2025-04-15@22:56:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 432

«Ramadan a masallacin Al Aqsa»:

    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Neja ta kaddamar da rabon sutura da jakunkunan hannu masu nauyin kilo 8 ga maniyyatan bana, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen aikin Hajji na shekarar 2025. A lokacin da yake jawabi yayin kaddamar da rabon, Shugaban Hukumar, Sheikh Muhammad Awwal Aliyu, ya bayyana cewa rabon kayayyakin na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sauƙin tafiya da kuma aikin Hajji ba tare da wata tangarda ba ga maniyyatan jihar. Shugaban wanda Daraktan Gudanarwa, Babani Aliyu Yahaya, ya wakilta a yayin bayar da kayan ga Jami’in Alhazai na Ƙaramar Hukumar Chanchaga, ya ce kayayyakin na maniyyatan  da suka kammala biyan kuɗin kujerunsu ne. Daraktan Gudanarwar ya kuma yi kira ga waɗanda har yanzu ba su...
    A cewar Ministan, samun wannan ƙwarewar ya zama wajibi a wannan zamani da kowa da kowa – wato daga masana hulɗa da jama’a zuwa shugabannin kamfanoni – yake taka rawa a matsayin mai magana da yawun wani.   Idris ya ce: “Yau a wannan zamani da kowa ke zama mai magana da yawu – ko ɗan hulɗa da jama’a ne ko shugaban kamfani a ɓangaren gwamnati da masu zaman kan su – wajabcin samun ilimi kan kafofin watsa labarai ya zama abu mai matuƙar muhimmanci, domin yana ba da damar fahimta, nazari da tantance sahihancin saƙonnin da ke yawo a kafafen watsa labarai, wanda hakan zai ba da damar yanke sahihin hukunci da mu’amala da labarai yadda ya kamata.  ...
    Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da yin luguden wuta kan zaman taron shugabannin sojojin Ukraine a birnin Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, ta kai hari kan wani ofishin rundunar sojojin Ukraine da ke dauke da makamai masu linzami na Iskander a yayin wani zaman taron manyan sojojin kasar a birnin Sumy, inda aka kashe jami’ai sama da 60. Ma’aikatar tsaron Rasha ta kara da cewa sojojin na Ukraine na ci gaba da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa gare su, tare da kafa cibiyoyin soji da kuma shirya tarurruka tare da halartar sojoji a tsakiyar birni mai yawan jama’a, tare da yin nuni da cewa; Rasha ta kai harin...
    Al’ummar Babura sun shirya gagarumin taron girmamawa domin karrama Dr. Salisu Mu’azu, bayan nada shi a matsayin Daraktan kuma babban likitan asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke jihar Jigawa, da kuma samun matsayin mamba na Cibiyar Kasa (mni). Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Rabiu Umar, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin nuna godiya ga Allah da kuma murnar manyan nasarorin da Dr. Mu’azu ya samu. Ya yaba da kokarin Daraktan wajen gudanar da aikinsa da kwarewa, da kuma ci gaba da tallafa wa al’umma. A sakon da aka gabatar a madadin Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmoud, wanda Mai Girma Alhaji Usman Sayyadi, Babban Hakimin Masarautar, ya wakilta,...
    Majiyar Falasdinawa a Gaza sun bada labarin kissan wasu sojojin HKI  a unguwar Shuja’iyya kusa da Gaza a jiya Litini,  inda wasu kuma suka ji rauni. Kafafen yada labarai da yahudawan da kuma larabawa sun bayyana cewa kungiyar Jihadul Islami a Gaza ta ce nayakanta masu farautar yahudawa daga nesa sun bayyana cewa suk halaka wasu yahudawa wadanda suka boye a wani gida a garin Rafah kudancin Gaza, inda suke halakasu. Sannan a sauran wuraren kuma sojojin yahudawan da dama ne  suka ji rauni. Kuma sun ga jiragen yakin masu sauran ungulu na yahudawan sun zo sun tafi da wadanda abin ya shafa. Wannan dai kadan Kenan daga hare-haren maida martanin da dakarun falasdinawan suke mayarwa ga sojojin yahudawan, tun...
    Rundunar ‘yansandan ta ce ta fara bincike kan lamarin, kuma ta ja kunnen jama’a da su guji irin wannan aiki da ya ke barazana ga rayuka, tsaro da tattalin arziƙin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sai dai har yanzu rundunar ‘yansandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, kuma ƙoƙarin da samun martaninsu ya ci tura.   A gefe guda kuma, gwamnatin jihar Filato ta nuna damuwa kan hare-haren da ake samu a wasu sassan faɗin jihar, lamarin da ke ƙara haifar da damuwa a zuƙatan jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran. Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa:  Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage. Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.
      Kungiyar Kwararrun Masu Fasahar Injiniya ta Ƙasa (NATE) ta rantsar da sabbin shugabannin reshen Jihar Kaduna da za su jagoranci harkokin kungiyar a jihar.   Mataimakin Shugaban Yankin Arewa maso Yamma na NATE, Injiniya Bala Muhammad, yayin bikin rantsarwa da aka gudanar a Kaduna, ya bukaci sabbin shugabannin da su fifita haɗin kai da ci gaban ƙungiyar.   Sabbin shugabannin da aka rantsar sun hada da: Injiniya Audu John a matsayin Shugaba, AbdulKadir Julde a matsayin Mataimakin Shugaba, sannan Williams Okonkwu a matsayin Sakataren reshen.   Sauran su ne Sim Marca Maikege a matsayin Ma’ajin Kuɗi, AbdulGaniu Isah a matsayin Sakataren Kuɗi, da Racheal Ovbiagele a matsayin Sakataren Fasaha.   Haka kuma, Engr. Ishaya Buba daga Radio Nigeria Kaduna...
    Labaran da suke fitowa daga kasar Ukraine sun bayyana cewa, gwamnatin kasar tana son karban iko da bututun iskar gas na kasar Rasha wanda yake yammacin kasar da Turai, wanda kuma yake kai iskar gasa zuwa kasashen Turai. An gina bututun tun zamanin tarayyar Soviet kuma kasashen biyu suna samun kudade masu yawa daga wannan bututun. Gwamnatin kasar Amurka dai tana son ta dawo da kudaden da ta kashewa kasar Ukraine na makamai wacce ta karba a likacin shugaban Biden. Daga cikin dai Amurka ta bukaci Ukraine ta bada ma’adinanta na kimani dalar Amurka biliyon $500. Wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an gwanatocin kasashen Amurka da Ukraine sun tattauna wannan batun a ranar jumma’an da ta gabata, don tattauna batun...
    Jiragen yakin HKI HKI sun yi ruwan boma-bomai kan astin Al-Ahli, asbiti tilo da ya rage yake aiki a arewacin zirin Gaza, a safiyar yau Lahadi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin HKI sun wargaza bangaren ’emagencu’ bukatar kula na gaggawa a asbitin da kuma kofar shiga asbitin. Har’ila yau hare-haren sun lalata bangaren Iskar Oxigen na kula da wadanda suke bukatar kula mai tsanani a asbiti. Kuma sanadiyyar haka mutane da dama sun rasa rayukansu awannan bangaren daga ciki har da wani yaro dan shekara 12 wanda ya ji rauni a kai. Razan Al-Nahhas wani likita mai aiki a bangaren  kula na gaggawa a asbitin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa wannan...
    Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya. A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can. Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.” Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan...
    Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Za a ci gaba da tunawa da shi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko...
    Ya zamto kowacce rana kina hada salad me yawa ki cinye shi, kar ki cika cin abin da zai birki ta miki ciki don kuwa shifa zai dinga rage miki ruwan jikinki ne, ki dage da cin kayan dadi sosai a wannan watannin. (2b) Abubuwa masu mahimmacin da ya kamata su zama abincinki: Tuffa, Baure, Inibi, musanman sati 4 na karshe. (3). Sinadaran gyaran jiki: To a nan fa matsalar take don gaskiya a wannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kin sha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda an fi son a ga amarya a cike ba za ki gane da gaske nake ba sai kin zauna nan a waje namiji...
    Ministan ya ce maganar da ya faɗa da farko wadda ba a ruwaito ta a daidai ba ita ce: “E, lallai an samu cigaba a harkar tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, ko da yake ba a kawar da duk wani aikin tashin hankali gaba ɗaya ba. “Hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin da ake da su a wasu sassan Jihar Borno da wasu wurare. “Haɗin gwiwar da muke gani tsakanin hukumomin tsaro, musamman a shekaru biyu da suka wuce, da kuma gagarumin zuba jari a kayan aiki da na’urorin zamani da ake yi, yana nuna yadda Gwamnatin Tarayya take ɗaukar batun tsaro da matuƙar muhimmanci. “Gwamnatin Tinubu tana...
    Wannan ya hada da darajar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma fitar da su, wanda ke nuni da irin dimbin alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu. Kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa a cikin gida da na waje da jirgin ruwa ya kai dala miliyan 473.6 a watan Fabrairun 2025, kadan ya ragu daga dala miliyan 501 a watan Fabrairun 2024, wanda ke nuna raguwar kashi 5.5 cikin dari. A shekarar zuwa yau, fitar da kayayyaki na FAS ya ragu daga dala miliyan 792.8 a shekarar 2024 zuwa dala miliyan 687.4 a shekarar 2025, wanda ya nuna raguwar kashi 13.3 cikin dari. Amurka ta samu gibin ciniki a kan Nijeriya ne kawai a watan Janairun 2025,...
    Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa ‘yan jarida a Zariya. A cewar Malam Mukhtar, ikirarin da wasu ke yi musamman daga yankin Kudancin Kaduna na cewa Masarautar Kauru na son shiga cikin Jihar Gurara ba gaskiya ba ne kuma yana bata suna. “Mutanen Masarautar Kauru ba su da hannu a wannan yunkuri. Muna alfahari da kasancewarmu a cikin Jihar Kaduna, musamman saboda alakar tarihi, al’adu...
      -Mun lura da ilimomin harkokin zamaninmu a cikin Alkur’ani Cikin godiyar Allah, muna mika ziyara ga Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) da kuma ban gajiya da gabatar da Tafsirin Alkur’ani mai girma na Azumin Ramadan na bana. Allah ya kai mu na badi albarkar Annabi (SAW) da Shehu (RTA). Ya Shehi, a Tafsirinka na rana ta bakwai mun ji yadda ka yi bayani na ilimomin kiyaye hadurran hanya da ke kunshe a cikin aya ta 63 ta Suratul Furkan (Sura ta 25), “Wa Ibadur Rahman…”. Mun kara fahimtar cewa, ayar tana nusarwa a kan tafiya cikin tsari walau sufuri ne na titin mota, ko na jirgin sama ko na ruwa ko jirgin kasa, da dukkan alamomin da ake...
    Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago. Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan. Da yake ba da bayani kan halin da ake ciki, shugaban kungiyar NULGE ya ce, “A zahirin gaskiya muna fuskantar matsaloli da jihohi da dama, kusan jihohi 20 ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi ba. “Muna da Jihohi irinsu Sakkwato, Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Borno, Kurus Ribas, Abuja, da dai sauransu, wasu sun fara biyan ma’aikatan jiharsu albashi sun...
    Asusun ba da lamuni na ilimi na Najeriya ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan cibiyoyin da ke boye bayanai kan yadda ake biyan dalibai rancen kudi yayin da suke neman biyan kudaden makarantun daga hannun daliban.   Sanarwar da Manajin Darakta na NELFUND, Mista Akintunde Sawyerr ya fitar ta bayyana cewa, sakamakon binciken da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa wasu cibiyoyi bayan karbar lamunin dalibai kai tsaye a cikin asusunsu, sun kasa sanar da daliban da abin ya shafa ko kuma nuna kudaden da aka biya a cikin takardun kudin makarantarsu, wanda hakan ya haifar da rudani da bai kamata ba.   Mista Sawyerr wanda ya bayyana lamarin a matsayin rashin da’a, ya kuma gargade...
    Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Na Musamman Kan Ayyuka Na Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Aliyu Modibbo Umar ya ce, “Kalubalan Nijeriya ya ta’allaka a tsarin tarayyarmu,” in ji Shettima. “Ba batu ne na wai nawa ne kowace rukunin tarayya ke samu ba, magana ce ta yadda ake amfani da irin wadannan albarkatun.” “Ba kuma batu ne na cewa nawa ne kowace bangare ke samu ba, sai dai a yi batun yadda ake amfani da irin wadannan kayan.” Ya yaba wa LEADERSHIP bisa samar da wani dandali wanda “ba a samar da shi kadai don musayar ra’ayi ba sai don tsara manufofi masu ma’ana.” Ya kuma bayyana sauye-sauyen da ake yi a karkashin gwamnatin...
      Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar sassa daban daban na duniya, da kuma moriyar bai daya ta dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kamfanin Media Trust Limited na farin cikin sanar da al’umma cewa daga ranar Juma’a 11 ga watan Afrilun 2025, Rediyonta na Tusts Radio zai fara shirye-shiryen gwaji. Tashar za ta fara yaɗa shirye-shiryenta a kan mita 92.7 a zangon FM a birnin tarayya Abuja da kewaye, kuma wannan na daga cikin tsare-tsaren da kamfanin ke bi na faɗaɗa aikin watsa labarai sama da shekaru 27 a Nijeriya. An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta Kamfanin Media Trust shi ne mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya a Nijeriya kuma mamallakin Trust TV da kuma Trust Radio a yanzu. Ga waxanda ba su a birnin tarayya Abuja ko kuma...
    Wata sanarwa da Ma’aikatar Kuɗi ta fitar ta ce: “Wannan tsari ba na wucin gadi ba ne. Tsarin sayar da ɗanyen mai a farashin Naira wata dabara ce ta bunƙasa tace mai a cikin gida da kuma bunƙasa tsaron makamashi a Nijeriya.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu. Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin. Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in...
    “Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dokar bunkasa ci gaban Afirka da samar da dama ga yankin (AGOA), wacce ta bai wa kasashen yankin damar fitar da kayayyaki zuwa Amurka ba tare da haraji ba, ta shiga gararamba bisa yadda karin harajin zai kassara masana’antu kamar su masaku, da na karafa, da kuma noma.   Nijeriya da Afirka ta Kudu da suka fi karfin tattalin arziki a yankin, Amurka ta kakaba musu haraji na kaso 14% da 30% bi-da-bi, saboda rashin imani kuma karamar kasa kamar Lesotho wacce du-du-du karfin tattalin arzikinta na GDP bai wuce dala biliyan 2 ba, aka dankara mata karin harajin da kashi 50%.   Galibin tattalin arzikin kasashen Afirka ya fi dogaro ne da fitar da kayayyaki zuwa ketare don dorewar...
    Majalissar Dokokin Rasha ta amince da yerjejeniyar huldar ta shakaru 20 tsakanin kasar da Iran. Wannan na nuna muhimmin mataki na zurfafa dangantakar siyasa, soja da tattalin arziki tsakanin Moscow da Tehran. Yarjejeniyar ta tsawon shekaru 20, wakilan majalisar sun amince da ita ne a kuri’ar da aka kada a ranar Talata ta yadda kasashen biyu za su iya yin hadin gwiwa cikin tsari da inganci. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na kasar Iran Massoud Pezeshkian ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a cikin watan Janairu, da nufin karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban da suka hada da tsaro, makamashi, kudi, sufuri, masana’antu, noma, al’adu, da kimiyya da fasaha. Yarjejeniyar ta kuma bada damar zuba jari a...
    Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana. A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tura karin sojoji 20,000 zuwa yankin bayan Rasha ta kai hari Ukraine. A ranar Talata, NBC ta ruwaito cewa jami’ai shida daga Amurka da Turai sun tabbatar da tattaunawa kan rage yawan sojojin da aka tura, inda aka fi mayar da hankali kan rage adadin a Romania da Poland. Shugaba Donald Trump yana kokarin kawo karshen yakin Ukraine da aka shafe fiye da shekaru uku anayi tun bayan hawansa mulki, amma har yanzu bai cimma nasarar warware matsalar ba. Ya sha sukar NATO, yana mai jaddada cewa ya kamata Turai ta dauki karin nauyi...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne sun kashe masunta uku a wani hari da suka kai ƙauyen Sanyinna da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. Wata majiyar a ƙauyen ta ce ’yan bindigar sun kashe mutanen ne a lokacin da suka kawo hari da safiyar Talata yayin da mutanen suka fita sana’arsu ta su. Kazalika, majiyar ta ce ko a ranar Litinin da ta gabata ’yan bindigar sun kai hari garin Sutti da Takkau duk a karamar hukumar inda sun jikkata mutum biyu. Mataimaki na musamman ga shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza kan tsaro, Alhaji Gazali Raka ya tabbatar da faruwar lamarin. Alhaji Raka ya bayyana cewa ’yan bindigar sun sace dabbobi da suka haɗa da Shanu...
    Duk da wannan zullumi da ake ciki, a kwanakin baya, kasar Sin ta tattauna da wasu kamfanonin Amurka sama da 20 cikinsu har da Tesla, inda ta kara ba su tabbacin cewa, za ta ci gaba da bude kofarta ga kamfanonin kasashen waje da aiwatar da gyare-gyare a gida. Wannan shi ake nufi da babbar kasa mai sanin ya kamata, mai kuma la’akari da moriyar sauran kasashe maimakon moriyarta ita kadai.   Idan Amurka na ganin matakanta za su danne ci gaban wasu kasashe, su kuma bata fifiko a duniya, to ta yi kuskure, domin yanzu ta budewa duniya ido, kuma kasashe da ma kamfanoninsu, za su koma ne ga inda suka tabbatar da cewa za su samu moriya, kuma...
    Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu.   Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu.   Domin tabbatar da bin ka’ida, kwamishinan ya yi gargadin cewa, nan ba da jimawa ba, za a buga sunayen wadanda ba su bi ka’ida ba a jaridun kasar nan da kuma nuna su a allunan sanarwa a muhimman wuraren gwamnati da suka hada da dakin karatu na jihar Kano, Sakatariyar Audu Bako, Gidan Murtala, da kuma babbar kotun jihar. Daga kanmu, magana ta...
    Hukumar Kula da Jin DDaɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ayyana ranar Juma’a 11 ga Afirilun 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana ga dukkan maniyyatan jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da manema labarai a Ilori. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa jimillar kuɗin aikin hajjin bana ya kai naira miliyan 8,459,000. Ya yi kira ga dukkan maniyyatan da suka  fara biyan kuɗi da su tabbatar sun kammala ragowar kuɗin kafin ranar ƙarshe, wato 11 ga Afrilu, domin ba za a ƙara lokaci ba. Alhaji Abdulsalam ya kuma buƙaci maniyyatan da su gaggauta miƙa fasfo ɗin su na tafiya ƙasashen waje ga jami’ansu domin fara...
    Wasu daga cikin maharan sun tsere zuwa dajin Sambisa, bayan da sojoji, mafarauta da mazauna garin suka yi musu kaca-kaca. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
     Kasashen Uku Suna Yin Taron ne dai a matsayin kwararru domin tattauna batutuwa da dama daga cikinsu da akwai na shirin Nukiliya na Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Baka’i ne ya sanar da cewa za a yi wannan taron ne a birnin Moscow wanda kuma ya kuma kunshi wakilai daga kasashen Iran, China da kuma mai masaukin baki Rasha. Buku da kari Baka’i, ya kuma bayyana cewa za a yi wata tattaunawar a tsakanin Iran da tarayyar turai a matakin masana shari’a. A can kasar Rasha mai Magana da yawun harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta fada wa kafafen watsa labarun kasar ta Rasha cewa, a gobe Talata ne za a yi tattaunawar a tsakanin kwararru daga kasashen...
    Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana hare-haren baya-bayan nan da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar a matsayin shirin masu nufin tada zaune tsaye da kawo cikas ga zaman lafiyar jihar ne a maimakon a alakanta harin da rikicin manoma da makiyaya.   Da yake karin haske kan lamarin, Mista Aradong ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da kayan abinci da sauran kayayyaki.   Mista Aradong, wanda ya yabawa gwamnatin jihar da jami’an tsaro bisa fara gudanar da binciken gaggawa da suka yi, ya kuma bukaci a kara tura jami’an tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.   Da yake jawabi yayin ziyarar, Mista Jatau, wanda ya jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu yayin...
    A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana ci gaba da tsare kananan yara Palastinawa sama da 350 a gidajen yari da wuraren da ake tsare da fursunoni. Sanarwar hadin gwiwa da hukumar kula da harkokin tsare-tsare, da “Kungiyar Fursunonin palasdinu”, da kuma “Cibiyar Kare Hakkokin Bil Adama ta Al-Dameer” suka fitar, ta bayyana cewa, yaran na fuskantar matsaloli Ciki har da azabtarwa, yunwa da gangan, da rashin kulawar likita. Wadannan cibiyoyi sun jaddada cewa yaran Palasdinawa su ma suna fuskantar tauye hakkinsu, wanda irin wannan hali ne ya yi sanadin shahadar wani yaro a cikin makon...
    Gwamnatin Kasar Iran ta bada sanarwan samun sabbin ci gaba a fagen fasaha da kuma kayakin da suka shafi makamashin Nukliya, wanda za’a baje kolinsa a ranar 9 ga watan Afrilu na wannan shekarar , wato ranar makamashin Nukliya ta kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto mataimakin shugaban kasa kuma shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Mohammad Eslami yana fadar haka a yau Lahadi. Ya kuma kara da cewa, masana fasahar nukliya ta kasar sun samar da sabbin ci gaba a fagen makamashin nukliya wadanda suka hada da magungun wadanda suka yi amfani da sinadarin Nkliya don samar da su, da kuma ci gaba a fannin ilmi da dama, duk tare da fasaha da kuma...
    Ya kuma bukaci jama’a musamman mazauna Damaturu da su kwantar da hankulan su, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.   Abdulsalamu ya bada tabbacin aniyar gwamnati na wanzar da zaman lafiya da tsaro, yayin da ya yi gargadi kan yada labaran karya da ka iya haifar da firgici a tsakanin ‘yan kasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Olunloyo ya jagoranci jihar Oyo tsakanin 1 ga Oktoba, 1983 zuwa 31 ga Disambar 1983.   Rasuwar marigayi dan siyasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon Editan jaridar Nigerian Tribune, Barista Oladapo Ogunwusi ya fitar a ranar Lahadi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin kasar Sin ta yi kakkausar suka da bayyana adawarta ga matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya.” A cikin wata sanarwar da ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin na Amurka, wanda ya kasance daukar mataki bisa radin kai, da kuma kariyar cinikayya da cin zarafin tattalin arziki. Sanarwar ta kara da cewa, ta hanyar fakewa da abin da take kira “ramuwar gayya” da “adalci,” a zahiri dai Amurka ta tsunduma a aiwatar da dabarun danniya da babakere, tana neman cimma manufarta ta “Amurka na gaba da komai” da kuma “Amurka ta fi kowace kasa.” Har ila yau, Amurka na amfani da harajin fito don kawo cikas ga tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa,...
    A yayin hirar Abdullahi Shuaibu ya ce “Ni dai suna na Abdullahi Shuaibu, amma al’uma na kirana da Karkuzu, ko kuma Abdullahi Kano, yanzu shekaru 43 kenan ina wannan harka ta fina finan Hausa, amma yanzu wasu lokutan sai in kwana ba ni da abin da za a ci a gida na, kuma wani abin tausayi, ni Karkuzu a yanzu zancen da na ke, wannan gida da nake ciki an sa shi a kasuwa, ba gida na ba ne, haya nake yi. Ya ci gaba da cewa, yanzu a cikin wannan al’amari da na ke yi, in an ce na mallaki gida mai dimbin yawa, wadansu da za su ke kallo na sai su ce gaskiya ne, amma wallahi tallahi,...
    Ministan harkokin wajen kasar Nijar ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a Rasha za ta aika tawagar diflomasiyya a Nijar. Nijar ta tabbatar da aniyar ta na karbar bakuncin ofishin jakadancin Rasha a karon farko cikin sama da shekaru talatin, in ji ministan harkokin wajen kasar ta yammacin Afirka, Bakari Yaou Sangare a ranar Alhamis. Bayanin ya fito ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Moscow bayan tattaunawa tsakanin ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da takwarorinsa na kasashen Nijar, Mali, da Burkina Faso. M. Sangare ya bayyana cewa, a halin yanzu Nijar na neman wurin da ya dace domin gina ofishin jakadanci na tawagar diflomasiyyar Rasha a kasar, ya kara da...
    Alhamdulillah, a makon jiya ne muka fara gabatar da wannan rubutu wanda fahimtar malaman Mazhabar Malikiyya ce a kan azumin Sitta Shawwal a wani yunkuri na warware shubuhar da ake samu a tsakanin mabiya mazhabar a nan Najeriya. Yayin da wadansu ke kokarin haramta azumin wadansu kuma nema suke yi su mayar da shi wajibi. Muna fata da wannan dan rubutu da muka ciro daga shafin Cibiyar Imam Malik ta Intanet (Markazu Imam Malik) za a kawar da wannan takaddama. Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan 1. Na ce ya dace a gabatar da biyan azumi ban ce ya wajaba daga farko ba. Ya inganta a yi Sitta Shawwal...
    Gwamnatin Jihar Borno ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo wajen yin kalamai masu nuna barazana da al’adunmu na rashin ɗa’a da rashin sanin ya kamata. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar yaɗa labarai da tsaron cikin gida ta jihar Borno ƙarƙashin Kwamishinanta Farfesa Usman A. Tar ta fitar, gwamnatin ta yi Allah-wadai da irin munanan kalamam da suke yi da kan iya haifar da barazana. An kai wa motar haya hari an kashe mutum 2 da sace wasu a Benuwe ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi Inda ta yi nuni da cewa, waɗannan kalaman sun saɓawa al’adunmu da tsarin rayuwarmu, musamman a shafukan sada zumunta na...
    A ranar Alhamis ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Amurka da jakadan Sin a Burtaniya Zheng Zeguang, suka bayyana matukar kin amincewa da harajin fito “na ramuwar gayya” da Amurka ta kakaba.  Suna masu nuni da cewa, Amurka ta sanar da karin harajin fito kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe da dama ciki har da kasar Sin, ta hanyar fakewa da abin da take kira ramuwar gayya, ofishin jakadancin Sin da ke Amurka ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, matakin ya saba wa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kuma ya saba wa ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban. Kana, ya bukaci Amurka da ta gyara kurakurenta, tare da warware sabanin cinikayya tsakaninta da kasar Sin...
    Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce hare-hare da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan jihar wasu ne ke ɗaukar nauyinsu ba rikicin manoma da makiyaya ba ne. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin baje kolin kayayyaki da fasaha da ƙungiyar Tincity Fashion Week ta shirya a daren Juma’a a Abuja. An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya bayar da rahoton cewa, a ranar 2 ga watan Afrilu, wasu ’yan bindiga sun kai hari a ƙauyukan Manguno, Daffo da Josho na ƙaramar hukumar Bokkos  ta jihar. Maharan sun kashe mutane da dama tare...
    Kasar ta sha alwashin ci gaba da taimakawa kasashen nan guda uku na kawancen sahel da suka hada da Mali, Burkina faso da kuma Nijar a fannin tsaro. Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ne ya bayyana haka ranar Alhamis bayan ya gana da takwarorinsa na ƙasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar a birnin Moscow, yana mai cewa a shirye suke su taimaka domin bunƙasa alaƙar soji da ƙasashen. “Ina jaddada aniyar Moscow ta taimakawa domin samar da gamayyar rundunar soji ta yankin Sahel, tare da ƙarfafa dakarun soji da sauran jami’an tsaro na waɗannan ƙasashe uku ta hanyar ba su horo da makamai,” in ji Lavrov. Wannan bayanin ya fito ne a yayin taron manema labarai da bangarorin...
    SShugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana  alhininsa bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma’a yana mau shekaru 68 a duniya.   Mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan Harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da sanarwar, inda ya jaddada muhimmancin gudummawar Dr. Abdulaziz wajen koyar da addinin Musulunci da kuma ci gaban matasa.   Shugaba Tinubu ya yabawa ƙoƙarin marigayin wajen yaki da tsattsauran ra’ayi da rikicin Boko Haram tun farkon bayyanar kungiyar. Ya ce al’ummar Musulmi sun yi babban rashi bisa mutuwar Dr. Abdulaziz wanda kan jajirce kan gaskiya da ɗa’a.   Shugaban ya kuma yi addu’a ga Allah Ya jikansa, tare da...
    Shugaba Tinubu ya zanta da manema labarai bayan kammala Sallar Idi na karshen watan Ramadan a filin da aka gabatar da Sallar Idi na kasa a Abuja ranar Lahadi. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su koma kan aikata abubuwan da su ba ta dace ba, a maimakon haka, ya bukace su da su dage wajen aiwatar da kyawawan dabi’un game da darusan da suka koya a watan Ramadan. A cikin hudubar da babban limamin masallacin kasa dake Abuja, Dakta Abdulkadir Salman Sholagberu, wanda ya jagoranci Sallar ya gabatar, ya jaddada bukatar Musulmi su ci gaba da gudanar da ibadar da suka koya a Azumin watan Ramadan,...
    Matakan harajin fito na Amurka na haifar da koma-bayan tsarin cinikayyar duniya. Game da wannan batu, kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ta gudanar da wani binciken jin ra’ayin al’umma ga masu amfani da intanet na sassan kasa da kasa, inda suka yi tir da irin wannan abun da Amurka ta yi, al’amarin da a cewarsu, ka iya janyo ramuwar gayya daga kasashe daban-daban, har ma zai iya ta’azzara yakin harajin fito a duniya, da kawo babbar illa ga tattalin arzikin duniya. Kashi 82.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna cewa, yayin da ake fuskantar rashin daidaiton ci gaba da karfin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, neman cike gibin cinikayya da...
    Ya roƙi Allah da Ya ji ƙansa, tare da bai wa iyalansa da almajiransa haƙurin rashinsa. Hakazalika, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana kaɗuwarsa game da fitaccen malamin. Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta. “Ina miƙa ta’aziyya ta ga iyalai da almajiran Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi. “Dokts Dutsen Tanshi ya kasance abin tunawa saboda jajircewarsa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci. “Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi,” in ji Kwankwaso. Dokta Abdulaziz ya kasance mashahurin malami wanda aka san shi wajen faɗar gaskiya, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi da ƙarfafa zaman...
    Na ji dadi da yadda ka yi kira ga sauran Malamai da su zama masu kwadaitar da neman Ilimi a kowanne fanni, sannan su kaurace wa furta haramci a kan abubuwan da Shari’a ba ta yi haramci a kai ba. Tabbas, ayoyin Alkur’ani suna nan kamar yadda aka saukar kuma ba za su sauya ba har duniya ta nade, amma fahimtarsu tana sauyawa daidai da zamani, don haka, bai dace a yi watsi da kimiyya da fasahar zamanin nan ba da ake ganin na turawa ne kawai, matukar ba a samu fiye da tasu ba. Akramakallah, gaskiya ne, ya dace Malamai su rika ba da fatawa da ta yi daidai da zamaninsu da kuma fahimtar da al’ummar Musulmai Isharori na...
    Yayin gabatar da rahoton an raba lambar yabo ga Hakiman da aka fi samun gudunmawar Zakkar daga gundumominsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar. A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi, ya yi kira ga mambobin kungiyar SCO da su yi Allah wadai da kalaman da shugaban na Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya ce yana da hadari. Majid Takht Ravanchi ya yi kakkausar suka ga barazanar harin bam da Trump ya yi a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, hakan ya keta...
    Ministocin harkokin wajen kasashen kawacen sahel na AES da ya hada Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar, na wata ziyarar aiki a kasar Rasha. Ana sa ran ministocin za su kasance a birnin Moscow a yau Alhamis da gobe Juma’a, don tattaunawa, da zurfafa hulda tsakanin bangarorin biyu, kamar dai yadda aka bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwarsu. Sanarwar, ta ce shawarwarin da ministocin kasashen kungiyar ta AES za su yi tare da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, wani bangare ne na burin shugabannin kasashen uku na yankin sahel da sojoji ke mulki da kasar Rasha, na fadada hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki da kuma tsaro. Har ila yau, sassan biyu za su zanta game...
    Ana yi wa Shehin Malamin laƙabi da Dr. Tauhidi saboda da’awarsa ta ƙarfafa ne akan Tauhidi da kuma riƙo da Sunnar Annabi (S.A.W.) da kuma yaƙi da fararrun al’amura a cikin addinin Islama. Za a yi sallah jana’izar Babban Limamin da misalin ƙarfe 10 na safe a Masallacin Idi na Games Village, Jihar Bauchi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
    Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi Amurka da cewa. duk wani harin soji a kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai haifar da “mummunan sakamako” ga daukacin yankin. Sergei Ryabkov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata mujallar harkokin kasa da kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari idan har ta kasa cimma matsaya da Washington kan shirinta na nukiliya. Ryabkov ya ce, “Hakika ana jin barazanar, ana kuma jin bayanai kan abubuwan da suka dace,” in ji Ryabkov, yana mai cewa “Sakamakon hakan, musamman idan harin ya kasance kan kayayyakin nukiliya, na iya zama bala’i ga daukacin yankin.” Ya ce sabbin kalaman na Trump za su kara...
    A kokarin magance matsalar karancin ruwan sha da garin Rano ke fuskanta na tsawon shekaru, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da ta fara amfani  da  Madatsar Tiga don samar da ruwa mai a garin. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin Sarkin Rano, Ambasada Dr. Muhammad Isa Umar, wanda ya kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a Fadar Gwamnati da ke Kano. Gwamna Yusuf ya yaba wa Sarkin Rano bisa jajircewarsa wajen kare muradun al’ummarsa, inda ya tabbatar masa da cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalar ruwa a garin. Ya bayyana cewa an riga an tsara shirin gina rijiyoyin burtsatse tare da hadin gwiwar ƙaramar...
    Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kai wadannan hare-hare ne a garin Rasul Isa da lardin Salif a yammacin birnin Hudaida na kasar ta Yemen. Sannan tashar talabijin ta Almasirah ta bayyana cewa akalla mutum guda ne ya rasa ransa a wannan harin sannan wani guda ya ji rauni. Har’ila yau jiragen yakin Amurkan sun kai hare-hare kan yankin...
    Sojojin HKI sun kashe akalla mutane 80 a asbitin Jabaliya a safiyar yau Alhamis, sannan sji ne hari mafi muni da ta kai kan gaza tun bayan da ta sake komawa yakin tufanul Aksa, makonni biyu da suka gabata. Asbitin hukumar UNRWA ta MDD na daga cikin wuraren da yahudawan suka kai  hare-hare a garin a safiyar yau. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Asbitin na daga cikin wuraren da HKI ta kaiwa hari a jiya Laraba inda. Sannan a safiyar yau ta kashe mutane akalla 22 a kan cikin asbitin kadai sannan daga ciki har da yara, da mata da kuma jami’an yansanda na gaza. A jiya laraba kadai sojojin yahudawan sun kai hare-hare masu...
    Daga ƙarshe, ya buƙaci sojojin da su ƙara ƙwazo domin tabbatar da cikakken tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su. Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar. Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama. Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano. Kano, jiha ce da hamayyar siyasa da rikicin masarauta ya dabaibaye ta. Akwai hamayyar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyun NNPP mai mulki a jihar da takwararta ta...
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai. Da yake amsa...
    Shugaba Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin babban ginshikin masarauta kuma mai neman ci gabanta.   Shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kano da majalisar masarautar Kano da kuma iyalan marigayin bisa wannan rashi mara misaltuwa.   Shugaban ya yi addu’ar Allah ya sa Jannatul Firdaus, ta zama makoma ga Galadima. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Talata, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dauki matakan ramuwar gayya domin mayar da martani game da sanarwar da Amurka ta fitar ta saka takunkumin biza a kan jami’an kasar Sin, bisa hujjar hana izinin shiga yankin Xizang mai cin gashin kansa, da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A yayin taron manema labarai da aka saba yi a-kai-a-kai, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana cewa, yankin Xizang a bude yake ga kowa da kowa, kuma ba a hana baki daga kasashen waje shiga ba, inda ya kara da cewa, yankin yana karbar dimbin matafiya da sauran al’ummomi da dama daga sassa daban-daban a kowace shekara, domin ko a shekarar...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu. A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekara 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka gwabza na tirjiya a kan zaluncin kasar Japan, da kazamin yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet, da kuma yakin duniya na biyu. Atisayen Dakarun PLA Horo Ne Mai Tsanani Ga Masu Rajin Neman ’Yancin Kan Taiwan Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara Wang, ya yi...
    Yakin cinikayya ba zai taba durkusar da kasar Sin ba, sai dai kaikayi ya koma kan mashekiya. Yayin da wasu kasashen ke aiwatar da kariyar cinikayya da kokarin rufe kofarsu ga sauran sassan duniya, kasar Sin ta kara bude kofarta, tana kuma maraba da ’yan kasuwa daga kasa da kasa. Maimakon kawo cikas, kasar Sin za ta lalubo hanyoyin samun karin ci gaba ga kanta da sauran sassan duniya, kuma kariyyar cinikayya da ake yi, zai rikide ya zamo alheri a gare ta.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Hukumomin Myanmar sun buƙaci ƙasashen duniya su hanzarta tura agaji, yayin da jami’an ceto ke ƙoƙarin gano mutanen da suka maƙale a cikin baraguzan gine-gine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kebbi, NUJ, ta taya gwamnatin jihar da al’ummar musulmin jihar murnar zagayowar ranar Sallah.   Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar da Sakatare, Ismail Adebayo, ta yi murna da al’ummar musulmin jihar kan kammala azumin kwanaki 29 na watan Ramadan da kuma bikin Eid-Fitr.   Ta yi kira da a zauna lafiya da juna a tsakanin al’ummar jihar bisa koyarwar addinin Musulunci da manzon Allah mai tsira da amincin Allah tare da la’akari da muhimmancin watan Ramadan da Idi-El-Fitr.   Majalisar ta yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Nasir Idris kan kayayyakin abinci da aka rabawa musulmi a...
    Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan.   Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara.   Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.   Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
    Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai; Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Karshe. Bayan haka, a karshen ko wane azumin watan Ramadan akan samu tambayoyi kan matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Imamuna Malik (RA) da hukuncin azumtarsu kafin biyan azumin Ramadan musamman ga iyaye mata.  A yau za mu gabatar da wani abu kan bayanan malaman wannan mazhaba game da wannan lamari musamman ganin ana samun wadanda suke ganin azumin bai inganta ba: Shin ya wajaba a gabatar da biyan azumin Ramadan kafin yin Sitta Shawwal? Mai tambaya ya yi tambaya cewa: Mace ce akwai azumin Ramadan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Al-Qur’ani mai girma a cikin suratul Baqarah, Allah Ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharuɗan azumtar watan Ramadana. Kamar yadda malamai suka sha faɗi, wannan wata na ɗauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji. Kazalika, hadisai sun ruwaito falalar azumtar kwanaki shida na watan Shawwal, watan da ke biye da Ramadan. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan falalar da ke akwai ga wanda ya azumci kwanaki shidda na watan...
    Mai martaba Sarkin Lere dake Kaduna Alhaji Sulaiman Umaru ya amince da nadin Sani Ahmed Lere Sardaunan Matasa zuwa Falakin Lere.   Hakan na kunshe ne a cikin takardar nadin da Sakataren Majalisar kuma Sadaukin Lere Alhaji Muhammad Lawal Ahmed ya sanya wa hannu. Alhaji Muhammad Lawal Ahmed yace sabon nadin ya fara aiki ne nan take. Ya bayyana cewa nadin Sani Ahmed Lere a matsayin Falakin Lere daga matsayinsa ne daga Sardaunan Matasan Lere wakilin Matasa a Masarautar zuwa Falakin Lere dan Majalisar Sarki kuma PPS ga Sarki.
    Kungiyar bada agaji ta RED CROSS ta yi allawadai da HKI saboda kissan likitoci 8 a garin Rafah na kudancin gaza a ranar 23 ga watan Maris da muke ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a jiya lahadi bayanda aka basu daman dauko gawakin likitocin wadanda suka rasa rayukansu a cikin watan Motar amblance ta daular marasa lafiya. Labarin ya bayyana cewa lokitocin suna kan hanyarsu ta zuwa unguwar Hashasha inda HKI ta kai hare-hare kan Falasdinawa don basu taimakon gaggawa. Banda haka sai da aka dauki mako guda cur da kashe likitocin kafin sojojin yahudawan su bada damar a dauki gawakin nasu. Ya zuwa yanzu dai tun bayan fara yakin Tufanul...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumin Ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka haɗa da ƙara ƙaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da al’umma da kuma falala masu yawa da ba su misaltuwa. Wani sauyi da watan azumin watan Ramadana ke zuwa da shi shi ne canjin yanayin cimar al’umma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma buɗe-baki. Bayan kwanaki 29 zuwa talatin na samun waɗannan canji, ta waɗanne hanyoyi ne al’umma za su koma cimaka kamar yadda suka saba gabanin watan Ramadana NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah...
    Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya. Bayan haka, a ranar Asabar ce muka kawo karshen azumin watan Ramadan mai albarka na bana. Saudiyya ta kama wasu ’yan Najeriya da suka daga hotunan ’yan siyasa a Harami An kai hare-haren ta’addanci fiye da dubu 5 cikin shekaru 3 a Yammacin Afrika Yanzu kuma za mu duba wasu batutuwa da suka shafi Azumin Sitta Shawwal, musamman a Mazhabar Malikiyya wadda muke bi a nan Najeriya da sauran kasashen yammacin Afirka. Wani lokaci akan samu wadansu cikinmu har ma da malamai su soki azumin da sunan bai inganta ba a Mazhabar Malakiyya, don haka...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan  na Ramadan. Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa  shugabanni jagorancin  don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma. Namadi ya kuma yi addu’ar samun  zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa. ...
    Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji cin mutuncin shugabanni yayin da suke bayyana matsalolinsu, inda ya jaddada cewa girmamawa da ladabi suna fi tasiri wajen samun mafita. “Idan ka zagi shugabanka, ta yaya kake so ya taimaka maka?” in ji shi. Masar ta miƙa wa Hamas da Isra’ila tayin tsagaita wuta Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah “Amma idan ka yi magana da ladabi, zai saurare ka kuma ya ɗauki mataki.” Da yake jawabi bayan sallar Idi a Sakkwato, Sarkin Musulmi, ya buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a da kuma zaman lafiya da ci gaban ƙasa. “Ku yi wa Shugaban...
      Ku kasance masu tausasawa da rahama, ku sadar da zumunta, ku sanya farin ciki azukatan al’umma kuma ku yada farin ciki, sannan ku nemi kusanci zuwa ga Ubangijinku ta hanyar ji da ɗa’a ga umarnin shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ranar idin Karamar Sallah rana ce da Musulmi ke farin cikin kammala azumin watan Ramadan wacce ke zuwa a ranar daya ga watan Shawwal din shekarar Musulunci. Allah Madaukakin Sarki ya shar’anta Sallar Idi a matsayin ibadar kammala Azumin Ramadan wacce take kan kowane Musulumi, baligi, mai hankali, kuma mazaunin gida —  namiji ko mace. Zakatul Fidr: Yadda ake fitar da Zakkar Kono Zakkar Fidda Kai ta fi kayan sallah da abincin sallah A yayin da ake shirin shan shagalin Kamar Sallah, malamai sun bayyana muhimman abubuwan da ya kamata su aikata a ranar, kamar yadda Hadisan Annabi (SAW) suka nuna: Duk Musulumi maza da mata manya da kanana su halarci sallar Idi. Fitar da zakkar fid da kai, wato...
    A birnin Roma masu goyon bayan al-ummar Falasdinu sun gudanar da zanga-zanga ta goyon bayan Falasdinawa, sun kuma ya allawadai da kungiyar tarayyar Turai da kuma Amurka kan yadda suka kasance manay-manyan masu taimakawa HKI a kissan kiyashin da take aikatawa a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa daubban wadanda suka fito kan tituna a tsakiyar birnin Roma na kasar Italiya suna rera taken ‘Free Free Palastine, wato yanci yanci Falasdinusun kammala ba tare da wata matsala ba. Amma a jami’ar Colombia ta kasar Amurka rikicin rikicin jami’ar tare da masu goyon bayan kasar Falasdinu ya kaiga, shugabar jami’ar ta yi murabus daga matsayinta, don bada dama ga wani sabon shugaba, wanda zia aiwatar da...
    Kamfanin hakar ma’adinai mai suna RUSAL na kasar Rasha ya aika da tawaga zuwa kasar Saloyo a yammacin Afirka don nazarin yiyuwar fara hakar ma’adinin bauxite a kasar nan gaba. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya nakalto jakadan kasar Rasah a Saliyo yana fadar haka. Labarin ya nakalto Mohammad Yongawo wani jami’in gwamnatin kasar ta Saliyo yana cewa kasarsa a shirye take ta kammala yarjeniya tsakanin kamfanin Rusal na kasar Rasha don fara aiki a yankunan da ske da ma’adinin bauxite. Ya kuma kara da cewa a halin yanzun bangarorin biyu suna cikin tattaunawa a tsakanionsu. Sannan yana fatan daga karshen gwamnatin kasar zata bawa kamfanin lisisin fara hakar ma’anin a kasar nan ba da dadewa ba. Kafin...
    Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Nijeriya, kamar yadda kwamitin duban wata ya tabbatar. Baya ga Nijeriya, ƙasashen Saudiyya, Bangladesh, da Indiya suma sun ga watan a yau, Asabar 29 ga watan Ramadan, 1446. An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge Mijinki Sai dai wasu ƙasashe kamar Malaysia sun sanar da cewa za su yi Sallah ranar Litinin. Hakan na nufin cewa azumin watan Ramadan ya ƙare, kuma al’ummar Musulmi a Nijeriya za su gudanar da bikin ƙaramar sallah gobe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana. Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi. Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.  
    An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana. Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi. Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.  
    Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Nijeriya, kamar yadda kwamitin duban wata ya tabbatar. Baya ga Nijeriya, ƙasashen Saudiyya, Bangladesh, da Indiya suma sun ga watan a yau, Asabar 29 ga watan Ramadan, 1446. An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge Mijinki Sai dai wasu ƙasashe kamar Malaysia sun sanar da cewa za su yi Sallah ranar Litinin. Hakan na nufin cewa azumin watan Ramadan ya ƙare, kuma al’ummar Musulmi a Nijeriya za su gudanar da bikin ƙaramar sallah gobe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300.   A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da yunwa da kuma samar da abinci ga al’umma. A cewar sa, karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara domin fara noman rani a karo na farko dan fadada harkar noma a kan Tudu.   Alhaji Jamilu Danmalam yace an zabi kauyen Tunubu dake mazabar Kanwa domin fara noman Rani. Ya kara da cewar, wadanda suka anfana da tallafin za su ci moriyar kaso...
    Kungiyar JIBWIS a Karamar Hukumar Giwa ta bukaci al’ummar Yakawada da su ci gaba da rungumar koyarwar Al-Qur’ani a rayuwarsu ta yau da kullum. Mataimakin Shugaban kungiyar, Malam Ibrahim Mustafa Shatiman Giwa, ya yi wannan kira ne yayin bikin rufe Tafsirin Ramadan na bana da aka gudanar a Masallacin JIBWIS da ke Yakawada. Malam Ibrahim Mustafa ya bayyana jin daɗinsa kan goyon baya da jajircewar al’ummar Yakawada a duk tsawon Tafsirin. Ya jaddada muhimmancin kiyaye darussan da aka koya a cikin Ramadan tare da amfani da su a rayuwa bayan karewar watan mai alfarma. A nasa jawabin, Sheikh Suleman Abdulkarim Fatika ya nuna godiyarsa ga dukkan mahalarta Tafsirin da suka daure suka halarta tun daga farkon watan Ramadan...
    Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a cikin tekun farisa wanda aka sanyawa suna Shahid Baghiri mai kuma  tsawon mita 180. Sannan   Labarin ya kara da cewa gwamnatin shugaba Donal Trump na kasar Amurka ta bawa Iran razarar watanni biyu ta amince da zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ta yi shirin yaki da kasar ta Amurka. Dakarun...
    Kungiyar bada agajin ta gaggauwa ta “white Helmets” na kungiyar Al’kaida, wacce kuma take samun tallafin gwamnatin Amurka ta hukumar USAID ta rasa tallafin da take don gudanar da ayyukanta. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana cewa, kasashen yamma musamman Amurka sun yi amfani da kungiyar ta Al-qaeda a lokacin yakin kasar Syriya a shekara ta 2011 zuwa 2017 don ingiza kasashen yamma kan gwamnatin kasar Siriya na cewa ta yi amfani da makaman guba a kan mutane, don cimmmai manufofinsu a kasar ta Siriya. A halin yanzu dai shugaban Trump zai dakatar da tallafin da ya ke bawa kungiyar mai yuwa saboda sun cimma manufarko a kasar Siriya ta kifar da gwamnatin Bashar a Al’asad. A...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.” Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam Khumaini ( r.a) da ya ayyana ranar Kudus a duniya a 1979, wacce ita ce juma’ar karshe ta watan Ramadan, a wancan lokacin manyan kasashen duniya masu takama da karfi suna kokarin ganin an mance da batun Falasdinu da kuma kasakantar da shi da cewa batu ne na Larabawa kadai. Limamin na Tehran ya kuma kara da cewa, abinda Imam Khumain ( r.a) ya yi...