2025-04-26@09:18:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 76

«da demokuradiyya»:

    Gwamnan ya bayyana cewa ba za a yi amfani da kudin al’umma ba ga mutanen da ba za su iya kula da mahajjata yadda ya kamata ba.   Gwamna Radda ya kara da cewa ya yi taro da shugabannin kananan hukumomi guda 34 domin tabbatar da cewa malaman da suka cancanta ne kadai aka zaba a matsayin masu koyarwa a ayyukan aikin hajjin bana.   Ya kuma yi alkawarin kafa kwamitin yada labarai domin yada ayyukan aikin hajjin tare da ba da kulawa ta musaman kan shawarwarin da aka bayar kan rahoton da kwamitin aiki hajjin ya gabatar.   Da yake gabatar da rahoton, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Katsina kuma Amirul Hajj, Alhaji Tukur, ya bayyana wasu muhimman batutuwa da...
    Li ya kara da cewa, Sin da Rasha sun bayyana goyon baya ga Iran wajen karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da hukumar IAEA. (Mohammed Yahaya)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Irin wannan zanga-zangar, ta sha ban-ban, da irin wadda ake gudanawar a kasashen da suka ci gaba kuma suke gudanar da mulki, irin na Dimokiradiyya, kamar da kasar Amurka, Birtaniya, Isara’ila da sauransu.   Sashe na 40, na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, ya bai wa ‘yan kasar ikon haduwa a waje guda su kuma yi hudda da sauran jama’a.   Kazalika, sashe na 11 na yarjejeniyar nahiyar Afirka, da ke magana kan ‘yancin ‘bil’Adama, wanda ita kanta Nijeriya ta rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar na barin ‘yan kasar su gudanar da zanga a cikin lumana.   Amma sai dai, abin takaicin duk da ‘yancin na wannan sashen, mahukunta Nijeriya, suna yawan take wannan ‘yancin, kan...
    Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a cikin yankunan Siriya, a cikin abin da gwamnatin Isra’ila ta kira “yankin da ke da kariya,” wanda ya hada da mamaye wasu sassan garuruwan Quneitra da Dara’a. Majiyoyin cikin gida a garin Nawa da ke cikin karkarar Dara’a na cewa, mahukuntan kasar Siriya na ci gaba da daukan matakan matsin lamba, ta hanyar shugabannin kabilu da kwamandojin ma’aikatar tsaro a Dara’a, na tilastawa bangarorin da...
    Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata cewa adadin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata tun ranar 18 ga Maris, shekara ta 2025 ya kai shahidai 1,890 da kuma jikkata wasu 4,950 na daban. An tabbatar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a sakamakon harin ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa shahidai 51,266 da jikkatan wasu 116,991 tun daga ranar 7 ga...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya mika ta’aziyya game da  rasuwar shugaban ‘yan darikar katolika na duniya Paparoma Francis. A wani sako da ya aike a jiya Litinin, Pezeshkian ya ce Paparoma Francis a matsayinsa na shugaban darikar Roman Katolika ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yada koyarwar Yesu Almasihu. Shugaban ya ce Paparoma ya yi kokari wajen samar da zaman lafiya a duniya, da yekuwar samar da adalci, da ‘yanci, da mu’amala da tsaro a tsakanin addinai. Daya daga cikin shi ne bayyanannen matsayinsa na yin Allah wadai da kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza da kuma kiran da ya yi na kawo karshen kisan kiyashin da ake yi wa mata da kananan yara Falasdinawan...
    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya NDLEA, ta yi nasarar kama hodar iblis wadda aka ɓoye a cikin littattafan addini da ake shirin kaiwa Saudiyya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Hukumar NDLEA ɗin ta fitar a ranar Lahadi. Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas Hukumar ta bayyana cewa ta kama ɗauri 20 na hodar iblis ɗin wanda jimillar nauyinsu ya kai giram 500 a cikin littattafan addini. NDLEA ta ce jami’anta sun gano hodar ne a yayin da suke gudanar da bincike a wani kamfanin da ke jigilar kayayyaki a Legas a ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, yayin da yake shirin kai...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna adawa da fadada dangantakar Iran da Saudiyya Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da ministan tsaron Saudiyya Khalid bin Salman a jiya Alhamis. A yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, alakar da ke tsakanin Iran da Saudiyya za ta kasance mai amfani ga kasashen biyu, kuma kasashen biyu za su iya taimakawa juna. Imam Khamenei ya yi nuni da cewa, akwai makiya da suke adawa da fadada alaka a tsakanin kasashenmu biyu, kuma wajibi ne a shawo kan wadannan munanan manufofin, kuma a shirye Iran take ta yi hakan. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi ishara da ci...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta tsakiya Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar dogaro da karfinsu a hade ba tare da bukatar shiga tsakani daga kasashen waje ba. Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya tarbi ministan tsaron kasar Saudiyya Khalid bin Salman a yammacin jiya Alhamis, wanda ke ziyarar aiki a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dauke da wata babbar tawagarsa. Shugaban na Iran ya jaddada cewa Iran ta kuduri aniyar karfafa alakar ‘yan uwantaka a tsakanin kasashen musulmi. Pezeshkian ta kara da cewa: Saboda wata wasiyya ta...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Tal al-Za’atar da ke gabashin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza. A cewar majiyoyin yankin, gidan da aka kai harin na dangin Nasiyo ne, kuma yana dauke da ‘yan gudun hijira daga iyalai sama da biyar a cikinsa, inda harin ya turbude su a karkashin baraguzan gine-gine.
    Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa, Iran a shirye take yin aiki tare da Saudiyya a dukkanin bangarori, domin cin gajiyar al’ummomin kasashen biyu da ma duniyar musulmi, tare da yin ishara da cewa, dukkanin ci gaban da Iran ta samu a dukkanin bangarori na ilimin kimiyya da fasaha, a shirye take ta taimaka ma  Saudiyya a wadannan bangarori. Wannan na zuwa ne a lokacin da Ministan tsaro Yarima Khalid bin Salman dan uwa ga Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya gana da Ayatollah Khamenei a Tehran da yammacin jiya Alhamis don mika sakon Sarki Salman na Saudiyya. Jagoran ya ce: “Mun yi imanin cewa dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiyya za su iya zama abin koyi ga hadin gwiwar yankin, yana mai jaddada cewa hadin kan kasashen musulmi wani lamari ne da ake bukata don samun zaman lafiya, tsaro, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa a yankin. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da ya yi da ministan tsaron kasar Saudiyya Yarima Khalid bin Salman da tawagarsa a birnin Tehran, bayan da ministan na Saudiyya ya isa babban birnin kasar Iran domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin da alakar kasashen biyu. Shugaban na Iran ya jaddada zurfafa dangantakar addini da al’adu da tarihi a tsakanin kasashen musulmi, yana mai jaddada wajabcin karfafa hadin...
    Iran ta jaddada shirinta na fadada huldar soji da kasar Saudiyya a wani bangare na batutuwan da ziyarar ministan tsaron kasar Saudiyya Tehran ta kunsa. Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri ya shaidawa Yarima Khalid bin Salman a Tehran a wannan Alhamis cewa “Kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da sojojinsu za ta kawo yanke kauna ga makiyanmu da kuma sanya farin ciki ga abokanmu da sauran musulmi”. Bagheri ya godewa Saudiyya a kan halartarta a matsayin mai sa ido a babban atisayen sojojin ruwa na tekun Indiya (IONS), wanda aka fi sani da IMEX 2024. Iran, Rasha, da Oman ne suka gudanar da atisayen a tekun Indiya, tare da halartar tawagogin masu sa ido...
    Rasha ta ce tana ta na sa ido sosai game da tattaunawa karo na biyu tsakanin Amurka da Iran kuma a shirye take ta taimaka wajen warware shirin nukiliyar Iran ta hanyar siyasa da diflomasiyya. Makomar shirin nukiliyar Iran da kuma zaman lafiyar yankin na iya danganta ne kan ko Washington da Tehran za su koma kan teburin shawarwari. Yayin da tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ta tsaya cik a baya, manyan kasashen duniya musamman Rasha da China sun yi yunkurin ganin neman farfado da tattaunawar ta diflomasiyya. Tunda farko a makon da ya gabata Majalisar Tarayyar Rasha ta amince da yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsawon shekaru 20 a hukumance da Iran, wanda ke karfafa kawancen dogon lokaci tsakanin kasashen...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja ta kaddamar da rabon sutura da jakunkunan hannu masu nauyin kilo 8 ga maniyyatan bana, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025. A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Shugaban Hukumar, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa rabon kayayyakin na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sauƙin tafiya da kuma aikin Hajji ba tare da wata tangarda ba ga maniyyatan jihar. Shugaban wanda Daraktan Gudanarwa, Babani Aliyu Yahaya, ya wakilta a yayin bayar da kayan ga Jami’in Alhazai na Ƙaramar Hukumar Chanchaga, ya ce kayayyakin na maniyyatan  da suka kammala biyan kuɗin kujerunsu ne. Daraktan Gudanarwar ya kuma yi kira ga waɗanda har yanzu ba su...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki a Gaza, zai yi tasiri ga wadanda ke tunanin shiga cikin sahunsu. Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoto ga rundunar ‘yan sandan birnin Landan ne mai kunshe da shaidun da suka shafi ‘yan Birtaniya guda 10 da suka yi aikin soja karkashin rundunar mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai...
    A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Indonesia, Prabowo Subianto suka yi musayar taya juna murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Inda shugaba Xi ya ce, yana dora matukar muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Indonesia, kuma a shirye yake ya yi amfani da bikin cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, a matsayin wata dama ta yin aiki tare da shugaba Prabowo, wajen kara zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da karfafa hadin gwiwa a batutuwan da suka shafi bangarori daban daban bisa manyan tsare-tsare, da ci gaba da inganta al’ummar Sin da Indonesiya mai kyakkyawar makomar bai daya daga dukkan fannoni, kuma...
    Ya soki masu ra’ayin cewa dimukradiyya wani sharadi ne na ci gaba, yana mai cewa “karya ne” shi akwai wata kasa da ta ci gaba a karkashin tsarin dimukradiyya?. Burkina24 ta nakalto cewa “Babu wata kasa da za a iya bayyanawa da ta ci gaba a dimukradiyya. Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sadarwa, bayyanawa, da kuma fahimtar da mutane mene ne juyin juya hali. Traore ya yi fice wajen yanke shawarar ce bayan hayewarsa a matsayin shugaban kasar da ke yammacin Afirka. Shugaban mai shekaru 37 da haihuwa wanda ya hau karagar mulki a watan Satumban 2022 ta hanyar juyin mulkin da ya hambarar da shugaban kasar na wucin gadi Paul-Henri Damiba kwanan nan...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baqaei ya bayyana cewa, ma’a, kwana guda gabanin tattaunawar da ake jira a kasar Oman tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliyar kasar Iran, damammaki da daman a diflomasiyya da Amurka za ta iya tabbatar da aniyarta a kansu Baqaei ya rubuta a dandalin  X, “Ya kamata Amurka ta mutunta wannan shawarar da aka yanke duk da cewa ana fama da rikici.” “Ba za mu yanke hukunci ba, Muna da niyyar tantance niyyar dayan bangaren kuma za mu tabbatar da hakan a wannan Asabar,” in ji jami’in diflomasiyyar na Iran, ya kara da cewa Iran “za ta yi tunani kuma ta mayar da martani ga kowane mtaki.” A ranar Litinin shugaban Amurka Donald...
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga kasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a kasar har...
    Haka kuma, an gargaɗi kamfanonin da ke da alhakin kawo mutane Umrah cewa idan suka ƙi bayyana sunayen waɗanda suka ƙi dawowa gida, za a ci su tara har riyal 100,000. Ma’aikatar ta buƙaci kowa ya bi doka domin guje wa hukunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 30 a Kongo Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga ƙasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma’aikatar ta...
    Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa  ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza. Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta yawon buɗe idanu. Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas “Rashin yin biyayya ga wannan tsarin ka iya jawo haramta shiga kasar sawon shekaru biyar” a cewar sanarwar. Sai dai Cibiyar yawon buɗe ido ta Saudiyya ta bayyana wa manema labarai cewa waɗannan sabbin dokokin sun takaita ne ga lokacin aikin hajji....
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana sharuddan da Tehran ta gindaya na ci gaba da tattaunawa kan shirinta na nukiliya, yana mai jaddada aniyar kasar ta fuskar diflomasiyya tare da tsayawa tsayin daka kan muradun kasa. Da yake magana a wani taron sabuar shekarar Nowruz tare da jami’an Iran, jakadu, da wakilan kasa da kasa a daren ranar Asabar, Araghchi ya jaddada daukar nauyin Iran kan harkokin duniya. Ya lura cewa martanin Iran ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump an yi shi ne don dacewa da sauti da kuma abin da ke cikin saƙon na asali, ta hanyar buɗe hanyoyin diflomasiyya. Araghchi ya yi nuni da cewa, yin cudanya kai tsaye da jam’iyyar da ke ci gaba da...
    Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce Iran ba ta neman yaki da kowace kasa, amma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kanta saboda tana da kyakkyawan shiri a kan hakan. Da yake magana a wata tattaunawa ta wayar tarho da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta shiga yin shawarwari don warware wasu matsaloli, bisa maslaha da mutunta juna, inda ya kara da cewa: “Ba ma neman yaki da wata kasa, amma ba mu da wani shakku wajen kare kanmu, kuma mun riga mun shirya tsaf dangane da hakan.” Shugaba Pezeshkian ya mika sakon taya murna ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya,...
    Ya kara nuna shakku kan dalilin da ya sa aka kafa dokar ta-baci a Jihar Ribas, yana mai cewa rashin tsaro ya addabi wasu sassan kasar nan, amma ba a kakaba dokar ta-baci ba ko kuma wani abu makamancin haka. “Idan shugaban kasa ya ce saboda rashin tsaro ne, saboda sun fasa bututun mai, yaya batun sassan kasar da ake fama da rashin tsaro? Shugaban kasar yana cewa su ma su kafa masa dokar ta-baci a kansa. Ba za su iya ba, saboda shi shugaban kasa ne da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, babu wanda zai iya sanya masa dokar ta-baci, saboda akwai rashin tsaro mai tsanani a arewa maso gabas, arewa maso yamma, hatta a kudu maso gabas da...
    Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hango jinjirin watan Shawwal, wanda ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadana. Shafin Haramain ne ya ruwaito hakan, bayan daukar awanni ana neman wata. Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar karamar Sallah a kasar ta Saudiyya.
    Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin ɗaukar matakin da ya dace bisa doka. Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo Bidiyon, wanda ya bayyana a ranar Juma’a, ya nuna matar tare da wata ƙawarta suna tunkarar wajen da aka kange, inda jami’an tsaro suka hana su wucewa. Sai dai matar ta fusata, tare da marin ɗan sandan,...
    A zantawa ta water tarho ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Turkiya sun bukaci kasashen musulmi su magance matsalar jinkai da kayakin agaji na Falasdinawa a kasarsu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Hakan Fidan na kasar Turkiya da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi suna fadar haka a jiya Litinin. A lokacinda yake Magana a kan rikicin da ke faruwa a kasar Turkiyya Abbas Aragchi ya bayyana cewa, rikici ne na cikin gida, kuma yana fatan gwamnatin kasar zara iya magancece ta yadda ta ga ya dace, kuma yana da imani zata iya magance matsalar. Aragchi ya kara da cewa, wannan shi ne matsayin iran a cikin al-amuran da ke faruwa a...
    Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a ranar Litinin. Hukumomin Rasha sun ruwaito cewa fadar White House da Kremlin za su fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Talata kan tattaunawar da suka yi, wanda Moscow ta bayyana tun da farko a matsayin “mai wuyar gaske.” Tattaunawar yanzu tana mai da hankali kan yiwuwar tsagaita wuta a tekun Black Sea, domin ba da damar komawa kan yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsin da yake da muhimmanci ga samar da abinci a duniya. Ministan tsaron Ukraine Rustem Umerov ya bayyana ganawar da suka yi da Amurkawa a ranar Lahadi a matsayin...
    Ya kuma kara da cewa dorewar tsarin dimokiradiyya na bukatar hadin gwiwa daga kowane bangare, “Jam’iyyun siyasa su ne ginshikin dorewar dimokiraɗiyya, kuma yayin da hamayya take da muhimmanci a lokacin zabe, dole ne mu hada kai wajen gina kasar mu, hakan ya sa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda babban jami’in dimokiradiyya ne yake mutunta gasa mai tsafta, amma kuma ya na fifita hadin kai da ci gaban kasa fiye da komai. Shugaban IPAC na kasa, Honourable Yusuf Dantalle, ya ce shirin fim din na tarihi zai bayyana ci gaban da aka samu a fannonin gina ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da hadin kan al’umma, ya kuma ci gaba da “Fim din zai zama wani muhimmin tarihin kasa,...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya fada ya bayyana a wannan Laraba cewa ya yi tattaunawa mai kyau” da Volodymyr Zelensky, washegarin da ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin. Ya kara da cewa tattaunawar ta yi armashi yayin da Amurka ke yunkurin tsagaita wuta a Ukraine. “Na yi magana da shugaban Ukraine Zelensky, ta dauki kusan awa daya, kuma galibin tattaunawar ta ta’allaka ne kan kiran da suka yi da shugaba Putin na jiya domin daidaita batun kasashen Rasha da Ukraine, kuma  “Muna kan hanya madaidaiciya,” inji shugaban na Amurka a shafinsa na True Social Network. Tunda farko dama wakilin Amurka Steve Witkoff ya bayyana a ranar Talata bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Donald Trump da takwaransa...
    Iran ta ce za ta fifita diflomatisyya ta tsakaninta da kasashe makobtanta na yankin. Ministan harkokin wajen kasar ne Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar kan harkokin diflomasiyya a yankin, yana mai bayyana cewa kasashen da ke makwabtaka da kasar na cikin tsarin Jamhuriyar Musulunci. “Makwabtanmu sune fifikonmu,” in ji ministan harkokin wajen Iran a cikin wani sako da aka wallafa a shafinsa na X. Mista Araghchi ya tattauna da takwarsana na Omani, Badr bin Hamad Al Busaidi, a Muscat, babban birnin kasar Omani, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu da na shiyya-shiyya. Babban burinmu shi ne kare zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar diflomasiyya. Ziyarar ta Araghchi a birnin Muscat na zuwa ne a...
    Shugaban kasar Angolan João Lourenço, wanda kuma shi ne ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka (AU) ya yi kira ga gwamnatin Congo Democradiyya da mayakn M-23 su kawo karshen yaki kafin taron tattauna batun tsagaita wuta a gabacin kongo nan gaba. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afirca News” ya nakalto shugaban yana kira ga bangarorin biyu su tsagaita wuta da misalign tsakiyar daren jiya Lahadi don a tattauna batun samar da zaman lafiya cikin Nutsuwa. Majiyar fadar shugaba Lourenco na cewa yakamata tsagaita wutan ya hada har da rashin kokarin mamayar karin iko a wasu wurare. Da kuma dakatar da fada. Da kashe fararen hula da sauransu. An shiya cewa gwamnatin kongo Democradiyya da kuma wakilan yan...
    Kalmar demokuradiyya kalma ce da jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te ke yawan ambata, amma aikin da ya yi bai bi hanyar demokuradiyya ba. A baya-bayan nan, Lai Ching-te ya gabatar da wani shirin neman ‘yancin kan Taiwan, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokuradiyya ce mai mulkin kanta. Lai Ching-te ya kan yin amfani da demokuradiyya don ya cuci jama’ar yankin Taiwan da sauran kasashen duniya, amma a wannan karo kowa ya san yunkurinsa na neman mulki irin na kama karya ta hanyar demokuradiyya. Ya kamata a yi amfani da demokuradiyya don tabbatar da hakkin jama’a, a maimakon kawo illa ga hakkin jama’a. Jama’ar yankin Taiwan suna neman zaman lafiya, da samun ci gaba, da yin mu’amala,...
    Shi ma, Manajan Darakta na CDI, Roland Oroh, ya goyi bayan wannan ra’ayi na Dakta Anyebe Idoga, inda ya sanar da cewa; wannan aiki, zai kara karfafa karfin Nijeriya wajen fitar da kaya zuwa ketare. “Mun ji dadi kan fara wannan yarjejeniya da mu, domin wannan zuba hannun jari, zai taimaka wa Nijeriya wajen kara habaka fitar da ingantaccen nama zuwa ketare”, in ji Oroh. Kazalika, an bijiro da wannan hadaka ce, sakamakon yadda Saudiyya ta nuna sha’awarta, na son shigar da nama zuwa kasarta daga Nijeriya, wanda ya kai tan 176,000 a duk shekara, tare da kuma ciyawar dabbobi ta alfalfa hay da abincin dabbobi da ake sarrafawa da kuma Waken Soya. A yanzu haka, CDI na ci gaba...
    “Muna kokarin kawar da bangaren dala. Abin da muke so mu yi shi ne mu biya a cikin kudin gida na duk kamfanonin jiragen sama. Kuma za a biya kudin ne daidai da farashin dala a halin yanzu a lokacin da ake biya. “Kason da ya dace ya ba ku damar gudanar da ayyukanku dukkan ne za a biya ku, bayan kammala aikin za a karasa biyanku sauran,” ya shaida. Tun da farko, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya ce, ayyukan jirage na sufuri na daga cikin muhimman ayyukan da ke gabansu wajen sauke nauyin aikin hajji. “Lamarin na bukatar kwarewa matuka gaya da kuma himma da azama. Wannan lamarin ba kawai ga batun sufuri ba ne, ya shafi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas. Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar...
    A nata ɓangaren, Amurka ta ce za ta yi amfani da wannan dama don fahimtar matsayin Ukraine kan kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin ta da Rasha. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni. Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump. Tun bayan...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministocin harkokin wajen Iran da Saudiyya sun tabbatar da aniyar kaasashensu na ci gaba da kara azama domin bunkasa alakoki a tsakaninsu a dukkanin bangarori. Wannan dai na zuwa ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Saudiyya Faisal bin Farhan suka yi ne a wannan Juma’a a gefen taron gaggawa karo na 20 na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Jeddah. A yayin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan matsayin dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma masarautar Saudiyya, tare da jaddada aniyar kasashen biyu na ci gaba da fadada hadin gwiwa tsakaninsu. Bangarorin biyu sun kuma yi nazari...
    Shugaba Zelensky   na Ukiraniya zai kai ziyara kasar Saudiyya a ranar Litinin, gabanin bude tattaunawar da za a yi tsakanin kasarsa da kuma Amurka da zummar kawo karshen yaki da Rasha. Shugaban na kasar Ukiraniya ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa; Manufar ziyarar tashi ita ce haduwa da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, sannan kuma tawagar da zai je da ita, za ta ci gaba da zama a can Saudiyya din saboda yin aiki tare da mutanen Saudiyya da kuma Amurka.” Zelensky ya kara da cewa; Kasarsa Ukiraniya tana son ganin an sami zaman lafiya mai dorewa. Bugu da kari shugaban na kasar Ukiraniya ya ce; Matakin farko da kasarsa ta gabatar a matsayin shawarar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tafi kasar Saudiyya domin halartar taron ministocin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, domin tattauna matakan da za a dauka na tinkarar shirin Amurka na tilastawa mutanen Gaza gudun hijira. A yammacin ranar Alhamis ne Araghchi ya tashi zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiyya inda za a gudanar da taron a yammacin ranar Juma’a, in ji ma’aikatar harkokin wajen Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce Iran ta bukaci taron ne domin jawo hankalin kungiyar OIC, a matsayinta na babbar kungiya a duniyar musulmi, kan batun da ya shafi al’ummar musulmi da kasashen musulmi. Shirin shugaban Amurka Donald Trump na raba Falasdinawan Gaza da kasarsu ta asali...
    Tsohon Gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya musanta cewa akwai wata ƙullaliyar gaba tsakaninsa da tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikinsu da za a iya ɗora wa alhakin haddasa saɓanin siyasar da ya shiga tsakaninsu a baya. Cikin wani bidiyo da karaɗe dandalan sada zumunta, Shekarau ya bayyana cewa rashin jituwar da ke tsakaninsu na siyasa ya samo asali ne daga yanayi da ya fi ƙarfinsu gaba ɗaya. “Gaskiya ni na yi imanin cewa ni da Kwankwaso ba mu da wata matsala ta zama tare a ƙarƙashin inuwar jam’iyya ɗaya. A duk abubuwan da suka faru, da ni da shi duk babu mai laifi,” inji shi. Da yake tsokaci kan lokacin da suka...
    Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar. A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi. Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar za su cika domin samun gudanar da ibadar a kwanaki 10 ma ƙarshen watan Ramadan a masallatan Haramin Makkah da Madina da sauransu masallatan ƙasar. Bayanan da ake buƙata sun hada da: Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan MDD ta taya Musulmi murnar zuwan watan Ramadan 1- Ƙasar mutum: Ta asali...
    Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar. A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi. Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar za su cika domin samun gudanar da ibadar a kwanaki 10 ma ƙarshen watan Ramadan a masallatan Haramin Makkah da Madina da sauransu masallatan ƙasar. Bayanan da ake buƙata sun hada da: Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan MDD ta taya Musulmi murnar zuwan watan Ramadan 1- Ƙasar mutum: Ta asali...
    Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Jihar Kano, ya bai wa jihar da wasu jihohin Arewa kyautar dabino katan 1,250, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafin Ramadan na kowace shekara. Wannan shiri na cikin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarki Salman (KSrelief), ke gudanarwa don tallafa wa masu buƙata da kuma ƙarfafa dangantakar Saudiyya da Najeriya. Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2025 na N54.99trn Yayin bikin rabon dabinon, Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Admawy, ya gode wa Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima Mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa ƙoƙarinsu na ci gaba da tallafa wa al’ummar Musulmi a faɗin duniya. Ya jaddada aniyar Saudiyya na ci gaba da...
    Hukumomi a Ƙasar Saudiyya, sun tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin yau Juma’a. Hakan na nuni da cewa azumin bana zai fara a ranar Asabar, 1 ga watan Maris, 2025. Shafin Haramain Sharifain ne, ya tabbatar da wannan sanarwa, yayin da aka ga jinjirin watan a wurare daban-daban na ƙasar. Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano Wannan na nufin cewa Musulmai a Saudiyya za su fara azumi a ranar Asabar. Hakazalika, ƙasashen Qatar da Oman sun sanar da cewa za su fara azumin Ramadan a wannan ranar Asabar. A yayin da ake shirin shiga wannan wata mai alfarma, an yi kira ga Musulmai...
    Kasashen Iran da kuma Saudiyya sun tattauna kan halin da ake ciki a yankin dama batun taron kungiyar kasashen Musulmi ta OIC da za’ayi a cikin kwanaki masu zuwa a Jeddah. Tattaunawar ta wakana ne ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan da Abass Araghchi, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran (RII). A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan halin da ake ciki a yankin, tare da tattauna taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar OIC da za a yi a Jeddah. Dama a kwanan baya bangarorin sun tattauna kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na kwace zirin Gaza dama tilasta wa falasdinawan yankin kaura zuwa Masar da Jordan, shirin da dukkan kasashen...
    Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa tasirin dimokuradiyya a Afirka ta Yamma na raguwa saboda rashin shugabanci nagari. Da yake jawabi a Abuja ranar Talata a matsayin babban mai jawabi a wani taro mai taken, “Mahanga kan makomar zabe a Afirka ta yamma”, wanda wata kungiyar al’umma ta ‘Yiaga Africa’ ta shirya, ya danganta komowar juyin mulkin soji a yankin da rashin shugabanci nagari. An Gudanar Da Taron Dandalin Ciniki Tsakanin Sin Da Habasha A Addis Ababa Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa Ya yi nuni da juyin mulkin baya-bayan nan da aka yi a Mali, Burkina Faso, Guinea, da Nijar, a matsayin alamu karara...
    Wani kamfani dan kasar Saudiyya mai suna Mashariq Al Dhabia, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aiki aka yi wa kwaskwarima da hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) domin hidima ga Alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin 2025. LEADERSHIP ta rahoto cewa, kamfanin a baya ya yi barazanar maka NAHCON a kotu bisa zargin karya sharudan kwangilar da hukumar ta rattaba wa hannu kan hidima ga Alhazan Nijeriya a Masha’ir a lokacin aikin Hajjin 2025. Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha Amma a wani al’amari mai ban mamaki, sai aka hangi wata tawaga daga kamfanin na Saudiyya a karkashin jagorancin shugaban kamfanin, Muhammad Hassan, ta...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kira da a gaggauta bibiyar bayanan manyan laifuka na shugabannin gwamnatin mamayar Isra’ila A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Holland, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da ci gaba da mamaya da kuma laifukan da yahudawan sahayoniyya suke yi a Falasdinu, tare da yin kira ga kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa wajen hanzarta bibiyar bayanan shari’a da laifuka a kotunan duniya dangane da kisan kiyashi da laifukan yaki da shugabannin mamayar Isra’ila suka aikata. Kamfanin dillancin labaran Fars ya habarta cewa: Ministan harkokin wajen kasar Holand Caspar Veldkamp da takwaransa na Iran Abbas Araqchi sun tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashen...
    An shawarci shugabanni da aka zaba da su girmama hukuncin kotu domin tabbatar da dimokuradiyya a ƙasar. Wani malami a Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Kamilu Fagge, ya bayar da wannan shawara a Kaduna, yana nuna damuwarsa kan zargin karya dokokin kotu a harkokin siyasa. Ya bayyana damuwarsa kan matakin da Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun ya dauka na gudanar da zaɓen kananan hukumomi duk da umarnin kotu da ke hana hakan. Farfesa Fagge ya gargaɗi shugabanni da aka zaɓa cewa rashin mutunta hukuncin kotu, duk da rantsuwar da suka yi na kare kundin tsarin mulkin ƙasa da bin doka, na iya zama barazana ga dimokuradiyya. SULEIMAN KAURA 
    Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas zai saki fursunonin ‘yan sahayoniyya guda 6 a madadin fursunonin Falasɗinawa 602 A cikin tsarin yarjejeniyar musayar fursunoni na Ambaliyar Al-Aqsa da kuma a cikin kashi na bakwai na matakin farko na shirin musaya … za a sako wasu sabbin fursunonin Isra’ila guda 6 da suke hannun dakarun Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas, a ranar Asabar, tare da bayyana sunayensu. A sakamakon haka, mamayar za ta saki fursunonin Falasdinawa 602: Falasdinawa 50 daga cikinsu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai ne, wasu 60 daga cikinsu kuma an yanke musu hukunci mai tsawo, da kuma fursunoni 47 na Wafa al-Ahrar da aka sake kama su, bayan zaman gidan yari a baya. Haka...
    Iran ta jadadda anniyarta ta karfafa alaka da kasashen Afrika, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar. A cikin wani sako da ya aike ta shafin X a ranar Juma’a, kakakin ma’aikatar, Esmaeil Baghaei, ya yi tsokaci kan ganawar da aka yi a ranar Alhamis tsakanin mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad Reza Aref da jakadun kasashen Afirka a Tehran. Baghaei ya bayyana cewa, taron ya nuna aniyar Iran na karfafa alaka da fadada hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannoni daban-daban na moriyar juna. A yayin ganawar, Aref ya bayyana cewa, dabarun gwamnatin Iran, karkashin shugaba Masoud Pezeshkian, ya yi daidai da ainihin manufofin Iran na inganta alaka da kasashen Afirka. Ya jaddada manufar karfafa hadin gwiwa tsakanin...
    Jami’an diblomasiyya da dama daga kasashen kungiyar G20 ne suka isa birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, don halattar taro na kwanaki biyu. Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya isa birnin Johannesburg a jiya Alhamis kwanaki biyu kacal da ya gana da tokwaransa na kasar Amurka a birnin Riyad na kasar Saudiya. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ yace ana saran kasashen turai zasu kara jaddada goyon bayansu ga kasar Ukraine a yakin da take fafatawa da kasar Rasha. Duk tare da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son kawo karshen yakin ba tare da su ba. Kasashen Burtaniya , Faransa, Jamus da kuma tarayyar Turai EU gaba daya suna goyon bayan Ukraine a yakinta da Rasha....
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su. Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata. Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar  gwagwarmayar...
    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki shugabancin Ukraine, inda ya bayyana cewar su ne suka haddasa yaƙin da Rasha ke yi da su. Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda ya ce yana mamakin yadda ba a gayyaci ƙasarsa zuwa taron tattaunawar zaman lafiya a Saudiyya ba. ’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa A cewar Trump, Ukraine ce ta jawo wa kanta matsalar. “Da ba ku fara wannan yaƙin ba, da kun cimma yarjejeniya tun farko,” in ji shi. “Da ni ne, da na samo muku mafita, kuma babu wanda za a kashe.”...
    Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin ficewarta daga yankin Zirin Gaza da kuma yin fatali da bukatar ajiye makamai a matsayin wani bangare na kowace yarjejeniya. A yayin da ake fara shirye-shiryen fara gudanar da mataki na biyu na shawarwari tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar Hamas bisa tsarin tsagaita bude wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni, gwamnatin yahudawan sahayoniyya yana ci gaba da yin jinkiri ta hanyar kokarin kafa sabbin...
    Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
    Kasar Iran ta bayyana cewa: Barazanar gwamnatin mamayar Isra’ila ga jirgin saman da ke dauke da fararen hula na Lebanon cin zarafi ne ga ‘yancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine kan barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, yana mai nuni da hakan a matsayin ci gaba da keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa a fili, da kuma keta hurumin kasar Lebanon. Baqa’i ya yi nuni da cewa: Barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, wanda hakan ya haifar da dakatar da zirga-zirgar...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas Ta ce hukumar ta riga ta biya kuɗin gurabe 26,287 na maniyyata, sannan ta tanadi wasu 26,000, da za a tabbatar da su gaba ɗaya kafin ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025. Domin cika wa’adin da Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayar, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tafi Makka domin ƙulla yarjejeniya. Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a...
    Da marecen jiya Litinin ne aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakin ministocin harkokin wajen Iran da na Saudiyya akan shirin Donald Trump na korar Falsdinawa daga Gaza,inda kasashen biyu su ka ki amincewa da shi. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci, da takwaransa na Saudiyya Faysal Bin Farhaan, sun nuna kin amincewarsu da shirin na shugaban kasar Amurka akan mutanen Gaza. Ministan harkokin wajen Saudiyya Faysal Bin Farhan ya ce, Saudiyya tana da matsaya tabbatacciya da ita ce kin amincewa da duk wani shiri na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza zuwa wata kasa.” Ministan na Saudiyya ya nuna goyon bayansa ga kiran da Iran ta yi na yin taron kungiyar kasashen musulmi domin tattaunawa wannan batu....
    Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan shawarar Amurka da Isra’ila kan Falasdinu. A yayin tattaunawar shi ma ministan harkokin wajen Saudiyya  ya nuna adawar Saudiyya ta tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga Gaza ko wasu yankunan. Tunda farko...
    Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar cewa, kasar za ta karbi bakuncin taron gaggawa na kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan Fabrairun nan, domin tunkarar al’amura na baya-bayan nan da suka shafi batun Falasdinu da zirin Gaza. Sanarwar ta ce, an yanke shawarar gudanar da taron ne bayan muhimman shawarwarin da Masar ta yi da kasashen Larabawa, ciki har da Falasdinu da ta bukaci gudanar da taron, tare da hadin gwiwar Bahrain. A wani labarin kuma, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka kan munanan kalamai da kuma rashin da’a da firaministan Isra’ila ya yi na yin kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya. A ranar Alhamis, ne Netanyahu ya ba da shawara...
    Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai. Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988),...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na kin amincewa da kalaman Netanyahu dangane da korar Falasdinawa daga Zirin Gaza Kasar Saudiyya ta jaddada yin tofin Allah tsine, da kuma karfafa kin amincewa da kasashen Larabawa suka yi dangane da furucin Benjamin Netanyahu kan neman korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar a yau Lahadi, ta jaddada cewa: Saudiyya ta tabbatar da yin watsi da irin wadannan kalamai da ke da nufin karkatar da hankali daga jerin laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a Gaza, ciki har da kisan kare dangi da ake yi musu. Sanarwar ta kara da cewa: Wannan tunani na...
    Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa. Ya kara da cewa:...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar  na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON Naira Biliyan Huda da Miliyan Dari Biyar da Ashirin (4.520), a yayin da take sa ran za ta kara biyan wasu kudaden kafin cikar wa’adin da NAHCON din ta bayar. Ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa jihar kujeru 1,809. A cewarsa, tuni hukumar ta raba kashi 40 cikin 100 ga kananan hukumomin jihar domin gudanar da aikin hajjin bana. Don...
      Yayin da Hukumar Kula da Hajji ta Kasa ta kara wa’adin biyan kudin Hajjin bana zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta umarci dukkan ofisoshin da suke alhakin yin rajista su tabbatar da an yi wa duk masu sha’awar tafiya Hajji rajista kafin ƙarshen wa’adin da aka ƙara.   Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ya kuma yi kira ga dukkan maniyyatan da ba su kammala biyan kuɗinsu ba da su gaggauta yin hakan.   Ya jaddada cewa ba za a ƙara wa’adin bayan ranar 10 ga Fabrairu ba, don haka ya bukaci maniyyata su yi amfani da wannan damar su kammala rijistarsu kafin ko zuwa Litinin, 10 ga Fabrairu, 2025.   Rel/Adamu...
    Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci-gaba da kuma albarka ga Najeriya. Khalifa Muhammad Mahi Inyass, ɗa ga Jagoran Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, ya jinjina wa Gwamnatin Tinubu, inda ya yi wa shugaban ƙasa addu’ar samun nasara da ƙarin basira da nasara a shugabanci domin kawo gagarumar ci-gaba a Najeriya. Masu yi wa ƙasa hidima za su karɓi N77,000 daga Fabrairu – Shugaban NYSC ’Yan...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta Sanar da cewa: Ma’aikatar tsaron kasar ta kebe jirgin saman maras matuki ciki kirar “Arash-2” da ta kera ne don kai hari kan haramtacciyar kasar Isra’ila A ci gaba da gudanar ranakun atisayen soji domin ayyukan tsaron kasa, da sojojin Iran suke gwajin kai hare-hare da kuma sarrafa manyan na’urorin makaman tsaro a yankin da ke yammacin kasar, a karon farko sun nuna wasu jiragen saman yaki maras matuki ciki da aka kera a cikin gida masu tsnanin karfin munanan hare-hare irin na kunan bakin wake kirar “Ababil” da “Arash-2” da dakarun sojin kasar Iran zasu yi amfani da su wajen kare tsaron kasa duk lokacin da ya dace. Jiragen saman “Ababil” ne suka jagoranci...
    Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa...
    Kwamishinan ya yi ikirarin cewa ayyukan Madakin Gini na nuna rashin jajircewa ga waɗanda suka zaɓe shi. “Madakin Gini ya bayyana cewa ba ya cikin waɗanda suka goyi bayan shi da suka zabe shi. Saboda haka, babu dalilin ci gaba da kasancewarsa a wannan muƙamin idan ba ya wakiltar buƙatun mutanen Dala. Da zarar shugabannin jam’iyyar sun amince, ni na shirya fara aiwatar da aikin kiranyesa,” in ji Waiya. Taron ya samu halartar shahararrun mutane, ciki har da Alhaji Lawan Husaini Dala, shugaban NNPP na Dala; da Alhaji Dayyab Ahmad Maiturare, Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, da Hon. Suraj Kwankwaso, da sauransu.
۱