2025-04-21@22:23:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 110
«Bana mai ɗan wake»:
An kama wata malamar makarantar sakandare ta California a Amurka da ake zargi da lalata da wani ɗalibi mai shekaru 17. Wannan da ba shi ne karon farko ba da aka tuhumi wani da irin wannan hali ba a makaranatar. Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi...
A lokacin da Abba Musa angon da za a daura wa aure, da wasu mutum huɗu suka kama hanya zuwa kauyen Murno daga garin Boto a Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, babu wanda ya yi tunanin cewa shi angon da ’yar uwar amaryarsa, Raihanatu Sulaiman za su rasa ransu mintoci kadan kafin a...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba. Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar, Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa kotun kawai ta dakatar da aiwatar da hukuncinta har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kan shari’ar. MC Tagwaye ya fice...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da tuni Najeriya ta faɗa cikin mummunan yanayin matsin tattalin arziƙi ban da gwamnatinsa ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci. Da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana wa wata tawagar tsofaffin ’yan majalisa cewa dole ne gwamnatinsa ta ɗauki matakai...
Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da Matatar Dangote domin sayar mata da ɗanyen man fetur a farashin naira za ta ƙare a wannan wata na Maris. Sai dai kamfanin ce yana tattaunawa da Matatar Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira. An hana tashe...
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar damu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan alherai goma ga ma’aurata cikin Ramadan. 4. Salon buɗa baki Ma’aurata za su yi amfani da lokacin buɗa baki don ƙara kusanci, farfaɗo da shau’uka cikin zuciya...
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta sake ɗage babban taronta na ƙasa (NEC), zuwa ranar 15 ga watan Mayu, 2025. A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, wanda babban sakatarenta, Sunday Ude-Okoye, ya bayyana hakan. Iyalan Abacha sun gargaɗi Babangida kan ɓata sunan mahaifinsu An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba Tun asali,...
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas da ta Yola, da Jihar Adamawa, sun yanke wa wasu dillalan miyagun ƙwayoyi huɗu da aka kama da safarar ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.6 hukuncin ɗaurin shekaru 95 s gidan yari. Ɗaya daga cikinsu, Ogbuji Christian Ifeanyi, jami’an hukumar NDLEA sun kama shi a filin...
Ya bayyana cewa samun damar karɓar baƙuncin wannan babban taro wata gagarumar nasara ce ga Nijeriya, kasancewar ita ce ƙasar Afirka ta biyu da za ta karɓi baƙuncin taron. Ya ce: “Wannan babban cigaba ne ga Nijeriya kuma yana da alaƙa da manufofin gwamnatin mu na inganta martabar ƙasar a idon duniya. A daidai...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da mutane bakwai da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ƙauyen Anchuna da ke masarautar Ikulu a ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna. An samu rahoton cewa harin wanda ya auku a daren ranar Larabar, ya jefa al’ummar yankin...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya buɗa-baki a Fadar Gwamnati da ke Abuja, inda ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar nan na kan hanya gyaruwa nan ba da jimawa ba. A yayin jawabinta, ta jaddada muhimmancin tausayi da jin-ƙai a tsakanin rayuwar ɗan adam. Wani mutum ya yanke jiki ana salla a...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yana ƙara danƙon zumunci da ƙaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu ƙarin kusanci da shaƙuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu...
Daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Joseph Sarwuan Tarka da ke Jihar Binuwai sun kubuta. Daliban sun lubauta ne bayan shafe kwanaki takwas a hannun ’yan ta’addan.
Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona. Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar...
Liverpool na farautar ɗan wasan Bournemouth mai shekara 21 daga Hungary Milos Kerkez kan fam miliyan 40. (Telegraph – subscription required) West Ham na kokarin ganin ta saye ɗan wasan tsakiya a Ingila, Angel Gomes mai shekara 24 daga Lille a sabuwar kaka. (Guardian) Manchester United na tunanin ɗauko mai tsaron raga a...
Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda. Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da yi wa dokar da ta kafa Hukumar Tace Fina-finai ta jihar gyare-gyare. Ɗaya daga cikin sabbi gyaran da aka yi mata shi ne na wajabta wa masu wuraren bukukuwa da taruka yin rajista da hukumar. Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da ƙalubale – ba don sun shirya mishi ba kuma ba don sun gaza shiryawa ba. Wani rukunin waɗannan mutane shi ne na...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area...

A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya — ’Yan sanda
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa...
Bidiyon batsa ya ja wa wasu ’yan Tiktok biyu hukuncin ɗaurin shekara guda kowannensu a gidan yari bayan an gurfanar da su gaban kotu a Jihar Kano. Kotun Majiatare da ke Norman’s Land a Ƙaramar Hukumar Fagge ta yanke wasu ’yan Tiktok din hukunci ne bayan samun su da laifin saɓa wa dokokin Musulunci da...
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki domin tallafa wa mabuƙata a wannan wata mai albarka na Ramadana. Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya ƙaddamar da rabon abincin a cibiyar Dandali da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a jihar. HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja NLC ta yi fatali...
’Yan sanda sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki. Bayanai sun ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi. Burina in yi...
Wata kotun majistare da ke zamanta a Ago Iwoye, Jihar Ogun, ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 21, Adebanjo Segun, hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kaza. Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar tsaro ta Civil Defence , Dyke Ogbonnaya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya...
An shiga ruɗani bayan Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya koma majalisar tare da rakiyar ’yan sanda. An sauke Obasa daga muƙaminsa a ranar 13 ga watan Janairu kan zargin yin amfani da ofis ɗinsa ba daidai ba. An yi wa mutane damfarar Naira biliyan 52 ta banki —NIBSS Boko Haram ta...
Tauraron tawagar Super Eagles Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya faɗo daga wani gini ya mutu a kasar Uganda. A jiya Litinin aka ba da rahoton mutuwar Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce ɗan wasan haifaffen Sakkwato ya mutu ne bayan...
Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa. Ana zargin wanda a...
Wata kotu a lardin Aceh da ke ƙasar Indonesia ta yanke wa wasu ɗalibai maza biyu hukuncin bulala a bainar jama’a. A ranar Litinin ce kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin bayan samun su da laifin luwaɗi da juna. Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu An yi zanga-zangar kisan ɗalibi...
A wannan Litinin ɗin ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma FUDMA suka shiga rana ta biyu ta zanga-zangar kisan wani ɗalibi da ake zargin jami’an bijilanti na JTF sun yi a ranar Lahadi. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bijilantin sun buɗe wa wasu ɗalibai da ke tafe kan babur wuta ba tare da sun...
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa babu wani ɗan Arewa mai mai hankali da zai goyi bayan APC a zaɓen 2027. PDP ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan zargin cewa Sanata Lawal Adamu, Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, baya aikin komai sai ɗumama kujera. Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas...
Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa. Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka...
Gwamnatin Amurka ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan yadda gwamnatocin da suka gabata suka riƙa sarrafa kuɗaɗen da aka fitar domin bai wa Nijeriya da wasu ƙasashen tallafi. Hakan dai ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurkan, Donald Trump ya ɗauka a watan Janairu na dakatar da duk wani tallafi da Amurkan ke bayarwa...
Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya sake jaddada cewa ƙasashen waje ne ke tallafa wa ’yan ta’addan Boko Haram da kuɗi da makamai. A wata hira da ya yi da Al Jazeera, Janar Musa ya nuna damuwa kan yadda ƙungiyar ke ci gaba da aikata ta’addanci sama da shekaru 16, duk da...
Wani ɗan Nijeriya ɗan asalin Jihar Yobe, Saidu Abdulrahman, ya lashe kambun lambar yabo ta Kundin Bajinta na Duniya a matsayin wanda ɗaukar hotuna kai tsaye cikin sa’a ɗaya. Bayanai sun ce a cikin mintuna 60 Sa’idu Abdulrahman mai shekara 28, ya ɗauki hotuna 897 masu ɗaukar hankali a watan Satumba na bara, lamarin da...
Hukumomin Jami’ar Nnamdi Azikiwe (Unizik) da ke, Awka a Jihar Anambra ta kori ɗalibar nan mai suna Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, saboda cin kwalar wani malamin jami’ar Dakta Chukwudi Okoye. A cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga Goddy-Mbakwe ta far wa malamin jami’ar, Dakta Chukwudi bayan ya ratsa ta cikin bidiyon...
Rahotanni sun nuna cewa an ɗage taron mahaddata al-Qur’ani da ake yi wa laƙabi da Qur’anic Convention a Turance da ya rage ƙasa da mako biyu wanda za a gudanar a Abuja kamar yadda BBC Hausa ta bayyana. An dai ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 a matsayin ranar da za a gudanar...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko...
Jami’ai a yankin kudu masu yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 sun mutu sakamakon fashewar wata motar da ke ɗauke da masu haƙar ma’adinai a yankin Harnai da ke lardin Balochistan. Jami’an yankin sun ce suna ci gaba da bincike kan abin da ya haifar da fashewar, to amma ana kyautata zaton abubuwan fashewa...
Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran...
Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda...
An tafi da shi tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ɗan uwansa da matarsa da ɗansa a yayin harin. An tattaro cewa, jigon na APC ya kai ziyara gidan ɗan uwansa ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin. Sai dai, an tsinci gawar matar dan uwansa mai suna, Madam...
Ya ce: “A baya, muna da wasu hukumomi da ke ƙayyade farashin kayan abinci, amma domin kasuwanci na ’yanci da bunƙasa harkokin noma, gwamnati ba ta ga dacewar ci gaba da hakan ba. “Yanzu abin da gwamnati ke yi shi ne ta tabbatar da cewa ana samar da isassun kayan abinci, domin idan abu...
An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan...
Kotu ta tsare wani ɗan fashi da ya yi wa ɗalibai mata uku na Jami’ar Jihar Kwara fyaɗe. Matashin da dubunsa ta cika yi wa ɗaliban fyade ne a yayin wani fashi a ɗakunan kwanan ɗalibai mata a cikin dare. Ya yi musu wannan aika-aika tare da yunƙurin kisa ne a daƙinsu kwanan ɗalibai mata...
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ’yan mata shida masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17 a yankin unguwar Pandogari da ke Ƙaramar hukumar Rafi ta Jihar Neja. Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, da tsakar daren Laraba ne ’yan bindigar suka kaiwa unguwarsu hari inda suka kashe wani ɗan banga mai suna...
Ma’aikata a Jihar Alaska da ke Amurka sun bazama neman wani ƙaramin jirgin sama na kasuwanci a ranar Juma’a da ya ɓace ɗauke da mutum 10. Kamar yadda hukumomin yankin suka ce, a wani sabon afkuwar da ya afku ta jirgin Amurka. Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai Lakurawa...
Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh...
An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita. Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom. A safiyar Alhamis ne kakakin...