2025-04-16@04:35:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 359
«Wannan yana»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A bisa tafarkin addini da kuma al’ada, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su. Domin sauke shirin, latsa nan
Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga ma’aikata da jami’an Alhazai na kananan hukumomi a Otal din Grand Central. Alhaji Danbappa ya bayyana cewa za a ci gaba da karbar kudaden maniyyata har zuwa ranar daya ga watan Ramadan. Ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yau 25 ga watan Fabrairun 2025, hukumar ta bada sama da naira biliyan 22 ga hukumar alhazai ta kasa a madadin Alhazan jihar Kano. Bugu da kari, babban daraktan...
Ministar harkokin wajen Madagascar Rasata Rafaravavitafika ta bayyana a Tananarive, hedkwatar kasar jiya Litinin cewa, ana godiya ga Sin da ta dade take tura tawagogin likitanci zuwa kasar cikin shekaru 50 da suka gabata, don ba da tallafin jinya na zamani a yankuna masu nisa na Madagascar, da ceton rayuka na miliyoyin mutane dake wuraren. Rasata ta bayyana hakan ne yayin halartar bikin sa hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar tawagogin likitanci ta Sin tsakanin Sin da Madagascar. Ji Ping, jakadan Sin dake Madagascar da Randriamanantany Zelyarivelo, ministan kiwon lafiyar jama’a na Madagascar, suka sa hannu a kan yarjejeniyar. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi mu zauna kan teburin tattaunawa da mutumin da yake fitowa fili yana yi mana barazana, kuma ya sa hannunsa a wuyansa ya sheke mu. Shugaban kasar ta Iran wanda ya gana da ‘yan majalisa masu wakiltar gundunar Hamadan a daren jiya Litinin ya ce; Mu mutane ne da mu ka yarda da tattaunawa,kuma a halin yanzu abinda ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yake yi kenan da kasashen makwabta. Da ya tabo batun takunkuman da Amurka take kakaba wa Iran kuwa, shugaban kasar ta Iran ya ce, babu yadda za a yi a kakaba takunkumin ya yi tasiri akan kasar da take da iyaka mai tsawo da...
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya kuma nuna cewa kungiyar Hizbullah, na da karfinta da kuma akidar kyamar sahyoniyawan. Sanarwar ta kara da cewa: “Bikin da ya samu halartar miliyoyin mutane, a daidai lokacin da ake barazana da jiragen yakin Isra’ila, ya zama wata alama ta karfin Musulunci da cikakken hadin kan al’ummar kasar Labanon. Sanarwar ta yi nuni da cewa, gagarumin taron makoki daga kasashe daban-daban, addinai da kabilu, da...
Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya. An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko. Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya bayyana a yayin bikin, cewa “Tutar kungiyar AES, launin kore, tana dauke da tambarin kungiyar a tsakiyarta.” Ya jaddada cewa launin kore yana nuna alamar bege da wadata, wanda ke wakiltar dukiya da karfin tattalin arziki. Wannan sabuwar alamar ta kunshi hadin kai da muradin bai daya na kasashen uku, inda suka kuduri aniyar yin aiki tare domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar yankin inji...

IRGC Ta Bayyana Cewa Taron Jana’izar Nasarallah Ya Yi Tisara A Duniya Gaba Daya Saboda Barazanar Da Jiragen Yakin HKI Ta Yi Wa taron
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta gudanar na shahidan shuwagabanninta a jiya, ya tabbatar da cewa kungiyar tana da karfi kuma tana da karfin kawo karshen HKI a yankin da kuma kwato kasashen Larabawan da aka mamaye. Rahoton ya kara da cewa a fagen kasa da kasa kuma, mutanen da suka taru ko suka yi gangami a jana’izar ya tabbatar da yadda wannan kungiyar take da karbuwa a cikin kasar a...
To, ma iya cewa kasar Amurka ta riga ta fusata dukkan kasashen duniya. Idan an sa wata kasar dake nahiyar Afirka fuskantar matakin da kasar Amurka ta dauka ita kadai, to, za ta ji akwai matsin lamba. Sai dai yanzu za a saki jiki, saboda ko da yake kasar Amurka ta kan ci zarafin sauran kasashe, amma ba ta da karfin cin zarafin dukkan kasashe a sa’i daya. Wannan shi ne dalilin da ya sa ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a wajen taron aikin tsaro na Munich da ya gudana a kwanan nan, cewa bai kamata a ji tsoron aikace-aikacen kasar da ta ke ta nuna fin karfi a duniya ba, saboda galibin kasashen duniya dake...
Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta da suka hada da Sanata da wasu ‘yan majalisar tarayya uku bisa zargin zagon kasa ga jam’iyyar. Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda ya bayyana rashin jin dadin jam’iyyar da halayyar ‘yan majalisar da aka dakatar. NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje ‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, da kuma ‘yan majalisar wakilai uku, wato Alhaji Abdullahi Sani Rogo (Mazabar Tarayya ta Rogo),...

Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyararsa A Birtaniya Da Ireland Da Halartar Taron Kolin Kwamitin Sulhu Da Na Tsaro A Munich Da Na G20
A jiya Asabar 22 ga wannan wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani ga kafofin watsa labaru na kasar Sin bayan da ya kammala ziyararsa a Birtaniya da Ireland, da halartar taron kiyaye tsaro na Munich karo na 61, da shugabantar taron kolin kwamitin sulhun MDD a birnin New York, da kuma halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a kasar Afirka ta Kudu. A matsayin kasar da take shugabantar kwamitin sulhun MDD a wannan wata, kasar Sin ta yi kira ga taron koli na kwamitin mai taken “Bin ra’ayin bangarori daban daban da yin kwaskwarima kan kyautata aiwatar da harkokin duniya”. Inda game da hakan, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi...
dimbin Asarar Da Manoman Cittta Suka Tabka: Shugabar kungiyar manoman Citta da sarrafata ta kasa (GGPMAN) Florence Edwards, ta alakanta samun raguwar Cittar da ake fitarwa daga kasar nan zuwa kasashen ketare da barkewar cutar da ta lalata gonakin wasu manomanta. Florence ta kara da cewa, akasarin irin samfurin Cittar da manoman ke shukawa a fadin kasar nan, sun shafe sama da shekaru 20 suna amfani da shi. Ita ma wata manomiyar Cittar a Jihar Kaduna, Joy Bolus ta bayyana cewa, ta kashe sama da Naira miliyan daya a shekarar da ta gabata wajen aikin noman Cittar a tata gonar, ta hanyar yin hadaka da miinta, amma saboda barkewar cutar a bara, hakan ya jawo gonar ta lalace baki-daya....
Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi. A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya, sannan za a bai wa kwararren manomi guda hamsin wanda zai koyar da su dubarun kiwo. Tun da farko da take jawabi, kwaminisiyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta bayyana wannan tallafi a matsayin wata gagarumar gudummawa da gwamnati za ta bunkasa harkokin mata ta hanyar dogoro da kai. A cewarta, taimakon da Gwamna Radda ya bayar ko shakka babu zai amfani...

Ministan Wajen Sin Ya Yi Kiran Hadin Gwiwar Kasashen G20 Don Gina Duniya Mai Adalci Da Ci Gaba Na Bai-daya
Taron na farko na ministocin harkokin wajen G20 a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu ya kasance mai cike da tarihi, domin shi ne taron ministocin wajen kungiyar na farko a nahiyar Afirka, kamar yadda ministan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya bayyana, yayin da yake yabawa da taron, a wani taron manema labarai bayan kammala taron, inda har ila yau ya kara da cewa, taron “mai matukar fa’ida” ya yi gagarumar tattaunawa a kan dabarun da suka shafi yanayin shiyyoyin duniya da tasirinsu a kan gudanar da ayyukansu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Dauda ya kara da cewa, babu wata waka da zai yi ba tare da an bukaci ya yi ta don isar da wani sako ba. Haka zalika, Shugaba Tinubu, ba shi da wani buri na tara dukiya a halin yanzu; illa kawai dai fatan barin tarihi mai kyau a matsayinsa na Shugaban kasa, kamar yadda sauran mazan jiya; irin su Sir Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa suka bari. Dangane da abin da wasu ke dauka cewa, ana biyana makudan kudade; don yin wakokin da za su kawar da hankalin mutane, su sani cewa; na fi mayar da hankali a kan noma fiye da yadda nake yi wa harkar waka, dalili kuwa; ni manomi ne wanda a yanzu haka duk...
“Duk da cewa an dan samu raguwar kai hare-hare amma har yanzu ana samun wasu su shiga su kashe mutane sannan su tafi da wasu domin kuɗin fansa” in ji ɗan majalisar. Sannan ya kuma kalubalanci rashin hanya mai kyau a yankunan wanda a cewarsa hakan ma yana kawo tsaiko wajen fatattakar yan ta’adda. Danlami Stingos ya kuma yabi gwamnatin jihar Kaduna bisa kokarin da take yi na yaƙi da yan ta’adda sannan ya kuma riko gwamnatin da ta dage wajen samar da hanyoyi a yankunan da suke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai shekaru 28, Samuel Alfred bisa zargin yi wa wata agolarsa fyaɗe har ta samu juna biyu. An cafke mutumin ne tare da wani abokinsa, Ikechukwu Obi mai shekaru 30 kan zargin wannan aika-aikar. An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines Ko Real Madrid za ta iya lashe Gasar Zakarun Turai bana? Bayanai sun ce ababen zargin sun kai budurwar mai shekaru 14 wani ɗaki da ke yankin Ojo na jihar ta Legas inda suka raba ta da budurcinta. Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce mahaifiyar yarinyar mai suna Deborah ce ta kai ƙorafi ofishinsu da ke Okokomaiko. Hundeyin ya ce...

Yake-Yaken Kasa Da Kasa Ne Suka Mamaye Taron G20 Na Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar A Afirka Ta Kudu
A jiya Jumma’a ce aka kammala taron kungiyar kasashen G20 a birnin johanasboug na kasar Afrika ta Kudu, kuma inda batun yake-yake a yankunan daban-daban na duniya ne suka mamaye taron. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yakin Ukraine da Rasha Hamas da HKI, Congo da sauransu ne suka mamaye taron inda ministocin harkokin wajen kasashen na G20 suka tattauna a kansu. Ministan harkokin wajen na kasar Afrika ta Kudu Ronal Ramola ya bayyana cewa duk tare da cewa babu wani babban jami’an gwamnatin kasar Amurka a taron amma taron ya gudana kamar yadda ake saba. Kungiyar G20 Taron kasashe masu arziki a duniya, wadanda suke da kasha 85% na tattalin arziki a duniya sannan suna...
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar suka ga hare-haren da kuma ci gaban da kungiyar M23 ke ci gaba da yi a arewacin Kivu da Kivu ta Kudu tare da goyon bayan dakarun tsaron kasar ta Rwanda”. A wani labarin kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi kira da a tsagaita bude wuta nan take a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Kenya...
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ya bayyana cewa wasu yankunan Abuja za su fuskanci katsewar wuta a ƙarshen mako saboda aikin gyara da za a yi wa na’urorin lantarki. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, ya ce ana yin wannan aikin ne na shekara-shekara, kuma za a gudanar da shi a ranakun Asabar da Lahadi. Zaɓen ƙananan hukumomin Osun na nan daram – Gwamna Adeleke Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi A sakamakon haka, za a dakatar da wutar lantarki a wasu yankuna na tsawon sa’o’i bakwai a kowace rana. “Aikin zai gudana daga ƙarfe 9 na safe zuwa 4 na yamma a ranakun biyu,” in ji kakakin TCN, Ndidi Mbah....
Ƙasurgumin fitaccen shugaban ‘yan Bindiga, Bello Turji, ya ƙaƙaba harajin Naira miliyan 22 a wasu ƙauyuka huɗu na jihar Sokoto, kan kashe ɗaya daga cikin mutanensa a wani samame da sojoji suka yi a yankin. Acewar mutanen yankin, wannan harajin, yana matsayin diyya ga makaman da suka bace yayin artabun da mutanensa suka yi da sojoji. Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Da Lita 60,000 Daftarin Sin Ya Samar Wa Kamfanoni Masu Jarin Waje Damammaki Masu Kyau Kauyukan a cewar dan majalisar mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta yamma a majalisar dokokin jihar, Hon. Aminu Boza ya hada da Garin Idi, mahaifar mataimakin gwamnan jihar mai ci, Injiniya Idris Gobir. Boza ya kuma ce, Turji ya koma da...
Daftarin Sin Ya Samar Wa Kamfanoni Masu Jarin Waje Damammaki Masu Kyau
Kungiyar wasan Kareti ta Iran ta zama ta daya a nahiyar Asiya, yayin da Iraki ta zo ta biyu sai kuma Tajikistan ta uku. An yi wannan gasar ne ta Asiya a garin Calus dake Arewacin Iran wanda ya sami halartar kasashe da dama. Daga cikin kasashen da su ka shiga gasar wasannnin da akwai Iraki, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman sai kuma Tajikistan. An bude wannan gasar ne dai daga ranar 19 ga watan nan na Febrairu, kuma za a rufe ta zuwa gobe 22 gare shi. Da akwai ‘yan wasa 120 na cikin gida da waje da su ka shiga cikin gasar, da ‘yan kallo 700 a cikin dakin wasa.

Binciken Ra’ayoyi Na CGTN: Watan Daya Da Dawowar Trump Mulki, Mutanen Duniya Sun Ce Da Wuya A Ce An Gamsu Da Salonsa
Binciken Ra’ayoyi Na CGTN: Watan Daya Da Dawowar Trump Mulki, Mutanen Duniya Sun Ce Da Wuya A Ce An Gamsu Da Salonsa
Sun ci gaba da cewa, tattalin arzikin ya karu zuwa kaso 3.5, a zango na uku a 2024, daga kaso 3.2 a zango na biyu a 2024. A cewarsu, Nijeriya ta samu wannan nasarar ce, saboda tsaurara tsare-tsaren hada-hadar kudade, inda kuma fannin da bai shafi Man Futur na kasar ba, ya bayar da gagarumar gudunmawa, tare da samar da tsare-tsaren sakuka yin hada-hadar kasuwanci a kasar. Sun kara da cewa, fannin Mai ya ci gaba da bayar da gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar, musamman duba da yadda Matatar Man Fetur ta dangote ke samar da yawan Man a kasar, inda hakan ya kuma daidaita samar da Man da kuma rabar da shi, a cikin farashi mai rahusa. Sai...
Tambuwal ya bukaci ‘yan adawa da su hada kai su tsara dabarun tunkarar zaben 2027, yana mai jaddada bukatar bai wa ‘yan Nijeriya mafita mai inganci. “Babu wani abin burgewa a APC wanda ya wuce amfanin kashin kai. Mu da muke kokarin saka kishin kasar nan wajen yi wa kasa hidima na gaskiya mu hada kai don korar wannan gwamnatin a 2027, domin ta gaza share wa ‘yan Nijeriya hawayensu.” A halin da ake ciki kuma, jam’iyyar PDP a yankin arewa maso yamma ta sake jaddada aniyarta ta kwato mulki a shekarar 2027, inda ta jaddada muhimmancin hadin kai a tsakin ‘ya’yan jam’iyyar. Sanarwar da aka fitar a karshen taron, wanda shugaban jam’iyyar PDP na yankin arewa maso yamma, Sanata...
Idan za a iya tunawa dai, malaman addini sun taka rawa wajen zaburar da jama’arsu domin yin rajistar masu zabe. Duk da haka, a babban zaben 2023 wanda yana daya daga cikin mafi zaben da ya janyo rarrabuwar kawuna a Nijeriya, masallatai da coci-coci sun taka rawar gani wajen tursasa mabiyansu su zabi nasu ‘yan takara. Mafi yawancin wa’azi da khudubobi sun kasance wurin tattauna harkokin siyasa. A wasu majami’u, fastoci sun yi da’awar manzancin kan ‘yan takararsu, yayin da a cikin malaman addinin musulmi, limamai sun bukaci mabiya da su yi zabe ta hanyar addini. Abin mamaki, yawancin wadannan hasashen addini ba su tabbata ba. A kwann nan dai an tafka cece-kuce kan taron da aka shirya gudanarwa a...

Wasu Motocin Bas-Bas Sun Tarwatse A Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yankin Bat Yam A Kudancin Tel-Aviv
Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Ma’aikatan tsaron cikin gidan haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Shin Bet ta fara binciken wadanda ake zargin dasa ababen fashewa da suka yi sanadiyyar tarwatsewar motocin bas-bas din, kuma sun ba da rahoton zargin cewa; An samu wasu bama-bamai guda biyu wadanda ba su fashe ba. Har ila yau, kafofin watsa labaran ‘yan mamayar sun ruwaito cewa: An dakatar da zirga-zirgan jiragen kasa gaba...
Gwamnatin jihar Kano ta dauki wani gagarumin mataki na bunkasa ilimin addinin musulunci a jihar ta hanyar hada hannu da kungiyar Agaji ta Musulunci da ke Birtaniya, wato Muslim Charity For United Kingdom a turance. Wannan haɗin gwiwar na nufin tallafa wa makarantun Islamiyya da kayayyakin koyon ilimi na zamani, da sauransu. A cewar daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, wannan shiri ya yi daidai da kokarin da gwamnati ke yi na karfafa fannin ilimi. Haɗin gwiwar zai magance matsalolin da ke addabar ilimin addinin Islama, da tabbatar da cewa makarantun Islamiyya sun sami tallafin da ya dace don samu ingantaccen yanayin karatu da koyarwa. Ya yi nuni da cewa, Kwamishinan Ilimi...
Yawan Kamfanonin Da Aka Kafa Da Jarin Waje A Sin Ya Zarace Miliyan 1.23
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ogbugo Ukoha, Babban Darakta a sashen rarraba mai tare da adanawa na NMDPRA, ya ce matakin ya biyo bayan karuwar firgicin hadurran da ke tattare da manyan motocin dakon man. “Kwamitin fasaha na masu ruwa da tsaki ya gana a yau don cimma wasu muhimman kudurori guda 10 da nufin rage karuwar yawan hadurran tankokin mai da ke janyo asarar rayuka,” in ji Ukoha. An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da DSS, hukumar kashe gobara ta tarayya, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kungiyar masu sufurin mota ta kasa (NARTO), kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas...
Ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Uganda Jeje Odongo a cibiyar MDD da ke birnin New York. Yayin ganawar a ranar 18 ga wata, Wang Yi ya bayyana cewa, ana bukatar ra’ayin Afirka yayin da ake yada ra’ayin bangarori daban daban da kuma daidaita harkokin duniya baki daya. Ya ce kasar Sin tana son hada hannu da kasashen Afirka wajen kafa tsarin daidaita harkokin duniya mai adalci da kuma samar da gudummawa wajen shimfida zaman lafiya da samun ci gaba a duniya. Wang Yi ya ce Sin tana yabawa kasar Uganda bisa muhimmiyar rawar da ta taka yayin da take shugabantar kungiyar kasashe ‘yan ba ruwanmu wato NAM, da taya ta murnar zama kasar...
Yanzu-yanzu: Gini Ya Rufta Wa Ɗaliban GGTC Potiskum
Jakadan Sin dake kasar Najeriya Yu Dunhai ya gana da karamar ministar harkokin waje ta kasar Bianca Odumegu-Ojukwu. Jakada Yu ya bayyana cewa, a shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, wanda ya zama babban ci gaba ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. A farkon shekarar bana kuma, memban hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya kai ziyara Najeriya cikin nasara, hakan ya kara kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi. A cewar jakadan, Sin tana son...

Kungiyoyin Falasdinawa A Gaza Sun Bukaci Yin Taron Musamman Domin Dakile Batun Tilasa Wa Mutanen Gaza Yin Hijira
Kungiyoyin Falasdina mabanbanta sun yi kira da a gudanar da taron musamman na al’ummar Falasdinu domin a tattauna hanyoyin da za a dakile batun tilastawa mutanen Gaza yin hijira. Kungiyoyin na falasdinawa sun bayyana hakan ne dai a wani taro da su ka yi a Gaza domin karfafa gwiwar mutanen wannan zirin su ci gaba da jajurcewa da tsayin dakar da suke yi, tare da kara da cewa; Babu yadda za a yi al’ummar Falasdinu su fita daga kasarsu. Mahalarta taron na Gaza sun bayyana furucin da shugaban kasar Amurka ya yi akan fitar da Falasdinawa daga Gaza da cewa yana nuni akan yadda Amurka da ‘yan sahayoniya su ka yi tarayya a laifukan da aka tafka akan Falasdinawa, haka...

Trump Na Amurka Ya Zargi Shugaban Kasar Ukiraniya Da Kama –Karya Da Kuma Rusa Kasarsa Ba Tare Da Wani Dalili Ba
Shugaban kasar na Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na “Truth Social” da a ciki ya bayyana Volodymyr Zelenskyy dad an kama-karya, kuma abinda ya fi yi masa alheri shi ne ya yi wani abu da sauri, domin idan ba haka ba,zai yi asarar kasarsa baki daya. Shugaban na kasar Amurka ya kara da cewa; Volodymyr Zelenskyy ya sa Amurka ta kashe dala biliyan 350 da ya shiga cikin yakin da ba zai iya samun nasara ba. Har ila yau, shugaban na Amurka ya ce, shi kanshi Volodymyr Zelenskyy ya yi furuci da cewa, rabin kudaden da mu ka aika masa sun bace, kuma ya ki gudanar da yin zabe, don haka masu goyon bayansa ‘yan kadan...
A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci. Bayan taron, ya kuma amsa tambayoyin ‘yan jaridu, game da yadda kwamitin sulhu na MDD zai karfafa kwarewarsa ta gudanar da ayyuka, da matsayin kasar Sin kan batun Gaza da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Jarin da kasar Sin ke zubawa wajen inganta lafiyar muhalli mai dorewa a duniya ya nuna muhimmiyar rawar da take takawa ta wannan fuskar. A shekarar 2024, kasar ta jagoranci duniya wajen zuba jarin sauya makamashi, inda ta zuba dalar Amurka biliyan 818 a wannan bangare. Wannan jarin ya sanya kasar Sin ta zama cibiyar samar da makamashi mai tsafta a duniya domin ita ke da kusan kashi 50 cikin dari na tasoshin samar da man “hydrogen” mara gurbata muhalli a duk duniya. Kasar Sin ta nuna wa duniya kyakkyawan misali abin koyi kamar yadda Shugaba Xi na kasar ke ci gaba da yayata muhimmancin kiyaye halittun doron kasa da kuma maye makamashi mai gurbata muhalli da mai tsafta. Shi...
Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar. Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana. Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci. Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani. Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma,...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Irin Gagarumar Rawar Da Iran Ta Taka A Fegen Tsaro Yakin Tekun Pasha
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana taka rawa ta musamman wajen wanzar da kwanciyar hankali da tsaron yankin Tekun Pasha Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar mallakar mafi yawan layukan kan iyaka da tekun Pasha da kuma iko da mashigar Hormuz, ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da tsaron wannan ruwa da yankunan makwabtanta. Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yayin taron tarihin huldar kasashen waje na Iran karo na 8, mai taken “Manufar harkokin wajen Iran da gabar tekun Pasha a cikin mahallin tarihi,” wanda aka gudanar a safiyar yau Talata a cibiyar nazarin siyasa da kasa da kasa na ma’aikatar harkokin...

Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da shahadar Muhammad Shahin wanda daya ne daga cikin kwamandojinta da ya yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai masa a birnin Saida na kasar Lebanon. Sanarwar ta dakarun “Kassam” ta ce, Muhammad Ibrahim Shahin wanda ake yi wa lakabi da Abul-Bara’a ya yi shahada ne a karkashin “Tufan-ak-Aksa” bayan da ‘yan mamayar HKI su ka yi masa kisan gilla a garin Saida dake kudancin Lebanon a jiya Litinin. Har ila yau dakarun Kassam sun yi bayani akan rawar da shahidin ya taka a fagen gwgawarmaya da jihadi akan ‘yan mamaya, tun daga boren Intifada na Aksa, har zuwa farmakin guguwar Aksa. Haka nan kuma bayanin na Kassam ya ce, Abul-Baraa ya...
A ranar 15 ga watan Fabrairu, ministocin harkokin waje na kasashen Amurka, Japan, da Koriya ta Kudu sun yi shawarwari a Munich na kasar Jamus. A cikin sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, a karon farko, sun bayyana goyon bayansu ga yadda Taiwan za ta shiga cikin kungiyoyin kasa da kasa da suka dace, tare da jaddada muhimmancin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan. Dangane da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Guo Jiakun, ya sake nanata cewa, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi da ita ba, kuma batun Taiwan lamari ne na cikin gidan kasar Sin kawai, kuma ba ta yarda da wata tsangwama daga...
Ya ce harin da aka kai ta sama ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda da dama tare da dakile harin da suka kai wa jami’an rundunar ‘yansanda (PMF) da jami’an tsaro na cikin unguwanni (Community Watch Corps, CWC) na jihar Katsina. AVM Akinboyewa ya bayyana cewa, an kaddamar da harin ne a matsayin martani ga bayanan sirri da ke nuna cewa, an kai harin ta’addanci a wani sansanin PMF da ke cikin al’umma, inda aka ce, ‘yan bindigar sun kashe jami’an PMF biyu da CEC hudu.
Kungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tsallake zuwa matakin zagaye na 16 a gasar zakarun Turai, amma kuma sabon kocin na fatan ganin ya lashe babbar gasar ta kasar Sifaniya.
MD. Abdullahi ya ce ita gwamnati a tsare-tsarenta ba ta neman kamfanoni, kuma rashin neman kamfanoni ke hana samun nasara wajen tsara yanda za a tallafa wa manoma na samun saukin taki da yanda za su biya.
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin. A cikin jawabin da ya gabatar a wajen bude taron ministocin kasashen tekun Indiya karo na 8 a birnin Muscat na kasar Oman a yau Lahadi, Araqchi ya ce: A yau mun hadu a kasar da aka sani tsawon shekaru aru-aru a matsayin gada da ta hada tsakanin gabas da yamma, kuma tsakanin manyan wayewa da al’ummomi na kusa da na nesa. Ya kara da...

Mujallar “Qiushi” Ta Gabatar Da Muhimmin Sharhin Xi Jinping Game Da Inganta Tsarin Daukar Kwararan Matakai Wajen Kula Da Harkokin Jam’iyya
Mujallar “Qiushi” da aka buga a yau Lahadi, ta gabatar da muhimmin sharhi na sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping mai taken “Inganta tsarin daukar kwararan matakai wajen tafiyar da jam’iyya a dukkan fannoni”. A cikin sharhin an nuna cewa, har yanzu ana fuskantar matsanancin yanayi da sarkakiya wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta dade tana fuskantar wannan jarrabawar. Saboda haka, dole ne dukkan mambobin jam’iyyar a ko da yaushe su sa lura da nuna karfin zuci, da daukar kwararan matakai wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar na dukkan fannoni, ta yadda za a iya raya jam’iyyar yadda ake bukata. Ban da haka, ya kamata...
Har ila yau a jiya Asabar, Wang Yi ya kuma gana da jami’an kasahen Brazil, da Czech, gami da Austria. (Bello Wang)
Ƙasashen da suke da saukin cin hanci a duniya Mafi yawan kasashen da rahoton ya nuna cewa babu yawaitar matsalar cin hanci da rashawa suna a nahiyar Turai ne. Bakwai daga cikin kasashen 10 na farko, wadanda ba su da matsalar Rasha duk a yankin Tarayyar ta Turai suke. Qasar da ta fi kowace a duniya samun maki a bangaren yaki da rashawa ita ce Denmark, wadda take da maki 90. Sai kuma Finland mai maki 88, ta uku kuma ita ce Singapore, wadda ke a kudu maso gabashin nahiyar Asiya. Ga yadda kasashen 10 na farko suka kasance: 1. Denmark – Maki 90 2. Finland – Maki 88 3. Singapore – Maki 84. 4. New Zealand – Maki 83....
A jiya Asabar ne aka sami hatsari a wani wurin hako zinariya dake yammacin kasar Mali da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 48. ‘Yan sanda a yankin da lamarin ya faru ne su ka sanar da faruwar hatsarin a wurin da ake hako zinariya ba tare da izinin hukuma ba,wanda kuma ya rutsa da wata mace da karamin yaronta. Wani jami’in yankin da lamarin ya faru ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a wani wurin hako zinariya da aka kauracewa,da a halin yanzu mata ne su ka fi hako zinariya a cikinsa. A nashi gefen shugaban hukumar masu hako zinariya a kasar ta Mali Abubakar Keita ya bayyana cewa; A kalla mutane 48 ne su ka kwanta dama...
Mataimakin shugaban ya umarci shugabannin NAHCON da su gaggauta daukan kwararan matakan da suka dace domin tabbatar da kare martabar dukkanin maniyyatan Nijeriya. Da yake magana kan soke kwantiragin da suka yi da kamfanin kasar Saudiyyan, shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Saleh Usman, ya ba da tabbacin cewa lamarin ba sai shafi kowani maniyyancin Nijeriya ba. “Ba wani abun damuwa kwata-kwata. Ba wani maniyyancin Nijeriya muddin an masa rajista da za a bar shi,” Usman ya shelanta. Ya kuma yi watsi da zargin da kungiyar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi (FSPWA) ke yi na cewa takaddamar kwangilar na iya kawo cikas ga aikin hajjin.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres wanda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka AU da aka bude a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kai daukin gaggawa ga kasar Sudan ta fuskar bada kayakin agaji. Guterres ya nanata muhimmancin kai kayakin abinci da sauran kayakin da ake bukatuwa da su, domin taimakawa mutanen kasar ta Sudan da yaki ya daidaita. Babban magatakardar MDD ya yi ishara da rawa ta jarunta da kungiyoyin mata suke yi a cikin yanayi mai hatsari,tare dayin kira da a kare rayukan fararen hula. Har’ila yau ya yi kira da a kawo karshen shigar da makamai zuwa kasar ta Sudan da bai wa zaman lafiya dama, a cikin...
Kungiyoyin kare hakkin fararen hula da kungiyoyin fafutuka sama da 70 ne suka bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya yi watsi da shirinsa na kwace iko da yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kaura zuwa kasashe makwabta. Wasikar da aka aike wa Donald Trump ta bayyana matukar damuwar kungiyoyin da suka sanya hannu kan shirin korar Falasdinawa kusan miliyan biyu daga kasarsu ta asali. Wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sun yi kira ga gwamnatin Amurka mai ci da ta karfafa yunkurin diflomasiyya a baya da ya kai ga tsagaita bude wuta a Gaza, maimakon aiwatar da manufofin da za su kawo cikas ga yankin yammacin Asiya. A cikin wasikar da suka fitar sun ce matakin na Amurka...
Ya ce wajibi ne Sin da Amurka su kauracewa rikici, idan ba haka, duniya ce za ta wahala. Sannan ya yi kira da a karfafa tattaunawa da inganta fahimta da karfafa aminci. Ya ce kamata ya yi kasashen biyu su hada hannu wajen shawo kan kalubalen duniya, domin hakki ne da ya rataya a kan Sin da Amurka. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
An Kammala Gasar Wasannin Lokacin Hunturu Ta Kasashen Asiya A Harbin
Ya ce kungiyar ta lura da yadda ake samun karuwar wasu cututtukan daji da aka yi watsi da su a Nijeriya kamar cutar Kansar colo-rectal, yara, obarian, da kuma ciwon daji na jini. Ya yi kira ga ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya, da ta mai da hankali sosai kan cutar daji da aka yi watsi da su a Nijeriya. Shugaban NCS ya kuma bukaci majalisar dokoki ta kasa da ta ware naira biliyan 25 don sauya tsarin kiwon lafiyar cutar Kansa zuwa asusun inshorar lafiya. Ya kara da cewa, NCS ta bukaci majalisar dokoki ta kasa da gwamnatin tarayya da su dace da karin kudade don rufe ba da tallafin naira biliyan 97.2 a cikin shirin nan na...
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Zhang Xiaogang ya fitar da sanarwa kan batutuwan da suka shafi aikin soja a baya-bayan nan. Ya ce, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin. Kuma babu wata tsokana da sojojin Amurka za su yi da za ta iya canza wannan lamari, sabanin haka, za ta iya nuna munafuncin da Amurka ta dade ta na yi ga al’ummomin duniya, kuma za ta iya kara karfafa niyyar jama’ar kasar Sin ta kare ikon kasa da cimma cikakkiyar dunkulewar yankunan kasar baki daya. Game da zarge-zarge marasa tushe da sabon ministan tsaron Amurka ya yi kan Sin, Zhang Xiaogang ya ce, Sin na adawa sosai da hakan. Kuma jama’ar kasar Sin na son zaman lafiya....
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kammala ziyarar da yake yi a Birtaniya. Kakakin ma’aikatar Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce ziyarar ta Wang Yi ta cimma nasara da kyawawan sakamako. Ya ce wannan shi ne karon farko da ministan harkokin wajen Sin ya ziyarci Birtaniya cikin shekaru 10, kuma karon farko da Sin da Birtaniya suka gudanar da muhimmiyar tattaunawa cikin shekaru 7, lamarin dake nuna kudurin bangarorin biyu na ci gaba ingantawa da daidaita dangantakarsu. 2027: Ganawar Kwankwaso Da Aregbesola Ta Haifar Da Cece-kuce A Fagen Siyasar Nijeriya Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Rufe Gasawar Wasannin Hunturu Ta Asiya Karo Na 9 Yayin taron, Sin...
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) karkashin jagorancin shugaban kasa Alhassan Yahaya, ta jaddada aniyar ta na inganta aikin jarida da kuma jin dadin ‘yan jarida a fadin Najeriya. Kungiyar tana aiki tukuru don ganin an zartar da kudurin dokar inganta kafafen yada labarai a majalisar dokokin kasar don karfafa masana’antar. A cikin sanarwar da ta fitar a karshen taron kaddamar da kwamitin koli (CWC), wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, kungiyar na hada kai da Majalisar Dokoki ta kasa, kungiyoyin farar hula, da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an samar da dokar inganta harkokin yada labarai. Sanarwar ta bayyana cewa, CWC ta yanke shawarar gano harkokin kasuwanci don samun kudaden shiga don...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa ‘Operation Safe Corridor’ zai ta tabbatar da canja ƙwaƙwale, haɗe kai magance duk al’amuran da suka shafi ’yan bindiga. Sanarwar ta ƙara da cewa, an tsara shirin ne a ƙarƙashin Operation Safe Corridor a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya yi nasarar sauya ƙwaƙwalen tsoffin mayaƙan Boko Haram tare...
Tawagar ta tattaro hukumomi da suka hada da hukumar kula da yanayi (NiMET), hukumar kula da ayyukan ruwa, da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa. Wannan yana tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (OCHA). A duk duniya, OCHA, wacce ke kula da CERF da Asusun Kula da Ruwa na Kasa (CBPFs) irin su Asusun Ba da Agajin Gaggawa (NHF), tana jagorantar matakai don taimaka wa miliyoyin mutane ta hanyar magance annoba kamar ambaliyar ruwa, fari, da kwalara. A watan Oktoban 2024, CERF ta saki Dala miliyan 5 domin a kara kaimi wajen magance ambaliyar ruwa da kuma magance muhimman bukatu a jihohin Borno da...
“Ba wai kawai sun fatattake su ba ne, sun kwace makamansu, kuma tun a wancan lokacin, har yanzu, zai yi wuya ka ji wani labarin mahara a Tafawa Balewa, don haka, shawo kan kalubalen tsaro, dole sai an saka duk wasu masu ruwa da tsaki a cikin lamarin. “Tsammanin sojojin Nijeriya, ‘yansanda, ko DSS, za su kare kowane dan Nijeriya ko kowace gwamnati, Hakan ba zai yi wu ba,” in ji shi. Ajayi ya kara da cewa, dole ne kasar ta samar da matakan tsaro domin rage nauyi a kan tushen tsare-tsaren tsaron kasa.
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas Ta ce hukumar ta riga ta biya kuɗin gurabe 26,287 na maniyyata, sannan ta tanadi wasu 26,000, da za a tabbatar da su gaba ɗaya kafin ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025. Domin cika wa’adin da Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayar, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tafi Makka domin ƙulla yarjejeniya. Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a...
Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta sanar a yau Alhamis cewa, firaministan kasar Li Qiang, zai halarci bikin rufe gasar wasannin lokacin hunturu ta kasashen Asiya karo na 9, wanda za a yi gobe Juma’a a Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang na kasar Sin. Li Qiang zai kuma shirya liyafar maraba da shirye shiryen da suka shafi huldar kasa da kasa ga shugabannin kasashen waje da za su halarci bikin rufe gasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Kwamandan sojan na Iran Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa, Iran tana da cikakken shirin na aiwatar da umaranin babban kwamandan sojin kasa, kuma akidarmu ta yaki, ta ginu ne akan kariya, amma kuma a lokaci daya za mu fuskanci duk wanda ya kawo mana hari, da karfi. Birgediya janar Hamid Wahidi ya bayyana hakan ne dai a lokacin bikin kaddamar da lambobin yabo da sadaukarwa ga iyalan shahidai na sojan sama, inda ya ce: “A wannan lokacin da ake ciki, Muna cikin wani yanayi mai matukar hatsari a duniya, amma a ranar sojan sama jagoran juyin juya halin musulunci ya shata mana ka’idoji masu kima da za mu yi aiki da su da, kuma za su kasance wadanda...
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bankaɗo ma’aikatan bogi 2,363 da ke karɓar jimillar N193,642,097.19 a kowane wata bayan gudanar da tantancewar ma’aikatan gwamnati. Gwamna Dauda Lawal ya kafa kwamitin tantance ma’aikata a watan Agustan bara don tabbatar da biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000. Kakakin gwamnan, Sulaiman Idris, ya bayyana cewa binciken ya nuna akwai ƙananan yara 220 da ke karɓar albashi a matsayin ma’aikatan gwamnati. Gwamna Lawan Ya Shaidawa Bankin Duniya Cewa Sun Yi Nasarar Yakar ‘Yan Bindiga A Zamfara Babu Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Tsarinmu – Gwamnan Zamfara Rahoton kwamitin ya tabbatar da cewa an tantance ma’aikata 27,109, yayin da 2,363 suka kasance ma’aikatan bogi, 1,082 sun dace su yin ritaya, 395 na aikin kwantiragi, 261 ba su...

Shugaban kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Son Shiga Yaki Amma Tana Shirye Wajen Fuskantar Barazana
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin lamba, yana mai jaddada cewa; Kasarsa ba ta neman yaki da wata kasa, sai dai tana kokarin karfafa dangantakar abokantaka da kasashen makwabta. Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai lardin Bushahar inda ya gana da al’umma tare da jinjinawa sadaukarwar shahidai musamman shahidan wannan lardin, a daidai lokacin da ake cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci,...
Hukumar kula da ‘yan sama jannati na kasar Sin (CMSA), a yau Laraba, ta bayyana sunayen tufafin ‘yan sama jannati da motar zirga-zirga a duniyar wata na aikin binciken wata na kasar. CMSA ta ce, an sa ma tufafin na ‘yan sama jannati suna Wangyu, wanda ke nufin kallon duniyar sama, kuma ya yi daidai da sunan tufafin da ‘yan sama jannati su kan sa lokacin da suka fita daga tashar sararin samaniya, wato Feitian, wanda ke nufin tashi zuwa sararin samaniya. Wata Ɗalibar Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Da Ke Bauchi Ta Rasa Ranta A Haɗarin Mota Yawan Motocin Da Sin Ta Fitar Zuwa Ketare A 2024 Ya Karu Da Kaso 23% Kazalika, sunan motar zirga-zirga a duniyar wata shi...

Kungiyar Hamas Ta Godewa Kasashen Duniya Wadanda Suka Ki Amincewa Da Shirin Trump Na Korarsu Daga Gaza
Kungiyar Hamas a Gaza ta godewa kasashen duniya musamman kasashen Jordan da Masar dangane da kin amincewarsu da korar Falasdinawa a Gaza. Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai kwace zirin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan zai tsugunar da su a kasashen Masar da kuma Jordan, suna so ko basa so. Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto kungiyar tana fadar haka a yau Laraba. Ta kuma kara da cewa. Mutanen gaza basa son rabuwa da kasarsu, ta kaka da kakanni. Kuma suna maraba da dukkan shawarorin da kasashe larabawa da sauran kasashe duniya zasu bayar, don ganin an sake gina Gaza ba tare da an kori falasdinawa daga kasarsu ba. A wani Labari...
Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saïd Iravani, ya bayyana cewa kalaman na Trump na tada hankali sun sabawa dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin MDD. Trump ya ce zai gwammace ya kulla yarjejeniya da Iran maimakon “harba mata bam fiye da kima,” a wata hira da manema labarai a ranar Asabar. “Na fi son kulla yarjejeniya da ba za ta cutar...
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Sake gina Gaza na bukatar kudi sama da dala biliyan 53 Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya fada a ranar Talata cewa: Sake gina yankin Zirin Gaza da yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya lalata yana bukatar kudi sama da dala biliyan 53, ciki har da sama da dala biliyan 20 cikin shekaru uku na farko. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya rubuta a cikin wani rahoto da aka shirya bisa bukatar babban zauren Majalisar Dinkin Duniya cewa: Adadin kudaden da ake bukata don farfado da sake gina yankin a cikin gajeren lokaci, matsakaita da kuma dogon lokaci a Zirin Gaza “an kiyasta kimanin dala biliyan 53 da miliyan 142. A cikin...

’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.” ’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida...
Wani sanatan Amurka yana barazana ga shugaban kasar Tunisiya da neman rusa nasarar dimokuradiyyar kasar Sanatan Amurka Joe Wilson, dan majalisar wakilai daga shiyar kudancin jihar Carolina, ya kaddamar da hari kan shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id, inda ya dauke shi a matsayin “dan mulkin kama karya” tare da yin kira da a kakabawa Tunisiya takunkumi har sai ta dawo kan tsarin dimokiradiyya. Maganganun Wilson, wanda ya shahara da kare matakan muggan laifukan yahudawan sahayoniyya da kuma tsantsar kiyayya ga kungiyoyin gwagwarmaya da dukkan gwamnatocin Larabawa da na Musulunci da suka ki amincewa da Shirin daidaita alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ya fuskanci mayar da martani mai yawa a tsakanin ‘yan siyasar Tunisiya da masu fafutuka kare hakkokin dan Adama,...
3. Wallafa labarin a kasan wannan sanarwar a ɓangaren tsokaci. 4. Wallafa labarin a shafinka na sada zumunta na facebook tare da makala #tak na #GasarLabarunSoyayya #LeadershipHausa #GasarLeadership 5. A kiyaye ƙa’idojin Rubutun Hausa da kuma amfani da daidaitacciyar Hausa da aka amince a yi amfani da ita a hukumance. 6. Ka tabbatar ka sanya lambar wayarka da sanya adireshinka na Imel a kasan labarin da ka kawo, ka kuma turo mana ta Imel dinmu na: [email protected] Za a rufe karɓar gajerun labaran a ranar Alhamis mai zuwa 13/02/2025 da karfe 12, na rana.
Sam Nujoma, dan gwagwarmaya neman yencin kasar Namibiya karkashin gwamnatin wariyar launin fata ta Afrika ta kudu, ya rasu a jiya Lahadi kamar yanda gwamnatin kasar ta Namibi a ta bada sanarwa. Shugaban kasar ta Namibia mai ci, Nangola Mbumba ya ce tsohon shugaban kasar ya na jinya a as wani asbiti a babban birnin kasar Windhoek na kimani makonni 3 amma rai yayi halinsa a daren Asabar da ta gabata ya na dan shekara 95. Shafin yanar gizo na Labarai ‘Africanews’ ya bayyana cewa kasar Namibia ta sami yencin kanta ne daga hannun gwamnatin wariya ta Afirka ta kudu a shekara 1990. Sannan Nujoma ya zama shugaban kasar na farko na tsawon shekaru 15. Sannan aka zabi shugaba mai...
An yi wa dubban mutane gwajin lafiya kyauta a Indonesiya don kauce wa mutuwa da wuri. Za a yi gwajin ga ɗaukacin ‘ƴan kasar ne a ranar murnar bikin haihuwarsu, domin cika alkawarin da shugaba Prabowo Subianto ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe. Jarirai da ƙananan yara da kuma tsofaffi na cikin waɗanda za a fara yi wa gwajin. A watan da ya gabata, gwamnatin mista Prabowo ta fara bai wa miliyoyin yara ƴan makaranta da kuma mata masu ciki abinci kyauta domin rage rashin abinci mai gina jiki da ke shafar yaro ɗaya cikin biyar a Indonesia.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan ziyara ta gwamnan, za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Bankin na Duniya. Cikin jawabin sa a wurin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa dangantakar ta Bankin Duniyar. “Ina so in fara da nuna godiya ta ga Bankin Duniya game da tallafin da ya ke bayarwa a jihar mu. Mun jingina da manufofin Bankin Duniya wajen inganta rayuwar al’ummar mu kawar da talauci da ci gaban ayyukan inganta rayuwa. “Muna sane da ƙalubalen da muka fuskanta, wanda ya shafi gudanar da ayyukan ci gaba a jihar Zamfara, musamman waɗanda suka samu matsala wajen aiwatarwa, sakamakon yanayin da aka shiga. Amma, lallai babu shakka muna...

Kasafin 2025: Kar A Yi Sakaci Macizai Da Birai Su Haɗiye Dala Biliyan 1.07 Da Aka Ware Wa Kiwon Lafiya – Atiku
Ya kuma yi kira da a samar da tsari na gaskiya da rikon amana don bin diddigin yadda ake kashe kudaden da aka ware domin amfanin jama’a.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta yi kokarin dakile duk wani makirce-makircen da makiya ke kitsawa. Shugaban na Iran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga dimbin jama’a da suka halarci bikin cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a shekara ta 1979 a birnin Tehran yau Litinin. Shugaba Pezeshkian Ya soki ikirarin shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan na cewa yana son tattaunawa da Iran yayin da a lokaci guda ya ba da umarnin kakaba wa Iran takunkumi kan man da take fitarwa zuwa sifiri.” Trump ya yi ikirarin cewa Iran na kawo cikas ga tsaron yankin amma “Isra’ila ce, tare da goyon bayan Amurka,...

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Ce: Hamas Ta Yi Rawar Gani Wajen Kare Kanta
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai. Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988),...
Wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda (ASP), Shafi’u Bawa, da ke aiki da Rundunar 61 Police Mobile Force a Kontagora da ke Jihar Neja, ya hallaka kansa har lahira. Wani jami’in dan sanda ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar. Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari An tsinci gawarsa rataye a cikin dakinsa. Majiyoyi sun ce mahaifinsa, Malam Usman Bawa ne, ya fara gano abin da ya faru sannan ya kai rahoton lamarin zuwa ofishin ’yan sanda da ke Kontagora. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce: “A ranar 8...
A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ta gudana a birnin Beijing na Sin, a shekarar 2022. An ce, gasar wasannin kankara ta wannan karo ta samu halartar ‘yan wasa fiye da 1270 da suka zo daga kasashe da yankuna 34 dake nahiyar Asiya, alkaluman da suka kai matsayin koli a tarihi. Inda har wasu kasashen da ba sa samun yanayi mai sanyi da muhalli mai kankara a cikin gida, kamarsu...
An bayyana cewa Iran ce kasar ta 10 a duniya wajen samar da wutar lantarki, da yawan megawati dubu 94 da 846. Manajan da yake kula da tsara manyan ayyuka a ma’aikatar makamashi ta Iran, Behruz Muradi ya bayyana cewa, shekru 46 da su ka gabata, wato a lokacin juyin juya halin musulunci, yawan megawatin da Iran take samarwa ya yi kasa da wanda ake da shi a yanzu har sau hudu. Manajan ya kuma kara da cewa wutar lantarki da ake da ita a Iran da karfin tsarin da take da shi, tana taka rawa mai muhimmanci wajen gina tattalin arzikin kasar. Haka nan kuma ya ce, da akwai kyakkyawan tsarin da ake da shi ya samar da cigaba...
A ranar Lahadi ne mahukuntan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars suka bayar da sanarwar dakatar da mai koyarwa, Usman Abdallah mako uku, sakamakon rashin kokarin kungiyar a baya bayan nan a bana da kuma nuna halin rashin hakuri ga magoya bayan kungiyar a lokacin da aka tashi daga wasan da kungiyar ta tashi canjaras da kungiyar Bayelsa United a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata a Kano. A wata sanarwa da aka fitar a shafin sada zumunta na facebook, kungiyar ta ce kociyan ya nuna halin rashin da’a, bayan tashi ba ci a wasa da Bayelsa ba kuma halayyar da ya nunawa magoya baya ba ta dace ba saboda a matsayinsa na mai koyarwa dole ne sai...
Wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iraki ya ce: Juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wani sabon samfuri na hadin kan al’umma Ayatullah Mojtaba Hosseini, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iraki ya bayyana muhimmancin hadin kan al’ummar musulmi da kuma nauyin da ya rataya a wuyan musulmi na daidaiku da na al’umma dangane da manufofin juyin juya halin Musulunci, yana mai cewa: juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wani sabon salo na hadin kan al’ummar musulmi. A jawabin da ya gabatar na zagayowar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran da aka gudanar a tsohon gidan da Imam Khumaini (r.a) da ya zaune a birnin Najaf, Ayatullah Husaini ya jaddada muhimmancin hadin...
Ga wasu manyan ‘yan kwallo da tauraronsu ke haskawa a duniya, wadanda asalin ‘yan Nijeriya ne, wato ko dai iyayensu baki daya ko wani daga cikin iyayen ‘yan Nijeriya ne. Jamal Musiala (Jamus) Matashin dan wasa Jamal Musiala, wanda aka haifa a ranar 26 ga Fabrairun shekarar 2003, fitaccen dan kwallon kasar Jamus ne da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta Jamus din kuma yana cikin matasan ‘yan kwallon da suke tashe a duniya a yanzu saboda ba za ka lissafa matasan ‘yan wasa guda biyar ba a duniya ba tare da ka saka sunansa ba. An haife shi ne a garin Stuttgart da ke Jamus, amma mahaifinsa mai suna Daniel Richard asalin can Nijeriya ne, wanda ya...
A daren ranar 6 ga wannan wata, an gudanar da wani biki mai taken “Bikin Bazara Namu” a cibiyar hukumar bunksa ilmi da kimiyya da fasaha da al’adu ta MDD, wato UNESCO dake birnin Paris na kasar Faransa, wanda babban rukunin Sin dake hukumar, da gidan talabijin na lardin Henan na kasar Sin suka karbi bakuncin gudanar da shi, don murnar cewa, Bikin Bazara na al’ummar kasar Sin ya shiga cikin jerin bukukuwan al’adun gargajiya da bil’adama ya yi gado a duniya. Babbar wakiliyar Sin dake hukumar UNESCO, Yang Xinyu ta bayyana cewa, an yi wannan shagali ne don murnar bikin gargajiya na al’ummar kasar Sin don more al’adu tare da sassan duniya, da kara matsa kaimi ga yin hadin...

Thomas Bach Ya Bai Wa Cmg Izinin Sarrafa Watsa Labarun Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Milan Ta 2026
Albarkacin bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 dake gudana a birnin Harbin na Sin, shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa, Thomas Bach ya ziyarci cibiyar yada labarai ta gasar a jiya Juma’a, kuma ya yi hadin kai da shugaban rukunin gidajen rediyo da talibijin mallakin kasar Sin, wato CMG, Shen Haixiong, don bai wa runkunin na CMG damar tsarawa da kuma sarrafa watsa labarun gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Milan da Cortina d’Ampezzo ta shekarar 2026. Shen Haixiong ya ce, gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya da ake shiryawa a birnin Harbin, wata kasaitaciyyar gasa ce ta kasa da kasa da Sin ta shirya bayan...
Xi: Kasar Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da IOC Don Inganta Wasannin Olympic Na Duniya

Aikin Gina Babbar Mayankar Dabbobi Zai Taimaka Wajen Kara Samar Da Wadataccen Nama A Nijeriya – Minista
A cewar Maiha, kafa wajen bayar da horo da kamfanin na ABIS ya yi, zai cike gibin da ake da shi a fannin kiwo da kuma bayar da gudunmawa wajen kara habaka tattalin arzikin fannin. Ministan ya kara da cewa, bayar da ingantaccen horo a fannin bunkasa kiwo, zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci da kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar, musamman ma matasa. Maiha, ya kuma bai wa kamfanin na ABIS tabbacin cewa, ma’aikatarsa, za ta bai wai kamfanin goyon bayan da ya dace, domin samar da kwararru a fannin bunkasa kiwon kasar. Da yake yin tsokaci kan jajircewa da mayar da hankali na kamfanin na ABIS, Maiha ya bukaci kamfanin ya yi hadaka da ma’aikatarsa,...
Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu damar baiwa karin wurare hidima, mun fadada zirga-zirga daga Indode da Adama zuwa Mojo, Dire Dawa, da kuma wurin ajiye kaya na Sabata.” Uma ya kara da cewa, EDR yana maye gurbin tsoffin kayayyakin aiki da sabbi, da kuma gyara wadanda suka lalace, kana ya kara yawan jiragensa daga jiragen kasa takwas zuwa 21 da taragu 892 zuwa 935. Yana mai cewa “Jajicewar da muka...
“Kowannen masu hada-hadar musayar kudade da aka san da zamansu da suka biya kudinsu na sake sabunta lasisinsu na 2025, an shawarce su da su rubuta zuwa ga Daraktan sashen kudi da tsare da sanya ido na Bankin, domin su karbi kudansu, da aka dakatar da biyan kudi, zuwa cikin asusunsu.” Inji Takardar Takardar ta bayar da tabbacin cewa, Bankin na CBN, har yanzu a tsaye yake akan kafarsawajen ganin ya samar da daidaito da bin ka’ida, musamman wajen gann ana gudanar da hada-hadar musayar kudade na waje a kasuwar musayar kudi.
Bayanin da babban bankin kasar ta Najeriya ya fitar, ya bayyana cewa an sami wannan koma bayan ne a cikin makwanni uku da su ka gabata. Bayanin na babban bankin na Najeriya ya ci gaba da cewa, kudaden ajiyar Najeriya na waje da a cikin watan Disamba sun kai dala biliya 40,887, sun ragu, sun zama dala biliyan $39.723 daga ranar 31 ga watan Janairu 2025. An bayyana koma bayan ne a kudaden waje na ajiya da babban bankin kasar yake da su, da ya kamata ace a ranar 4 ga watan Febrairu ne za a fitar da kididdiga akan halin da kudaden wajen suke ciki,amma ba a yi ba. Bugu da kari wannanbayanin ya fito ne daga kamfanin dake...

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Lokacin Hunturu Ta Asiya Karo Na 9
An kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta nahiyar Asiya karo na 9 a yau 7 ga wata da dare, a birnin Harbin dake lardin Heilongjiang na kasar Sin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin tare da kaddamar da gasar a hukumance. (Zainab Zhang)
Kazalika, a Arewacin Nijeriya, Robar Tumatir mai nauyin kilo 25 yanzu, ana sanar da ita kan Naira 6,500. Shugabar kungiyar masu noman Tumatair da sarrafa shi ta kasa, Rabiu Zuntu ta sanar da cewa, an samu girbin Tumatir mai yawan gaske, duba da cewa; yanzu ana cikin watan Fabrairu, lokacin da ake samun yawaitarsa. A cewar tata, tarin yawan nasa ne ya sa aka samu faduwar farashinsa a kasuwanni, wannan dalili ne ma ya sanya, don gudun kada manoman su yi asara; suke sayar da shi kan farashi mai sauki. “Daga watannin Janairu, Fabrairu zuwa Maris; ana samun kwantan Tumatir, yanzu kuma muna da injinoni masu kyau na sarrafa Tumatirin, wanda hakan zai sa a samu raguwar farashin”, in ji...
In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba. Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya...
Hujjar mu a nan ita ce, kundin tsarin mulkin Nijeriya, sama yake da kowanne dan kasar da kuma sauran dokokin kasar, duba da cewa, kundin ya bayar da damar a yi Shari’ar a bisa adalci kuma a bayyane, ga wadanda ake tuhumar da aikata laifi. Bugu da kari, dole ne mu tuhumi matakan da mahukuntan kasar suka dauka na yiwa wadanda ake tuhumar Shari’ar a, asirce. Akwai dimbin tambayoyi a zukatan ‘yan Nijeriya wanda kuma suke bukatar amsa, misali, a ina ne aka cafke su? ta yaya ne, aka kama su? yaushe ne, aka gurfanar da su, a gaban Kotu? Shin an barsu sun dauki Lauyoyin da za su tsaya masu gaban Kotu? har tsawon wanne lokaci ne, suke ci...
Gwamnatin Iran ta bayyana cewa duk wata matsin lamba kan kasar ta Donald Trump za ta cutura. Iran dai ta caccaki matakin da shugaban AMurka ya dauka ind aya sanya hannu kan umurnin sanya sauraren matakn matsin lamba kan Tehran a game da shirinta na nukiliya. Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana a wani sako a X cewa siyasar matsim lamba ta gaza a baya, kuma za ta ci karo da tsayin daka mai karfi. Abbas Araghchi ya kara da cewa abu ne mai sauki a samu hanyoyin tabbatar da cewa Iran ba ta nemi kera makamin nukiliya ba. To amma a sa’i daya kuma wajibi ne Amurka da kasashen yammacin duniya su dage takunkumin karya tattalin arziki da suka...
Yayin da ake fuskantar matakan cin zarafi daga wata kasa daya tilo a duniya, kasar Sin ta lashi takobin daukar kwararan matakai don kare hakkoki da muradunta, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, He Yongqian ta bayyana a yau Alhamis. Mai magana da yawun ma’aikatar ta fada a wani taron manema labarai da aka gudanar cewa, kakaba karin haraji da Amurka ta yi ita kadai, ta yi matukar saba wa ka’idojin kungiyar kasuwanci ta duniya, wato WTO, wanda ke nuni baro-baro a fili da ra’ayi na kashin kai da gicciye kariyar ciniki. Don haka, a cewar jami’ar ma’aikatar, yunkurin na Amurka ya yi matukar kawo cikas ga tsarin gudanar da ciniki a tsakanin bangarori daban-daban,...

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Lokacin Hunturu Ta Kasashen Asiya Karo Na 9 A Harbin
Xi Jinping Zai Halarci Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Lokacin Hunturu Ta Kasashen Asiya Karo Na 9 A Harbin