2025-02-22@06:28:41 GMT
إجمالي نتائج البحث: 41
«kawar da kai»:
Annabi (SAW) yana da Alfadarai Bakwai, akwai wazanda ya rike har ya rasu suna wurinsa akwai kuma wazanda ya bai wa wasu daga cikin sahabbansa. Wacce ya je yakin Hunaini da ita, wani sarkin Larabawa (zan makafatul kinani) ne ya bashi, akwai wacce sarkin Ailatu ya bashi akwai ta sarkin Limatul Jandali, akwai ta Sarki Najjashi, akwai ta sarkin Kisra, akwai ta sarkin Mukaukisu akwai Jindilu. Jindilu itace mashhuriya wacce Annabi ya rasu ya bar ta Sayyidina Aliyu ya ci gaba da hawanta, duk yakukuwan Sayyidina Ali, mafi yawancinsu a kanta ya yi, ranar yakin Wak’atu Jamal, Sayyada A’isha (RA) ta ganshi a kanta, sai ta ce “ya yi kama da zan’uwansa” sai mai rike da akalar rakuminta ya jefar...
Hamshakan attajirai da ’yan siyasa sun bayar da gudunmawar sama da Naira biliyan 16 a bikin kaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Taron ƙaddamar da littafin, mai suna ‘A Journey in Service’, wanda aka gudanar a Abuja ya tara manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya. Mahalarta taron da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis sun bayar da gudunmawar ne domin ginin dakin karatun da tsohon shugaban ƙasan ke shirin ginawa. Attajiri mafi yawan arziki a Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote, Alhaji Alikon Ɗangote ya ba da gudunmawar Naira biliyan takwas, Naira biliyan biyu a duk shekara, na tsawon shekara huɗu. Ya kuma yi alƙawarin karin biliyan biyu a duk shekara...
“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne a bar masu amfani da kayayaki su amfana da wannan rage farashin abincin da aka samu,” in ji Kyari. An dai bayar da rahoton cewa, hauhawar farashin kayan abinci ya ragu zuwa kashi 24.48 da kuma kashi 26.08 a watan Janairun 2025, inda ya ragu daga kashi 34.8 bisa dari da kuma kashi 39.84 a watan da ya gabata, sakamakon sake fasalin farashin kayan masarufi...

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Najeriya. Shugaban kasar a bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin, tarihin rayuwar Janar Babangida da gwagwarmayarsa yayin aiki, wanda aka gudanar a Abuja. A yayin da yake jawabi a matsayin babban bako na musamman, Tinubu ya bayyana ga irin jagoranci Babangida a yayin mulkinsa, wanda ya ce ya abin koyi ne ga kowa. Ya kuma yaba da rawar da IBB ya taka wajen kafa sabbin bankuna na zamani, wanda ya kawo kyakkyawa sauyi a fannin hada-hadar kudi na Najeriya. Tinubu ya kuma yabawa manufofin Babangida da salon shugabancinsa da suka...
An yi zaman farko na tattaunawar sulhu a tsakanin kasashen Habasha da Somaliya a birnin Ankara wanda kasar Turkiya take a matsayin mai shiga tsakani. Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Hakan fidan ya yi ganawa da daban-daban da ministocin harkokin wajen kasashen na Habasha da Somaliya. Bayan wannan ganawar minstan harkokin wajen na Turkiya ya bayyana cewa; Yin aiki tare a tsakanin kasashen yankin yana da matukar muhimmanci a wannan zamanin da duniya take cike da sarkakiya.” Haka na kuma ya kara da cewa: Kai wa ga nasara a wannan tattaunawar yana da matukar muhimmanci fiye da kowane lokaci a baya. Kamfanin dillancin labarun “Anatol” na Turkiya ya nakalto ministan harkokin wajen kasar yana yin ishara da babbar dama da...
Taron dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da majalisar dattawan kasar a ranar Laraba ta gayyaci shugabannin hukumar leken asiri don gudanar da bincike kan zargin da dan majalisar dokokin Amurka, Perry Scott ya yi na cewa, hukumar bayar da tallafi ta kasa da kasa ta Amurka, USAID na tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Da yake jawabi a zaman taron na ranar Laraba, Akpabio ya ce Nijeriya ba za ta bar Hukumar USAID ta ci gaba da aiki a Nijeriya ba idan aka same ta da laifin daukar nauyin ta’addanci. Ya ci gaba da cewa, yana da muhimmanci Nijeriya ta tabbatar da gaskiyar wannan zargi.
Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na yau Talata, yana mai cewa, ko da yaushe kasar Sin tana da yakinin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin, kuma ta himmatu wajen inganta shawarwari don samar da zaman lafiya. Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata tambaya game da ganawar da jami’an...
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata. Wannan ne karon farko da hukumar ta NBS ta fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi, abin da ke nufin da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu. Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasu Alƙaluman sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 26.08 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Da yake yi wa manema labarai jawabi shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya faɗa ranar Talata cewa sun sauya tsarin ne saboda...
An tsinci gawar wani Sufeton ’Yan Sanda, mai suna Haruna Mohammed, a cikin wani ɗakin otal a Jihar Ogun. Marigayin, wanda ke aiki da Hedikwatar ’Yan Sanda ta Ishashi a Jihar Legas. NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa saboda tsaro Ya je otal ɗin Super G Royal da ke rukunin gidaje naAnthony Uzum tare da wata mata da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Asabar. Da misalin ƙarfe 8:52 na safiyar washegari ne, manajar otal ɗin, Deborah Adejobi, ta gano cewar ɗakin da suka kama ba a kulle yake ba. Lokacin da ta shiga, sai ta tarar da ɗan sandan a kwance babu rai, kuma matar da...
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar NNPP ita ma ta shiga cikin rikici, inda ake zargin Kwankwaso ne ke jagorantar daya daga cikin bangarorin jam’iyyar. A makon da ya gabata ne wani bangare na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin wanda ya assasa jam’iyyar, Dakta Boniface Aniebonam ya gudanar da babban taro a Legas, inda aka zabi sabbin mambobin kwamitin zartarwa na kasa. Kwankwaso ya tabbatar da ganawarsa da Aregbesola a wani sako da ya fitar. Ya ce, “A yammacin yau na yi farin cikin ziyartar tsohon gwamnan Jihar Osun kuma tsohon ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, a gidansa da ke Legas. Taron ya ba mu damar tattaunawa a kan harkokin siyasar kasar nan da gudanar...
Gwamnatin jihar Kano, KNSG, ta ce ta tanadi hanyoyin dakile mace-macen mata masu juna biyu maimakon rage yawan mace-macen. Kwamishinan lafiya na jihar Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa na Partners Coordination Forum (PCF) da aka gudanar a Kano. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi, ta bayyana cewa, Dakta Abubakar Labaran ya bayyana cewa gwamnati ta himmatu sosai wajen kawo sauyi a fannin kiwon lafiya a karkashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da niyyar ganin ba macen da ta mutu a lokacin haihuwa. Ya yi karin haske kan gyare-gyaren da aka...
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Li Qiang, zai halarci bikin rufe gasar wasannin lokacin hunturu ta kasashen Asiya karo na 9, wanda za a yi gobe Juma’a a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang na kasar Sin. Li Qiang zai kuma shirya liyafar maraba da shirye shiryen da suka shafi huldar kasa da kasa ga shugabannin kasashen waje da za su halarci bikin rufe gasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Amurka Tana Son Ta Maida Rasha Da China Gefe A Duk Wata Tattaunawa Ta Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Iran
Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya na cewa rashin halartar kasashen Rasha da China a cikin duk wata tattaunawa dangane da shirin Nukliyar kasar Iran, zai kawo gibi mai yawa a harkokin siyasa da tsaro a yankin Asiya. Jami’in diblomasiyyan ya kara da cewa kasahen yamma suna son maida kasashen biyu gefe a cikin tattaunawar, a yayinda kasancewarsu a cikin taron yana da matukar muhimmanci saboda al-amarin zai shafi yankin gaba...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara jaddadawa Sarkin Jordan Abdullahi II kan shirinsa na kwace yankin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan ya maida shi wurin shakatawa, da kuma kan cewa kasar Jordan da Masar ne zasu dauki nauyin kula da Falasdinawa kimani miliyon 2 a Gaza a cikin kasashen su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump yana fadar haka a ganawarsa da Sarkin a birnin Washington a yau Laraba. A nashi bangaren Sarkin kasar ta Jordan ya bayyana cewa yana ganin kasashen larabawa zasu dauki mataki guda ne a cikin wannan al-amarin, sannan zasu ji ta bakin Yerima Muhammad bin Salman na kasar Saudiya da kuma Shugaba Abdul Fattah Assisi na kasar Masar, wadanda suke...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jaddada buƙatar samar da manyan gonakin gudanar da noman rani domin yaki da matsalar karancin abinci a Yankin Tafkin Chadi. Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin taron Gwamnonin Tafkin Chadi da aka gudanar makon da ya gabatar a garin Maiduguri fadar Jihar Borno karo na biyar, inda ya jadadda cewar, Allah SWT ya azurta wannan Yanki na Tafkin Chadi da dimbin filayen noma wanda idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, na iya ba da gudummawa sosai wajen samar da abinci a yankin har ma da yankuna makwabta. Zulum ya bayyana muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnonin yankin da abokan haɗin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya domin kafa gonakin noman...

Jaridar Telegraph Ta Ce; Shugabannin Sojojin Iran Sun Bukaci Jagora Da Ya Soke Fatawar Haramci Kera Makamin Nukiliya
Jaridar Daily Telegraph ta watsa labarin cewa: Shugabannin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Khamenei da ya janye fatawarsa kan haramcin mallakar makamin nukiliya Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta watsa rahoton cewa: Shugabannin sojojin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da haramcin mallakar makaman nukiliya da ya fitar da fatawa kanta a farkon takaddamar Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Jaridar ta ruwaito a cikin wani rahoton da wakilinta na musamman Akhtar Muhammad Makoy ya fitar cewa: Manyan jagororin sojojin Iran sun ce dole ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya soke fatawar da ta haramta kera makaman nukiliya matukar gwamnatin Iran na son ci gaba...
Duk da cewa, cikakken bayani kan wannan ziyara bai fito fili ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, LEADERSHIP ta tattaro cewa, ganawar ba za ta rasa nasaba da burin Atiku na tsayawa takarar shugabancin Nijeriya ba a zaben 2027 mai zuwa. Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, manyan ‘yan siyasar ba su kammala ganawar ba.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaban Ƙasa kuma tsohon uban gidansa, Olusegun Obasanjo. Obasanjo da Atiku sun yi ganawar ne a yayin ziyarar da tawagar Atiku ta kai gidan Obasanjo da ke mahaifarsa a Jihar Ogun. A ranar Litinin ne Atiku tare da rakiyarsa ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal da kuma Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya. Isar tawagar Atiku da tawagarsa gidan Obasanjo ke da wuya shugabannin biyu suka sanya labule domin ganawar sirri.
Wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda (ASP), Shafi’u Bawa, da ke aiki da Rundunar 61 Police Mobile Force a Kontagora da ke Jihar Neja, ya hallaka kansa har lahira. Wani jami’in dan sanda ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar. Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari An tsinci gawarsa rataye a cikin dakinsa. Majiyoyi sun ce mahaifinsa, Malam Usman Bawa ne, ya fara gano abin da ya faru sannan ya kai rahoton lamarin zuwa ofishin ’yan sanda da ke Kontagora. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce: “A ranar 8...
Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar. Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.
Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar. Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.

Xi Ya Umarci Ceto Daukacin Mutanen Da Suka Nutse A Ruftawar Kasar Da Ta Auku A Kudu Maso Yammacin Sin
Xi Ya Umarci Ceto Daukacin Mutanen Da Suka Nutse A Ruftawar Kasar Da Ta Auku A Kudu Maso Yammacin Sin
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sha alwashin gyara wa da faɗaɗa sansanin horas da matasan maus yi wa ƙsa hidima (NYSC) na dindindin a jihar. Da yake karɓar babban Daraktan NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed a Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta gaggauta gina sansanin dindindin domin karɓar ƙarin ‘yan bautar ƙasa. Ya kuma yaba da gudunmawar da likitoci da malaman kimiyya ke bayarwa a makarantu. Sin Ta Yi Bikin Tunawa Da Wadanda Aka Hallaka Yayin Kisan Kiyashin Birnin Nanjing Tinubu Ya Amince Da Naira Biliyan 80 Domin Sake Gina Madatsar Ruwa Ta Alau Da Ke Borno Shugaban NYSC ya gode wa gwamnatin Borno bisa tallafin da take bai wa ‘yan bautar ƙasa, ciki har da alawus na...
Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025. A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan yankin da Jami’ar Bayero. Gwamnan ya yi kuma alkawarin samar da Asibitin sha-ka-tafi da samar musu da hanya da kai hasken wutar lantarki da rijiyoyin burtsatsai da bai wa iyalan mamatan jari da daukar dawainiyar karatun yaransu gwargwadon iko da kuma daukar nauyin jinyar wadanda suka ji rauni a yankin a yayin rusau da aka yi a makon da ya gabata.
Babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Cai Qi, ya yi kira a ranar Laraba, da a ci gaba da yin kokari wajen kawar da ayyukan da ba su da ma’ana, da rage nauyin da ke wuyan jami’an kananan matakai, don tabbatar kyakkyawan salon aiki tsakanin ’yan jam’iyya da jami’ai wajen cimma burin da aka sa a gaba a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 14 wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025. Cai, wanda kuma mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ne, kuma mamba a sakatariyar kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a wani taro na matakin koli game da wannan batu. Taron ya bayyana cewa, ya kamata a mayar da hankali wajen...
An tsinci gawar mai shari’a Azuka, Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Onitsha ta Arewa a Majalisar Dokokin Jihar Anambra. An gano gawar Azuka da aka sace a jajibirin Kirsimeti a shekarar 2024 a kan gadar 2nd Niger Bridge, a cikin Anambra, ranar Alhamis. Uwa ta fusata ta jefa ’yarta cikin kogi a Bayelsa Yadda matar aure ta kashe dan kishiyarta da tafasasshen ruwa Marigayin yana hanyarsa ta zuwa bukukuwan ƙarshen shekara ne tare da ‘yan uwansa a lokacin da ’yan bindiga suka yi awon gaba da shi a Ugwunakpamkpa da ke cikin garin Onitsha. Sai dai jami’an tsaro da ke binciken sace shi sun cafke wasu da ake zargin sun kai su inda aka gano gawarwakin mambobin jam’iyyar Leba. Da...
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra. Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki. Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a bude ba yadda suka saba ba, kasancewar yaran suka kulle gidan a duk lokacin da za su je wasa. Da shigarma’auratan cikin gidan ne kuma suka ga gawarwakin yaran an sanya a cikin firinjin kayan kankara. Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe...
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra. Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki. Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a bude ba yadda suka saba ba, kasancewar yaran suka kulle gidan a duk lokacin da za su je wasa. Da shigarma’auratan cikin gidan ne kuma suka ga gawarwakin yaran an sanya a cikin firinjin kayan kankara. Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe...
Jami’in tsaron kasar Iran ya karyata sabuwar da’awar jaridar New York Times ta kasar Amurka Jami’in tsaron kasar Iran ya musanta wasu sabbin zarge-zargen da jaridar New York Times ta Amurka ta wallafa game da zargin Iran cewa tana bunkasa ayyukannta na kera makaman kare dangi. Jami’in tsaron ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Tasnim cewa: Ikirarin da jaridar New York Times ta yi game da wata kungiyar asiri ta masana kimiyyar Iran da ke aikin samar da hanyoyin kera makaman nukiliya cikin sauri, ba komai ba ne illa shirme da zage-zage marasa tushe da kan gado. Jami’in ya kara da cewa: “Wadannan rudun tunani ba su da alaka da gaskiya, kuma kawai labaran karya ne da wasu kafafen yada...
Bisa wannan batu za mu iya ganin cewa, a wannan zamanin da muke ciki na samun ci gaban fasahohi cikin matukar sauri, ya kamata a kara nuna ra’ayi na bude kofa, da karfafa hadin gwiwa da cudanya da juna, maimakon nuna ra’ayin ‘yan mazan jiya da kasar Amurka da wasu kasashe suke yi, inda suke neman yin amfani da takunkumi da babakere wajen kiyaye fifikonsu a bangaren kimiyya da fasaha, matakin da ya raunana su ta fuskar karfin kirkiro sabbin fasahohi, abin da ya zama “Don auki ake yin kunu, ya koma ya rasa auki” ke nan. Sai dai ko da yake batun nan ya kasance gargadi ga kasar Amurka da wasu, zai karfafa gwiwar ‘yan Afirka. A ganin masaniyar...

Mutanen Amurka Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyin Bayan Falasdinawa Bayan Tattaunawar Trump Da Natanyahu Dangane Da Gaza
Mutanen kasar Amurka sun fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da korar Falasdinawa daga Gaza ne, bayan taron da yan jaridu na Trump Da Natanyaho a birnin washintong a jiya Talata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zangar su na rera taken cewa “gaza ba na sayarwa bane”. Maganganun Trump a baya-bayan nan, dangane da yankin Gaza dai, ya jawo cece-kuce da dama kan al-amiran a duniya, A birnin Washington dai mutane sun yi ta kawo batun kare hakkin ‘yan kasa’ da kuma tauya hakkin wata al-umma wacce ta yi shekarun fiye 75 tu na neman hakkinta na komawa kasarta, daga kasashen da suke rayuwa, rayuwa irin ta yan gudun hijira na lokaci mai tsawo. A lokacin...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargaɗi al’umma kan wata alawar yara mai da sanya maye, da ke yawo a gari. Hukumar ta gargaɗi, musamman iyaye da su yi hattara da alawar da sauran kayan tanɗe-tanɗe da ke ɗauke da sinadarai masu sanya maye. Kakakin Hukumar a jihar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya kuma yi kira ga iyaye da suka riƙa lura da irin kayan tanɗe-tanɗe da ’ya’yansu ke saya. Ya bayyana cewa alawar tana kama da cakulet, amma a cikinta an sanya abin da ke bugarwa, kuma yawanci an fi sayarwa a makarantu. NHIS: Kotu ta tsare Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA...
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa. Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya fi aikin gwamnati ko siyasa riba. Sannan, shin su wa ke amfani da kudaden fansar da ake biya ga masu garkuwa da mutanen? Hasashe ya nuna cewa, mai yiwuwa a yi amfani da kudaden don kara sayen bindigogi da sauran makamantansu. Tambayoyin Da Ke Bukatar Amsa Da Matsalolin Da Ke Bukatar Warwarewa A cikin wannan rudani, ka da mu manta da irin yadda gwamnati...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran na fuskantar barazanar mutuwa a makonni masu zuwa. Likitocin hudu, wadanda suka yi aikin sa kai a Gaza sun bayyana mummunan halin da yanayin kiwon lafiyar yankin ke ciki, wanda yakin ya yi wa illa. Guterres ya ce ya ji dadin matuka bayan tattaunawarsa da likitocin Amurka ranar Alhamis. Ya kuma”Dole ne a kwashe yara 2,500 ba tare da bata lokaci ba, tare da ba...
Tinubu ya gode wa shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, da shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka, Akinwumi Adeshina, saboda ƙoƙarinsu na samar da karin wutar lantarki a Afirka. Ya kuma ce yadda masu zuba jari ke gamsuwa da shirye-shiryen gwamnatinsa ya sa aka samu jarin dala biliyan shida a ɓangaren samar da makamashi a shekarar da ta gabata. Hukumar IFC ta sanar da cewa za ta saka dala miliyan 70 domin taimaka wa ‘yan kasuwa su samar da wutar lantarki ta hanyoyin da ba sa gurɓata muhalli. Rahotanni sun nuna cewa Nijeriya na buƙatar aƙalla dala biliyan 23.2 domin inganta ɓangaren wutar lantarki da tabbatar da wadatarta ga al’umma. Taron ya samu halartar shugabannin ƙasashen Afirka da dama, ciki har da...
Sabbin waɗanda aka rantsar sun haɗa da Hon. Sanusi Khalifa, babban mashawarci kan albarkatun ƙasa; Hon. Haladu Ayuba, Mai Bada shawara kan daidaita ɗabi’un jama’a; Hon. Jidauna Tula, babban shawarcesa kan harkokin Shari’a da kuma Hon. Adamu Bello da aka sanya a matsayin babban mashawarci a ɓangaren kasuwanci da masana’antu. Sauran sun haɗa da Alh. Danladi Mohammed Danbaba, babban mai bada shawara kan harkokin jin-ƙai; Hon. Sani Mohammed Burra, babban mai bada shawara kan harkokin majalisar dokokin jihar da na tarayya; Hon. Yakub Ibrahim Hamza, babban mai bada shawara kan ilimi mai zurfi da kuma Hon. Shitu Zaki da ya zama babban mai bada shawara kan harkokin siyasa. Ƙarashin su ne Usman DanTuraki, babban mai bada shawara kan...
A Yau Litinin ne dai da safe dubban Falasdinawa su ka fara komawa Arewacin Lebanon bayan gushewar watanni 15 na yaki. Dubban Falasdinawan ne dai suke tafiya a kafa, yayin da wasu suke tafiya a cikin manyan motoci suna bi ta titin Salahuddin. Tun da fari tashar talabijin din 12: ta HKI, ta watsa labarin cewa; sojoji sun janye daga mashigar Natsarim, da su ka kafa domin yin bincike tun ranar 27 ga watan Oktoba 2023. Da dama daga cikin Falasdinawan sun kwana a wannan mashigar bayan da sojojin HKI su ka hana su wucewa a jiya Lahadi. Barin Falasdinawan su koma arewacin Gaza, yana a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakaninsu da Hamas,dangane da fursunonin yaki. A jiya...
Ya kuma yi gargadi cewa rashin ɗaukar matakai na gyara tattalin arziƙi zai ci gaba da haifar da asara mai yawa, inda tallafin man fetur da na musayar kuɗaɗe ke laƙume kashi biyar cikin ɗari na GDP na ƙasar. Wannan, in ji shi, babban ƙalubale ne ga cigaban tattalin arziƙin Nijeriya.
Wasu jami’an MDD sunn bayyana cewa, a cikin halin da ake ciki a kudancin kasar Lebanon ba ya yuwa mutane yankin su koma gidajensu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ba bayyana cewa a yau ne wa’adin kwanaki 60 na ficewar sojojin HKI daga kudancin kasar Lebanon kamar yadda ya zo a cikin yarjeniyar da suka cimma da gwamnatin kasar Lebanon watanni biyu da suka gabata. A safiyar yau ne sojojin HKI suka kashe mutan akalla 15 sannan wasu kimani 83 suka ji rauni a lokacinda suka yi kokarinn komawa gidajensu da ke kudancin kasar Lebanon wadanda sojojin HKI suke mamaye su. Wakilin MDD na musamman a kan al-amuran kasar Lebanon Jeanine Hennis-Plasschaertand da kuma shugaban rundunar UNIFEL ta...