika ta Kudu a kasar wa’adin sa’o’i 72 na ya san idna dare ya yi masa. Hakan dai na zuwa ne bayan da Amurkar ta ce ba ta maraba da Jakadan na Afirka ta Kudu a kasar Ebrahim Rasool. Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya zargi jakadan da na Afrika ta Kudu da nuna “kiyayya” ga shugaban Amurka Donald Trump. Marco Rubio ya ce Ambasada Ebrahim Rasool “yana kara ruruta wutar rikicin kabilanci kuma gwamnatin Trump ba ta da wani abin da za ta ce masa.” Tuni Fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta mayar da martani inda ta ce ta yi na’am da matakin. Sanarwar ta ce “abin takaici ne korar jakadan na Afirka...
Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da matakin hadin gwiwa da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na hana watsa tashar talabijin ta Al-Aqsa ta Larabci ta Falasdinu da ke da alaka da kungiyar gwagwarmayar. Kungiyar ta bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na toshe muryar Falasdinawa. Sanarwar da Hamas ta fitar ta kara da cewa, wannan shawarar toshe ‘yancin watsa labaru ne da kuma hakki na al’ummar Falasdinu na a ji muryarsu a duniya.” Hamas ta yi kira ga cibiyoyin yada labarai na kasa da kasa da su yi Allah wadai da wannan shawarar, kuma kada su yi shiru dangane da cin zarafin da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin jin kai. Bisa shawarar...
Gwamnatin Trump na duba yiwuwar sanya takunkumin hana zirga-zirga ga ‘yan kasashen duniya 41 a wani bangare na yaki da kwararar bakin haure da aka kaddamar a farkon wa’adin shugaban na Amurka na biyu. Wani bayanin cikin gida da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nakalto ya nuna cewa an rarraba wadannan kasashe zuwa rukuni uku. Rukunin farko na kasashe goma, da suka hada da Afghanistan, Iran, Syria, Cuba da Koriya ta Arewa, za a sanya musu takunkumi baki daya. A rukuni na biyu, Eritrea, Haiti, Laos, Myanmar, da Sudan ta Kudu za su fuskanci dakatarwar wani bangare da ya shafi bizar masu yawon bude ido da dalibai, da kuma biza na bakin haure, tare da wasu kebantattu. Rukuni na...
Rahotannin dake fitowa daga Falasdinu na cewa wani hari da Isra’ila ta kai a arewacin zirin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa tara, ciki har da ‘yan jarida uku a cikin gida, in ji ma’aikatan lafiya. An kai harin ta sama a wata mota a garin Beit Lahiya da ke arewacin zirin yau Asabar. A cewar likitocin, mutane da dama sun samu munanan raunuka, tare da jikkata a ciki da wajen motar. “An kai shahidai tara zuwa asibiti, da suka hada da ‘yan jarida da dama da ma’aikata daga kungiyar agaji ta Al-Khair, sakamakon harin da aka kai wa motar da wani jirgi mara matuki a garin Beit Lahia, tare da luguden wuta a yankin,” in ji kakakin hukumar tsaron farar...
Kasar Sin ta bayyana matukar adawa da zarge-zargen kungiyar G7 kan tekun kudancin kasar da manufofinta na tattalin arziki, kuma ta bayyana korafinta ga kasar Canada. Ofishin jakadancin kasar Sin dake Canada ne ya bayyana haka a yau Asabar. A cewar ofishin jakadancin, sanarwar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 da sanarwar ministocin game da tsaron teku, sun yi shisshigi cikin harkokin gidan Sin, kana sun bata mata suna. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce fim ɗin tarihin zai nuna nasarori, ƙalubale, da darussan da aka koya a wannan tafiya. Ya ce: “Na yi farin cikin ganin ƙoƙarin da IPAC da shugabannin ta suke yi wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya, musamman ta hanyar fim ɗin wanda zai zama wata muhimmiyar shaida ta tarihi, domin girmama jaruman siyasar ƙasar mu da kuma nuna jajircewar Nijeriya a harkar dimokiraɗiyya. A kan haka, Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, za ta goyi bayan shirya wannan fim na musamman.” Ya jinjina wa IPAC kan jajircewar ta wajen cigaban dimokiraɗiyya tare da jaddada muhimmancin haɗin kan jam’iyyun siyasa bayan zaɓe domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da cigaba. “Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed...
A ranar Litinin, Ratcliffe ya shaida wa BBC cewa wasu daga cikin ‘yan wasan Manchester United ba su da ƙwarewa, amma ana biyansu albashi mai yawa fiye da yadda ya dace. Ya kuma bayyana shirin gina sabon filin wasa mai tsadar Yuro biliyan 2, wanda zai iya ɗaukar mutum 100,000 idan aka kammala. A ‘yan kwanakin nan, magoya bayan Manchester United sun ci gaba da nuna fushinsu kan iyalan Glazer, masu mallakar sama da kashi 70 na kulob ɗin. Har ila yau, Ratcliffe bai samu cikakken goyon baya daga ma’aikatan ƙungiyar ba tun bayan zuwansa a shekarar da ta gabata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
’Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani gwarzon musabaƙar karatun Al-Qur’ani a Jihar Katsina, Abdulsalam Rabi’u Faskari, suna neman naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa Da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, Kwamishinan watsa labarai da al’adu na Katsina, Bala Salisu-Zango ya ce Abdulsalam da mahaifinsa da ɗan uwansa da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, suna nan da ransu a hannun ’yan bindiga, ba a kashe su ba. ’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu Minista ya caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu da APC Ya ce “Gwamnati ta samu labarin wani saƙon jaje da ake yaɗawa wanda mai ba gwamnan jihar Kebbi shawara kan harkokin watsa labarai ya sa...
Ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya caccaki Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, kan sukar jam’iyyar APC da kuma Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. A cikin wata sanarwa da hadiminsa, Seyi Olorunsola, ya fitar, ministan ya zargi El-Rufai da haddasa rikici saboda bai samu muƙamin minista ba. Sojoji sun hallaka shugabannin ’yan bindiga 2 da wasu a Katsina Kotun ɗaukaka ƙara ba ta soke naɗin Sanusi II ba — Gwamnatin Kano Ya ce tsohon gwamnan mutum ne da ƙware wajen haddasa ce-ce-ku-ce da kuma yanke tsauraran hukunci a harkokin siyasa. Ata ya ce lokacin da El-Rufai yake gwamnan Kaduna, an samu matsaloli da suka haɗa da rashin tsaro, rikicin ƙabilanci da addini. Ya kuma ce komawar...
A jiya juma’a ne dai firma ministan kasar Iraki Muhammad Shi’ya al-Sudani ya sanar da cewa sojojin kasar sun kashe babban dan ta’adda Abdullahi Makki wanda ake yi wa lakabi da Abu Hadiza. Al-Sudani ya kara da cewa; Iraki taba cigaba da samun nasara akan ‘yan ta’adda, bayan da jami’an tsaro na kasa da kasa su ka yi nasarar kashe Abdullahi al-makki, wanda ya kasance a matsayin mataimakin shugaban abind ake kira da Daular Musulunci a Iraki da Syria.
Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’oi ta nuna rashin jin dadinta da wasu manufofi na Gwamnatin tarayya musamman ma irin nau’oin harajin da ake cirewa duk wata ya maida albashinsu ya kasance tamkar miyar da babu Gishiri bare Maggi ko kuma Daddawa, shi yasa karin da aka yi na mafi karancin albashi na Naira 70,000 ya zama tamkar tafiyar Kura ne inda take yin Gaba ta kuma koma Baya. Wannan bayanin ya fito ne bayan da aka kammala taron kwamitin zartarwa na kungiyar manyan ma’aikatan Jami’oi na 50 wanda aka yiu a Jami’ar Gwamnatin tarayya ta Otuoke, Jihar Bayelsa, inda kungiyar ta nuna damuwarta kan manyan lamurra wadanda suke damuwar jin dadin ‘yan kungiyarta,kamar yadda ake samun toge a albashi inda bai...
Dakarun Sojin Saman Najeriya (NAF), sun kashe manyan shugabannin ’yan bindiga guda biyu, Gero (Alhaji) da Alhaji Riga, tare da wasu mayaƙansu sama da 20 a wani hari ta sama da suka kai a Jihar Katsina. Harin ya faru ne a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, a dajin da ke Ƙaramar Hukumar Faskari. Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin Amurka kan cin zarafin Kiristoci Kotun ɗaukaka ƙara ba ta soke naɗin Sanusi II ba — Gwamnatin Kano Rundunar Operation Fansan Yamma ta NAF ce ta ƙaddamar da harin bayan samun sahihan bayanai kan maɓoyar maharan. A cewar Mataimakin Kakakin NAF, Kyaftin Kabiru Ali, ya ce dakarun sun lalata sansanin maharan. “An kashe ƙarin ‘yan ta’adda a tsaunukan da ke kusa,...
Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau. Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa: Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma aiki tare.” Baya ga batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu, da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, Anwar Karkash ya zo da wasiki daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.
Cibiyar da take fitar da amfanin gona zuwa waje ta kasar Rasha, ta sanar da cewa; a cikin shekarar 2024 an sami karuwar kayan abincin da take fitarwa zuwa wasu kasashen Afirka da kaso 19% da kudin da su ka hau da dala biliyan 7. Wasu kasashen da Rashan za ta linka yawan alkamar da take aikewa su ne Moroko, Najeriya da kuma Kamaru. Yawan alkamar da kasar Rashan za ta aike zuwa Moroko ta kai ton 124,000,a 2024 kuwa yawan alkamar da ta aikewa ita ton 54,000. Ita kuwa kasar Najeriya yawan alkamar da Rashan ta aike mata ta tashi daga ton 48,000 zuwa ton 131,400. Alama ce muhimmin kayan abincin da kasar Rasha take aike wa nahiyar Afirka....
Kusan sojoji 1,300 ne kungiyar kasashen gabashin Afirka ta SADC su ka fice daga kasar jamhuriyar Demokradiyyar Congo, a lokacin da mayakan kungiyar ‘yan atwaye ta M23 suke cigaba da kama yankunan kasar. Wani mai sharhi akan al’amurran siyasar kasar ta Congo, Christian Moleka ya yi gargadi akan sake dagulewar al’amurra a gabashin kasar wanda dama can yana fama da matsalolin tsaro. Janyewar da sojojin na SADC su ka yi daga cikin kasar tana a matsayin wani babban koma baya ne, alhali gwmanatin Kinshasha tana fatan ganin wadannan sojojin sun taka rawa wajen takawa mayakan M23 birki,kamar yadda su ka taba yi a 2023. Sojojin na Congo suna fama da karancin kayan aiki da makamai, da hakan ya bai wa...
Gwamnatin kasar Pakistan ta ce da akwai hannuwan Afghanistan da kuma India a garkuwa da jirgin kasa na soja da aka yi a cikin kasar a ranar 13 ga watan Maris,wanda ya jefa mutanen kasar cikin damuwa akan batun tsaro. Mahukuntan kasar ta Pakistan sun kuma ce; Binciken farko ya tabbatar da cewa wasu masu dauke da makamai ne su ka yi garkuwa da jirgin kasar, da sun shigo ne daga iyakar Pakistan sai kuma wani dan India wanda ya shiya yadda za a yi. Gwamnatin kasar ta Pakistan ta sanar da tsananta matakan tsaro domin kame wadanda su ka yi garkuwa da jirgin da kuma daukar matakan hana, irin haka faruwa a nan gaba. Ya zuwa yanzu babu wata...
Ministan ayyuka da sufuri na kasar Lebanon Yusuf Rasamani ya bayyana cewa; Asarar da HKI ta jazawa kasar Lebanon a lokacin yaki ta kai dalar Amurka biliyan 14, tare da bayyana cewa kasar Rasha ta bijiro da cewa za ta taimaka. Rasamani ya fada wa Radiyon “Sputnik” na Rasha cewa; Suna ci gaba da aiki tare da babban bankin duniya, domin tantance barnar da yakin Isra’ila ya haddasa a Lebanon.” Bugu da kari ministan ayyukan na kasar Lebanon ya kuma ce; Ma’aikatar ta fara aikin debe baraguzai a cikin garuurwan da za su iya isa, wadanda babu sojojin HKI a cikinsu.” Haka nan kuma ya ce; Kasar ta Lebanon da kuma Bankin Duniya da Asusun bayar da Lamuni suna aiki...
Shi ma, Manajan Darakta na CDI, Roland Oroh, ya goyi bayan wannan ra’ayi na Dakta Anyebe Idoga, inda ya sanar da cewa; wannan aiki, zai kara karfafa karfin Nijeriya wajen fitar da kaya zuwa ketare. “Mun ji dadi kan fara wannan yarjejeniya da mu, domin wannan zuba hannun jari, zai taimaka wa Nijeriya wajen kara habaka fitar da ingantaccen nama zuwa ketare”, in ji Oroh. Kazalika, an bijiro da wannan hadaka ce, sakamakon yadda Saudiyya ta nuna sha’awarta, na son shigar da nama zuwa kasarta daga Nijeriya, wanda ya kai tan 176,000 a duk shekara, tare da kuma ciyawar dabbobi ta alfalfa hay da abincin dabbobi da ake sarrafawa da kuma Waken Soya. A yanzu haka, CDI na ci gaba...
“ Zuba hannun jari a bangaren da ake sauke kaya a Tashohin Jiragen Ruwa da kara fadada hanyoyin layin Jiragen kasa, za su iya taimakawa wajen bunkasa aiki da kuma kara sanya gasa a ayyukan tafiyar da Tashoshin Jiragen Ruwa. A cewar Dantsoho Ya sanar da cewa, samar da kyakaywan yanayin kasuwanci a kasar nan na da alaka da kokari da kuma yanayin gasar da aka samar na kasa a Tashishin Jiragen Ruwan, inda ya yi nuni da cewa, wadannan abubuwan sun taimaka wajen samun musayar kudade, daidaita tattalin ardikin kasar, kara habaka kauswanci da kuma samun masu zuwa zuba hannun jari. Dantsoho ya godewa Ministan Bunkasa Tattalin Arziki na Ruwa Adegboyega Oyetola, bisa goyon bayan ada yake ci gaba...
Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin da wani ɗan majalisar Amurka, Chris Smith, ya yi cewa ana tauye wa Kiristoci ’yancin addini a Najeriya. Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta ba su da alaƙa da addini, domin hare-haren ’yan ta’adda na shafar dukkanin Musulmi da Kiristoci. Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo Wadda ke damfara da sunan matar gwamnan Katsina ta shiga hannu Tuggar ya ce hare-haren da ake kai wa a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma ba sa ware mabiyan wani addini. Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa kan yadda ake yaɗa rahotannin da ba su dace ba, waɗanda ka iya haddasa rarrabuwar kawuna a...
Ya kara da cewa bisa sashin 10.7 da aka sake nazarinsa a 2019, ya rage cajin daga N65 zuwa N35 kan kowace hada-hada. Sai dai ya bayyana cewa za a biya Naira 100 ga duk wanda aka cire na Naira 20,000 ga kwastomomi daga wasu bankunan da ke yin mu’amala da ATM a harabar bankin. Onobun ya jaddada cewa abokan hulda daga sauran bankunan da ke yin mu’amala da ATMs a wajen harabar bankin, manyan kantuna, kasuwanni, da sauran wuraren taruwar jama’a, za a rika biyan su Naira 100 da karin N500. Majalisar a cikin kudurorin ta ta bukaci CBN da ya gaggauta dakatar da aiwatar da wannan manufa, har sai an yi huldar da ta dace da kwamitocin da...
“Gwamnati gaba daya ta dogara ne kan yadda za ta kyautata rayuwar jama’a, mun dauki lamarin matasa da muhimmanci sosai.” Ya tabbatar wa matasan cewa gwamnatinsa a kowani lokaci a shirye take wajen yin ayyukan tukuru domin kyautata rayuwar matasa da saukaka matsalolin da Nijeriya ke fuskanta. Kan kwamitin da ya kaddamar, Tinubu ya kalubalancesu da su yi aiki tukuru domin ganin rayuwar matasa ya samu tagomashi a kowani lokaci. Shi kuma a jawabinsa, ministan bunkasa harkokin matasa, Ayodele Olawande, ya ce, kwamitin za su yi aiki sosai wajen ganin an samu inganta shigo da matasa cikin sha’anin mulki. Olawande ya lura cewa gwamnatin Shugaba Tinubu gwamnati ce mai saurare da ke shirye ta mai da hankali tare da hada...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa jami’an ‘yan sanda kyautar gidaje 280 tare da bayar da gudunmuwar motoci 110 da babura 500 domin inganta tsaro a jihar. Wannan shiri na da nufin inganta jin daɗin jami’an tsaro da kuma ƙarfafa yaƙi da aikata laifuka da ta’addanci. MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3 A wajen bikin rabon kayayyakin a Maiduguri, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya jinjina wa gwamna Zulum kan goyon bayansa ga jami’an tsaro. Ya ce wannan tallafi mataki ne mai kyau wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Borno. “Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen...
Ma’aikatar harkokin wajen tarayyar Najeriya a Abuja ta musanta zargin da cewa ana kishe kiristoci a kasar. Jaridar Premium timnes ta Najeriya ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Jumma’a ta kuma kara da cewa rahotannin da suka yada wannan karaiyar sun son ingiza gwamnatin Amurka ta dauki Najeriya a cikin jerin kasashen da suke nuna bambanci a cikin mutanen kasashensu. Wanda ba hakaba. A ranar laraban da ta gabata ce kwamiti mai kula da al-amuran Afirka a majalisar dokokin kasar ta bukace gwamnatin Amurka ta dauki mataki a kan Najeriya saboda abinda ya kira kissan kiristoci a Najeriya . Shugaban karamin kwamitin Chris Smith yayi kira ga shugaba Trump ya dorawa Najeriya takunkuman tattalin arziki masu tsanan kan...

Jumhuriyar Najer Ta Bukaci Tarayyar Najeriya Ta Taimaka Don Warware Matsalar Karancin Makamashi A Kasar
Kimani makonni biyu Kenan jumhuriyar Najer tana fama da karancin man fetur a gidajen man kasar, wanda ya rage zirga-zirgan ababen hawa a duk fadin kasar har da Yemai babban birnin kasar, har’ila yau ya shafi harkokin tattalin arzikin kasar. Shafin yana labarai na yanar gizo IR News, ya bayyana cewa bayan da gwamnatin sojojin kasar ta kasa magance matsalar a cikin gida, ta tura wata tawaga karkashin jagorancin Ministan man fetur na kasar zuwa tarayyar Najeriya tare da bukatar ta aiko mata tataccen man fetur don magance matsalar. Labarin ya kara da cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya dai tuni ta amince da bukatar, tare da bada umurnin a aikawa Jumhuriyar ta Niger tankunan man fetur har 300. Wasu wadanda suka...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye ta bada sanarwan cewa a shirye take da saki fursinonin HKI da Amurka, har ma da gawakin wasu 4, idan HKI ta dawo kan ci gaba da aiwatar da abubuwan da yarjeniyar tsagaita wuta a tsakaninta da HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani Jami’in kungiyar yana fadar haka a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, wasu daga cikin wadanda suke tsakanin kungiyar da HKI ne ya bata wannan shawarar, sannan ya kara da cewa, sai dai wannan matakin yana da sharudda, kuma sune HKI ta amince ta dawo kan tattaunawa marhala ta biyu don aiwatar da yarjeniyar da aka cimma...
Jakadan JMI na din din din a MDD Amir Saeed Iravani ya yi tir da HKI kan yadda take amfani da Kalmar “ta’addancin Addinin musulunci’ don rabawa addinin ayyukan ta’addanci. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Iravani yana fadar haka, a taron yaki da kin addinin musulunci a kasashen yamma da kuma kasashen da suke fama da karancin sanin addinin musulunci a duniya. Iravani ya kara da cewa, shekaru uku da suka gabata ne babban zauren MDD ya samar da kuduri mai lamba 73/254 don yaki da kin musulmi da addinin musulunci a duniya. Jakadan ya yi tir da Banyamin Natanyahu Firai ministan HKI da yawan amfani da kalmomi wadanda suke rabawa addinin musulunci ayyukan ta’addanci. A...
Gwamnatin kasar Amurka ta ce bata bukatar samuwar jkadan kasar Afrika ta kudu Ebrahim Rasool a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Jumma’a, ya kuma kara da cewa Rasool mutum ne wanda yake nuna wariya, yake kuma kin Amurkawa. Don haka bama da abinda zamu tattauna da shi, kawai bama son ganinsa a cikin kasar babba. Rubio bai bayyana dalilan daukar wannan matakin a kan jakadan ba, amma hakan ya faru ne bayan da Jakadan Rasool ya wata cibiyar bincike na Afrika ta kudu inda a jawabin da ya gabatar ya zargi shugaban kasar Amurka Donal Trump da, da samar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta ƙaryata zargin da Tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ya yi cewa jami’an tsaro sun sace tsohon Kwamishinansa, Jafaru Sani. El-Rufai ya yi wannan iƙirari ne a shafinsa na sada zumunta cewa an ɗauke tsohon Kwamishinan kamar fursuna ba tare da bin ƙa’idojin doka ba. Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi Ya yi zargin cewa wata “ƙungiyar masu garkuwa da mutane” da ke da alaƙa da Gwamna Uba Sani ce ke da alhakin ɗauke tsohon Kwamishinan. Da yake mayar da martani, kakakin ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ya bayyana zargin a matsayin ƙarya. “Babu wata ƙungiyar...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba. Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar, Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa kotun kawai ta dakatar da aiwatar da hukuncinta har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kan shari’ar. MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP Baffa Bichi da Barau Jibrin sun gana a Abuja Ya jaddada cewa kawai Kotun Ƙoli ce ke da ikon sauya hukuncin mayar da Sanusi kan karagar mulki. “Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke hukuncinta na baya ba. Kawai dai ta dakatar da aiwatar da shi har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe,” in ji Dederi yayin da yake magana...
Babban dan majalisar zartaswar kasar Sin, kuma shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Zhao Leji, ya jaddada matsayar kasar Sin ta dakile duk wani yunkuri na samun ’yancin yankin Taiwan, da yunkurin ’yan aware, da duk wasu matakan tsoma hannu cikin harkokin gidan kasar Sin daga sassan waje. Zhao, wanda ya bayyana hakan yau Juma’a a nan birnin Beijing, yayin wani taron karawa juna sani, albarkacin bikin cika shekaru 20 da fara aiwatar da dokar haramta ware wani yankin kasa, ya jaddada muhimmancin ci gaba da bunkasa manufar dinke sassan kasar Sin wuri guda. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Wani jami’in yada labarai na babban yankin kasar Sin ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ba za a amince da duk wani mahaluki ko wata runduna da za ta raba yankin Taiwan da kasar Sin ba, kuma babu yadda za a yi a lamunce da ayyukan “ballewar Taiwan” ta ko wace hanya. Jami’in yada labarun, da ke aiki a ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin, Chen Binhua ya kara da cewa, matukar dakarun ‘yan awaren suka kuskura suka bari tura ta kai bango, za a dauki kwararan matakan mayar da martani a kansu. Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta...
Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi da tsohon Kwamishinan sa ido da tantance ayyuka Muhammad Diggol sun gana da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin a Abuja. Taron ganawar wanda ya haɗa sauran masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan samar da ci gaba a Jihar Kano da kuma ciyar da ƙasa gaba. MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a Legas A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau ya wallafa hotunan ganawar da aka yi tare da bayyana muhimmancin haɗin gwiwa wajen samun ci gaba mai ɗorewa. “Ci gaban jiharmu da ƙasa a kodayaushe yana kan gaba a ajandarmu, za...
Da yake jaddada cewa ya kamata mutane su fahimci cewa a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, ba wai shi kadai ke wakiltar mazabarsa da jam’iyyarsa ba, har ma da yankin da ba a taba rike wannan mukami ba tsawon shekaru 46 da suka gabata.Shugaban majalisar ya bukaci wadanda ke sukar sa da su yi shiru da bakinsu. Akpabio ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa ba wai kansa kadai yake wakiltar ba, al’ummar yankin Neja Delta gaba daya ba yake wakilta. A yayin da yake jawabi a kan batun samar da kujerun zama da ya shafi Natasha Akpoti-Oduaghan, wanda ya kai ga zargin cin zarafi, Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa mutane suna ihu ne kawai ba tare da fahimtar ka’idojin...
Rashford, mai shekaru 27, ya buga wa Ingila wasanni 60 tare da cin ƙwallaye takwas. Amma bai samu dama a hannun tsohon koci Gareth Southgate ba, inda aka cire shi daga gasar Euro 2024 da kuma Nations League ta 2024-25. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mahukuntan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, sun sanar da shirin fara yiwa ’yan mata dake makarantun karamar sakandare allurar rigakafin cutar HPV, mai haifar da karin bakin mahaifa kyauta, tun daga watan Satumban bana, a wani mataki na dakile karuwar mata dake kamuwa da cutar. A cewar sanarwar hadin gwiwa ta cibiyar kandagarki da shawo kan cututtuka ta birnin da sauran hukumomi masu alaka da aikin, wadda aka fitar a jiya Alhamis, ya zuwa karshen watan nan na Maris, ’yan mata da a yanzu haka ke ajin karshe na makarantun firamare, za su cike takardun amincewa da karbar rigakafin, kana ya zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, za a kammala yi musu kashin farko na rigakafin. An shirya gudanar...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da aka yi a baya-bayan nan a yammacin Syria, inda ya yi kira ga hukumomin rikon kwarya a kasar, da su kare “dukkan ‘yan Syria ba tare da nuna bambanci ba,” ba tare da la’akari da kabila, addini ba. Majalisar ta yi kakkausar suka kan tashe-tashen hankulan da ke faruwa a lardunan Latakia da Tartus tun daga ranar 6 ga Maris, ciki har da kisan kiyashin da aka yi wa fararen hula, musamman a cikin al’ummar Alawite, ‘yan tsirarun da ke da alaka da dangin tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad.
Iran ta yi kakkausar suka kan sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Ministan Man Fetur na aksar Mohsen Paknejad da wasu hukumomi da jiragen ruwa masu ruwa da tsaki a harkar danyen man fetur da kasar ke fitarwa, tana mai cewa matakin keta doka da munafunci ne daga bangaren Amurka. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baghaei ne ya bayyana hakan yau Juma’a, kwana guda bayan da ma’aikatar baitul malin Amurka ta kakaba takunkumi kan ministan man fetur na kasar Paknejad da wasu kamfanoni uku da ke da hannu a cinikin man Iran a kasar Sin. Mista Baghaei ya ce, sabbin takunkumin sun karyata ikirarin da jami’an Amurka suke yi kan aniyarsu ta yin shawarwari tare da Iran. Ya kara...
Dubun dubatar musulmi masu ibada ne suka gudanar da sallar Juma’a ta biyu na watan Ramadan a harabar masallacin Al-Aqsa, duk da tsauraran matakan da Isra’ila ta dauka na hana Falasdinawa shiga wurin mai tsarki. Sashen kula da masallacin da ke birnin al-Quds ya ce kimanin masu ibada 80,000 ne suka taru A daidai lokacin da ake fargabar ci gaba da tashin hankalin da gwamnatin Isra’ila ke yi ga mazauna yankin. Duk da wannan takunkumin, masu ibada sun yi ta tururuwa daga yankuna daban-daban na Yammacin Kogin Jordan don shiga wurin mai tsarki. Sojojin Isra’ila sun hana matasan Falasdinawa shiga daga Jenin da Tulkarm. Hamas ta yi Allah wadai da takunkumin Isra’ila a Masallacin Al-Aqsa
A jawabinsa na godiya a wurin taron, dan majalisar dokokin ya bayyana godiya ga al’ummar Funtuwa, ya ce zai ci gaba da kawo ayyukan alheri tare da abubuwan jin dadin more rayuwar ga al’ummar mazabunsa na Funtuwa da kewayenta gaba daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An tabbatar da mutuwar wata mata da har yanzu ba a bayyana sunan ta ba bayan ta yi tsalle ta faɗa kogin Legas daga gadar Third Mainland a Jihar Legas. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne daga wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Juma’a cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4 na yamma kusa da bakin ruwan kogin da ke hanyar jami’ar Legas. Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar “Tawagar ’yan sandan ruwa da ke aiki a wurin sun gano ta gaɓar ruwan da ke hanyar jami’ar Legas...
Takardar da aka yi nazari a karshen watan Janairu ta nuna cewa a watan Fabrairun 2025, an ware shirin samar da mai na kan naira zuwa jirgin dakon mai hudu ne kawai, rukuni hudu zalla, kuma a watan Maris, dakon man biyu ne kawai aka yi da ya kai ganga 950,000 (ganga miliyan 1.9 ga watan). Wannan yana wakiltar rabon ganga 61,290 a kowace rana kasa da makasudin 385,000 bpd a karkashin tsarin. Karancin samun danyen mai ya tursasa wa matatar man Dangote garzaya wa kasashen waje domin neman danyen man. A baya-bayan nan kamfanin ya samu gangar danyen mai miliyan 12 daga Amurka. Duk da dai har yanzu matatar Mai ta Dangote ba ta fito a hukumance ta yi...
Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi (Sarkin Dawaki Babba) bai gamsu da wannan hukunci ba, don haka ya shigar da ƙara yana neman a dakatar da aiwatar da hukuncin har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci. Ya shigar da Gwamnatin Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokokin Jiha, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Hukumar NSCDC, da sauran hukumomin tsaro ƙara. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta amince da buƙatar Dan Agundi, inda ta ce akwai hurumin shari’a a cikin ƙarar. Mai shari’a Abang ya bayyana cewa kotu dole ne ta yi adalci wajen yanke hukunci. Wannan hukunci yana nufin cewa dole ne dukkan ɓangarorin su ci gaba da zama yadda suke kafin Babbar Kotun Tarayya ta yanke hukunci. Bugu da ƙari, kotu ta umarci Dan...
Na hudu, kudurin Sin shi ne inganta hadin gwiwa ta hanyar tattaunawa, tare da adawa da neman kwamitin sulhu na MDD ya shiga tsakani. Bugu da kari, ministan ya ce Sin za ta tsaya kan dabarar daukar matakai daya bayan daya da saka alheri da alheri, da neman cimma matsaya ta hanyar tattaunawa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Jigawa, tare da hadin gwiwar Bankin Duniya, ta dauki nauyin dalibai sama da 500 a wani mataki na tsara makomar matasa a fannin fasahar zamani. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da shirin da kuma mika takardun shaidar karatu ga wadanda suka ci gajiyar shirin fasahar zamani na Innovation Development and Effectiveness in the Acquisition of Skills (IDEAS) a Jihar Jigawa. Malam Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatinsa na karfafawa matasa ta hanyar kirkire-kirkire a fannin fasahar zamani da kuma koyon sana’o’i don habaka tattalin arziki. “A yau, mun kammala horar da dalibai 240 da suka koyi yadda za su bunkasa harkokinsu na kasuwanci don tabbatar da ci gaba mai dorewa,” in ji gwamnan. “Haka...
Wani direban motar bas ya murƙushe wata yarinya ’yar shekara biyu a ƙoƙarin gujewa kamun jami’an hukumar kare haƙƙin jama’a na Jihar Edo. Lamarin ya faru ne a kan titin Ring Road da ke birnin Benin a ranar Laraba lokacin da jami’an hukumar suka yi artabu da wani direban motar bas a lokacin da suke ƙoƙarin kama shi. Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar Mun ceto Najeriya daga faɗa wa mummunan yanayi — Tinubu Shaidu sun ce lamarin ya ta’azzara ne a lokacin da jami’an da ke aikin suka tunkari direban inda yake ƙoƙarin tserewa ya sauya hanyar motar, amma jami’an sun kama sitiyarin motar. “Motar ta murƙushe wata yarinya da ke tsaye kusa da...
Sun nuna wannan bukatar ce, biyo bayan hasashen raguwar bukatar Manfetur din da kuma dabarar fitar da shi, daga kasashen da ba sa cikin kungiyar ta OPEC+. Sai dai, a ranar Litinin da ta gabata kungiyar ta tsaya daram kan tsarinta na kara yawan Man da ake hakowa a watan Afirilu. Kazalika, binciken na kafar Reuters ya kuma gano yawan adadin karuwar Man na OPEC wanda ya kai Ganguna 80,000 da suke fitowa daga kasar Iran wanda ya kai Ganuna miliyan 3.30, wannan ya kai daidai na alkaluman watan Satumba, wanda ya haura tun a 2018. Bugu da kari, binciken ya sanar da cewa, fitar da danyan mai daga Iran ya farfado lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka, Joe Biden duk...
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa sansanin soji a Ƙaramar Hukumar Arewa domin inganta tsaro. Ya yi wannan roƙo ne bayan ziyarar da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira a Kangiwa, bayan harin da wasu da ake zargin Lakurawa ne suka kai musu. Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3 Harin da aka kai a ranar 9 ga watan Maris ya yi sanadin mutuwar mutum 11 tare da ƙone ƙauyuka bakwai. Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Dogon Daji, Danmarke, Yar Goru, Tambo, Birnin Debi, Garin Nagoro, da Garin Rugga. “Sansanin soji a yankin zai taimaka...
Dan majalisar ya zurfafa da cewa kasashe da dama a yankin Asiya, Afrika da Gabas ta Tsakiya sun kafa dokokin da suka haramta yada abubuwan da suka shafi batsa a kasashensu. Domin tabbatar da kudirinsa, dan majalisar Katsina ya yi tsokaci kan gargadin da masana ilimin halayyar Dan’adam da ilimin zamantakewa suka yi game da mummunan tasirin batsa ga al’umma. A cewarsa, kallon batsa na iya janyo mutane zuwa ga tafka zina, karuwanci, da sauran ababen lalata. “Kwararrun masana ilimin halayyar Dan’adam da na ilimin zamantakewa a fadin duniya sun gabatar da gargadi kan kallon batsa, wanda ke kaiwa ga aikata manyan badala,” ya shaida. Kakakin Majalisar Dokoki na tarayya, Tajudeen Abbas, ya nemi mambobin majalisar da su tafka muhawara...
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa mutane bakwai sun rasa rayukansu a gobara daban-daban da suka afku a jihar cikin watan Fabrairu 2025. Rahoton ya kuma nuna cewa an samu tashin gobara 77, an gudanar da ceto 11, yayin da aka samu ƙarar bogar bogi guda uku a cikin wannan lokaci. Sanarwar da Kabiru Isah Jaafar ya fitar a madadin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ta bayyana cewa kadarori da darajarsu ta kai naira miliyan 50.3 sun lalace sakamakon gobara, yayin da aka ceto wasu kayayyaki da darajarsu ta kai naira miliyan 180.3. Haka kuma, an ceto rayuwa mutane bakwai da daga gobarar. Sabon Kwamishinan ‘Yansanda Ya Kama Aiki A Kano ‘Yansanda Sun...
Jihohin Sakkwato da Kebbi na fuskantar ƙalubale sakamakon cutar sanƙarau da ta ɓulla a jihohin, inda rahotanni suka tabbatar da cewa cutar ta kashe aƙalla mutum 50, yayin da sama da mutum 200 suka kamu da cutar. A Jihar Kebbi, ƙananan hukumomin Aliero, Jega, da Gwandu ne suka fi fuskantar matsalar, inda cutar ta fara yaɗuwa kafin a ɗauki matakan gaggawa. Wadda ke damfara da sunan matar gwamnan Katsina ta shiga hannu NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Ta A Najeriya A Jihar Sakkwato kuwa, ƙaramar hukumar Tambuwal ce ta fi fama da cutar, lamarin da ya sa hukumomin lafiya suka sanar da ɗaukar matakan daƙile cutar domin hana ta yaɗuwa zuwa sauran yankunan. Dalilin Yawaitar Cutar...
Alhaji Dangote, hamshakin attajirin nahiyar Afirka, ya ce sun hada kai da gwamnatin jihar ne wajen tabbatar da ganin an raba abincin ga mabukata a kowace jiha dake fadin Nijeriya. Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin abincin a matakin kasa na wannan shekara, ya ce aiwatar da wannan shiri ya nuna tsantsar halin nuna jinkai da kulawar Alhaji Aliko Dangote wajen kawar da yunwa da fatara a Nijeriya. Gwamnan wanda mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce za a raba buhun shinkafar guda dubu 120, mai nauyin kilogram 10 a daukacin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano. A jawabinta ga manema labarai, Babbar Darakta kuma Babbar jami’ar gudanarwar gidauniyar Aliko...
Sabon kocin Ingila, Thomas Tuchel ya cire ɗan wasan bayan Ingila Harry Maguire cikin jerin ƴanwasan Ingila da za su buga wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026. Cikin jerin ƴan wasa 26 da sabon kocin ƙasar Thomas Tuchel ya fitar, ranar Juma’a ya sanar da sunan Marcus Rashford bayan cire shi a wasannin baya. Haka ma kocin ya saka sunan tsohon ɗan wasan Liverpool da ke taka leda a ƙugiyar Ajax, Jordan Henderson cikin tawagar. A karon farko mai tsaron ragar Burnley, James Trafford da ɗan wasan bayan Liverpool, Jarell Quansah za su iya samun damar buga wa babbar tawagar Ingila ƙwallo ba a ke cikin tawagar A ranar Juma’a, 21 da watan Maris ne tawagar Ingila...
Gwamnatin mulkin sojin Sudan ta ayyana haramta duka kayayyakin da aka shigar da su ƙasar daga Kenya, a wani mataki na martani karɓar baƙuncin RSF da ƙawayenta da Nairobin ta yi. Ministan kasuwancin Sudan, ya ce an ɗauki matakin ne bisa shawarar, majalisar ikon ƙasar, wadda ta zargi Kenya da rura tashin hankali a Sudan. A ganawar da aka yi a Nairobi ce, RSF ta yanke shawar kafa gwamnatin ƴan adawa a wuraren da take iko da su tare da sanya hannu kan abin da ta kira ‘rubuta kundin tafiyar gwamnatin’. Sudan ce ƙasa ta 10 a duniya, sannan ta biyu a Afirka, cikin jerin ƙasashen da suka fi sayen ganyen shayin Kenya.
“Muna kokarin kawar da bangaren dala. Abin da muke so mu yi shi ne mu biya a cikin kudin gida na duk kamfanonin jiragen sama. Kuma za a biya kudin ne daidai da farashin dala a halin yanzu a lokacin da ake biya. “Kason da ya dace ya ba ku damar gudanar da ayyukanku dukkan ne za a biya ku, bayan kammala aikin za a karasa biyanku sauran,” ya shaida. Tun da farko, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya ce, ayyukan jirage na sufuri na daga cikin muhimman ayyukan da ke gabansu wajen sauke nauyin aikin hajji. “Lamarin na bukatar kwarewa matuka gaya da kuma himma da azama. Wannan lamarin ba kawai ga batun sufuri ba ne, ya shafi...
An kusa shiga mako guda daga lokacin da aka fara fuskantar karancin mai a gidajen man fetur da hakan ya jefa masu ababan hawa cikin damuwa. Rabon man fetur da kamfanin SONIDEP yake yi bai wadatar da masu abubuwan hawa ba, yana kuma kawo cikas a harkokinsu na yau da kullum. Da akwai dalilai da dama da su ka haddasa karancin man fetur din, sai dai al’ummar kasar suna son ganin mahukunta sun fito fili sun yi musu bayanin abinda yake faruwa. Wani mazaunin birnin Yemai Assoumane Hamadou suley ya fada wa manema labaru cewa; Ba mu da cikakken bayani akan abinda yake faruwa, domin mahukanta da ya kamata su fito su yi bayani, ba su yin hakan. Su kuwa...
Shugaban kungiyar agajin Falasdinawa ta “UNRWA’ wacce MDD ta kafa, ya yi gargadin rushewarta da hakan zai hana Falasdinawa na yanzu samun ilimi, haka nan kuma bayar da kayan agaji da bukatun yau da kullum ga mutane miliyan 6 a Falasdinu. Shugaban kungiyar Agajin Philippe Lazzarini ya fada wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa; Da akwai hatsari da gaske da kungiyar take fuskanta na rushewa, da hakan zai kara dagula yanayin da al’ummar Falasdinu suke ciki.” Philippe Lazzarini ya kara da cewa; Idan hakan ta faru, to mun sadaukar da falasdinawan da suke rayuwa a wannan lokacin da hana su ilimi. Tun bayan farmakon Aksa 2023 ne dai HKI da Amurka su ka dauki matakin haramta kungiyar da dakatar da...
A jiya Alhamis sojojin HKI sun cigaba da keta aiki da kuduri mai lamba 1701 ta hanyar yin shawagi a samaniyar Lebanon da kuma kai hare-hare a yankunan Jenta da Biqa. Tashar talabijin din ‘almanar ta watsa labarin da yake cewa; Jiragen yakin abokan gaba ‘yan sahayoniya sun kai hare-hare har sau uku a yankin al-sha’arah’ dake gabashin Jenta a Biqa. Da marecen jiya Alhamis din dai jiragen yakin HKI sun yi shawagi a kasa-kasa yankin Biqa, kamar kuma yadda sojojin nasu su ka jefa bama-bamai masu haske a yankunan Kafar-Shuba, dake kudancin Lebanon. Irin wadannan keta tsagaita wutar da sojojin HKI suke yi, yana sanya alamar tambaya akan aikin da kwamitin dake kula da tsagaita wutar yakin yake yi....

Taron Kasashen Iran, Rasha Da China A Birnin Beijing Ya Bukaci A Kawo Karshen Takunkumai Akan Tehran
A yau Juma’a ne aka bude taron kasashen Iran, Rasha da China, a matakin mataimakan ministocin harkokin waje inda su ka tattauna shirin makamashin Nukiliya na Iran. Mahalarta taron sun bukaci ganin an dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata, sannan kuma a warware batun shirinta na makamashin Nukiliya ta hanyar tattaunawa. Kasashen na China, Rasha da kuma Iran sun bayyana takunkuman na Amurka akan Iran da cewa, ba halartattu ba ne. Haka nan kuma sun ce; Tuntubar juna da kuma tattaunawar diplomasiyya bisa girmama juna ne kadai zabin da ake da shi domin cimma manufa. Taron da aka yi a yammacin birnin Beijing ya kunshi mataimakan ministan harkokin wajen Iran Garid Ridh Abadi, Sai Rasha Sergey Ryabkov da...
Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, tana yi ne da nufin gyara makomar yara masu tasowa. Yayin da yake jawabi ga kungiyar ‘Yan majalisa ta uku – wadda ya kasance cikin a Jamhuriya ta uku – da suka kai masa ziyara a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce a baya kasar na kashe kudaden yaran kasar da ba a kai ga haihuwarsa ba. “Shekara 50 da suka gabata, Najeriya na kashe kudaden yaran da ba a kai ga haihuwarsu ba, tare da mayar da hankali kan man fetur wajen samun kudin shiga. Ba a yi wani tsari na tallafa wa yaran da za a haifa a gaba ba,” kamar yadda ya ce....
Ya ce: “Bari in ce mun tsallake tudu, kuma wahalhalun da aka sha a baya suna raguwa yayin da tasirin waɗannan sauye-sauye suke fara bayyana. “A halin yanzu, muna gani muraran yadda farashin kayan abinci yake saukowa, farashin musayar kuɗaɗe yake daidaituwa, kuma farashin man fetur yana raguwa. Waɗannan duk alamu ne cewa ayyukan garambawul da ake aiwatarwa suna haifar da sakamako mai kyau.” Ministan ya bayyana cewa sauye-sauyen da suke da ma’ana ba su zuwa da sauƙi, domin suna buƙatar haƙuri, juriya, da kuma sadaukarwa don cimma cigaba mai ɗorewa. “Ƙasar mu tana kan wani muhimmin mataki yayin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake aiwatar da sauye-sauye masu ƙarfi domin gina sabuwar Nijeriya. Tarihi ya...
A makon da ya gabata Manchester United ta buga canjaras a wasan da Real Sociedad na gasar Europa League zagaye na farko a filin wasa na Reale Arena dake Sen Sebastian. Amma Man Utd ɗin ta gasgata abinda bahaushe ke cewa kowa a gidansa Sarki ne bayan ta zazzagawa Sociedad ƙwallaye 4 a raga, da kuma wannan sakamakon ne United wadda Ruben Amorim ke jagoranta ta tsallaka zuwa matakin na kusa da na kusa da na karshe a gasar ta Europa League. Manchester United Na Son Lashe Firimiya A Shekarar 2028 Bayan Shekaru 115 Manchester United Za Ta Gina Sabon Filin Wasa Kyaftin din masu masaukin baƙin Bruno Fernandes ne ya zura ƙwallaye uku rigis a wasan kafin Diogo Dalot...
Hukumar EFCC ta kama wata mata da mijinta bisa zargin yin sojan gona da sunan mai ɗakin Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda, wajen damfarar kuɗi Naira miliyan 197.75. An gurfanar da su a gaban babbar kotun Jihar Kaduna, tare da wasu mutum biyu da ake zargi suna taimaka musu wajen aikata laifin. ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3 NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Ta A Najeriya EFCC ta ce mutanen huɗu sun haɗa kai wajen amfani da sunan Hajiya Fatima Dikko Radda don samun canjin dala daga wani mai sana’ar canji. Matar ta gabatar da kanta a matsayin Fatima Dikko Radda, tana buƙatar a yi mata canjin dala. Mijinta...
Wannan lamari ci gaban da haifar da zazzafar martani daga jam’iyyun adawa da manazarta siyasa wadanda suka yi zargin cewa hakan ya saba wa dokar zabe da kundin tsarin mulkin 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima. Masana harkokin shari’a da masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa irin wannan kamfen da ba a kai ba, yana kawo cikas ga dimokuradiyya, da bin doka da oda da kuma tsarin zabe. A watan da ya gabata ne jam’iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa, Tinubu da Gwamna Nasir Idris a Jihar Kebbi as zaben 2027. Taron wanda aka gudanar a babban filin wasa na garin Birnin Kebbi, ya samu halartar ministan kasafi da tsare-tsare na tattalin arziki, Sanata...
‘Yan mata 74,452 ne suka ci gajiyar tallafin kudi a karkashin shirin samar da ilimi da karfafawa ‘yan mata matasa AGILE a fadin kananan hukumomi 19 da ke Kano, wanda ya kunshi rukuni daya da na biyu. AGILE wani shiri ne na taimakon Bankin Duniya na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya wanda aka tsara don inganta damar samun ilimin sakandare ga ‘yan mata masu tasowa tsakanin 10 zuwa 20. Aikin yana samar da cikakkiyar hanya don inganta daidaiton samun ingantaccen ilimi ga ‘yan mata masu tasowa ta hanyar inganta kayan aikin makaranta, samar da kudade na sharaɗi ga gidaje masu karamin karfi, magance ƙa’idodin zamantakewa waɗanda ke hana ‘yan mata zuwa makaranta, da kuma ƙarfafa ‘yan mata, da...
Babban magatakarda, sashin Nephrology, Federal Teaching Hospital Gombe (FTHG), Dr. Fidelis Linga ya bukaci jama’a da su rungumi salon rayuwa mai inganci domin hana kamuwa da cutar koda. Ya bayyana haka ne ga manema labarai a Gombe a yayin bikin ranar ciwon koda ta duniya. Dokta Fidelis Linga ya bayyana halaye marasa kyau kamar yawan shan barasa, shan taba, cin abinci mara kyau, da kuma salon rayuwa a matsayin abubuwan da ke haifar da hauhawar cututtukan da ke da alaƙa da koda. Ya kuma jaddada mahimmancin ziyarar asibitoci akai akai, da daidaita tsarin abinci, da motsa jiki a kai a kai wajen hana kamuwa da cutar koda. Ya bayyana cewa a duniya baki daya, mutane miliyan...
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Samar da Dokar Shirye-Shiryen Matasa Da Ayyukan Ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na karfafa matasa domin samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasar nan. Ministan ya ce ziyarar da ya kai jihar Sokoto na da nufin kara cudanya da matasa a cikin watan Ramadan da bayar da tallafi mai mahimmanci. Olawande, wanda ya samu rakiyar Seyi Tinubu, ya jaddada mahimmancin shirye-shiryen da suka shafi matasa, ciki har da samar da dandalin tattaunawa kan ci gaban matasa na kasa. Ya yi nuni da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da Gwamna Ahmed Aliyu suna da manufa daya na ci gaban matasa, ta yadda za...
Hukumar raya yankin arewa maso yamma NWDC ta bukaci gwamnatocin jihar Kano da su taimaka tare da hadin gwiwa da nufin cimma manufofinta. Shugaban Hukumar Alhaji Isma’il Lawal Abdullahi Yakawada ya nemi hadin kan a lokacin da ya jagoranci mambobin hukumar a ziyarar ban girma da suka kai wa gwamnan a gidan gwamnatin Kano. Ya ce hukumar ta NWDC na da burin tabbatar da ci gaba da bunkasar jihohin Arewa maso Yamma, tare da mai da hankali wajen magance matsalolin da suka addabi kasa kamar rashin tsaro, yunwa, fatara, da rashin abinci mai gina jiki. Ya nemi goyon bayan da ake bukata da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kano domin cimma aikin da ke gabansa. ...