2025-04-16@04:42:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 359

«Wannan yana»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan sabuwar dokar da ta hana ‘yan wasan da sukai sauyin jinsi (transgender) shiga wasannin mata. Ya bayyana cewa wannan dokar zata kawo ƙarshen “cece ku ce da ake yi kan wasannin mata” tare da tabbatar da kariya ga ‘yan wasa mata daga fuskantar rashin adalci. A dokar Trump na neman a dakatar da makarantu daga samun tallafin gwamnati idan suka bari ‘yan wasan transgender su taka leda a ƙungiyoyin mata. Sin Ta Sanar Da Daukar Matakan Mayar Da Martani A Kan Karin Harajin Amurka Sin Za Ta Mai Da Martani Kan Dukkanin Cin Zalin Ciniki Da Aka Yi Mata Haka zalika, Trump ya shirya matsa wa ƙungiyar wasannin Olympics ta duniya...
    Kasashen larabawa masu kawance da Amurka sun kasance a sahun gaba wajen mayarwa da shugaban kasar Amurkan martani, bayan da ya bayyana cewa kasarsa za ta shimfida ikonta a Gaza, bayan fitar da Falasdinawa da Gaza. Gabanin wannan sanarwar ta  Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ya tuntubi kasashen Jordan da Masar masu makwabtaka da Falasdinu da su karbi bakuncin mutanen Gaza na wani lokaci har zuwa sa’adda za a gyara wajen. Masar da Jordan sun yi watsi da wannan shirin da suke dauka a matsayin wata dabara ce ta fitar da Falasdinawa daga cikin kasarsu, da maye gurbinsu da yahudawa ‘yan share wuri zauna. A wani bayani da kungiyar hadin kan Larabawa ta fitar ta bayyana cewa; Abinda  Trump...
    A wani umurnin da ya bayar Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Alilul Khami’nae ya sanya babban sakataren kungiyar Hizbullah a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Bayan shahadar Sayyed Hassan Nasarallah da kuma Sayyed Hashim safiyuddeen An zabi sheikh Na’em Kasim a matsayin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah a kasar Lebanon. Kafin haka dai Shahid Sayyed Hassan Nasarallah ne mai wakiltar jagoran a kasar ta Lebanon. Sheikh Qasim dai  ya taka rawar a zo a gani  wajen yakin da kungiyarsa ta shiga da HKI na watanni 15.. Kuma ana saran shi ne zai zama mai fitar da kungiyar zuwa tudun na tsira daga halin da ta shiga ciki ya kuma ci gaba da yakar kungiyar.
    Kamfanin hakar ma’adinai na Jiuling Lithium, na kasar Sin, na shirin zuba jarin sama da dala miliyan 200 a domin haƙar lithium a Endo da ke jihar Nasarawa. A ziyarar da gwamna Abdullahi Sule ya kai, shugaban kamfanin, Mista Xiong Jin, ya jaddada aniyarsu ta gina daya daga cikin manyan masana’antar samar da lithium a jihar. Ya kuma bayyana cewa ma’aikatan da aka dauka aiki a wurin za su sami mafi karancin albashi na N500,000. Saurayi Ya Fille Kan Budurwarsa A Nasarawa Gwamna Sule Ya Rushe Majalisar Zartarwar Nasarawa, Ya Sauke Sakataren Gwamnati Gwamna Sule ya bukaci matasa da su rungumi sana’o’in hannu domin cin gajiyar guraben ayyukan yi a fannin hakar ma’adinai. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya nada Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Marigayi Sayyid Hassan Nasrullahi tsohon babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ya yi shahada, a yakin baya-bayan nan kan kasar Lebanon, shi ne tsohon wakilin mai martaba Imam Khamenei a kasar Lebanon kafin shahadarsa.
    Shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya sanar da tsawaita wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025 zuwa ranar 10 ga Fabrairu, 2025. Karin wa’adin na zuwa ne biyo bayan koke-koke da aka kai wa hukumar na a kara wa maniyyatan da suka gaza kammala biyan kudinsu a kan lokaci. Nijeriya Na Iya Fuskantar Ƙarancin Maniyyata A Hajjin Bana EFCC Ta Gurfanar Da Manajan Darakta Kan Damfarar ₦144m A Gombe Farfesa Usman ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da ya gudana a manhajar ‘Zoom’ a ranar Talata 4 ga watan Fabrairu, 2025, tare da masu ruwa da tsaki a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji. Shugaban Hukumar NAHCON ya yi kira ga Sakatarorin...
      Yayin da Hukumar Kula da Hajji ta Kasa ta kara wa’adin biyan kudin Hajjin bana zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta umarci dukkan ofisoshin da suke alhakin yin rajista su tabbatar da an yi wa duk masu sha’awar tafiya Hajji rajista kafin ƙarshen wa’adin da aka ƙara.   Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ya kuma yi kira ga dukkan maniyyatan da ba su kammala biyan kuɗinsu ba da su gaggauta yin hakan.   Ya jaddada cewa ba za a ƙara wa’adin bayan ranar 10 ga Fabrairu ba, don haka ya bukaci maniyyata su yi amfani da wannan damar su kammala rijistarsu kafin ko zuwa Litinin, 10 ga Fabrairu, 2025.   Rel/Adamu...
    Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar mafarauta sun kashe wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a Dajin-madan, da ke karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi. Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a safiyar ranar Laraba, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce an kashe ‘yan bindigar ne ta hanyar amfani da bayanan sirri da hadin gwiwa da masu sa ido da ke cikin al’ummomin da abin ya shafa. Tinubu Ya Amince Da Naira Biliyan 80 Domin Sake Gina Madatsar Ruwa Ta Alau Da Ke Borno Masana Kimiyyar Sin Sun Kirkiro Sabuwar Fasahar AI Mai Hasashen Zuwan Mahaukaciyar Guguwa Ya kara da cewa, bayan artabun, wasu daga cikin ‘yan bindigar sun tsere da raunukan harbin...
    Kungiyar Hizbullah ta fitar da wani bayani a jiya Talata da ta yi Allawadai da takuhkumin da kasar Australia ta kakaba wa babban sakatarenta Sheikh Na’im Kassim. Bayanin na kungiyar Hizbullah ya kunshi cewa; Matakin, yana sake nuni ne da hakikanin fuskar wannan kasa da a kowace rana take tabbatar da cewa, ita makami a hannun Amurka da Isra’ila. Hizbullah ta kuma bayyana matakin da cewa na zalunci ne wanda bai jingina da kowane irin dalili na shari’a da halayyar kwarai ba, yana nuni ne kai tsaye da cewa; Suna goyon bayan HKI ne da kuma kare laifukan da take tafkawa da ta’addancinta, tare da yin kira cewa kamata a yi ace kasar ta Australia da ta dauki matakai ne...
    Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima. Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban. Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma...
    Babban wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong, ya gudanar da taron manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York, jiya Litinin bisa agogon birnin, domin gabatar da muhimman tsare-tsare na wa’adin shugabancin kasar Sin a kwamitin sulhu, na wannan wata. A cewar Fu Cong, a yayin wa’adin shugabancin kwamitin sulhu na MDD a watan nan, kasar Sin za ta mai da hankali kan ra’ayoyin bangarori daban-daban da gudanar da tsarin mulkin duniya, da kula da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma yanayin da ake ciki a wasu kasashen Afirka. Da aka tambaye shi game da samfurin kirkirarriyar basira ta DeepSeek, wanda wani kamfanin kula da fasahohin kirkirarriyar basira na kasar Sin ya fitar,...
    A kwanan baya, kasar Amurka ta kakaba wa kayayyakin kasar Sin da ake neman shigar da su cikin kasuwanninta karin harajin kwastam na kaso 10%, bisa dalilin wai Sin na sayar da magani mai suna Fentanyl a kasar. Hakika maganar Fentanyl din wani batu ne da kasar Amurka ta dade tana kokarin ruruta shi, inda wasu ‘yan siyasar kasar ke neman dora laifin yadda mutanen kasar ke amfani da maganin a matsayin miyagun kwayoyi kan kasar Sin, cewa wai “Sin na samar da sinadarin hada maganin Fentanyl, wanda aka sarrafa shi zuwa miyagun kwayoyi a Mexico, tare da kai su cikin Amurka”. Sa’an nan Amurka ta fake da wannan dalili tana kakaba wa kamfanonin Sin takunkumi, har ma ta kaddamar...
    Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI. Yace dukaninsu...
    A yayin da aka bude wasannin lokacin sanyin na Asiya karo na 9 a birnin Harbin na arewacin kasar Sin a ranar Litinin ta hanyar gabatar da tseren kunna fitila, mai dauke da fitilar, kuma mamban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC), Yu Zaiqing, ya bayyana cewa, gasar za ta sa kaimi ga kara yawan wasannin lokacin sanyi a nahiyar Asiya. Yu ya kara da cewa, tseren fitilar na dauke da ruhin Olympics, wanda ke sanya karin mutane samun zurfin fahimtar wasannin, yana mai cewa, wannan shi ne karo na biyu da Harbin ya karbi bakuncin wasannin lokacin sanyi na Asiya, bayan na karo na 3 da ya gudana a shekarar 1996. Ana matukar sa ran samun ingantattun...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke da goyon bayan al’ummar Siriya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i ya tabbatar a yau Litinin, a taron manema labarai na mako-mako cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke samun goyon bayan al’ummar Siriya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya gudanar ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu dangane da batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa da kuma huldar diflomasiyyar Iran. Baqa’i ya tabo batun ziyarar da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya kai zuwa kasar Qatar, inda ya bayyana cewa ziyarar ta zo ne bisa tsarin alakar diflomasiyya ta al’ada tsakanin kasashen biyu....
    Hukumar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA ta ce an yi wa wani mutum mai shekara 59 tiyata domin ciro sunƙin hodar ibilis 57 cikin guda 81 da ya haɗiye kwanaki bakwai da suka gabata a Addis Ababa da ke kasar Habasha. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ta ce an kama mutumin ne a lokacin da ake tantance fasinjoji bayan isar su filin jirgin sama na Murtala Muhammad daga Habasha a ranar 26 ga watan da ya gabata. Kakakin hukumar ya ce bincike ya gano cewa mutumin wanda ya yi iƙirarin ɗan kasuwa ne a yankin Oshodi da ke jihar Lagos, ya tafi Addis Ababa inda ya haɗiyi sunƙi...
    Shuwagabannin kasashen turai guda uku wato EU3 sun bayyana cewa daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar ya fi karfinsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran yana fadar haka a wata hira ta musamman da ta hada ta da tashar. Mohammad Eslami ya ce kasashen turan guda uku wadanda suka hada da Jamus, Faransa da Ingila sun aiko masa da sako inda suke tabbatar haka. A cikin shugaban Muhammad Eslami ya fadawa tashar talabijan ta Presstv irin ci gaban masu yawa wadanda JMI ta samu a cikin shekarun da suka gabata. Shugaban ya kara da cewa sakon da EU3 ya nuna irin yadda rikicin shirin Nukliyar kasar Iran...
    Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan gaba daya. Francesca Albanese ta bayyana haka ne a shafin ta na X, a jiya Lahadi, ta kuma yi kira ga kasashen duniya su shigo cikin al-amarin don kawo karshen kisan kare dangi da kuma rusa gidajen Falasdiwa da ta fara a yankin Jeneen. Daga karshe Jami’ar ta MDD ta bayyana cewa a halin yanzu kissan kiyashi da rushe-rudhen gidajen falasdinawa bai tsaya kan Gaza...
    Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta cafke wasu matasa a yankin Sheka bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, yana mai cewa rikicin ya fara ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Yusuf Aminu, ɗan unguwar Sheka Babban Layi, wanda ake zargi da aikata fashi da sauran laifuka. Dabaru Irin Na Sin A Kan Daidaita Harkokin Duniya A 2024 An Yi Taro Don Tattauna Dabarar Aiwatar Da Shawarar Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya A MDD Rahotanni sun nuna cewa marigayin mamba ne na ƙungiyar ‘Yan Shida,’ wacce ta addabi yankin Sheka da aikata fashi da tashin hankali. Wasu mazauna unguwar sun kama shi, suka kakkarya masa ƙafa tare da...
    Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow. Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Ukraine da aka dakatar a yakin da ake yi da Rasha, suna bukatar a gduanar da su. “Yawancin kasashen dimokuradiyya suna gudanar da zabe a lokacin yakinsu. Ina ganin yana da mahimmanci su yi haka,”in ji Kellogg. Kamfanin dillancin labaran reuters ma ya rawaito wasu jami’an fadar White House sun tattauna batun matsawa...
    A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
    Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909.   Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14.   Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001).   Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56.   Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949).   Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960).   Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021).   Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
    Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar. Labarin ya kara da cewa taron ya sami halattar ministocin harkokin waje na kasashe Masar, Jordan, Saudia, Qatar, da gwamnatin Palestinian Authority, sannan da wakilia daga sauran kasashen kungiyar ta ‘Arab League’ . Kungiyar ta bayyana cewa kasashen kungiyar basy amince da duk wani kokari na canza yadda kasashen larabawa suke ciki don tabbatar da samuwar HKI a yankin ba, kamar...
    Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke samun horo a sansaninsu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Darakta Janar na NYSC wanda ke rangadi a sansanin masu yi wa kasa hidimar a jihar Zamfara, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ak tsaurara matakan tsaro a sansanin. Ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin matasan na da matukar muhimmanci ga hukumar. Birgediya Janar Ahmad ya jaddada bukatar...
    Har ila yau ya ce, idan aka yi maganar mukaman da gwamnatin tarayya da ta jihohi suka bai wa wasu daga cikinmu, ba yana nufin cewa; an taimaki masana’antar ba ne, domin kuwa; mafi yawancin wadanda suka samu wadannan mukamai, babu wani ci gaba ko hobbasa da suka yi wajen ciyar da Masana’antar Kannywood gaba. Musa ya ce, illa kawai dai suna taimakon kansu da kuma na kusa da su, wanda kuma ba haka ya dace a ce suna yi ba, dalili kuwa shi ne, har yau babu wani daga cikin masana’antar tamu da ya taba samun wani mukamin gwamnati, ya taimaka wa ita kanta masana’antar, illa kalilan daga cikinmu. A bangaren abokanan fada kuwa a Masana’antar Kannywood, Mai Sana’a...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kaddamar da sabbin na’urori masu linzami da na tsaro Babban sakataren rundunar da ke sa ido kan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya sanar da kaddamar da wasu sabbin na’urori masu linzami da na tsaro a cikin tsarin baje kolin “Malik Ashtar”, wanda za a gudanar a ranar Litinin mai zuwa a kasar. Birgediya Janar Hamid Bazmashahi ya kara da cewa a wani taron manema labarai a yau Asabar, za su yaye shamakin makaman dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kare karfinsu bisa tsarin baje kolin. Ya yi nuni da cewa, baje kolin zai hada da, a karon farko, baje kolin jami’an tsaron da ke sintiri da jiragen ruwa...
    Yadda aka raba jadawalin AFCON 2025: Rukunin farko: Morocco, Mali, Zambia, Comoros — Rukuni na biyu: Egypt, South Africa, Angola, Zimbabwe—- Rukuni na uku: Nigeria, Tunisia, Uganda, Tanzania Rukuni na hudu: Senegal, DR Congo, Benin, Botswana Rukuni na biyar: Algeria, Burkina Faso, Ekuatorial Guinea, Sudan Rukuni na shida: Cote d’Iboire, Cameroon, Gabon, Mozambikue
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana bayyana matakan da sabuwar gwamnatin Amurka zata dauka idan har tana son sake samun yardar samun yardar kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-jazeera ta kasar Qatar a birnin Doga. Ministan ya kara da cewa gwamnatocin Amurka da suka shude daga ciki har da gwamnatin Trumps suka yi a baya musamman ficewarta su daga yarjeniyar JCPOA.  Abbas Argchi ya bayyana cewa abu mafi muhimmanci wanda dole ne Amurka ta yi idan tana son jawo hankalin iran dangane da tattaunawa da ita shi ne sako kudaden ta masu yawa wadanda ta hana a yi amfani...
    Shugaban kasar Iran Ma’suod Pezeskiyan tare da majalisar ministocinsa sun sabonda bai’a da jagoran juyin juya halin musulunci, wanda ya kai kasar ga samun nasarar tumbuke gwamnatin sarki Muhamma Reza Sha sannan ya sannan ya kaisu ga nasarar kafa JM a Iran,  shekaru 46 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a safiyar yau Asabar ce shugaban kasar Iran, Masuod Pezeshikyan tare da majalisar ministocinsa suka kara sabonta bai’a wato marigayi Immam Khomani (q).   Labarin ya kara da cewa Sayyid Hassan Khomani, jikan Imam(q) wanda kuma yake kula da hubbaren nasa ne, ya tarbi shugaban kasar ya kuma jagorance su zuwa hubbaren kakansa Imam Khumaini(q). Imam Khomani (q) ne ya jagoranci mutanen kasar...
    Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin  kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...
    Kafafen watsa labarun Amurka sun sanar da cewa wani karamin jirgin sama ya fadi akan wata cibiyar kasuwancin dake Philadelphia  a jihar Pennsylvania tare da kashe mutane 6 da suke cikinsa. Kafafen watsa labarun na Amurka sun ce ‘yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe gobarar da ta tashi a cikin gidaje da dama a yankin da jirgin ya fado. Tashar talabijin din “Fox News” ta sanar da cewa jirgin da ya fado na jigilar marasa lafiya ne, yana dauke da  wani mara lafiya daya da dan’uwansa, sai kuma likitoci biyu da suke tare da shi. Ita kuwa jaridar “Philadelphia Enquiry” ta ambato ‘yan sanda suna cewa, jirgin ya fado ne da misalin karfe 6;pm agogon yammacin gabashin Amurka. A ranar...
    Sanarwar ta ci gaba da cewa, Kamfanin na Biba Atlantic da Didam, sun sana son ra’ayin a cikin wasikar su ta samun umarni tare da samun bayanan sirri, daga gun ma’aikata, ba bisa ka’ida ba, wanda hakan ya ba su dama tabka badakala da aikata cin hanci da rasahawa. Kazakla, sanarwar ta bayyana cewa, daga cikin yarjejeniyar, kamfanonin na Biba Atlantic Limited da Technology House Limited da kuma Didam, sun amsa laifinsu da kuma zubar da kimarsu. Sanarwar ta bayyana cewa, wasu daga cikin abubuwan da ake bukatar Kamfanonin da kuma Didam da ake son su cika sharudda dole ne su bi ka’idar samun haro, kuma wajbi ne, su karfafa kimar bin ka’idar tsare-tsaren su. Bugu da kari, dole ne...
    Da yake magana ta cikin shirin siyasa na talabijin Channels, ministan ya ce, shugaban kasa bai yi wasu tafiye-tafiyen da suka isa ba. “Har yanzu wannan gwamnatin sabuwa ce. An rantsar da shi a 2023. Ta fuskancin duniya har yanzu shi sabon shugaban kasa ne. Yana bukatar tattaunawa da ganawa da takwarorinsa domin gina alaka mai kyau a tsakaninsu, sannan kuna iya ganin amfanun irin wadannan tafiye-tafiyen. “Za ka sake tafiya ka samu zuba jari na dala biliyan 2 kamar yadda ya yi a Brazil. A zahiri, ba mu ma yi tafiye-tafiyen da suka isa ba. Ina ba da shawarar mu sake yin wasu karin tafiye-tafiyen. “Nijeriya tana da dinbin dukiya. Nawa ne tafiyar zai lakume idan aka kwatanta da...
    Ishara ”Kada Mu Manta” taron, ya ba da haske game da lokutan soyayyar dangi da alakar kud da kud da ke wanzuwa a cikin iyalai na Yahudawa da al’ummomin kafin Holocaust da alhakinmu na kare hakkin kowa na rayuwa cikin mutunci da zaman lafiya.   Da yake gabtar da jawabi a yayin taron jakadan kasar Isra’ila Inbar Lipman Garden, cewa ya yi   A wannan rana mai girma muna tuna Yahudawa maza da mata da yara miliyan shida da aka kashe a cikin Holocaust tare da miliyoyin wasu da ke shan wahala a ƙarƙashin mulkin Nazi.   Muna girmama abubuwan tunawa da su ba wai kawai nuna rashin jin dadi ba a a har ma da sake tabbatar da aniyarmu...
    A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...
    Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa rahotanin da ya samu game  kyawawan dabi’u da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje suke nunawa a kasashen da suke, yana mai cewa hakan zai zaburar da matasa kan dabi’un da ke kara martabar kasa. Shugaban ya yabawa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin da ya karbi wasiku daga jakadan kasar  Kanada a Najeriya, Pasquale Salvaggio, da jakadan Saliyo, Dr Julius F. Sandy, a fadar gwamnati. Har ila yau, shugaba Tinubu ya karbi wasikun amincewa da nuna gamsuwa daga Legesse Geremew Haile, jakadan kasar Habasha a Najeriya, da Archbishop Michael Francis Crotty, shugaban Bishop Bishop na fadar Vatican a Najeriya. Babban Kwamishinan na Kanada ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa ’yan Najeriya suna...
    A ranar 11 Ga Watan Fabarainu na wannan shekarar ne JMI take cika shekaru 46 cib da samun nasara, da kuma kafa JM a Iran, wadanne nasarori ne kasar ta samu a cikin wannan lokaci?. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kadan daga cikin nasarorin da kasar ta samu daga ciki. 01-Tsawon shekarun da Iraniyawa suke rayuwa ya karu daga 55 zuwa 76.2 , saboda ci gaban da kasar ta samu a bangaren kiwon lafiya. Wadanda suka hada da kayakin aiki magunguna da kwararrun likitoci da ma’aikatan jinya. Sannan wannan duk ya faru ne a cikin takunkuman kasashen yamma wadanda basa son ci gaban kasar, tun ranar kafuwarta har yau. 02-JMI ta iran ce kasa ta farko...
    Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
    Kamfanin dillancin labaran BBC ya bayyana cewa mutane 64 ne suke cikin jirgin fasinja na kamfanin American Airline, sannan mutane 3 ne a cikin jirgin yaki mai saukar ungulu samfurin Black Hawk suka yi karo a birnin washinton a safiyar yau Alhamis. Labarin ya kara da cewa, a halin yanzu sun tashi daga kubutar da wadanda suke da rai zuwa neman gawaki kawai, tunda ana ganin da wuya a sami wani da rai a cikin fasinjojin jirgin. Ya zuwa yanzu dai an tsamo gawakin mutane 30, kuma suna ci gaba da aikin gano wasu karin gawakin. Jami’an gwamnatin kasar Amurka sun bayyana cewa jirgin fasinjar ya rabu zuwa kasha ukku sannan ya fada cikin wani ruwa mai zurfin mita 7....
    Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata na bai daya ga duniya. Shi ma a jiyan, shugaban Zambia Hakainde Hichilema, ya aikewa shugaban kasar Sin Xi Jinping gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar, yana mai fatan samun ci gaban kasashen da al’ummominsu. Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10 Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje A ranar Talata kuma, shugaban Angola...
    Wani uba a ƙasar Pakistan ya kashe ɗiyarsa matashiya bayan ta saka wasu faifan bidiyo da ya ɗauka a matsayin waɗanda ba su dace ba a manhajar sada zumunta ta TikTok, in ji ‘yan sanda a ranar Alhamis. Shugaban ‘yan sandan yankin, Babar Baloch, ya ce mutumin wanda aka ce yana da shekara 50 a duniya, ya dawo da iyalansa daga ƙasar Amurka kwanan nan, domin su zauna a birnin Ƙuetta da ke Kudu maso Yammacin Pakistan. Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Jirage sun yi karo a sararin samaniya a Amurka Mahaifin, wanda yanzu haka yake tsare, ya amsa laifin harbe ’yarsa a farkon wannan makon bayan ta ƙi sanya suturar da ta dace kuma ta daina...
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara.   Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi da ‘yan bindiga.   “Dole ne in yaba wa sojoji, DSS, da ‘yan sanda, musamman ma Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, bisa nasarar aiwatar da wannan gagarumin kame.   “Ina so in jaddada cewa waɗannan nasarori da aka samu tare da wasu na daƙile ‘yan bindiga a jihar, sun samo asali ne daga haɗin kai da goyon bayan da gwamnatin jihar Zamfara ke baiwa ɗaukacin...
    Ya ƙara da cewa, “Da har yanzu ina cikin wannan gwamnati, zan fadi gaskiya a cikin tarurruka na sirri, kuma idan ba a ɗauki mataki ba, zan yi magana a fili. Duk wanda ke shakkar haka, ya duba tarihin aikin gwamnati na tun daga 1998.” El-Rufai ya kuma soki wasu da ya kira “’yan amshin shata” a gwamnatin Tinubu, yana mai cewa suna amfani da kuɗaɗen tsaro don kare duk wani abu da gwamnati ke yi, ko da kuwa ba abin karewa bane. Ya buƙaci Bwala da ya tuna cewa “Alkawari na farko shi ne ga Allah da ƙasa, kafin wani mutum ko hukuma.”
    Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba. Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi. Ministan ya ce Iran ta riga ta shiga tattaunawa da bangarorin Turai da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, kuma tana jiran Washington ta fayyace manufofinta. “Ba a aika ko karbo wani sako na musamman ba tsakanin kasashen biyu ba; saidai abubuwan da muke ji a kafafen yada labarai kawai.” An yi ta rade-radin cewa gwamnatin Trump ta yi musayar sakonnin sirri da Iran. “A baya mun cimma yarjejeniya; Iran ta...
    Kungiyar fursunonin Falasdinu ta ce za a sako wasu karin Falasdinawa 110 daga gidajen yarin Isra’ila a yau Alhamis a mataki na uku na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas. Ana sa ran galibin Falasdinawan da aka ‘yantar za su isa yankin Radana na Ramallah da ke yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye da misalin karfe 12:00 na safe agogon kasar, in ji kungiyar fursunonin Falasdinu. Wannan ba zai hada da fursunoni 20 da za a tura gudun hijira a wajen Falasdinu ba. Kungiyar ta kuma fitar da jerin sunaye da shekarun fursunonin da za a saki wadanda suka hada da akalla yara 30. Sakin da za’ayi wa Falasdinawan 110 a yau zai sanya...
    Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU) ta bayyana cewa jami’o’in gwamnati da dama a Najeriya sun shafe sama da watanni uku ba tare da wutar lantarki ba da za su gudanar bincike ko darussa ba. Kungiyar ta kuma yi barazanar ɗaukar tsattsauran mataki kan gwamnatocin jihohi da kamfanoni da suka ki fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba na Naira dubu 70 da sauran sauye-sauye da ke tattare da shi zuwa ƙarshen watan Maris na shekarar nan ta 2025.   Shugaban Ƙungiyar SSANU ta Kasa, Kwamred ohammed Ibrahim, ne ya sanar da haka a yayin taron Majalisar Tuntuba ta Ƙasa (NAC) da ƙungiyar ta gudanar a Abuja. Kwamred Ibrahim ya bayyana cewa har yanzu Gwamantin Tarayya da na wasu jihohi ba...
    Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga  Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa.  Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20  da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Dole ne kasashen duniya su gane irin wahalhalun da al’ummar Iran ta sha wajen yaki da ta’addanci Jakadan kasar Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya aike da wasika ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya dangane da laifukan da kungiyar ta’addanci ta munafukai {MKO} ta aikata, wanda ya yi sanadin shahadan mutane 23,323, Irawani ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa sun yi furuci da ire-iren wahalhalun da al’ummar Iran suka sha tsawon shekaru da dama da kuma wadanda suka yi shahada a fagen yaki da ta’addanci. A cikin wannan sakon, Irawani ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta himmatu wajen aiwatar da dokokin kasa da kasa...
    Duk da ficewarsu daga ECOWAS, ƙasashen AES sun yanke shawarar cewa ‘yan ƙasashen ECOWAS za su iya shiga ƙasashensu, domin ƙarfafa dangantakar hada-hadar kasuwanci a tsakanin yankin. Wannan ficewa na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Sahel ke fama da matsalolin tsaro, wanda ya haifar da juyin mulki a ƙasashen uku. Yanzu haka, suna fatan sabuwar ƙungiyarsu ta AES za ta taimaka wajen magance waɗannan matsaloli da inganta tsaro a yankin.
    Ɗan wasan Nijeriya kuma gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afrika, Ademola Lookman, ba zai buga wasan da Atalanta za ta kara da Barcelona a gasar cin kofin Zakarun Turai yau Laraba ba, sakamakon rauni da ya ji a gwiwarsa. A wata sanarwa da kulob ɗin Atalanta ya fitar, ya ce ɗan wasan mai shekaru 27 ya samu rauni a gwiwar dama a lokacin atisayen safiyar Talata, wanda ya hana shi tafiya Spain don buga wasan da ƙungiyarsa ke neman cancantar shiga zagayen 16 na ƙarshe. Tinubu Ya Yi Alƙawarin Inganta Wutar Lantarki A Nijeriya Gwamnan Bauchi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Da Za Ta Daƙile Satar Yara A Bauchi  Duk da cewa kulob ɗin bai bayyana tsawon lokacin da Lookman zai...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a wata hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta Sky News a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, ban tsamman zasu yi haka ba. Amma idan sun, to kuwa ba zasu ji ta da dadi ba. Yace: JMI ta rattaba hannu a kan yarjeniyar Nukliya da manya-manyan kasashe 6 a duniya kan shirin ta na makacin Nukliya wanda...
    Runduna daya ta sojojin Najeriya ta gudanar da bikin jana’izar marigayi Mascot, Sajan Dalet Danfari Akawala, a shalkwatar rundunar dake jihar Kaduna. Wanda dokin sojojin ne.   A wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar, ya ce Kanar Akabike ne ya jagoranci jana’izar, wanda ya wakilci babban hafsan rundunar, Manjo Janar Mayirenso Lander David Saraso.   A cewar sa, Marigayi Sajan Dalet Danfari Akawala ya yi hidimar sashen sadaukarwa da aminci, tare da nuna jajircewa da juriya a gidan Soja.   “Bikin shi ne hanyar mu na girmamawa ta ƙarshe ga wani wanda ya kawo sauyi da farin ciki da aiki tukuru da kuma daukaka sashen da yayi...
    A cim ma burin Gwamna Umar Namadi na ci gaban bil’adama a cikin ajandar mai dauke da abubuwa 12, majalisar zartaswar jihar Jigawa ta kafa wani kwamiti mai mambobi 10 domin samar da hanyoyin da za a bi wajen nemo masu hazaka domin karfafa kirkire-kirkire a tsakanin matasa masu tasowa a jihar.   Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka bayan taron majalisar da aka gudanar a Dutse.   Ya ce, kwamitin ya kunshi kwamishinonin lafiya, muhalli, kananan hukumomi yayin da kwamishinan ilimi mai zurfi zai zama shugaba.   Sauran mambobin sun hada da masu ba da shawara kan fasaha, ICT da tattalin arziki na dijital, ilimi mai zurfi, aikin gona,...
    A ranar 25 ga wata, agogon Najeriya, ofishin karamar jakadiya kasar Sin dake Legas, da tawagar Sinawa wadanda ke kasar, sun gudanar da jerin ayyuka don yin maraba da murnar bikin Bazara na shekarar maciji bisa kalandar gargajiyar Sinawa. An gudanar da bikin nune-nunen abinci, da nune-nunen kayayyaki, da liyafar maraba bi da bi, wanda ya samu halartar mutane sama da 2,000 da suka hada da Sinawa dake kasar da abokai ‘yan Najeriya. Kafin an fara liyafar a maraice, an watsa bidiyon dandanon shagalin murnar bikin Bazara na shekarar maciji na babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, Kyan hoton bidiyon mai kayatarwa kuma mai cike da ma’anar kimiyya da fasaha ya matukar burge bakin da ke...
    Rundunar Sojin Najeriya ta 8 da ke Sokoto ta bayyana ayyukanta na zamantakewar jama’a na yammacin Afirka WASA, a matsayin muhimmin kayan aiki don wanzar da hadin kai da ci gaba a yankin yammacin Afirka.   Babban Kwamandan Rundunar, Manjo Janar Ibikunle Ajose ya bayyana haka a wajen taron na bana da aka gudanar a Bataliya ta 26 dake jihar Sokoto.   Ajose ya ce hukumar ta WASA tana baiwa hafsoshi da sojoji da iyalansu damar yin mu’amala cikin yanayi mai kyau.   Ya bayyana cewa, tarihin wannan biki ya samo asali ne tun a shekarar 1901, a lokacin shigar da Najeriya cikin rundunar sojojin kasashen yammacin Afrika, saboda al’adu daban-daban na sojojin kasashen yammacin Afirka, shi yasa mahukunta a...
    “Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni. “Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara da walwalarsu. A matsayinsu na ginshiƙin makomarmu, dole ne mu tabbatar da cewa yara suna cikin aminci da kulawa don cimma burinsu. “Dokar nakasassu ta jihar Zamfara ta nuna ƙudurinmu na kare haƙƙin nakasassu. Wannan na neman kawar da wariya da haɓaka damar shigarsu cikin al’umma. Mun haɗa da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da nakasassu, don tabbatar da jin muryoyinsu. “Saboda haka,...
    Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau. Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren. Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin...