2025-02-25@22:01:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1300
«Gajerun Labari»:
Gwamnatin Tarayya ta sanar das shirye-shiryenta na sake kara kudin wutar lantarki nan da watanni masu zuwa. Ta bayyana cewa ana tsara karin ta yadda zai zo da tallafi ga masu karamin karfi cikin masu amfani da wutar. Mashawarciyar Shugaban Kasa kan Makamashi, Olu Verheijen, ce ta sanar da hakan a Babban Taron Shugabannin Lantarki...
Shuwagabannin kasashen turai guda uku wato EU3 sun bayyana cewa daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar ya fi karfinsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran yana fadar haka a wata hira ta musamman da ta hada ta da tashar. Mohammad Eslami ya...

Iran Da Pakisatan Sun Jaddada Bukatar Samar Da Harkokin Kasuwanci Na Akalla Dalar Amurka Billiyon $10 A Tsakaninsu
Jakadan kasar Iran a Pakisatan ya bayyana bukatar shuwagabannin kasashen biyu su kara yawan musayar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, zuwa dalar Amurka biliyon $10. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Amiri Moghadam yana fadar haka a wani taro da aka gudanar tsakanin Jami’an kasashen biyu a cibiyar kasuwanci ta Rawalpindi a...

Wasu Hukumomi A MDD Sun Bada Sanarwan Cewa HKI Ta Fadada Yaki Kan Falasdinawa Daga Gaza Zuwa Dukkan Kasar Falasdinu
Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan...

Shugaban Kasar Amurka Ya Ce Nan Ba Da Dadewa Ba Zai Kara Kudin Fito Na Kayakin Da Ake Shigo Da Su Amurka Daga Kasashen Turai
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara...

Sheikh Na’im Kassim: Za A Yi Jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah A Rana 23 Ga Febrairu Da Ake Ciki
Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin. Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba...
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya yaba wa yadda kungiyar Hamas ta jajurce da ci gaba da wanzuwa a dunkunle duk da cewa kwamandan dakarunta Muhamamd Dhaif ya yi shahada. Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya gabatar da jawabi ne na tunawa da zagayowar lokacin shahadar Salih al-Simad wanda daya ne daga...
Ma’aikatan Agaji suna ci gaba da fito da gawawwakin shahidan Falasdinawa da Isra’ila ta rushe gidaje akansu, a tsawon lokacin yaki,wasu kuma akan hanyoyi. Wani jami’in agaji ya ce, bayan gushewar fiye da shekara daya na yaki, da wuya suke iya samun cikakkiyar gawar wani daga cikin shahidai, sai dai rabi da rabi, a wasu...
Da marecen jiya Lahadi ne dai shugaban Majalisar dokokin Iran Mahmud Mashahadani ya iso Tehran domin fara ziyarar aiki da zai gana da jami’an gwamnatin kasar. Mataimakin shugaban Majalisar Shawarar musulunci ta Iran Hamid Ridha Haji Babbayi da kuma shugaban kwamitin kawancen majalisun kasashen biyu ne su ka tarbi Mashhadani a filin saukar jiragen sama...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a jiya Lahadi Fira minista Benjamin Netanyahu ya bayar da umarnin a rushe gidajen na Falasdinawa. Kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa wannan shi ne hari irinsa na farko da aka rushe gidaje 100 a lokaci kadan. Masu bin diddigin abinda yake faruwa suna cewa, da alama...
Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta sanar da cewa ta kwato mutane 23 da masu garkuwa da mutane su ka kama a cikin dajin Kajuru da ke karamar hukumar Kajuru. Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan ya sanar a jiya Lahadi cewa sun kwato mutanan ne a ranar...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta bayyana cewa sama da mahajjata 3,000 da suka yi aikin Hajjin 2023 sun karɓi ragowar kuɗinsu da ya yi saura. Mai magana da yawun hukumar, Malam Yunusa Abdullahi ne, ya bayyana hakancikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Kaduna. ’Yan sanda sun ceto mutum...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, tare da Sojoji sun samu nasarar ceto mutum 23 da ’yan bindiga suka sace a wani artabu da aka yi a ƙauyen Doka, da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Mansur Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa babban jami’in ’Yan Sandan yankin Kajuru ne...
Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta cafke wasu matasa a yankin Sheka bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, yana mai cewa rikicin ya fara ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Yusuf Aminu, ɗan unguwar Sheka Babban Layi, wanda ake zargi da aikata...
Arsenal ta doke Manchester City a wani yanayi mai ban mamaki a filin wasa na Emirates dake birnin Landan, ƙwallaye da Odegaard, da Partey, da Skelly, da Harvertz da Nwaneri suka jefa ya sanya Man City cikin garari. Tun minti na 2 da fara wasan kyaftin ɗin tawagar Arsenal Martin Ordegaard ya jefa ƙwallo a...
Kawo yanzu Kano Pillars, wadda take mataki na 10 da maki 29 za ta fafata da Remo Stars a wasan mako na 23.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Manchester City ta ci 5 da 1 a Gasar Firimiyar Ingila. Ƙungiyoyin biyu sun ɓarje gumi da yammacin ranar Lahadi a filin wasa na Emirates, a mako na 24 na gasar. Fasinjoji 30 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Ondo Asibitin Malam Aminu...
Masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta kafa wani sabon tarihi a hutun bikin bazarar 2025, inda daga ranar 29 ga watan Janairu zuwa ranar 1 ga Fabrairu, kudaden da aka samu daga kallon fina-finai ya kai biliyan 5.75 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 802, wanda ya zarce mafi yawan kudin da aka samu a baya...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba da ci gaban da Iran ta samu a fagage daban-daban, yana mai cewa kasar ta samu bunkasa a dukkan bangarori cikin shekaru 40 da suka gabata. Iran ta yau ba Iran ce ta shekaru 40 da suka gabata ba – mun ci...
Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qasem ya ce gwamnatin Lebanon ce ke da alhakin tabbatar da cewa Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar ta Lebanon. “Gwamnatin Lebanon, bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ita ce ke da alhakin bibiyar lamarin da kuma matsa lamba kan kasashe masu sa...
Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan mayar da mazauna Gaza zuwa kasashen Masar da Jordan dake makwabtaka da ita. A cikin wata sanarwar da ya fitar, shugaban kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ya yi tir da irin wadannan shawarwari a matsayin “abin dariya kuma maras amfani,” yana mai cewa,...
Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow. Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin...
La’anannen dan siyasar Sweden din nan mai kyamar addinin Islama, Rasmus Paludan, ya sake tozarta kur’ani mai tsarki a birnin Copenhagen na kasar Denmark. Paludan mai shekaru 43 shugaban jam’iyyar adawa ta kasar Denmark Stram Kurs, ya sake haifar da cece-kuce ta hanyar aikata wannan aika aika a wajen ofishin jakadancin Turkiyya da ke Denmark....
Aƙalla fasinjoji 30 ne suka ƙone ƙurmus a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan titin Ore-Lagos a Jihar Ondo, bayan da wasu motoci biyu suka yi karo da juna sannan suka kama wuta. Ganau, sun ce motocin suna tafiya zuwa Gabashin Najeriya ne, kuma suna gudun wuce ƙima kuma ga cunkoson ababen...
Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ƙara farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa, tana mai cewa hakan ya zama dole domin samar da tsarin farashin da ya dace da kuɗin aiki, wanda zai jawo zuba hannun jari daga fannoni masu zaman kansu a ɓangaren makamashi. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu...
Kasar Sin Na Ci Gaba Da Inganta Kiyaye Dausayi
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta nuna adawa da rashin amincewa da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasar Sin, kuma za ta dauki matakan da suka dace...
A jiya Asabar kasar Amurka ta sanar da kakaba karin harajin kwastam na kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa Amurka. Dangane da batun, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta bayyana rashin jin dadi da kin amincewa daga bangaren Sin. Cikin sanarwar da ma’aikatar ta gabatar, ta ce matakin Amurka ya keta ka’idojin...
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba...
Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Nijeriya da ke buga wasa a ƙungiyar Galatasaray Victor Osimhen, ya shigar da ƙarar wani ɗan jaridar Turkiya Tolga Bozduman bisa zargin ɓata masa suna. A cikin wani saƙo da wani makusancin Osimhen ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a fara sauraron ƙarar da...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karrama wasu mutum 35 ’yan asalin Jihar Kano waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa. Daga cikin waɗanda gwamnan ya karrama akwai janar-janar ɗin soji 19, Farfesoshi 6 da wasu fitattun Kanawa 10. Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa Mahaifin ma’aikacin Aminiya...
Kasashen 3 na yankin sahel sun kafa ta su kungiyar mai suna “Kawancen Sahel” (AES). Yadda ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ecowas ka iya raunata kungiyar Ficewar kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso daga kungiyar Ecowas a ranar Laraban nan bayan kwashen fiye da shekara guda ana zaman tankiya tsakanin kungiyar...
Rahotanni da suke fitowa daga kasar Syria sun ce, ana ci gaba da yi wa daidaikun mutane kisan gilla a sassan kasar mabanbanta. A kusa da garin Hamah, an kashe mutane 7 a bayana nan, bayan da wasu masu dauke da makamai su ka shiga cikin garin Tal-Zahab. Masu dauke da bindigar sun kutsa gidan...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar da sanarwa da a ciki ta bukaci Isra’ila da ta janye sojojinta daga kudancin Lebanon tana mai cewa wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci. Ministan harkokin wajen kasar ta Masar Badar Abdulatif ya ce, wajibi ne ga Isra’’ila da ta janye sojojin nata daga Lebanon ba tare...
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Sudan sun ce rundunar kai daukin gaggawa mai fada da sojojin kasar Sudan ta kai wa garin “Tandalti” hari da jirgen sama marasa matuki jim kadan bayan ziyarar shugaba majalisar shugabancin kasar Janar Abdulfattah al-Sisi. Majiyar sojan kasar Sudan ta ce, sun yi amfani da na’urorin kakkabo jiragen sama,...
Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909. Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14. Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001). Dan...
Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin...
A wani mataki na tsaro da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu da ke Kano ya fitar saboda magance barazanar tsaro da yake fuskanta, ya fara aiwatar da dokar hana motoci masu baƙin gilas wato tinted glass shiga harabar asibitin. Mahukuntan asibitin sun bayyana cewa, motocin da ke ɗauke da marasa lafiya ko ma’aikata za su...
Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya sha alwashin ci gaba da shirin kasar na kera makaman nukiliya har sai baba ta gani. Kafar yada labaran kasar ta rawaito Mista Kim ya kai ziyara cibiyar da ake kera makaman, inda ya ce shekarar da muke ciki na da matukar muhimmanci a tsarin da...
Allah Ya yi wa mahaifin ma’aikacin Aminiya, Abubakar Abdurrahman Adoro, rasuwa. Mahaifin nasa, Farfesa Abdurrahman Lawal Adoro, ya rasu ne a gidansa da ke garin Batagarawa a Jihar Katsina, ranar Litinin 27 ga watan Janairu, 2025, a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, ya yi fama da jinya na wani lokaci. Majalisar Matasa ta...
Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin...
Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da...
Jami’ar Michigan ta Amurka ta dakatar da karatun wasu daliban jami’ar saboda rawar da suka taka, a zanga-zangar goyon bayan Gaza a yakin watanni 15 da suka yi da HKI. Kamfanin dillancin labaranSahab ya nakalto kamfanin dillancin labaran Mehr yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, hukumar Jami’ar Michigan ta kori wasu daliban daga...
Ƙungiyoyin alarammomi da matasa daga jihohin Arewa sun nuna goyon bayansu a kan taron karatun Kur’ani na ƙasa da ake shirya gudanarwa a Abuja a ranar 22 ga watan Fabrairu. Shugaban ƙungiyoyin, Kwamred Murtala Mohammed Garba, wanda aka fi sani da Gamji, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya...
A yau Lahadi ce 2 ga watan Fabraiyu na wannan shekara, wanda yayi dai-dai da 3 ga watan Shaban ranar haihuwar tauraro na 3 daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon All..(s), har’ila yau shi ne ranar “tsaro” nan JMI. Imam Hussain (a) shine limami daga cikin liamai masu tsarki wadanda...
Shuwagabannin kungiyar kasashen raya tattalin arziki da kuma tsaron kasashen Afrika da kudu ta ce zasu ci gaba da wanzar da sojojinsu a kasar Congo duk tare da sauye-sauyen da kungiyar yan tawaye na M23 suka yi a yankin arewacin KIVU. Shafin yanar gizo na Labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa shuwagabannin kungiyar sun bada...
A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa. Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya...
Iyalai da dama da ’yan fashin daji suka raba da matsugunansu a wasu jihohin Arewa-maso-Yamma da Arewa-maso-Gabas sannan daga bisani kuma aka kore su daga birnin Abuja, inda suka samu mafaka a halin yanzu, suna wani hali a wasu sassan Jihar Nasarawa da ke makwaftaka da Babban Birnin Tarayya Abuja. Binciken da wakilinmu ya yi...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za a ci gaba da bada tallafi ga al’umma a dukkan mazabu 30 na ‘yan majalisar dokokin Jihar. Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake kaddamar da bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Miga wanda Shugaban majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya...