2025-03-03@16:45:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 476
«rasuwa»:
Hamas ta bayyana komawar Falasɗinawa a matsayin nasara, tana mai cewa hakan ya karya yunƙurin da aka yi na tilasta wa mutanen barin gidajensu.
Wani shaida ya bayyana wa kotu yadda tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Sanata Hadi Sirika ya ba wa kamfanin da bai cancanta ba aikin gyaran Filin jirgin Katsina a kan Naira biliyan 2.8. tsohon Daraktan Sayayya ne a ma’aikatar, Musa Obinyan ya bayyana wa kotu cewa a lokacin da Hadi Sirika yake ministan ba wa...
Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as. Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara...
Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce al’ummar kasar Labanon ba za su manta da irin goyon bayan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Iraki ta yi musu ba a lokacin da Isra’ila ke kai musu hare-hare. Sheikh Naim Qassem ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka watsa kai tsaye a...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gudanar da taron tattaunawa da wakilan baki kwararru wadanda ke aiki a kasar da wadanda suka samu lambar yabo ta Abota ta Gwamnatin Sin. Yayin taron wanda ya gudana jiya Lahadi, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, Li Qiang ya kuma mika gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta...

Na’im Kassim Ya Dora Wa Amurka da Faransa da MDD alhakin Abinda Zai Faru Idan Isra’ila Ba Ta Janye Daga Labanon Ba
Abinda Ya Faru A Lebanon Nasara Ce Akan Isra’ila Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi na farko bayan cikar kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki da HKI. A jawabin nasa sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa a lokuta da dama sun yi tunanin mayar da martani akan keta tsagaita wutar...
A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar ta samu ci gaba mai inganci wajen zurfafa raya zamanantarwarta a cikin “yanayoyi masu sarkakiya da kalubale” a tsakanin watanni 12 da suka gabata. Ya furta hakan ne yayin gudanar da wata kasaitacciyar liyafar maraba da sabuwar shekara ta kasar Sin. Ana Shirin...
Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe...
An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko. An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025. Shi ma firaministan kasar Labanon Najib...
Kwamishinan ya yi ikirarin cewa ayyukan Madakin Gini na nuna rashin jajircewa ga waɗanda suka zaɓe shi. “Madakin Gini ya bayyana cewa ba ya cikin waɗanda suka goyi bayan shi da suka zabe shi. Saboda haka, babu dalilin ci gaba da kasancewarsa a wannan muƙamin idan ba ya wakiltar buƙatun mutanen Dala. Da zarar shugabannin...
Jagoran kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa: A shirye suke su tunkari duk wani harin Amurka kuma ya gargadin sojojin haya Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya tabbatar da cewa: Amurka ta yi amfani da dukkan karfinta wajen tallafawa haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma kokarin murkushe al’ummar Falasdinu, yana mai jaddada...
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Tun a shekara ta 2000 al’ummar Lebanon suka tabbatar da cewa su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta jaddada cewa: Daidaiton sojoji da al’umma da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke kare...
Wata nakiya ta fashe a Sabon-Pegi da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata da kuma jikkata wasu mutum shida. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 7:30 na safe....
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya,...
Real Madrid za ta fafata da Leganes, yayin da Barcelona za ta je Valencia a zagayen kwata fainal a Copa del Rey, bayan da aka raba jadawali ranar Litinin. Wani wasan da zai yi zafi shi ne tsakanin Atletico Madrid da Getafe, yayin da za a yi tata-ɓurza tsakanin Real Sociedad da Osasuna. Shin wannan...

CMG Ya Gabatar Da Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin A Amurka Da Myanmar Da Indonesia Da Habasha Da Faransa Da Jamus Da Paraguay
Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar...
Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da...
Hukumar Kula Da Taswira Ta Jihar Kebbi (KEBGIS), ta tsara wani gagarumin shiri na samar da kudaden shiga na sama da Naira biliyan daya a shekarar 2025. Babban Manajan Hukumar, Bashiru Saidu Bakuwai, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan tabbatar da nadinsa a matsayin babban Manaja,...
Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Atisayen sojin mai take “‘Manzon Allah Mai Girma na 19” ya bayyana ƙarfin sojojin Iran Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” a cikin ruwan Tekun Fasha ya bayyana Alamar da ƙarfin sojojin...
Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69...

Falasdinawa Sun Gudanar Da Bukukuwan Tarbar Fursunonin Falasdinawa 114 Da Aka Sako Daga Gidan Yarin Isra’ila
Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan...