2025-03-01@00:07:09 GMT
إجمالي نتائج البحث: 201
«Hukumar Alhazai Ta Kaduna Ta Nemi Goyon Bayan Sarkin»:
Jami’ar Michigan ta Amurka ta dakatar da karatun wasu daliban jami’ar saboda rawar da suka taka, a zanga-zangar goyon bayan Gaza a yakin watanni 15 da suka yi da HKI. Kamfanin dillancin labaranSahab ya nakalto kamfanin dillancin labaran Mehr yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, hukumar Jami’ar Michigan ta kori wasu daliban daga...
Ƙungiyoyin alarammomi da matasa daga jihohin Arewa sun nuna goyon bayansu a kan taron karatun Kur’ani na ƙasa da ake shirya gudanarwa a Abuja a ranar 22 ga watan Fabrairu. Shugaban ƙungiyoyin, Kwamred Murtala Mohammed Garba, wanda aka fi sani da Gamji, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya...
Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta biya fiye da Mahajjata dubu uku da suka kammala aikin Hajjin shekarar 2023 kudaden da Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta mayar masu. Mai Magana da Manema Labarai na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, shine ya bayyana hakan sannan ya kara da cewa an turawa kowane...
A jiya Jamu’a, wakilin CMG ya samu labari daga ofishi mai kula da aikin ceton mutane daga bala’in girgizar kasa da ya abku a gundumar Tingri karkashin birnin Shigatse na kasar Sin cewa, yanzu haka, an kafa gidajen wucin gadi 7733, da tantuna 9941, tare da tsugunar da mutane 47787 da bala’in girgizar kasa ya...
Tun bayan ’yan kwanaki da Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar cewa Hukumar ta daina kamen masu aikatawa da yada baɗala, sai dai ta yi musu wa’azi, aka fara ganin yaɗuwar bidiyoyin da suka saɓa da al’ada da Addinin Musulunci suna ɓulla kafofin sada zumunta. Daga watan Disamban 2024...
Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na...
Jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aikin soje na zamani duk da cewa wasu daga cikin jiragen tsoffin kira ne. Kamfanin dillancin labaran Sahaab na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na JMI yana fadara haka. Ya kuma kara da cewa sojojin saman kasar sun samarda wasu sabbin kayakin aikin Soje wadanda...
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako...
Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro sun kai samame a wasu gidajen jama’a a birnin, inda suka kama wasu da ake zargin ɓarayi ne tare da ƙwato kayayyakin da aka sace. Wasu daga cikin kayayyakin da aka ƙwato da suka haɗa da: naɗin igiyoyin wutar lantarki masu...
’Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu 24 a wasu jerin hare-hare a wasu kauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara. ’Yan ta’adan sun kai hare-haren ne ranar Alhamis, a ƙauyukan Shinkafi da Jangeru da Shanawa da Birnin Yero. A garin Shinkafi, ’yan bindigar sun kashe mutum...
Wani direba da ake zargin yana cikin maye ya kutsa da motarsa cikin wani gungu na sojoji daga barikin Myoung da ke Yaba dake jihar Legas, yayin da suke atisayen motsa jiki da safiyar yau Juma’a, lamarin da ake jin tsoron cewa ya yi sanadiyyar mutuwar Sojojin da dama. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya...
Dakarun Ezzeddine al-Qassam, reshen kungiyar gwagwarmayar Hamas masu dauke da makamai, sun sanar a jiya Alhamis shahadar babban kwamandan kungiyar Mohammad “Abu Khaled” Deif tare da wasu manyan kwamandoji da dama, a wani bangare na farmakin guguwar al-Aqsa. Da yake magana a cikin wani faifan bidiyo da aka fitar ta kafar yada labaran soji ta...
Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu. Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar...
Kungiyar Hamas ta yaba da rawar da Iran ke takawa wajen tallafawa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yanci kai Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da wata tawaga daga jagororin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, karkashin jagorancin shugaban majalisar gudanarwa (wanda aka kafa bayan kisan jagoran kungiyar Yahya Sinwar) Mohammed Darwish, a babban birnin...

Kafafen Yasa Labaran Sweden Sun Tabbatar Da Mutuwar Selwan Momika Wanda ya Kona Alkuranai A Kasar A shekarum Baya
Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta...
Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun...
Shugabna Pual Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa ba zai dakatar da goyon bayana da yake bawa kungiyar yan tawaye ta M23 ba, wadanda a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kwace wurare da dama a arewacin Kivu na kasar DMC daga cikin har da birnin Goma babban birnin lardin. Shafin yanar gizo...
Shugaba Felix Tsisekedi na Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo ya bukaci hadin kai na al’ummar kasar tare da sanar da mayar da martini kan rikicin gabashin kasar dake da nasaba da kungiyar ‘yan tawaye ta M23. A yayin wani jawabi ga al’ummar kasar, shugaban na Kongo ya yi kira da a hada kai tare da ba da...
Aƙalla mutane 20 ne ska rasu a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a Jihar Unity da ke Sudan ta Kudu. Rahoton gidan rediyon Miraya, na tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ƙasar, ya bayyana cewa jirgin ya yi hatsari ne jim kaɗan bayan tashinsa daga wata rijiyar mai a Unity, inda ya ɗauki...
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air...
Gwamnatin Tarayya, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen Max Air na tsawon wata uku, bayan ɗaya daga cikin jiragen kamfanin, tayarsa ta yi bindiga yayin sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a daren ranar Talata. Jirgin Max Air ƙirar Boeing 734 mai lamba 5N-MBD ne ya samu matsalar kamar yadda rahotanni suka bayyana. Za...
Wani jami’in fadar mulkin Amurka ( White Hosue) ya nakalto shugaban kasar Amurka Donald Trump yana fada a yau Laraba cewa, shugaban kasar Amurkan ya rattaba hannu akan wata doka ta fada da kin jinin yahudawa da ta kunshi cewa duk wasu dalibai ‘yan kasashen waje da masu ci rani a kasar, idan su ka...
Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar. A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a...
Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar,...
Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ya bayyana wa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Aiwatar da dokokin Isra’ila kan hukumar UNRWA zai zama bala’i Babban Kwamishinan Hukumar Kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya ce: Aiwatar da cikakken dokar...
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce karamin yankin Gaza ya durkusar da gwamnatin Isra’ila duk da makaman da ta ke dasu da kuma cikakken goyon bayan Amurka. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa : tsayin daka da aka fara a Iran din, ya jawo farkawar wasu al’ummar musulmi kuma...
Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun ce sun ƙwato tarin makamai a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda na Jihar Zamfara. Dakarun tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (DSS), sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan masu safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya. Tankar mai ta sake fashewa a Neja Jadawalin Gasar...
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a...
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta yi tsokaci a karon farko kan labarin da ke yawo cewa sojojinta sun kama ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji. Rundunar tsaron ta sanar da gaskiyar lamarin ne bayan raɗe-raɗin kama Bello Turji ya karaɗe kafofin sada zumunta. Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya sanar cewa babu...
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta yi tsokaci a karon farko kan labarin da ke yawo cewa sojojinta sun kama ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji. Rundunar tsaron ta sanar da gaskiyar lamarin ne bayan raɗe-raɗin kama Bello Turji ya karaɗe kafofin sada zumunta. Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya sanar cewa babu...
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta yi tsokaci a karon farko kan labarin da ke yawo cewa sojojinta sun kama ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji. Rundunar tsaron ta sanar da gaskiyar lamarin ne bayan raɗe-raɗin kama Bello Turji ya karaɗe kafofin sada zumunta. Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya sanar cewa babu...
Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na...
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce al’ummar kasar Labanon ba za su manta da irin goyon bayan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Iraki ta yi musu ba a lokacin da Isra’ila ke kai musu hare-hare. Sheikh Naim Qassem ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka watsa kai tsaye a...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, Sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan “jajircewar mutanen kudancin kasar Lebanon fuskantar sojojin HKI’ yan mamaya’ wanda ni tahir amin. ///…A Jiya lahadi be wa’adin ficewar HKI daga yankuna da garuruwan da suka mammaye a kudancin kasar Lebanon, amma karfe 4 da safe yana cika mutanen...

Sanarwar Yiwuwar Kai Harin Ta’addanci Kano Lokacin Maulidi: Mun Cafke Wani Da Bama-bamai – Kwamishina
Ya bayyana cewa, wadanda ake zargin sun tsere daga jihar biyo bayan tona musu asiri, amma an cafko daya an dawo da shi Kano bayan ya tsere da farko. CP Dogo, ya jaddada mahimmancin samun rahoton leken asiri wajen dakile barazanar da ake iya fuskanta, tare da yin cikakken bayani kan yadda ‘yansanda suka...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi ƙarin haske dangane da barazanar harin ’yan ta’adda da ta yi gargaɗin aukuwarsa a bayan nan. Da yake yi wa manema labarai jawabi, Kwamishinan ’Yan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya ce sun ɗauki matakan da suka dace biyo bayan barazanar harin ’yan ta’adda musamman a yayin taron...
Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe...
Gomman sojoji da mayaƙan sa-kai na Sibiliyan JTF sun kwanta da dama a wata arangama da mayaƙan Boko Haram a yankin Mai-saleh da ke tsakanin jihohin Borno da Yobe. Majiyoyin tsaro sun bayyana ce ’yan na Boko Haram sun kai wa jami’an tsaron hari ne bayan da jami’an tsaron sun kwace wani babban sansaninsu da...
Bayan da jami’an tsaro a kasar Burtania suka kama wani fitaccen mai gwagwarmayar kare hakkin Falasdinawa da kuma goya masu baya, a kwanakin da suka gabata. Wasu yan kasar sun gudanar da taro don tattaun makomar incin fadin albarkacin baki a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka yi magana...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda...
’Yan bindiga sun kai hari garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta. Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta, Alhaji Auwalu....
Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewa watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Gasar Firimiyar Ingila. Hakan ya biyo bayan shan kashin da ƙungiyar ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a karawar mako na 22 na gasar Firimiyar. Hakan ya kai United matsayi na...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagorori na kasar Sin sun ziyarci ko kuma sun gayyaci wasu su ziyarci tsoffin jami’ai da suka yi ritaya, sun mika gaisuwa gabanin bikin Bazara na al’ummar Sinawa na ranar 29 ga watan Janairun nan. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar...
Majiyoyin leken asirin da suka tabbatar da harin, sun kara da cewa maharan sun kai hari sansanin ne dauke da muggan makamai, inda suka ce ‘yan ta’addan sun lalata gine-gine da dama da kuma motocin aikin soji a yayin harin.
Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana...