2025-03-30@22:19:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2695
«da lantarki»:
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan na Ramadan. Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa shugabanni jagorancin don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma. Namadi ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa. ...
Hukumar Ƴansandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 20, Usman Sagiru, bisa zargin kashe wani ɗan Bijilanti a tawagar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II bayan Sallar Eid. Iftila’in ya faru ne da ƙarfe 12:40 na rana a Lahadi, lokacin da ayarin Sarkin Kano ke watsewa daga filin Sallar Idin. A cewar kakakin Ƴansanda SP Haruna Kiyawa, ana zargi Sagiru da wasu da suka tsere da soka makami ga wani ɗan sa kai mai suna Surajo Rabiu daga unguwar Sabon Titi Jaba, wanda ya mutu sakamakon raunin. Yadda Sarki Sunusi Lamido Ya Yi Bikin Shiga Fadar Kano Tsakar Dare Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II Wani ɗan Bijilanti, Aminu Suleman daga...
A Bikin Yawan Sallah na Jafi da aka yi a fadar Sarkin Gombe, Mai Martaba Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III, ya yi kira ga manoma da makiyaya da su zauna lafiya da juna. Sarkin ya ce zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaba, kuma haɗin kai tsakanin manoma da makiyaya zai hana rikice-rikice da ke barazana ga jihar. Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina “Ina roƙon manoma da makiyaya da su zauna lafiya don guje wa rigingimu. “Kowa yana da haƙƙin tabbatar da zaman lafiya domin hakan na kawo ci gaban tattalin arziƙi da walwalar al’umma,” in ji Sarkin. Haka kuma, ya tabbatar da cewa...
Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare. Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman na biyu, ya jaddada muhimmancin hadin kai wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a lokacin da ya gabatar da sakon Sallar a fadarsa da ke Kauru. Alhaji Zakari Ya’u Usman ya kuma yi gargadi game da masu ba da labari da ke taimaka wa masu laifi tare da karfafa gwiwar mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi. Dangane da...
Rundunar ’Yan Sandan Kano, ta kama wani matashi bisa zargin kashe jami’in tsaron sa-kai a filin Idi yayin hawan sallah ƙarama. A cewar sanarwar da ’yan sanda suka fitar, matashin mai shekara 20, ya daɓa wa jami’in wuƙa yayin da yake aiki tare da tawagar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, bayan sallar Idi a ranar Lahadi. Farashin fetur ya ƙaru sakamakon hana Dangote mai a Naira Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi Haka kuma, wani jami’in sa-kai ma ya ji rauni kuma yana jinya a Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano. Rundunar ’yan sandan ta ce ta fara bincike kan lamarin, kuma ta gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku, domin amsa tambayoyi. A baya-bayan...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, Iran ba ta shiga tattaunawa da Amurka kai tsaye ba, yana mai mayar da martini kan wasikar da shugaban Amurka ya aike mata, amma kuma ya bayyana cewa hakan zai bude kofa ga tattaunawar kai tsaye. Da yake magana a wani taron majalisar ministocin a ranar Lahadi, Pezeshkian ya tabbatar da cewa an isar da martanin Iran ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump ta hanyar Oman. Ya jaddada cewa, yayin da Iran ta yi watsi da tattaunawar kai tsaye, ba ta taba rufe kofar yin shawarwarin kai tsaye ba matukar dai aka cimma wani abu da bai yi karo da manufofin Iran ba. Ya kara da cewa, “Kamar yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran...
Shugaban majalisar mulkin kasar Sudan kuma kwamandan Sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya tabbatar da cewa, farin cikin samun nasara a Sudan ba zai cika ba har sai an kawar da tungar karshe ta mayakan RSF a kasar, yana mai jaddada cewa kasar ba za ta ja da baya ba har sai an murkushe wadannan mayakan ‘yan tawaye, wadanda suka aikata munanan laifuka kan al’ummar Sudan. Al-Burhan ya yi nuni da cewa, za a ci gaba da gwabzawa har sai an samu cikakken adalci, yayin da ya tabbatar da cewa ya tsaya tsayin daka da dukkan ‘yan kasar, kuma ya yi imani da ci gaba da kokarin maido da tsaro da kwanciyar hankali a kowane sako na kasar Sudan. Al-Burhan...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Amurka na da hannu a ayyukan haramtacciyar kasar Isra’ila na yada rashin tsaro da zaman lafiya a yankin. A wata ganawa da ya yi da Hans Grundberg, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen a birnin Tehran, Araghchi ya yi Allah wadai da ci gaba da hare-haren soji da Amurka ke kaiwa sassa daban-daban na kasar Yeman, wanda ke sanadin mutuwar fararen hula da kuma lalata kayayyakin more rayuwa. Ya kara da cewa: Hare-haren da sojojin Amurka suke kai wa kasar Yamen, wanda ya zo daidai da irin yadda gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da aiwatar da kisan gilla a zirin Gaza da kuma hare-haren da take kaiwa kasashen Lebanon...
Rundunar sojin Amurka ta kaddamar da wani hari ta sama a ranar Asabar din da ta gabata kan mayakan IS a yankin Puntland na Somalia, inda suka kashe wasu mambobin kungiyar da dama, a cewar rundunar sojin Amurka . A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Amurka da ke nahiyar Turai ta tabbatar da cewa, harin da aka kai tare da hadin gwiwar gwamnatin Somaliya, ya kashe da dama na mayakan ISIS a Somaliya. Yayin da kungiyar IS ke hankoro hada karfinta a Somalia wanda bai bunkasa ba idan aka kwatanta da kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaeda, kungiyar ta mayar da hankalinta ne wajen kara fadada karfinta a yankin Puntland mai cin gashin kansa. “Harin ya auke...
A wani hatsarin mota da ya faru a hanyar Malumfashi-Kafur a Jihar Katsina, mutane tara sun rasu yayin da wasu 11 suka jikkata. Hatsarin dai ya shafi wata babbar motar bas da ke ɗauke da fasinjoji 20. Aliyu Ma’aji, Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya bayyana cewa binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa gaggawar tuki ne ya haifar da hatsarin, inda direban ya rasa ikon sarrafa motar. An Gabatar Da Motar Asibiti Ta Farko Mai ISO Na Matsayin Kasa Da Kasa A Hukumance Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Kano – FRSC Haɗarin ya yi sanadin mutuwar mutane...
Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira. Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi Wannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Rahotanni sun nuna cewa farashin...
Akwai karin tawagogin ceto da dama na kasar Sin da suka shiga ayyukan ba da agaji tare da takwarorinsu na Myanmar. Girgizar kasar mai karfin maki 7.7 ta afku a kasar ce da ke kudu maso gabashin Asiya, a ranar Jumma’ar da ta gabata. A jiya Asabar da dare, tawagar yada labarai ta majalisar gudanarwar kasar ta bayyana cewa, sama da mutum 1,700 ne suka mutu, kana sama da 3,400 suka jikkata, yayin da kuma kimanin 300 suka bace, a kakkarfar girgizar kasar da ta faru a kasar ta Myanmar. A yinin yau Lahadi kuma, wani jirgin saman kamfanin China Eastern Airlines ya tashi daga Kunming, babban birnin lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin, dauke da kayayyakin agaji...
Mai martaba Sarkin zazzau,kuma shugaban majalisar sarakunan jihar kaduna, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya bukaci Dagatan da ke masarautar zazzau da su rinka sanya ido sosai akan zirga-zirgar bakin fuskokin da ba su gane ba a cikin su. Ya yi kiran ne a sakon sa na sallah bayan kammala azumin watan Ramadan a fadar sa dake Zaria. Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana cewa harkar tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a hakki ne na kowa amma ba gwamnati ita kadai ba,a don haka akwai bukatar ganin an hada karfi da karfe domin samun nasara a game da tsaron. Mai martaba Sarkin ya kuma bukaci Dagatan da su rinka kai rahoton zuwan duk wani bako ko bakuwa da kuma dalilin zuwan. Ya ce...
Jihar Lagos ta samu rahoton kamuwar matasa 10 da cutar Mashaƙo tsakanin ranar 1 ga Janairu zuwa 27 ga Maris 2025, yayin da hukumomin lafiya ke ƙara ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar. Kwamishinan lafiya na Jihar, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana cewa ana iya samun rahoton cutar har sama da 15 a rana. Daga cikin samfurorin da aka yi wa gwaji guda 76 an samu 10 da aka tabbatar da sun kamu, yayin da sauran samfurorin 63 sakamakonsu ya ke lafiya. Kwamishinan ya ƙara da cewa cutar ta afkawa ƙananan hukumomi da dama, inda Eti-Osa ta fi yawan wanda abin ya shafa. Kisan Mummuken Cutar Mashako A Nijeriya Da Sassan Duniya Fasaha Da Balagar Harshen Manzon Allah (SAW) II Abayomi ya...
A bana aka cika shekaru 60 da kafuwar jihar Xizang mai cin gashin kanta ta kasar Sin. A ranar 28 ga watan Maris, wato ranar tunawa da ’yantar da miliyoyin bayi manoma a Xizang, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani mai taken “Ci gaban hakkin bil’adama a Xizang a sabon zamani”, wadda ta yi amfani da cikakkun bayanai na gaskiya don nuna yadda aka samu manyan sauye-sauye a jihar a cikin shekaru gommai da suka wuce. Takardar ta kuma shaida mana ma’anar “Jin dadin zama ga jama’a babban hakki ne na dan Adam”. “Ci gaba da aka samu a Xizang ya wuce yadda na yi zato, kuma mutane a nan suna rayuwa irin ta zamani sosai.” Wannan...
Iyayen Abdulsalam Rabi’u Faskari, wanda aka sace tare da mahaifinsa a Jihar Katsina, sun bayyana cewa sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ba tare da biyan kuɗin fansa ba. Abdulsalam, wanda ya lashe gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa da aka gudanar a Jihar Kebbi, an sace shi tare da mahaifinsa da wasu makonni biyu da suka gabata, bayan Gwamnan Katsina ya karrama shi. Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi. Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi Mahaifinsa, Malam Rabiu Zakariya Faskari, ya shaida cewa suna tsare a hannun ’yan bindiga a Katsina har sai da wani babban ɗan bindiga mai suna Yellow daga Zamfara ya zo ya karɓe su da ƙarfi. “Ya yi...
A shekarar 2009 ne Cristiano Ronaldo ya saka hannu akan kwantiragin da ya sa ya zama sabon dan wasan Real Madrid, tun daga wancan lokacin Ronaldo ya jefa kwallaye 311 a wasanni 292 da ya bugawa Madrid, hakazalika ya lashe kofuna 15 a shekaru 9 da ya kwashe a Santiago, to amma yanzu Fionrentina Perez ya dauko wani Bafaranshe daga PSG, wanda yanzu haka ya dauko hanyar doke tarihin Ronaldo a Real Madrid. Kylian Mbappe ne ya jefa kwallaye 2 a wasan da Real Madrid ta doke Leganes, wanda hakan ya sa ta samu maki daya da abokiyar hamayyarta Barcelona dake saman teburin La Liga, kwallaye biyun da Mbappe ya ci ya sa kwallayen da Mbappe ya ci a kakar...
Ya ce: “Ya ‘yan uwa Musulmi na Jihar Zamfara da ma sauran wurare, ina miƙa saƙon barka da Sallah tare da taya mu murnar kammala azumin shekarar Hijira ta 1446, wannan wata mai alfarma ta kasance lokaci na sadaukarwa ga Allah (SWT). “Yayin da muke gudanar da bukukuwan Ƙaramar Sallah, ina kira ga kowannenmu da ya ci gaba da ayyukan ƙwarai, da haƙuri, da karamcin da aka yi a watan Ramadan. “Ƙalubalan da ke gabanmu suna da yawa kuma suna buƙatar haɗin kai don ganin an magance su, don haka mu ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mu yi aiki tare a matsayin al’umma ɗaya, mu goyi bayan ajandar gwamnati na ceto da sake gina jiharmu. Gwamna Lawal...
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji cin mutuncin shugabanni yayin da suke bayyana matsalolinsu, inda ya jaddada cewa girmamawa da ladabi suna fi tasiri wajen samun mafita. “Idan ka zagi shugabanka, ta yaya kake so ya taimaka maka?” in ji shi. Masar ta miƙa wa Hamas da Isra’ila tayin tsagaita wuta Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah “Amma idan ka yi magana da ladabi, zai saurare ka kuma ya ɗauki mataki.” Da yake jawabi bayan sallar Idi a Sakkwato, Sarkin Musulmi, ya buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a da kuma zaman lafiya da ci gaban ƙasa. “Ku yi wa Shugaban...
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya musanta cewa akwai tsamin dangantaka tsakaninsa da Gwamnatin Sakkwato. Ana iya tuna cewa bayan karɓar akalar jagoranci ne Gwamna Ahmed Aliyu ya yi wa Dokar Masarautar Sakkwato gyaran fuska tare da sauke wasu sarakunan gargajiya, lamarin da aka riƙa raɗe-raɗin wani yunƙuri ne tsige shi kansa Sarkin Musulmin. Hotunan Sallar Idi daga sassan duniya Masar ta miƙa wa Hamas da Isra’ila tayin tsagaita wuta Sai dai da yake jawabi a saƙonsa na barka da sallah, Sarkin Musulmi ya ce “ba wata rashin jituwa ko faɗa a tsakaninmu. “Muna aiki tare a koyaushe. Aikinmu mu taimaka wa gwamnatin [Sakkwato] kan shirye-shiryen da ta ɗauko domin ciyar da jama’a gaba.” Ya yi kira ga al’ummar musulmi...
Bugu da kari, tawagar za ta gana da shugabannin al’ummar Hausawa na jihar domin tattauna lamarin tare da bayar da shawarwarin da suka dace. Sanarwar ta bukaci ‘yan jihar da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa duk wani abu da zai iya haifar da tarzoma, tare da tabbatar wa jama’a cewa, ana daukar matakan da suka dace na diflomasiyya da na shari’a don magance lamarin yadda ya kamata. Gwamnatin jihar Kano ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa tare da yin addu’ar Allah ya jikansu da rahama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Miliyoyin Musulmi ne a faɗin duniya ke bikin Ƙaramar Sallah bayan kammala azumin Ramadana. Ku ci gaba da kasancewa da shafin Aminiya domin samun hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a wasu sassan duniya da kuma nan gida Nijeriya. Musulmi a Filin Idi na Kubwa da ke birnin Abuja Wasu da suka fito sallar idi bayan wani coci da ke daura da Filin Idin Kubwa da ke Abuja Masallata a Filin Idi da ke garin Kafanchan Filin Idin garin Kafanchan
Sarkin Kano mai daraja ta daya wanda ya bayyana zaman lafiya a matsayin kashin bayan ci gaban kowace al’umma, don haka, ya amince da janye duk wasu shirye-shiryen bikin hawan Sallah mai ban sha’awa, wanda ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da al’adu (UNESCO) ta bayyana a matsayin gadon bil’adama mara misaltuwa. LEADERSHIP ta rawaito cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Adamu Bakori ne ya sanar da dakatar da bikin hawan Sallah, saboda barazanar tsaro da jami’an leken asiri suka rahoto a jihar. Dangane da haka, Sarki Sanusi ya yi kira ga al’umma da su kasance masu zaman lafiya da bin doka da oda tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda...
Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sari ya sanar da cewa sau uku su ka yi taho mu gama da sojojin da suke cikin jirgin dakon jirayen yakin Amurka “ Trauman” a cikin sa’oi 24. A wata sanarwa da janar Yahya Sari ya yi a jiya Asabar ya bayyana cewa; Sun kai wa jirgin dakon jiragen yakin na Amurka da kuma sauran jiragen da suke ba shi kariya a cikin tekun “Red Sea”. Kakakin sojan na kasar Yemen ya kuma ce; Sun kai wa jiragen na Amuka hare-hare ne da jiragen sama marasa matuki da kuma makamai masu linzami mabanbanta. An shiga makwanni na uku kenan da sojojin na Yemen suke mayar da martani akan hare-haren da sojojin Amurka da...
A jiya Asabar dubun dubatar ‘yan hamayyar siyasa su ka yi gangami a birnin Stanbul bayan da jam’iyyar “National Party” ta gayyace su, domin ci gaba da yin tir da kamun da aka yi wa Akram Imam Uglu wanda shi ne magajin garin na Stanbul. Shugagan jam’iyyar “Turkish National Party’ ta adawa, Uzgur Ozil ya bayyana cewa adadin wadanda su ka halarci gangamin sun kai miliyan 2.2. Daga cikin mahalarta gangamin da akwai mata da mahaifan Akram Ima wadanda su ka rika bayar da taken cewa za a ci gaba da yin gwgawarmaya ako’ina.” Tun da asubahin jiya Asabar ne dai mutane su ka fara yin tururuwa a cikin birnin na birnin Sitanbul suna dauke da tutocin turkiya da kuma...
Shugaban gwamnatin soja na kasar Guinea Janar Mamadi Doumbouya ne ya yi wa tsohon shugaban sojan kasar Camara afuwa bayan da aka yanke masa zaman gidan kurkuku bisa laifin kisan kiyashin da ya faru a 2009 a birnin Conakry. Kafafen watsa labarun kasar ta Guinea ne su ka sanar da afuwar da shugaba Mamadi ya yi wa Camara bisa dalilai na rashin lafiya. Bugu da kari kakakin fadar shugaban kasa Janar Amara Camara wanda ya yi sanarwar ya ce, an yi hakan ne bisa shawarar da ma’aikatar shari’a ta gabatar. Camara dai ya mulki kasar ta Guinea ne daga 2008-2009, an kuma yi masa shari’a ne a watan Yuli na 2024, saboda yadda a zamanin mulkin nashi aka yi amfani...
Ku kasance masu tausasawa da rahama, ku sadar da zumunta, ku sanya farin ciki azukatan al’umma kuma ku yada farin ciki, sannan ku nemi kusanci zuwa ga Ubangijinku ta hanyar ji da ɗa’a ga umarnin shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50. Babban jami’in Hamas da baya zaune a Gaza, Khalil al-Hayyam, ya ce ƙungiyar ta amince da ƙudirin da masu shiga tsakani daga Masar da kuma Qatar suka gabatar. Miji ya kama matarsa da kwarto ta na’urar drone Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah Ofishin firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ma ya ce ya karɓi tayin, amma ya gabatar da nasa tayin ”wanda ya ci karo da wanda masu shiga tsakanin suka gabatar masa, a...
Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50. Babban jami’in Hamas da baya zaune a Gaza, Khalil al-Hayyam, ya ce ƙungiyar ta amince da ƙudirin da masu shiga tsakani daga Masar da kuma Qatar suka gabatar. Miji ya kama matarsa da kwarto ta na’urar drone Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah Ofishin firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ma ya ce ya karɓi tayin, amma ya gabatar da nasa tayin ”wanda ya ci karo da wanda masu shiga tsakanin suka gabatar masa, a...
Rahotanni sun ce, wani ɗan kasar China ya kama matarsa tana cin amanarsa da wanda ya ba ta aiki a lokutan aiki ta hanyar amfani da wata na’urar ɗaukar hoto ta jirgi mara matuƙi da ake sarrafa ta daga nesa, tana leƙen asiri daga nesa. Mutumin mai hazaka da aka fi sani da Jing ya fara zargin cewa, matarsa na yin wata alaƙa ne bayan ta yi nisa sosai da shi kuma ta canza mu’amalarta sosai, ciki har da ziyartar iyayenta fiye da kowane lokaci da kuma kawo uzuri a duk lokacin da ya yi mata rakiya da kuma ƙarin lokaci a wurin aikinta. Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar...
Ranar idin Karamar Sallah rana ce da Musulmi ke farin cikin kammala azumin watan Ramadan wacce ke zuwa a ranar daya ga watan Shawwal din shekarar Musulunci. Allah Madaukakin Sarki ya shar’anta Sallar Idi a matsayin ibadar kammala Azumin Ramadan wacce take kan kowane Musulumi, baligi, mai hankali, kuma mazaunin gida — namiji ko mace. Zakatul Fidr: Yadda ake fitar da Zakkar Kono Zakkar Fidda Kai ta fi kayan sallah da abincin sallah A yayin da ake shirin shan shagalin Kamar Sallah, malamai sun bayyana muhimman abubuwan da ya kamata su aikata a ranar, kamar yadda Hadisan Annabi (SAW) suka nuna: Duk Musulumi maza da mata manya da kanana su halarci sallar Idi. Fitar da zakkar fid da kai, wato...
Sheikh Na’im Qasim babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa JMI ce ginshikin goyon bayan al-ummar Falasdinu, kuma itace gaba-gaban a duk wani yunkuri na yentar da falasdinawa da Falasdinu daga hannun HKI da masu goya mata baya. A wani jawabin da ya gabatar a jiya Asabar, shugaban kungiyar ta Hizbullah, ya bayyana cewa ware ranar jumma’a ta karshe na watan Ramadan wata hikima ce ta jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ruhullah Alkhomaini(q) wanda ya dace da hakan kan musulmi a kan wannan al-amari. Kuma tare da yardarm All…ana ci gaba da samun nasara a kan wannan manufar. Sheikh Kasim ya kara da cewa duk tare da gagarumin taimakon da HKI take samu daga kasashen yamma...
A birnin Roma masu goyon bayan al-ummar Falasdinu sun gudanar da zanga-zanga ta goyon bayan Falasdinawa, sun kuma ya allawadai da kungiyar tarayyar Turai da kuma Amurka kan yadda suka kasance manay-manyan masu taimakawa HKI a kissan kiyashin da take aikatawa a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa daubban wadanda suka fito kan tituna a tsakiyar birnin Roma na kasar Italiya suna rera taken ‘Free Free Palastine, wato yanci yanci Falasdinusun kammala ba tare da wata matsala ba. Amma a jami’ar Colombia ta kasar Amurka rikicin rikicin jami’ar tare da masu goyon bayan kasar Falasdinu ya kaiga, shugabar jami’ar ta yi murabus daga matsayinta, don bada dama ga wani sabon shugaba, wanda zia aiwatar da...
An fara wallafawa ranar 13 ga Mayu, 2022 A halin yanzu al’ummar Musulmi sun yi haramar fara shagulgulan Karamar Sallar bana bayan kammala Azumin Ramadan. A kan haka ne muka rairayo muku abubuwan da malamai suka kwadaitar da Musulmai su yi a irin wannan rana ta farin ciki da godiya ga Allah bisa ni’imominsa da kammala azumin Ramadan: Kabbarori: Daga lokacin da aka ga jinjirin watan Shawwal (Karamar Sallah) ana so mutum ya rika yin kabbarori a bayyane har zuwa lokacin da za a tayar da Sallar Idi. Daya daga cikin siffoffin yadda ake kabbarorin shi ne: Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar la ilaha illal Lah, Allahu Akbar Allahu Akbar walil Lahil hamd. Zakkar Kono: Wajibi ne ga duk wanda...
Kungiyar Hamasa a gaza ta bada sanarwan cewa ta amince da shawarar da kasashen da suke shiga tskaninta da HKI kan cewa ta amince da kafa gwamnatin hadin kan Falasdinawa, amma ba zata taba mika makamanta ga wani ba ko waye shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban Kungiyar Khalil Al-Hayya yana fadar haka a jiya Asabar a wani jawabin da ya gabatar da faifen bidiyo. Al-Hayya ya kara da cewa muna karban dukkan shawarori masu ma’ana idan an bijirosu gare mua. Amma batun makamanmu, ba zamu taba kyale mutanemmu a hannun yahudawan sahyoniyya ko kuma wasu shuwagabannin Falasdinawa wadanda zasu mika su ga yahudawa ba suna ta yawo da hanka;linsu ba. Yace fatammu ne gwamnatin...
A kasar Jordan gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa a gobe Litinin ce za’a gudanar da bukukuwan sallah karama bayan azumun watan Ramadan na kwanaki 30. Muftin kasar ta Jordan Ahmed Hasanat a lokacinda yake bada sanarwan a jiya Asabar yace, ranar Litinin 31 ga watan Maris, ita ce ranar Sallah daya ga watan shawwal shekara ta 1446 Kmariya. Kasashen Saudia, Qatar, UAE, Kuwait, Bahrain, Yemen, da kuma Palestine sun bada sanarwan cewa yau Lahadi ce sallah karama a kasashensu. Sai kuma kasashen Oman, Siriya da sun bayyana cewa gobe litinin ne salla karama. A tarayyar Najeriya ma, sultan Sa’ad Abubakar na sokoto ya bada sanarwan sallah a yau Lahadi. Majalisar koli ta al-amuran musulunci a Najeriya, karkashun shugabancin sultan...

Jakadan Kasar Rasha A Saliyu Ya Ce Kasar Rasha Tana Nazarin Yiyuwar Fara Hakar Ma’adinin bauxite A Kasar
Kamfanin hakar ma’adinai mai suna RUSAL na kasar Rasha ya aika da tawaga zuwa kasar Saloyo a yammacin Afirka don nazarin yiyuwar fara hakar ma’adinin bauxite a kasar nan gaba. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya nakalto jakadan kasar Rasah a Saliyo yana fadar haka. Labarin ya nakalto Mohammad Yongawo wani jami’in gwamnatin kasar ta Saliyo yana cewa kasarsa a shirye take ta kammala yarjeniya tsakanin kamfanin Rusal na kasar Rasha don fara aiki a yankunan da ske da ma’adinin bauxite. Ya kuma kara da cewa a halin yanzun bangarorin biyu suna cikin tattaunawa a tsakanionsu. Sannan yana fatan daga karshen gwamnatin kasar zata bawa kamfanin lisisin fara hakar ma’anin a kasar nan ba da dadewa ba. Kafin...
Shugaban Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam ya kaddamar da rabon kayan sallah da kuma kudin dinki ga al’ummar yankin. A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a garin Jahun, shugaban Karamar Hukumar yace Hakimai na gundumomin Jahun da Aujara da Gunka da Kadawawa da Limaman masalatan juma’a 79 na yankin za su amfana da kayan sallah da kuma kudin dinki. Jamilu Muhammad Danmalam ya bayyana rashin Jin dadinsa bisa yadda ake mantawa da iyayen kasa da Malaman Addini a irin wannan lokacin da ya kamata a taimake su. Ya ce yana daya daga cikin kudurorinsa na shigo da kowanne bangare na al’umma cikin tsarin shugabancinsa dan kowa ya anfana. Danmalam ya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Fiji: Ya Kamata A Koyi Fasahohin Da Kasar Sin Ta Samu A Fannin Raya Kasa
Shugaban majalisar dokokin kasar Fiji Filimone Jitoko, ya ce yadda kasar Sin ta samar da nagartattun manufofi, da samun nasarar kawar da fatara, da inganta tsarin dimokradiyya, ta yadda za ta shafi dukkan bangarorin zaman al’umma, sun kasance abin koyi ga kasarsa. Filimone Jitoko, ya bayyana hakan ne kwanan nan yayin zantawarsa da wata wakiliyar CMG a birnin Beijing, lokacin da ya ziyarci kasar Sin a karon farko, inda ya ce ziyarar ta ba shi damar samun karin ilimi, da kuma yin tunani mai zurfi. Ya kara da cewa, kasar Fiji na godiya ga kasar Sin bisa yadda take fahimtar bukatun kananan tsibiran dake yankin tekun Pasifik ta fuskar tinkarar sauyin yanayi, kuma Fiji na fatan zurfafa hadin gwiwa da...
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na Janhuriyar Congo Jean-Claude Gakosso, jiya Juma’a a birnin Beijing, inda suka yi alkawarin hada hannu wajen inganta raya dangantakar Sin da Afrika. Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce dangantakar dake tsakanin Sin da Janhuriyar Congo, ta zama misalin hadin gwiwa da goyon baya dake tsakanin Sin da Afrika. Wang Yi ya kuma yi kira ga kasashen Sin da Afrika da su hada kai da kara hadin gwiwa domin kare muradun kasashe masu tasowa, da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a duniya yayin da ake fuskantar hargitsi. A nasa bangare, Jean-Claude Gakosso, ya ce...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Nijeriya, kamar yadda kwamitin duban wata ya tabbatar. Baya ga Nijeriya, ƙasashen Saudiyya, Bangladesh, da Indiya suma sun ga watan a yau, Asabar 29 ga watan Ramadan, 1446. An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge Mijinki Sai dai wasu ƙasashe kamar Malaysia sun sanar da cewa za su yi Sallah ranar Litinin. Hakan na nufin cewa azumin watan Ramadan ya ƙare, kuma al’ummar Musulmi a Nijeriya za su gudanar da bikin ƙaramar sallah gobe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana. Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi. Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.
An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana. Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi. Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana jin daɗin yadda shugaban ƙasar Bola Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa. Buhari ya ce har yanzu Tinubu bai sauya ba daga tsari da manufofin da jam’iyyar APC ta kafa wanda har ya sanya shi kansa ’yan Nijeriya suka zaɓe shi a 2015. An ga watan Sallah a Saudiyya Dalilin da Aminu Bayero ba zai iya jagorantar hawan Sallah ba — Kurawa Buhari ya bayyana hakan a saƙonsa na taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, wanda ya cika shekaru 73 a doron ƙasa. Sanarwar da mai magana da yawun Buhari, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ta ce tsohon shugaban yana alfahari da alaƙarsa da shugaban ƙasar na yanzu. Sanarwar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jakadan kasar Sin a kasar Laberiya Yin Chengwu da ministar harkokin wajen kasar Laberiya Sara Nyanti, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da fasaha, a madadin gwamnatocin kasashensu, jiya Juma’a a Monrovia, babban birnin kasar Laberiya. Minista Nyanti ta godewa gwamnatin kasar Sin bisa gagarumin goyon bayan da take bai wa kasar Laberiya, ta kuma ce yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da fasaha da bangarorin biyu suka rattabawa hannu, za ta taimaka wa kasar Laberiya wajen cimma muradin raya kasa na ARREST. Ta ce Laberiya na son yin amfani da wannan dama wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin raya kasa, da tattalin arziki, da cinikayya, gami da zuba jari....
Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hango jinjirin watan Shawwal, wanda ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadana. Shafin Haramain ne ya ruwaito hakan, bayan daukar awanni ana neman wata. Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar karamar Sallah a kasar ta Saudiyya.
Ofishin jakadancin Amurka da ke Damascus ya fitar da wata sanarwar gaggawa, inda ya yi kira ga daukacin Amurkawa da su gaggauta ficewa daga kasar Syria, sakamakon karuwar hare-haren da ake kai wa a lokacin bukukuwan sallar Idi, wanda ke kawo karshen azumin watan Ramadan mai alfarma. A cikin wata sanarwa da ta fitar ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta daukaka tafiye-tafiye zuwa Syria zuwa mataki na 4 mafi girman inda aka gargadi, Amurkawa da kada su je kasar Siriya bisa kowane dalili. Ofishin jakadancin ya gargadi ‘yan kasar game da yiwuwar kai hari kan “ofisoshin jakadanci, kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyin jama’a na Syria” a Damascus. Halin tsaro a Syria ya tabarbare bayan da kungiyoyin ‘yan ta’adda, karkashin jagorancin...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan kungiyoyin kare fararen hula da masu aikin ceto Palasdinawa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza, tare da bayyana hakan da aikata laifukan yaki. Sojojin Isra’ila sun amince a ranar Asabar 29 ga watan Maris cewa sun yi luguden wuta kan motocin daukar marasa lafiya a zirin Gaza, inda Hamas ta yi Allah wadai da harin” da ya janyo asarar rayukan ma’aikatan ceto. Rahotanni sun ce an gano gawarwakin ma’aikatan ceto goma sha biyar, wadanda aka binne a kusa da motocinsu, wadanda suka lalace gaba daya sakamakon harin na Isra’ila. Har ila yau kungiyar ta jaddada cewa kai hare-hare da gangan...
Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 20 ne suka mutu sakamakon hatsaniyar da aka samu tsakanin sojoji da masu jerin gwanon ranar Kudus ta duniya a Abuja fadar mukin Najeriya. Hotunan faifan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar ke neman mafaka yayin da karar harbe-harbe ke kara kamari a kusa da su. An ce an kai gawarwakin mutanen goma sha hudu zuwa wani wuri da ba a sani ba. Ana gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya duk shekara a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.
Hukumomi a Myanmar sun ce adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar ya kai 1,644, yayin da wasu 3,408 suka jikkata, ye zuwa ranar Asabar din nan. Tunda farko dai mutane 1,007 ne aka sanar sun mutu sai wasu 2,389 da suka jikkata. Girgizar mai karfi maki 7.7 ta shafi Kasashen Myanmar da Thailand wadanda suk suka ayyana dokar ta baci a ranar Juma’a. Tuni kasar Myanmar ta nemi taimakon kasashen duniya da kuma kungiyoyi don agazawa wadanda girgizar kasarta shafa. Kasar Iran ta ce a shirye take ta taimakawa kasashen biyu da girgizar kasar ta shafa. A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya fitar yau Asabar ya ce Iran a shirye take ta shiga...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Nijeriya, kamar yadda kwamitin duban wata ya tabbatar. Baya ga Nijeriya, ƙasashen Saudiyya, Bangladesh, da Indiya suma sun ga watan a yau, Asabar 29 ga watan Ramadan, 1446. An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge Mijinki Sai dai wasu ƙasashe kamar Malaysia sun sanar da cewa za su yi Sallah ranar Litinin. Hakan na nufin cewa azumin watan Ramadan ya ƙare, kuma al’ummar Musulmi a Nijeriya za su gudanar da bikin ƙaramar sallah gobe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal, wanda ke nuna ƙarshen azumin watan Ramadan na bana. Kwamitin duban wata na ƙasar ya bayyana cewa an ga jinjirin wata a yammacin yau, wanda ke tabbatar da cewa gobe za a fara bukukuwan Sallah. Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge Mijinki Wannan na nufin cewa al’ummar Musulmi a Saudiyya za su yi bikin ƙaramar Sallah, domin kammala azumin da suka gudanar a tsawon watan Ramadan. Hukumomi sun buƙaci jama’a da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da bin dokoki don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Sunana Naja’atu Baffa Jihar kaduna: Ni dai a gaskia ban son akwai wani anko da za ai wannan sallar ko babu ba. Ina son saka takalmi mai dan tudu ba sosai ba, sai mayafi blue black, sai atamfa ta riga (half bubu) da ‘skirt’, sai sarka da dankunne da Awarwaro ‘silver’. Ina sha’awar cin Snacks irinsu meatpie, samosa, doughnut da kuma cake, sai kuma Yoghurt mai inibi. Ina son in ziyarci kanwar babata wacce take a cikin garin Adamawa. Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa: To batun shidimar sallah sai mu ce Alhamdullilah domin duk tanadin da mutum yayi sai ya kare, duba da yadda kayayyakin suturu ko tufafi suke tsada don haka sai mutum yayi amfani da...
Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne. A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira gudun tayar da hargitsi a Jihar Kano. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Gabanin yanzu dai, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da shi kansa Sarki Aminu sun ɗaura azama ta gudanar da haye-hayen sallah bana. Sai dai da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, Kurawa...
Rikicikin ya turnuke jam’iyyar SDP a yayin da aka samu shugabanni bangare biyu a Jihar Kogi, rikicin ya kunno kai ne bayan da wani bangare ya kaddamar da kwamitin gudanarwa a Lakwaja. Taron da aka gudanar a sakateriyar jam’iyyar na jihar, an zabi tsohon shugaban sashi na APC, Hon. Ahmed Attah a matsayin sabon shubagaba, tare da Alhaji Idris Sofada a matsayin sabon sakatare na jam’iyyar a jihar. Wakilai 3,890 ne daga kananan hukumomi 21 na jihar suka zabi shugabanni 21 na jam’iyyar. Sannan kuma jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) sun kasance a wannan wuri lokacin zaben. A jawabinsa na farko, Attag ya yi alkawarin zai yi gaskiya da adalci tare da daga martabar jam’iyyar SDP...
Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300. A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da yunwa da kuma samar da abinci ga al’umma. A cewar sa, karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara domin fara noman rani a karo na farko dan fadada harkar noma a kan Tudu. Alhaji Jamilu Danmalam yace an zabi kauyen Tunubu dake mazabar Kanwa domin fara noman Rani. Ya kara da cewar, wadanda suka anfana da tallafin za su ci moriyar kaso...
Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia. Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda lamarin ya shafa. Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu. “Kamar yadda aka...
Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin ɗaukar matakin da ya dace bisa doka. Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo Bidiyon, wanda ya bayyana a ranar Juma’a, ya nuna matar tare da wata ƙawarta suna tunkarar wajen da aka kange, inda jami’an tsaro suka hana su wucewa. Sai dai matar ta fusata, tare da marin ɗan sandan,...
A shekarar 1468 wanda yake mulkin Sonni Ali Shugaban Songhai ya ci wurin da yaki.Shi ba wanda yake ya saki jikinsa bane musamman ma musulmai wadanda suke da ilimin musulunci,amma wanda ya gaje shi Askia Muhammad na daya (1) wanda ya yi mulkin kasar daga shekarar( zuwa 1493–1528)ya yi amfani ne da wadanda suka yi karatu a matsayin wadanda yake tuntuva dangane da abinda ya shafi shari’a da al’amura na yau da kullum. Bayan da kasar Morocco ta mamaye ta a shekarar 1591, daga nan sai Birnin ya fara komawa baya.Aka bada umarni na kama Malamanta a shekarar 1593 saboda ana yi masu kallon basu goyon bayan abinda aka yi; an kashe wasu daga cikinsu lokacin da aka yi wani...
Gwamnatin Soji ta Myanmar, ta bayyana cewa mutum 1,002 sun rasa rayukansu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta auku a ranar Juma’a. Sama da mutum 2,000 sun jikkata, kuma ana ci gaba da ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe. Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo An kashe mutum 10 a wani sabon hari a Filato Jami’an agaji sun ce girgizar ƙasar ta fi shafar birnin Mandalay, inda asibitoci suka cika maƙil da waɗanda suka jikkata. Shugaban mulkin soji na Myanmar, ya nemi taimakon ƙasashen duniya, amma ana fargabar yaƙin basasa da ke ci gaba a ƙasar zai hana ayyukan jin-ƙai tafiya yadda ya kamata. Hukumar kare haƙƙin bil adama ta...
Yawancin wadanda suke da HNd basu samu damar tafiya aikin Yiwa kasa Hidima/Aikin Bautawa kasa wanda hakan ne kuma aka gay a kamata ayi masu adalci kan lamarin Sai dai kuma irin ci gaban da aka samu ya kawo ko samar da wata matsala ta yadda wadanda suka yi karatun suka kammala a makaranta sai ta kasance wasu daga cikinsu basu samu damar tafiya aikinyiwa kasa hidima ba saboda irin karatun da suka yi. Da yake bada ta shi gudunmawa darekatan lamurran ‘yan jaridu da hulda da jama’a ma’aikatar ilimi ta tarayya Boriowo Folasade, ya fitar da sanarwa wadda take tabbatar da gaskiyar lamarin na abubuwan da suka biyo bayan dukkan tarurrrukan da kuma ganawar da aka yi. Sanarwa ta...
Kungiyar JIBWIS a Karamar Hukumar Giwa ta bukaci al’ummar Yakawada da su ci gaba da rungumar koyarwar Al-Qur’ani a rayuwarsu ta yau da kullum. Mataimakin Shugaban kungiyar, Malam Ibrahim Mustafa Shatiman Giwa, ya yi wannan kira ne yayin bikin rufe Tafsirin Ramadan na bana da aka gudanar a Masallacin JIBWIS da ke Yakawada. Malam Ibrahim Mustafa ya bayyana jin daɗinsa kan goyon baya da jajircewar al’ummar Yakawada a duk tsawon Tafsirin. Ya jaddada muhimmancin kiyaye darussan da aka koya a cikin Ramadan tare da amfani da su a rayuwa bayan karewar watan mai alfarma. A nasa jawabin, Sheikh Suleman Abdulkarim Fatika ya nuna godiyarsa ga dukkan mahalarta Tafsirin da suka daure suka halarta tun daga farkon watan Ramadan...
’Yan Sanda sun kama mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan matafiya 16 ’yan Arewa a kan titin Uromi zuwa Obajana, a Jihar Edo. Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya yi tir da wannan hari, kuma ya bai wa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Hedikwatar Rundunar da ke Abuja, yin bincike. Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 1,800 aiki An cafke mutum 19 bayan arangama tsakanin sojoji da ’yan shi’a a Abuja Bayan faruwar lamarin, rundunar ’yan sandan Jihar Edo, ta tura jami’anta zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya. Har ila yau, ana ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere. Kakakin rundunar ’yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce Sufeto-Janar ya ba da...
Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya a birnin Kano sun haramta daban da aka saba yi a karshen watan azumi a birnin. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Jami’an tsaron kasar suna bada wannan sanarwan ne bayan da sarki na 15 Wato Aminu- Ado Bayero ya bada sanarwan janye daban da ya shirya gabatarwa a kwanakin salla Karamah. Shugaban Jami’an tsaron ya bayyana haka ne a wani taron yan jarida da ya gabatar a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa baza su amince da gudanar da taron Durba a karamar sallah a wannan shekara ba. Kakakin yansada na jihar Kano Haruna Kiyawa, ya sanya sanarwan a shafinsa na Facebook. Kafin haka aranar 18 ga watan Maris da muke ciki...
Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Tehran tana kan bakanta na maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a nan Iran daga cikin har da wani barikin sojoji a nan birnin Tehran a shekarar da ta gabata. Safari ya kara da cewa, jinkirin da aka samu na maida-martani yana da hikima a...

Wani Jami’in Leken Asirin HKI Ya Bukaci Kasashen Afirka Su Taimaka Su Karmi Falasdinawan Da Za;a Kora Daga Gaza
Gwamnatin HKI ta bukaci hukumar hukumar ayyukan leken asiri na kasar MOSAD ta nemi kasashe musamman a nahiyar Afirka wadanda zasu amince su karbi Falasdinawan da za’a kora daga Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin HKI na cewa Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu yana neman wata kasa ko kasashen nesa da HKI da dukkan kilomita don maida mutanen kaza zuwa can. Wasu ma’aikatan MOSAD biyu, da kuma wani jami’in gwamnatin Amurka sun fadawa shafin labarai na yanar gizo Axios, kan cewa tun sun rika sun tattauna da kasashe Somalia da Sudan ta kudu da kasar Indonasia da wasu da dama dangane da wannan batun. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin HKI ta kashe fiye da mutanen...
Wannan hanya, na matukar taimakawa sosai wajen sarrafa sinadarin insulin a jikin mutum. 2-Maganin Hawan Jini (Hypertension) Ganyen mangwaro na rage matsin jini, sannan kuma yana karfafa jijiyoyin jini. Saboda haka, a nan sai a nemi sabbin ganyen mangwaro, a tafasa su sosai a tace, sannan a sha rabin kofi da safe da kuma yamma. 3-Maganin Basir Sadidan Idan ana fama da basir, za a iya amfani da ganyen mangwaro don rage kumburi da ciwo. Bayan an samu wannan ganye na mangwaro, sai a busar da shi a kuma daka shi har sai ya zama gari. kana sai a dauki cokali daya na garin a hada da rabin kofi na ruwan dumi, sannan a zuba zuma a ciki...
Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a cikin tekun farisa wanda aka sanyawa suna Shahid Baghiri mai kuma tsawon mita 180. Sannan Labarin ya kara da cewa gwamnatin shugaba Donal Trump na kasar Amurka ta bawa Iran razarar watanni biyu ta amince da zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ta yi shirin yaki da kasar ta Amurka. Dakarun...
Kungiyar bada agajin ta gaggauwa ta “white Helmets” na kungiyar Al’kaida, wacce kuma take samun tallafin gwamnatin Amurka ta hukumar USAID ta rasa tallafin da take don gudanar da ayyukanta. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana cewa, kasashen yamma musamman Amurka sun yi amfani da kungiyar ta Al-qaeda a lokacin yakin kasar Syriya a shekara ta 2011 zuwa 2017 don ingiza kasashen yamma kan gwamnatin kasar Siriya na cewa ta yi amfani da makaman guba a kan mutane, don cimmmai manufofinsu a kasar ta Siriya. A halin yanzu dai shugaban Trump zai dakatar da tallafin da ya ke bawa kungiyar mai yuwa saboda sun cimma manufarko a kasar Siriya ta kifar da gwamnatin Bashar a Al’asad. A...
Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta yi ala wadai da kisan gilla da aka yi wa ‘yan Arewa 16 a Uromi, Jihar Edo, a ranar 28 ga Maris, 2025. Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda abin ya shafa suna kan hanyarsu daga Fatakwal zuwa Kano lokacin da aka kai musu farmaki, aka sare su, sannan aka banka musu wuta a abin da gidauniyar ta bayyana a matsayin abin “aikin rashin imani” na tashin hankali bisa la’akari da bambancin kabilanci. A cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na gidauniyar, Injiniya Dakta Abubakar Gambo Umar, ya fitar, gidauniyar ta nuna damuwarta kan yadda hare-haren da ake kai wa ‘yan Arewa ke ƙaruwa a wasu sassan Kudancin kasan nan, tana...
Gwamnatin Jihar Kaduna, ta sanar da shirin ɗaukar ma’aikatan lafiya 1,800 aiki don inganta tsarin Kiwon Lafiya a Matakin Farko (PHC) a faɗin jihar. Wannan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin ma’aikata da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar. Ƙungiyar JNI ta raba wa marayu 50 kayan Sallah a Borno An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Kamar yadda Kwamishiniyar Lafiya, Hajiya Umma Ahmad, ta bayyana, wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da yara. “Wannan mataki zai cike giɓin da ake da shi a cibiyoyin lafiya, domin tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Kaduna,” in ji ta. Gwamnatin jihar ta fara gyara cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda...
Wannan ya sa murnar da wasu ke yi ta komawa da haska finafinan Hausa masu dogon zango a tashar YouTube ta fara komawa ciki. Me ya sa ba a gamawa din? BBC Hausa ta ci gaba da cewa wani faifan bidiyo na wata tattaunawa da jagoran shirin Izzar so, Ahmad Lawan ya yi a tasharsa ta Bakori TV, ya ce masu kallo ne ba su gaji da kallon shirin ba, shi ya sa ba zai daina ba. Ya ce kasancewar Youtube ya dade kudu, amma bai je arewacin Nijeriya ba ne ya sa su ka gwada domin su koya wa mutanen arewa kallon fim a YouTube, shi kuma wannan fim din ya na ciki, ko in ce shi ne daya...
Ya kara da cewa cire Jami’oi daga tsarin albashi na (IPPIS),wanda hakan ne ya ba su Jami’oin tsayawa da kansu kan lamarin da ya shafi ayyukansu wanda har ila yau hakan ya sa ayyukamsu suka kara ingantuwa. Wike ya yi karin bayani,“akwai maganar amincewa da maganar kudaden bincike na Hukumar TETFund a cikin wasu makarantu, hakan ya kar bunkasa lamarin daya shafi bincike da kirkiro wasu abubuwa.” Su wadannan lamurran na ci gaba sun kara daidaita Jami’oi su maida hankali kan ilimin da suke samarwa domin ya cimma matsalolin da ake fuskanta a karni na ashirin da daya. da yake bayyana yadda ya ji dangane da karramawar da Hukumar Jami’ar kalaba ta yi masa na ba shi digirin digirgir,Wike ya...
Babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya yi gargadi a jiya juma’a da safe, akan abinda ya kira ‘yanayi mai cike da damuwa da yake faruwa a cikin kasar Sudan ta Kudu. An sami tashin hankali da fadace-fadace a cikin kasar ta Sudan ta kudu a ranar Laraba da jami’an tsaro su ka yi wa mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar daurin talala a cikin gidansa. Babban magatakardar MDD ya yi kira ga ‘yan siyasar kasar ta Sudan ta Kudu da su ci gaba da riko da yarjejeniyar sulhu da zaman lafiya,inda ya ce: “ A dawo da gwamnatin hadin kan kasa, da aiki da alkawullan da aka yin a zaman lafiya da sulhu, da hakan ne kadai hanyar dawo...
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne. A yayin ziyarar da sakataren na harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan har ta kai wa Guyanan hari. Rubio ya kara da cewa; Idan haka ta faru, to kuwa Venezuela za ta gwammace kida da karatu a wannan rana. Amurkan dai ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar ta Guyana a yayin ziyarar da Rubio ya kai. Shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela da yake mayar da martani ya ce; Marco Rubio wawa, ya zo yana yi wa...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakinta Dr. Isma’ila Baka’i, ta yi tir da sabbin hare-haren da HKI ta kai wa kasar Lebanon a daidai lokacin da ake bikin ranar Kudus. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar ta Iran ya bayyana cewa; Abinda HKI ta yi keta tsagaita wutar yaki ne,wanda abin a yi tir da shi ne. Haka nan kuma ya yi ishara da nauyin da ya rataya akan wuyan Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kasashen da suke cikin sa-ido da ‘yarjeneniyar tsagaita wutar yaki, haka nan kuma ya yi kira zuwa ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki mataki na gaggawa domin kawo karshen maimaita keta tsagaita wutar yaki da ‘yan sahayoniyar suke yi. Har ila...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.” Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam Khumaini ( r.a) da ya ayyana ranar Kudus a duniya a 1979, wacce ita ce juma’ar karshe ta watan Ramadan, a wancan lokacin manyan kasashen duniya masu takama da karfi suna kokarin ganin an mance da batun Falasdinu da kuma kasakantar da shi da cewa batu ne na Larabawa kadai. Limamin na Tehran ya kuma kara da cewa, abinda Imam Khumain ( r.a) ya yi...
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon harin da wasu mahara suka kai wa al’ummar Ruwi da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato. Maharan sun kai harin ne a daren ranar Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mutanen da suka halarci wata jana’iza da misalin ƙarfe 9:30 na dare. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Wani mazaunin yankin ya ce: “Mummunan hari ne. Sun zo kwatsam suka fara harbi. Muna roƙon hukumomin tsaro da su ɗauki mataki don kare al’ummarmu.” Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da faruwar harin, amma ba ta bayyana adadin waɗanda suka rasu ba. Kakakin rundunar, DSP Alabo...
A wannan Juma’a ce 28 ga watan Maris na shekarar 2025, aka gudanar da taruka da jerin wano na ranar Qudus ta duniya wadda ta zo daidai da ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma. An gudanar da wadannan taruka da jerin gwano ne a kasashe daban-daban da suka hada da wasu kasashen musulmi da na larabawa, har da wasu da wasu daga cikin kasashn ymmacin duniya da kuma na Afirka, ta hanyar shirya gagarumin gangamin da ke jaddada aniyarsu ta tabbatar da al’ummar Palastinu ta samu hakkokinta da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramta musu, tare da nuna cikakken goyon baya ga gwagwarmayarsu ta neman samun wadannan hakkoki nasu. A safiyar Juma’ar ne aka fara gudanar da jerin gwano...
Aƙalla mutum 19 aka kama bayan wata arangama tsakanin mabiya ɗarikar shi’a da jami’an tsaro a Abuja. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Banex, da ke Wuse 2, inda mutane da dama sun jikkata, sannan mutum ɗaya ya rasu. An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, ta ce ’yan shi’a sun kai wa jami’an tsaro hari da bindigogi, duwatsu, da wasu makamai. A sakamakon haka, aka tura ƙarin dakaru domin kwantar da tarzomar. “Kwamishinan ’yan sanda, CP Ajao Saka Adewale, ya yi tir da wannan hari da aka kai wa jami’an tsaro,” in ji kakakin rundunar,...
Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [20] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [19] Fashin Baƙi: Maganar da Ibn Juzai ya fadi a kan tawakkali tana bayyana ainihin ma’anar dogaro ga Allah cikin dukkan al’amura na rayuwa, wato samun alheri, da kiyaye shi, da kuma kauce wa masifa, ko kuma fita daga cikin masifa idan ta afku. Tawakkali yana nufin dogaro ga Allah da zuciya ɗaya tare da yin ƙoƙari da dalilan da Allah ya tanadar don cimma buri. Ba wai kawai mutum ya jingina da Allah ba tare da yin aiki ba, ko kuma ya dogara da aikinsa ba tare da tawakkali ba, sai dai a haɗa su duka. Bangarorin Tawakkali: Ibnu Juzai ya kasa tawakkali zuwa...
A yammacin yau Juma’a ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a birnin Lhasa na jihar Xizang wato Tibet, inda aka fitar da “Takardar bayanin ci gaban sha’anin kare hakkin dan Adam a Tibet a sabon zamani”. Takardar ta yi nuni da cewa, a ko da yaushe, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suna mai da hankali kan ayyukan da suka shafi Xizang, kuma suna ci gaba da kyautatawa da raya tsarin mulkin Xizang, da daukar matakai masu inganci don raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a, da kawo alheri ga jama’a, da inganta hadin kai da ci gaban kabilu, da kuma kare hakkin dan Adam na dukkan kabilun...
Tsadar rayuwa tun daga wancan lokacin ne bayan cire tallafin mai,da kwana daya kawai zuwa biyu sai rayuwar wasu dole ta fara sauyawa,kaya ko kayayyakin da ake saya a farashi na kashi 75 zuwa 100 sai abin ya koma farashin wasu har sai da,ya kai kashi 200 zuwa kashi 300 kai wani abin ma, har ya zarce haka,kuma kamar yadda Hausawa suka ce dole ce kanwar na ki ta sa hakan ta kasance,wannan kuma haka ne. Dole ce tasa haka saboda har an kai ga ganin abinda ya cirewa Buzu nadi wato wahala ke nan.Kuma dole ne cin kasuwa da makiyi wasu abubuwan abin ba,a iya cewa komai sai dai ayi gum da Baki kawai. Matsalar tsaro Ko shakka babu...
Ma’aikatar Ayyuka da Samar da Kayayyakin More Rayuwa, tare da hadin gwiwar First Impression Communication Limited, ta shirya wani taro kan shirin Samar da Ruwa Mai Tsafta a Birane da Karkara da Tsabtace Muhalli da Kiwon Lafiya (SURWASH) da ya gudana a Arewa House, a Kaduna. Da yake bude taron, Kwamishinan Ayyuka da Samar da Kayayyakin More Rayuwa, Dakta Ibrahim Hamza, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na magance matsalar karancin ruwa a jihar. Kwamshinan wanda Mataimakin Daraktan Albarkatun Ruwa, David Roven Aliyu ya wakilta, ya bayyana kokarin da gwamnati ke yi, ciki har da gina rijiyoyin burtsatse a wasu al’ummomi domin inganta tsaftar muhalli da kiwon lafiya. “Shirin SURWASH na Najeriya wani shiri ne da Asusun...
Yau Juma’a, shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG Shen Haixiong, ya gana da ministar raya al’adu ta kasar Rasha Olga Lyubimova dake ziyara a kasar Sin. Shen Haixiong ya ce, yana maraba da Rasha ta shiga a dama da ita cikin bikin fina-finai na kasa da kasa da 0za a yi a kasar Sin a bana. A nata bangare, Olga Lyubimova ta ce, a shekarun baya bayan nan, Rasha da Sin suna kara musaya a fannoni daban-daban, ciki har da fina-finai, kuma sun samu kyawawan sakamako. Ta kara da cewa, tana fatan bangarorin biyu za su zurfafa hadin gwiwarsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
A cikin shekaru da ya yi a masana’antar, Karkuzu ya nuna ƙwarewa wajen kawo canji da kuma nishaɗantar da al’umma. A madadin gwamnatin Kano da al’ummar jihar, gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin, ‘yan Kannywood, da masana’antar. Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya jiƙan jarumin, Ya kuma Aljanna Firdausi ta zama makomarsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma wanda ake samarwa a cikin kasar, ya ragu da tan miliyan 1.4. Kazalika, a gonar da ake noman Kwakwar Manja, za a iya samar da tan 12.5 a kowace hekta daya a duk shekara. Misali, a 2023 a heckta 20 a cikin shekara daya, an girbe Kwakwar da ta kai kimanin tan 250, inda akalla aka samu ribar kimanin Naira 150,000 na kowanne tan daya,...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da raunata jama’ar kasar tare da lalata kayayyakin more rayuwa na kasar. Ya ce ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen rashin daukar mataki da kuma yin shiru dangane da farmakin da sojojin Amurka ke kaiwa Yemen. Ya ce Amurka na ci gaba da kai hare-haren soji kan kasar Yemen tare da...
Miliyoyin al’umma daga sassa daban daban na duniya sun gudanar da jerin gwanon zagayowar ranar Kuds ta duniya wacce ta gudana yau. An dai kebance ranar ce domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu, kuma ana gudanar da ita ne a ko wacce Juma’ar karshe ta watan ramadana bisa fatawar jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatollah Khumeiny. A Iran ma kamar sauren sassan duniya jama’a sun fito kan tituna domin gudanar da bukukuwan ranar Qudus ta duniya, inda suke bayyana goyon bayansu ga Falasdinawa tare da yin tir da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza. An kuma yi irin wannan gangamin a kasashe da dama na yankin yammacin Asiya da suka hada da Iraki da...
A yau Juma’a aka kammala taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya na Boao. Cikin kwanaki 4, kimanin wakilai 2,000 daga kasashe da yankuna sama da 60 ne suka hallara a lardin Hainan na kasar Sin tare da musayar ra’ayi mai zurfi karkashin jigon na “Gina makomar asiya a duniya mai sauyawa.” A matsayinta na mai masaukin bakin, kasar Sin ta gabatar da shawarwari 4 da suka yi daidai da ra’ayin mahalarta taron. Shawarwarin sun hada da karfafa hadin kai da hadin gwiwa wajen inganta aminci, da inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kofa da dunkulewa, da samar da ci gaba da wadata na moriyar juna, da kiyaye zaman lafiya da tsaro da zaman jituwa. Alkaluma sun...
Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da Osasuna Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis...
Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, da shugabannin al’ummar Uromi bisa matakin da suka ɗauka domin daƙile yiwuwar tashin hankali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis tare da ba da umarnin ƙaddamar da bincike a kai. Wata sanarwa da Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya fitar, ta...
Da safiyar yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan da suka fito daga sassan masana’antu da cinikayya na kasa da kasa a nan birnin Beijing. Yayin ganawar, Xi ya jadadda cewa, a cikin shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama’ar Sin musamman ma cikin shekaru 40 da aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, Sin ta cimma gaggaruman nasarori wajen samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da dorewar walwalar al’umma dogaro da jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Sin wato jKS da kokarin al’ummar Sinawa cikin hadin kai, kuma ba za a raba wadannan nasarori da taimakon da kasashen duniya ke ba ta ba, cikin hadda gudunmawar da kamfanonin ketare dake kasar Sin suke bayarwa....
Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Fred Itua, ya bayyana cewa waɗanda aka kashe sun fito daga Fatakwal, a Jihar Ribas, amma ‘yan banga sun ɗauka cewa ‘yan ta’adda ne. Gwamna Okpebholo ya kai ziyara wajen da lamarin ya faru, inda ya jaddada cewa za a gudanar da bincike mai zurfi domin hukunta masu hannu a kisan. Amnesty International da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sun yi kira da a tabbatar da an yi adalci. Gwamnan Edo ya yaba wa shugabannin Arewa bisa yadda suka kwantar da hankula tare da guje wa ɗaukar fansa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Akwai yiwuwar Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa wata dokar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) a wasan gasar La Liga wanda ta doke Osasuna. Rahotanni na cewa ƙungiyar Osasuna za ta shigar da ƙorafi kan wasan da Barcelona ta doke ta da ci 3-0, saboda zargin saɓa dokar FIFA kan amfani da ɗan wasan da bai cancanta ba. Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara A jiya Alhamis ce Barcelona ta karɓi baƙuncin Osasuna a wani kwantan wasa na gasar La Liga, inda to doke baƙin nata da ci 3-0. Wannan nasarar ta bai wa Barcelona damar yin zaman faɗi da tazarar maki 3 a...
Kimanin mutum 150 ne suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wata mummunar girgizar ƙasa daban-daban da suka auku a ƙasashen Myanmar da Thailand. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa girgizar ƙasar wadda ta auku a wannan Juma’ar ta jikkata ɗaruruwan mutane a yayin da baraguzai suka danne gommai. An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Hukumar binciken yanayin ƙasa ta Amurka (USGS) ta bayyana cewa an fuskanci wata mummunar girgizar kasa har kashi biyu masu ƙarfin awo 7.7 da 6.4 a Myanmar, tare kuma da wata girgizar ƙasar mai karfi da ta yi ɓarna a kasar Thailand wacce ta shafi wasu wurare a yankin. Girgizar ƙasa ta...