2025-04-19@16:59:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 162

«Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta yi allawadai da kutsawar da firai ministan HKI da kuma ministan yakin sa Israel Kantz zuwa cikin sansanin yan gudun hijira na Tulkaram a yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa sojojin HKI sun kutsa cikin sansanonin yan gudun hijira na Palasdinawa a Tulkaram da kuma Jenin tana rusa gidajen falasdinawa tana kuma kora da kuma kashe wadanda suka samu a cikin gidajen nasu. A wani labarin kuma kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta yi allawadai da rushe-rushen gidajen da gwamnatin HKI take yi a yankin yamma da kogin Jordan.  Kungiyar ta yi kira da kasashen duniya...
    Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba. Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni. Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da...
    Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas zai saki fursunonin ‘yan sahayoniyya guda 6 a madadin fursunonin Falasɗinawa 602 A cikin tsarin yarjejeniyar musayar fursunoni na Ambaliyar Al-Aqsa da kuma a cikin kashi na bakwai na matakin farko na shirin musaya … za a sako wasu sabbin fursunonin Isra’ila guda 6 da suke hannun dakarun Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas, a ranar Asabar, tare da bayyana sunayensu. A sakamakon haka, mamayar za ta saki fursunonin Falasdinawa 602: Falasdinawa 50 daga cikinsu an yanke musu hukuncin daurin rai da rai ne, wasu 60 daga cikinsu kuma an yanke musu hukunci mai tsawo, da kuma fursunoni 47 na Wafa al-Ahrar da aka sake kama su, bayan zaman gidan yari a baya. Haka...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ca zata saki ‘yan Isra’ila shida yau Asabar a matakin karshe na yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko da ta cimma da Isar’ila. An kuma tsara Isra’ila za ta saki fursunonin falasdinawa Falasdinawa 602 a wannan Asabar a musayar wacce ita ce ta bakwai tun cimma yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu tsakanin Isra’ila da Hamas. Tun dai bayan cimma yarjejeniyar Hamas ta saki Isra’ilawa 22, a yayin da ita kuwa Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa sama da 1,100. A karshen matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta, za a yi musayar fursunonin Falasdinawa 1,900 da aka yi garkuwa da ‘yan Isra’ila  su 33 da suka hada da matattu takwas. Ana dai ci gaba...
    Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Shirye-shiryen Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
    Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da aka gudanar karkashin hadin gwiwarta da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da shirin samar da rigakafin cututtuka a kasashe masu tasowa(GAVI) a cikin shekaru uku da suka gabata. Haɗin gwiwar wanda aka fara shi da yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattaba hannu a shekarar 2022, an yi shi ne don haɓaka tsarin bada lafiya na jihar, da inganta tsarin rigakafi ta hanyar samar da kayan aiki da wadatattun ma’aikatan lafiya. A wajen mika kayan aikin da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, Gwamna Umar Namadi ya ce shirin ya bayar da gudunmawa musamman wajen samar da inshorar lafiya...
    Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za ta gudanar da bikin tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara karo na 11 a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu, 2025, a Bauchi, Jihar Bauchi. Taron, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Bauchi, zai girmama marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato kuma Firaministan tsohuwar Yankin Arewa. A bana, taken laccar shi ne “Arzikin Halitta: Juya Albarkatun Yankin Arewa Zuwa Ci Gaban Tattalin Arziki Mai Dorewa.” Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da albarkatun noma da ma’adanai da ruwa don bunkasa ci gaban tattalin arzikin...
    Jarin da kasar Sin ke zubawa wajen inganta lafiyar muhalli mai dorewa a duniya ya nuna muhimmiyar rawar da take takawa ta wannan fuskar. A shekarar 2024, kasar ta jagoranci duniya wajen zuba jarin sauya makamashi, inda ta zuba dalar Amurka biliyan 818 a wannan bangare. Wannan jarin ya sanya kasar Sin ta zama cibiyar samar da makamashi mai tsafta a duniya domin ita ke da kusan kashi 50 cikin dari na tasoshin samar da man “hydrogen” mara gurbata muhalli a duk duniya. Kasar Sin ta nuna wa duniya kyakkyawan misali abin koyi kamar yadda Shugaba Xi na kasar ke ci gaba da yayata muhimmancin kiyaye halittun doron kasa da kuma maye makamashi mai gurbata muhalli da mai tsafta. Shi...
    Kungiyar Hamas ta jinjinawa kungiyar tarayyar Afrika ta AU kan yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza bayan da kungiyar ta soki Isra’ila da keta dokokin kasa da kasa a jawabin rufe taron da ta yi na kwanaki biyu a Addis Ababa. Hamas ta ce tana matukar godiya da matsayin da kasashen Afirka suka dauka a kan Isra’ila da “mummunan” ayyukanta a Gaza. A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta AU ta ce tana adawa da keta dokokin kasa da kasa da kuma “kai hari kan fararen hula da kayayyakin more rayuwa da Isra’ila ke yi”. Kungiyar dai ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman...
    Iran ta bayyana cewa za ta aike da tawaga a matakin koli zuwa jana’izar mirigayi babban sakataren kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon Hassan Nasrallah. Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce kasar za ta halarci gagarumin bikin mai matukar muhimmanci, Tunda farko dai kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa tawagogin kasashe 79 za su halarci bikin tunawa da marigayi babban sakataren kungiyar Sayyid Hassan Nasrallah da kuma shugaban majalisar zartarwarta Sayyid Hashem Safieddine. Sheikh Ali Daher, kodinetan babban komitin jana’izar Nasrallah da Safieddine, ya bayyana cewa bikin da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Fabrairu, zai kasance “ranar tunawa da shugaban wanda aka zalunta a kan...
    Bangaren kungiyar Hamas da ke dauke da makamai ya tabbatar da shahadar wani daga cikin jami’in kungiyar a wani harin Isra’ila. Muhammad Ibrahim Shaheen, ya yi shahada ne a wani harin da wani jirgin yakin Isra’ila ya kai a Sidon. Kassam Brigades ta bayyana shi  a matsayin wanda ya yi tsayin daka kan zalincin Isra’ila, ciki har da lokacin yakin Gaza. Ita ma Isra’ila ta tabbatar da kashe jami’in na Hamas a harin da ta ce ta kai kan a Lebanon Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin ta sama a Sidon, inda suka ce sun kashe wani “dan ta’adda” Bafalasdine. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kokarin ganin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma...
    Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca. Tashar talabijin ta Presstv  na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a yankin yamma da kogin Jordan. Kungiyoyin sun bayyana cewa, wannan shi ne halin ta’addanci da kuma kekacewar zuciya yahudawan sahyoniyya. Daga karshe kungiyoyun sun yi kara da wadanda abin ya shafa su rika sanya ido sannan su aikata abinda ya dace don kawo karshen wahalar falasdinawa a gidajen yarin Ofer.
    Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Nan da wasu ‘yan makonni za a fara tilastawa Falasdinawa mazauna Gaza fara yin gudun hijira Ministan kudin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana tuntubar Amurka domin tattaunawa kan aiwatar da shirin shugaban Amurka Donald Trump na tsugunar da mazauna Zirin Gaza a wasu kasashe. A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila Smotrich ya furta cewa: Za a fara aikin kwashe mutanen daga Gaza nan da makonni masu zuwa. Smotrich ya ci gaba da cewa: Mazauna Gaza ba za su samu abin da suke nema ba a Gaza nan da shekaru goma zuwa goma...
    Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga kasarsu ta gado yana ci gaba da fuskantar tofin Allah da Allah wadai a duk fadin duniya da kuma a taruka daban-daban, kuma batun Falasdinu shi ne kan gaba a ajandar taron kolin Afirka karo na 38 da aka yi a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha. A yayin bude zaman taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki, ya yi gargadi game da kiraye-kirayen da ake yi na tilastawa Faladinawa gudun hijira, yana mai jaddada cewa ci gaba da tauye wa Falasdinawa ‘yancinsu abin kunya ne ga bil’Adama, yana mai sukar...
    Ƙasashen da suke da saukin cin hanci a duniya Mafi yawan kasashen da rahoton ya nuna cewa babu yawaitar matsalar cin hanci da rashawa suna a nahiyar Turai ne. Bakwai daga cikin kasashen 10 na farko, wadanda ba su da matsalar Rasha duk a yankin Tarayyar ta Turai suke. Qasar da ta fi kowace a duniya samun maki a bangaren yaki da rashawa ita ce Denmark, wadda take da maki 90. Sai kuma Finland mai maki 88, ta uku kuma ita ce Singapore, wadda ke a kudu maso gabashin nahiyar Asiya. Ga yadda kasashen 10 na farko suka kasance: 1. Denmark – Maki 90 2. Finland – Maki 88 3. Singapore – Maki 84. 4. New Zealand – Maki 83....
    kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika wasu ‘yan Isra’ila uku da ta yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross a wani musayar fursunonin da aka sako Falasdinawa 369 a wata musanya ta baya-bayan nan a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. An saki ‘yan Isra’ilan uku a birnin Khan Yunus da ke kudancin Gaza, inda Isra’ilawan suka yi jawabi ga jama’a kafin mika su ga kungiyar agaji ta Red Cross. Sakin dai shi ne na shida tun bayan da tsagaitawar ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu bayan fargabar da ake yi a makon da ya gabata cewa yarjejeniyar ta kusa rugujewa bayan da Isra’ila ta ki ba da isassun kayan agaji a Gaza. Yawancinsu...
    Sojojin HKI sun kaseh Falasdinawa 4 a yankin yamma da kogin Jordan a lokacinda suke fadada hare-haren da suke kaiwa kan falasdinawa wanda kuma yake daukar rayukar Falasdinawa a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar WAFA ta falasdinwa wacce ta nakalti majiyar ma’aikatar kiwon lafiya a yankin tana cewa sojojin yahudawan sun kashe Adel Abdel Bashkar a sansanin yan gudun hijira na Askar a kusa da garin Nablus bayan albarusai sun sameshi a kirjinsa. Labarin ya kara da cewa bayan an kai shi asbine sai yace ga garinku, ko kuma yayi shahada. Har’ila yau majiyar ta kara da cewa Falasdinawa matasa uku ne suka yi shahada a lokacinda sojojin yahudawan suka kai hari a sansanin...
    Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira a ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu. Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Dage ziyarar ya zo ne domin shugaban kasar Masar ya shirya irin martani da zai mayar wa takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa hangen nesa da ke samun cikakken goyon bayan Larabawa kan shirin shugaban Amurka...
    Kungiyar Hamas ta yi kira ga ƙungiyoyin duniya da su fitar da matsayinsu a ranakun Juma’a da Asabar da kuma Lahadi don yin watsi da batun neman tilastawa Falasdinawa yin hijira daga Zirin Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kira ga al’ummar Falastinu, al’ummar Larabawa da al’ummar musulmi da dukkan ‘yantattun kasashe a duk fadin duniya da su fito domin gudanar da gagarumar zanga-zanga da tarukan goyon bayan al’ummar Falasdinu gami da hadin gwiwa a dukkanin birane da wuraren taruwar duniya, domin jaddada yin watsi da yin Allah wadai da shirin korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Laraba ta ce: Ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi masu zuwa...
    Gwamnatin Washington, ta sanar da cewa nan ba da jimawa ba shugaban kasar Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, zasu fara tattaunawa kan batun Ukraine da nufin tsagaita wuta don kawo karshen yakin da kasashen biyu ke yi ta hanyar tattaunawa. Shugaban na Amurka ya sanar a ranar Laraba cewa ya yi doguwar tattaunawa da takwaransa na Rasha, kuma shugabannin biyu Shugabannin biyu sun shirya ganawa a karon farko a kasar Saudiyya. Donald Trump da Vladimir Putin sun amince su “yi aiki tare sosai” tare da fara tattaunawa “nan da nan” kan Ukraine. Kremlin ta tabbatar da cewa tana son “magance rikicin Ukraine ta hanyar “tattaunawar zaman lafiya”. Tattaunawar ta wayar tarho tsakanin Donald Trump da Vladimir Putin...
    An bude babban taron majalisar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka, watau AU karo na 46, a hedkwatar kungiyar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda taron ya jaddada bukatar gaggauta karfafa kokarin da ake yi na bunkasa ci gaban nahiyar, da kwanciyar hankali. Taron na kwanaki biyu, wanda ya kunshi ministocin harkokin waje na mambobin kungiyar ta AU, ana gudanar da shi ne a karkashin taken da kungiyar ta AU ta fitar na shekarar 2025 : “Adalci ga ‘yan Afirka ta hanyar biyan diyya.” Da yake jawabi a wajen taron, shugaban hukumar kula da harkokin AU, Moussa Faki Mahamat, ya jaddada muhimmancin samar da kokarin hadin gwiwa domin inganta zaman lafiya da tsaro a fadin nahiyar. Ya kuma bayyana wajibcin gudanar da shugabanci nagari, da...
    Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya na cewa rashin halartar kasashen Rasha da China a cikin duk wata tattaunawa dangane da shirin Nukliyar kasar Iran, zai kawo gibi mai yawa a harkokin siyasa da tsaro a yankin Asiya. Jami’in diblomasiyyan ya kara da cewa kasahen yamma suna son maida kasashen biyu gefe a cikin tattaunawar, a yayinda kasancewarsu a cikin taron yana da matukar muhimmanci saboda al-amarin zai shafi yankin gaba...
    Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu idan har Hamas ba ta sako fursunonin yahudawan sahayoniyyar Isra’ila kafin yammacin ranar Asabar ba. A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa cimmawa ta hanyar wuce gona da iri, ba zai yi nasara ba ta hanyar aiwatar da siyasar makirci da yaudara. Sanarwar ta ce, manyan al’ummar Gaza sun tsaya tsayin daka wajen fuskantar...
    Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya gargaɗi Hamas da ta yi gaggawar sakin Isra’ilawan da take tsare da su a hannunta. Netanyahu ya ce ya bai wa ƙungiyar wa’adin zuwa ranar Asabar da ta saki Isra’ilawan da take garkuwa da su kamar yadda aka amince a yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu ta tanada. Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman ‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’ Netanyahu ya ce ya yi ganawa ta awa huɗu da majalisar yaƙinsa inda kowa ya bayyana kaɗuwa da halin da mutane uku da Hamas ta saka ranar Asabar suka kasance. “Dukkanin mu mun yi maraba da buƙatar shugaba Trump na sakin mutanen zuwa ranar Asabar da...
    Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa dari a kan na shekarar 2023. Kasashen da ke kan gaba, wadanda aka kai wa motocin na kasar Sin sun hada da Rasha da Mexico da Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin da kasashen da suka ingiza ci gaban da Sin ta samu wajen fitar da motocin suka hada da Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa da Brazil da Belgium da Saudiyya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar da kiran taron kasahen larabawa a karshen wannan watan na Febrairu da ake ciki domin tattauna batun tilasta wa Falasdinawa yin hijira daga Gaza a karkashin shirin Amurka da Isra’ila. Da safiyar yau Lahadi ne dai ma’aikatar harkokin wajen ta Masar ta bayyana cewa za ta karbi bakuncin taron kungiyar kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan nan na Febrairu,domin tattauna sabbin batutuwan da su ka taso dangane da Falasdinu. Har ila yau sanarwar ta ce, Masar din ta yi wannan gayyatar ne bayan tattaunawa da kasar Bahrain wacce a halin yanzu take rike da shugabancin kungiyar kasashen Larabawan, haka nan kuma tuntubar babbar shalkwatar kungiyar. Bugu da kari Masar din ta sanar...
    Kungiyar kasashen musulmi  ( OIC) ta fitar da bayani da aciki ta yi tir da maganganun shugaban kasar Amurka Donald Trump akan fitar da mutanen  Gaza. Kungiyar ta OIC ta bayyana cewa; maganganun na shugaban kasar Amurka suna a matsayin goyon bayan ‘yan mamaya, masu mulkin mallaka domin kwace kasar Falasdinawa da hakan yake a matsayin take dokokin kasa da kasa da kudurorin MDD da su ka hada da kwamitin tsaro na wannan Majalisar mai lamba;2334. Haka nan kuma bayanin na kungiyar kasashen musulmin ya ce, abinda Trump ya furta zai iya hana zaman lafiya wanzuwa a cikin wannan yankin. Wani sashe na kungiyar kasashen musulmin ya bayyana kin amincewa da duk wani yunkuri na sauya tsarin iyaka da mutane...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina. Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya. Ya ce,...
    Iran ta bukaci taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta OIC, game da shirin shugaba Donald Trump na Amurka na kwace Gaza da kuma korar al’ummar Zirin. Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa haramtaccen shirin” na shugaban kasar Amurka kan Gaza ya gamu da kakkausan ra’ayi daga kasashe daban-daban, inda ya yi kira da a gudanar da taron gaggawa na ministocin kungiyar ta OIC domin tattaunawa da yanke shawara kan wannan batu. A wata tattaunawa daban daban ta wayar tarho da wasu takwarorinsa a yammacin jiya Asabar ministan harkokin wajen na Iran Sayyid Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Masar Badr Abdel-Aty, Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da Isra’ila “tana cikin hadari” kuma “zata iya rugujewa,” Bassem Naïm, ne wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar, ya bayyana hakan ga kamfanin AFP, yayin da tattaunawar da ake yi kan mataki na biyu na tsagaita bude wuta, da ya kamata a fara ranar Litinin, ke ja da baya ba kamar yadda aka fara ba inji shi. Da yake zargin Isra’ila da “jinkiri” wajen aiwatar da kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta na makonni shida, wanda ya fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, Bassem Naim ya yi gargadin cewa wannan lamarin ya jefa yarjejeniyar cikin hadari kuma zata iya haifar da rugujewarta....
    “Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a jihar Zamfara, musamman wadanda suka kawo cikas ga cimma burin da aka sanya a gaba. Duk da haka, muna samun ci gaba yayin da ake fuskantar ƙalubalen, kuma abubuwa suna komawa daidai.” “Mun inganta matakan tsaro ta hanyar kwararan matakai da jihar ta dauka na inganta tsaro da kara daukar matakan dakile barazanar tsaro.” “Gwamnatinmu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta...
      Mata a Karamar Hukumar Danja suna kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta gyara hanyar Tsangamawa a Babban Rafi saboda yawan rasuwar mata masu juna biyu da jariransu.   Sun yi wannan kira ne a yayin wani taron gaggawa da manyan jiga-jigan al’umma suka shirya domin tattauna matsalar da ta dade tana addabar jama’a – hanyar Tsangamawa.   Hanyar Tsangamawa da ke Babban Rafi, Karamar Hukumar Danja, Jihar Katsina, ta haddasa mutuwar mata masu juna biyu da jariransu, musamman a lokacin damina.   Duk da yawan koke da rokon gwamnati, har yanzu ba a dauki matakin gyara hanyar ba.   A wata hira da suka yi da Radio Nigeria, wasu daga cikin matan yankin sun bayyana cewa mata masu...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya gana ta tawagar shoura ta kungiyar Hamas a safiyar yau Asabar a nan Tehran inda ya bayyana cewa mayakan kungiyar sun sami nasara a kan Amurka da HKI a yakin da suka dora masu na tsawon watanni 15. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Imam Sayyid Aliyul Khaminae yana cewa tsagaita wuta da aka samu bayan wannan lokaci mai tsawo na fafatawa yayi dai-dai. Tawagar shuraa ta Hamas din dai sun hada da shugaban riko na kungiyar Khalil Al-Hayya, shugaban majalisar shoora ta kungiyar Muhammad Ismail Darwish da sauransu. Jagoran ya kara da cewa nasarar da mutanen Gaza suka samu a kan Amurka da kawayenta misdaki nan a...
    Yau Asabar shugabannin kasashen raya tattalin arzikin kasashen Gabashi da Kudancin Afrika EAC da SADC za su gana a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya domin tattauna rikicin gabashin DRC. Shugaban kasar Kenya, William Ruto, dake jagorantar kungiyar EAC, ya sanar da halartar takwarorinsa na Congo da Rwanda. Tun da farko a ranar Juma’a, ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun gana domin samun nasarar wannan tattaunawar, inda fadar shugaban kasar ta Kwango ta gabatar da bukatunta da suka hada da : tsagaita bude wuta nan take, janyewar dakarun M23 da na Rwanda daga yankin Congo, da sake bude filin jirgin saman Goma, da mayar da birnin ga hannun halastattun hukumomi. A ranar Juma’a, a wani taro a Malabo, Kungiyar...
    Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa. Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta Borno zuwa Kasuwar Garkida ta jihar Adamawa. “Ana zargin cewa ’yan Boko Haram ne suka dasa bama-baman, kuma motar da ke jigilar mutanen kauyen zuwa kasuwa a Garkida ta taka ta kuma ta fashe. “Wani dan shekara 25 ya mutu nan take, amma sauran fasinjojin an garzaya da su asibiti domin yi musu magani,” inji shi. Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wata tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a safiyar yau Juma’a a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan tunawa da kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci. Taron na yau ya zo daidai da zagayowar kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci, kuma taron tunawa da mubaya’a mai dimbin tarihi ga Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) a ranar 8 ga watan Fabrairun shekara ta 1979. Don haka a safiyar...
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na korar Falasdinawa daga zirin Gaza karkashin dabarar gudun hijira. Tajani ya bayyana cewa: Ba za a tilastawa Falasdinawan shiga kowane irin zabi ba, yayin da yake magana kan shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na neman kwace yankin Zaga. A cikin wani yanayi mai alaka da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya bayyana rashin amincewarsa da shawarar da...
    A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe, yayin da rahotanni ke cewa faɗa na kara yaɗuwa zuwa wasu sassan ƙasar, sannan take hakkin ɗan’adam na ƙara munana. Jakadan Congo a Geneva ya ce gwamnatin ƙasar na buƙatar MDD ta gudanar da cikakken bincike kan hakan. Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun yi amannar cewa ƴan tawayen M23 da sojojin Rwanda da na Congo duk sun aikata munanan laifuka. Sai dai har yanzu Rwanda...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, wani jami’in kungiyar wanda baya son a bayyana sunansa ya ce kungiyar a shirye take a fara tattaunawar.. A wannan tattaunawa dai ana saran za’a fayyace filla-filla kan yadda al-amura zasu kasance a nan gaba a zirin gaza. Labarin ya kara da cewa jami’an Hamas sun bayyana haka ne a ranar da aka yi musayar fursinoni da HKI a garin Khan Yunus....
    Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI. Yace dukaninsu...
    Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.
    Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar. Labarin ya kara da cewa taron ya sami halattar ministocin harkokin waje na kasashe Masar, Jordan, Saudia, Qatar, da gwamnatin Palestinian Authority, sannan da wakilia daga sauran kasashen kungiyar ta ‘Arab League’ . Kungiyar ta bayyana cewa kasashen kungiyar basy amince da duk wani kokari na canza yadda kasashen larabawa suke ciki don tabbatar da samuwar HKI a yankin ba, kamar...
    Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
    Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana kan zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake masa tambayoyi. Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya Zaftarewar ƙasa ta kashe mata masu haƙar zinare a Mali Garba wanda ɗan asalin garin Tappare Kona Uku ne a ƙaramar hukumar Jada ta jihar, ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan rasuwarsa. Shekara guda bayan binne shi,...
    Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin ya gagara. Sau hudu gwamnonin jihar daban-daban suna sa wa’adin kammalawa da kaddamar da wannan katafaren asibiti, ba tare da haka ba ta cimma uwa ba. A shekarar 2007 tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Namadi Sambo tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci na Duniya suka assasa aikin ginin asibitin da wa’adin kammala shi a cikin shekara biyar, wato 2012. An yi fatan zai kasance...
    Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu. Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za ta sako su ne Ofer Kalderon da Keith Siegel da kuma Yarden Bibas. Hakan na zuwa ne bayan a cikin dare jiragen yakin Isra’ila sun kashe Palasdinawa 10 a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke garin Tammun da ke yankin Yammacin Kogin Jordan. Kazailka ’yan sandan Isra’ila sun kama Palasdinawa 12 a yankin Gabashin Birnin Kudus a yayin da suke murnar sako ’yan...
    Kungiyar Hamas ta yaba da rawar da Iran ke takawa wajen tallafawa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yanci kai Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da wata tawaga daga jagororin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, karkashin jagorancin shugaban majalisar gudanarwa (wanda aka kafa bayan kisan jagoran kungiyar Yahya Sinwar) Mohammed Darwish, a babban birnin Qatar, Doha a jiya Alhamis. Sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta bayyana cewa, tawagar kungiyar ta hada da shugabannin Khalil Al-Hayya, Hussam Badran, Izzat Al-Rishq da Basem Na’im. Darwish ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tallafa wa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yancin kai, yana mai jaddada cewa: “Harin Daukan Fansa naAmbaliysar Al-Aqsa Mai Albarka” wani ci gaba ne a yunkurin al’ummar...
    Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan mamayar Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan sahayoniyya, tare da yin nuni da cewa, za ta ci gaba da kokarinta ba tare da wata matsala ba, domin kubutar da su ta kowace hanya. Kungiyar Hamas ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a a yayin bikin sakin wani sabon rukunin fursunonin Falasdinu, tana jaddada cewa: Hamas ta sake sanar da babban alfahari da girmamawa ga al’ummar Falastinu masu tsayin daka,...
    Isra’ila ta dakatar da sakin fursunonin Palasɗinawa ba zato ba tsammani yayin da ake ci gaba da musayar fursunoni da waɗanda aka kama ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, a cewar rahoton Army Radio. Hukumomi ba su bayyana dalilin dakatarwar ba, kuma babu tabbas kan lokacin da za a ci gaba da tsarin. Wani Ɗan Pakistan Ya Kashe ‘Yarsa Kan Ɗora Bidiyon Kanta A TikTok Hisbah Ta Kama Matashi Da Matashiya Kan Yin Aure Saɓanin Dokokin Musulunci A Kano Yarjejeniyar tsagaita wutar an ƙulla ta ne don bayar da damar musayar fursunonin da Hamas ke riƙe da su da kuma waɗanda ke tsare a Isra’ila. Sai dai wannan matakin ba zato ba tsammani ya haifar da rashin tabbas kan ci...
    Kungiyar fursunonin Falasdinu ta ce za a sako wasu karin Falasdinawa 110 daga gidajen yarin Isra’ila a yau Alhamis a mataki na uku na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas. Ana sa ran galibin Falasdinawan da aka ‘yantar za su isa yankin Radana na Ramallah da ke yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye da misalin karfe 12:00 na safe agogon kasar, in ji kungiyar fursunonin Falasdinu. Wannan ba zai hada da fursunoni 20 da za a tura gudun hijira a wajen Falasdinu ba. Kungiyar ta kuma fitar da jerin sunaye da shekarun fursunonin da za a saki wadanda suka hada da akalla yara 30. Sakin da za’ayi wa Falasdinawan 110 a yau zai sanya...
    Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga  Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa.  Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20  da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
    Bikin bazara shi ne biki mafi dadewa da muhimmanci a bukukuwan gargajiya na Sin. Kuma bikin na ci gaba da kara bazuwa da samun karbuwa a fadin duniya. A kwanakin baya-bayan nan, kasashe da hukumomin kasa da kasa da dama sun gudanar da shirye-shirye da nune-nunen dake da alaka da bikin bazara, kuma jama’a a fadin duniya sun hadu domin a dama da su cikin bikin murnar sabuwar shekarar ta Sin. A wannan lokaci, 1 bisa 5 na al’ummar duniya ne ke murnar bikin ta mabanbantan hanyoyi, lamarin da ya mayar da bikin bazara zuwa wata al’adar gargajiya ta duniya tare da inganta fahimta da abota tsakanin jama’ar dukkan kasashe. Alkaluman Watsa Shirye-Shiryen Shagalin Bikin Bazara Na CMG Na 2025...
    Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi,” in ji sanarwar, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 47,000 tare da lalata wargaza yankin Falasdinawan. An bayyana cewa sama da kashi 90%, yankin ya lalace sakamakon hare haren Isra’ila. An ruguza duk wasu wurare da cibiyoyi masu matukar mahimmanci kama daga asibitoci, makarantu, gidajen jama’a wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki. A yanzu Falasdinawan dake komawa wannan yankin...
    An tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon na tsawon kimanin makonni uku bayan da gwamnatin kasar ta ki janye dakarunta kamar yadda aka kulla da farko. An bayyana cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025. Shi ma firaministan kasar Labanon Najib Mikati ya tabbatar da tsawaita wa’adin, yana mai kara da cewa Lebanon za ta mutunta hakan. Bisa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanar tsakanin Isra’ila da Hizbullah a watan Nuwamba, a jiya ne ya kamata sojojin Isra’ila su fice daga kudancin Lebanon. “Gwamnatin Lebanon ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta har zuwa ranar 18 ga Fabrairu, 2025,”...
    Harkar Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa Da Tawagar Sin A MDD Ta Shirya Ta Nuna Al’adun Gargajiya
    Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
    Kungiyar kwamishinonin kudi ta kasa ta jinjinawa kokarin gwamnatin jihar Jigawa na bunkasa Ilmin ya’ya mata. Shugaban kungiyar kuma kwamishinan kudi na jihar Ekiti, Mr Akim Oyebode ya bayyana hakan a lokacin da suka ziyarci Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnati dake Dutse. Mr Akim Oyebode ya ce kungiyar tana alfahari da ayyukan raya kasa da Gwamna Umar Namadi ya aiwatar tun hawansa karagar mulki, a sassan jihar ta Jigawan. Yana mai cewar sun ziyarci jihar Jigawa ne domin yi wa Gwamnan ta’aziyyar rashin da aka masa. A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya yaba musu bisa wannan ziyara tare da fatan za su koma jihohinsu lafiya.   Usman Mohammed Zaria
    Majalisar dokokin jihar Jigawa ta jaddada aniyar ta na hada kai da ofishin kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF domin samun nasarar aiwatar da tsare-tsare da za su inganta rayuwar yara da marasa galihu a jihar.   Mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Sani Isyaku Abubakar, ya bada wannan tabbacin lokacin da ya karbi bakuncin tawagar ofishin UNICEF na Kano karkashin jagorancin Hajiya Fatima Adamu.   Ya lura cewa irin wannan haɗin gwiwa tsakanin majalisa, Action Against Hunger da Save the Children International sun haifar da sakamako mai kyau ta hanyar tallafawa matakan majalisa ta hanyar fasaha da ba da shawara don tsara manufofin da sauran tsare-tsaren a Jigawa.   Alhaji Sani Isyaku Abubakar ya bada tabbacin ci gaba...