2025-03-25@18:39:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 313
«Ramadan a masallacin Al Aqsa»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...
Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba. Ita kuma juriya cikin dauke bala’o’i, ita ce tsare rai cikin rashin damuwa lokacin da ake cikin tsananin damuwa, mutum ya nuna kamar abu bai faru ba. Ita kuma yafiya ko rangwame, ita ce barin ramuwa ga wanda ya yi maka ba daidai ba. Dukkan wadannan halaye, suna daga cikin wadanda Ubangiji ya ladabtar da ma’aikinsa (SAW) da su. Ubangiji yana fada masa a cikin hakkinsa...
Shugaban kasar Amurka ya rattaba hannu kan dokar ba da damar tsare bakin haure kusan 30,000 a sansanin Amurka da ke tsibirin Guantanamo Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce yana son gidan kurkukun sojoji da ke Guantanamo Bay, wanda aka kebance domin tsare fursunonin da ake zargi da ta’addanci, ya kasance a shirye domin karban bakin haure kusan 30,000 da suka shiga cikin Amurka ba bisa ka’ida ba. Trump yana cewa: “A yau zai rattaba hannu kan wani umarni na zartarwa wanda ke umurtar ma’aikatar tsaro da tsaron cikin gida da su shirya wata cibiya da za ta karbi bakin haure 30,000 a tsibirin Guantanamo Bay,” Trump ya kara da cewa: Guantanamo zai karbi “masu aikata laifuka” a cikin...
Olmo ya buga wa Barça wasa sau uku tun bayan hukuncin da CSD ta yanke, a wasan Supercopa da Real Madrid da kuma wanda ta doke Real Betis a Copa del Rey da kuma Getafe a La Liga.
Sabbin waɗanda aka rantsar sun haɗa da Hon. Sanusi Khalifa, babban mashawarci kan albarkatun ƙasa; Hon. Haladu Ayuba, Mai Bada shawara kan daidaita ɗabi’un jama’a; Hon. Jidauna Tula, babban shawarcesa kan harkokin Shari’a da kuma Hon. Adamu Bello da aka sanya a matsayin babban mashawarci a ɓangaren kasuwanci da masana’antu. Sauran sun haɗa da Alh. Danladi Mohammed Danbaba, babban mai bada shawara kan harkokin jin-ƙai; Hon. Sani Mohammed Burra, babban mai bada shawara kan harkokin majalisar dokokin jihar da na tarayya; Hon. Yakub Ibrahim Hamza, babban mai bada shawara kan ilimi mai zurfi da kuma Hon. Shitu Zaki da ya zama babban mai bada shawara kan harkokin siyasa. Ƙarashin su ne Usman DanTuraki, babban mai bada shawara kan...

Hukumar Gidagen Radiyo Da Talabijin Na Kasar Iran Ta Bada Sanarwan Kama Dan Rahotonta A Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye
A dai-dai lokacinda jijiyoyin wuya suke kara tashi tsakanin JMI ta kuma HKI, jami’an tsaron HKI sun kama daya daga cikin yan rahotomta sun tsare. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar gidajen radiyo da Talabijin ta kasar (IRIB), Peyman Jebelli yana fadar haka ya kuma kara da cewa dan rahoton hukumar baya Gaza, yana cikin kasashen Falasdinu da aka mamaye ne. Sannan hukumar ta fara kokarin ganin an sake shi. Labarin ya kara da cewa tun ranar da aka fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 jami’an tsaron HKI sun kashe yan jaridu 205, sannan ta kama wasu 75, sannan har yanzun wasu 42 kuma tana tsare da su....
“Ƙungiyar Al-Hilal ta gode wa Neymar bisa gudunmuwar da ya bayar, kuma tana masa fatan alheri a nan gaba,” in ji ƙungiyar. Wannan matakin ya zo ne yayin da ya rage wata bakwai kafin ƙarshen kwantaragin Neymar, wanda ya kai shekara biyu da ƙungiyar. A Al-Hilal, ana biyan Neymar Yuro miliyan 150 a shekara. Lokacin da ya koma ƙungiyar, Neymar ya bayyana burinsa na kafa tarihi, amma raunin da ya samu yayin wasan Brazil da Uruguay a shekarar 2023 ya hana shi buga wasanni da dama.
Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as. Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara 40. Babbar manufar gudanar da wannan biki ita ce tunawa da ranar aiko manzon Allah Nuhammad (SAW), wanda ya zo wa dan adam da sako tsira daga halaka da kuma fita daga duhun kafirci da jahilci. Manzon Allah (SAW) ya kasance mutum na musamman a cikin larabawa, wanda dukkanin al’ummar da ke tare da shi ta yi masa shedar gaskiya da rikon amana da karamci...
Buba ya ƙara da cewa ’yan ta’addan sun yi amfani da abubuwan fashewa (IEDs) don daƙile hari daga dakarun, amma hakan bai hana nasarar dakarun ba wajen fatattakar su daga maɓoyar su ba.

Sojojiun HKI A Kudancin Kasar Lebanon Sun Kashe Mutane Fararen Hula Wasu Kuma Suka Ji Rauni A Yau Lahadi
Ministan kiwon lafiya na kasar Lebanon ya bada sanarwan cewa sojojin HKI a kudancin kasar sun kashe fararen hula 15 sannan wasu 83 suka ji rauni a safiyar yau. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana cewa mutanen kudancin kasar Lebanon sun komawa gidajensu da suke kudancin kasar kan iyaka da kasar Falasdinu da aka mamaye ne, sai sojojin yahudawan, suka bude masu wuta suka kashe wannan adadin. A yau Lahadi ne 26 ga watan Jeneru ne, wa’adin ficewar sojojin HKI daga kasar Lebanon yake cika kamar yadda ya zo cikin yarjeniyar da suka sanyawa hannu da kasar Lebanon watanni biyu da suka gabata. Wannan bas hi ne kate hurumin yarjeniyar da aka sanyawa hannu da...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin. Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar. Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan gagarumin tallafi, da ya haɗa da bayar da kayayyaki da jari ga rukunin al’umma daban-daban. Yana mai nuni da cewar, wannan mashahurin shiri ya nuna kyakkyawan hangen nesa na Shugaban karamar hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, wajen tallafa wa mutanen karkara da ke fama da kalubale daban daban. Namadi, ya kaddamar da rabon tallafi ga mutane fiye da 350 a karamar hukumar Sule Tankarkar....

Falasdinawa Sun Gudanar Da Bukukuwan Tarbar Fursunonin Falasdinawa 114 Da Aka Sako Daga Gidan Yarin Isra’ila
Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, yayin da wasu fursunoni 16 daga cikinsu suka isa birnin Zirin Gaza. Jama’ar garin Ramallah sun dauki fursunonin da aka sako a kafadarsu a matsayin alamar nasara. Fursunonin sun bayyana godiyarsu ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan jajurcewar da suka yi a Gaza, kuma har ta kai ga kulla yarjejeniyar musayar. A yayin bikin,...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.