2025-03-24@13:26:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 432
«zuwa Naira biliyan»:
Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a sassa daban-daban na kasar Lebanon, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a kasar a baya-bayan nan. Baghaei ya alakanta hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan kasashen Labanon da Siriya da yunkurin kisan kiyashi da Tel-Aviv ta yi a baya-bayan nan a Gaza da kuma gabar yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye,...
Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar jirgin kasa. Da yake yiwa magoya bayansa jawabi, Rasool ya ce, Abin da ya faru yana a matsayin wulakanta ku ne ku al’ummar Afirka ta kudu, amma kuma idan kuka tsaya tsayin daka kan manufofinku na ‘yancin kai to za ku ci gaba da rayuwa a cikin mutunci da daukaka. Ya ce ba laifi muka yi ba, ammam kuma mun dawo gida ba tare da...
Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan. A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin...
Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin halin da ake ciki a yakin da sojojin kasarsa suke fafatawa da gwamnatin kasar Amurka. Ya kuma kara da cewa jiragen yakin ruwa na kasar Amurka sun zama matsala ga gwamnatin Amurka maimakon su taimaka mata. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata aiko da jirgin ruwan yaki mai suna USS Carl Vession zuwa tekun Maliya don karfafa USS Harry Truman...
Shugaba hukumar makashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bada sanarwan cewa a ranar 8 ga watan Afrilu mai zuwa. Yace hukumarsa za ta kaddamar da sabbin magunguna da ta samar tare da amfani da makamashin Nukliya, a dai dai na ranar makamashin Nukliya ta kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto Islami yana fadar haka a yau Lahadi, ya kuma kara da cewa wannan ci gaban kari ne, kan ci gaban da kasar ta samu a wannan fannin, wanda kuma zai kara kyautata bangaren lafiya na kasar sannan ya zama hanyar samar da kudade ga kasar. Shugaba hukumar makamashin nukliya ta Iran ya kara da cewa a cikin shekarar Iraniyawa wanda ya kara kadai kasar...
Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta. Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta...
Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. “ Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya aike da wasika zuwa Tehran domin fara tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran; yayin da shi da kansa ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a wa’adinsa na farko. A halin da ake ciki dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa...
Wani sabon kazamin harin sojojin Isra’ila ya yi sanadin shahadar mutum 40 cikin sa’o’I 24 da suka gabata ciki har da Salah al-Bardawil, dan majalisar Falasdinu kuma mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. A cikin wata sanarwa da ta fitar yau, Hamas ta ce an kai wa Bardawil hari ne a wani hari na ” yahudawan sahyoniya na ha’inci”, a lokacin da yake gudanar da sallar dare a daren 23 ga watan Ramadan. An kashe shi ne tare da matarsa a wani hari da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa da ke yankin al-Mawasi, yammacin birnin Khan Yunis na kudancin Gaza. Kungiyar ta bayyana Bardawil a matsayin “alama ta siyasa, yada labarai,” da ayyukan bunkasa...
Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda rasuwa. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajia Safara’u Umar Radda, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Katsina. Cikin wani saƙo da tsohon mai magana da yawun gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Hajiya Safara’u ta riga mu gidan gaskiya bayan ta yi fama da doguwar jinya. Mabiya dandalan sada zumunta na ci gaba da bayyana alhini dangane da rasuwar Hajiya Safara’u.
Iran, ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a wani masallaci a kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa masallata. Akalla mutane 44 ne suka mutu yayin da 13 suka jikkata a harin da aka kai a kauyen Fonbita da ke cikin kauyan Kokorou dake jihar Tillabery wanda ya faru a lokacin da wasu ‘yan ta’addan na kungiyar Da’ish a yankin Sahara (ISGS) suka far wa masallacin, inda suka auka wa masu ibada dake sallar Juma’a. Baghaei ya bayyana cewa, wannan ta’addancin da aka aikata a lokacin sallar Juma’a ya saba wa ka’idar Musulunci, kuma ya saba wa...
An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye. Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya. Malam Aliyu Musa, da yake yin jawabi a madadin sauran manoman da ke yankin ya bayyana cewa, samar da shirin a yankin da gwamnatin jihar ta yi, tamkar zuba hannun jari ne. A cewarsa, al’ummar yankin za su ci gaba da yin addu’a, domin shirin ya dore tare kuma da ganin an kara fadada shi, don su ma sauran yankunan jihar su amfana....
Kyari ya ci gaba da cewa, wannan bangare na noma don samun riba; shi ma zai amfana da Naira biliyan 500, wanda ya kai kimanin dala biliyan 300, wanda su ma wadannan kudaden za a bai wa Bankin Aikin na Noma. Kazalika, Kyari ya yi kira ga Bankin EBRD, da ya zuba hannun jari a fannin aikin noman kasar, domin kasar ta cimma burin da ta sanya a gaba, musamman domin Nijeriya ta rage asarar da take yi a yayin girbin amfanin gona da samar da kayan aikin noman rani da sauran makamantansu. Dakta Heike Harmgart, Manajan Daraknatan Bankin na EBRD da ke kula da yankin Afirka, wadda kuma ta jagoranci tawagar a nata jawabin ta ce, tawagar ta kawo...
KAmfanin dillancin labarun “al-Somariyya Newas” ya ambato jagoran ‘yan hamayyar siyasa na kasar Turkiya Uzgor Auzal yana fadin cewa: A daren jiya juma’a adadin wadanda su ka fito Zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Rajab Tayyib Urdugan sakamakon sauke da kama ‘yan hamayyar siyasa da ya yi kaga kan mukamansu da su ka hada da magajin garin birnin Istanbul. Magajin garin Istanbul Imam Uglu ya yi watsi da duk wata tuhuma da aa yi masa ta hannu a cin hanci da rashawa. Kamfanin dillancin labaran “Reusters” ya nakalto wata majiyar shari’a tana cewa Imam Uglu ya yi watsi da dukkanin thume-tuhumen da aka yi masa masu alaka a cin hanci da rashawa. Shi dai Imam Uglu zai tsaya takarar shugabancin kasa...
A wata hira da tashar talabijin din, manzon musamman na Amurka a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff ya rubuta a shafinsa na; X cewa; Sakon da Trump ya aike wa Tehran ba ta nufin yin barazana. Manzon na Amurka ya riya cewa;wasikar ta kunshi cewa; Ni shugaban kasa ne mai son zaman lafiya , abinda nake son bayyanawa kenan, don haka babu bukatar a yi magar yaki. Wajibi ne mu zauna mu tattauna.” Wittkoff ya kuma ce; Da akwai hanyoyi na bayan fage da ake tatatunawa da Iran. Har ila yau ya kara da cewa; Abinda Trump yake so shi ne warware sabanin da ake da shi. Shafin watsa labaru na Axos ya bayyana cewa; Waskiyar da Trump din...
Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayyana a jiya Juma’a cewa, fadin yankin kasar dake fama da zaizayar kasa ya ragu zuwa murabba’in kilomita miliyan 2.6019 a shekarar 2024, wanda ya samu raguwar murabba’in kilomita 25,700, idan aka kwatanta da na shekarar 2023. Wadanann alkaluman wani bangare ne na sakamakon aikin sa ido kan zaizayar kasa a kasar Sin a shekarar 2024, wanda aka kammala a kwanan nan. Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya Sin Ta Ba Da Jawabi A Kwamitin Kare Hakkin Bil’adama Na MDD A Madadin Kungiyar Abokantaka Ta Inganta Hakkin Bil’adama Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, sakamakon da aka samu ya nuna cewa, ana samun ci gaba bisa...
Wata karya ta hadiyi safa 24 da sauran kayan sawa, inda suka makale masa a mukamuki – lamarin da ya haifar da yi masa tiyatar ceton rai a Jihar California a Amurka, kamar yadda cibiyar kula da dabbobi ta bayyana. Wata karya mai suna Luna, jinsin Bernese Mountain da ta shafe wata 7 tana fama da rashin lafiya, sakamakon hadiye wasu kayayyaki na mamallakinta a ranar 16 ga Fabrairu bayan kamar yadda Cibiyar Ba da Agajin Dabbobi ta Corona ta ce a cikin wani sakon da ta wallafa a Instagaram. Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas Lokacin da ta fara amai,...
Gwamnatin Jihar Borno, ta ɗauki matakin hukunta wasu ma’aurata, Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri. Bayan bayyanar faifan bidiyon da ya nuna ma’auratan suna dukan yarinyar, mutane da dama sun yi tir da abin a shafukan sada zumunta. Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia Wannan ya sa Hukumar Tsaron Sibil Difens (NSCDC) ta cafke su nan take. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta musu sassauci ba. Ya ce ma’aikatun shari’a, ilimi, da harkokin mata sun haɗa kai domin ganin an hukunta waɗanda suka aikata laifi. Yarinyar, wacce...
Bubu da kari, abin mahimmancin shi ne, shi talakan Nijeriya zai iya gani a kas na irin wadannan shirye-shiyen da gwamnatin ke son aiwatarwa? Fannin Da Gwamnatin Za Ta Zuba Kudaden: A kasafin kudin na 2025, Gwamnatin Tarayya ta warewa bangaren tsaro Naira tiriliyan 6.11 wanda ya kai ta samar da karin kaso 88 daga cikin kasafin kudin da ta warewa fannin na Naira tiriliyan 3.25 a 2024. Shin wannan burin na Gwamnatin zai iya cika, duba da yadda aka gaza dakile ta’addanci, ‘yan fashin daji, wanda idan ba a mayar da hankali ba, a 2025, tarihi ne zai sake mai-maita kansa. An ware Naira tiriliyan 5.99 a cikin kasafin kudin don yin tituna, gadoji da kuma manyan ayyuka...
Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree, ya bayyana cewa, Dakarun Yemen sun harba makami mai linzami samfurin Falasdinu-2 a babban filin sauka da tashin jirgin saman Haramtacciyar Kasar Isra’ila na Ben Gurion. Saree ya jaddada cewa, filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci ga zirga-zirgar jiragen sama, yana mai gargadin cewa za su ci gaba da kasancewa a fagen daga har sai Isra’ila ta kawo karshen yakin da take yi a kan al’ummar Gaza. Tun da farko dai rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da cewa, an harba makamai masu linzami a yammacin jiya Juma’a a yankuna da dama da ke tsakiyar Falasdinu da ta mamaye, kuma Isra’ila ta tabbatar da cewa an harbo makaman...
Daruruwan Falastinawa fararen hula ne suka yi shahada tun bayan da Isra’ila ta dawo da hare-haren kisan kare dangi a kan al’ummar yankin zirin gaza, matakin day a yi hannun riga baki daya da yarejejeniyar dakatar da bude wuta da aka rattaba hannu a kanta karkashin jagorancin Amurka, Masar da kuma Qatar. Dakarun mamaya na Isra’ila sun kaddamar da wani farmaki mai matukar muni da manyan makamai a ranar Juma’a a kan yankunan arewa maso yammacin Gaza da suka hada da Sudaniya, al-Karamah, da kuma Beit Lahia, wanda hakan ya yi sanadin shahadar fararen hula masu yawa da suka hada da mata da kananan yara, yayin da kuma wasu daruruwa suka jikkata. Sojojin Isra’ila sun yi gargadi ga dukkanin Falasdinawa...
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; Amurkawa su kwana da sanin cewa, babu wani abu da za su samu, ta hanyar yi wa Iran barazana, kuma waninsu ma ya sani cewa, idan har su ka aikata wani abu maras kyau akan Iran, to za su fuskanci mayar da martani mai tsanani. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a yau Juma’a dangane da bikin sabuwar shekara ta Noruz a Husainiyyar Imam Khumaini dake nan Tehran, ya bayyana cewa; Babban kusakuren ‘yan siyasar Amurka da kuma na Turai , shi ne daukar ‘yan gwagwarmaya a wannan yankin da cewa ‘yan koren Iran, da hakan batunci a gare su.” Jagoran juyin musuluncin...
Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta sanar da kama Mista Peter Dike da ake zargi da kashe matarsa a gidansu da ke Unguwar Oke-Ira Ilogbo Eremi, Marogbo. Rundunar ’yan sandan a ranar Alhamis ta bayyana cewa wanda ake zargin ya daɓa wa matarsa wuƙa har lahira a lokacin da suka yi ƙazamin faɗa da ya ɓarke a gidan nasu sanadin taƙaddama a ranar Laraba. ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Shahararren ɗan kasuwa Nasiru Ahali ya rasu a Kano Wannan mummunan al’amari ya ƙara dagula al’amuran tashin hankali a cikin gidan ma’aratan da ya kawo sanadin mutuwar matar aure. A watan Oktoban 2024, an kuma kama Motunrayo Olaniyi da laifin daɓa wa amaryarsa, Olajumoke wuƙa har...
Kazalika, a wata-wata, hauhawar farashin abinci a watan Fabrairun 2025 ya tsaya da kashi 1.67 cikin dari, idan aka kwatanta da watan Janairun 2025, an samu raguwar matsakaicin farashin kayan abinci kamar su dawa, dankali, wake, masara da garin masara da rogo. Hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Nijeriya dai ya yi tashin gwauron zabi ne tun bayan da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cire tallafi mai da sauyi da ya kawo kan musayar canjin kudade bayan da ya aka rantsar da shi a 2023. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan, a sakonsa na karshe ga Iraniyawa a shekara ta 1403 na kalandar Iraniyawa, ya bukaci mutanen kasar su hada kai don kaiwa ga manufofin kasar, wadanda suka hada da bunkasar tattalin arziki, da kauda tsadar rayuwa da kuma rashin bawa makiya damar cutar da kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jawabinda na ‘Nuruz’ ko sabon shekara ta 1404 wanda ya shigo yau. Pezeshkiyan ya bukaci All…ya yi rahama ga shuwagabannimmu da muka rasa a shekaran da ta kare, wadanda suka hada da Shahid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyar, da sharing maso gwagwarmaya a ciki da wajen kasar, wadanda suka hada da shahidan Lebanon Falasdin Siriya da...
Shi wannan azumi, na wani lokaci ya fi na wani lokaci kamar an so a dinga yin azumi sau Uku a cikin kowanne wata, lokacin kwanan wata yana 13 da 14 da 15, wannan kwanaki hasken wata ya fi haske a cikinsu, to kamar yadda suke haske haka zuciyarka za ta kara haske sabida saduwa da hasken, sannan kuma hawa-hawa na musulunci guda Uku ne (Islam da Iman da Ihsan) to wanda ya riski wannan kwanaki Uku kamar Ya hau dukka wannan Matakan addinin ne. Akwai azumin Litinin da Alhamis, azumin ranar Litinin Annabi (SAW) ne yake yi, an tambaye shi cewa Ya Rasulullahi sabida me kake azumin ranar Litinin? sai ya ce ranar ce aka haife ni, ina godiya...
Shugaba Kaïs Saïed na Tunisiya ya kori firaministan kasar Kamel Madouri, da aka nada a watan Agustan da ya gabata yayin wani gagarumin garanbawul a majalisar ministocin kasar a daren jiya Alhamis. Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce an maye gurbin firaministan kasar Madouri nan take inda aka maye gurbinsa da Sarra Zaafrani Zenzri, ministar kayan aiki. Sanarwar ta ce sauren mambobin gwamnatin zasu ci gaba da aikinsu. Garan bawul na shugaban kasar ta Tunisia a baya baya nan shi ne na ranar 6 ga watan Fabrairu inda ya sallami ministan kudinsa Sihem Boughdiri Nemsia da tsakar dare, tare da maye gurbinsa da alkalin kotun Michket Slama Khaldi.
Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025. Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu yi wa ƙasa hidima a babban birnin tarayya, a ofishin NYSC na shiyya ta 3 da ke Wuse Zone 3 Old Parade Ground a yankin Garki a ranar Alhamis. Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Ya sanar da masu yi wa ƙasar hidima cewa ma’aikatar kuɗi ta sanar da...
Sabon Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya isa jihar domin ci gaba da aiki. Ibas ya isa filin jirgin saman Fatakwal da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar ranar Alhamis inda ya samu tarba daga manyan jami’ai da jami’an tsaro. ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas Sabon Gwamnan, tare da rakiyar Kwamishinan ’yan sandan jihar, Olugbenga Adepoju da mataimakin babban sufeton ’yan sanda na shiyya ta 16, nan take suka wuce gidan gwamnati da ke Fatakwal. Tuni dai Ibas ya isa gidan gwamnati inda wasu jami’an gwamnati suka zagaya da shi harabar gidan. A yanzu haka yana ganawar sirri...
Darakta mai kula da al-amuran mata da kuma kare hakkin bil’adama a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Forouzandeh Vadiati, ta hadu da jakadan kasar Jamus a nan Tehran da kuma mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehrana a ma’aikara. Inda ta bayyana masu bacin ranta da yadda kasashen biyu suka shigar da wata daftari ta tuhumar Iran da abinda ya shafi hakin mata da a hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Vadiati yana zargin Berlin da kuma London na shiga cikin al-amuran cikin gida na JMI. Sannan ta tunanatar da kasar Jamus kan abinda ta aikata na bawa Sadam Hussain makaman guba a yakin shekaru 8 da suka fafata da kasar ta...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Lijiang na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin da yammacin jiya, inda ya ziyarci lumbunan samar da furanni masu aiki da sabbin fasahohi na zamani da tsohon garin Lijiang, don fahimtar yadda ake raya aikin gona na musamman mai la’akari da yanayin wurin, da yadda ake gaggauta karewa da amfani da kayayyakin al’adu na tarihi da aiwatar da ra’ayin dunkulewar al’umomin Sinawa. Lambun renon furanni mai aiki da fasahar zamani na Lijiang na da fadin hekta 73.3, wanda ya hada aikin shuka da sufurin furanni da yawon bude ido tare, kuma ya habaka aikinsa zuwa harhada man furanni da samar da busassun furanni da sarrafa abinci mai hade...

A Jiya Laraba Ce Iran Take Bukukuwan Cika Shekaru 78 Da Kwatar Kamfanin Man Fetur Na Kasar Daga Hannun Turawan Burtaniya
A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da taimakon gwamnatin lokacin suka sami nasarar kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar, daga hannun wani kamfanin mai na kasar Burtaniya suka maida shin a kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce , wannan rana abin alfakhari ne ga mutanen kasar, don bayan haka ne kasar ta sami ikon kawo ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma shimfida harsashen samun yencin kasar daga hannun kasashen yamma wadanda suka mamaye bangarori da dama a cikin al-amuran kasar. A ranar 19 ga watan Maris na shekara ta 1951 ne, wato shekaru 78...
Shugaban kwamiti na musamman dangane da yaki a Ukrai ya bayyana cewa kasar Rasha ta aikata laifukan yaki a yakin da take fafatawa a kasar Ukraine shekaru uku da suka gabata. Shafin yanar gizo na Labarai, Africa News’ ya nakalto Erik Mose ya na fadar haka a taron kwamitin da yake jagoranra danagen da yaki a Ukraine a birnin Geneva a jiya Laraba. Mose a fadawa kwamitin mai mutane 47 kan cewa, ya sami shaidu wadanda suke tabbatar da cewa a cikin shekaru uku da suka gabata gwamnatin kasar Rasha ta azabtar da wasu yan kasar Ukraine wadanda ta kama a yankuna guda 3 na Ukraine da ta kwace, kuma jami’an tsaron rasha sun azabtar da su, wasu kuma an...
LEADERSHIP ta tattaro cewa, kuɗaɗen an turasu ne ga Abubakar da Sambo inda su kuma suka miƙa tsabar kuɗaɗen ga wasu agent-agent da makusantan gwamnan. An kuma gano cewa da fari Abubakar da ke gudanar da BDC ya tsallake sharaɗin beli amma an sake cafke shi. A lokacin da aka tuntuɓi kakakin EFCC Dele Oyewale kan wannan lamarin, ya tabbatar da batun kamun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar sojin Isra’ila ta sanar a ranar Larabar nan da cewa, ta kaddamar da hare-hare ta kasa a tsakiya da kudancin zirin Gaza, biyo bayan hare-haren wuce gona da iri kan yankin Falasdinu. Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin sun karbe iko tare da fadada shi zuwa tsakiyar hanyar Netzarim, da nufin fadada yankin tsaro da samar da wani bangare na raba tsakanin arewaci da kudancin Gaza. A halin da ake ciki kuma, ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi gargadin karshe ga Falasdinawa a zirin Gaza, inda ya bukaci da su sako Isra’ilawa da suke garkuwa da su, su kuma kawar da kungiyar Hamas, a cewar wata sanarwa daga ofishinsa. “Idan ba a sako dukkan mutanen Isra’ila da aka yi...
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada ya bayyana a wannan Laraba cewa ya yi tattaunawa mai kyau” da Volodymyr Zelensky, washegarin da ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin. Ya kara da cewa tattaunawar ta yi armashi yayin da Amurka ke yunkurin tsagaita wuta a Ukraine. “Na yi magana da shugaban Ukraine Zelensky, ta dauki kusan awa daya, kuma galibin tattaunawar ta ta’allaka ne kan kiran da suka yi da shugaba Putin na jiya domin daidaita batun kasashen Rasha da Ukraine, kuma “Muna kan hanya madaidaiciya,” inji shugaban na Amurka a shafinsa na True Social Network. Tunda farko dama wakilin Amurka Steve Witkoff ya bayyana a ranar Talata bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Donald Trump da takwaransa...
Ga shi dai kwanakin Ramadan suna ta gudu, har mun kawo ga goman ƙarshe wanda shi ne dama ta ƙarshe ga wanda ya yi sakaci a farkon watan, ko kuma ya zama cikon alheri ga wanda ya kyautata ya bayar da abin da ake so a baya. Ya ku masoya! Goman ƙarshe na watan Ramadan kasuwa ce babba da masu tsere suke tserereniya a cikinta. Abubuwan da ba a sakaci da su a Ramadan —Sheikh Daurawa DAGA LARABA: Abin Da Ake Yi A Goman Tsakiyar Ramadan A Addini Da Al’ada Lokaci ne da wanda ya yi sakaci yake ƙara ƙwazo a cikinsa, ake jarraba masu himma a cikinsa, ake tantance ma’abota Lahira da ma’abota duniya. Da yawa masu huɗuba sun...
Rahotanni daga sansanin ‘yan hijira na Nablus a yammacin kogin Jordan sun ambaci cewa sojojin mamayar HKI sun tilasta wa iyalai 10 ficewa daga gidajensu. Sojojin na HKI suna shirin kaddamar da wani gagarumin hari na tsawon kwanaki uku a cikin sansanin “Ayn.” Dake Nabilus. A gefe daya, kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa; Sojojin Amurka suna da shirin kai hare-hare ta kasa a cikin yankin Gaza. Jaridar “Wall Street Journal” ta bayyana cewa; Sojojin na mamaya za su ci gaba da zama a yankunan da su ka shiga a cikin Gaza, sannan kuma su kai wasu sabbin hare-hare ta kasa.
Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki 57 da kasar Ukiraniya ta harba zuwa yankuna mabanbanta na kasar. A yau Laraba ne ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta sanar da cewa; An harbo jiragen marasa matuki 35 da aka harba wa yankin Kursk dake yammacin Syria a jiya da dare. Sai kuma wasu jiragen 13 da aka harba a yankin Oryol da kuma wasu 7 a samaniyar tekun Azorf. Sauran yankunan da sojojin Ukuraniya su ka harba wa makamai masu linzamin sun hada Tola, da Biryansk. Kwanaki biyu da su ka gabaa ma dai sojojin na Rasha sun sanar da kakkabo wasu jirage marasa matuki na Kasar Ukiraniya 31 da aka harba a yankuna mabanbanta na...
A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, an kafa kamfanin ne domin rage tsadar sarrafa kayayyakin amfanin gona a fadin jihar. Ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da fitar da sama da naira miliyan dari tara da sittin da tara domin ci gaba...
Majiyar gwamnatin kasar Yemen ta basa sanarwan kai hare-hare har sau biyu kan kataparen jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki na kasar Amurka dake cikin Tekun Red sea, wato USS Harry Truman. Inda suka cilla makami mai linzami guda da kuma jiragen yake wadanda ake sarrafasu daga nesa kan jirgin. Har’ila yau sojojin yamen sun ce sun kaiwa wasu sojojin Amurka hare-hare da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa duk a cikin sa’oi 48 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Yahyah Saree ya na fadar haka a safiyar yau talata, ya kuma kara da cewa sojojin kasar za su ci gaba da maida martani da kuma hana jiragen...
A ranar Juma’a, fadar Kremlin ta ce Shugaba Putin ya aike saƙo zuwa ga Trump ta hannun manzon Amurka na musamman, Steve Witkoff, yana bayyana cewa Rasha tana nazarin batun tsagaita wuta amma tana taka-tsantsan. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta kai ga samun mafita, amma ya jaddada cewa dole ne Rasha ta mayar da yankunan da ta ƙwace. Tun a shekarar 2014, Rasha ta ƙwace yankin Crimea, sannan a shekarar 2022 ta mamaye wasu yankuna huɗu na gabashin Ukraine. Yanzu dai ana fatan wannan tattaunawa za ta kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana ci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Gwamna Abba Kabir Yusuf a wannan Litinin ɗin ya rantsar da sabon Kwamishinan Ma’aikatar Tsarawa da Bunƙasa Gidaje ta Kano, Ibrahim Yakubu Adamu. Wannan dai shi ne karo na huɗu cikin ƙasa da shekaru biyu ke nan da gwamnan yake faɗaɗa majalisar zartarwa jihar ta Kano. Ana zargin wa da ƙani da yi wa almajiri yankan rago a Adamawa Majalisar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara Aminiya ta ruwaito cewa gabanin wannan sabon naɗin, Ibrahim Yakubu Adamu shi ne Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Kano KNUPDA. Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Kano, Haruna Isah Dederi ne ya jagoranci rantsar da sabon Kwamishinan da aka gudanar a fadar Gwamnatin Kano. Da yake jawabi, Gwamnan ya yaba wa sabon kwamishinan...
Iran ta ce za ta fifita diflomatisyya ta tsakaninta da kasashe makobtanta na yankin. Ministan harkokin wajen kasar ne Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar kan harkokin diflomasiyya a yankin, yana mai bayyana cewa kasashen da ke makwabtaka da kasar na cikin tsarin Jamhuriyar Musulunci. “Makwabtanmu sune fifikonmu,” in ji ministan harkokin wajen Iran a cikin wani sako da aka wallafa a shafinsa na X. Mista Araghchi ya tattauna da takwarsana na Omani, Badr bin Hamad Al Busaidi, a Muscat, babban birnin kasar Omani, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu da na shiyya-shiyya. Babban burinmu shi ne kare zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar diflomasiyya. Ziyarar ta Araghchi a birnin Muscat na zuwa ne a...
Rundunar ’yan sandan Adamawa ta cafke wani ƙani da yayansa — Aliyu Abdulmalik da Ibrahim Abdulmalik — kan zargin yanke kan wani almajiri ɗan shekara 10, Abdallah Lawali. Bayanai sun ce ’yan uwan junan biyu sun aikata wannan ta’asa ce a ranar 7 ga watan Maris a unguwar Sarkin Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Jada. Majalisar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine Sanarwar da rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce an kama ababen zargin ne da gangar jikin almajirin a cikin wani buhu, yayin da aka ƙwaƙulo kansa a cikin wani rami da suka binne a harabar gidansu. Rundunar wadda ta ce yanzu haka bincike ya kankama a kan lamarin, ta...
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana shirin tuntuɓar takwaransa na Rasha Vladimir Putin da zummar tattauna batun kawo ƙarshen yaƙin Ukraine. Trump ya shaida wa manema labarai hakan a cikin jirgin shugaban ƙasa na Airforce One a kan hanyarsa ta zuwa Washington daga Florida cewa yana ƙoƙarin ganin cewa yaƙin ya zo ƙarshe. Madalla da hutu ga ’yan makaranta domin azumi Tsohuwar ɗaliba ta kai ƙarar makarantar da ta kammala Trump ya bayyana cewa an yi aiki sosai a game da kawo ƙarshen wannan rikici a cikin ƙarshen makon da ya gabata. Trump na ƙoƙarin samun goyon bayan Putin a game da tayin tsagaita wuta na kwanaki 30, wanda Ukraine ta aminnce da shi a makon jiya. Sai dai...
A jiya Lahadi ne dai kungiyar ta ‘yan ta’adda ta kai hare-hare akan iyakar Lebanon ta yankin Hermul Ma’aikatar tsaron Syria ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta riya cewa; harin nata martani akan wani hari da aka kai a can cikin kasar wanda ta jinginawa HIzbullah, da kuma ya yi sanadiyyar mutumar jami’an tsaro uku. Kungiyar ta Tahrirush-sham ta yi amfani da makamai rokoki da atalare wajen kai hari daga kan iyaka. Tuni dai kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta karyata zargin na kungiyar Tahrirus-sham. Ofishin da yake kula da watsa labaru na Hizbullah ya bayyana cewa; Babu gaskiya a cikin labaran da ake watsawa na cewa Hizbullah tana da hannu a...
Gidauniyar Aliko Dangote, a cikin shirye-shiryenta na 2025, na bayar da tallafin abinci ga ‘yan Nijeriya, ta ƙaddamar da rabon abinci, inda ta ware kimanin Naira Biliyan 16 domin tallafa wa talakawa ‘yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu nakasa. Shirin da fiye da mutum miliyan ɗaya ne za su rabauta da tallafin buhunhunan shinkafa mai nauyin kilo 10 daga wannan tsarin na gidauniyar Aliko Dangote. NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar, Shugaban gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce an tsara yin rabon shinkafar buhu miliyan ɗaya ne ga ‘yan Nijeriya...
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ta cafke shahararriyar jarumar nan ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya. Bayanai sun ce hukumar mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta cafke Murja Kunya bisa zargin wulaƙanta takardar Naira. NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi Wata majiya daga EFCC ta tabbatar da cewa an kama Murja a ranar Asabar a Kano, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin, a cewar Gidan Rediyon Freedom da ke Kano. Majiyar hukumar ta ce idan bincike ya kammala, za a gurfanar da ita a kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da kukan rashin aikin yi da a ko da yaushe ke ci gaba da addabar ‘yan Najeriya, a wasu lokutan ba rashin aikin yi ne matsalar ba, waɗanda za su cike guraben ayyukan ne suka yi ƙaranci a Najeriya. Alƙaluma na ci gaba da bayyana dubban ‘yan Najeriya ne dai ke fito wa daga manyan makarantun ƙasar a kowace shekara. A yayin da da yawa ba sa samun aikin yi, sau tari akwai ɗimbin guraben ayyuka da babu masu cike su don babu ƙwararrun da ake buƙata. NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Ta A Najeriya DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa? Shirin Najeriya A Yau...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya. Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wannan Lahadi, bayan da Washington ta zargi Tehran da taimakawa sojojin Yaman a hare-haren da suka rika kaiwa haramtacciyar kasar Isra’ila a baya-bayan nan tare da yin kira da ta daina yin wanann zargi maras tushe balantana makama. Salami ya ce, “Iran ba za ta taba zama mai fara yaki ba, amma idan aka fuskanci barazana, za ta mayar da martani mai tsanani.”...

Yunkurin Neman ‘Yancin Kan Taiwan Ya Shaida Yunkurin Lai Ching-te Na Neman Mulki Irin Na Kama Karya Ta Hanyar Demokuradiyya
Kalmar demokuradiyya kalma ce da jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te ke yawan ambata, amma aikin da ya yi bai bi hanyar demokuradiyya ba. A baya-bayan nan, Lai Ching-te ya gabatar da wani shirin neman ‘yancin kan Taiwan, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokuradiyya ce mai mulkin kanta. Lai Ching-te ya kan yin amfani da demokuradiyya don ya cuci jama’ar yankin Taiwan da sauran kasashen duniya, amma a wannan karo kowa ya san yunkurinsa na neman mulki irin na kama karya ta hanyar demokuradiyya. Ya kamata a yi amfani da demokuradiyya don tabbatar da hakkin jama’a, a maimakon kawo illa ga hakkin jama’a. Jama’ar yankin Taiwan suna neman zaman lafiya, da samun ci gaba, da yin mu’amala,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar JMIa bude yake ga kasashen Turai don tattaunawa da fahintar juna kan matsalolin da bangarorin biyu suke sabani a kansu, tare da mutunta hurumin Juna. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiyaAsabar a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Netherlands Caspar Veldkamp a jiya Asabar. Ministan ya kara da cewa dangantakar diblomasiyya tsakanin Dutch da Iran tsohuwar dangantaka ce. Sannan Iran tana da nufin fadada shi. A Nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Netherlands yay aba da yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu yake bunkasa. Sannan dangane da tsabirin kasar Iran guda uku, Abu Musa, Tumbe kucek da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran y ace gwamnatin kasar Amurka bata da hakkin tsarawa kasar Iran yadda zata gudanar da manufofinta harkokin waje, wannan ya wuce tun bayana nasarar juyin juya hali musulunci a kasar a shekara ta 1979. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X. Aragchi yana maida martani ne ga shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya tuta sojojinsa suka kai hare-hare kan kasar Yemen a jiya Asabar, don kada su hana jiragen ruwan HKI wucewa daga tekun Red Sea. Kuma ya ce: Ya gargadi Iran ta dakatar da tallafin da take bawa kungiyar Ansarullah. Don itace da alhakin duk abinda kungiyar take yi. Ministan ya kara da...
Duk da kokarin da ma’aikatan asibitin suka yi na ceto shi, rahotanni sun ce ya samu raunuka da dama ciki har da guda daya a zuciya. Jaridar Irish Mirror ta ruwaito cewa ‘yansanda suna tsare da Eghomwanre har zuwa lokacin da zai gurfana a gaban alkali Michele Finan a kotun gundumar Dublin. A yayin shari’ar, Garda Grainne Collier ya bayar da rahoton kama Eghomwanre, tuhuma, da kuma taka tsantsan. An ce wanda ake zargin yana fuskantar tuhume-tuhume da dama da suka hada da cin zarafin Babatunde a titin Anne South, da laifin cin zarafin abokinsa, Adetola Adetuilehin, a layin Duke, da kuma tashin hankali. Alkalin kotun mai shari’a Finan ya ba shi taimakon shari’a, inda aka tsare shi a gidan...
Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin tunawa da shahid Mahadi Bakiri a garin Tabriz ya bayyana cewa;; Babu yadda za ayi jamhuriyar musulunci ta Iran ta bude tattaunawa da Amurka a karkashin barazana, yana mai kara da cewa; yin gwawarmaya da jajurcewa a gaban masu girman kai da daga hanci, yana daga cikin muhimman koyarwar alkur’ani mai girma da kuma tsarin musulunci. Manjo janar Salami ya kara da cewa; ta hanyar tsayin daka da dunkulewar al’umma wuri daya, za a kai ga samun nasara. Haka nan ya kara da cewa; A tsawon shekaru 46 da su ka gabata, al’ummar Iran ta kasance a cikin fadaka wajen fuskantar duk wata...
Kamitin Zakka na Masarautar Hadejia ya raba zakkar kayayyakin amfanin gona da na kudi kimanin naira miliyan 63 a gundumar Birniwa dake Jihar Jigawa. Sakataren kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Injiniya Isma’ila Barde, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon zakka ga mabukata a gundumar Birniwa. Injiniya Isma’ila Barde ya lissafa abubuwan da aka bayar a matsayin zakka, da suka hada da buhunan Gero 668, da Bahunan Dawa 152 da bahunan shinkafa 8 da rabi da Kuɗi kimanin naira miliyan 17 da dubu ɗari tara da goma sha shida. A nasa jawabin, Shugaban kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Barrista Abdulfatah Abdulwahab wanda babban limamin masarautar Hadejia Ustaz Malam Yusuf Abdurrahman ya wakilta, ya yaba wa al’ummar Birniwa bisa bayar da...

Tsohon Firaministan Lebanon: Rashin Fahimta Da Shakku Daga Waje Ba Za Su Iya Dakatar Da Ci Gaban Kasar Sin Ba
Daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2024, an gudanar da taron kasa da kasa na “Fahimtar kasar Sin” a birnin Guangzhou. A yayin taron, fiye da baki 600 na kasar Sin da kasashen waje, ciki har da tsohon firaministan kasar Lebanon Hassan Diab, sun hallara don tattaunawa da yin musayar ra’ayi kan taken “Yin gyare-gyare-zamanintarwa irin ta kasar Sin da sabbin damammakin ci gaban duniya”, inda suka samu ra’ayin bai daya na gudanar da hadin gwiwa. A tattaunawar da ya yi da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, Hassan Diab ya bayyana cewa, fahimtar kasar Sin yana da matukar muhimmanci, domin kasar na bude kofarta ga duniya. A cikin...
Gwamnatin Trump na duba yiwuwar sanya takunkumin hana zirga-zirga ga ‘yan kasashen duniya 41 a wani bangare na yaki da kwararar bakin haure da aka kaddamar a farkon wa’adin shugaban na Amurka na biyu. Wani bayanin cikin gida da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nakalto ya nuna cewa an rarraba wadannan kasashe zuwa rukuni uku. Rukunin farko na kasashe goma, da suka hada da Afghanistan, Iran, Syria, Cuba da Koriya ta Arewa, za a sanya musu takunkumi baki daya. A rukuni na biyu, Eritrea, Haiti, Laos, Myanmar, da Sudan ta Kudu za su fuskanci dakatarwar wani bangare da ya shafi bizar masu yawon bude ido da dalibai, da kuma biza na bakin haure, tare da wasu kebantattu. Rukuni na...
Rahotannin dake fitowa daga Falasdinu na cewa wani hari da Isra’ila ta kai a arewacin zirin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa tara, ciki har da ‘yan jarida uku a cikin gida, in ji ma’aikatan lafiya. An kai harin ta sama a wata mota a garin Beit Lahiya da ke arewacin zirin yau Asabar. A cewar likitocin, mutane da dama sun samu munanan raunuka, tare da jikkata a ciki da wajen motar. “An kai shahidai tara zuwa asibiti, da suka hada da ‘yan jarida da dama da ma’aikata daga kungiyar agaji ta Al-Khair, sakamakon harin da aka kai wa motar da wani jirgi mara matuki a garin Beit Lahia, tare da luguden wuta a yankin,” in ji kakakin hukumar tsaron farar...
Shi ma, Manajan Darakta na CDI, Roland Oroh, ya goyi bayan wannan ra’ayi na Dakta Anyebe Idoga, inda ya sanar da cewa; wannan aiki, zai kara karfafa karfin Nijeriya wajen fitar da kaya zuwa ketare. “Mun ji dadi kan fara wannan yarjejeniya da mu, domin wannan zuba hannun jari, zai taimaka wa Nijeriya wajen kara habaka fitar da ingantaccen nama zuwa ketare”, in ji Oroh. Kazalika, an bijiro da wannan hadaka ce, sakamakon yadda Saudiyya ta nuna sha’awarta, na son shigar da nama zuwa kasarta daga Nijeriya, wanda ya kai tan 176,000 a duk shekara, tare da kuma ciyawar dabbobi ta alfalfa hay da abincin dabbobi da ake sarrafawa da kuma Waken Soya. A yanzu haka, CDI na ci gaba...
“ Zuba hannun jari a bangaren da ake sauke kaya a Tashohin Jiragen Ruwa da kara fadada hanyoyin layin Jiragen kasa, za su iya taimakawa wajen bunkasa aiki da kuma kara sanya gasa a ayyukan tafiyar da Tashoshin Jiragen Ruwa. A cewar Dantsoho Ya sanar da cewa, samar da kyakaywan yanayin kasuwanci a kasar nan na da alaka da kokari da kuma yanayin gasar da aka samar na kasa a Tashishin Jiragen Ruwan, inda ya yi nuni da cewa, wadannan abubuwan sun taimaka wajen samun musayar kudade, daidaita tattalin ardikin kasar, kara habaka kauswanci da kuma samun masu zuwa zuba hannun jari. Dantsoho ya godewa Ministan Bunkasa Tattalin Arziki na Ruwa Adegboyega Oyetola, bisa goyon bayan ada yake ci gaba...
Ya kara da cewa bisa sashin 10.7 da aka sake nazarinsa a 2019, ya rage cajin daga N65 zuwa N35 kan kowace hada-hada. Sai dai ya bayyana cewa za a biya Naira 100 ga duk wanda aka cire na Naira 20,000 ga kwastomomi daga wasu bankunan da ke yin mu’amala da ATM a harabar bankin. Onobun ya jaddada cewa abokan hulda daga sauran bankunan da ke yin mu’amala da ATMs a wajen harabar bankin, manyan kantuna, kasuwanni, da sauran wuraren taruwar jama’a, za a rika biyan su Naira 100 da karin N500. Majalisar a cikin kudurorin ta ta bukaci CBN da ya gaggauta dakatar da aiwatar da wannan manufa, har sai an yi huldar da ta dace da kwamitocin da...
Kudirin ya kuma nemi kafa wata hanyar warware takaddama don magance rikice-rikicen da suka shafi jam’iyyun siyasa, mambobinsu, ‘yan takara masu zaman kansu, da kuma kawance. Bugu da kari, ta tanadi hukunci kan keta haddi da bayar da shawarar gyara ga dokar zabe ta 2022 don cire rajistar jam’iyyun siyasa daga hukumar INEC. Bayan gabatar da shawarwari, an mika kudirin ga kwamitin majalisa mai kula da harkokin zabe da kwamitin jam’iyyun siyasa domin ci gaba da tattaunawa a kansa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
A jawabinsa na godiya a wurin taron, dan majalisar dokokin ya bayyana godiya ga al’ummar Funtuwa, ya ce zai ci gaba da kawo ayyukan alheri tare da abubuwan jin dadin more rayuwar ga al’ummar mazabunsa na Funtuwa da kewayenta gaba daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Takardar da aka yi nazari a karshen watan Janairu ta nuna cewa a watan Fabrairun 2025, an ware shirin samar da mai na kan naira zuwa jirgin dakon mai hudu ne kawai, rukuni hudu zalla, kuma a watan Maris, dakon man biyu ne kawai aka yi da ya kai ganga 950,000 (ganga miliyan 1.9 ga watan). Wannan yana wakiltar rabon ganga 61,290 a kowace rana kasa da makasudin 385,000 bpd a karkashin tsarin. Karancin samun danyen mai ya tursasa wa matatar man Dangote garzaya wa kasashen waje domin neman danyen man. A baya-bayan nan kamfanin ya samu gangar danyen mai miliyan 12 daga Amurka. Duk da dai har yanzu matatar Mai ta Dangote ba ta fito a hukumance ta yi...
Alhaji Dangote, hamshakin attajirin nahiyar Afirka, ya ce sun hada kai da gwamnatin jihar ne wajen tabbatar da ganin an raba abincin ga mabukata a kowace jiha dake fadin Nijeriya. Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin abincin a matakin kasa na wannan shekara, ya ce aiwatar da wannan shiri ya nuna tsantsar halin nuna jinkai da kulawar Alhaji Aliko Dangote wajen kawar da yunwa da fatara a Nijeriya. Gwamnan wanda mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce za a raba buhun shinkafar guda dubu 120, mai nauyin kilogram 10 a daukacin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano. A jawabinta ga manema labarai, Babbar Darakta kuma Babbar jami’ar gudanarwar gidauniyar Aliko...
Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki. Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau. A cewar Gidan-Goga, Ministan ya zabi bayar da kudi ne maimakon kayan abinci, saboda tuni wasu ‘yan siyasa a jihar suka raba wa magoya bayansu hatsi. Ya kuma jaddada cewa tallafin kudi zai baiwa magoya bayan jam’iyyar APC damar siyan wasu muhimman abubuwan da ake bukata a cikin watan Ramadan. “A wannan karon,...
Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da kungiyar al-Shabaab ta kai a wani otel da ke garin Baledweyne, inda shugabannin kabilu ke ganawa ya kai mutane 10, kamar dai yadda majiyoyin ‘yan sanda na kasar ta Somalia suka tabbatar. Sannan kuma bayanin hukumar ‘yan sandan ta kasar Somalia ya tabbatar da cewa, akasarin wadanda suka rasa rayukansu fararen hula ne. A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani otel da ke birnin Baledweyne da wata mota da aka shakare da bama-bamai, kafin daga bisa suka shiga cikin otal din suka kai farmakin da ya dauki tsawon yini guda. Majiyoyin ‘yan sandan sun tabbatarwa kamfanin dillanmcin labaran Reuters cewa, hudu daga cikin ‘yan ta’addan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto da ke nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru a Najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekara. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Haka kuma, binciken ya nuna cewa mutane da ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi samun aiki sama...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto da ke nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru a Najeriya da kaso 5.3 a farkon wannan shekara. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya Haka kuma, binciken ya nuna cewa mutane da ba su yi karatu mai zurfi ba sun fi samun aiki sama...
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ’yan ƙauye su goma daga wasu unguwanni uku da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a daren ranar Larabar, da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare inda wasu gungun ’yan bindiga suka kai farmaki a unguwar Unguwan Yashi-Maraban Kajuru tare da yin garkuwa da mutane shida. Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo Waɗanda aka sace su ne: God-Dream Ladan, Lady God-Dream, Philip Mudakas, Mercy Philip, Bitrus Philip, da Gmen Philip. Hakazalika, a ƙauyen Makyali, wasu mutane biyu sun samu raunuka na...
Gwamnatin Tarayya ta ce ‘yan Najeriya sun fara samun sauki yayin da farashin kayan abinci ke raguwa da farashin fetur ke daidaita, kuma naira ke karɓar ƙarfi. Da yake magana a taron manema labarai na ministoci karo na huɗu a Abuja, Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohamed Idris, ya ce ci gaban, suna nuna cewa gyare-gyaren tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu na yin tasiri. Ya amince da wahalhalun da ‘yan Najeriya suka sha amma ya tabbatar da cewa hakan ya fara wucewa. Mohamed Idris ya ce Gwamnatin Tarayya tana nan daram wajen daidaita tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma. A jawabinsa, Ministan Ilimi, Dr. Maruf Alausa, ya ce kudaden da aka...
Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta fara rabon tallafin kudi naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas ga iyaye mata marayu dari biyu da saba’in da bakwai da masu bukata ta musamman a jihar Sokoto domin tallafawa kananan sana’o’i. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Shugaban shirin, Malam Lawal Maidoki ya bayyana cewa, matakin ya yi daidai da kudurin wanda ya kafa na rage radadin tattalin arziki a tsakanin marasa galihu. Ya bayyana cewa an zabo mutane 12 da suka ci gajiyar tallafin daga kowace karamar hukumar jihar 23 da suka hada da zawarawa 10 ko marayu mata da kuma nakasassu biyu a kowace karamar hukumar. Ya ce kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tattauanwa da Iran ba komai ba ne illa wani yunkuri na yaudarar al’ummar duniya. “Mun zauna tsawon shekaru muna tattaunawa, mun zamna da su teburin tattaunawa, bayan hakan shi wannan mutumin ya yayyaga yarjejeniyar da aka sanya wa hannu,” kamar yadda jagoran ya bayyana yayin da yake jawabi ga taron dalibai a birnin Tehran a jiya Laraba. “tunda mu ka ga baya girmama yarjejeniya, menene ma’anar yin shawarwari kuma ?” “Saboda haka, kiraye-kirayen yin shawarwarin da tattaunawa na da nufin yaudarar jama’a na duniya.” Inji jagoran. Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce “Idan manufar tattaunawar ita ce a...
Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau. Kundin rahoton ya kuma bayyana cewa, a shekarar 2025 gwamnatin kasar za ta kara zage damtse wajen raya kauyukan dake rabe da birane da gyara gine-ginen da suka tsufa. Ga duk wanda yake shiga yankunan kauyuka da ke cikin birane (kamar unguwannin masu karamin karfi) ko wadanda suke rabe da su zai ga ba su da kyawun gani, domin kayayyakin alatu da kayatattun gine-gine da ababen more...
Majalisar Wakilai ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya dakatar da sabon tsarin ƙarin caji kan cire kuɗi ta na’urorin ATM. Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwa da CBN ya fitar, inda ya ƙuduri aniyar fara cajin Naira 100 kan duk cire Naira 20,000 daga ATM a banki, daga ranar 1 ga watan Maris, 2025. Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno Ɗan majalisa Marcus Onobun (PDP, Edo) ne, ya jagoranci ƙudirin da ya buƙaci a dakatar da wannan tsari, inda ya bayyana cewa tsarin zai ƙara jefa ’yan Najeriya cikin wahala. Ya bayyana cewa, a shekarar 2019, an rage cajin cire kuɗi ta...
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba wa ƙananan ’yan kasuwa da matsakaita su 9,403 a ƙananan hukumomin Biu da Hawul, tallafin Naira biliyan ɗaya. Wannan tallafi na da nufin ƙarfafa kasuwanci, haɓaka tattalin arziƙi, da rage talauci a yankunan. Dan ta’adda zai biya tarar miliyoyi bayan shan dukan kawo wuka a Katsina Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha A Biu da Hawul, gwamnan ya raba Naira miliyan 560.3 ga ’yan kasuwa 5,603, inda kowane mutum ya samu Naira 100,000. Hakazalika, ya raba Naira miliyan 439.7 ga matasa da magidanta 1,800 a Biu da kuma ’yan kasuwa 2,000 a Hawul. Gwamna Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ƙananan ’yan...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Trump ya dauka kan Iran, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba Ukraine ba ce, kuma ba za ta yi shawarwari da Amurka bisa barazana ko tilasci ba. “Dole ne mu kiyaye dangantaka da duniya. Ba ma son mu yi sabani ko jayayya da kowa, amma hakan ba yana nufin za mu durkusa cikin wulakanci a gaban kowa ba,” in ji Pezeshkian yayin wani taron kungiyar ‘yan kasuwan Iran a Tehran a ranar Talata. “Muna iya mutuwa da daraja, amma ba za mu taɓa rayuwa cikin kunya da kaskanci ba.” Pezeshkian ya yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin wa’adi daga Donald Trump,...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne. “Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.” Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da...
Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas. Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar...
Tare da cewa Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki fiye da 60 da Ukiraniya ta harba, sai dai an sanar da mutuwar mutum daya a birnin Moscow. Kantoman yankin Moscow Andrey Vorobyov ne ya sanar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu 3 su ka jikkata, sanadiyyar hare-haren da Ukiraniya ta kai wa birnin da makamai masu linzami masu yawa da safiyar yau Talata. Kantoman Mascow ya rubuta a shafinsa na “Telegram’ cewa; “ ya zuwa yanzu an sami labarin mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu 3 a garin Fidnoveh a kudancin Moscow.” Sai dai daga baya wasu kafafen watsa labarun Rasha sun ambaci cewa adadin wadanda su ka jikkata din ya karu...
Hukumar da take fada da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya ta’annatii ta kwato da kudaden da sun kusa dalar Amurka miliyan 500. Haka nan kuma hukumar ta kwato man fetur da sauran dangoginsa da sun kai ton 931,000, sai kuma gidajen da sun kai 975. A cikin rahoton da ta fitar a ranar litinin hukumar ta EFCC ta bayyana cewa, ta sa an hukunta masu laifi har su 4,000 wanda shi ne adadi mafi girma tun kafa ta. Tuni an zuba wasu kudaden da aka kwato a cikin ayyukan gwamnati. A karshen rahoton hukumar “Transparency International” ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 140, a jerin masu fama da cin hanci da rashawa, bayan da a baya ta kasance...
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki huɗu. Wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Litinin a Abuja, ta ce mutane su guji fita cikin tsananin zafi musamman daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3. Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’ Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar. Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Neja da Kwara da...
Kimanin fararen hula 1,000 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a hare-haren jiragen yaki marasa matuki a nahiyar Afirka, yayin da ake ci gaba da yin amfani da jirage marasa matuka a nahiyar. A cewar jaridar The Guardian, masu sharhi da nazari na cewa , daga shekara ta 2021 zuwa 2024, jami’an tsaro a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka sun yi amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kai hare-hare, wanda kuma sau tari ana kashe fararen hula ne, maimakon masu aikata laifuka. Dole ne wannan ya kawo karshe, kuma dole ne kasashen duniya su dauki matakai da suka dace waje saka kaidoji kan amfani da jiragen yaki marasa matuka, domin rashin yin hakan zai ci gaba da...
Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar Uttar Pradesh ta Indiya ya bukaci musulmi da su yi sallar Juma’a a gida. A cewar radiyon gwamnatin Pakistan, Firimiyan Jihar Uttar Pradesh Yogi Adityanath ya kare kalaman jami’in ‘yan sandan game da musulmi, inda ya ce, “A yayin da ake gudanar da bukukuwan Holi sau daya a shekara, ana gudanar da sallar Juma’a a duk mako.” Ya bayyana jami’in a matsayin gwarzo jarumi, tare da bayyana cewa wannan ra’ayi nasa daidai ko da kuwa hakan ya bakantawa wasu. Ya kara da cewa: “Bikin Holi ya fi sallar Juma’a muhimmanci, amma ana gudanar da shi sau daya ne kawai a shekara, don haka gudanar da shi yana da fifiko a kan Jum’a.” Jami’in...
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin. Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Francesca Albanese ta fada a ranar Litinin cewa shawarar da Isra’ila ta dauka na yanke wuta a Gaza na nufin tsaida hanyoyin samar da ruwa a zirin. Albanese ta kuma yi Allah wadai da rashin daukar mataki kan hakan daga kasashen duniya. A ranar Lahadin da ta gabata ne, kafofin yada labaran Isra’ila...
Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta. Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali da Nijar. Ci gaba da huldar tattalin arziki da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, na daga cikin jigon rangadin da shugaban Ghana ya kai a kasashen na AES. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta...
’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Wata majiyar ’yan sanda, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa maharan ɗauke da bindigogi sun auka yankunan ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka soma harbe-harbe kan mai uwa da wabi. Majiyar ta ce kawo yanzu dai an tsinto gawawwaki mutum 14 yayin da ake ci gaba laluben wasu. Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan...

Iran Ta Ce Shirinta Na Makamashin Nukliya Na Zaman Lafiya Ne, Kuma Ba Zata Tattauna Da Amurka Karkashin Barazana Ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi ya na fadar haka a shafinsa na X a yau Litinin, ya kuma ce wannan ita ce martanin Iran a kan sakon da Amurka ta ce aikawa jami’an gwamnatin kasar Iran, na cewa su zabi tattaunawa ko yaki. Kafin haka Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, kasashen yamma musamman...

Sojojin Ruwa Na Kasashen Rasha Da China Sun Shigo Kasar Iran Don Fara Atisayen Sojojin Ruwa Mai Suna “Damarar Tsaro 2025”
Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan gagarumin atisayen sojojin ruwa tsakanin manya-manyan kasashen guda uku zai sami halattan wasu kasashe da dama a matsayin masu kallo. Labarin ya kara da cewa manya-manyan jami’an sojojin ruwa na sojojin Iran da kuma na dakarun IRGC ne suka tarbi jiragen ruwan yaki na wadannan kasashe. Sannan ana saran wakilai daga kasashen Azerbaijan, Iraki, Kazakhstan, Oman, Pakistan, Qatar, Afirka ta Kudu, Sri Lanka da Haddiyar...
Yau Litinin, aka rufe taro na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran manyan jami’an gwamnati da jami’yyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, sun halarci taron. A gun bikin rufe taron, an zartas da kudurin rahoton aikin kwamitin dindindin na taron, da rahoton da kwamiti mai kula da kudurori ya gabatar game da bincike kan kudurorin da aka gabatarwa taron, kana da kudurin siyasa na taron da dai sauran muhimman takardu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai Okocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi. “Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha. Tun...
Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel din nan uku da suka balle daga kungiyar Ecowas. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kasashen uku na Sahel. Saidai a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na Nijar, hukumomin kasar sun tabbatar da cewa kasashen sun tabbatar da aniyarsu ta karfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashensu a fannonin siyasa, tattalin...
Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi, Cif Patrick Adaba ya riga mu gidan gaskiya. An ruwaito cewa Cif Adaba wanda ya shafe shekaru 78 a doron ƙasa ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya a Abuja. Abba ya ƙaddamar da bincike kan zaftare albashin ma’aikatan Kano Blatter da Platini sun sake gurfana a kotu kan zargin cin hanci Wata majiya daga iyalansa ta ce tsohon Mataimakin Gwamnan ya rasu ne cikin daren ranar Lahadi. Cif Patrick Adaba shi ne ya yi wa Prince Abubakar Audu mataimakin gwamna bayan samun nasara a Zaɓen 1999. Tsohon Mataimakin Gwamnan wanda ya fito daga Ƙaramar Hukumar Adavi da ke Jihar Kogin, ƙani ne ga tsohon Darekta Janar na Hukumar Kula da Kafofin Watsa Labarai...
Kasar Qatar ta bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da ta sanya ido kan cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta bayyana cewa, Doha ta bukaci hukumar ta (IAEA) da ta sanya damar gudanar da bincike da ka’ida daga hukumar ta MDD, kan dukkanin cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. Jakadan dindindin na Qatar a Majalisar Dinkin Duniya, Jasem Yacoub al-Hammadi, ya bukaci gwamnatin Isra’ila da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta ce “Al-Hammadi ya jaddada bukatar kasashen duniya da cibiyoyinta su tabbatar da alkawurran da suka dauka a karkashin kudurorin kwamitin sulhu na MDD, da babban taron...
Tawagar matasan yan wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta mata (Flamingos) ta yi nasarar doke mai masaukin baƙi Bantwana ta Afrika ta Kudu da ci 3-1 a wasan farko na gasar cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2025 a filin wasa na Lucas Moripe, Pretoria a ranar Asabar, in ji jaridar Prompt News. Shakirat Moshood ce ta jefa wa Nijeriya ƙwallon farko a wasan cikin mintuna 20 kacal da farawa, Harmony Chidi ta ninka damar da Nijeriya ke da ita daga bugun fanareti mintuna biyar kafin a tafi hutun rabin lokaci. Cinikayyar ‘Yan Kwallon Da Aka Yi A Watan Janairu Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya Za Ta Ba Mata Damar Cimma Burikansu Afrika ta...
Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa duk wani rikici da tashin hankali a yankin to zai illata kowa. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre a yammacin waannan Lahadi, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa ad suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma sauran batutuwa na yankin da kuma na kasa da kasa. Shugaban na Iran ya kara da cewa, Haramtacciyar Kasar Isra’ila na neman yada karya dangane da batun ayyukan nukiliyar Iran a matsayin tushen rashin tsaro a yankin. Har ila yau ya jaddada cewa Iran ba ta taba...
Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da gidajen jama’a da aka wawushe da kuma wadanda aka kona. Wannan dai na zuwa ne bayan wani tashin hankali da ya barke a yammacin kasar ta Syria, inda aka ga wasu dauke da makamai masu alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin kasar ta Syria da kuma dakarun tsaron cikin gida a cikin faifan bidiyo suna aikata munanan laifukan yaki da suka hada da kisan fararen...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki. Sai dai a lokacin da waɗannan mutane suke samun rangwame, akwai waɗanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu. Sau da dama irin waɗannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za su saka a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin...