2025-04-18@02:14:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 168

«ya lashe kyautar gwarzon»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Taron na farko na ministocin harkokin wajen G20 a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu ya kasance mai cike da tarihi, domin shi ne taron ministocin wajen kungiyar na farko a nahiyar Afirka, kamar yadda ministan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya bayyana, yayin da yake yabawa da taron, a wani taron manema labarai bayan kammala taron, inda har ila yau ya kara da cewa, taron “mai matukar fa’ida” ya yi gagarumar tattaunawa a kan dabarun da suka shafi yanayin shiyyoyin duniya da tasirinsu a kan gudanar da ayyukansu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)  
      Ya kuma bayyana kalubalen samar da ruwan sha da al’umma ke fuskanta, inda ya bayyana cewa suna da rijiyoyin burtsatse, amma ba sa aiki.
    Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa hukumomin tsaro na kara ɗaukar matakan daƙile matsalar a Kauru, Kachia da sauran yankunan da abin ya shafa. Wasu sassan Abuja za su kasance cikin duhu a ƙarshen mako – TCN Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi Ya gargaɗi duk masu bai wa ’yan ta’adda mafaka ko goyon baya da su daina, domin hukuma za ta ɗauki matakin ladabtar da su. Sanatan...
    Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta ce za ta dauki nauyin dalibai ‘yan asalin yankin su 80 da ke kwalejin Ilmi ta tarayya ta Jama’are a Jihar Bauchi, da kwalejin fasaha ta Dutse da kuma kwalejin fasahar sadarwa ta Kazaure. Shugaban Karamar Hukumar, Dr. Muhammed Uba Builder ya bayyana haka ga manema labarai a Birnin Kudu. Dr Muhammad Uba, yayi bayanin cewar, an zabo mutum uku-uku daga kowace mazaba goma sha daya dake yankin. Yana mai cewar, Karamar Hukumar ta yanke shawarar hakan ne domin bai wa dalibai damar karatu cikin sukuni. Dr Muhammad Uba Builder, ya kara da cewar nan gaba kadan Karamar Hukumar za ta kara zabo wasu daliban dan tafiya manyan jami’o’i dake kasar nan....
    Kungiyar wasan Kareti ta Iran ta zama ta daya a nahiyar Asiya, yayin da Iraki ta zo ta biyu sai kuma Tajikistan ta uku. An yi wannan gasar ne ta Asiya a garin Calus dake Arewacin Iran wanda ya sami halartar kasashe da dama. Daga cikin kasashen da su ka shiga gasar wasannnin da akwai Iraki, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman sai kuma Tajikistan. An bude wannan gasar ne dai daga ranar 19 ga watan nan na Febrairu, kuma za a rufe ta zuwa gobe 22 gare shi. Da akwai ‘yan wasa 120 na cikin gida da waje da su ka shiga cikin gasar, da ‘yan kallo 700 a cikin dakin wasa.
    Manyan jami’an MDD dake aiki a nahiyar Afirka sun yi gargadi a yayin taron gaggawa na kwamitin tsaro akan cewa hare-haren da ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rwanda suke kai wa a gabashin DRC, zai iya haddasa yakin da zai  hada kasashe da dama na yankin. ‘Yar sakon musamman ta MDD a DRC, Bintu Keita ta fadi cewa: “Ya zama wajibi ga kwamitin tsaron ya dauki matakan gaggawa domin hana barkewar yakin da zai hada kasashen yankin. Shi kuwa dan sakon musamman na MDD a yankin tekun Victoria Huang Xia cewa ya yi; “Yadda mayakan kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 ta kwace manyan garuruwan da suke a gabashin kasar ta DRC a cikin makwannin bayan nan yana nuni...
    Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
    Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba, Ogbugo Ukoha, Babban Darakta a sashen rarraba mai tare da adanawa na NMDPRA, ya ce matakin ya biyo bayan karuwar firgicin hadurran da ke tattare da manyan motocin dakon man.   “Kwamitin fasaha na masu ruwa da tsaki ya gana a yau don cimma wasu muhimman kudurori guda 10 da nufin rage karuwar yawan hadurran tankokin mai da ke janyo asarar rayuka,” in ji Ukoha.   An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki da suka hada da DSS, hukumar kashe gobara ta tarayya, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kungiyar masu sufurin mota ta kasa (NARTO), kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas...
    Kafofin yada labarai da manazarta na kasa da kasa, sun jinjinawa babban taron ‘yan kasuwan kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu da aka gudanar ranar Litinin, inda suka ce gwamnatin Sin na marawa wadannan kamfanonin baya wajen taka rawar gani a bangaren kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, kuma Sin ta gabatar da sako mai yakini na karawa wadannan kamfanoni kwarin gwiwar bunkasuwa. A wannan taro dai, ba nanata niyyar nacewa ga manufofi masu tushe da ake bi wajen raya kamfanoni masu zaman kansu a nan kasar Sin kadai aka yi ba, an kuma gabatar da alkiblar samun ingantattun ci gaba yadda ya kamata a wannan bangare. Hakan ya sa, “kwarin gwiwa” ta sake zama muhimmiyar kalma ga kasashen waje don...
    Ta ce: “Fafutukar sa, hikimar sa mai zurfi, da jajircewar sa wajen cigaban ƙasa sun sa shi ya zama murya mai matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya. Za a yi kewar shawarwarin sa masu amfani da kuma gudunmawar sa ba tare da son rai ba wajen gina ƙasa.”   Idris ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Cif Clark, da gwamnatin Jihar Delta, da ɗaukacin ’yan Nijeriya da suka amfana da irin rayuwar sa ta hidimar jama’a.   “Muna addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya uma ba iyalan sa da duk masu jimami haƙuri da juriya,” inji shi.
      Gwamnatin Tarayya tayi matukar alhinin rasuwar Dattijo kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da bakwai.   Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.   Ya ce, Marigayi Cif Clark gwarzo ne mai kishin kasa, mai fafutukar tabbatar da adalci da gaskiya, kuma ginshiki ne a ci gaban dimokuradiyyar Najeriya.   Mohammed Idris, ya kara da cewa, Marigayi ya sadaukar da kansa wajen bautawa kasa a fannoni da dama, musamman a matsayin shi na ɗan siyasa da mai kishin kasa, wanda ya bar gagarumar alama a harkokin mulki, hadin kai, da ci...
    An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Sanusi Tofa, ya fitar ranar Talata.   A nasa jawabin, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da romon dimokuradiyya da habaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jihar.   Ya kuma nuna jin dadinsa da goyon baya da hadin kai da mazauna Kano ke bai wa gwamnatinsa, ya kuma bukace su da su ci gaba da jajircewa kan manufofin gwamnatin.
    An kammala aikin gina wani jirgin ruwa sabon kira mai bambaro saman ruwa, da samarwa, da adanawa, da saukewa wato FPSO a takaice, wanda ke da na’urar rike iskar carbon da wurin adanawa, a Shanghai, a cewar Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin. Jirgin dai shi ne irinsa na farko a duniya kuma ana shirin isar da shi a karshen watan Fabrairu, a cewar jaridar. Jirgin na FPSO mai tsayin mita 333 da fadin mita 60, yana iya samar da danyen mai har ganga 120,000 a kowace rana. Kana yana iya aiki na musamman wajen rike iskar carbon dioxide da aka samar yayin kewayawa da ayyukan samar da mai. Bugu da kari, yana amfani da makamashin zafi daga iskar...
    Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu kai kan yadda za su kula da yaronsu idan sun koma gida. Ita kuwa Hasana Lawalli cewa ta yi har mai ciki ta kawo kuma ta haihu a wannan asibiti daga bisani aka sallame su suka koma gida. Ta ce yau kuma gashi ta kawo diyata ita ma a duba ta. Dahiru Magaji shi ne mai kula da wannan asibiti ta Magama Jibia ya yi...
    “Mutanen nan sun matsa mana iya matsi, suna kafa sabbin sansanoni, duk wanda ke yankin nan babu wanda bai san shi ba, kuma jami’an tsaronmu na iya bakin kokarinsu.” BBC ta tuntuɓi kakakin rundunar Fansar Yamma, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ta waya domin jin ko sun san da wannan sabon sansani, sai dai ba mu same shi ba, duk da an tura masa sakon kar-ta-kwana game da lamarin. A kwanan nan dai rahotanni daga jihar ta Zamfara na cewa ana ci gaba da samun gagarumar nasara wajen yaƙi da ‘yan bindiga, sai ga shi yanzu wasu al’umma na bayyana cewa sabbin mahara na sake dawowa.
    Ya ce kungiyar ta lura da yadda ake samun karuwar wasu cututtukan daji da aka yi watsi da su a Nijeriya kamar cutar Kansar colo-rectal, yara, obarian, da kuma ciwon daji na jini. Ya yi kira ga ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya, da ta mai da hankali sosai kan cutar daji da aka yi watsi da su a Nijeriya. Shugaban NCS ya kuma bukaci majalisar dokoki ta kasa da ta ware naira biliyan 25 don sauya tsarin kiwon lafiyar cutar Kansa zuwa asusun inshorar lafiya. Ya kara da cewa, NCS ta bukaci majalisar dokoki ta kasa da gwamnatin tarayya da su dace da karin kudade don rufe ba da tallafin naira biliyan 97.2 a cikin shirin nan na...
    Peters ya tsunduma cikin harkar mai da iskar gas a matsayin dan kasuwa a shekarar 1999 kuma ya fara gudanar da kasuwancinsa a fannin da ke samar da mai na karkashin ruwa, wato ‘Downstream Sector’. Duk da haka, Aiteo ya zama kamfani mafi girma da ke hako mai a Nijeriya cikin kankanin lokaci. A cikin 2015, Peters ya havaka darajar Aiteo tare da sayen (OML 29) Babban shingen bakin teku na Afirka Kudu da hamadar Sahara na Dala biliyan 3. A cikin shekara guda na sayen, Aiteo ya inganta yawan samar da mai daga ganga 17,000 na mai a kowace rana zuwa kusan bpd 70,000. A matsayinsa babban mai samar da makamashi na ‘yan asalin kasar, Aiteo yana havakawa gami...
    Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Yayin taron, ya ce, a ko da yaushe Sin tana kiyaye karfinta na nukiliya a matsayin mafi karancin mataki da ake bukata don tsaron kasa, kuma ba ta shiga gasar makamai da sauran kasashen duniya. Ya kuma ce, kudin da Sin ta kashe a fannin tsaron kasa a bayyane yake, kuma yana da ma’ana da kuma dacewa. Game da hadin gwiwar Sin da Rasha, Guo Jiakun ya ce, hadin gwiwar kasashen biyu bai shafi wani bangare na uku ba, kuma wani karin bangare ba zai yi tasiri kan hadin gwiwar ba. Bugu da kari, game da batun Amurka za ta kara...
    An yi nasarar watsa liyafar bikin fitilu na gargajiya na Sin na 2025 ta CMG jiya Laraba a mabambantan dandamali, lamarin da ya samu yabo sosai. Alkaluman masu kallo ta talabiji da sauran kafofi na zamani sun karu sosai fiye da bara. Kididdiga ta nuna cewa, an kalli liyafar da aka watsa kai tsaye ta kafofi daban daban sau miliyan 459, karuwar kaso 30 kan na bara. Kana an kalli liyafar ta talabijin har sau miliyan 189, karuwar kaso 12 idan aka kwatanta da bara. Baya ga haka, kallon liyafar kai tsaye ta kafofin zamani, ya kai sau miliyan 270, karuwar kaso 47 idan aka kwatanta da bara. A bangaren kasashen waje kuwa, kafar yada labarai ta CGTN wadda ke...
    Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba sai dai ta hanyar amincewa da tsarin zaman lafiya da zai kai ga samar da kasashe biyu na Falasdinawa dana yahudawan sahayoniyya. Hakan ya zo ne a yayin taron majalisar ministocin Saudiyya da yarima mai jiran gado kuma fira ministan kasar Mohammed bin Salman ya jagoranta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na...
    Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum, inda ya yi tsokaci game da rahoton dake da alaka da rarrabuwar iko tsakanin kasashen duniya na taron tsaro na Munich, yana cewa, bisa binciken da taron ya yi, kasa da kasa sun kara amincewa da kasancewar iko tsakanin kasashe daban daban a duniya. Kuma bangaren Sin ya yi imanin cewa, ba za a iya dakile wannan ci gaban da duniya ta samu ba. Da ya tabo batun sanya na’urar Buoy da Sin ta yi cikin ruwa don duba yanayin cikin tekun da batun ya shafa, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan ya dace da dokokin cikin gida...
    An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.” ’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida...
    Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga wayewar garin jiya Litinin ne, al’umma sun fito kan manyan hanyoyi kasa a jihohi kasar tamkar kwararan kogi don gudanar da murnar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, tare da tabbatar da aniyarsu ta yi riko da manufofin juyin juya halin na Musulunci da kuma sabunta mubaya’arsu ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.
    Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Akwai yiwuwar nan gaba kasar Ukraine ta iya zama wani bangare na tsarin tsaron kasar Rasha Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa: Dole ne kasar Ukraine ta tabbatar da tsaron kudaden Amurka da aka zuba a cikinta, saboda zata iya zama karkashin kasar Rasha wata rana. Trump ya kara da cewa a yayin zantawarsa da Tashar talabijin ta Fox News; Suna da kasa mai kimar gaske mai dauke da ma’adanai na musamman da man fetur da kuma iskar gas, da sauran abubuwa. Trump ya ci gaba da cewa: Yana son dukiyarsu ta kasance cikin aminci, domin suna kashe daruruwan biliyoyin dalolia cikin kasar. Ya karkare furucinsa da cewa; Za su...
    Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a gare shi) ya jagoranta, a cikin wadannan shekaru da dama, juyin juya halin Musulunci ya fuskanci makirce-makirce masu yawa da cikas, kuma ya samu gagarumar nasara, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne hambarar da gwamnatin sarki Shah da kasashen yammacin duniya suke goya masa baya, kamar yadda Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci ta yi nasarar kafa gwamnati da samar da ginshikanta da...
    Yanzu haka, an kara tura manyan injuna domin gudanar da aikin ceto a wurin da zaftarewar kasa ta auku a lardin Sichaun na kasar Sin. Da farko za su kwashe duwatsu da kasa da suka lullube wurin, kuma da zarar an ga alamun gini, za a sanar da ma’aikatan dake wurin domin kara bincike. Zuwa karfe 11:00 na safiyar yau agogon Beijing, an tabbatar da kasa ta binne gidaje 10 da wata masana’ata 1, sanadiyyar zaftarewar kasar, wadda ta auku a gundumar Junlian ta birnin Yibin na lardin Sichuan. Haka kuma, mutum 1 ya rasa ransa yayin da 28 suka bata. Zuwa yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da aikin ceto. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi. Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima! Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Idan aka dubi labarin Mariano Grinspun, ɗan shekara 23 daga González Catán, wani birni a lardin Buenos Aires na Argentina, wanda budurwarsa mai tsananin kishi ta caka masa wuka wanda ya yi sanadiyya mutuwarsa bayan ya gaisa da wata tsohuwar abokiyar karatunsa a titi, za a ga abin akwai ban mamaki. Abin ya faru ne...
      Mata a Karamar Hukumar Danja suna kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta gyara hanyar Tsangamawa a Babban Rafi saboda yawan rasuwar mata masu juna biyu da jariransu.   Sun yi wannan kira ne a yayin wani taron gaggawa da manyan jiga-jigan al’umma suka shirya domin tattauna matsalar da ta dade tana addabar jama’a – hanyar Tsangamawa.   Hanyar Tsangamawa da ke Babban Rafi, Karamar Hukumar Danja, Jihar Katsina, ta haddasa mutuwar mata masu juna biyu da jariransu, musamman a lokacin damina.   Duk da yawan koke da rokon gwamnati, har yanzu ba a dauki matakin gyara hanyar ba.   A wata hira da suka yi da Radio Nigeria, wasu daga cikin matan yankin sun bayyana cewa mata masu...
    Hukuma mai kula da samar da magungunan HIV/AIDS ko (UNAISD) ta MDD ta bada sanarwan cewa mai yuwa mutane kimani miliyon 6 ne zasu mutu a duk fadin duniya a cikin shekaru 4 masu zuwa saboda rashin samun tallafin Amurka a cikin shirin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayyana cewa, a ranarsa ta farko na kama aiki a matsayin shugaban kasan Amurka, ya dakatar da dukkan tallafin da Amurka take bayarwa a duniya na tsawon kwanaki 90. Labarin ya nakalto shugaban shirin samar da magunguna HIV/AIDS Christine Stegling tana cewa, duk tare da cewa Amurka ta ci gaba da tallafawa HIV/AIDS na wucin gadi, amma suna ganin cewa da wuya hakan ya ci gaba don tun...
    Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ’yan mata shida masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17 a yankin unguwar Pandogari da ke Ƙaramar hukumar Rafi ta Jihar Neja. Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, da tsakar daren Laraba ne ’yan bindigar suka kaiwa unguwarsu hari inda suka kashe wani ɗan banga mai suna Aliyu Aminu tare da yin garkuwa da ’yan matan. ’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace Mazauna yankin sun ce, maharan da suke da yawa sun shiga cikin unguwar ne daga yankin Birnin Gwari, ta Kwalejin fasaha ta Mamman Kontagora da ke Pandogari. Majiyoyi sun ce an kai ’yan matan da...
    Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da asuba. Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Yadda bom din Boko Haram ya kashe mutane a hanyar kasuwa a Adamawa Aƙalla masallata 10 da suka haɗa da Limamin ne aka ce an yi awan gaba da su a yayin harin. Jaridar Punch ta ruwaito DSP Ahmed Rufa’i, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a....
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na korar Falasdinawa daga zirin Gaza karkashin dabarar gudun hijira. Tajani ya bayyana cewa: Ba za a tilastawa Falasdinawan shiga kowane irin zabi ba, yayin da yake magana kan shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na neman kwace yankin Zaga. A cikin wani yanayi mai alaka da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya bayyana rashin amincewarsa da shawarar da...
    Ɗanbayan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake taka leda ba a sauran wasannin kakar nan saboda raunin da ya ji a guiwarsa, a ranar Lahadi. An fitar da ɗanwasan ne mai shekara 27, a karawar da United ta yi rashin nasara a gida a hannun baƙinta Crystal Palace, raunin da tun a lokacin kociyan ƙungiyar Ruben Amorim ya bayyana a matsayin babbar matsala. A ranar Alhamis ƙungiyar ta ce har yanzu ana duba yanayin raunin domin sanin yadda ya fi dacewa a yi masa magani da kuma tsawon lokacin da zai ɗauka yana jinya. Sanarwar ta ce kowa a ƙungiyar yana yi wa Lisandro Martinez fatan warkewa sarai, kuma za su ci gaba da tallafa masa a kodayaushe. Rashin...
    Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025.   A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan yankin da Jami’ar Bayero. Gwamnan ya yi kuma alkawarin samar da Asibitin sha-ka-tafi da samar musu da hanya da kai hasken wutar lantarki da rijiyoyin burtsatsai da bai wa iyalan mamatan jari da daukar dawainiyar karatun yaransu gwargwadon iko da kuma daukar nauyin jinyar wadanda suka ji rauni a yankin a yayin rusau da aka yi a makon da ya gabata.
    Gwamnatin kasar Argentina ta sanar da ficewarta daga hukumar lafiya ta duniya WHO. Mai magana da yawun shugaban kasar Manuel Adorni ya fadawa taron manema labarai cewa, shugaban kasar Javier Milei, ya umarci ministan harkokin wajen kasar Gerardo Werthein, da ya dauki matakin janye Argentina daga hukumar lafiya ta duniya. Adorni ya ce, ” ‘yan Argentina ba za su kyale wata kungiya ta kasa da kasa ta tsoma baki a harkokin da suka shafi ‘yancin kasarmu ba. “ Ya kara da cewa,”Ya kamata a fayyace cewa Argentina ba ta karbar kudade daga hukumar ta WHO don kula da lafiya, don haka, wannan matakin, kamar yadda wasu ke cewa, a kalla a shafukan sada zumunta, ba ya wakiltar asarar kudade ga kasar,...
    Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar Abuja Gobarar, wacce ta tashi da daddare a ranar Talata, ta kuma jikkata wasu almajirai bakwai, amma yanzu haka suna asibiti ana kula da su. Shugaba Tinubu ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Zamfara da iyalan waɗanda da suka rasa ’ya’yansu a wannan iftila’in, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata. Ya buƙaci makarantu...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya nada Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Marigayi Sayyid Hassan Nasrullahi tsohon babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ya yi shahada, a yakin baya-bayan nan kan kasar Lebanon, shi ne tsohon wakilin mai martaba Imam Khamenei a kasar Lebanon kafin shahadarsa.
    Kasar Afirka Ta Kudu ta ga yadda Palasdinawa suka jajirce wajen kare kansu daga HKI ne, ya sa ta gurfanar da HKI a gaban kutun ICC don kawo karshen kissan kiyashin da yahudawan suke masu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kasar Afirka ta gudu dai tana dade tana goyon bayan masu gwagwarmayan neman yencinsu a duniya daga ciki da da kasar Falasdinu da aka mamaye. Har ila yau da kuma ganin tarihin da kasar take da shi, na yaki da wariyar launin fata a kasar, duk sun hadu sun karfafa ta wajen daukar wannan matakin kan HKI. Jakadan kasar Afirka ta kudu a nan Tehran, Francis Moloi ne ya fadawa kamfanin dillancin labaran ‘Iran...
    Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima. Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban. Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma...
    Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a ranar Talatar nan, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Za a kashe Naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da cutar HIV a Nijeriya — Ministan Lafiya Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 “Dole ne mu yi wa waɗanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan...
    Majalisar Zartarwa ta ware naira biliyan 4.8 domin yaƙi da yaɗuwar cutar HIV a Nijeriya. Wannan na daga cikin matsayar da aka cimma a taron Majalisar Zartarwa da ya gudana a ranar Litinin kamar yadda Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya tabbatar. Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 Dalilin da Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Adamawa Ministan ya ce wannan yana daga cikin manufofin gwamnatin na inganta kiwon lafiya a matakin farko. A cewarsa, an tsara kashe kuɗaɗen ne a fannin ɗaukar ma’aikatan lafiya da ba su horo domin samun ƙwarewa da kuma tabbatar da an bayar da kulawar da ta dace domin hana yaɗuwar cutar HIV a sassan ƙasar....
    An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara.  Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar aiki ta musamman da aka kafa don saukake ayyukan da suka shafi zirga-zirgar bikin bazara, wanda aka fi sani da chunyun. Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Kuje Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Athletico Madrid Da Getafe Zirga-zirgar fasinjoji ya karu tun daga ranar 30 ga watan Janairu, inda adadin tafiye-tafiyen ya zarce miliyan 300 a...
    Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin ta fitar, ya zuwa karfe 6:30 na yammacin ranar 3 ga watan Febrairun 2025, agogon Beijing, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finai wato box office na sabuwar shekarar bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ya kai yuan biliyan 8.257, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.14, wanda ya kafa sabon tarihi. Ya zuwa yanzu dai, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finan kasar Sin a 2025 yana kan gaba a kasuwar fina-finan duniya da jimillar yuan biliyan 10.121, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.4 (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
    Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren  wurin shan shayi da taliya na zamani  a karamar hukumar Maigatari ta jihar. Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari.   Ta kara da cewa, an tsara wannan wurin na zamani ne domin samar da yanayi mai kyau da inganci ga mutane, inda za su ci abinci cikin gamsuwa, tare da bunkasa kasuwanci a yankin. Hajiya Hadiza ta kuma kaddamar wani tallafi ga mata 300 a karamar hukumar Maigatari.   An bayar da naira dubu talatin kowannensu, domin bunkasa kananan sana’o’i. Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa,...
    Mutum biyu sun rasu sakamakon bullar cutar zazzabin Lassa a Jihar Filato. Kwamishinan Lafiya na Jihar Filato, Dakta Cletus Shurkuk, ya sanar cewa mutum na uku da ya kamu da cutar yana samun kulawa a asibiti. Ya bayyana cewa mamatan sun kamu da cutar ne a Karamar Hukumar Kanam, na ukun da ke raye kuma a Karamar Hukumar Shendam. Daya daga cikin majinyatan ya rasu ne a Shendam na biyun kuma a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin Kano Kwamishinan ya bayyana cewa gwamanatin jihar tana aiki tare da Cibiyar Yaki da Yaduwar Cututtuka...
    Kasashen 3 na yankin sahel sun kafa ta su kungiyar mai suna “Kawancen Sahel” (AES). Yadda ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ecowas ka iya raunata kungiyar Ficewar kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso daga kungiyar Ecowas a ranar Laraban nan bayan kwashen fiye da shekara guda ana zaman tankiya tsakanin kungiyar da kasashen guda uku, wani abu da ke nuni da rashin tabbas ga cigaba da kasancewar kungiyar ta Ecowas. A ranar ta 29 ga watan Janairun 2024 ne kasashen guda uku da shugabannin mulkin soji ke jagoranta suka sanar da kungiyar Ecowas a hukumance dangane da bukatar ficewar tasu. To sai dai bisa dokokin Ecowas, kasashen na bukatar sanar da kungiyar shekara guda kafin amincewa...
    Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909.   Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14.   Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001).   Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56.   Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949).   Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960).   Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021).   Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
    Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance a matsayi na daya na wucin gadi a kasuwar fina-finan duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
    ‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad. Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a. A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu. Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da  duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako zuwa wurin rufe ‘gasar karatun akur’ani mai girma karo na 41 da aka yi a birnin Mashhad, ya bayyana cewa; Alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da musulmi a matsayin al’umma daya dunkulalliya, yake kuma yin kira a gare su da su yi riko da igiyar Allah da hadinkai, domin hana rabuwar kawuna. Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Shakka babu, wani sashe...
    Alkaluma daga ma’aikatar kudi ta kasar Sin sun nuna cewa, kudin shigar kamfanoni mallakin gwamnatin Sin ya karu da kaso 1.3 a shekarar 2024. A cewar ma’aikatar, kamfanonin sun samu karuwar yuan triliyan 84.72, kwatankwacin dala triliyan 11.7 na kudin shiga a 2024. Jimilar ribar da suka samu a shekarar 2024 kuma, ta karu da kaso 0.4 zuwa triliyan 4.35 a kan na shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Masu haƙar zinare aƙalla mutum 10 sun mutu wasu da dama sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a kansu a wani filin haƙar ma’adinai yankin Koulikokro na ƙasar Mali. Hukumomin yankin sun bayyana cewa mata ne yawancin masu haƙar zinaren da abin ya rutsa da su mata ne, kuma an kasa ciro gawarwakinau, “saboda tsananin sarƙaƙiyar yanayin.” Gwamnatin yankin ya bayyana cewa ajali ya rutsa da su ne a ƙauyen Danga, a cikin wani rami mai ruwa da laka, wanda zaftarewar ƙasar ta binne su a ciki a ranar Laraba. Ta bayyana a shafinta na Facebook cewa “abin takaicin shi ne babu ko mutum ɗaya da ya tsira a cikin su.” Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya...
    Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin ya gagara. Sau hudu gwamnonin jihar daban-daban suna sa wa’adin kammalawa da kaddamar da wannan katafaren asibiti, ba tare da haka ba ta cimma uwa ba. A shekarar 2007 tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Namadi Sambo tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci na Duniya suka assasa aikin ginin asibitin da wa’adin kammala shi a cikin shekara biyar, wato 2012. An yi fatan zai kasance...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci da kasar Kazakhstan a wata ganawa da firaministan kasar Kazakhstan Olzhas Bektenov. A yayin taron na ranar Alhamis, Aref ya bayyana bukatar samar da karin kwamitocin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Bayan goron gayyata day a samu a hukumance daga Bektenov, mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya isa kasar Kazakhstan a ranar Alhamis domin halartar taron koli na shugabannin gwamnatoci mambobi a kungiyar tattalin arzikin Eurasia (EAEU) da taron Almaty Digital Summit 2025, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 1 ga Fabrairu. Iran wadda a baya-bayan nan ta samu matsayin mamba mai sanya ido a...
    Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
    Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza.  Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...
    Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata na bai daya ga duniya. Shi ma a jiyan, shugaban Zambia Hakainde Hichilema, ya aikewa shugaban kasar Sin Xi Jinping gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar, yana mai fatan samun ci gaban kasashen da al’ummominsu. Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10 Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje A ranar Talata kuma, shugaban Angola...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama wani saurayi da budurwarsa bisa zargin yin aure a wajen wani taro ba tare da amincewar iyayensu ba. A cewar Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, matasan sun yi auren ne a wajen shaƙatawa bayan wani da ba su da alaƙa da shi ya biya sadakin amaryar. Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Kungiyar NLC ta kira zanga-zanga kan ƙarin kuɗin waya Ya bayyana cewa yin hakan ya saɓa wa ƙa’idar Musulunci kuma ba za a yarda da irin wannan lamarin ya ci gaba da faruwa a Kano ba. “Muna sanar da cewa mun kama ma’auratan, kuma za mu ci gaba da bincike don kama abokansu da duk wanda...
    Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
    Duk da ficewarsu daga ECOWAS, ƙasashen AES sun yanke shawarar cewa ‘yan ƙasashen ECOWAS za su iya shiga ƙasashensu, domin ƙarfafa dangantakar hada-hadar kasuwanci a tsakanin yankin. Wannan ficewa na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Sahel ke fama da matsalolin tsaro, wanda ya haifar da juyin mulki a ƙasashen uku. Yanzu haka, suna fatan sabuwar ƙungiyarsu ta AES za ta taimaka wajen magance waɗannan matsaloli da inganta tsaro a yankin.
    Kungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta tabbatar da ficewar ƙasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar a hukumance. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ECOWAS ɗin ta fitar, tana mai cewa har yanzu ƙofa a buɗe take ga waɗannan ƙasashe, a duk lokacin da suka sauya shawarar sake komawa. Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Kiristoci sun yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya a Kudancin Kaduna A cikin sanarwar, ECOWAS ta ce za a ci gaba da mutunta fasfon jama’ar waɗannan ƙasashen uku da ke ɗauke da tambarin ECOWAS, haɗi da katinsu na shaidar ɗan kasa. Kazalika, ƙungiyar ta ce za a ci gaba da kallon waɗannan ƙasashe tamkar mambobinta,...
    Ƙungiyar Shugabannin Kiristoci na Kudancin Kaduna (SKCLA) ta yi kira ga al’ummar yankin da su rungumi haɗin kai da ƙaunar juna a matsayin tubalin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba. Shugaban ƙungiyar SKCLA, Fasto Emmanuel Nuhu Kure ne ya yi wannan kiran ga mazauna yankin a wajen taron addu’ar shekara-shekara da ake gudanarwa a garin Kafanchan don kyautata alaƙarsu da Ubangiji tare neman ɗauki daga gare Shi don samun zaman lafiya da wadata. DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata An kama gungun masu yi wa Boko Haram da ’yan bindiga safarar babura “Lokaci ya yi da za mu haɗa kai da tunanin mu waje ɗaya da manufa ɗaya don sake gina al’ummomin Kudancin...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a fagen kasa da kasa, yana mai cewa; Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta zame a matsayin kungiyar ta’addanci ta masu aikata laifuka da kisa kiyashi a idon duniya. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Qasem ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar a yammacin jiya Litinin game da sabbin abubuwan da ke faruwa a kasar Lebanon da kuma yankin, inda ya ce: “Hare-haren wuce...
    Shettima ya yi alkawarin cewa, bisa umarnin shugaban kasa, gwamnati za ta hada hannu da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kan hanyoyin da hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa, da ma’aikatun sufuri na tarayya da na Jihohi za su hada kai don dakile yawaitar hadurran tankar mai a fadin kasar.
    Ana fargabar cewa wani mutum mai shekaru 30, Rabiu Sani, ya mutu a wani kududdufi da ke unguwar Kunture a Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun rundunar hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin. ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet Ya bayyana cewa ofishin karɓar koken gaggawa ne ya samu kira daga wani Silas Munkhaila dangane da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu sun isa kududdufin inda suka tsamo gawar mutumin wanda ya je ɗebo wa mahaifinsa ruwa. Ya ƙara da cewa sun miƙa gawar mamacin a hannun mai unguwar Kunture, Uba Abdulkadir. Kazalika,...
    Harkar Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa Da Tawagar Sin A MDD Ta Shirya Ta Nuna Al’adun Gargajiya
      Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta samar da matakan dakile yawaitar kauran likitocin daga jihar zuwa wasu kasashe, domin neman ingantacciyar rayuwa.   Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dakta Amina El-Imam ta bayyana haka, a lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin kungiyar likitoci ta kasa, a Ilorin.   A cewarta gwamnatin ta amince da biyan Asusun Horar da Likita masu neman kwarewa da sauran abubuwan karawa likitoci gwarin gwiwa.   Dokta El-Imam ta bayyana cewa gwamnatin jihar tana bakin kokarinta wajen ganin dukkan ma’aikatan jinya sun yi fice a aikin da suka zaba, domin dakile yawan barin kasan nan da likitoci ke yi zuwa kasashen waje.   Kwamishinan, ya yi kira ga kungiyar da ta ziyarce ta, da ta fahimci...