2025-04-04@19:48:38 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2871

«Hukumar Shige da Ficen»:

    Kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, ta shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka na kakaba harajin kwastam kan abokan cinikayyarta. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta ce, harajin kwastam da Amurka ta kakaba, ya matukar take halaltattun hakkoki da muradun kasashe mambobin WTO, kuma ya matukar dagula ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da kuma tsarin tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa. Bugu da kari, hukumar harajin kwastam ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, kasar Sin za ta kara sanya harajin fito na kaso 34% kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka,...
    Shugaba Tinubu ya zanta da manema labarai bayan kammala Sallar Idi na karshen watan Ramadan a filin da aka gabatar da Sallar Idi na kasa a Abuja ranar Lahadi. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su koma kan aikata abubuwan da su ba ta dace ba, a maimakon haka, ya bukace su da su dage wajen aiwatar da kyawawan dabi’un game da darusan da suka koya a watan Ramadan. A cikin hudubar da babban limamin masallacin kasa dake Abuja, Dakta Abdulkadir Salman Sholagberu, wanda ya jagoranci Sallar ya gabatar, ya jaddada bukatar Musulmi su ci gaba da gudanar da ibadar da suka koya a Azumin watan Ramadan,...
    Kungiyar kasuwanci ta duniya  ( WTO) da asusun bayar da lamuni           ( IMF) sun yi gargadi akan sakamakon dake tattare da Karin kudaden fito na kasuwanci da gwamnatin shugaban kasar Amurka Donald Trump ta yi a jiya Alhamis.  Kungiyar kasuwancin ta duniya, ta yi hasashen cewa ci gaban harkokin kasuwanci a duniya zai sami koma baya da kaso 1% a cikin 2025, wanda hakan yake nufin akasin yadda aka yi hasashe tun da fari. Babbar daraktar kungiyar kasuwancin ta duniya Ngoz Okonjo-Iweala ta yi gargadin cewa, Karin kudaden fito da aka yi zai iya jefa duniya cikin yakin kasuwanci,  idan kuwa kasashe su ka dauki matakin mayar da martani, to za a sami tsaiko a cikin harkokin kasuwanci a duniya....
    Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya isa birnin Juba na kasar Sudan ta kudu a yau Juma’a, a kokarin lalubo hanyar warware dambaruwar siyasar da kasar take ciki da hana barkewar sabon yakin basasa.  Jim kadan bayan yi wa mataimakin shugaban kasar Riek Machar daurin talala a gidansa ne kasar ta shiga zaman dar-dar da fargabar sake komawa cikin yakin basasa. Da akwai kawance a tsakanin shugabannin kasashen Uganda Mosaveni da kuma Silva Kiir na kasar Sudan Ta Kudu.  Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai kasar ta Uganda ta aike da sojoji masu yawa zuwa kasar ta Sudan ta Kudu, domin bayar da kariya ga gwamnatin Juba. Gwamnatin Salva Kir tana zargin Machar da cewa yana rura wutar...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan birnin Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi Fard; Duniyar musulmi tana fuskantar jarabawa mai girma da ita ce kare al’ummar Falasdinu, da takawa masu girman kai na duniya birki,haka nan ‘yan Sahayoniya ‘yan daba. Limamin na birnin Tehran ya jaddada muhimmacin fuskantar ‘yan sahayoniya ‘yan daba a cikin wannan yankin na yammacin Asiya. Limamin ya tabo zagayowar ranar kafa tsrin jamhuriyar musulunci na Iran  da kaso 98% na al’ummar kasar su ka kada kuri’ar amincewa da shi a 1979, yana mai jaddada cewa an kafa tsarin jamhuriya a Iran ne bisa koyarwa ta musulunci.
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Al’ummar musulmi suna fuskantar manyan hatsari guda biyu,  da su ka hada laifukan da HKI take tafkawa a Gaza, da kuma kokarin shafe hakkokin falasdinawa baki daya. Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma tabo batun keta tsagaita wutar yaki da HKI take yi a kasar Lebanon yana mai kara da cewa, keta hurumin kasar Lebanon da ‘yan sahayoniyar suke yi, ya isa har birnin Beirut. Akan kasar Syria ma, jagoran na kungiyar Ansarullah na Yemen ya yi ishara da hare-haren da ‘yan sahayoniya su ka kai  a cikin biranen Damascus, Hums da Dar’a. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce,abokan gaba sun mayar da keta hurumin kasashen al’umma abinda za...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’o’I 24 da su ka wuce, sun kai 86, yayin da wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 287. Asibitocin yankin na Gaza sun karbi wannan adadin na  shahidai da kuma wadanda su ka jikkata, suna karbar magani. Ma’aikatar harkokin kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta kara da cewa ya zuwa yanzu jumillar Falasdinawan da HKI ta kashe tun daga 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu sun haura dubu 50. Bugu da kari a halin da ake ciki da akwai gawawwakin shahidai masu yawa da suke kwance a karkashin baraguzan gidajen da HKI ta rushe da mutane a cikinsu, da kuma wadanda...
    Tsohon Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Kano kuma tsohon Mashawarci na Musamman ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, CP Muhammad Wakili (ritaya), ya jaddada cewa dole ne ’yan sanda su yi amfani da ikon da suke da shi cikin gaskiya da adalci, don tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Da yake jawabi a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Gombe, a matsayin wani ɓangare na bikin makon ’yan sanda, CP Wakili ya ce ba zai yiwu jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba tare da goyon bayan al’umma ba. An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu zuwa Kudu Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52 Ya buƙaci jami’an...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin tare da hadin gwiwar babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta sanar a yau Juma’a cewa, za ta fara aiwatar da matakan kiyaye fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje kan nau’o’in ma’adinai bakwai matsakaita da masu nauyi da ba kasafai ake samun su, wadanda suka hada da samarium, gadolinium, terbium, dysprosium, lutetium, scandium da yttrium. Kuma wannan sabon mataki ya fara aiki nan take. Har ila yau, ma’aikatar ta sanar cewa, ta yanke shawarar kara wasu kamfanonin Amurka 16 da ke barazana ga tsaron kasa da moriyarta a cikin jerin sunayen kamfanonin da ta dauki matakin hana fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a kansu, tare da sanya kamfanonin Amurka 11 cikin jerin sunayen kamfanonin...
    Ta ce, “Abin da nake gani shi ne, INEC na taimaka wa masu shigar da kara kan yadda za su kammala ayyukansu na haram. “Wannan shi ne karon farko da aka gabatar da koken, ba su da adireshi, lambobin waya, duk da hana amma INEC ta shiryar da su yadda za su gabatar da bayanan da za su kammala kokensu. “Masu shigar da kara, ‘ya’yan jam’iyyar APC a yanzu suka mika takarda mai dauke da adireshin da babu shi domin ganin an yi min kiranye.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce: “Ko muna so ko ba mu so, lokaci ya yi da za mu yi bankwana.” Ƙungiyar Manchester City ta ce za ta shirya wani bikin bankwana na musamman domin girmama ɗan wasan kafin kakar ta ƙare. De Bruyne ya koma City daga Wolfsburg a kan fan miliyan 55, kuma ya taimaka sosai wajen nasarorin da ƙungiyar ta samu, ciki har da lashe kofin Zakarun Turai karo na farko a tarihinta, inda suka doke Inter Milan a wasan ƙarshe a birnin Istanbul. Sai dai ɗan wasan ya sha fama da rauni a ‘yan shekarun nan, inda ya shafe watanni biyar yana jinya a kakar da ta wuce. A...
    An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP). Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito ne daga ƙauyen Minda da ke Ƙaramar hukumar Lau a Jihar Taraba. Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52 Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno A yayin da take zantawa da manema labarai a Jalingo, ranar Juma’a ta ce an yaudari yaran daga unguwar su aka yi safarar su zuwa jihohin Kudu maso Gabas. Ta ce, sun...
    Ya kara nuna shakku kan dalilin da ya sa aka kafa dokar ta-baci a Jihar Ribas, yana mai cewa rashin tsaro ya addabi wasu sassan kasar nan, amma ba a kakaba dokar ta-baci ba ko kuma wani abu makamancin haka. “Idan shugaban kasa ya ce saboda rashin tsaro ne, saboda sun fasa bututun mai, yaya batun sassan kasar da ake fama da rashin tsaro? Shugaban kasar yana cewa su ma su kafa masa dokar ta-baci a kansa. Ba za su iya ba, saboda shi shugaban kasa ne da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, babu wanda zai iya sanya masa dokar ta-baci, saboda akwai rashin tsaro mai tsanani a arewa maso gabas, arewa maso yamma, hatta a kudu maso gabas da...
    Adadin waɗanda suka mutu sakamakon hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato ya kai 52 kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana. Hakan ya biyo bayan sake gano wasu gawarwaki 40 ne a ranar Laraba da Alhamis da daddare yayin da masu aikin ceto suka ci gaba da kutsawa cikin dazuka don nemo waɗanda suka ɓata. Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi Shugaban Ƙungiyar al’adu ta Bokkos Cultural Development Council (BCDC) Vanguard, Farmasum Fuddang, ya shaidawa tashar Talabijin Channels cewa an yi jana’izar mutane 31 a ranar Alhamis tare da wasu  yara biyar da suka ƙone ƙurmus a ƙauyen Hurti. An kashe...
    A jiya Alhamis 3 ga wata ne, cibiyar daukar matakan gaggawa kan matsalolin kwayar cutar na’ura mai kwakwalwa ta kasar Sin, gami da ofishin gwajin ayyukan fasahohin magance kwayar cutar na’ura mai kwakwalwa na kasar, suka bullo da wani rahoto, kan binciken hare-haren yanar gizo da wasu kasashen waje suka kai kan tsarin adana bayanan gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta nahiyar Asiya karo na 9 da aka yi a birnin Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin a shekara ta 2025, gami da wasu muhimman ababen sadarwa dake lardin na Heilongjiang, inda ya shaida yadda kasar Amurka ta kaddamar da hare-haren intanet, kan tsarin adana bayanan gasar wasannin motsa jiki ta lokacin...
    A wani labarin makamancin wannan, kimanin kananan masu kiwo 100 ne a Jihar Kwara, suka amfana da tallafin kiwon Awaki na kashin farko. Wannan tallafi, na daga cikin dabarun gwamnatin jihar na son kara bunkasa fannin da kuma samar da kudaden shiga ga masu kiwon, domin samun riba. A jawabinta a garin Ilorin, wajen kaddamar da kashin rabon Awakin, kashi na farko; wato a karkashin shirin jin kan iyali na L-PRES, Kwamishin Bunkasa Kiwo, Oloruntoyosi Thomas ya sanar da cewa, masu ruwa da tsaki a fannin ne, suka bayar da tallafin Awakin Thomas ya sanar da cewa, kwalliya na biyan kudin sabulu dangane da shirin L-PRES a jihar ta Kwara. Ta sanar da cewa, Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak, ba...
    An kashe wani sufeton ɗan sanda a yayin wani kwanton ɓauna da wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a kwalejin horar da rundunar ’yan sanda (PMFTC) Camp Limankara, Gwoza a Borno.  Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa majiyar Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 0600 a ranar 3 ga Afrilu, 2025, yayin da tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da na makarantar horas da ’yan sanda ta Mopol Gwoza da wasu sassan rundunar ’yan sanda ke sintiri a ƙafa. Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Shettima kafin zaɓen 2027 Sufeta Andrawus Musa da ke aiki a rundunar 6PMF a Maiduguri ya samu munanan raunuka...
    Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci gaba saboda na gano cewa tsarin ya yi tasiri sosai ba kawai a kan farashin mai ba, har ma da kyautata ci gaban tattalin arziki. “Bugu da kari, kwamitin yana jiran hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta gabatar da rahoton aikin da aka ba ta dangane da wannan manufar. Da zarar an yi haka, abu na gaba shi ne a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Sheikh Dokta Idris Abdulaziz. Malamin ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya. Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — Wike Ya je ƙasashen Masar da Saudiyya domin neman magani kafin watan Ramadan. Tun da safiyar ranar Juma’a, ɗaruruwan ɗalibansa da mabiyansa daga Bauchi, maƙwabtan garuruwa da kuma wasu jihohi sun taru a gidansa domin halartar jana’izarsa. An gudanar da sallar jana’izar a ranar Juma’a a filin Idi na Games Village. Manyan malamai, ’yan siyasa, ’yan uwa...
    Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Sheikh Dokta Idris Abdulaziz. Malamin ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya. Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — Wike Ya je ƙasashen Masar da Saudiyya domin neman magani kafin watan Ramadan. Tun da safiyar ranar Juma’a, ɗaruruwan ɗalibansa da mabiyansa daga Bauchi, maƙwabtan garuruwa da kuma wasu jihohi sun taru a gidansa domin halartar jana’izarsa. An gudanar da sallar jana’izar a ranar Juma’a a filin Idi na Games Village. Manyan malamai, ’yan siyasa, ’yan uwa...
    Harbin dai ya samu Comfort ne a kai, inda nan take ta mutu, yayin da wasu harsasai suka samu mijinta a mukamuki da kafadarsa dama. Yayin da ‘ya’yansu ke kururuwar firgici, rahotanni sun ce jami’an sun gudu daga wurin. An kori Musiliu daga aikin ‘yansanda ne a ranar 17 ga watan Satumba, 2015, daga bisani kuma aka bayar da belinsa a shekarar 2017 ba tare da sanin dangin da ya kashewa ‘yan uwa ba. Bayanan kotun sun nuna cewa mai shari’a O.A. Taiwo na Kotun 26, Babban Kotun Ikeja, ya bayar da belin Musiliu a kan Naira miliyan 1 tare da mutane biyu. A hukuncin kotun, Mai shari’a Taiwo ya bayyana cewa, “Sashe na 115(1) na dokar shari’a ta shekarar...
    Jaridar BusinessDay tayi nazari kan manyan ayyuka biyar na Layukan Dogo da suka samar wani sauki, a zirga-zirgar Jirgin kasa a kasar nan. 1 Layin Dogo Daga Legas Zuwa Ibadan Ingantaccen aikin layin Dogo mai tsawon kilomita 157 da ya taso daga jihar Legas zuwa garin Ibadan. An faro aikin ne a watan Maris na 2017 aka kuma kaddamar da shi, a ranar 10 na watan Yununin 2021. Aikin ya kasance mai tagwayen hanya biyu da ake da shi, Afrika ta Yamma. An kammala aikin layin na Dogon ne, cikin shekaru hudu, wanda kuma aka kara fadada shi zuwa kimanin kilomita 7 domin ya hade da layin Dogo na tashar Jirgen Ruwa da ke Apapa. Wannan layin Dogon, na bayar...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan a zantawarsa tan wayar tarho da yerima mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya sannan Firai ministan kasar Muhammad bin Salman ya taya shi murnin salla karama ya kuma yiawa dukkan kasashen musulmi fatan alkhairi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, JMI bata neman yaki da kowa amma kuma a shirye take ta kare kanta a duk lokacinda wani ya takaleta. Pezeshkiyan ya kara jaddada cewa shirin Nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya ne, kuma wannan kamar ydda hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA ta tabbatar. Banda haka kamar yadda yake a shekarum baya, hukumar zata ci gaba da bincike don tabbatar da hakan. A wani bangare na maganarsa shugaban...
    Kotun kare kundin tsarin mulki a kasar Korea ta Kudu ta tabbatar da tsige shugaban kasa Yoon Suk Yeol daga kan kujerar shugabancin kasar a safiyar yau Jumma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalan kotun koli na kare kundin tsarin mulkin kasar, su 6 suna karanta wannan hukuncin da suka yanke kan tsahoin shugaban. Kafin haka dai Yeol lauya ne wanda ya shiga harkokin siyasa a yan shekarun da suka gabata, sannan ba zata ya lashe zaben zama shugaba a shekara ta 2022. Amma a shekarar da ta gabata wato 2024 ya kafa doka t abaci a kasar saboda kare kansa da matarsa daga wasu kura kurai da suka aikata. Wannan dokar day a kafa ya...
    Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a kasashen Turai ko Geneva Ali Gahraini ya yi tir da amincewar da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta yi da zargin kasar ta take hakkin bil’adama a taronta na baya-bayan nan abirnin Geveva. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baraini yana cewa, hukuncin da hukumar ta yanke a kan JMI na son zuciya ne kuma saboda siyasar JMI a duniya ne. Bahraini ya kara da cewa, wannan hukuncin ya taba mutucin hukumar ta yin adalci ga wasu kasashen a duniya. Bahraini ya kara dan cewa, abin mamakoi shigha ba’a taba jin wannan hukumar ta yankewa HKI irin wannan hukuncin ba, duk tare da cewa duk duniya tana ganin yadda...
    Na ji dadi da yadda ka yi kira ga sauran Malamai da su zama masu kwadaitar da neman Ilimi a kowanne fanni, sannan su kaurace wa furta haramci a kan abubuwan da Shari’a ba ta yi haramci a kai ba. Tabbas, ayoyin Alkur’ani suna nan kamar yadda aka saukar kuma ba za su sauya ba har duniya ta nade, amma fahimtarsu tana sauyawa daidai da zamani, don haka, bai dace a yi watsi da kimiyya da fasahar zamanin nan ba da ake ganin na turawa ne kawai, matukar ba a samu fiye da tasu ba. Akramakallah, gaskiya ne, ya dace Malamai su rika ba da fatawa da ta yi daidai da zamaninsu da kuma fahimtar da al’ummar Musulmai Isharori na...
    Jam’iyyar APC, ta musanta jita-jitar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na shirin sauya Mataimakinsa, Kashim Shettima, kafin zaɓen 2027. Jam’iyyar ta ce babu wata matsala tsakaninsu kuma maganar sauya Shettima ba ta da tushe. Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Bala Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa wasu ne ke yaɗa wannan jita-jitar don tayar da ƙura. “Wannan jita-jita ce kawai marar tushe. Maganganu ne da bai kamata a ɗauke su da muhimmanci ba,” in ji shi. Ya ƙara da cewa, “Ko da a ce akwai wani dalili da zai sa shugaban ƙasa ya sauya mataimakinsa, ba zai iya yin hakan...
    Yayin gabatar da rahoton an raba lambar yabo ga Hakiman da aka fi samun gudunmawar Zakkar daga gundumominsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ya yanke jiki ya faɗi har aka kai shi asibiti a ƙasar waje. Ya ce wannan ƙarya ce da maƙiyansa na siyasa suka ƙirƙira don kawar da hankalin mutane. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu Wike, ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Alhamis yayin da ya kai ziyara wajen wani aiki da ake shirin ƙaddamarwa a watan gobe domin bikin cikar Shugaba Bola Tinubu shekara biyu a mulki. A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa, Anthony Ogunleye, ya fitar, Wike ya ce waɗanda ke yaɗa wannan labari suna ƙoƙarin...
    Jiragen yakin Isra’ila sun kai karin hare-hare ta sama kan kasar Siriya, inda suka bijirewa gargadin Majalisar Dinkin Duniya game da hadassa asarar fararen hula yayin da suke ci gaba da kai wa kasar ta Larabawa hare-hare. Rahotanni sun ce a ranar alhamis, jiragen saman Isra’ila sun kai hare-hare a kalla sau biyu a kan wuraren da sojoji a kusa da birnin Damascus, inda bayanai suka ce sun kai hari a yankunan Al-Kiswah da Al-Muqaylibah. Kawo yanzu dai babu rahoton asarar rayuka. Hare-haren sun zo ne kasa da kwana guda bayan hare-haren da Isra’ila ta kai makamancin haka inda ta kashe mutane 13. Fararen hula 9 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari da jiragen...
    Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini tare da shan alwashin ramuwar gayya game da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta musu kankan kayayyakin da ake shigowa da su kasar.  Gwamnatoci da kamfanoni da dama sun sanar da matakan gaggawa na samar da matakan dakile matakin da Amurkan ta dauka kansu. A ranar Laraba ne, ya sanya harajin kan duk kayayyakin da ake shigowa da su Amurka da kuma karin haraji kan wasu manyan abokan kasuwancin kasar. Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga kamfanonin Turai da su dakatar da shirin zuba jari a Amurka. “Ina ganin abin da ke da muhimmanci, shi ne a dakatar da saka hannun jarin da za a cikin ‘yan...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar. A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi, ya yi kira ga mambobin kungiyar SCO da su yi Allah wadai da kalaman da shugaban na Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya ce yana da hadari. Majid Takht Ravanchi ya yi kakkausar suka ga barazanar harin bam da Trump ya yi a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, hakan ya keta...
    Kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi Isra’ila game da harin da ya yi sanadin mutuwar ma’aikatan ceto a Gaza yana mai cewa hakan zai iya kasancewa ‘lafin yaki’. Ma’aikatan agaji 15 ne suka ras arayukan a wani kazamin hari da Isra’ila ta kai kan motocin daukar marasa lafiya a Gaza wada ya fiddo a fili irin ” laifuffukan yaki da sojojin Isra’ila suka kwashe tsawon lokaci suna aikatawa a zirin Gaza”. Kafin hakan dama hukumar kula da hakkin bil adama ta MDD ta amince da kudurin dake kira ga Isra’ila da kada ta aikata kisan kiyashi a zirin Gaza. An amince da kudurin ne ranar Laraba yayin taron hukumar na 58, bayan ya...
    Ministocin harkokin wajen kasashen kawacen sahel na AES da ya hada Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar, na wata ziyarar aiki a kasar Rasha. Ana sa ran ministocin za su kasance a birnin Moscow a yau Alhamis da gobe Juma’a, don tattaunawa, da zurfafa hulda tsakanin bangarorin biyu, kamar dai yadda aka bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwarsu. Sanarwar, ta ce shawarwarin da ministocin kasashen kungiyar ta AES za su yi tare da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, wani bangare ne na burin shugabannin kasashen uku na yankin sahel da sojoji ke mulki da kasar Rasha, na fadada hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki da kuma tsaro. Har ila yau, sassan biyu za su zanta game...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Akwai cututtuka da dama da ke yaɗuwa, kuma mafi yawan mutane da ke ɗauke da su, ba su san suna da su ba. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce zaman lafiya, samun abinci da wadata, da rashin damuwa a ƙwaƙwalwa na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da lafiyar mutum. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari Ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke damun mutane da yawa, ita ce cutar hawan jini. Wannan cuta na kashe aƙalla mutane miliyan biyu a duk shekara a Najeriya. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi bayani ne...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da hada karfi da karfe wajen gina kyakkyawar kasar Sin, da kuma sa kasar ta kara zama kore shar ta hanyar dasa itatuwa. Xi wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na sojan kasar, ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar aikin sa kai na dashen itatuwa a nan birnin Beijing a yau Alhamis. Yana mai cewa, a halin yanzu, yawan gandun daji na kasar Sin ya zarce kashi 25 bisa dari, wanda ya ba da gudummawar kusan kashi 25 cikin dari na sabon koren yanki na duniya. Kana yanayin muhalli yana ci gaba da ingantuwa, kuma mutane na ganin hakan...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Mohammed Hassan a matsayin Darakta Janar na farko na Hukumar Fasahar Sadarwa da inganta Tattalin Arzikin ta fasahar zamani ta Jihar Jigawa. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar a Dutse. Kafin nadin nasa, Dr. Muhammad Hassan shi ne shugaban hukumar Fasahar Sadarwa da Kimiyya ta Jigawa, wato Galaxy ITT. Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa sabo  shugaban hukumar ya sami digirinsa na farko a fannin Lissafi daga Jami’ar Bayero, Kano, a shekarar 2008. Daga bisani, ya samu digiri na biyu a fannin Kimiyyar Kwamfuta daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Afirka (AUST), Abuja, a shekarar 2011, sannan...
    Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar. Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce wannan shiri ne da aka samar ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da Bankin Raya Musulunci (IsDB) na Saudiyya domin kafa ingantattun abubuwan more rayuwa ga masu zuba jari da manoma a fannin sarrafa nama da madara. Dakta Isiaka, wanda ya jaddada muhimmancin wannan aiki, ya bayyana cewa wannan ne karon farko da wani gwamna mai ci ke jagorantar kwamitin da ke kula da irin wannan babban shiri....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu. Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare da wani tsohon Ambasada da sauran waɗanda ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su. Gobara ta lalata wani ɓangare na gidan Ado Bayero Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Aminiya ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da tsohon shugaban Hukumar NYSC daga mahaifarsa a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina, a ranar 5 ga Fabrairu, 2025. Da yake jawabi gabanin miƙa su a...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
    Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi Amurka da cewa. duk wani harin soji a kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai haifar da “mummunan sakamako” ga daukacin yankin. Sergei Ryabkov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata mujallar harkokin kasa da kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari idan har ta kasa cimma matsaya da Washington kan shirinta na nukiliya. Ryabkov ya ce, “Hakika ana jin barazanar, ana kuma jin bayanai kan abubuwan da suka dace,” in ji Ryabkov, yana mai cewa “Sakamakon hakan, musamman idan harin ya kasance kan kayayyakin nukiliya, na iya zama bala’i ga daukacin yankin.” Ya ce sabbin kalaman na Trump za su kara...
    Shugaban kasar Burundi ya yi gargadin cewa Rwanda na da shirin kai wa kasarsa hari, bayan da sojojin Burundi suka taimakawa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) a yakin da take yi da ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda. Shugaban kasar ta Burundi Evariste Ndayishimiye ya bayyana cewa, ya samu “sahihan bayanan sirri” da ke nuni da shirin Rwanda na kai wa Burundi hari, ko da yake bai bayar da karin bayani kan shirin da yake yin zargin a kansaba, wanda Rwanda ta musanta. “Mun san cewa yana da shirin kai hari Burundi,” in ji Ndayishimiye a wata hira da wata kafar yada labarai yayin da yake magana kan shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, yana mai jaddada cewa “‘yan...
    Dakarun Yaman sun sanar da mayar da martani kan harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan kasarsu, wanda ya hada da hare-hare ta sama har sau 36 a yankuna da dama a cikin gundumomin Sanaa, Sa’ada, da wasu jahohin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama. Kakakin Rundunar sojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree ya tabbatar da cewa, sojojin Yaman sun gudanar da wani shiri na soji na hadin gwiwa, inda suka yi arangama da jirgin ruwan Amurka Harry Truman da jiragen yakin da yake dauke da su  a arewacin tekun Bahar Maliya. Saree ya ci gaba da cewa, a harin an yi amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka, kuma harin...
    Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka. A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman musulmi ta duniya ta yi kira ga duniya da ta bayyana goyon bayanta ga al’ummar Palasdinu ta hanyar daukar matakan gaggawa da suka hada da dukkanin hanyoyin soja, tattalin arziki, da diflomasiyya mai  inganci. Dangane da haka ne kungiyar ta yi kira ga limaman masallatan Juma’a a fadin duniya da su sadaukar da hudubar sallar Juma’a na gobe don magana kan wajabcin magance wahalhalu da...
    Aljeriya ta kira taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin tattauna halin da Falasdinu ke ciki. Bayan karuwar laifuffukan da yahudawan sahyoniyawa da suke aikatawa a kisan gillar da suke yiwa Palastinawa a yankin zirin Gaza da kuma ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahyoniya suka yi a yammacin gabar kogin Jordan, Aljeriya ta bukaci gudanar da wani taron gaggawa na kwamitin sulhu kan halin da Falasdinu ke ciki. Kasar Aljeriya ta ba da misali da karuwar hare-haren da Isra’ila ke kai wa a yankunan Falasdinawa da ta mamaye musamman a yankin zirin Gaza a matsayin dalilin bukatar gudanar da wannan zama. Sama da wata guda kenan da Gaza ke cikin...
    Ya ce, “Akwai rahoton cewa Turji ya shirya zai ziyarci yankin Gabashin Gatawa domin gudanar da bukukuwan Sallah, amma matakin da jama’a suka dauka na sanar da jami’an tsaro ya dakatar da shi ga hakan.   “Wannan na iya zama dalilin da ya sa Bello Turji ya huce fushinsa a kan manoman da ba su ji ba gani ba.”   Sai dai hukumomin ‘yansanda a jihar sun ki cewa komai kan lamarin.   Majiyar ‘yansandan ta yi ikirarin cewa, “tunda ana ci gaba da aikin hadin gwiwa na sojoji a yankin, ‘yansanda ba su da hurumin yin magana kan ci gaban tsaro a yankin.   Da aka tuntubi runduna ta 8 ta sojojin Nijeriya ta mika wakilinmu ga rundunar ‘Operation...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Alhamis ta lalata wani sashe na shahararren gidan Ado Bayero da ke ƙofar Nassarawa a Kano. Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a hawa na tara na ginin da cibiyar Jami’ar Northwest University take. Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Rahoton na cewa gobarar ta shafi wani sashe na sashen ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa na jami’ar. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’an kashe gobara amma abin ya ci tura domin an kasa samun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ta wayar salula zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
    A kokarin magance matsalar karancin ruwan sha da garin Rano ke fuskanta na tsawon shekaru, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da ta fara amfani  da  Madatsar Tiga don samar da ruwa mai a garin. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin Sarkin Rano, Ambasada Dr. Muhammad Isa Umar, wanda ya kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a Fadar Gwamnati da ke Kano. Gwamna Yusuf ya yaba wa Sarkin Rano bisa jajircewarsa wajen kare muradun al’ummarsa, inda ya tabbatar masa da cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalar ruwa a garin. Ya bayyana cewa an riga an tsara shirin gina rijiyoyin burtsatse tare da hadin gwiwar ƙaramar...
    Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka yi ta taimakon kai don taimakawa matafiya a kan hanya. Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a Legas Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Gadar taimakon kai da aka gina a madadin babbar gadar da ta rufta watanni bakwai da suka gabata, ta kasance hanyar shiga ga masu ababen hawa da ke bin hanyar. Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas...
    Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel. Tana da digiri na uku (Ph.D.) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare, tare da gogewa a harkar koyarwa daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu. “Dr. Jummai ta rike mukamai da suka gada da Darakta a Makarantar Sakandaren gwamnati ta ‘yan mata da ke Kazaure da kuma Darakta a Makarantar Sakandare ta larabci da ke Babura. Mace ce...
    “A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya fara rangaɗin wuraren haƙar ma’adanai da masana’antu, inda ya fara ziyarar aiki a wani kamfani mai zaman kansa na Comet Star Industry da ke Ƙaramar Hukumar Anka.   “Ma’aikatar, mallakin Prince James Uduji OON, tana sarrafa kusan tan 1,000 a kullum. Tana da cikakkun kayan aiki da sabbin fasahohin haƙar ma’adinai don tabbatar da gudanar da ayyuka masu inganci. “Lokacin da ya je masana’antar, Gwamna Lawal ya zagaya wurare da dama, inda ya fara tun daga magudanar ruwa da zuwa duka sassan injina da kayan aiki.   “Gwamna Lawal ya kuma ziyarci wurare daban-daban a cikin masana’antar, ciki har da gidan wutar lantarki da ke samar da wutar lantarki ga ɗaukacin kamfanin,...
    A jiya Laraba 2 ga wata, rundunar sojojin ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar, ta kaddamar da wani atisayen soji mai taken “Strait Thunder-2025A”, a yankunan tsakiya da kudancin zirin Taiwan, wanda ya kasance matakin da aka dauka dangane da kalamai na shirme da jagoran yankin Taiwan, Lai Ching-te ya furta a kwanakin baya, da ma yunkurin jam’iyyar DPP da ke karkashin jagorancinsa na neman ‘yancin kan yankin Taiwan. Duk da haka, wasu ‘yan tsirarrun kasashen yamma da ma kungiyoyi sun sake fitowa suna kara wa miya gishiri a kan batun, inda suka ce wai suna kin amincewa da daukar matakin kashin kai na canza yanayin da ake ciki a zirin tekun Taiwan. To, bari...
    Sama da gidaje 70 ne suka lalace da rumfuma a wata guguwa da ta yi ɓarna a unguwar Mabudi, Sabon Gida, da sauran unguwanni a ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mamakon ruwan sama da aka yi a daren Laraba, wanda ya biyo bayan ruwan sama, ya yi ɓarna matuƙa. INEC ta yi watsi da buƙatar yi wa Sanata Natasha kiranye Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa kimanin gidaje 70 ne rufinsu ya ɗaga, yayin da wasu gine-gine suka ruguje. Nanbol Nanzing, wani mazaunin ɗaya daga cikin unguwar da lamarin ya shafa, ya koka da yadda lamarin ya faru tare da...
    Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa takardar neman tsige Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ba ta cika sharuɗɗan doka da kundin tsarin mulki ya tanada ba. INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa takaitacciya da ta wallafa a shafinta na Facebook yau Alhamis, tana cewa: “Takardar neman tsige Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya ba ta cika sharuɗɗan da ke cikin sashi na 69(a) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ba.” INEC Ta Karɓi Takardun Yi Wa Sanata Natasha Akpoti Kiranye  Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha Sai dai hukumar ta yi alƙawarin fitar da cikakken bayani kan wannan ci gaba nan ba da...
    Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa buƙatar da wasu suka shigar don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Mazaɓar Kogi ta Tsakiya kiranye, bai cika sharuɗa ba. INEC ta ce yunƙurin bai cika sharuɗan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar ba. Bello Turji ya kashe manoma 11 a wani sabon hari a Sakkwato  NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Wannan sanarwa ta fito ne daga shafukan sada zumunta na INEC a ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025. Wasu ƙungiyoyi sun yi ƙoƙarin yi wa Sanata Natasha kiranye, wanda suka ce Sanatan na neman jefa su cikin rikicin da ka iya hana su samun romon dimokuraɗiyya. Ƙungiyoyin sun...
    Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, da mayaƙansa sun kai mummunan hari garin Lugu da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, inda suka kashe manoma 11. Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne yayin da Turji ke dawowa daga wata ziyarar sallah da ya kai yankin. Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Wani mazaunin Isa, Basharu Altine Giyawa, ya ce, “Tun a ranar Asabar muka samu bayanai cewa Turji zai ziyarci Gatawa, kuma mun sanar da hukumomi. “Duk da haka, shi da mutanensa sun bi ta ƙauyukanmu, sun yi bikin sallah, sannan suka kashe manoma 11 a hanyarsu ta komawa Fakai.” Ɗan...
    Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yakin Sahel (AES) mai mambobi uku – Mali da Nijar da Burkina Faso – da ke ƙarƙashin mulkin soja sun ɗorawa sauran kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka haraji na kayakin da suke shigowa kasashen uku. Jaridar Premium Time Hausa ta kara da cewa Sahel ta sanya haraji na 0.5% kan dukkan kayan da za a shigo da su ƙasashensu, daga ƙasashe da suke mambobin ƙungiyar raya tattalin arziƙi na yammacin Afirka (ECOWAS). A cikin wata sanarwa haɗin guiwa a makon da ya gabata, ƙungiyar AES ta ce tana son amfani da kudaden ne don tafiyar da al-amuran ƙungiyar. Harajin, wanda ya fara aiki daga ranar Juma’ar da ta gabata zai shafi duk wani...
    Gwamnatin HKI ta sha mamaki da ganin gwamnatin shugaba Trumo na kasar Amurka ta sanya mata harajin shigowar kayakin HK zuwa kasar Amurka, a yayinda, kafin haka ta bada sanarwan cire dukkan kudaden fito ko haraji ga kayakin Amurka da ke shigowa HK. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta majiyar kafafen yada labarum HKI na fadar haka daga bakin wani jami’an gwamnatin kasar. Labarin ya kara da cewa, Amurka ta dorawa HKI kudaden fito na kasha 17% kacal, sai dai ba abinda take tsammani zai faruba, tsammaninta shi ne irin wanda ta yi wato babu kudaden fito. Gwamnatin Amurka dai ta rikita harkokin kasuwanci da dama a duniya saboda kudaden fito da ta karawa kusan kasashen duniya gaba...
    Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kai wadannan hare-hare ne a garin Rasul Isa da lardin Salif a yammacin birnin Hudaida na kasar ta Yemen. Sannan tashar talabijin ta Almasirah ta bayyana cewa akalla mutum guda ne ya rasa ransa a wannan harin sannan wani guda ya ji rauni. Har’ila yau jiragen yakin Amurkan sun kai hare-hare kan yankin...
    Sojojin HKI sun kashe akalla mutane 80 a asbitin Jabaliya a safiyar yau Alhamis, sannan sji ne hari mafi muni da ta kai kan gaza tun bayan da ta sake komawa yakin tufanul Aksa, makonni biyu da suka gabata. Asbitin hukumar UNRWA ta MDD na daga cikin wuraren da yahudawan suka kai  hare-hare a garin a safiyar yau. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Asbitin na daga cikin wuraren da HKI ta kaiwa hari a jiya Laraba inda. Sannan a safiyar yau ta kashe mutane akalla 22 a kan cikin asbitin kadai sannan daga ciki har da yara, da mata da kuma jami’an yansanda na gaza. A jiya laraba kadai sojojin yahudawan sun kai hare-hare masu...
    Harajin kan motocin da ake shigo da su Amurka daga ƙasashen waje zai kai 25, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 12 na daren ranar Laraba. Shugaba Trump ya ce matakin na nufin kare tattalin arziƙin Amurka da muradun ‘yan ƙasarta. Ana sa ran ƙasashe kamar Tarayyar Turai, China, Japan, da Koriya ta Kudu za su mayar da martani cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’ar Bayero Ta Kaddamar da shirin amfani da adaidaita Sahu wajen zirga zirga a Jami’arA wani gagarumin yunkuri na bunkasa zirga zirga da walwalar dalibai, Shugaban Jami’ar Bayero Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya kaddamar da shirin amfani da babura masu kafa uku ko adaidaita a harabar jami’ar a hukumance. Wannan yunƙurin na nufin samar wa ɗalibai da ma’aikata hanyar sufuri mafi aminci, mafi dacewa, da sauƙaƙe ƙalubalen da ke tattare da zirga zirga tsakanin sassan jami’ar. Shugaban jami’ar wanda ya samu rakiyar magatakarda Haruna Aliyu da mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Haruna Musa da shugaban dakin karatu na jami’ar Dr. Kabiru Dahiru Abbas da shugaban hulda da jama’a na jami’ar Lamara Garba da Farfesa Yakubu Magaji Azare, Shugaban jami’ar ya...
    Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga har suka yi ƙarfi. Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Da yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da jiragen yaƙi marasa matuki da bama-baman da aka ƙera a Najeriya, wanda kamfanin Briech UAS ya samar, Mutfwang ya buƙaci haɗin gwiwa da kamfanonin fasahar tsaro na cikin gida. “Dole ne mu tabbatar da cewa babu wata ƙungiya da...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani matashi mai shekaru 27, Rabiu Suleiman, ya daɓa wa abokinsa Yunusa Muazu wuƙa, tare da yi masa mummunan rauni, a kan budurwa a yankin Gwagwalada da ke Abuja. Lamarin ya faru ne a daren Talata a wani gidan kallon fina-finai a Unguwar Dodo. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Suleiman ya zargi Muazu da yin soyayya da budurwarsa wadda yake shirin Jamila Yakubu. Faɗan ya fara ne lokacin da Suleiman ya samu Jamila da Muazu suna tattaunawa a gidan kallon fina-finan. Suleiman, ya fusata lokacin da ya ga Jamila tare da abokinsa, sai ya tafi kai-tsaye ya hau abokinsa da duka. A lokacin da suke...
     Wakilan kungiyar tarayyar Afirka sun isa birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu, a kokarin da suke yi na shiga tsakanin hana komawa yakin basasa. Tarayyar Afirkan ta fara kokarin shiga tsakani ne, bayan daurin talala da aka yi wa mataimakin shugaban kasa Riek Machar a gidansa,lamarin da ya sake jefa kasar cikin zaman dar-dar. Gwamnatin Salva Kir tana zargin Machar da cewa yana rura wutar wani sabon yaki a cikin kasar. A ranar Laraba ta makon da ya shude ne dai aka yi wa mataimakin shugaban kasar daurin talala a gidansa saboda fadan da ake yi a yankin Upper Nile tsakanin sojojin gwamnati da kuma masu dauke da makamai na rundunar “White Army”. A lokacin yakin basasar da kasar...
    Gwamnatin Afirka Ta Kudu ta sake jaddada azamarta ta bibiyar HKI a kotun duniya ta manyan laifuka akan laifukan kisan kiyashi da ta aikata a Gaza. Gwamnatin ta Afirka ta kudu, ta kuma yi watsi da duk wani matsin lamba da Amurka yake yi ma ta domin tilasta ma ta, ta ja da baya. Ministan alakar kasashen waje da aiki tare, Ronald Lamola wanda ya yi Magana da ‘yan jaridar kasar tasa, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi kasar ta janye karar da ta shigar a gaban kotun kasa da kasa ta manyan laifuka. Haka nan kuma ya ce; Neman yardar Amurka ba shi ne aikin da Afirka ta Kudu ta sanya a gaba ba, abinda yake gabanta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce jiragen yakin HKI sun kai hari a garin “Naqura” dake kudancin Lebanon da safiyar yau Alhamis. Jiragen yakin na ‘yan sahayoniya sun kai harin ne har sau uku ajere akan wata tsohuwar cibiyar kiwon lafiya dake cikin garin, haka nan kuma akan wasu gudajen mutane da suke a kusa. Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan asarar rayuka sanadiyyar wadannan hare-haren na’yan sahayoniya. A shekaran jiya Talata ma dai sojojin na mamaya sun kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beirut hari wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama da kuma jikkata wasu. Hari na shekaran  jiya shi ne irinsa na biyu a cikin unguwar Dhahiya tun bayan tsagaita wutar yaki. Haka nan...
    Da marecen jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan biranen Damascus, Hums,  Dar’ada Humah. Tashar Talabijin din ‘almayadin’ wai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta bayyana cewa; An kai harin ne akan wata cibiyar bincike a yankin Barzah dake arewacin birnin Damascus. Wata majiyar asibiti ta shaida wa tashar talabijin din ta almayadin cewa, an sami wadanda su ka jikkata. A garin Humah, jiragen yakin na HKI sun kai wasu hare-haren har sau 10, sannan kuma jiragen sun dauki lokaci mai tsawo suna shawagi a samaniyar birnin wanda ya yi sanadiyyar harin. A birnin Hums, kafafen watsa labarun yankin sun ce an ji karar fashewar abubuwa masu karfin gaske a kusa da filin saukar jiragen sama...
    Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su. Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar. Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya kai shekara 40 ko sama da haka, zai iya tuna irin tarbiyyar da ya samu daga iyayensa a baya, da kuma yadda alaƙar da ke tsakanin yara da iyaye ta ke cike da girmamawa, kulawa, da soyayya. A yau, abubuwa sun canza sosai. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu Yawancin iyaye na fuskantar ƙalubale iri-iri, musamman yadda nauyin rayuwa ke ƙaruwa a kansu. Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka samu shi ne yawaitar mata masu aiki, ko dai a gwamnati ko a kamfanoni masu zaman kansu. Wannan sauyin yana iya shafar irin...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanin kowa ne, ciniki mai inganci na bukatar kasuwa mai ‘yanci, da takarar da ake yi cikin daidaito, gami da manufa mai dorewa. Idan kasar Amurka ta ki samar da wadannan abubuwa, to, babu wani abun da za a yi, in ban da mai da kasar saniyar ware, da kara tabbatar da hadin kai tare da sauran abokan hulda. (Bello Wang)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su.   Ya kara da cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a kara musu kudin fansa, amma hakan ba ta yi wu ba.   Wata majiya mai tushe ta sojoji ta kuma tabbatar da sakin Tsiga. Majiyoyi na kusa da dangin sun ce yana cikin koshin lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga. An sace Janar Tsiga, wanda Tsohon Shugaban Hukumar NYSC ne, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025. Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Hakazalika, aharan sun sace mutum tara a tare da shi a lokacin da suka kai harin. Duk da cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa, ’yan bindigar sun ci gaba da tsare shi na tsawon makonni. Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a san adadin kuɗin da aka biya a matsayin kuɗin fansar ba. Wasu sun ce Naira...
    A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama. Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano. Kano, jiha ce da hamayyar siyasa da rikicin masarauta ya dabaibaye ta. Akwai hamayyar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyun NNPP mai mulki a jihar da takwararta ta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai. Da yake amsa...
    Shugaba Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin babban ginshikin masarauta kuma mai neman ci gabanta.   Shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kano da majalisar masarautar Kano da kuma iyalan marigayin bisa wannan rashi mara misaltuwa.   Shugaban ya yi addu’ar Allah ya sa Jannatul Firdaus, ta zama makoma ga Galadima. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sojojin kasar na karbe iko da wasu yankunan zirin Gaza, a wani mataki na kara matsin lamba kan kungiyar Hamas domin tilasta ta sakin mutanen da ta ke garkuwa da su. “Muna karbe zirin Gaza tare da kara matsin lamba mataki-mataki domin tilasta su mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su,”inji  Netanyahu a wani faifan bidiyo da ofishinsa ya fitar. Ya kara da cewa, Sojoji na karbe yankuna, suna kai farmaki kan ‘yan wadanda ya danganta da ‘yan ta’adda in ji shi, yana mai sanar da samar da wata sabuwar hanya karkashin ikon Isra’ila don raba garuruwan Khan Younis da Rafah (kudu). Tunda farko dama ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya...
    Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) mai hedkwata a birnin Hague ta yi Allah-wadai da matakin da kasar Hungary ta dauka na kin mutunta sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da zai ziyarci kasar da ke tsakiyar Turai a ranar Alhamis. Mai magana da yawun kotun, Fadi El Abdallah, ya fada yayin wani taron manema labarai cewa, bai kamata mambobin kotun ICC su yi watsi da hukuncin kotun ba. Kakakin ya ci gaba da cewa dole ne mambobin kotun su aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke. Ana sa ran Netanyahu zai isa Budapest a yammacin yau Laraba don ziyarar kwanaki hudu, bisa gayyatar Firaministan Hungary Viktor Orbán. Shugaban na Hangari mai tsatsauran ra’ayi ya gayyaci takwaransa...
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in ji Araghchi a wata wayar tarho da takwaransa na Holland, Caspar Veldkamp, yau Laraba. Ya jaddada cewa wannan “yana bukatar yanayi mai kyau da kuma nisantar hanyoyin da suka shafi barazana.” Ministan ya yi Allah wadai da barazanar da jami’an Amurka suka yi wa Iran da cewa “ba za a amince da su ba”, ya kara da cewa sun saba wa kundin tsarin mulkin MDD...
    Gwamnatin Nijar ta saki kusan mutane 50 da suka hada da ministocin da aka tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023. Baya ga tsaffin ministocin da akwai wasu sojoji da ake zarginsu da yunkurin juyin mulki a shekarar 2010 da suma aka sake su.  “An sako wadannan mutane ne bisa ga shawarwarin da babban taro na kasar ya bayar,” kamar yadda sakataren gwamnatin kasar ya karanta a gidan talabijin din kasar a cikin daren jiya. Cikin tsaffin ministocin da aka saki har da tsohon ministan man fetur Mahamane Sani Issoufou, dan tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou, da kuma tsohon ministan tsaro Kalla Moutari, da tsohon ministan kudi Ahmat Jidoud, da kuma tsohon...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun daga ranar 1 ga watan Afrilu, dakarun rundunar sojojin ’yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar ta kaddamar da atisayen hadin gwiwar rukunoni masu kunshe da sojojin kasa, da na ruwa, da na sama da dai sauransu a kewayen tsibirin Taiwan. Atisayen da ya kasance wani salo na jan kunne mai karfi ga mahukuntan gwamnatin Lai Ching-te dake rajin “’yancin kan Taiwan”, kana mataki mai karfi da ya wajaba na kare ikon mulkin kai da cikakkun yankunan kasar Sin. Kamar yadda aka sani, Taiwan wani sashe ne na kasar Sin, wanda ba ta taba zama kasa ba, kuma ba zai taba zama ba a nan gaba. Sunan yankin Taiwa a MDD shi ne “Lardin Taiwan...
    Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda yake ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki a Kano. Alhaji Sunusi, ya rasu yana da shekaru 92 bayan fama da doguwar rashin lafiya. Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin Musulunci Ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama, ciki har da Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora nagari da ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin gargajiya. Ya ce gudunmawar da ya bayar za a ci...
    A lokacin da yake wurin, Kefas ya shaida wa masu ababen hawa da matafiya cewa, gwamnatin jihar za ta samar musu da wata hanyar da za su amfani da ita kafin a kammala gyaran gadar, alkawarin da har yanzun bai cika ba, ga kuma wani mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Talata, wanda ya wanke gadar wucin gadi da mutanen yankin suka gina a matsayin madadi.   Wakilin LEADERSHIP a wurin gadar da sanyin safiyar Larabar nan, ya gano cewa, hanyar wucin gadi da mazauna kauyen suka gina, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren ranar Talata ya wanke ta, lamarin da ya sa masu ababen hawa da matafiya suka makale a gaɓar...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16. Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano. Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Barau ya gana da iyalan mamatan a Masallacin At-Taqwa da ke Bunkure a ranar Laraba tare da Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da sauran manyan jami’ai. Barau, ya yi ta’aziyya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci. “Na zo nan ne domin na taya ku jaje kan...
    Karin harajin kwastam na iya haifar da yakin kasuwanci. Kasashen da wannan harajin ya shafa za su iya mayar da martani, lamarin da ka iya haifar da rudanin da zai cutar da kasuwancin duniya. Wannan na iya haifar da karin farashin kayayyaki, sallamar ma’aikata daga aikinsu, dakile hanyoyin samar da kayayyaki, da takaita ci gaban tattalin arziki a duniya. Don haka, ana kyautata tsammanin cewa, wannan sabon tsarin harajin zai sake fasalin yanayin kasuwanci a duniya, ganin cewa, wasu masana’antu za su fuskanci tsadar kayayyaki da kuma durkushewar hanyoyin samar da kayayyaki.       Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 13 da suka ɓace yayin wani hatsarin jirgin ruwa a Jihar Bayelsa. Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi. HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — Jamus Masu nutso a ruwa sun fara ƙoƙarin ceto waɗanda suka ɓace. Bayanai sun nuna cewar wani jirgi mai suna ‘Meeting Marine’ wanda ya taso daga Anyama Ijaw zuwa Lubia da Foropa ya yi karo da jirgin kamun kifi. Jirgin na da injin 115HP kuma wani mutum da ake kira Saturday ne yake tuƙa shi. Shugaban...
    An yi jana’izar marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi, a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, inda dubban jama’a suka halarta. Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, sun halarci jana’izar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi. Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin Musulunci Tinubu zai tafi ziyarar makonni biyu a Faransa An gudanar da sallar jana’izar ne a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu, inda Farfesa Sani Zahradden ya jagoranci sallar. Dubban jama’a ne suka halarci jansiza5 marigayin. Har ila yau, Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ya halarci jana’izar. Marigayi Alhaji Abbas Sunusi, ya rasu ne a daren ranar...
    Wani basakkwace, Musa Abubakar, wanda a bayan nan ya yi ridda saboda zullumin ’yan bindiga masu kai hare-hare da ta’adar garkuwa da mutane, ya sake karɓar addinin Musulunci. A ranar Asabar ce mutumin tare da matansa biyu suka sake karɓar addinin Islama bayan  ridda da suka yi a kwanan baya. Tinubu zai tafi ziyarar makonni biyu a Faransa Kisan Mafarauta: Babu wanda aka kai wa harin ramuwar gayya a Kano — Ƙungiyoyin Matasa Bayanai sun ce Musa Abubakar ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Sakkwato ya yi ƙaura zuwa Jihar Taraba a sakamakon yanayin tsaro a mazauninsa. Bayan komawa Taraba ne kuma ya shawarci matansa uku da su  karɓi addini Kiristanci, kuma ya yi nasara biyu suka amince....
    A wannan Larabar Shugaban Kasa Bola Tinubu zai tafi ziyarar aiki ta makonni biyu a ƙasar Faransa. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce a yayin ziyarar shugaban ƙasar zai yi bitar ƙwazo da nasarorin da gwamnatinsa ta samu.
    Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi wa Hausawa kuma tana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Kazalika, ƙungiyoyin sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa koƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da ɗorewa a jihar ta hanyar ɗaukar...
    Haka kuma, yana shirin gina masana’antar sarrafa itace da samar da sabbin hanyoyin ruwa domin rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa na Apapa da Lekki. Wannan jari ya zo ne a daidai lokacin da Kamaru ke faɗaɗa tashar jiragen ruwa na Kribi domin ƙara inganta kasuwanci a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jamus ta ce tana ci gaba da samun galaba na daƙile kwararar baƙin haure masu shiga ƙasar tare da mayar da wadanda aka yi watsi da takardunsu na neman mafaka zuwa inda suka fito. Ministar harkokin cikin gida ta Jamus, Nancy Faeser, ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar mai barin gado ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile shigar baƙin haure cikin ƙasar. Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta Faeser ta ce gwamnatin na ci gaba da daukan matakin mayar da baƙin haure ƙasashen da suka fito, inda yanzu haka aka samu raguwar masu ajiye takardun neman mafaka a ƙasar, mafi ƙarfin tattalin arziki tsakanin ƙasashen Turai. Faeser ta...