2025-02-22@06:39:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 27
«yara masu nakasa»:
Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari. Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi online – Kula da shafukan da suke ziyarta da kuma mutanen da suke magana da su. Amfani da ‘Parental Control’ – A saita wayoyin yara domin hana shiga shafuka masu illa. Ilimantar da yara kan sirri – A koya musu kada su bada bayanan sirrinsu kamar lambar waya, adireshi, ko hotuna. Kafa iyaka kan amfani da intanet – Iyaye su saka ka’ida kan lokacin da...
Ƙungiyar Masu Nakasa ta ƙasa reshen Jihar Gombe (JONAPWD), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Masu Nakasa ta Jihar, Dokta Isiyaku Adamu. Ƙungiyar ta shirya taro na musamman tare da iyayen yara da suke fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali. NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah Wannan taron na musamman, wanda aka gudanar a ofishin JONAPWD da ke Gombe, ya zama wata muhimmiyar dama don tattauna matsaloli, musayar ƙwarewa da kuma ƙarfafa fafutuka don kare haƙƙoƙin yara masu fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali. A...
Ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa a bangarori da dama da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare yara, da al’umma. Shugaban ofishin , Mista Rahama Rihood Farah ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jiharJigawa. Ya kara da cewa, hadin gwiwar da UNICEF ya yi da gwamnatin jihar Jigawa ya samu nasarori da dama, kamar karfafa tsarin tantance yaran da suke cikin kangin talauci, ta hanyar binciken da aka gudanar a kwanan baya (GHS), da samar da muhimman tsare-tsare da tsare-tsare, da kuma sanya masu ruwa da tsaki a tsarin....
Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, kwamfutar da kasar Sin ta kera da kanta ta zamani na uku mai sarrafa bayanai tare da warware matsaloli cikin matukar sauri ko kwamfutar quantum a takaice, wato Origin Wukong, ta samu masu amfani da ita sama da miliyan 20 daga sassan duniya baki daya, wanda ya kasance wani muhimmin ci gaba a fannin bunkasa ayyukan da suka shafi kwamfutar quantum. A cewar cibiyar nazarin injiniyan kwamfutar quantum ta Anhui, masu amfani daga kasashe ko yankuna 139 sun samu damar shiga Origin Wukong, tare da Amurka, Rasha, Japan da Kanada a matsayin mafi yawan yin amfani da ita. A cikin wadannan kasashe, Amurka ce ke kan gaba a...
Tawaga ta farko ta ‘yan kasuwan Sin mai kai ziyara ketare da kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje ya kafa a sabon shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da muke ciki, ta kai ziyara Kazakhstan, don gaggauta mu’amala tsakanin kamfanonin kasashen biyu da kulla yarjejeniyar hadin gwiwa. Kuma, kamfanonin kasashen biyu sun samu sabon ci gaba a bangaren makamashin gas da man fetur. Tawagar ta yi tattaunawa mai zurfi da asusun kasar Kazakhstan na Samruk Kayzana da kungiyar ‘yan kasuwar kasar ta Atamekeh a Astana hedkwatar kasar Kazakhstan, tare da gudanar da taron tattaunawa kan tattalin arziki da ciniki tsakanin ‘yan kasuwar kasashen biyu da kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa 8, wadanda ke shafar bangaren makamashin...
Jakadan Iran a Lebanon ya bayyana cewa: Suna maraba da matakin jigilar jiragen saman Lebanon zuwa Iran da sharadin rashin soke jigilar jiragen Iran zuwa Lebanon Jakadan kasar Iran a kasar Lebanon Mujtaba Amani ya bayyana cewa: Bangaren Iran yana maraba da samar da jigilar jiragen saman kamfanonin jiragen saman kasar Lebanon zuwa kasar Iran, ba tare da batun soke jigilar jiragen saman Iran zuwa kasar Lebanon ba. Gidan talabijin din kasar Iran a yau Juma’a ya sanar da cewa: An yi watsi da furucin wasu kamfanonin jiragen sama guda biyu da suka ce, gwamnatin Lebanon ta hana tafiyar jiragen saman Iran guda biyu zuwa kasar Lebanon da suke tashi a ranakun Alhamis da Juma’a, don haka ofishin jakadancin Iran...
Dokokin Gyaran Haraji sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi a tsakanin ’yan majalisar. Tun da farko, an gabatar da ƙudirorin guda huɗu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar, amma an haɗe su zuwa guda ɗaya domin sauƙaƙa nazari a kansu. An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC Jagoran majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne, ya jagoranci tattaunawar, inda ya jaddada buƙatar sauta tsarin harajin Najeriya. Ya ce dokokin za su sauƙaƙa biyan haraji, cire harajin kayayyakin buƙatu na yau da kullum kamar abinci da kiwon lafiya, tare da samar da rangwame ga ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi. Yawancin ’yan majalisar...
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar na nuna da cewa, Kano tana da kimanin yara 837,479 da ba sa zuwa makaranta, adadi mai ban mamaki da jihar ke kokarin magancewa. Tawagar tantancewar, karkashin jagorancin jami’a mai kula da ilimin yara mata ta jihar, Hajiya Amina Kassim, ta ziyarci kauyuka da dama, inda ta tattauna da iyaye, da shugabannin gargajiya, da malaman addini. “Tawagar ta gano muhimman abubuwan da...
An yi wa dubban mutane gwajin lafiya kyauta a Indonesiya don kauce wa mutuwa da wuri. Za a yi gwajin ga ɗaukacin ‘ƴan kasar ne a ranar murnar bikin haihuwarsu, domin cika alkawarin da shugaba Prabowo Subianto ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe. Jarirai da ƙananan yara da kuma tsofaffi na cikin waɗanda za a fara yi wa gwajin. A watan da ya gabata, gwamnatin mista Prabowo ta fara bai wa miliyoyin yara ƴan makaranta da kuma mata masu ciki abinci kyauta domin rage rashin abinci mai gina jiki da ke shafar yaro ɗaya cikin biyar a Indonesia.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sha alwashin gyara wa da faɗaɗa sansanin horas da matasan maus yi wa ƙsa hidima (NYSC) na dindindin a jihar. Da yake karɓar babban Daraktan NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed a Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta gaggauta gina sansanin dindindin domin karɓar ƙarin ‘yan bautar ƙasa. Ya kuma yaba da gudunmawar da likitoci da malaman kimiyya ke bayarwa a makarantu. Sin Ta Yi Bikin Tunawa Da Wadanda Aka Hallaka Yayin Kisan Kiyashin Birnin Nanjing Tinubu Ya Amince Da Naira Biliyan 80 Domin Sake Gina Madatsar Ruwa Ta Alau Da Ke Borno Shugaban NYSC ya gode wa gwamnatin Borno bisa tallafin da take bai wa ‘yan bautar ƙasa, ciki har da alawus na...
Kwamishiniyar Mata, Yara da Nakasassu ta Jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi, ta gargadi ma’aikatan Cibiyar Reformatory Institute ta Kiru da su guji karkatar da kayayyakin da aka ware domin gina cibiyar. A yayin ziyarar duba aikin gyare-gyaren, kwamishina Amina ta jaddada muhimmancin yin amfani da kudaden da aka ware wajen abubuwa masu inganci a wannan cibiyar. Cibiyar da aka sabunta za ta ƙunshi abubuwan more rayuwa na zamani, waɗanda suka haɗa da dakunan kwanan dalibai, asibiti, wurin shakatawa, wuraren aikin kafinta da walda, ɗakin cin abinci. Kwamishina Amina ta yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa na inganta rayuwar al’ummar jihar Kano. Ana sa ran kammala aikin gyaran nan ba da jimawa ba, daga nan...
Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu varna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya. “Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu. “Haka zalika za a bukaci masu gudanar...
Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu barna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya. “Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu. “Haka zalika za a bukaci masu gudanar...
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra. Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki. Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a bude ba yadda suka saba ba, kasancewar yaran suka kulle gidan a duk lokacin da za su je wasa. Da shigarma’auratan cikin gidan ne kuma suka ga gawarwakin yaran an sanya a cikin firinjin kayan kankara. Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe...
Wasu ma’aurata sun tsinci gawarwakin kananan ’ya’yansu uku a boye a cikin wani firinji a yankin Nnewichi da ke Nnewi a Jihar Anambra. Iyayen yaran, Mista Udochukwu da Misis Chikazor Ejezie, sun tsinci gawar ’ya’yan nasu a cikin firinji ne bayan da suka dawo gida daga wurin aiki. Bayan dawowarsu ne suka samu gidan a bude ba yadda suka saba ba, kasancewar yaran suka kulle gidan a duk lokacin da za su je wasa. Da shigarma’auratan cikin gidan ne kuma suka ga gawarwakin yaran an sanya a cikin firinjin kayan kankara. Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata Kotu ta ɗaure Farfesa shekara 3 kan aikata maguɗin zaɓe...
Hukumar Kula da Magunguna ta Najeriya (PCN) ofishin Kano ta kai ziyarar gani da ido ga hukumar samar da magunguna ta jihar Kano (DMCSA). Wannan ziyarar alama ce ta farkon tsarin ba da izini ga DMCSA don zama cibiyar rarraba magunguna ta mega da cibiyar bada horo. Jami’ar Jihar Kano mai kula da ofishin PCN Kano Pharmacist Hasiya Abubakar Ladan ce ta jagoranci tawagar da suka kai ziyarar. Wannan ziyarar wani mafari ne na tantancewa da wata tawagar kwararru daga hedikwatar PCN ta kasa da ke Abuja. Ta bayyana cewa ziyarar na da nufin tantance yadda DMCSA ke bin ka’idoji, don ba da Takaddar Rijistar wuraren sayarda magunguna. Pharmacist Ladan ta yabawa shugabannin DMCSA bisa...
Gwamnatin jihar Neja ta karbi yara ashirin da daya da aka kama a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar yayin da ake safarar su zuwa Sudan. Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Yakubu Garba wanda ya bayyana haka a lokacin da yake karbar yaran a madadin gwamnatin jihar Neja a Minna, ya ce an kama yaran ne a cikin kasashen Kamaru da Mali da Jamhuriyar Nijar da kuma Sudan. Kwamared Yakubu Garba ya bayyana cewa yaran da aka ceto ‘yan karamar hukumar Magama ne a jihar Neja, amma ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da kuma hukumar fataucin bil’adama bisa nasarar ceto yaran. Ya ci gaba da cewa ta’addancin ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargaɗi al’umma kan wata alawar yara mai da sanya maye, da ke yawo a gari. Hukumar ta gargaɗi, musamman iyaye da su yi hattara da alawar da sauran kayan tanɗe-tanɗe da ke ɗauke da sinadarai masu sanya maye. Kakakin Hukumar a jihar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya kuma yi kira ga iyaye da suka riƙa lura da irin kayan tanɗe-tanɗe da ’ya’yansu ke saya. Ya bayyana cewa alawar tana kama da cakulet, amma a cikinta an sanya abin da ke bugarwa, kuma yawanci an fi sayarwa a makarantu. NHIS: Kotu ta tsare Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA...
Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan Nijeriyar da suka kasa daukaka kasar. Ahanotu ya kara da cewa, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su bai wa matasa damar gyara matsalolin da suka faru a baya. Ya ce, “Gaskiya ni ba masoyin Buhari ba ne kuma ban taba tsammanin zai yi abin kirki ba. Don haka ban yi mamakin cewa bai yi komai tsawon shekaru takwas ba. Amma abin da nake...
Ana zargin wani ɗan ƙabilar Ibo mai suna Oguchwku da yin lalata yaran makarantar Firamare masu shekaru 9 da 10 da haihuwa, kuma ‘ya’yan Hausawa ne. Aminiya ta bibiyi lamarin a inda ta garzaya Cibiyar Kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Ƙofar Gayan Zariya a Jihar Kaduna. Shekara 18 aikin Asibitin Sabuwar Kaduna na tafiyar hawainiya Tankar fetur ta yi bindiga a gidan mai Jigawa Daraktan cibiyar Salama Centre da ke Asibitin Gambo Sawaba ƙofar Gayan Zariya, Hajiya Aishatu Ahmad, ta shaida wa Wakilin namu cewar a ranar 27 ga watan ɗaya na wannan shekarar ne hukumar ‘yan sanda da ke Kasuwar Mata a ƙaramar hukumar Sabon Gari ta kawo wani mai suna...
Hukumar Kula da Hanyoyi da Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA), ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran wasu motocin aiki guda biyar. Haka kuma, hukumar ta kashe Naira miliyan 250 domin sayen sabbin motoci domin amfanin da su. Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a Sweden Kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kuɗi na Jihar, Musa Sulaiman Shanono ne, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka amince da shi. Ya bayyana cewa ingantaccen tsarin sufuri yana da matuƙar muhimmanci ga bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaban al’umma. Ya kuma ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin inganta kayan sufuri domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki a...
Bugu da ƙari, dokar za ta bai wa direbobin da ke jigilar fasinjoji damar kula da yanayin fasinjojin da za su ɗauka ta yadda in sun ga yara dole sai sun tantance wanene ya ɗaukosu kuma meye nasabarsu dukka da nufin daƙile satar yara da safararsu. Sannan gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokar da ta bai wa kamfanonin sadarwa (Telecom Service Providers) dama ta yadda ba za a cajesu ko kwabo ba, da nufin inganta lamarin yanar gizo da inganta kamfanonin sadarwa domin jama’a suke morar amfani da tauraruwar ɗan adam da nufin sauƙaƙa harkokin kasuwanci a jihar. Gwamnan ya yi gargaɗin cewa duk wani direban da ya ƙi bin umarnin da aka sanya na sanya ido...
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta 2025. Ya kara da cewa alkaluma sun nuna cewa ‘yan mata miliyan 7 da 600 ba sa zuwa makaranta, inda shiyyar Arewa maso Yamma da arewa maso gabas ke da kashi 48 cikin 100 na adadin. Ya danganta wannan kididdigar da abubuwan da suka hada da talauci da ka’idojin zamantakewa da nuna wariyar jinsi, wadanda ke dakile bai wa ‘ya’ya mata damar...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan yara miliyan 5.4 ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, inda aka yi hasashen za a samu Karin masu wannan matsala su miliyan daya nan da watan Afrilun 2025. Wakiliyar UNICEF a Najeriya Ms Cristian Munduate ta bayyana hakan a wani taron manema labarai kan rikicin da ya addabi miliyoyin yara a jihar Zamfara da kuma fadin Najeriya da aka gudanar a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ms Munduate wadda ta yi tsokaci kan halin da kananan yara ke ciki a Zamfara, ta ce jihar na da yara miliyan...
Majalisar dokokin jihar Jigawa ta jaddada aniyar ta na hada kai da ofishin kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF domin samun nasarar aiwatar da tsare-tsare da za su inganta rayuwar yara da marasa galihu a jihar. Mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Sani Isyaku Abubakar, ya bada wannan tabbacin lokacin da ya karbi bakuncin tawagar ofishin UNICEF na Kano karkashin jagorancin Hajiya Fatima Adamu. Ya lura cewa irin wannan haɗin gwiwa tsakanin majalisa, Action Against Hunger da Save the Children International sun haifar da sakamako mai kyau ta hanyar tallafawa matakan majalisa ta hanyar fasaha da ba da shawara don tsara manufofin da sauran tsare-tsaren a Jigawa. Alhaji Sani Isyaku Abubakar ya bada tabbacin ci gaba...