2025-02-27@18:51:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 131
«Layya»:

Wasu Hukumomi A MDD Sun Bada Sanarwan Cewa HKI Ta Fadada Yaki Kan Falasdinawa Daga Gaza Zuwa Dukkan Kasar Falasdinu
Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta bayyana cewa sama da mahajjata 3,000 da suka yi aikin Hajjin 2023 sun karɓi ragowar kuɗinsu da ya yi saura. Mai magana da yawun hukumar, Malam Yunusa Abdullahi ne, ya bayyana hakancikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Kaduna. ’Yan sanda sun ceto mutum...
Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ƙara farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa, tana mai cewa hakan ya zama dole domin samar da tsarin farashin da ya dace da kuɗin aiki, wanda zai jawo zuba hannun jari daga fannoni masu zaman kansu a ɓangaren makamashi. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta nuna adawa da rashin amincewa da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasar Sin, kuma za ta dauki matakan da suka dace...
A jiya Asabar kasar Amurka ta sanar da kakaba karin harajin kwastam na kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa Amurka. Dangane da batun, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta bayyana rashin jin dadi da kin amincewa daga bangaren Sin. Cikin sanarwar da ma’aikatar ta gabatar, ta ce matakin Amurka ya keta ka’idojin...
Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909. Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14. Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001). Dan...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta biya fiye da Mahajjata dubu uku da suka kammala aikin Hajjin shekarar 2023 kudaden da Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta mayar masu. Mai Magana da Manema Labarai na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, shine ya bayyana hakan sannan ya kara da cewa an turawa kowane...

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Bayyana Matakan Da Amurka Zata Bi Don Kyautata Dangantaka Da Iran
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana bayyana matakan da sabuwar gwamnatin Amurka zata dauka idan har tana son sake samun yardar samun yardar kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-jazeera ta kasar Qatar a birnin...
Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na...
A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana alhininta na shahadar babban hafsan mayakan rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas Muhammad Dhaif tare da wasu abokan aikinsa, tare da bayyana rawar da suka taka a fagen gwagwarmaya. Kungiyar ta Hizbullaha ta mika sakon ta’aziyya da kuma barka akan shhadar Muhammad Dhaif ga kungiyar...
An bayyana dangantakar cinikayya tsakanin kasar Sin da Afrika a matsayin wadda ta taimaka wajen gaggauta ci gaba da samar da irin zamanantarwar da nahiyar ke bukata domin ta kasance cikin takara a duniya. Muya Guo, shugabar sashen Sin a bankin Stanbic na Kenya ne ta bayyana haka yayin wata hira a Nairobin Kenya, inda...
Masu haƙar zinare aƙalla mutum 10 sun mutu wasu da dama sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a kansu a wani filin haƙar ma’adinai yankin Koulikokro na ƙasar Mali. Hukumomin yankin sun bayyana cewa mata ne yawancin masu haƙar zinaren da abin ya rutsa da su mata ne, kuma an kasa ciro gawarwakinau, “saboda tsananin sarƙaƙiyar...
A nata jawabin, babbar mai shari’a ta Jihar Gombe, Mai Shari’a Halima S. Mohammed, ta bayyana cewa an shigar da kararraki guda 616 wadanda suka shafi manya da kananan laifuka da kuma cin zarafi a babbar kotun jihar, daga cikinsu 555 an kammala shari’arsu, inda wadanda suka rage ba su kai 70 ba. Ta bayyana...
A ranar Litinin, hukumar Tsaro ta DSS da Majalisar Ulama sun kira Sheikh Bin Uthman da AY Maikifi don tattaunawa. Majalisar Ulama ta shawarci Sheikh Bin Uthman da ya koma masallacinsa na asali, amma har yanzu ba a san ko zai amince da hakan ba.
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kori kwamishinoni guda biyar daga muƙamansu. Wannan ma cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Architect Samuel Jatau, ya fitar da yammacin ranar Alhamis. Ɓarayin dabobbi sun shiga hannu, an ƙwato awaki 85 a Gombe Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai Sanarwar ta bayyana cewa...

An Tsamo Gawakin Mutane 30 A Karon Da Wani Jirgin Fasinja Ya Yi Da Wani Jirgi Mai Saukar Ungulu A Birnin Washinton
Kamfanin dillancin labaran BBC ya bayyana cewa mutane 64 ne suke cikin jirgin fasinja na kamfanin American Airline, sannan mutane 3 ne a cikin jirgin yaki mai saukar ungulu samfurin Black Hawk suka yi karo a birnin washinton a safiyar yau Alhamis. Labarin ya kara da cewa, a halin yanzu sun tashi daga kubutar da...
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar. Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a...
Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun cafke Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, bayan kai sumame a gidansa da ke Abuja. Aminiya ta tabbatar da cewa jami’an EFCC ɗauke da makamai sun isa gidansa da misalin ƙarfe 4:46 na yammacin ranar Laraba, inda suka...
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce karamin yankin Gaza ya durkusar da gwamnatin Isra’ila duk da makaman da ta ke dasu da kuma cikakken goyon bayan Amurka. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa : tsayin daka da aka fara a Iran din, ya jawo farkawar wasu al’ummar musulmi kuma...
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya bayyana cewa gwamnatin jihar na hada rijistar manoma da masu rike da mukaman siyasa a cikin shirinta na inshorar lafiya domin tabbatar da ayyukan kiwon lafiya ga daukacin ‘yan kasa. Gwamnan ya bayyana haka ne a Minna, a lokacin da ya karbi bakuncin abokan hulda na...
Kungiyar masu ruwa da tsakin masana’antu a fannin mai ta Najeriya NEITI da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, na kokarin kwato kusan dala biliyan shida da kuma wani naira biliyan 66 da gwamnatin tarayya ke bin gwamnatin tarayya bashin. Sakataren zartarwa na hukumar Mista Orji Ogbonnaya Orji, wanda ya...
Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya bayyana damuwarsa game da matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka na dakatar da taimakon kasashen waje daga Amurka yayin da sabuwar gwamnatin Amurka ke aiwatar da sabbin manufofinta na ketare, kamar yadda mai magana da yawun Guterres ya bayyana. “Ya yi kira da a yi...
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya na da wadataccen arzikin da za ta ci gaba da ɗawainiyar duk wasu tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa ƙetare. A bayan nan dai ’yan Nijeriya na ci gaba da bayyana damuwa kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi a kai-a kai zuwa ƙetare la’akari da...
Ana fargabar cewa wani mutum mai shekaru 30, Rabiu Sani, ya mutu a wani kududdufi da ke unguwar Kunture a Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun rundunar hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin. ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da...
Ana zargin ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun ɓullo da sabon salon cin hanci inda suke tatsar jami’o’i da sauran manyan cibiyoyin ilimi na tarayya. Kafar yaɗa labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa ’yan majalisar suna barazana ga kowane shugaban jami’a ya ba su cin hancin Naira miliyan takwas kafin sun amince da kasafin...
Wani magidanci mai suna Rabiu Sani mai shekaru 30 ya rasa ransa bayan ya zame cikin wani tafki a lokacin da yake diban ruwa a garin Kunture da ke karamar hukumar Ungogo. Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullah, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a...
Wasu jami’an MDD sunn bayyana cewa, a cikin halin da ake ciki a kudancin kasar Lebanon ba ya yuwa mutane yankin su koma gidajensu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ba bayyana cewa a yau ne wa’adin kwanaki 60 na ficewar sojojin HKI daga kudancin kasar Lebanon kamar yadda ya zo a cikin yarjeniyar...
“Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni. “Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara...
Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Atisayen sojin mai take “‘Manzon Allah Mai Girma na 19” ya bayyana ƙarfin sojojin Iran Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” a cikin ruwan Tekun Fasha ya bayyana Alamar da ƙarfin sojojin...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan...