2025-04-27@10:24:19 GMT
إجمالي نتائج البحث: 494
«Shahid Raja»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana hare-haren baya-bayan nan da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar a matsayin shirin masu nufin tada zaune tsaye da kawo cikas ga zaman lafiyar jihar ne a maimakon a alakanta harin da rikicin manoma da makiyaya. Da yake karin haske kan lamarin, Mista Aradong ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da kayan abinci da sauran kayayyaki. Mista Aradong, wanda ya yabawa gwamnatin jihar da jami’an tsaro bisa fara gudanar da binciken gaggawa da suka yi, ya kuma bukaci a kara tura jami’an tsaro a yankunan da lamarin ya shafa. Da yake jawabi yayin ziyarar, Mista Jatau, wanda ya jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu yayin...
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana ci gaba da tsare kananan yara Palastinawa sama da 350 a gidajen yari da wuraren da ake tsare da fursunoni. Sanarwar hadin gwiwa da hukumar kula da harkokin tsare-tsare, da “Kungiyar Fursunonin palasdinu”, da kuma “Cibiyar Kare Hakkokin Bil Adama ta Al-Dameer” suka fitar, ta bayyana cewa, yaran na fuskantar matsaloli Ciki har da azabtarwa, yunwa da gangan, da rashin kulawar likita. Wadannan cibiyoyi sun jaddada cewa yaran Palasdinawa su ma suna fuskantar tauye hakkinsu, wanda irin wannan hali ne ya yi sanadin shahadar wani yaro a cikin makon...
Gwamnatin Kasar Iran ta bada sanarwan samun sabbin ci gaba a fagen fasaha da kuma kayakin da suka shafi makamashin Nukliya, wanda za’a baje kolinsa a ranar 9 ga watan Afrilu na wannan shekarar , wato ranar makamashin Nukliya ta kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto mataimakin shugaban kasa kuma shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Mohammad Eslami yana fadar haka a yau Lahadi. Ya kuma kara da cewa, masana fasahar nukliya ta kasar sun samar da sabbin ci gaba a fagen makamashin nukliya wadanda suka hada da magungun wadanda suka yi amfani da sinadarin Nkliya don samar da su, da kuma ci gaba a fannin ilmi da dama, duk tare da fasaha da kuma...
Ya kuma bukaci jama’a musamman mazauna Damaturu da su kwantar da hankulan su, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba. Abdulsalamu ya bada tabbacin aniyar gwamnati na wanzar da zaman lafiya da tsaro, yayin da ya yi gargadi kan yada labaran karya da ka iya haifar da firgici a tsakanin ‘yan kasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Olunloyo ya jagoranci jihar Oyo tsakanin 1 ga Oktoba, 1983 zuwa 31 ga Disambar 1983. Rasuwar marigayi dan siyasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon Editan jaridar Nigerian Tribune, Barista Oladapo Ogunwusi ya fitar a ranar Lahadi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin kasar Sin ta yi kakkausar suka da bayyana adawarta ga matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya.” A cikin wata sanarwar da ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin na Amurka, wanda ya kasance daukar mataki bisa radin kai, da kuma kariyar cinikayya da cin zarafin tattalin arziki. Sanarwar ta kara da cewa, ta hanyar fakewa da abin da take kira “ramuwar gayya” da “adalci,” a zahiri dai Amurka ta tsunduma a aiwatar da dabarun danniya da babakere, tana neman cimma manufarta ta “Amurka na gaba da komai” da kuma “Amurka ta fi kowace kasa.” Har ila yau, Amurka na amfani da harajin fito don kawo cikas ga tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa,...
(3).sinadare gyaran jiki: to anan fa matsalar take don gaskiya awannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kinsha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda anfison aga amarya acike baza ki gane dagaske nake ba sai kin zauna nan awaje namiji yagama tsaraki yana ce miki kin hadu kina jin kanki kawai sai ranar daran farko za ki fara ganin canji. Saboda haka koda bayanshi ma akwai wasu supplement dazasu kara miki kyau lokacin aurenki yakamata kinemo asalin original kisha domin yawancin mata dakike ganin jikinsu sumul sumul kamar su sukayi kansu ki gansu kamar alashe yanzu duk su suke sha shikuma gaskiya beda wata matsala da yawa domin suna kokari wurin inganta...
A yayin hirar Abdullahi Shuaibu ya ce “Ni dai suna na Abdullahi Shuaibu, amma al’uma na kirana da Karkuzu, ko kuma Abdullahi Kano, yanzu shekaru 43 kenan ina wannan harka ta fina finan Hausa, amma yanzu wasu lokutan sai in kwana ba ni da abin da za a ci a gida na, kuma wani abin tausayi, ni Karkuzu a yanzu zancen da na ke, wannan gida da nake ciki an sa shi a kasuwa, ba gida na ba ne, haya nake yi. Ya ci gaba da cewa, yanzu a cikin wannan al’amari da na ke yi, in an ce na mallaki gida mai dimbin yawa, wadansu da za su ke kallo na sai su ce gaskiya ne, amma wallahi tallahi,...
Ministan harkokin wajen kasar Nijar ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a Rasha za ta aika tawagar diflomasiyya a Nijar. Nijar ta tabbatar da aniyar ta na karbar bakuncin ofishin jakadancin Rasha a karon farko cikin sama da shekaru talatin, in ji ministan harkokin wajen kasar ta yammacin Afirka, Bakari Yaou Sangare a ranar Alhamis. Bayanin ya fito ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Moscow bayan tattaunawa tsakanin ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da takwarorinsa na kasashen Nijar, Mali, da Burkina Faso. M. Sangare ya bayyana cewa, a halin yanzu Nijar na neman wurin da ya dace domin gina ofishin jakadanci na tawagar diflomasiyyar Rasha a kasar, ya kara da...
Alhamdulillah, a makon jiya ne muka fara gabatar da wannan rubutu wanda fahimtar malaman Mazhabar Malikiyya ce a kan azumin Sitta Shawwal a wani yunkuri na warware shubuhar da ake samu a tsakanin mabiya mazhabar a nan Najeriya. Yayin da wadansu ke kokarin haramta azumin wadansu kuma nema suke yi su mayar da shi wajibi. Muna fata da wannan dan rubutu da muka ciro daga shafin Cibiyar Imam Malik ta Intanet (Markazu Imam Malik) za a kawar da wannan takaddama. Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan 1. Na ce ya dace a gabatar da biyan azumi ban ce ya wajaba daga farko ba. Ya inganta a yi Sitta Shawwal...
Gwamnatin Jihar Borno ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo wajen yin kalamai masu nuna barazana da al’adunmu na rashin ɗa’a da rashin sanin ya kamata. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar yaɗa labarai da tsaron cikin gida ta jihar Borno ƙarƙashin Kwamishinanta Farfesa Usman A. Tar ta fitar, gwamnatin ta yi Allah-wadai da irin munanan kalamam da suke yi da kan iya haifar da barazana. An kai wa motar haya hari an kashe mutum 2 da sace wasu a Benuwe ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi Inda ta yi nuni da cewa, waɗannan kalaman sun saɓawa al’adunmu da tsarin rayuwarmu, musamman a shafukan sada zumunta na...

Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Amurka Da Jakadan Sin A Burtaniya Sun Nuna Adawa Da Matakin Harajin Fito Na Ramuwar Gayya Da Amurka Ta Dauka
A ranar Alhamis ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Amurka da jakadan Sin a Burtaniya Zheng Zeguang, suka bayyana matukar kin amincewa da harajin fito “na ramuwar gayya” da Amurka ta kakaba. Suna masu nuni da cewa, Amurka ta sanar da karin harajin fito kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe da dama ciki har da kasar Sin, ta hanyar fakewa da abin da take kira ramuwar gayya, ofishin jakadancin Sin da ke Amurka ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, matakin ya saba wa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kuma ya saba wa ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban. Kana, ya bukaci Amurka da ta gyara kurakurenta, tare da warware sabanin cinikayya tsakaninta da kasar Sin...
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce hare-hare da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan jihar wasu ne ke ɗaukar nauyinsu ba rikicin manoma da makiyaya ba ne. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin baje kolin kayayyaki da fasaha da ƙungiyar Tincity Fashion Week ta shirya a daren Juma’a a Abuja. An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya bayar da rahoton cewa, a ranar 2 ga watan Afrilu, wasu ’yan bindiga sun kai hari a ƙauyukan Manguno, Daffo da Josho na ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar. Maharan sun kashe mutane da dama tare...
Kasar ta sha alwashin ci gaba da taimakawa kasashen nan guda uku na kawancen sahel da suka hada da Mali, Burkina faso da kuma Nijar a fannin tsaro. Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ne ya bayyana haka ranar Alhamis bayan ya gana da takwarorinsa na ƙasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar a birnin Moscow, yana mai cewa a shirye suke su taimaka domin bunƙasa alaƙar soji da ƙasashen. “Ina jaddada aniyar Moscow ta taimakawa domin samar da gamayyar rundunar soji ta yankin Sahel, tare da ƙarfafa dakarun soji da sauran jami’an tsaro na waɗannan ƙasashe uku ta hanyar ba su horo da makamai,” in ji Lavrov. Wannan bayanin ya fito ne a yayin taron manema labarai da bangarorin...
SShugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana alhininsa bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma’a yana mau shekaru 68 a duniya. Mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan Harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da sanarwar, inda ya jaddada muhimmancin gudummawar Dr. Abdulaziz wajen koyar da addinin Musulunci da kuma ci gaban matasa. Shugaba Tinubu ya yabawa ƙoƙarin marigayin wajen yaki da tsattsauran ra’ayi da rikicin Boko Haram tun farkon bayyanar kungiyar. Ya ce al’ummar Musulmi sun yi babban rashi bisa mutuwar Dr. Abdulaziz wanda kan jajirce kan gaskiya da ɗa’a. Shugaban ya kuma yi addu’a ga Allah Ya jikansa, tare da...
Shugaba Tinubu ya zanta da manema labarai bayan kammala Sallar Idi na karshen watan Ramadan a filin da aka gabatar da Sallar Idi na kasa a Abuja ranar Lahadi. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya bukaci ‘yan Nijeriya da kada su koma kan aikata abubuwan da su ba ta dace ba, a maimakon haka, ya bukace su da su dage wajen aiwatar da kyawawan dabi’un game da darusan da suka koya a watan Ramadan. A cikin hudubar da babban limamin masallacin kasa dake Abuja, Dakta Abdulkadir Salman Sholagberu, wanda ya jagoranci Sallar ya gabatar, ya jaddada bukatar Musulmi su ci gaba da gudanar da ibadar da suka koya a Azumin watan Ramadan,...
Matakan harajin fito na Amurka na haifar da koma-bayan tsarin cinikayyar duniya. Game da wannan batu, kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ta gudanar da wani binciken jin ra’ayin al’umma ga masu amfani da intanet na sassan kasa da kasa, inda suka yi tir da irin wannan abun da Amurka ta yi, al’amarin da a cewarsu, ka iya janyo ramuwar gayya daga kasashe daban-daban, har ma zai iya ta’azzara yakin harajin fito a duniya, da kawo babbar illa ga tattalin arzikin duniya. Kashi 82.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna cewa, yayin da ake fuskantar rashin daidaiton ci gaba da karfin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, neman cike gibin cinikayya da...
Ya roƙi Allah da Ya ji ƙansa, tare da bai wa iyalansa da almajiransa haƙurin rashinsa. Hakazalika, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana kaɗuwarsa game da fitaccen malamin. Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta. “Ina miƙa ta’aziyya ta ga iyalai da almajiran Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi. “Dokts Dutsen Tanshi ya kasance abin tunawa saboda jajircewarsa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci. “Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi,” in ji Kwankwaso. Dokta Abdulaziz ya kasance mashahurin malami wanda aka san shi wajen faɗar gaskiya, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi da ƙarfafa zaman...
Na ji dadi da yadda ka yi kira ga sauran Malamai da su zama masu kwadaitar da neman Ilimi a kowanne fanni, sannan su kaurace wa furta haramci a kan abubuwan da Shari’a ba ta yi haramci a kai ba. Tabbas, ayoyin Alkur’ani suna nan kamar yadda aka saukar kuma ba za su sauya ba har duniya ta nade, amma fahimtarsu tana sauyawa daidai da zamani, don haka, bai dace a yi watsi da kimiyya da fasahar zamanin nan ba da ake ganin na turawa ne kawai, matukar ba a samu fiye da tasu ba. Akramakallah, gaskiya ne, ya dace Malamai su rika ba da fatawa da ta yi daidai da zamaninsu da kuma fahimtar da al’ummar Musulmai Isharori na...
Yayin gabatar da rahoton an raba lambar yabo ga Hakiman da aka fi samun gudunmawar Zakkar daga gundumominsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar. A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi, ya yi kira ga mambobin kungiyar SCO da su yi Allah wadai da kalaman da shugaban na Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya ce yana da hadari. Majid Takht Ravanchi ya yi kakkausar suka ga barazanar harin bam da Trump ya yi a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, hakan ya keta...
Ministocin harkokin wajen kasashen kawacen sahel na AES da ya hada Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar, na wata ziyarar aiki a kasar Rasha. Ana sa ran ministocin za su kasance a birnin Moscow a yau Alhamis da gobe Juma’a, don tattaunawa, da zurfafa hulda tsakanin bangarorin biyu, kamar dai yadda aka bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwarsu. Sanarwar, ta ce shawarwarin da ministocin kasashen kungiyar ta AES za su yi tare da ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov, wani bangare ne na burin shugabannin kasashen uku na yankin sahel da sojoji ke mulki da kasar Rasha, na fadada hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki da kuma tsaro. Har ila yau, sassan biyu za su zanta game...
Ana yi wa Shehin Malamin laƙabi da Dr. Tauhidi saboda da’awarsa ta ƙarfafa ne akan Tauhidi da kuma riƙo da Sunnar Annabi (S.A.W.) da kuma yaƙi da fararrun al’amura a cikin addinin Islama. Za a yi sallah jana’izar Babban Limamin da misalin ƙarfe 10 na safe a Masallacin Idi na Games Village, Jihar Bauchi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi Amurka da cewa. duk wani harin soji a kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai haifar da “mummunan sakamako” ga daukacin yankin. Sergei Ryabkov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata mujallar harkokin kasa da kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari idan har ta kasa cimma matsaya da Washington kan shirinta na nukiliya. Ryabkov ya ce, “Hakika ana jin barazanar, ana kuma jin bayanai kan abubuwan da suka dace,” in ji Ryabkov, yana mai cewa “Sakamakon hakan, musamman idan harin ya kasance kan kayayyakin nukiliya, na iya zama bala’i ga daukacin yankin.” Ya ce sabbin kalaman na Trump za su kara...
A kokarin magance matsalar karancin ruwan sha da garin Rano ke fuskanta na tsawon shekaru, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da ta fara amfani da Madatsar Tiga don samar da ruwa mai a garin. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin Sarkin Rano, Ambasada Dr. Muhammad Isa Umar, wanda ya kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a Fadar Gwamnati da ke Kano. Gwamna Yusuf ya yaba wa Sarkin Rano bisa jajircewarsa wajen kare muradun al’ummarsa, inda ya tabbatar masa da cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalar ruwa a garin. Ya bayyana cewa an riga an tsara shirin gina rijiyoyin burtsatse tare da hadin gwiwar ƙaramar...
Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kai wadannan hare-hare ne a garin Rasul Isa da lardin Salif a yammacin birnin Hudaida na kasar ta Yemen. Sannan tashar talabijin ta Almasirah ta bayyana cewa akalla mutum guda ne ya rasa ransa a wannan harin sannan wani guda ya ji rauni. Har’ila yau jiragen yakin Amurkan sun kai hare-hare kan yankin...
Sojojin HKI sun kashe akalla mutane 80 a asbitin Jabaliya a safiyar yau Alhamis, sannan sji ne hari mafi muni da ta kai kan gaza tun bayan da ta sake komawa yakin tufanul Aksa, makonni biyu da suka gabata. Asbitin hukumar UNRWA ta MDD na daga cikin wuraren da yahudawan suka kai hare-hare a garin a safiyar yau. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Asbitin na daga cikin wuraren da HKI ta kaiwa hari a jiya Laraba inda. Sannan a safiyar yau ta kashe mutane akalla 22 a kan cikin asbitin kadai sannan daga ciki har da yara, da mata da kuma jami’an yansanda na gaza. A jiya laraba kadai sojojin yahudawan sun kai hare-hare masu...
Daga ƙarshe, ya buƙaci sojojin da su ƙara ƙwazo domin tabbatar da cikakken tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su. Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar. Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama. Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano. Kano, jiha ce da hamayyar siyasa da rikicin masarauta ya dabaibaye ta. Akwai hamayyar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyun NNPP mai mulki a jihar da takwararta ta...
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai. Da yake amsa...
Shugaba Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin babban ginshikin masarauta kuma mai neman ci gabanta. Shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kano da majalisar masarautar Kano da kuma iyalan marigayin bisa wannan rashi mara misaltuwa. Shugaban ya yi addu’ar Allah ya sa Jannatul Firdaus, ta zama makoma ga Galadima. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau Talata, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dauki matakan ramuwar gayya domin mayar da martani game da sanarwar da Amurka ta fitar ta saka takunkumin biza a kan jami’an kasar Sin, bisa hujjar hana izinin shiga yankin Xizang mai cin gashin kansa, da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A yayin taron manema labarai da aka saba yi a-kai-a-kai, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana cewa, yankin Xizang a bude yake ga kowa da kowa, kuma ba a hana baki daga kasashen waje shiga ba, inda ya kara da cewa, yankin yana karbar dimbin matafiya da sauran al’ummomi da dama daga sassa daban-daban a kowace shekara, domin ko a shekarar...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu. A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekara 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka gwabza na tirjiya a kan zaluncin kasar Japan, da kazamin yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet, da kuma yakin duniya na biyu. Atisayen Dakarun PLA Horo Ne Mai Tsanani Ga Masu Rajin Neman ’Yancin Kan Taiwan Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara Wang, ya yi...
Yakin cinikayya ba zai taba durkusar da kasar Sin ba, sai dai kaikayi ya koma kan mashekiya. Yayin da wasu kasashen ke aiwatar da kariyar cinikayya da kokarin rufe kofarsu ga sauran sassan duniya, kasar Sin ta kara bude kofarta, tana kuma maraba da ’yan kasuwa daga kasa da kasa. Maimakon kawo cikas, kasar Sin za ta lalubo hanyoyin samun karin ci gaba ga kanta da sauran sassan duniya, kuma kariyyar cinikayya da ake yi, zai rikide ya zamo alheri a gare ta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
Hukumomin Myanmar sun buƙaci ƙasashen duniya su hanzarta tura agaji, yayin da jami’an ceto ke ƙoƙarin gano mutanen da suka maƙale a cikin baraguzan gine-gine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kebbi, NUJ, ta taya gwamnatin jihar da al’ummar musulmin jihar murnar zagayowar ranar Sallah. Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar da Sakatare, Ismail Adebayo, ta yi murna da al’ummar musulmin jihar kan kammala azumin kwanaki 29 na watan Ramadan da kuma bikin Eid-Fitr. Ta yi kira da a zauna lafiya da juna a tsakanin al’ummar jihar bisa koyarwar addinin Musulunci da manzon Allah mai tsira da amincin Allah tare da la’akari da muhimmancin watan Ramadan da Idi-El-Fitr. Majalisar ta yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Nasir Idris kan kayayyakin abinci da aka rabawa musulmi a...
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan. Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara. Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai; Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Karshe. Bayan haka, a karshen ko wane azumin watan Ramadan akan samu tambayoyi kan matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Imamuna Malik (RA) da hukuncin azumtarsu kafin biyan azumin Ramadan musamman ga iyaye mata. A yau za mu gabatar da wani abu kan bayanan malaman wannan mazhaba game da wannan lamari musamman ganin ana samun wadanda suke ganin azumin bai inganta ba: Shin ya wajaba a gabatar da biyan azumin Ramadan kafin yin Sitta Shawwal? Mai tambaya ya yi tambaya cewa: Mace ce akwai azumin Ramadan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Al-Qur’ani mai girma a cikin suratul Baqarah, Allah Ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharuɗan azumtar watan Ramadana. Kamar yadda malamai suka sha faɗi, wannan wata na ɗauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji. Kazalika, hadisai sun ruwaito falalar azumtar kwanaki shida na watan Shawwal, watan da ke biye da Ramadan. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan falalar da ke akwai ga wanda ya azumci kwanaki shidda na watan...
Mai martaba Sarkin Lere dake Kaduna Alhaji Sulaiman Umaru ya amince da nadin Sani Ahmed Lere Sardaunan Matasa zuwa Falakin Lere. Hakan na kunshe ne a cikin takardar nadin da Sakataren Majalisar kuma Sadaukin Lere Alhaji Muhammad Lawal Ahmed ya sanya wa hannu. Alhaji Muhammad Lawal Ahmed yace sabon nadin ya fara aiki ne nan take. Ya bayyana cewa nadin Sani Ahmed Lere a matsayin Falakin Lere daga matsayinsa ne daga Sardaunan Matasan Lere wakilin Matasa a Masarautar zuwa Falakin Lere dan Majalisar Sarki kuma PPS ga Sarki.
Kungiyar bada agaji ta RED CROSS ta yi allawadai da HKI saboda kissan likitoci 8 a garin Rafah na kudancin gaza a ranar 23 ga watan Maris da muke ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a jiya lahadi bayanda aka basu daman dauko gawakin likitocin wadanda suka rasa rayukansu a cikin watan Motar amblance ta daular marasa lafiya. Labarin ya bayyana cewa lokitocin suna kan hanyarsu ta zuwa unguwar Hashasha inda HKI ta kai hare-hare kan Falasdinawa don basu taimakon gaggawa. Banda haka sai da aka dauki mako guda cur da kashe likitocin kafin sojojin yahudawan su bada damar a dauki gawakin nasu. Ya zuwa yanzu dai tun bayan fara yakin Tufanul...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumin Ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka haɗa da ƙara ƙaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da al’umma da kuma falala masu yawa da ba su misaltuwa. Wani sauyi da watan azumin watan Ramadana ke zuwa da shi shi ne canjin yanayin cimar al’umma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma buɗe-baki. Bayan kwanaki 29 zuwa talatin na samun waɗannan canji, ta waɗanne hanyoyi ne al’umma za su koma cimaka kamar yadda suka saba gabanin watan Ramadana NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah...
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya. Bayan haka, a ranar Asabar ce muka kawo karshen azumin watan Ramadan mai albarka na bana. Saudiyya ta kama wasu ’yan Najeriya da suka daga hotunan ’yan siyasa a Harami An kai hare-haren ta’addanci fiye da dubu 5 cikin shekaru 3 a Yammacin Afrika Yanzu kuma za mu duba wasu batutuwa da suka shafi Azumin Sitta Shawwal, musamman a Mazhabar Malikiyya wadda muke bi a nan Najeriya da sauran kasashen yammacin Afirka. Wani lokaci akan samu wadansu cikinmu har ma da malamai su soki azumin da sunan bai inganta ba a Mazhabar Malakiyya, don haka...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan na Ramadan. Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa shugabanni jagorancin don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma. Namadi ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa. ...
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji cin mutuncin shugabanni yayin da suke bayyana matsalolinsu, inda ya jaddada cewa girmamawa da ladabi suna fi tasiri wajen samun mafita. “Idan ka zagi shugabanka, ta yaya kake so ya taimaka maka?” in ji shi. Masar ta miƙa wa Hamas da Isra’ila tayin tsagaita wuta Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah “Amma idan ka yi magana da ladabi, zai saurare ka kuma ya ɗauki mataki.” Da yake jawabi bayan sallar Idi a Sakkwato, Sarkin Musulmi, ya buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a da kuma zaman lafiya da ci gaban ƙasa. “Ku yi wa Shugaban...
Ku kasance masu tausasawa da rahama, ku sadar da zumunta, ku sanya farin ciki azukatan al’umma kuma ku yada farin ciki, sannan ku nemi kusanci zuwa ga Ubangijinku ta hanyar ji da ɗa’a ga umarnin shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ranar idin Karamar Sallah rana ce da Musulmi ke farin cikin kammala azumin watan Ramadan wacce ke zuwa a ranar daya ga watan Shawwal din shekarar Musulunci. Allah Madaukakin Sarki ya shar’anta Sallar Idi a matsayin ibadar kammala Azumin Ramadan wacce take kan kowane Musulumi, baligi, mai hankali, kuma mazaunin gida — namiji ko mace. Zakatul Fidr: Yadda ake fitar da Zakkar Kono Zakkar Fidda Kai ta fi kayan sallah da abincin sallah A yayin da ake shirin shan shagalin Kamar Sallah, malamai sun bayyana muhimman abubuwan da ya kamata su aikata a ranar, kamar yadda Hadisan Annabi (SAW) suka nuna: Duk Musulumi maza da mata manya da kanana su halarci sallar Idi. Fitar da zakkar fid da kai, wato...
A birnin Roma masu goyon bayan al-ummar Falasdinu sun gudanar da zanga-zanga ta goyon bayan Falasdinawa, sun kuma ya allawadai da kungiyar tarayyar Turai da kuma Amurka kan yadda suka kasance manay-manyan masu taimakawa HKI a kissan kiyashin da take aikatawa a Gaza. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa daubban wadanda suka fito kan tituna a tsakiyar birnin Roma na kasar Italiya suna rera taken ‘Free Free Palastine, wato yanci yanci Falasdinusun kammala ba tare da wata matsala ba. Amma a jami’ar Colombia ta kasar Amurka rikicin rikicin jami’ar tare da masu goyon bayan kasar Falasdinu ya kaiga, shugabar jami’ar ta yi murabus daga matsayinta, don bada dama ga wani sabon shugaba, wanda zia aiwatar da...

Jakadan Kasar Rasha A Saliyu Ya Ce Kasar Rasha Tana Nazarin Yiyuwar Fara Hakar Ma’adinin bauxite A Kasar
Kamfanin hakar ma’adinai mai suna RUSAL na kasar Rasha ya aika da tawaga zuwa kasar Saloyo a yammacin Afirka don nazarin yiyuwar fara hakar ma’adinin bauxite a kasar nan gaba. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya nakalto jakadan kasar Rasah a Saliyo yana fadar haka. Labarin ya nakalto Mohammad Yongawo wani jami’in gwamnatin kasar ta Saliyo yana cewa kasarsa a shirye take ta kammala yarjeniya tsakanin kamfanin Rusal na kasar Rasha don fara aiki a yankunan da ske da ma’adinin bauxite. Ya kuma kara da cewa a halin yanzun bangarorin biyu suna cikin tattaunawa a tsakanionsu. Sannan yana fatan daga karshen gwamnatin kasar zata bawa kamfanin lisisin fara hakar ma’anin a kasar nan ba da dadewa ba. Kafin...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Nijeriya, kamar yadda kwamitin duban wata ya tabbatar. Baya ga Nijeriya, ƙasashen Saudiyya, Bangladesh, da Indiya suma sun ga watan a yau, Asabar 29 ga watan Ramadan, 1446. An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge Mijinki Sai dai wasu ƙasashe kamar Malaysia sun sanar da cewa za su yi Sallah ranar Litinin. Hakan na nufin cewa azumin watan Ramadan ya ƙare, kuma al’ummar Musulmi a Nijeriya za su gudanar da bikin ƙaramar sallah gobe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana. Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi. Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.
An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana. Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi. Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Nijeriya, kamar yadda kwamitin duban wata ya tabbatar. Baya ga Nijeriya, ƙasashen Saudiyya, Bangladesh, da Indiya suma sun ga watan a yau, Asabar 29 ga watan Ramadan, 1446. An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge Mijinki Sai dai wasu ƙasashe kamar Malaysia sun sanar da cewa za su yi Sallah ranar Litinin. Hakan na nufin cewa azumin watan Ramadan ya ƙare, kuma al’ummar Musulmi a Nijeriya za su gudanar da bikin ƙaramar sallah gobe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300. A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da yunwa da kuma samar da abinci ga al’umma. A cewar sa, karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara domin fara noman rani a karo na farko dan fadada harkar noma a kan Tudu. Alhaji Jamilu Danmalam yace an zabi kauyen Tunubu dake mazabar Kanwa domin fara noman Rani. Ya kara da cewar, wadanda suka anfana da tallafin za su ci moriyar kaso...
Kungiyar JIBWIS a Karamar Hukumar Giwa ta bukaci al’ummar Yakawada da su ci gaba da rungumar koyarwar Al-Qur’ani a rayuwarsu ta yau da kullum. Mataimakin Shugaban kungiyar, Malam Ibrahim Mustafa Shatiman Giwa, ya yi wannan kira ne yayin bikin rufe Tafsirin Ramadan na bana da aka gudanar a Masallacin JIBWIS da ke Yakawada. Malam Ibrahim Mustafa ya bayyana jin daɗinsa kan goyon baya da jajircewar al’ummar Yakawada a duk tsawon Tafsirin. Ya jaddada muhimmancin kiyaye darussan da aka koya a cikin Ramadan tare da amfani da su a rayuwa bayan karewar watan mai alfarma. A nasa jawabin, Sheikh Suleman Abdulkarim Fatika ya nuna godiyarsa ga dukkan mahalarta Tafsirin da suka daure suka halarta tun daga farkon watan Ramadan...
Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a cikin tekun farisa wanda aka sanyawa suna Shahid Baghiri mai kuma tsawon mita 180. Sannan Labarin ya kara da cewa gwamnatin shugaba Donal Trump na kasar Amurka ta bawa Iran razarar watanni biyu ta amince da zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ta yi shirin yaki da kasar ta Amurka. Dakarun...
Kungiyar bada agajin ta gaggauwa ta “white Helmets” na kungiyar Al’kaida, wacce kuma take samun tallafin gwamnatin Amurka ta hukumar USAID ta rasa tallafin da take don gudanar da ayyukanta. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana cewa, kasashen yamma musamman Amurka sun yi amfani da kungiyar ta Al-qaeda a lokacin yakin kasar Syriya a shekara ta 2011 zuwa 2017 don ingiza kasashen yamma kan gwamnatin kasar Siriya na cewa ta yi amfani da makaman guba a kan mutane, don cimmmai manufofinsu a kasar ta Siriya. A halin yanzu dai shugaban Trump zai dakatar da tallafin da ya ke bawa kungiyar mai yuwa saboda sun cimma manufarko a kasar Siriya ta kifar da gwamnatin Bashar a Al’asad. A...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.” Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam Khumaini ( r.a) da ya ayyana ranar Kudus a duniya a 1979, wacce ita ce juma’ar karshe ta watan Ramadan, a wancan lokacin manyan kasashen duniya masu takama da karfi suna kokarin ganin an mance da batun Falasdinu da kuma kasakantar da shi da cewa batu ne na Larabawa kadai. Limamin na Tehran ya kuma kara da cewa, abinda Imam Khumain ( r.a) ya yi...
A wannan Juma’a ce 28 ga watan Maris na shekarar 2025, aka gudanar da taruka da jerin wano na ranar Qudus ta duniya wadda ta zo daidai da ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma. An gudanar da wadannan taruka da jerin gwano ne a kasashe daban-daban da suka hada da wasu kasashen musulmi da na larabawa, har da wasu da wasu daga cikin kasashn ymmacin duniya da kuma na Afirka, ta hanyar shirya gagarumin gangamin da ke jaddada aniyarsu ta tabbatar da al’ummar Palastinu ta samu hakkokinta da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramta musu, tare da nuna cikakken goyon baya ga gwagwarmayarsu ta neman samun wadannan hakkoki nasu. A safiyar Juma’ar ne aka fara gudanar da jerin gwano...
Yau Juma’a, shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG Shen Haixiong, ya gana da ministar raya al’adu ta kasar Rasha Olga Lyubimova dake ziyara a kasar Sin. Shen Haixiong ya ce, yana maraba da Rasha ta shiga a dama da ita cikin bikin fina-finai na kasa da kasa da 0za a yi a kasar Sin a bana. A nata bangare, Olga Lyubimova ta ce, a shekarun baya bayan nan, Rasha da Sin suna kara musaya a fannoni daban-daban, ciki har da fina-finai, kuma sun samu kyawawan sakamako. Ta kara da cewa, tana fatan bangarorin biyu za su zurfafa hadin gwiwarsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
A cikin shekaru da ya yi a masana’antar, Karkuzu ya nuna ƙwarewa wajen kawo canji da kuma nishaɗantar da al’umma. A madadin gwamnatin Kano da al’ummar jihar, gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin, ‘yan Kannywood, da masana’antar. Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya jiƙan jarumin, Ya kuma Aljanna Firdausi ta zama makomarsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aikin na tura danyen Man, ya kai akalla tsawon kilo mita 180 wanda a tura shi, daga wajen hako shi da ke a yankin Neja Delta. danyen Man da Nijeriya ke hakowa, ya kai kasa da yawan wanda Hukumar OPEC ta iyakan ce, a watan Fabirairun 2025, wanda ya kai yawan Ganga 1,465,006 da ake hakowa a kullum. A yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da bincike, domin a gano musababbin abinda ya janyo fashewar man Bututun dan Man da irin asarar da aka tabka da kuma yawan adadin wadanda suka samu raunuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Marigayi Imam Khomeni ne ya ayyana ranar karshe ta kowane Radan a matsayin ranar Kudus ta duniya tun fiye da shekaru 40 da suka gabata, kuma ana ci gaba da gudanar tarukan wannan rana a kowace shekara a Iran da sauran sassa na duniya.
Wakilin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad a Tehran ya bayyana cewa: Ranar Qudus wata dama ce ta samar da hadin kai. A wannan rana al’ummar musulmi suna sabunta alkawarin da suka yi da Allah dangane da batun Palastinu. Ranar Kudus tana hada kai tare da karfafa gwagwarmayar Musulunci a yankin. Ya ci gaba da cewa, dukkanin bangarori na sun yi imanin cewa, hanya daya tilo ta kubutar da Kudus da kuma ‘yantar da kasar Falasdinu ita ce goyon bayan Kudus da kuma tinkarar mamaye yankunan Falastinu da hakan ya hada da wannan masallaci mai alfarma da yahudawan sahyuniya suke yi. Ranar Kudus ta duniya ita ce ranar da ke bayyana dukkan sharrin Amurka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma...
A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a. A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na bikin na shekara-shekara. A halin da ake ciki dai jama’a a birnin Tehran sun fara taruwa daga wurare daban-daban a kan titin juyin juya hali domin tunawa da wannan rana. A cewar wakilin...
Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da yamma. Ya kuma kara da cewa fitowar zanga-zangar ranar Kudus ta duniya alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, sannan cika alkawali ne ga al-ummar kasar Falasdinu kan cewa mutanen kasar Iran ba zasu taba barinsu su, su kadai ba. Ranar Qudus ta duniya dai, rana ce wacce Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya ware a ko wace ranar Jumma’a ta karshe...

Iran Ta Gudanar Da Faretin Jiragen Ruwa A Tekun Farisa Da Kuma Tekun Caspian Don Raya Ranar Kudud Ta Duniya
Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar da faretin jiragen ruwan yaki don raya ranar Kudus ta duniya kwana guda kafin ranar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dubban jiragen yaki da na masu sa kai a tekun Farisa da ke kudancin kasar da kuma tekun Caspian da ke arewacin kasar suna jerin gwano a cikin ruwayen yankunansu don raya wannan ranar. Dakarun IRGC sun gudanar da wannan atisai ne a jiya Alhamis, don nuna goyon bayansu ga Falasdinwa musamman a Gaza, wadanda a halin yanzu, sojojin HKI sun yi masau kawayya, sun hana shigowar abinda da abinsha cikin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Lokutan sallah su ne lokuta na farin ciki, godiya ga ni’imar Allah, da kuma ibada. A wannan lokaci, yana da muhimmanci a tabbatar da ayyukan da ake aikatawa sun kasance masu inganci da dacewa da koyarwar addini. NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Amma mene ne ya kamata musulmi su yi kafin da kuma ranar sallah? Ta wacce hanya za a tabbatar da zaman lafiya da tsari yayin bukukuwan sallah? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari kan muhimman abubuwan da Musulmi ya kamata su aikata kafin da kuma lokacin sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira hadin kan kasashen duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinu gabanin ranar Kudus ta Duniya. Kungiyar ta yi kira da a samar da hadin kai a kasashen duniya a ranar Juma’a da Asabar da Lahadi masu zuwa domin nuna goyon baya ga Gaza da Kudus, yayin da Isra’ila tare da goyon bayan Amurka ke ci gaba da yakin kisan kare dangi da suke yi wa Falasdinawa. A cikin sanarwar da ta fitar, Hamas ta yi kira da a gudanar da gagarumin jerin gwano na hadin gwiwa a dukkan birane da manyan birane na duniya. “Muna kira ga daukacin al’ummar Falasdinu, kasashen Larabawa da na Musulunci, da dukkan al’ummarmu masu son ‘yanci na...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga al’ummar kasar da su nuna hadin kai a yayin bukukuwan ranar Kudus ta duniya wato ranar JUma’ar kashe ta watan Ramadana da ke gabatowa, yana mai jaddada cewa hakan zai nuna matukar goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Falastinu. Pezeshkian, ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar ministocin kasar na farko sabuwar shekarar kalandar farisa, inda yake cewa “Ina fatan tare da halartar al’ummar kasar, za a gudanar da ranar Kudus mai daraja, kuma a wannan rana al’umma za su nuna hadin kai ga duniya.” Ranar Kudus ta duniya dai marigayi Imam Khumaini ne ya ayyana ta kuma ana gudanar da ita a kowace shekara a ranar Juma’ar...

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata a matsayin hutun sallaGwamnati Ta Ayyana 31 Ga Maris Da 1 Ga Afrilu A Matsayin Ranakun Hutu Don Bukin Eid-el-Fitr Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, a matsayin ranakun hu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mai Magana da yawun gwamnatin Iran malam Fatima Muhajirani ta yi ga al’ummar Iran da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin halartar jerin gwanon ranar Kudus ta duniya, wacce take fatan ganin ta taka rawa wajen taimakawa al’ummar Falasdinu. Muhajirani wacce ta yi bayanin haka a wata hira ta tashar talbijin ta kuma kara da cewa; Gwargwadon yadda al’umma za su fito wajen yin jerin gwanon saboda hadakar da ake da ita a tsakanin al’ummar Iran da Falasdinawa ta fuskokin addini da al’adu, da kuma tarayya akan manufofin juyi, tasirin haka zai fi fitowa. Malama Fatima Muhajirani ya kuma ambato maganar Imam Khumaini ( r.a) akan fatansa na ganin an sami fitowa mai yawa domin karfafa al’ummar Falasdinu. A na...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////.. Madallah, masu sauraro shirinmu na yau zai yi dubi dangane da “ranar Qudus ta Duniya’ wacce aka rayata a jiya Jumma’a ce 27 ga watan Ramdan shekara ta 1446 wanda yayi dai-dai da 28 ga watan Maris shekara ta 2025 miladiyya ne aka gudanra da ranar Qudus ta duniya, a nan kasar Iran da kuma...
Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a karamar hukumar Babura. Yace, an sami gudunmawar kudade da kayan abinci daga al’umma da kungiyoyi. Sheihk Hassan Musa ya kara jadadda bukatar cewar, ya zama wajibi a rika jibintar al’amuran marayu domin samun falala daga Allah. A jawabinsa, shugaban kwamitin tallafawa marayu, Malam Nura Sale ya ce wannan shine karo na goma Sha biyu na shirin. Ya godewa wadanda suka bayar...
Ya ce, “Da misalin karfe 7:28 na safe ne wasu da ke sharar masallacin suka ga mutumin a kwance a cikin masallacin, sai suka yi kokarin tayar da shi domin su yi shara amma shiru. Nan da nan, sai mutanen suka sanar da Musulman yankin lamarin, inda suka garzaya da shi zuwa asibiti, likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa. Musa ya ce, daga bisani aka mika gawar marigayin ga ‘yan uwansa domin yi masa jana’iza. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Fadar Gidan Gwamnatin Amurka (WhiteHouse), ta ce Rasha da Ukraine sun amincewa Jiragen jigilar kayayyakin kasuwanci gudanar da zirga-zirga cikin aminci a tekun Black Sea ba tare da kai musu hare-haren soji ba. Amurka ta fitar da wannan sanarwar ne bayan jami’an Amurka sun gana da wakilan kasashen biyu a Saudiyya a ranar Talata. Dole Ne A Tauna Tsakuwa Don Aya Ta Ji Tsoro Sin Na Ci Gaba Da Kasancewa Cibiyar Rarraba Hajojin Da Masana’antu Ke Sarrafawa Sai dai Rasha ta ce, dole ne a dage wasu takunkuman da aka sanya wa bankuna, kamfanonin inshora, da masu fitar da abinci, kafin yarjejeniyar tsagaita bude wutar ta fara aiki. Sai dai, Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da “kwarara...
Kasar Rasha ta bayyana a wannan Talata cewa tana nazarin sakamakon tattaunawar da ta yi da Amurka kan Ukraine a Saudiyya, Rasha ta ce ba wani bayyani da za’a fitar game da tattaunawar, kuma ba wani lokaci da aka a sanya na ranar da za a sake ganawa da Amurkawa ba. “An ba da sakamakon tattaunawar da aka yi a manyan biranen, Kuma “Ana nazarin su,” in ji mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov yayin jawabinsa na yau da kullun. Rahotanni sun ce ana tattaunawa tsakanin Amurka da Ukraine har zuwa yau Talata. Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a...
Sai dai duk da yaba wa Amurka bisa irin taimakon da ta bayar a baya, Byanyima ta nuna damuwa kan yadda aka dakatar da tallafin kwatsam ba tare da shiri ba. Wannan na iya haddasa koma baya a ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi na rage yawan masu kamuwa da cutar, musamman a yankunan da ke fama da talauci da ƙarancin kayan kiwon lafiya. Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa, idan ba a samu sabbin hanyoyin tallafi ba, yiwuwar ƙaruwar mace-mace sakamakon cutar HIV na da matuƙar girma. Hakan na iya rusa nasarorin da aka samu a yaƙin da duniya ke yi da cutar. Ana ci gaba da kira ga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin agaji da su ceto shirin...
Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi ta raba kayan abinci da kudi ga iyalan mambobinta da suka rasu a lokacin da suke kan aikin jarida, a matsayin kyautar azumin Ramadan. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar, ya ce suna gudanar da wannan shiri a duk shekara, tun bayan kaddamar da shi da tsohon shugaban kungiyar na jiha Alhaji Aliyu Jajirma ya yi, domin faranta ran iyalan abokan aikinsu da suka rasu. Kwamared Sarki Abubakar ya bayyana cewa dukkan shugabannin kungiyar da suka gabata sun tabbatar da ci gaba da gudanar da wannan shiri a duk lokacin azumin Ramadan domin rage wa iyalan mamatan radadin wahalhalun rayu. Ya sanar...
Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a ranar Litinin. Hukumomin Rasha sun ruwaito cewa fadar White House da Kremlin za su fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Talata kan tattaunawar da suka yi, wanda Moscow ta bayyana tun da farko a matsayin “mai wuyar gaske.” Tattaunawar yanzu tana mai da hankali kan yiwuwar tsagaita wuta a tekun Black Sea, domin ba da damar komawa kan yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsin da yake da muhimmanci ga samar da abinci a duniya. Ministan tsaron Ukraine Rustem Umerov ya bayyana ganawar da suka yi da Amurkawa a ranar Lahadi a matsayin...
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG ya gabatar da taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take gabatarwa ga duniya” a ran 20 ga watan nan da muke ciki a kasar Rasha. Kuma Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Jakadan Sin dake kasar Rasha, Zhang Hanhui da wakilan bangaren siyasa da ba da ilmi da yada labarai na kasar Rasha sun halarci taron don tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen biyu da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da musanyar al’adu da kuma hadin kan kafofin yada labarai da sauransu. Wakilai na Rasha sun hada da Andrey Denisov, mataimakin shugaba na farko na kwamiti...
Shirin ya fuskanci suka sosai a shafukan sada zumunta, inda suke ganin cewa, Arewa ta cancanci kulawa fiye da haka, yayin da wasu kuma ke ganin tallafin ya dace. A wani faifan bidiyo da Daily Trust ta gani, an ga wasu fusatattun matasa suna kwashe kayan abinci a wata babbar mota da aka ajiye a bakin titi. An ga matasan suna jefo kayan ga wadanda suke kasa domin tattarawa musu, sannan suka yi awon gaba da kayayyakin. Abubuwan da ke cikin Tirelar sun haɗa da shinkafa, sukari, man girki, gishiri da taliya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo a wasan da Portugal ta doke abokiyar karawarta ƙasar Denmark a daren ranar Lahadi, ƙwallon ita ce ta 929 da tsohon ɗan wasan na Manchester United ya jefa a tarihinsa na ƙwallon ƙafa, duk da cewar ya ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da Portugal ta tsallake rijiya da baya, hakan ya sa ta kai wasan dab da na kusa da na karshe a gasar ta Nations League. An tashi wasan ne da ci 3-3 jimilla bayan mintuna 90, amma Francisco Trincao ya sake zura kwallo a minti na 10 na ƙarin lokaci bayan da mai tsaron ragar Denmark Kasper Schmeichel ya ture wata ƙwallon da Goncalo Ramos ya buga....
Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar jirgin kasa. Da yake yiwa magoya bayansa jawabi, Rasool ya ce, Abin da ya faru yana a matsayin wulakanta ku ne ku al’ummar Afirka ta kudu, amma kuma idan kuka tsaya tsayin daka kan manufofinku na ‘yancin kai to za ku ci gaba da rayuwa a cikin mutunci da daukaka. Ya ce ba laifi muka yi ba, ammam kuma mun dawo gida ba tare da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƴansandan sun gayyaci Sanata Sunday Karimi domin bayani kan zarginsa na cewa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar Rasha ta KGB ta samu shiga cikin Majalisar Dokoki, wanda ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Zargin ya samo asali ne daga rahoton da Sanata Karimi ya raba akan ƙungiyar ta WhatsApp a Majalisar Dattijai a ranar 23 ga Fabrairu, 2025. Rahoton, wanda aka wallafa ta gidan jaridar The Reporters, ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin Majalisar, inda Sanata Natasha H. Akpoti-Uduaghan, wacce aka dakatar, ta shigar da buƙatar yin bincike ga Shugaban ‘Yansanda. Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha A cikin ƙarar da ta...
Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya. A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina. Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci Bayan rasuwar ce gwamnoni da wasu fitattun ’yan siyasa da a halin yanzu suna ƙasa mai tsarki suka kai wa Gwamna Radda ziyara domin jajanta masa dangane da wannan babban rashi. Daga cikin gwamnonin akwai Mohammed Umar Bago na Jihar Neja, da Farfesa Babagana Zulum na Jihar Borno da Gwamna Uba Sani na Kaduna, da Dauda Lawal...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hausawa sun yi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane su be kasuwa’. Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikinsu na ɗaya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so. Sai dai da zarar an ce watan Ramadana ya kama wasu daga cikin harkokin kasuwancin kan samu naƙasu, yayin da wasu kuma ke haɓaka. Wasu kuwa kasuwar ce ke sauya salo, inda take dakushewa a wasu sa’anni ta kuma haɓaka a wasu sa’anni. NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna Shirin Najeriya A Yau na wannan rana...

Za’a Gudanar Taron Tattaunawa Tsakanin Rasha Ta Amurka A Karo Na Biyu 2 A Birnin Rayad na Kasar Saudiya
A gobe Litinin 24 ga watan Maris ne tawagogin masu tattaunawa na kasashen Amurka da Rasha zasu hadu a birnin Rayida na kasar Saudiya don ci gaba da tattaunawan da suka fara a yan makonnin da suka gabata dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine, shekaru fiye da 3 da suka gabata, da kuma dangantaka a tsakanin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto Yury Ushakov mai bawa shugaba Putin shawara kan al-amurin siyasa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa Sanata Georgy Karasin ne zai jagoranci tawagar masu tattaunawa ta kasar Rasha sannan ta kasar Amurka an rika an samar da tawagar, wasu zata hadu da na Rasga a gobe litin a birnin...
Ya sanar cewa karamar hukumar ta kuduri aniyar daukar tsauraran matakai don dakile wannan barazana ta hanyar tura jami’an GOSTEC da Operation Hattara don inganta tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta. Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta...
Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. “ Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya aike da wasika zuwa Tehran domin fara tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran; yayin da shi da kansa ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a wa’adinsa na farko. A halin da ake ciki dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa...
Ana sa ran, za a yi jana’izarta yau Lahadi 23 ga watan Maris, 2025 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada da misalin 4 na yamma (4pm) a garin Radda, ƙaramar hukumar Charanchi da ke jihar Katsina. Hajiya Radda, jigo ce da za a rika tunawa da ita bisa hikima da juriya wanda hakan ya yi tasiri matuka ga iyalai da makusantanta. Allah ya jikan Hajiya Safara’u Umaru Barebari, ya albarkaci zuri’arta, ya sa ta huta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda rasuwa. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajia Safara’u Umar Radda, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Katsina. Cikin wani saƙo da tsohon mai magana da yawun gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Hajiya Safara’u ta riga mu gidan gaskiya bayan ta yi fama da doguwar jinya. Mabiya dandalan sada zumunta na ci gaba da bayyana alhini dangane da rasuwar Hajiya Safara’u.
Gwaje-gwajen da aka yi a ranar 17 ga Maris sun nuna cewa dan wasan tawagar farko Marc Casadó yana da rauni a gefen damansa, za a kara yin gwajin dan wasan don sanin girman raunin da kuma kwanakin da zai shafe ta na jinya, hakazalika Gwaje-gwaje a wannan rana kuma sun tabbatar da cewa dan wasan bayan kungiyar Iñigo Martinez yana da kumburi a gwiwarsa ta dama, za a yi wa dan wasan magani a Barcelona karkashin kulawar ma’aikatan lafiya na kungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...