2025-02-23@05:38:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 801
«Giya»:
Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan...
Kasar Aljeriya ta yi marhabin da shirin Iran na gudanar da taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a zirin Gaza, wanda shugaban na Amurka ya ce yana son karbe iko tare da raba al’ummar kasar baki daya. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya gabatar da shawarar gudanar da wani zama na...
Iraniyawa mazauna kasar Burkina Faso sun gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a birnin Ouagadougou. A wannan karon, kasashen biyu sun daukaka kyakkyawar dangantakarsu da aka gina a shekarar 1984. Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Ouagadougou, Mojtaba Faghihi, wanda ya halarci bikin, ya bayyana...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jaddada buƙatar samar da manyan gonakin gudanar da noman rani domin yaki da matsalar karancin abinci a Yankin Tafkin Chadi. Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin taron Gwamnonin Tafkin Chadi da aka gudanar makon da ya gabatar a garin Maiduguri fadar Jihar Borno karo na biyar,...
Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya tabbatar da cewa Shugabancin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ba zai gaza ba duk da ƙoƙarin yaɗa jita-jita da wasu ke yi. Kwankwaso, ya musanta wani rahoto da ke cewa mahajjata na iya rasa zuwa aikin Hajjin 2025, inda...

Jaridar Telegraph Ta Ce; Shugabannin Sojojin Iran Sun Bukaci Jagora Da Ya Soke Fatawar Haramci Kera Makamin Nukiliya
Jaridar Daily Telegraph ta watsa labarin cewa: Shugabannin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Khamenei da ya janye fatawarsa kan haramcin mallakar makamin nukiliya Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta watsa rahoton cewa: Shugabannin sojojin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da haramcin...
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Sake gina Gaza na bukatar kudi sama da dala biliyan 53 Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya fada a ranar Talata cewa: Sake gina yankin Zirin Gaza da yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya lalata yana bukatar kudi sama da dala biliyan 53, ciki har da sama da dala...
Duk da haka, da alama cewa, waɗannan binciken ƙila ba su da isasshen ikon gano bindigogin da suka ɓace. A yanzu haka dai, kwamitin majalisar dattawa yana zaune a Abuja domin ci gaba da bincike kan lamarin.
Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba...
Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana cewa: Sudan ce kasar da aka fi fama da matsalar jin kai a duniya A zaman tattaunawa da Kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar ta bayyana yakin basasar Sudan a matsayin “mafi girman matsalar jin kai a duniya,” inda ta yi gargadin irin mummunar illar da yake yi kan fararen hula,...
An tafi da shi tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ɗan uwansa da matarsa da ɗansa a yayin harin. An tattaro cewa, jigon na APC ya kai ziyara gidan ɗan uwansa ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin. Sai dai, an tsinci gawar matar dan uwansa mai suna, Madam...
Masu fafutikar kare haƙƙin bil Adama da ƙwararru a fannin kiwon lafiya haɗi da fasihai a ɓangaren shari’a sun buƙaci a tsananta hukunci kan masu yi wa mata kaciya a Nijeriya. Masu ruwa da tsakin sun yi kira da a ƙara wayar da kan al’umma domin ganin an daƙile kaciyar mata gaba ɗaya a ƙasar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa. Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya?...
An Yi Hasashen “Ne Zha 2” Zai Zama Fim Na Kagaggun Hotuna Mafi Samun Kudi A Duniya
“Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin. “A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin. “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta...
Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum, inda ya yi tsokaci game da rahoton dake da alaka da rarrabuwar iko tsakanin kasashen duniya na taron tsaro na Munich, yana cewa, bisa binciken da taron ya yi, kasa da kasa sun...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun harbe wasu jami’an ’yan sanda biyu a ofishinsu da ke Kolere a Ƙaramar Hukumar Fune ta Jihar Yobe. Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Janairun da ya gabata ne gungun wasu ’yan ta’adda suka harbe DSP Ali Pindar, wani jami’in ɗan sanda da ke ofishin....

’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A...
Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya gargaɗi Hamas da ta yi gaggawar sakin Isra’ilawan da take tsare da su a hannunta. Netanyahu ya ce ya bai wa ƙungiyar wa’adin zuwa ranar Asabar da ta saki Isra’ilawan da take garkuwa da su kamar yadda aka amince a yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu ta tanada. Gwamnatin Kano...
Har kullum, na kan ce, ci gaban kasar Sin wata dama ce ba kalubale ba. A matsayin ’yar Afrika, ci gaban kasar Sin daidai yake da ci gaban nahiyar Afrika domin duk wata nasara da ta samu, ba ta kyashin kai wa Afrika, kuma burinta shi ne ta ga nahiyar ta amfana, ta samu ci...
Kungiyoyin da suke dauke da makamai sun kashe fararen hular da ba su gaza 55 ba a wani hari da su ka kai wa wasu kauyuka da sansanin ‘yan hijira a Arewacin DRC. Mahukunta a yankin na Arewacin DRC sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai na kungiyar CODECO sun kai wa wasu kauyuka...
Nijeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024 a cewar ƙungiyar Transparency International. A cikin rahoton wanda ta fitar a yau, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa....
Nijeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024 a cewar ƙungiyar Transparency International. A cikin rahoton wanda ta fitar a yau, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa....
Kamfanin Siminti na BUA ya raba magungunan cututtuka daban-daban na kimanin naira miliyan 35 a ƙananan asibitoci da ɗakin shan magani 16 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Wamakko a Sakkwato. Daraktan Kamfanin BUA, Injiniya Yusuf Halliru Binji, a wurin rabon tallafin maganin ya ce BUA ya ba da tallafi ga asibitoci da ɗakunan shan magani...
ATM da ke cikin shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan duk wani cire kuɗi na N20,000. ATM da ke wajen shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan N20,000 da kuma ƙarin haraji har zuwa N500. Cire kuɗi a ƙasashen waje: Za a yi caji bisa ga yawan kuɗin da mai ATM ya buƙata. CBN...
Ɗan Majalisar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC
Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Zangon Kataf/Jaba daga Jihar Kaduna, Honorabul Amos Gwamna Magaji ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki. A safiyar Talata Shugaban Majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar da sauya shekar, yana mai bayyana rikicin cikin gidan PDP a mastayin dalilin ficewar dan majalisar daga jam’iyyar. Dan majalisar ya ...
Abin Kunya Ne Nijeriya Har Yanzu Ba Ta Iya Ciyar Da Kanta – Gwamna Bala
’Yan sanda sun kama gungun wasu makiyaya 47 ɗauke da makamai kan zargin kutse da yunƙurin aikata kisa a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya ta Umaru Waziri da ke Shinkafi a Jihar Kebbi. Kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar ya ce makiyayan sun haɗa baki ne da wani mutum wajen rusa katangar...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sirrin nasarar da Iran ta samu shine haɗin kai da kasancewar mutane a cikin kowane fagen neman ci gaba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa juyin juya halin Iran ya samu nasarar korar azzalumai daga kasar Iran ce, kuma sirrin ire-iren nasarorin da aka samu bayan nasarar...
Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Akwai yiwuwar nan gaba kasar Ukraine ta iya zama wani bangare na tsarin tsaron kasar Rasha Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa: Dole ne kasar Ukraine ta tabbatar da tsaron kudaden Amurka da aka zuba a cikinta, saboda zata iya zama karkashin kasar Rasha wata...
Wani sanatan Amurka yana barazana ga shugaban kasar Tunisiya da neman rusa nasarar dimokuradiyyar kasar Sanatan Amurka Joe Wilson, dan majalisar wakilai daga shiyar kudancin jihar Carolina, ya kaddamar da hari kan shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id, inda ya dauke shi a matsayin “dan mulkin kama karya” tare da yin kira da a kakabawa Tunisiya...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi kokarin dakile duk wani makirce-makircen da makiya ke kitsawa. Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga dimbin jama’a da suka halarci bikin cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a shekara ta...
Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro...
Gungun aiki na Majalisar Dinkin Duniya kan tsare mutane ba bisa ka’ida ba, ya yi kira da a gaggauta sakin hambararen shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum da matarsa Hadiza. Tun a watan Yulin 2023 ne ake tsare da Bazoum a wani reshe na fadar shugaban kasar da ke Yamai, inda Likitansa ne kawai aka yarda...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin...
Kamfanin kula da sufurin layin dogo na kasar Sin, ya ce jarin manyan kadarori da kasar ta zuba a bangaren layin dogo ya kai yuan biliyan 43.9, kwatankwacin dala biliyan 6.12, a watan Janairun bana. A cewar kamfanin, adadin ya karu da kaso 3.7 bisa dari idan aka kwatantan da makamancin lokacin a bara. A...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano, Umar Farouk Ibrahim. An dai rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin ne a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar ofishin gwamnan. ’Yan bindiga sun kashe fasto a Gombe An shiga nuna wa juna yatsa tsakanin Hamas da Isra’ila Aminiya ta ruwaito cewa, Kwamishinan Shari’a kuma...
’Yan bindiga sun kashe wani fasto, Rabaran Bala Galadima yayin harin da suka kai garin Lubo da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe. Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun kuma yi fashin kuɗi har Naira dubu 300 a yayin harin da suka kai cikin dare wayewar gari Lahadi. Wani mazaunin garin ya...
Sama Da Masu Amfani Da Kayayyakin Laturoni Miliyan 20 Ne Suka Nemi Tallafin Musayar Kayan Laturoni
Hamas ta sanar da yanke shawarar jinkirta sakin fursunonin Isra’ila nan gaba har sai abin da hali ya yi. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu ta fitar tana mai cewa an ɗauki matakin ne a matsayin mayar da martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta yi. Dalilin da...
A yau Litinin, kasar Sin ta sanar da sabbin ka’idojin kyautata kare sirrikan jama’a yayin kare tsaron al’umma. Firaministan kasar Sin Li Qiang ne ya rattaba hannu kan wata dokar majalisar gudanarwar kasar, domin fitar da ka’idojin, wadanda za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Afrilu. Ka’idojin na da nufin tafiyar da harkokin...
3. Wallafa labarin a kasan wannan sanarwar a ɓangaren tsokaci. 4. Wallafa labarin a shafinka na sada zumunta na facebook tare da makala #tak na #GasarLabarunSoyayya #LeadershipHausa #GasarLeadership 5. A kiyaye ƙa’idojin Rubutun Hausa da kuma amfani da daidaitacciyar Hausa da aka amince a yi amfani da ita a hukumance. 6. Ka tabbatar ka sanya...
Sai dai yadda gwamnatin Trump ta sanar da rufe USAID ya ba da damar tona asirinta, kuma tabbas tarihi zai tabbatar da cewa, gaskiya na hannun wadanda ke kokarin samar da ci gaba da kiyaye hadin gwiwar cin moriyar juna da ma wadanda ke kokarin tabbatar da makomar dan Adam ta bai daya.
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin ziyarar da ya kai wa tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a wannan Litinin ɗin. Aminiya ta ruwaito cewa, da misalin ƙarfe 12:36 na yau Litinin ce tawagar da Atikun ya jagoranta ta isa gidan tsohon Shugaban Ƙasar da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun. Gwamnan Zamfara...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata taba zama don tattaunawa da kasar Amurka ba a dai-dai lokacin take kara takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka bikin ciki shekaru 46 da samun nasarar juyin juya...
Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Sace Iyali 3 A Filato